Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a zancensa
sai gaba dayan jama ar dake cikin
fadar suka kamu da tsananin mamaki
kuma
hankalin jamaar gari ya dugunzuma
bisa
jin cewar akwai makiyansu a cikinsu
basu sani ba.
Take a wajan aka rinka kallon kallo
tsakanin baki da yan gari koda ganin
abinda
ke faruwa sai sarki ya daga hannu aka
yi tsita a lokacin da fadar ta cika da
hayaniya
sannan sarki yace yaku jama ata ku
kwantar da hankalinku kuyi sani cewar
na sanya gawurtaccen tsaro a cikin
garin nan don haka da izinin Allah babu
wani makiya
ida zai iya cutar da waninmu ina so ku
sani cewa
ba aikin ku bane ku binciko makiyan
dake cikinmu domin zaku iya
zargi wasu daga cikin bakinmu
wadanda basu da laifin
komai idan ma kunga wani kuna
zarginsa sai dai kuzo ku
sanar da mu mu koma mu dauki mataki
a kansa.
Duk wani bako da yake son ganawa
dani yanzu yaje ya sameni a can dakin
gani
na wajan fada duk wanda yasan akwai
wani alkawari a tsakanina dashi ya
tabbatar
da cewar shi ma yaje can dakin gani ya
jirani
koda sarki yazo nan a zancensa sai
hankalin Sarki Damnashi ya tashi ainun
saboda
ya gano cewa wannan wani mataki ne a
ka dauko da za a iya tona asirinsa
kawai saiya dubi shugaban dakarunsa
yace
dashi maza kaje can dakin gani ka
wakilceni idan wannan sarki ya
tambayeni kace dashi bani da lafiya ne
shi
yasa ban fito ba
sarki damnashi ya sake duban wani
hadimin nasa mai suna
KAIZUR yace kai kuma kayi
sauri ka koma can masaukinmu tare da
sauran jama armu ka yi irin shigar da
nayi
ta bad da kama don ni yanzu akwai
abinda zanje na
gabatar a wani wurin daban
koda gama fadin hakan sai sarki
Damnashi ya kutsa cikin jamar dake
fada ya fita daga cikin fadar ya bace
bat!
Bayan sarki ya fito daga fada sai ya
kirawo jarumi Darusi da gimbiya
suzaina
yayi musu kwatancen gidan Attajiri
damnashi da kuma kwatancen
kamanninsa yace
su yi maza suje can masaukin nasa
suyi bincike a kansa sosai domin yana
zarginsa
nan take kuwa suzaina da darusi suka
hau dawakai suka zabureshi izuwa
hanyar
da zata kaisu can bayan gari inda gidan
Attajiri Damnashi yake ashe
sarila da yazirina na labe a can gefe
daya suna kallon
abindake faruwa
koda sukaga su darusi sun tafi sai
suma sukayi bad da kama sukayi shiga
irin ta
'yan kasuwar garin suka rinka bin
sawun dawakan
su Jarumi Darusi a kasa ba tare da su
Darusi
sun sani cewa Ana biye dasu ba.....
ME ZAI FARU MU HADU A LITTAFI NA
TARA DONJIN KARSHEN WANNAN
LABARIN
TASKAR AJALI
Littafi na Takwas 8
Na Abdulaziz Sani M Gini
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu [email protected]

TASKAR AJALI
Littafi na Tara 9
Marubucin littafin
Abdulaziz Sani M gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu [email protected]


Part A
Al amarin mujahid kuwa lokacin da fada ta watse kowa
ya kama gabansa sai
yayi sauri ya koma cikin gidan sarautar bai zame ko
ina ba sai masaukin su jaruma sarila da yake dakarun
dake
tsaron wajen sun sanshi kuma suna ganinsa
tare da jarumi Darusi babu wanda ya tsayar dashi
ko ya tuhumeshi akan dalilin da yasa zai shiga cikin
turakarsu sarila
A she jarumi darusi ne ya umarceshi da ya shiga
cikin turakar tasu ya bincike kayansu gaba daya idan yaga
waddannan taswirori na zuwa kogon TASKAR AJALI ya
konasu.
