Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banda wacce tayi mana a
cikin
gari,yanzu mene ne abin yi?Lokacin
da Sarki
Ubaiyu yazo nan a jawabinsa sai Boka
Matawus
yaja dogon numfashi sannan yace
hakika duk
abinda ka fada gaskiya ne babu
kuskure a cikinsa
to amma tunda dai yanzu Sarila ta
aminta da duk
abinda na fada mata zamuyi amfani
da dutse daya
mu jefi tsuntsu biyu.Abinda nake nufi
shine zamu
iya cutar da Sarila mu bata wani abun
dazata sha
wanda zai zamo sanadin ajakinta ko
ya jirkitar da
hankalinta yadda zamu iya kwafe
wannan taswira
dake zane a gadon bayanta,shike nan
ta rasa
dukkan karfin jikinta dana sihirin
tsafinta,kuma ba
zasu sake dawowa gareta ba face ta
kone wannan
taswirar wacce aka kwafa Koda kuwa
takai guda
miliyan daya ma'ana ya zamana cewa
babu guda
daya irinta.Sa'adda Sarki Ubaiyu yaji
wannan batu
sai ya girgiza kai yace tabbas muna
da babbar
dama amma kuma hadarin dake
cikinta tamkar
mutum ya sayi ajalinsa ne da
kudinsa.Idan har
asirinmu ya tonu Sarila ta gane cewa
mun zuba
mata wani abu a cikin abin sha ko ci
domin cutar
da ita saita kashe kowa dake cikin
gidan sarautar
nan hatta iyalaina kuwa kuma ba'ama
san iya inda
barnar tata zata tsaya ba,watakila ma
ya zamo
sanadin da zata rushe gaba daya
gidajen dake
cikin birnin ta kone su kuma ta kashe
duk wani
abu mai rai dake cikinsa,ina mai baka
shawara da
idan akwai wata hanyar mafi saukin
hadari da
zamu cutar da Sarila to mu ajiye
wannan tunda dai
ance tsalle daya shi ke sawa a fada
rijiya.Koda jin
wannan batu sai Boka Matawus ya
kawo gwauron
numfashi ya ajiye sannan yace tabbas
kaima kayi
tunani mai kyau saboda haka zan
duba wannan
al'amari da idanun basira nan da
rabuwar dare
domin na yanke hukunci,amma a
halin yanzu ba
zamu dauki wani mataki ba akan
Sarila.Koda gama
fadin hakan sai Sarki
™Abubakar Haleefah Physicist™
yasa aka kirawo hadimansa suka
dauke shi suka
tafi dashi izuwa cikin turakarsa domin
ya cigaba
da jinyar raunin dake jikinsa.Shima
Boka Matawus
saiya ja sarkin yaki suka tafi izuwa
wani bangaren
daban na gidan sarautar inda aka
saba saukarsa
idan zaiyi yan kwanaki a cikin fada
yayin da wani
gagarumin abu ya taso.
*Al'amarin Sarila kuwa lokacin da
wadannan
kuyangi suka kamata suka tafi da ita
izuwa
masaukinta sai taga har aka shigar da
ita cikin
kewayen aka cire mata dukkan
makamanta na yaki
daga jikinta kuma aka cire dukkan
tufafin jikinta
jikin kuyangin bai daina tsuma ba
saboda tsoronta
da suke ji.Koda fahimtar hakan sai
Sarila ta dubi
shugabar wadannan kuyangin tace ku
kwantar da
hankalin ku na rantse da girman
iyayena ba zan
cutar da dayanku ba saboda yanzu ina
cikin
nishadi da farin ciki bisa sanin cewa
na sami
wanda zai taimake ni na gaggauta
cika burina na
kashe yar uwata Yazirina.Nan da kuka
shigo dani
ya tuno mini da irin rayuwar Ni'ima
dana tsinci
kaina a ciki a can tsibirin Jannatul
Duniya.Maza ku
shigar dani cikin bahon wankan nan
kona huce
gajiyar jikina.Koda Sarila tazo nan a
zancenta sai
kuyangin suka sami nutsuwa gami da
kwanciyar
hankali don haka nan da nan suka
shigar da Sarila
cikin wani katon bahon wanka na
zinare wanda ke
cike da ruwan dumi na wanka ga
furanni a cikinsa
gami da kanshin turaren miski dake
tashi.Nan take
suka fara yiwa Sarila wanka a hankali
ita kuwa ta
lumshe idanunta saboda jin dadin
dukin ruwan da
kuma wankan da akeyi mata.Bayan an
gama yi
mata wankan ne aka fito da ita daga
cikin bahon
tsirara aka shiga goge danshin dake
jikinta.Wohoho! !!Hakika babu wani
'da namiji da
zaiyi arba da Sarila a cikin wannan
yanayi batare
daya dimauce ba ya fita daga
haiyacinsa
ba,saboda irin tsananin kyawun surar
da Allah ya
bata,abin yafi gaban kwatance sai
abinda idanu
suka gani kawai,saidai ku wannan
kyawu nata na
banza ne domin kyan dan maciji ne
tunda bata da
