Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take domin gani take a
koyaushe zata iya ganin Sadauki Sharkas a
gabanta.Haka dai Sulaira tacigaba da tafiya a
cikin
daren janye da wannan saniya a cikin dajin ta
durfafi hanyar da zata
TSIRA DA HALAKA!!!
Littafi Na Daya (1)
Part D
Inda takai sarki Garzub ta boye.Saida ta shafe
sa'a
uku da rabi tana tafiya sannan ta iso wannan
kogo
ba tare da ta hadu da wani mugun abu ba.Cikin
murna Sulaira ta shafi kofar kogon ta bude
sannan
ta shiga cikon kogon janye da farar saniyar.Suna
shiga kofar ta bace bat.Cikin gaggawa Sulaira ta
sawa Sarki Garzub wannan batta a bakinsa
wacce
ke cike da madarar shanu.Bisa mamaki kuwa sai
taga ya kama kwankwadar madarar yana
shanyewa
ashe idonsa biyu ba bacci yake ba.Saidai Garzub
yasha madarar ya koshi sannan ya bude
idanunsa
da kyar ya dubi Sulaira yayi mata wani guntun
murmushi a lokacin da yake ciza lebensa saboda
tsananin zogi da radadin da yake ji.Gashi yana
bude baki kamar zaiyi mata magana amma ya
kasa.A wannan lokaci ne Sulaira ta lura da
wadanan manyan raunika guda biyu dake jikin
Garzub ta fahimci cewa a kalla sai yayi kwana
goma sha biyu a kwance kafin ya iya ma tashi
zaune.Al'amarin daya dugunzuma hankalinta
kenan
domin bata ga yadda zasu iyayin rayuwa ba a
cikin wannan kogo ita dashi da kuma saniyarta
alhalin babu ruwa a cikin kogon babu isasshen
abincin guzuri.Ida kuwa tace zata rinka yawan
fita
daga cikin kogon abokan gaba zasu iya ganinta
su
gano inda ta boye Garzub su biyosu su hallakasu
gaba daya.Nanfa Sulaira ta zauna tayi tagumi ta
shiga tunani mai zurfi tana kallon yanayin cikin
wannan kogon dutse wanda ke cike da ciyayi da
kananan bishiyoyi.Tana cikin wannan tunanin
wata
dabara ta fado mata kawai sai ta mike tsaye ta
zare
wata gajeriyar adda a kuibin cinyarta ta hagu ya
kama tonan kasa da ita.Bisa mamaki saiga ruwa
ya fara bulbulowa.Cikin tsananin murna ta cigaba
da kwakule kasar wajen ta samar da yar karamar
rijiya wadd ta ciko da ruwa.Al'amarin da yai
matukar bata mamaki kenan."Abinda bata sani
ba
shine wannan dutse da suke cikinsa a saman
wata
korama yake."
**** *** **
A can Sansanin yaki kuwa lokacin da gari ya
waye
sai kowanne bangare sukayi shiri aka fito filin
daga
aka tsaitsaya tsawon rabin sa'a ana tsaitsaye
amma an kasa cigaba da yaki saboda kowacce
runduna babu mai bata umarni sai kallon kallo
ake
ana muzurai kamar aci babu.Daga can sai wani
babban barde daga cikin larabawa ya fara
baiyana
yana mai cewa yaku abokan gaba kuyi sani cewa
mu daku duk muna cikin tashin hankali bisa
rashin
ganin shuganninmu saboda haka ina mai
shawartarmu da mu tsaida wannan yaki har
izuwa
tsawon kwana bakwai in yaso mu zabi mutum
bakwai bakwai su bazama cikin wannan daji don
neman inda shugabanninmu suke.Ma'ana mu mu
tafi neman namu shugaban kuma ku tafi neman
naku.Idan wakilan namu suka dawo ko an gansu
ko ba'a gansu ba sai mu cigaba da yaki wadanda
ke da sa'a a tsakaninmu sai su sami
nasara.Lokacin da wannan barde ya gama
wannan
jawabi sai wani dan uwansa balarabe ya fassara
jawabin nasa a cikin yaren mutanen sarki
Garzub.Koda jama'ar Sarki Garzub sukaji wannan
batu sai suka aminta da hakan.Nan take
kowacce
rundunata zabo mutum bakwai daga cikinta
kuma
akayi alkawarin cewar wadannan mutane goma
sha
hudu ba zasu yaki juna ba a cikin daji har suje su
dawo kuma dayansu ba zai cutar da wani daga
cikin abokan gaba ba koda za'a yi kicibus mugun
gamo a cikin daji.Bayan an gama wannan
alkawari
ne dakarun guda goma sha biyu suka hau
dawakansu suka nausa cikin daji.Masu wakiltar
bakaken fata sukayi gabas,su kuma masu
wakiltar
larabawa sukayi yamma.Wannan shine abinda ya
faru a tsakanin rundunar mayakan biyu a rana ta
biyu bayan an fara wannan yaki.