Ba komai bane yasa darusi yayi wannan tunani ba face
yaji a jikinsa cewa akwai wani makiyi a boye
wanda ya shigo cikin gari domin farautar wadannan
taswirori kai tsaye mujahid ya kunna kai har
zuwa cikin kuryar dakin barcinsu Sarila ya shiga
bude akwatunan su da dukkan jakukunansu yana bincike
sai da ya zazzage komai amma ko alamar taswirorin bai
gani ba
nan take ya shiga mayar da komai inda yake
cikin hanzari yana cikin wannan haline ya juyo motsi
takun sawu an durfafo kofar dakin
nan take hantar cikin
sa ta kada ya firgita ainun baisan sa adda ya bude
daya daga cikin manyan akwatunan ba ya shige ciki ya
kulle kansa
kawai sai ya tuno da wata addu a wadda yaji
darusi na yawan karantata da daddare don neman
tsari daga sharrin mutum da Aljan kawai sai ya kama
karantata a cikin zuciyarsa duk
daya san cewa bai karbi addinin musulunci ba
a wajan darusi.
Ashe kuwa ba wani bane ya durfafo wannan daki ba face
sarki DAMNASHI maimakon damnashi ya bude kofar
dakin ya shigo kawai sai ya ratso ta cikin garu kamar
yadda danshi ke ratsa kasa take ya baiyana a tsakiyar
dakin cikin hanzari ya shiga bude jakukkunan da
akwatuna yayi ta bincike
yana neman wadannan taswirori guda uku har yazo
kan akwatin karshe wacce mujahida ke ciki bai ga komai
ba
koda ya bude wannan akwatin karshe sai ya ganta wayam
babu komai a cikinta
hakika Allah shine sarkin iko kuma shine mai yin
yadda yaso a zahirin idan Damnashi baya ganin mujahida
a cikin akwatin amma
kuma a badini ga mujahid nan kwance a cikin
akwatin gaba daya jikinsa na karkarwa saboda tsananin
razanar da yayi saboda ya tabbatar da cewa koma
menene
ya shigo dakin yana daga cikin makiyansu
kuma indai yayi arba da shi sai ya kasheshi
ba komai ne ya hana sarki Damnashi ganin mujahid ba
face karfin addu ar da yake karantawa a cikin ransa
in ba don wannan hijabi da Allah ya sa tsakaninsa
ba da ko sautin bugabar zuciyar mujahid dake fita daga
cikin akwatin ya isa
ya tona masa asiri amma sai Allah ya dodar da kunnen
damnashi baiji ba
tabbas addu a itace babbar makami mai tarwatsa
azzalumai
cikin matukar karfin hali mujahid ya dago kansa domin
yaga ko wanene wanda ya shigo cikin dakin ai kuwa
yana dago kansa yayi arba da sarki damnashi a tsaye yana
huci da kumburi
tamkar bakin kumurci saboda tsananin bakin ciki ranshin
ganin wadannan taswirorin.