imani kuma bata da tausayi ko
kadan.Sarila bata
san wani abu waishi sabo ba domi ta
mayar da ran
dan adam tamkar na kiyashi.Bayan an
gama goge
danshin jikin Sarila sai aka jata izuwa
wajen
kewayen aka shigar da ita cikin wani
kasaitaccen
dakin barci aka tsayar da ita a gaban
wani katon
madubi aka shiga shafe jikinta da mai
sannan aka
sanya mata wata farar doguwar riga
irinta
sarakai.Gashin kanta kuwa bayan an
tsefe shi an
busar da danshin dake jikinsa sai aka
shafe shi ya
rinka kyalli sannan aka tattare shi aka
daure shi ya
zubo gadon bayanta har izuwa kan
mazaunanta
masu tudu.Koda Sarila ta dubi kanta a
cikin
madubin taga irin kyawun da Allah ya
bata da
yadda tayi matukar kyau sakamakon
wannan ado
da akayi mata saita kama murmushi
nan take taji
babu abinda takeso sama data
gaggauta cika
burinta na mallakar wannan dukiya ta
Boka
Salmara domin ta zamo SARAUNIYAR
DUNIYA!!!A
sannan ne zata nemi namijin daya
dace da ita ta
aura domin ya zamo abokin
rayuwarta,to waishin
wanene wannan 'da namiji wanda zai
dace da
zabinta?Koda Sarila tayiwa kanta
wannan tambaya
a cikin zuciyarta lokacin data kurawa
fuskarta
idanu a cikin wannan madubi sai
kawai hoton
fuskar Mujahid ya fado a kan
Madubin ta kura
masa idanu tana mai cewa a cikin
ranta tabbas
wannan shine saurayin daya dace dani
domin yana
da kyau da sura irin wacce zuciyata
keso.Koda
gama aiyana hakan sai zuciyar Sarila
ta buga da
karfi tace a ranta lallai yanzu ne ta
gane cewa ashe
kamuwa tayi da son Mujahid shi yasa
ta kasa
kashe shi alhalin kuma gashi tana
ganin cewa yana
taimakon abokiyar gabarta.Lallai kuwa
idan ta daka
ta wannan SOYAYYA zata fuskanci
babbar matsala
wajen samun biyan bukatarta,ya zama
dole tasan
hanyar da zatabi ta gaggauta kashe
Yazirina ta
rabata da wadannan taswirori guda
biyu tun kafin
soyayyarta da Mujahid ta kara zurfi
akai munzalin
da zata cutar da kanta,yanzu dai zata
zuba ido
taga iyakar taimakon da wannan boka
zaiyi mata
idan ta fuskanci akwai karya da
yaudara a cikin
lamarinsa kawai zata kashe shi ne ta
kashe sarkin
nasa kuma ta cigaba da farautar
Yazirina a cikin
birnin koda kuwa yin hakan zai janyo
sanadin
mutuwar gaba dayan mutanen kasar
gami da
konewar komai dake bisa doron kasar
birnin.Sarila
na cikin yin wannan tunanin zuci ne
kuyangin suka
janyeta daga gaban madubin suka
fitar da ita falo
Inda Sarila taga wani dogon tebur
mai tsawo kamu
dari,a karkashinsa dama da hagu
akwai kujeru
guda hamsin hamsin bisa teburin an
zuba farantai
cike da abinci iri iri sama da kala
dari.Ruwan
inibi,ruwan tatattun sauran yayan
itatuwa kuwa a
cikin tambuka sun kai kamar kala
ashirin.Koda
Sarila taga an shirya wannan daula
duk saboda ita
sai tasha jinin jikinta tayi zargin cewa
lallai akwai
wani abu da ake shirin kulla mata na
cutarwa.Koda
aka zaunar da Sarila akan wannan
tebur aka bude
mata kwanukan abincin domin ta zabi
wanda take
sha'awar ci a zuba mata sai tayi
murmushi ta dubi
shugabar kuyangin tace inason kisa
yaranki su
debi loma dai dai daga cikin dukkanin
wannan
abincin su ci yanzu take a gaban
idanuna har sai
bayan cikar sa'a guda in banga wani
abu ya
samesu ba sanna zan iya yarda da
wannan abinci
naci.Koda jin wannan umarnin sai
shugabar
kuyangin tayi murmusgi tace ya
shugabata ai duk
wannan mai sauki ne,nan take kuwa
shugabar
kuyangin ta umarci kuyangin dasu
aikata yadda
Sarila keso sukabi umarnin cikin
gaggawa,saida
sa'a gudan ta cika Sarila taga babu
abinda ya sami
kuyancin walau na cuta kona jirkitar
hankali
sannan taci wannan abincin ta cika
cikinta ta
koshi.Koda ta kammala cin abincinta
sai ta tafi
izuwa dakin barci tana shiga ta turo
kofar dakin ta
kulleta sannan
™Abubakar Haleefah Physicist™
ta fada kan gado ta kama shara barci
abinta tamkar
a cikin turakarta take dake can tsibirin
Jannatul
Duniya.