*** *** ***
Al'amarin Sadauki Sharkas kuwa lokacin da suka
fado daga kan tsaunin nan shida sarki Garzub
izuwa cikin kogi har kawunansu suka gwaru da
duwatsu suka suma a cikin kogin har ruwa ya
tafi
da Sharkas,sai igiyar ruwa ta cigaba da tafiya
dashi
tamkar an dora takarda akan ruwa.Saida yayi
tafiyar sa'a biyu da rabi akan ruwan bai fardado
ba.Lokacin da ruwan ya kawoshi saman wani
dutse dabam mai tsananin zurfin gaske ne ya
farfado.Yana bude idanunsa yaga zai rikito izuwa
kasan dutse mai tsananin zurfi saiya kwala
ihu,ihun
nasa ya cika dajin gaba daya yana amsa
kuwwa.Saida yai dakika dari da tamanin sannan
ya
iso karshen dutsen ai kuwa sai ya fado akan
wata
bishiya reshenta ya cakeshi a kuibin cikinsa ya
bullotso ta gadon bayansa nan yake ya sake
sumewa.Sadauki Sharkas bai farfado ba sai
bayan
rabin sa'a.Yana farfadowa yaga jini na zuba daga
cikinsa,yana shafawa haka yaji ice a cikin cikinsa
kawai sai ya kama icen ya fara zareshi yana
kwala
ihu.(Kaji maza masu juriya da tsananin
jarumta).Ai
kuwa yana gama zare icen ya sake sumewa a
karo
na uku.Jim kadan saiya farfado yaga har a
sannan
jini bai daina zuba ba daga cikinsa.Cikin matukar
karfin hali ya cire rawanin kansa ya daure cikin
nasa sannan ya fado daga kan bishiyar ya tumu
da kasa yana numfashi sama sama.Duk da cewar
ya daure raunin cikin nasa da rawaninsa amma
sai
yaga har yanzu jini bai daina zuba ba.Al'amarin
daya dugunzuma hankalinsa kenan ya tabbatar
da
cewa idan bai dinke wannan rauni ba lallai zai iya
zama sanadin ajalinsa a koyaushe.Koda gama
aiyana hakan sai sadauki Sharkas ya rinka jan
ciki
ya isa gaban wani dutse ya jingina bayansa akan
dutsen sannan ya cire jakar guzurinsa daga
kafadarsa ya budeta da kyar ya dauki allura da
zare irin wanda ake dinke rauni dashi ya shiga
yiwa kansa likitanci.Duk da cewa yana jin mugun
zogi da radadi a duk sa'adda ya soka allurar a
cikin fatar jikinsa yaje zare amma sai ya daure
baiyi ihu ba ya rinka ciza lebe kawai.A haka dai
ya
samu ya gama dinke raunin dake kuibin cikinsa
wanda ke can gadon bayansa ne ba
bu damar ya dinkeshi dole sai garin magani ya
debo ya cusa a cikin ramin raunin har ya
cikashi.Saida Sharkas ya kwana uku a wannan
wuri yana jinyar rauninsa sannan ya sami saukin
daya iya mikewa tsaye da kyar amma sai tafiya
ta
gagara dole ya karyo reshen wata bishiya ya
rukeshi a matsayin sanda ya rinka
dogarashi.Yana
tafe yana rike da cikinsa kamar zai fadi kasa
amma
saboda naci bai fasa yin tafiyar ba.Babu abinda
ke
cikin zuciyar Sharkas face ya lalubo inda Sarki
Garzub da Sulaira suke domin ya hanzarta kashe
su sannan ya koma sansanin yaki yaga abinda ya
kwana.Shidai Sharkas bashi da wani buri a ransa
wanda yafi ya sami nasarar cika aikin da aka
turoshi izuwa wannan nahiya ta bakaken
fata,wato
ya tattaro bayi da dukiya adadin da sarki
Madarus
ke bukata.Da yke Sharkas mutum ne mai