Haka dai damnashi yayi duru duru sannan ya sake
ratsawa ta cikinbango ya fice daga cikin dakin a sannan
ne mujahid yayi doguwar ajiyar zuciya tamkar wanda ya
kubuta
da kyar daga cikin bakin kura kawai sai ya dafe kirjinsa da
hannayansa biyu yace ''
Godiya a gareka ya ubangijin musulunci tabbas kaine
kadai ubangijin da ya
cancanci a bauta masa gama fadin haka keda wuya
sai mujahid ya fito daga cikin akwatin da sauri ya fice
daga cikin dakin
Sarki na zaune a dakin gani shi kadai saiga
wani hadimin attajiri damnashi ya shigo tare da dakarun
sarki suna masu yi masa jagora koda ganin
hadimin sai sarki ya buga tsaki ya dubeshi a fusace tun
kafin
ya risina ya gaishe shi yana mai daka masa tsawa
yace ina mai gidan naka saboda me zai aiko ka
shi yaki zuwa nan da kansa
koda jin wannan tambaya sai hadimin ya zube kasa
kamar zai yiwa sarki
sujjada jikinsa na karkarwa yace ka gafarceni ya
shugabana
ya sarkin sarakuna kayi sani cewa tun daren jiya zazzabi
ya kamashi don haka akwance yake
bai sami karfin fitowa ba
koda jin haka sai sarki yayi ajiyar zuciya yace to shi kenan
ka saurara a nan ka jira
zan aiko da kudin hajarku ka kaiwa shugaban naku
koda gama fadin hakan sai sarki ya mike tsaye ya fice
daga cikin dakin ganin
yayin da hadimin yayi ta godiya
+
A can gidan da attajiri damnashi sauka kuwa jarumi
darusi da gimbiya suzaina na isowa kofar gidan sai suka
ja linzamin
dawakansu suka tsaya cak sannan suka sauko daga
kan dawakan nasu suka daure su a jikin dirkar gini
faruwar hakan keda wuya sai suka ga an bude kofar
gidan saiga wannan hadimi na damnashi wanda yace
dashi yayi irin shigarsa ya fito fuskarsa cike da gashi
idonsa guda like
shi dai wannan hadimin yana matukar kama da sarki
damnashi hatta tsawonsa da kaurin jikinsa yazo
iri daya dana damnashi abin da ya banbantasu
kawai shine shekaru shi wannan hadimin matashine
dan shekara ashirin da biyar zuwa talatin
shi kuwa sarki damnashi ya haura shekara arba in da
biyar
koda jarumi darusi yayi arba da wannan hadimi
a karon farko sai ya zabura ya zare takobinsa domin a
zatonsa sarki Damnashi ne
Amma da yaga cewa hannayensa biyu ne lafiyayyu
kuma ya lura da cewa ai matashine shekarunsa basu kai
na sarki damnashi ba sai
yayi sauri ya mayar da takobin tasa cikin kofenta ya dubi
hadimin yace munzo ne muyi bincike a cikin
wannan gida naku bisa wani abu da muke zargi
koda jin wannan batu sai hadimin yayi murmushi
yace ai babu matsala ko zamuje kuyi bincikenku
amma ina mai tabbatar muku da cewa babu
wani abin laifi da zaku gani domin sarkinku ma ya zo
da kansa tare da dakarunsa sun bincike komai da ko ina
a cikin wannan gidan
.
Sa adda jarumi darusi yaji wannan batu sai yayi.
Murmushi aikasan shi bincike indai ba a gama shi ba
ba a gajiya da yinsa
nan take darusi da suzaina suka kunna kai izuwa cikin
gidan wannan hadimin
na biye dasu a baya
da shigowarsu suka ga sama da dakaru dari a zazzaune
sun kura musu idanu kawai
rabon da jarumi darusi yaga manyan mutane masu
tsawo kauri da kirar
sadaukantaka haka kamar wadannan tun a bayan
can cikin wani daji da ya shiga a yankin kasar
birnin rum kimanin shekaru biyar da suka gabata
kallo daya sukayi dakarun shida suzaina suka san cewa
indai yaki za ayi da wadannan mutane to fa sai abin
da hali yayi ko zasu sami nasarar hallaka su
amma bayan sun sha bakar wahala ko kuma
idan sun sami taimakon Allah ba dai jarumtarsu da
karfin damtsensu ya cecesu ba
Abinka da wanda ya dogara da Allah ba tare da shakkar
komai ba darusi da suzaina suka shiga aikin bincike
har saida suka gama duba ko ina dake cikin
gidan amma basuga wani abin laifi ba har darusi da
suzaina
sun jyo zasu fita daga cikin gidan sai sukaji sautin
faduwar wani abu daga cikin wani daki
kawai sai suka juyo da nufin su koma dakin amma sai
wadannan dakaru masu kirar mutanan farko suka mike
tsaye suka yi masu kawanya
saigashi Darusi da
suzaina sun zama yan kanana tamkar 'yan tsaki a gaban
muzuru.