*A can gidan Matsafiya Muznaira
kuwa lokacin da
dare ya raba,Yazirina na kwance a
cikin dakin barci
shi kuwa Mujahid a falon dakin ya
kwanta bisa
kilishi yana ta faman rusar barci
abinsa.Ashe dai
ita Yazirina idanunta biyu ko rintsawa
batayi ba
don haka saita mike zaune daga kan
gadon ta
karanta wadansu dalasimai na tsafi
sannan ta fito
falon ta tashi Mujahid daga barci.A
firgice Mujahid
ya mike zaune firgigit ya dubeta cikin
tsananin
kaduwa yace lafiya me ke faruwa ne?
Yazirina ta
dubeshi cikin bata rai tace tashi
zakayi muje mu
sace wannan Kambun Sihiri dake
hannun Muznaira
yanzu mu sulale mu bar gidannan ko
ta halin kaka.
Toohfahh!!!Su Yazirina zasu sace
Kambun Sihiri Bari dai in tsaya nan in
buya kar su ballo mini ruwa dan
nasan za'a gwabza gumurzu.Mu bar gidan nan ko ta halin
kaka.Koda jin wannan
batu sai hankalin Mujahid ya
dugunzuma cikin
alamun matukar firgita yace haba ya
shugabata ta
yaya kike zaton cewa zamu iya zuwa
har cikin
turakar Muznaira mu sace wannan
kambun sihiri
alhalin duk abinda muke takama
dashi ta
fimu.Koda jin wannan batu sai
Yazirina ta dakawa
Mujahid harara ta dubeshi cikin
karamar murya
tamkar rada tace amma dai ka bani
mamaki da
haushi tace,yanzu kai baka ji kunya
ba kake fada
mini haka?Shin ka manta ne cewa
kaine shugaban
dukkan barayin wannan nahiya,kai fa
saboda
shahararka da gawurtarka bakawa
karamin attajiri
sata sai masu mulki da hamshakan
attajiran da
suka tumbatsa.Gaba daya manyan
sarakunan nan
guda hudu babu wanda bakaje har
cikin
masarautarsa ba kayi masa sata,akan
wane dalili
yanzu zaka yi shakkar karamar
bokanya wacce
bata kai su ba a komai?Maza ka tashi
mu nemi
inda turakarta take yanzun nan ku
kuma nasa
takobina na sare hannayenka da
kafafunka tunda
baka da sauran amfani a wajena.Koda
jin wannan
batu sai Mujahid ya mike zumbur da
sauri yace ya
na iya da ciwon ido dole sai hakuri
muje kawai
amma dai kece zakiyi mini
jagora.Yazirna tace
babu matsala.Koda gama fadin hakan
saita juya ta
nufi kofar fita cikin hanzari Mujahid
ya bita har
yana tuntube,kai tsaye Yazirina ta fito
daga cikin
dakin da suke ta nufi cikin gidan kai
tsaye ba tare
da tayi wani dube dube ba tamkar a
cikin nata
gidan take,shi kuwa Mujahid saiya
cigaba da binta
a baya a tsorace yana waigen bayansa
tamkar ace
kyat ya fita da gudu.Ta cikin fadar
Muznaira
Yazirina da Mujahid suka ratso bayan
sun wuce
kofofi goma sha daya kuma ko ina a
tsaye masu
gadi ne,duk inda sukazo da an
tambaye su inda
zasuje sai yazirina tace yar uwata
Muznaira nake
son gani.Ko musu ba'ayi musu ake
bude musu
kofar su shige,da suka iso kofa ta sha
biyu ne
sukayi kicibus da wani narkeken aljani
mai matukar
kwarjini da sura irin ta manyan
sadaukai,Aljani n ya
dubi Yazirina fuskarsa a murtuke yace
ai maigirma
Muznaira bata gaya mini cewa zaku
kawo mata
ziyara ba a matsayina na sarkin
gida,don haka
babu wani dalili da zaisa na barku ku
wuce.Koda
jin wnnan batu sai Yazirina tace ai
kuwa babu wani
mahaluki wanda ya isa ya hanani
ganin yar uwata
tunda dai ubanmu daya,idan kaga ban
wuce cikin
wannan kofa ba na isa turakarta to
saidai idan
bana numfashi a doron kasa.Koda jin
wannan batu
sai Aljanin yayi dan guntun murmushi
irin na
manyan jarumai masu takama da
kansa sannan
yace ai kuwa idan kika ga kema kin
wuce ta cikin
wannan kofa saidai idan na zama
gawa domin ina
kan aiki na ne na tabbatar da
tsaro,idan kina ganin
cewa zaki iya kawar dani ki shige to
sai mu RABA
GARDAMA.Koda gama fadin hakan sai
Aljanin ya
zare wata sharbebiyar takobi dake
rataye a
bayansa sannan ya bude ya dubi
sauran yaran
nasa yayi musu inkiyar su gusa su
basu wuri.Nan
take kuwa dakarun suka ja da baya ba
tare da
shakkar komai ba kuwa sai Yazirina ta
zare tata