nutsuwa,kaifin tunani da hangen nesa sai ya
aiyana
a ransa cewa babu inda zaiga su sarki Garzub
face
a can baya domin ya gani cewa sa'adda suka
fado
kasan tsaunin nan lallai suma yayi kuma ruwane
ya
janyoshi ya kaishi inda ya tsinci kansa
yanzu.Koda
gama aiyana haka sai ya juya da baya ya cigaba
da tafiya yana dogara sandarsa yana dingishi
kamar ma bazai iya doguwar tafiya ba.Haka dai
ya
cigaba da tafiya har rana ta take ya gaji likis yaje
karkashin wata bishiya ya zauna yana hutawa
sannan ya bude jakar guzurinsa ya fiddo abinci
yaci ya sake zuba garin magani akan ciwon dake
gadon bayansa ya mike ya cigaba da tafiya.Saida
Sharkas ya shafe kwana uku yana tafiya a cikin
wannan daji bai ga su Sarki Garzub kuma bai
hadu
da wata halitta ba.Abinda yafi daga masa hankali
shine duk nisan tafiyar da yayi bai jiyo sautin
alamar cewa ana yaki ba a cikin daji kuma baiga
ungulaye suna yawo a sama ba bare ya gane
cewa
anyi gumurzu an sami gawarwaki.Koda ganin
haka
sai Sharkas ya yanke hukuncin ya koma can inda
sansanin yaki yake,kawai sai ya cigaba da tafiya
yana dogara wannan sanda kamar
nakasasshe.Yana cikin tafiyar ne kwatsam yayi
gamo da wadannan dakaru guda bakwai dakarun
kabilar bakaken fata.Yana ganinsu sai ya zare
makami don ya yakesu amma sai yaga ko motsi
basuyi ba bare suyi yunkurin yin yaki dashi.Kawai
sai suka ratse hanya suka falfala da gudu izuwa
wata nahiyar daban suka barshi nan a tsaye cikin
tsananin takaici domin inda lafiyarsa kalau sai
duk
ya kure musu gudu ya hallakasu.Abinda ya daure
masa kai shine me yasa wadannan dakaru
bakwai
suka baro can sansanin yaki suka shigo daji?Ko
kuwa GUDUN TSIRA sukayi bayan an gama yakin
mutanensa sun sami nasara akansu?Nan dai
Sharkas ya cigaba da tafiya har izuwa tsawon
sa'a
guda sannan ya sake kicibis da nasa mutanen
wadannan mutane bakwan wadanda suka shigo
cikin dajin domin nemansa.Koda Dakarun sukayi
arba da Sharkas suka ganshi a cikin wannan hali
sai sukayi turus suka kura masa idanu cikin
matukar mamaki saboda a tarihin jarumtakar
Sharkas bai taba samun rauni ba a wajen yaki
amma yau gashi harma yana dogara sanda da
kyar yake iya tafi.Sharkas ya dubi wadannan
dakaru bakwai ya daka musu tsawa yace menene
dalilin da yasa kuka baro sansanin yaki kuka
shigo
cikin wannan daji?Koda jin wannan tambaya sai
daya daga cikinsu ya kwashe labarin duk abinda
ya
faru ya zaiyane masa a karshe ya shaida masa
cewa sunga Sulaira a can bakin wani katon dutse
amma sai ta bace bat suka nemeta sama da
kasa
suka rasa.Koda jin wannan batu sai Sharkas ya
cika da murna ya tambayi hanyar da zaibi yaje
wajen da sukaga Sulaira.Nan take sukayi masa
nuni da hanyar.Cikin gaggawa Sharkas ya karbi
dokin daya daga cikinsu ya hau ya zabureshi da
gudu ya nufi wannan hanyar.Koda ganin haka sai
wadannan dakaru sukayi sauri suka bi bayansa
da
gudu.