Babban hadimin mai kama da sarki damnashi ya dubi su
darusi a fusace
me kuma zaku koma ku duba alhalin kum gama duba ko
ina darusi yace ai duban da mukayi dazu babu
kowa a cikin gidan nan sabanin ku da kuke zaune a nan
kuma babu dakin
da bamu shiga ba mun caje shi amma yanzu munji
motsin
mutum a cikin wancan daki don haka dolene mu koma
mu ga ko wanene
kafin darusi ya gama rufe bakinsa tuni wadannan
dakarun sun zare makamansu
kawai sai hadimin ya dubi jarumi darusi da suzaina yace
idan kuna son kuje
ku duba abin dake cikin wancan daki sai kun fara
kawai da wadannan jama ar tamu
kafin darusi ko suzaina daya daga cikinsu ya ce
wani abu tuni dakarun sun afka musu an ruguntsume da
masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro
Nidai gUyson komawa gefe nayi ina kallo
ashe dai kan rufin wannan gida sarila da yazirina ne a
kwance suna leken duk abin dake faruwa ta cikin wata
karamar kofa
koda sukaga yaki ya barke tsakanin su suzaina da
wadannan mugayan dakaru
sai suka yunkura da nufin su diro kasa daga kan rufin
gidan amma sai sukaji an dako su sun fado kasa tim !
A matukar galabaice kafin su yunkura su tashi tuni irin
wadancan samudawan
dakaru mikanin su arba in sun turmushe su
da karfin tsiya sun rufe su da raga kuma sun watsa musu
hodar barci take suka bingire kasa suka kama sharar
barci
lokacin da aka ruguntsume da masifaffen yaki tsakanin
su jarumi da darusi da wadannan
samudawan dakaru ya zamana cewa ana kaiwa
juna sara da suka cikin zafin nama juriya da bajinta sai
hankalin darusi da na suzaina ya dugunzuma ainun
ba don komai ba sai saboda sara da sukan baya tasiri a
jikin dakarun kuma duk karfin naushi da bugunsu
darusi dakarun shanye shi suke tamkar shafarsu suke in
ba don
su darusi suna da matukar zafin nama ba fiye da dakarun
kuma sun iya yaki
matuka da farat daya dakarun zasu gama dasu.
Su dai wadannan samudawan dakaru musamman sarki
damnashi yaje
yayi hayarsu daga can birnin Rum kuma ko kadan
basa aiki da tsafi face tsagwaran karfi da kuma
maganin tauri na saiwoyin bishiyoyi da itatuwa da suke
sha sudai wadannan
dakaru anbasu hayan yaki ne na musamman tsawon
shekaru takwas
wanda yasa har suna iya shafe sa a ashirin da hudu
suna yaki ba tare da sungaji ba sai da sarki damnashiya
biya dinare miliyan dubu daya sannan aka ba shi
wadannan dakaru
su dari da arbain
farko gwajin da aka yiwa wadannan dakaru bayan sun
gama karbar horon yakinsu na shekara takwas wani birni
mai suna baitul hurus
aka tura su a shirin sukashe gaba dayan mazajen garin
suka kama matansu da yara a cikin kwanaki uku kacal
tabbas karfin damtsen wadannan dakaru da juriyarsu
ta yaki ta wuce gaban kwatance
Ana cikin yin wannan bakin artabu ne daya da cikin
samudawan dakarun ya shammaci suzaina ya gabza mata
wawan naushi a ciki
saboda karfin naushin sai da yayi sama ya bugu
da ciki a matukar galabaice tana zubar da jini
ta hanci da baki a sannane samudawan dakarun su da
yawa suka daga manyan addunansu zasu gididdiba
suzaina
koda jarumi Darusi yaga abinda ake shirin faruwa sai ya
kwala kabbara
da karfin gaske kuma ya daka tsalle sama daga inda yake
gumurzu tamkar an harbo shi da kibiya
Guyson sunana ..