takobin itama ta bude tana mai gyara
tsayuwarta.Koda ganin haka sai tsoro
ya kama
Mujahid yasha gaban Yazirina yace
saboda me
zakiyi tunanin yakar dakarun gidan
nan alhalin so
muke mu gama komai cikin sirri da
sa'a.Maimakon Yazirina tace dashi
wani abu sai
tasa hannunta ta bangaje shi yaje ya
buga kai da
bango ya fadi kasa sumamme ko
kallonsa batayi
ba,saita fuskanci wannan Aljani wato
shugaban
dakarun gidan tace lallai kuwa yau
saidai uwarka ta
haifi wani domin babu abinda zai
hanani wucewa
ta cikin wannan kofa.Koda jin wannan
batu sai
Aljanin ya tuntsire da dariya yace
suna nan Lafwas
Bin Zabbar yau shekarata dari da
ashirin kenan ina
aikin tsaro a gidajen manyan bokaye
na
duniya.Nayi aiki a gidajen Bokaye
saba'in da uku
kuma a tarihin wannan aiki nawa ba a
taba zuwa
an shiga inda nake tsaro ba walau da
KARFIN
DAMTSE kona Sihiri,tabbas yau kin
taba tsuliyar
dodo don haka zaki gane
kuskurenki.Koda gama
fadin hakan sai Lafwas ya dako tsalle
a sama yana
mai daga takobinsa sama ya kawowa
Yazirina
mugun sara a wuya da nufin ya cisge
mata
kai.Cikin bakin nama Yazirina ta goce
takobin tasa
ta sari dirkar gini take dirkar ta rabe
gida biyu ta
fadi kasa amma duk da haka rufin
ginin saman bai
fado ba kasa sakamakon cewa
dirkokin suna da
yawa.Nanfa Yazirina ta taso da
dukkan karfinta
suka kacame da masifaffen yaki na
ban al'ajabi da
ban tsoro wanda ya jefa sauran
dakarun cikin
tsananin mamaki saboda a iya
zamansu a cikin
wannan gida basu taba ganin wani
mahaluki mai
tsaurin ido daya taba tarar Aljani
Lafwas da yaki ba
sai Yazirina kuma gashi ta kasance
bil'adama kuna
'ya mace ba komai ne yasa wadannan
dakarun
aljanun sukayi mamakin Yazirina ba
face sanin
cewa a cikin jaruman Aljanu na
duniya a yanzu
babu mai karfin Damtsen Lafwas gami
da iya
yakinsa.Koda aikin tsaro babu mai iya
daukarsa
face wanda yake da dimbin dukiya
mai tsananin
yawangaske,sabo da a duk karshen
wata ana
biyansa albashin dabai gaza dinare
miliyan uku
ba.Wani lokacin kuma koda Boka
bashi da kudin
da zai iya biyansa yana dubwa ya
gani ko wannan
boka yana da wani babban aiki a
gabansa wanda
idan ya kammaka shi zai iya samun
babbar
daukaka ko kuma wata gagarumar
dukiya sai suyi
hakkinsa na iya watannin dayayi yana
aiki a biya
shi,tabbas Aljani Lafwas ya kasance
mai rike
alkawari da amana don haka komai
tsanani baya
yarda a sami sabani.Saida Yazirina da
Aljani
Lafwas suka sha tsanainin zafin
nama,juriya da
bajinta ta gaban kwatance amma
dayansu bai sami
nasarar koda lakutar jikin daya ba
saboda iya yakin
nasu yazo iri daya tamkar malamin
daya koya
musu yaki daya ne.Abinda
™Abubakar Haleefah Physicist™
ya daurewa Aljani Lafwas kai shine
hatta zafin
namansa yazo daya alhalin shi yana
matsayin
Aljan ita kuma bil'adama.Bisa dole
duk su biyun
suka ja da baya sukayi cirko cirko
suna haki da
kallon juna kamar zakaru.Duk tsawon
wannan
lokaci da ake fafatawa Bokanya
Muznaira dake can
cikin turakarta tana ta fama shara
barci bata ma
san abinda akeyi ba duk da cewa
sakamakon
artabun da Lafwas da Yazirina keyi
wasu garuka na
gidan sun rurrushe kuma kayan alatu
dayawa sun
ragargaje.Shima Mujahid tunda yayi
wannan dogon
suma bai fardado ba.Bayan anyi kallo
tsakanin
Aljani Lafwas da Yazirina sai Lafwas
ya mayar da
takobinsa cikin kufe ya dubi Yazirina
a fusace a
lokacin da har wani tiriri na takaici ne
ke fitowa
daga cikin bakinsa tace tunda iya
yakinmu yazo
daya ai sai mu jarraba karfin damtse
mu gani kafin
ta kaimu gayin amfani da karfin
sihirin tsafi,idai
nasani cewa ruwa ba sa'an kwando
bane.Koda
gama fadin hakan sai Sadauki Lafwas
ya dunkule
tafin hannayensa biyu take kwanjin
jikinsa ya
kumburo,jijiyoy insa suka kumbura
yana mai gyara
tsayuwarsa kuma yana kada fuka
fukansa guda