TSIRA DA HALAKA!!!
Littafi Na Daya (1)
Part E
A CAN KOGON DUTSE kuwa,bayan Sulaira ta ga
ruwa ya samu sai tayi tunanin ta dafa ruwan
dumi
domin ta dan gasa jikin sarki Garzub amma inda
matsalar take shine babu tukunyar da zata iya
dafa
ruwan a ciki kuma babu busassun ice wanda
zata
iya dafa ruwan dashi domin koda ma tayi amfani
da wutar tsafi ba zata sami biyan bukata ba
kamar
yadda takeso domin duk sa'adda zata yiwa mara
lafiya magani bata amfani da karfin sihirinta.Bisa
wanna dalili ne yasa Sulaira ta fita daga cikin
kogon dutsen ta tafi neman tukunya da icen
wuta.
Da kyar da sidin goshi ta faki ido taje har can
sansanin yakin ta dauko tukunyar kasa gami da
icen girki ta dawo cikin kogon dutsen tayi sauri
ta
hada wuta a karkashin wadansu kananan
duwatsu
sannan ta dora tukunyar kasar akan duwatsun ta
zuba ruwa a cikinta kuma ta zuba wani garin
magani a cikin tukunyar sannan ta rufe.
Saida ruwan ya tafasa sannan ta dauko ganyen
ta cire
wani farin kyalle a jikinta wanda tayi damara
dashi ta rinka tsomashi a cikin tafasasshen
ruwan tana
gasa sassan jikin Garzub.Kafin Sulaira ta fara
wannan aiki Sarki Garzub bacci yakeyi amma
tana
dandana masa tsumman a karo na farko sai ya
kwala ihu sakamakon wani mugun zogi da yaji
sa'adda ruwan maganin ya ratsa cikin kofofin
gashin jikinsa.Haka dai Sulaira ta cigaba da
wanna
aiki har ya zamana cewa ta gama gasa ko ina a
jikin sarki Garzub.Bayan ruwan maganin ya ratsa
ko ina a jikinsa sai idanunsa suka bude sosai a
karon farko tunda aka shigo dashi cikin kogon
dutsen tsawon kwana uku a sannan ne ya dawo
cikin haiyacinsa sosai ya dubi gabas da yamma
kudu da arewa ya fahimci a inda yake,sannan ya
kurawa Sulaira idanu cikin matukar mamaki.Da
kyar sarki Garzub ya budi baki yace da ita yake
wannan MA'ABOCIYAR KYAWU yaya akayi muka
zo
nan cikin wannan kogon?
Dajin wannan tambaya sai
Sulaira ta kwashe labarin duk abinda ya faru a
baya ta zaiyane masa tun daga lokacin da taga
ya
suma har izuwa sa'adda ta jashi a kas da kyar ta
shigar dashi cikin wannan kogo ta shiga jinyarsa
har izuwa sa'adda ta tafi neman dabbobinsu don
ta samo madarar da zata bashi ya sha tayi sa'a
kuwa
ta gano inda dabbobin nasu suke ta taho da
saniyarta.Daga wannan rana ta cigaba da
jinyarsa
har tsawon kwana uku.Lokacin da Sarki Garzub
yaji wannan labari sai taga idanunsa sun ciko da
kwalla har hawaye ya zubo masa.Al'amarin
dayayi matukar baiwa Sulaira mamaki kenan ta
dubeshi
tace yakai wannan sarki mai dara ta daya a cikin
wannan nahiya,kai kuwa menene dalilin da yasa
ka
zubar da hawayenka yanzu sakamakon jin
wannan labari dana baka?