Yayita filfilawa akan dakarun dake shirin sassara suzaina
ya gabza musu naushi a kan fuskokinsu
su duka a lokaci guda suka tarwatse kowannansu sai
gashi ya furzo gudan jini
gami da hakori guda daga cikin bakinsa
karfin naushin kuma suka kife kasa a matukar galabaice
al amarin da yayi
matukar baiwa sauran samudawan dakarun mamaki
kenan kuma ya fusata su
ainun suka tasowa darusi gaba dayansu da
suyi masa rubdugun da zasuyi filla filla da sassan jikinsa
kaico idan mutum ya yanka kazar wahala dolene
ya fige a banza hakika wanda duk ya dogara
da Allah ba mai taba tozarta sa ashe lokacin da
jarumi darusi ya kwallah wannan kabbara da karfi
sai ya ci gaba da yiwa Allah kirari a cikin zuciyarsa
yana mai neman tsari daga wadannan samudawan
dakaru
aikuwa nan take yaji wani irin gagarumin karfi yana
shigarsa cikin jikinsa wanda
bai taba jiba sai da yaji kamar zai iya aza gammo a kansa
a dora masa duniya gaba dayanta yayi dako+
hahahah Kai madakin gini wannan anya kuwa
Guyson dai yana mamakin wannan jarumta kufa+
maimakon jarumi darusi yaci gaba da yakar dakarun da
makami
sai ya yarda takobinsa ya rinka buge makaman dake
hannunsu suna zubewa kasa kuma ko hannu suka
hada dashi take suke karyewa
idan kuwa ya danki hannun mutum ko kafarsa
sai dai kaji kal !!
Ya karyata tamkar ya karya silin kara
duk sa adda suka kawo masa sara suka saidai suga
suna samun iska sabida kaucewar da yakeyi
cikin bakin zafin nama na gaban kwatance
A hankali ne samudawan dakarun suka rinka kurma ihu
sakamakon tsananin zafi da zugin da suke ji
suna zubewa kasa nakasassu koda wannan hadimin sarki
Damnashi yaga wannan irin barnar
da ake yiwa dakarunsa sai ya firgita ainun ya ruga da
gudu
izuwa wannan daki wanda su darusi suka jiyo motsi
wadancan samudawan dakaru guda arba in kuwa
wadanda suka kama su
sarila suka daure ko da suka jiyo ihun yan uwansu a cikin
gidan sai suka ruga gaba dayansu izuwa cikin gidan
domin
sukai dauki suna shiga suka iske tuni jarumi darusi
ya bazar da kimanin mutum sittin daga cikin yan uwan
nasu,
koda ganin haka sai suka juya da baya da gudu suka
nausa cikin daji ganin
haka sai ragowar tsirarun dake yakar darusi suma suka
tsere suka barshi a tsaye tare da nakasassun
Ehm lallai Jarumi Darusi sadaukine kamar Guyson. Hh.
A sannan ne darusi ya ruga izuwa inda suzaina ke kwance
ya tasheta zaune kawai sai yaga ta goge
jinin dake kan hancinta da bakinta da kanta
sannan ta dubeshi cikin murmushi tace kada ka damu
yakai masoyina babu abinda ya sameni kyaleni na dan
huta saboda na bugu sosai a ciki maza ka ruga izuwa cikin
dakin nan kaga ko meye a ciki
batare da gardamar komai ba kuwa sai darusi
ya mike zumbur ya ruga izuwa cikin dakin yana
shiga sai yaga ashe akwai wata rijiya a gefe daya
wacce a farkon shigarsu dakin basu ganta ba
amma yanzu an kauta murfinta daga kanta
koda darusi ya leka cikin rijiyar sai yaga ashe hanyace ta
fita
daga cikin gidan nan take ya gane cewa adazu da suka
jiyo.
Motsi a wannan daki wani ne ya shigo yanzu kuma
wannan hadimi ne ya fice ta cikin rijiyar ya tsere
take darusi ya aiyana a cikin ransa yace duk yadda akayi
attajirin da ya sayarwa da sarki haja shine ya taara
wadannan dakaru kuma lallai akwai abinda yazo nema
ko shakka babu yana daga cikin makiya cikin hanzari.