biyu.In badon fukafukan Aljani
Lafwas ba da kuma
kahon dake kansa guda biyu gami da
manyan
kunnuwansa guda biyu da kuma
faratan
hannayensa dana kafafunsa da dauka
za'ayi
mutum ne shi ba aljan ba saboda
komai nasa irin
na bil'dama ne kuma ya kansace
kyakkyawa a
cikin jinsin Aljanu.Ita kanta Yazirina
da taga irin
murdewar Aljani Lafwas gami da tarin
kwanjinsa
saida ta dan tsorata ta tabbatar da
cewa ya cika
zarto kuma jarumin maza domin
alamar karfi tana
ga mai kiba amma a rayuwarta tada
da kuma irin
gwagwarmayar data sha gami da
fafatawa da
miliyoyin aljanu sai taji ko kadan bata
shakkar
komai don haka sai itama ta dunkule
hannayenta
biyu suka rugo da gudu izuwa kan
juna suka
kacame da sabon masifaffen fadan
hannu ya
zamana cewa suna kaiwa junansu
naushi da bugu
da hannu da kafa.Ana fara wannan
gumurzu ne
mamaki ya kama Aljani Lafwas bisa
ganin irin
tsananin karfin damtsen Yazirina da
kuma juriyarta
domin duk irin uban naushin da yake
gabza mata
a sassan jikinta tana iya shanyesu
kuma ta maida
masa martani ya zamana cewa suna
hadawa
kansu jini da majina.Fara wannan
gumurzu keda
wuya labari yasha bambam domin a
lokacin ne
hankalin sauran dakarun dake wajen
ya
DUGUNZUMA ainun suka firgice suka
kama boye
boye saboda masifar ta fara
shafarsu.Saboda duk
sa'adda Aljani Lafwas ko Yazirina suka
kawo
naushi dayansu ya goce duk Aljanin
da aka samu
saidai kaga ya baje kasa
sumamme.Adaidai
wannan lokaci ne Mujahid ya farfado
daga dogon
suman da yayi,koda yaga ana yin
wannan
masifaffen yaki yaga saman rufin
gidanma ya fara
runguzowa kasa yana danne Aljanun
suna tsira da
kyar sai shima ya ruga izuwa
karkashin wata
rusasshiyar dirkar gini ya buya.Karar
rugujewar
gidan ce tasa matsafiya Muznaira ta
farka daga
bacci a dimauce,koda ta jiyo sautin
rushewar wani
bangare na gidan nata sai ta sauko
daga kan
gadonta ta debi makamanta tayi
girgiza ta bace
bat,bata baiyana a ko ina ba sai a can
inda ake
gumurzun.Koda taga cewa tsakanin
Aljani Lafwas
da Yazirina akeyin wannan gumurzu
kuma alokacin
duk su biyun sun dako tsalle sama
tamkar daga
cikin baka aka cillosu da nufin su
yiwa kawunansu
gware sai itama Muznaira ta daka
tsalle sama da
nufin ta shiga tsakiyarsu ta raba
fadan.Koda
Yazirina ta kyallara ido taga wannan
Kambun Sihiri
a hannun Muznaira sai ta shammaceta
ta sunkui
da kanta kasa,ai kuwa sai kan Aljani
Lafwas ya
gwaru dana matsafiya Muznaira,take
Muznaira ta
dimauce kuma ta fita haiyacinta
sakamakon
tsananin zafi da zogin da yaji don
hakar saida taga
taurarin wuya a idanunta.Damar da
Yazirina ta
samu kenan ta cisge wannan kambun
sihiri daga
jikin hannun Muznaira ta diro kasa
daidai inda
Mujahid uake tasa hannayenta biyu ta
sure shi
sukayi sama tamkar ta kasance
tsuntsuwa mai
fukafukai,kawai sai ta naushi nurin
sama gidan ya
burma suka fice ta cikinsa suka luluka
a cikin
gajimare suka bace bat tamkar basu
taba wanzuwa
ba.Muznaira da Aljani Lafwas suka
diro kasa suna
sosa fuskokinsu wadanda ke yoyon
jini ta cikin
hanci da baki,koda suka watstsake
suka dawo
cikin hayyacinsu Muznaira ta dubi
sama da
kasa,gabas da yamma kudu da arewa
bataga
Yazirina da Mujahid ba sai ta kurma
uban ihu mai
tsananin firgitarwa ta dubi Aljani
Lafwas tana mai
daka masa tsawa tana mai cewa sun
sace mini
kambuna maza ka bisu ka kwato shi
kuma lallai ka
kawo mini Yazirina a raye tare da
wadannan
taswirori guda biyu dake
hannunta.Idan har ka
sami wannan nasara nayi maka
alkawari idan na
debo dukiyar mahaifina dake can
kogon Taskar
Ajali kaine zaka zama wazirina a
yayin dana zamo
SARAUNIYAR DUNIYA.Koda jin
wannan batu sai
Aljani Lafwas ya daki kasa da tafin
hannunsa yayi
sama a cikin tsananin gudu tamkar
tafiyar
tauraruwa mai wutsiya ya luluka a
cikin gajimare.