Da jin wannan tambaya sai Sarki
Garzub yayi ajiyar zuciya sannan yace yake
ma'abociyar kyawu kiyi sani cewa kece mace ta
farko dana taba kadaita da ita a rayuwata sama
da
tsawon rabin sa'a gashi harma mun shafe
kwanaki
uku tare.A rayuwata in banda mahaifiyata babu
wani mahaluki daya taba ceton rayuwata sai ke.
Ita kanta mahaifiyata ta ceci rayuwata ne
sa'adda ina
yaro karami.Kece mace ta farko data taba
jikina.Lallai al'amarinki ya bani tsoro kuma ya
bani
matukar mamaki.Shin zaki iya sanar dani
labarinki
da kuma dalilin da yasa jama'arku suka shigo
cikin wannan daji har suka kafa wannan karamin
kauye?
Ba tare da boye komai ba Sulaira ta kwashe
labarinta tun daga farko har karshe ta zaiyanewa
sarki Garzub har da wasiyyar da mahaifinta yayi
mata a karshe cewar kada ta kashe kanta lallai
tayi aure domin ta bar zuri'arsu a doron
kasa.Lokacin
da Sulaira tazo nan a labarinta sai taga hawaye
ya
kara zubowa a idanun sarki Garzub saboda
tausayinta,kawai sai taga ya yunkura da kyar ya
mike zaune a karon farko tunda ta shigo dashi
cikin kogon sannan ya kura mata idanu yace
yake Sulaira kiyi sani cewa ni dake da iyayenmu
sun
barmana wasiya iri daya.Ki sani cewa a da can
bani da burin yin aure amma duk sa'adda na tuno
da wasiyyar mahaifina sai naga cewa bani da
wani
zabi wanda yafi nayi auren.Shin zaki iya yarda
dani
na zama ABOKIN RAYUWArki?
Koda jin wannan batu sai Sulaira ta rungume
sarki Garzub ta fashe
da kuka tana mai cewa kaine 'da namiji dayafi
cancanta dani domin a duniya ban taba jin naso
wani ba ba sai kai.
Dajin haka sai farin ciki ya
kama sarki Garzub.Nan take ya kama hannun
Sulaira ya yanki babban dan yatsanta yasa dan
yatsan a cikin bakinsa ya tsotsi jinin daya
fito.
Itama Sulaira ta kama nasa hannun ta yanki
dan yatsansa tasa a bakinta ta tsotse jini.
Wannan itace al'adar mutanen birnin
Hirtoliya.Indai mace
da namiji sukayi haka sun zama miji da
mata.Faruwar hakan keda wuya sai sukaji
sukuwar dawakai a kofar kogon da suke ciki.
Cikin firgici
Sulaira ta mike zumbur ta zare makaminta amma
sai Sarki Garzub yayi caraf ya rukota ya fara
karanta wadansu dalasiman tsafi.Nan take ya
gani
a cikin idanunsa cewa Sadauki Sharkas ne da
dakarunsa mutum bakwai sukazo gaban kogon
dutsen bisa dawakai sukayi turjiya.Nan take
Sadauki Sharkas ya sauko daga kan dokinsa ya
dubi wannan kogon dutse kawai sai wani irin
haske
ya fito daga cikin idanunsa ya dira a daidai inda
kofar kogon dutsen take.Hasken ya fara kokarin
bude kogon.Cikin hanzari sarki Garzub ya cigaba
da karanta wadansu dalasimai na tsafi sai gashi
duk su biyun sun fara yin zufa kuma jikinsu na
karkarwa.Gaba dayan kogon dutsen ya kama
girgiza kamar zai nutse izuwa karkashin
kasa.Saida
rabin sa'a ta shafe a haka ya zamana cewa
Garzub da Sharkas sun jike sharkaf da gumi
sannan duk
su biyun suka fadi kasa suna numfashi da
kyar.Jim kadan sai Sharkas ya mike tsaye
zumbur
ya kama doki ya haye ya dubi wadannan dakaru
nasa yace ku zo mu koma can sansanin yaki mu
karar
da sauran abokan gaba sannan nayi sabon shiri
mu dawo nan a hallaka wadanda ke cikin
kogon.Koda gama fadin hakan sai Sharkas ya
zaburi dokinsa da gudu ya durfafi inda sansanin
yakin yake.Su kuwa wadannan dakaru nasa sai
suka bishi a baya da gudu suna karawa
dawakansu kaimi.