Ya dawo wajan suzaina ya taimaka mata ya tasheta tsaye
suka fice daga cikin gidan
tana dingishi'
da fitarsu sai sukayi kicibis da sarila da yazirina
kwance a kas kuma daure cikin raga suna ta fama shara
barci
cikin kaduwa da mamaki suzaina ta dubi darusi tace
wadannan kuma menene ya kawo su nan
ko kuwa satosu akayi
koda jin wannan tambaya sai jarumi darusi ya gyada kai
yace ba sato su akayi ba
su da kansu suka kawo kansu suzaina tayi ajiyar zuciya
tace ko dai
suna son su munafuncemu ko kuma su hada kai da
makiya
darusi yace Ai baki da tabbas kawai kina
zargine yanzu yaya zamuyi da su
suzaina tace kawai kabarsu a nan inda ka gansu
in yaso wayonsu da karfinsu ya kwacesu
darusi yace A a idan muka barsu a nan makiya
suka dawo suka riskesu zasu iya hallaka su
ba karamin asara bace rashin sarila da yazirina saboda
idan suka karbi addinin Allah zasu musuluntar
da mutane da yawa wadanda bame zan iya adadin su ba
saboda su masu jama ane
koda gama fadin hakan sai darusi ya sa takobinsa ya
yanke
ragar data lullube sarila da yazirina kawai saiya kamo
dokinsa ya dora sarila da yazirina a kai sannan
ya dubi suzaina yace ai saiki hau kan naki dokin mu tafi
nan fa gardama ta karke a tsakaninsu suzaina na cewa sai
dai ya zo ya hau nata dokin ko kuma ita ma ta taka da
kafarta
cikin Alamun fushi ya dubeta yace
kinsan cewa haramunne hada jikina da naki
tunda ke ba matata bace kuma ke ba muharramata bace?
Koda gama fadin hakan sai darusi yaja linzamin dokinsa
yayi gaba yazirina da sarila
na bisa dokin suna ta faman shara barci
suzaina tayi tsaki tace a ranta ba zan iya jiran sai mun
dawo daga kogon Taskar Ajali ba
sanna na sami ikon kusantarka dolene na tafi a matsayin
matarka
nan take itama ta kada dokinta ta bi shi a baya da sauri
suka tafi
Guyson nake
Al amarin sarki Damnashi kuwa lokacin da ya
baro turakarsu sarila bayan ya caje ko ina baiga wannan
taswirar da yake
nemaba sai ya yi amfani da karfin sihirinsa
ya dawo masaukinsa a cikin dakika goma kacal
koda ya baiyana a kofar gidan yaga dawakai guda biyu
a daure sai jikinsa ya bashi cewa lallai makiya ne suka zo
domin haka sai ya zagaya bayan gidan ya bude
wannan hanya ta sirri dake karkashin kasa ya shige
gidan bai bullo ta ko ina ba sai cikin wannan dakin rijiya a
dai dai lokacinne
darusi ya fara samun nasara akan samudawan dakarun
nan
sarki Damnashi na fitowa daga cikin rijiyar
sai ga wannan hadimin nasa mai kama dashi
ya shigo a firgice ya na ganin sarki Damnashi sai ya
dubeshi cikin
dimauta da tsananin tsoro yace
ya shugabana jarumi Darusi ne ya shigo gidan
nan ga shi can yana ta karkarya wadannan dakarun
daka hayo tabbas in ya gama dasu kanmu zai dawo
ka tuna cewa sa adda kake da hannayanka ma biyu
ya sami nasara akanka
bare yanzu
da kake da guda daya
idan baka bar nan ba yanzu har a bada ba zaka
dauki fansa ba
akan darusi kuma ba zaka taba cika burinka ba na
mallakar dukiyar dake cikin TASKAR AJALI.
koda hadimin yazo nan a zancensa sai hankalin
sarki Damnashi ya tashi ainun kuma ransa ya baci
a lokacin da bakin ciki mara misaltuwa ya turnuke
shi kawai sai ya zare takobinsa da lafiyayyan
hannun nan ya yunkura zai fita can inda ake wannan
gumurzun ya fafata da Jarumi Darusi amma sai hadimin
nasa ya janye shi suka shige cikin rijiyarnan
mai matattakala suka manta basu rube ba shine dalilin da
yasa Jarumi Darusi yaga rijiyar
Da karfin sihirin tsafi sarki damnashi da hadiminsa suka
bace bat
basu baiyana a ko ina ba sai a wani gida daban wanda
suka kama dake can kudancin birnin.