*Acan gidan sarautar Sarki Ubaiyu
kuwa kashe gari
da sassafe Sarila nata fama shara
bacci akan gado
tamkar tana cikin tsiribirin Jannatul
Duniya sai taji
ana tashinta daga bacci tana bude
idanunta tayi
arba da shugabar wadannan kuyangi
tsaye a kanta
kawai sai ta dubeta tace ya shugabata
ga ruwan
wanka can yana jiranki kuma an
shirya miki abinci
Buda baki,mai girma Boka Matawus
yace in gaya
miki akwai labari mai dadi don haka
yana jiranki a
fada.Koda jin wannan batu sai Sarila
ta sauko da
sauri daga kan gado ta ruga izuwa
kewaye kafin
kuyangin da zasuyi mata wanka su
shigo tuni ta
kwabe kayanta ta fada cikin bahon ta
fara yiwa
kanta wanka don haka da kuyangin
suka shigo
karasa mata sukayi.Ana gama yi mata
wankan ta
dauki makamanta na yaki ta
™Abubakar Haleefah Physicist™
daurasu a jikinta bayan ta mayar da
asalin kayan
da tazo dasu gidan,ba ta yarda an
sanya mata
wadansu tufafin ba kuma bata tsaya
anyi mata
wani ado ba amma abinka da
kyakkyawa sai gashi
kamar ma tayi kwalliyar,ko tsayawa
yin buda bakin
batayi ba ta durfafi fada.Tana isa
fadar kuwa ta iske
Boka Matawus a zaune tare da sarkin
yaki da
kuma dakaru dubu daya a
tsaitsaye.Koda Boka
Matawus ya hango Sarila ta nufo su
sai ya mike
tsaye ya tarbeta yana mai risina mata
kuma ya
gaisheta cikin girmamawa sannan ya
dubeta cikin
nutsuwa yace,ya shugabata ina mai
sanar dake
cewa a halin yanzu nasan inda
Yazirina take don
haka ina so na kai ki wajen domin ki
cika burinki
na karbar wadannan taswirori guda
biyu dake
hannunta amma bisa sharadi guda
sharadin kuwa
shine inason ki daukar mini alkawarin
cewa nan
birnin Yamein shine zai zama babban
birninki na
mulkin duniya kuma ni da sarkina
zamu zamo
manyan fadawanki.Ina mai tabbatar
miki da cewa
da zarar mun isa inda Yazirina take ni
zanyi miki
maganin wannan yaro dan baiwa
wato Mujahid
saboda shi kadai ne zai iya tarwatsa
miki dukkan
shirinki ya tserar da Yazirina daga
hannunki.Koda
jin wannan batu sai Sarila tayi shiru
tana tunani da
nazarin al'amarin har izuwa tsawon
yan dakiku
daga can sai ta dago kai ta dubi Boka
Matawus
tace na yarda da wannan sharadi naka
kuma na
rantse da darajar iyayena zan zamo
mai cika
alkawari a gareka amma kasan cewa
idan muka isa
inda Yazirina take ka kasa yi mini
maganin
Mujahid saina kasheka na kashe Sarki
Ubaiyu
sannan na baje birnin Yamein yadda
har abada ko
a tarihi ba za'a sake tunowa da ita
ba.Koda jin
wannan batu sai hantar cikin Boka
Matawus ta
kada yaji kamar yace ya janye
wannan yarjejeniyar
amma daya tuna cewa yana zuwa da
wani abu
akasin hakan rai zai iya baci sai ya
amsa cewa
shima ya amince da nata
sharadin.Nan take suka
dunguma suka fice daga cikin fadar
suka iso
babban fili na gidan sarautar inda
suka iske Sarki
Ubaiyu tare da dukkanin fadawansa
da sauran
mutanen gari a tsaitsaye sunyi jugum
jugum Cikin
yanayi na jimami da fargaba da
tsananin
damuwa.Da isowarsu sai Boka
Matawus ya iso
gaban sarki Ubaiyu ya risina ya
gaisheshi a
wannan lokaci hannun sarki Ubaiyu a
sakale yake
kuma a daure da yanki sakamakon
raunin da Sarila
tayi masa.Nan take Boka Matawus ya
kwashe
labarin duk abinda ya faru tsakaninsu
ya zaiyane
masa.Koda sarki Ubaiyu da jama'arsa
sukaji
sharadin da Sarila ta shimfida sai
hankalonsa ya
dugunzuma ainun fiye da ko
yaushe.Ba tare da
bata lokaci ba aka kawo dawakai
Boka
Matawus,jaruma Sarila da dakaru
dubu suka hau
suka fice daga cikin gidan
sarautar.Fitars u keda
wuya sai sarki Ubaiyu ya dubi gaba
dayan jama'ar
tasa cikin alamun karayar zuciya yace
to kunji dai
sharadin da Sarila ta gindaya don
haka mecece
shawarku da kuka yanke?Koda jin
wannan tambaya
sai gaba dayan yan majalisar suka
kama kace nace
wasu sukace kawai ayi hijira gaba
daya abar birnin
ya zamana fanko,wadansu kuwa sai
sukace a bari
aga dawowar Boka Matawus tunda
ana da yakinin
cewa duk bala'i ma da zai biyo baya
shi zai iya
guduwa ya tsira daga sharrin
Sarila,haka dai akayi
ta kace nace aka rasa hukuncin daya
dace a yanke.
*Al'amarin Yazirina da Mujahid kuwa
lokacin da
suka luluka a cikin gajimare suka bace
bat basu
sake baiyana a ko ina ba sai a tsakiyar
wani daji
mai ni'ima wanda ke dauke da
korama,bishiyoy i da
yayan itatuwa iri iri.Koda Mujahid ya
bude
idanunsa yaga ni'imomin dake cikin
wannan daji
sai ya ruga izuwa cikin wata korama
yana mai cire
rigarsa ya fada ciki ya kama wanka.Ita
kuwa
Yazirina sai ta dauko wannan kambun
sihiri na
Muznaira daga cikin aljihunta ta kura
masa
idanu.Take taga hoton Sarila bisa doki
tare dasu
boka Matawus a sukwane sun durfafo
wannan daji
da suke ciki kuma dawakan nasu wani
irin gudu
suke yi mai tsananin karfi na sihiri
wanda suna iya
shafe tafiyar sa'a guda cikin dakika
goma.Koda
ganin wannan Al'amari sai hankalin
Yazirina ya
dugunzuma ainun ta mike tsaye
zumbur da nufin
ta ruga izuwa inda Mujahid yake
domin ta sanar
dashi abinda ke shirin
afkuwa.Kwatsam sai taga
Aljani Lafwas ya diro daga sama
tsulum ya dira a
gabanta.Saboda nauyinsa saida kasar
dajin gaba
daya tayi girgiza har wajen daya dira
ya loba
kamat zai rufta ciki.Babu shiri Yazirina
taja da
baya kadan ta zare takobinta kuma
Lafwas saiya
zare takobinsa ya nuna yazirina da ita
yace...:
Ya nuna Yazirina da ita yace,kina
zaton cewa akwai
inda zaki iya zuwa ne ki tsare mini a
cikin wannan
duniya,ina mai shawartarki daki dauko
wadannan
taswirori guda biyu dake wajenki ki
bani na kaiwa
uwargida Muznaira wato yar uwarki
idan har
kinason ki tsira da rayuwarki,in ba
haka ba kuwa
zan kasheki a banza.Duk wannan
bayani da Aljani
Lafwas ke fadi Muhajid dake cikin
korama ya tsaya
cak yana sauraro don haka lokacin da
yaji batun
Aljani Lafwas na karshe sai ya tari
numfashinsa
yace,Kai Lafwas kayi babban kuskure
har da kake
tunanin cewa zaka iya raba Yazirina
da wadannan
Taswirori guda biyu don kaima ina
mai baka
shawara da ka cire hannunka daga
cikin wannan
al'amari domin yafi karfinka.Har
Aljani Lafwas ya
bude baki zai maidawa Mujahid
martani sai
Yazirina ta sake tarar numfashinsa
tace a yanzu
haka ga Sarila anan ta taho nan kuma
nan da cikar
rabin sa'a zata iso tare da Boka
Matawus na birnin
Yamein da dakarunsa guda dubu
daya.Shin yanzu
zamu cigaba da yaki ne nidakai kafin
su iso ko
kuwa zamu jira ne su iso mu hada
karfi da karfe
mu yaki Sarila mu kasheta domin mu
kwafe
taswira ta uku sannan ka kashe ni ka
hada
taswirori guda ukun ka kaiwa
uwargidan naka?
Koda jin wannan tambaya sai Aljani
Matawus ya
kama duru duru ya rasa abinda zaiyi
wanda zai
fishshe shi haka dai suka yi cirko cirko
su
duka.Koda Mujahid yaga aljani Lafwas
ya kasa
yanke hukunci sai ya dubi Yazirina
yace kizo kawai
mu gudu mubar wajen nan domin
idan muka bari
Sarila tazo nan ta riske mu tamu ta
kare domin
wannan karon ba zamu iya tsira daga
sharrinta ba
saboda nasan cewa Boka Matawus zai
iya yin
maganina kuma kin sani cewa nine
kadai wanda
zai iya tserar dake.Koda jin wannan
batu sai
Yazirina ta dubi Mujahid cikin alamun
tsananin
mamaki tace Ashe dai kai ne bakon
jarumin da
aka tabbatar mini da cewa zaka iya
kubutar dani
daga sharrin Sarila,shin kai ne dan
baiwa mai sa'a
da rabo bisa duk abinda yasa a
gabansa?Koda jin
wannan tambaya sai Mujahid yace
tabbas nine
amma dai ki dauki shawarata indai
kinason ki tsira
da rauwarki.Yaziri na tace ni ban
damu da rayuwata
ba muddin gudun banza zanyi wanda
babu kubuta
kuma babu tabbacin tsira.Kai meye
yasa bazaka
gudu ba tunda kana son ka tsira da
rayuwarka?