A cikin tsakiyar falon gidan suka baiyana sarki
damnashi nata huci gami da ciza lebe saboda
tsananin fushi kawai sai ya zauna akan kujera yayi
tagumi shima hadimin sai yaje ya zauna akan wata
kujerar dake gefe daya
duk su biyun sukayi tagumi
a dai dai wannan lokaci ne wata zukekiyar Kuyanga ta
shigo cikin falon
dauke da tambulan giya gami da kofuna guda biyu ta
ajiye
a gabansu kuma ta zubawa kowannansu ruwan
ta mika musu
maimakon sarki Damnashi ya karbi kofin yasha sai ya
buge hannun kuyangar
ya daka mata tsawa ya namai korarta
kuyarngar ta mike da sauri jikinta na tsuma ta fice daga
cikin falon faruwar hakan keda
wuya sai sarki Damnashi ya dubi Hadimin yace' tun da
dai yanzu
asirinmu ya tonu babu sauran batun boye
boye kaje can wajan alkalan gasar da sarkin garin nan
ya shirya ka bayar da sunana a cikin jaruman da zasuyi
wannan gasa
koda jin wannan batu sai idanun hadimin suka zazzaro ya
dubi sarki Damnashi
cikin firgici yace ya shugabana ai idan ka bayyana kanka
kama ka za ayi a kashe ka ko a tsire ka a kurkuku
koda jin wannan batu sai sarki Damnashi ya bushe da
dariya yace
kai ba sarki bane shi yasa bakasan cewa kashe sarki ba
abune mai sauki ba
ka tuna cewa sarkin garin nan da jama arsa sun karbi
addinin
musulunci sannan kuma shi jarumi darusi bashi da burin
ayita zubar da jini
a doron kasa yafi son jama a sukarbi addinin nasa ya
yadu ko ina idan na
shiga wannan gasa darusi da sarkin garinnan zasuyi
murna da hakan saboda a tunaninsu zuciyata zata karaya
bisa ganin irin abubuwan Al ajabin da darusi
zaiyi na jarumtaka akan hanyarmu ta zuwa kogon Taskar
ajali
har nayi imani na karbi Addininsa
jama ar dake karkashina sunfi miliyan goma
kaga ashe ina karbar addinin suma zasu karba
abin da basu sani ba shine babu wata masifa da zata iya
sani na bar addinina na iyaye da kakanni na
da kuma al adun dana gada daga garesu zanyi
amfani da wannan dama ne kawai na mallaki dukiyar
dake cikin taskar ajali
sannan na kashe su Darusi na zamo SARKIN DUNIYA
koda gama fadin hakan sai sarki damnashi ya sake
bushewa da dariya a karo na biyu yayi ta kyalkyala
dariyar kamar ba zai dainaba
+ Ni kaina da nake muku typing dinnan wato Ni guyson
na dan tsorata da dariyar tasa fa +
koda ganin haka sai shima hadimin ya taya shi yin dariyar
suna cikin
wannan haline daya hadimin da yaje gidan sarki
karbo kudi ya shigo cikin falon dauke da katuwar akwati
fuskarsa cike da annuri kawai sai ya ajiye
akwatin a gaban sarki Damnashi ya budeta babu komai a
cikin akwatin face Lu'u lu'u
koda ganin wannan dukiya sai sarki damnashi ya bushe
da mahaukaciyar dariyar farin ciki sannan yace
sarki ya sayi baki da kudinsa wadannan kyayyaki
dukkaninsu ba kaya bane muna barin garin nan don
tafiya
kogon TASKAR AJALI kayan zasu rikide izuwa
dakarun bakaken Aljanu suci birnin da yaki
mata da kananan yara kadai za a bari a raye kaga kenan
ina dawowa daga TASKAR AJALI a nan birnin zan fara
yada
zango nayi sha anina.