Koda jin wannan batu sai Mujahid ya
risina yace
abinda yasa banzan gudu na barki ba
shine tun a
ranar farko dana fara haduwa dake
duk da cewa
ina matukar tsoranki naji kuma na
kuma da
tsananin SONKI irin son da nake jin
kamar zan iya
salwantar da rayuwata domin
taki.Saboda haka ni
yanzu na zabi na mutu tare dake anan
wurin idan
kuma zamu tsira to mu tsira tare.Koda
jin wannan
batu sai Yazirina ta kamu da tsananin
mamaki
kuma nan take taji ta kamu da
tsananin SON
Mujahid bata san sa'adda taji kwallar
farin ciki ta
cika mata idanu ba,saboda Mujahid
ne saurayi na
farko a duniya wanda ya taba furta
mata KALMAR
SO gaba da gaba.Kafin Yazirina ta
budi baki tace
da Mujahid wani abu sai kawai
Mujahid yaga wata
igiyar tsafi mai kaurin gaske ta
kanannade shi daga
kasan kafafuwansa har izuwa kan
kirjinsa ta
daureshi tamau yadda ko motsin kirki
ba zai iya
ba,kawai sai jiyo sukuwar dawakai
sukayi a
bayansu suna waigawa sukayi Arba da
Sarila,Boka
Matawus da dakaru dubu a sukwane
sun durfafo
kansu kuma tazarar dake tsakaninsu
bata wuce
taku ashirin ba.Koda ganin hakan sai
Aljani Lafwas
ya dubi Jaruma Yazirina yace a yanzu
mun zama
abokai kuma yan uwan juna don haka
inason mu
hada karfi da karfe ni dake mu yaki
Sarila kada ki
damu da Boka Matawus da sauran
dakarunsa
inada maganinsu.Masoy inki dai
Mujahid bansan
yadda zanyi na iya kwance igiyar data
daureshi ba
saidai bayan wannan yaki idan mun
tsira da
rayuwarmu sai mu nemi mafita.Aljani
Lafwas na
gama fadin hakan sai shida Yazirina
suka daka
tsalle sama suka kaiwa Sarila mugun
hari a lokacin
da take bisa dokinta,koda ta hango su
a sama sun
taho kanta sai ita ma ta daka tsalle
sama daga kan
dokinta cikin matukar zafin nama ta
doki kirazansu
suka fado kasa a galabaice suna sosa
kirazansu
sakamakon mugun zafin da sukaji
amma sai suka
mike tsaye zumbur a tare suka rike
takubbansu da
hannayensu biyu suna masu gyara
tsayuwarsu.Adai dai wannan lokaci ne
ta dubi Aljani
Lafwas da Yazirina tayi musu wani
dan guntun
murmushi sannan tace yanzu ku a
tunaninku kuna
ganin cewa zaku iya dani ne?To ai
shike nan masu
iya magana sun ce ba'a kwacewa yaro
goruba don
haka sai ya gwaguya yaci iya cikinsa
duk da cewa
bashi da hakori kuma indai babu kasa
anan ake
gardamar kokawa.Tabbas yanzun nan
zan gama
daku na cika burina.Kafin Aljani
Lafwas ko Yazirina
daya daga cikinsu yace wani abu tuni
Sarila ta zare
takobinta ta daka tsalle sama ta dira a
tsakiyarsu
sun ruguntsume da azababben
yaki,nanfa ita kadai
ta zame musu alakakai ta kuntatasu
ya zamana
cewa da kyar ma suke iya kare hare
harenta amma
basa iya mai da martani.Hakika mai
karfi sai Allah
ya isa kuma duk wanda ya riga kwana
dole ne ya
riga ka tashi,ana fara wannan
gumurzu Yazirina da
Aljani Lafwas suka raina kanus suka
tabbatar da
cewa Sarila tafisu karfin damtse gami
da iya yaki
nesa ba kusa ba domin bambancin a
bayyane
yake.Shi kuwa Matawus sai ya tafi
izuwa inda
Mujahid ke tsaye a daure cikin igiyar
tsafi ya dube
shi ya bushe da dariya sannan yace
rana da yawa
ta barawo rana daya tak ta mai
kaya,yau shekara
biyar kenan maigidanka Boka Kausi
yana turoka
har gidana kana yi mini sata na kasa
kamaka
amma yau gashi ka fada tarkona a
saukake.
WAYE ZAI SAMI NASARAR A
WANNAN BAKIN
GUMURZUN DA AKEYI TSAKANIN
SARILA DA SU
YAZIRINA?
INA LABARIN MANYAN
SARAKUNAN DUNIYA KUMA WANE
MATAKI SUKA
DAUKA AKAN YAZIRINA DA SARILA?
YAYA
SOYAYYAR YAZIRINA DA MUJAHID
ZATA
KASANCE?
SHIN MUJAHID ZAI TSIRA DAGA
SHARRIN BOKA
MATAWUS?
YAUSHE ZA'A TAFI KOGON TASKAR
AJAKI KUMA
WAYE ZAI IYA DEBO WANNAN
DUKIYA TA
MARIGAYI BOKA SALMARA? INA
LABARIN BASMA
MAHAIFIYAR YAZIRINA?
Mu hadu A "Taskar Ajali" Littafi na
Hudu don jin
cigaban wannan labari.TASKAR AJALI
Littafi na Uku
Na Abdulaziz sani M gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu [email protected]
TASKAR AJALI
Littafi na Uku
Na Abdulaziz sani M gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya

Please Login or Register in order to submit comment