Koda jin wannan gagarumin shiri sai hadiman suka
rungume
sarki Damnashi suna masu yi masa kirari da jinjina
kwatsam sai sukaga sarki Damnashi ya murtuke fuskarsa
a lokacin da hawaye ya zubo masa cikin kaduwa
suka janye jikinsu daga cikin nasa suka dubeshi a firgice
babban hadimin
da karamin suka dubi junansu sannan babban yace ya
shugabana ina dalilin
wannanp
Sauyin yanayi a tare dakai farat daya
koda jin wannan tambaya sai sarki Damnashi yayi ajiyar
numfashisannan yace ai iya gumurzun
da gwagwar mayar da nayi a rayuwata ba a taba fitar
mini da koda digon
jini ba a filin daga bare a yi mini wani babban rauni
amma saigashi jarumi darusi ya sare mini hannuna guda
yanzu gashi zan
zama sarkin duniya nan kaf amma bani da hannu guda
hm caka buri kenan wai.
Nakasa ga sarki ba karamar kankanta bace na rantse da
darajar ikona
sainayiwa jarumi darusi kisan wulakanci irin wanda ba a
taba yiwa wani mahaluki ba a doron kasa
saina wulakanta gangar jikinsa yadda labarin wulakantar
sa zai baza duniya baki daya.Final Round.
A can gidan sarki kuwa lokacin da sarki
yaga an
dade sosai su jarumi darusi basu dawo
ba sai hankalinsa
ya sosu nan take ya bayar da umarnin a
kawo
masa kayan yakinsa da dokinsa kuma
ya umarta wasu
dakaru wadanda zasuyi masa rakiya
nan da nan kuwa aka gama shiri tsaf
har sarki ya kamo dokinsa zai hau sai
ga jarumi darusa janye da doki mai
dauke
da sarila da yazirina suna barci gimbiya
suzaina na biye dashi bisa nata dokin
cikin kaduwa da mamaki sarki ya taho
garesu
ya taryesu yana mai duban darusi yace
menene
ya faru ya kai uban jaruman duniya
Darusi ya numfasa sannan ya risina
ga sarki cikin girmamawa yace tabbas
abinda kake
zargi akan wannan attajiri gaskiya ne
shine wanda yayi kokarin hallakani a
filin gasa domin a masaukin nasu akwai
wadansu samudawan dakaru daga
birnin Rum kimanin su dari da doriya
In ba don taimakon Allah ba da tuni
sun hallakamu
ni da gimbiya mun caje ko ina a gidan
bamuga
komai ba sai wata rijiya a cikin wani
daki
wacce hanyace ta karkashin kasa ta fita
daga gidan
bayan mun fito daga gidan sai muka
tsinci sarila da yazirina kwance a daure
cikin wannan hali da suke ciki yanzu
amma sa adda zmu shiga gidan babu
su a wurin
lokacin da jarumi darusi yazo nan a
zancensa sai sarki yayi
doguwar ajiyar zuciya sannan yace
tabbas koma menene wannan attajiri
dolene ya kasance daya daga cikin
manyan sarakunan duniyar nan
dole ne muyi iya kokarinmu
mutabbatar da cewa mun kamashi mun
kaishi
kurkuku mun tsare
shi kafin mu tafi zuwa kogon taskar ajali
saboda gama san irin mugayan
abubuwan da yake
kokarin shiryawa a cikin birnin nan ba
to amma kuma ai in daso yake ya
yakeni da tun
a farkon zuwansa zai sa samudawan
dakarunsa su afma mana duk yadda
akayi dai yana da wata bukatar a
wajanku bisa
wannan daliline yasa aka kama sarila
aka daure
dajin wannan batu sai mamaki ya kama
darusi
da suzaina sannan yace''
ya shugana yanzu kuna nufin kace tare
da kai zamu tafi kogon taskar ajali?
Sarki ya

Please Login or Register in order to submit comment