Tafiyarsu Sharkas keda wuya sai
Sarki Garzub ya yunkura ya mike tsaye da kyar
yana tangadi sakamakon raunikan dake jikinsa ya
zare takobinsa ya nufi hanyar fita daga
kogon.Koda ganin haka sai Sulaira ta ruga da
gudu tasha
gabansa ta rike kafadunsa a sa'adda idanunta
suka
ciko da kwalla tace kada ka fita yaki yakai
mijina,domin ko kadan babu kwari a jikinka,ba
zaka iyayin komai ba.kuma abokan gaba zasu iya
samun lagonka nan danan.Sa'adda Garzub yaji
wannan batu sai yayi ajiyar zuciya sannan ya
dubi
Sulaira yace yake matata kiyi sani cewa idan ban
fita ba yanzu za'a gama karar da dukkanin
sauran
jama'ata a kama na kamawa a kashe na
kashewa
sannan abokan gaba su karasa izuwa birnina su
bajeshi su kwashe dukiyarmu su debi bayi.Sanin
cewa ina nan a raye yanzu shine yasa su
Sharkas
basu tafi izuwa birnin nawa ba domin sun san
cewa idan suka tafi kamar sun bar BAYA DA
KURA
ne.
Ki sani cewa idan muka cigaba da zama anan
har Sharkas ya dawo ni dake duk ba zamu tsira
ba.Lallai yanzu bamu da wani zabi face mu fita
mu tunkari abokan gaba domin komai zai iya
faruwa.Kodai mu tsira ko kuma mu hallaka.Gama
fadin hakan keda wuya sai Garzub yayi nuni da
hannunsa izuwa ga kofar kogon.Take kofar ta
wanzu suka fice daga ciki Sulaira na rike da
kugun
Garzub yana takawa a hankali da kyar.
Ai kuwa suna fitowa daga cikin kogin sai wannan
saniya ta
Sulaira ta biyota.Kwatsam kuma sai ga dakaru
bakwai na jama'ar sarki Garzub sun iso bakin
kogon dutsen bisa dawakai.Koda wadannan
dakaru
sukayi arba da Garzub suka ganshi a raye sai
suka cika da matukar farin ciki suka zube kasa a
gabansa suka kwashi gaisuwa.Sarki Garzub ya
dubesu yaga har da SARKIN YAKINsa wato
sadauki
Zamud.
Garzub yayi murmushi sannan ya dubi su
Zamud yace kuyi gaisuwa ga gimbiya Sulaira
domin a yaune ta zama MATATA.Dajin haka sai
su Zamud sukayi sujjada ga Sulaira suka kwashi
gaisuwa sanna suka dago a lokaci guda suka
fuskanci sarki.Garzub ya dubi Zamud yace yakai
dirkar Hirtoliya me ake ciki acan filin yaki?
Zamud yayi murmushi sannan yace ya
shugabana damu
da abokan gaba kowanne bangare sunyi asarar
miliyoyin rayuka musamman bangarenmu domin
ka sani cewa sun fimu yawa.Lokacin da muka
nemeka muka rasa sai hankalinmu ya
dugunzuma
kuma muka sami karayar zuci domin mun
tabbatar
da cewa indai babu kai a wannan yaki cikin
kankanin lokaci abokan gaba zasu sami nasara
akanmu.
Ya shugaba yanzu ina dabara take tunda
gashi kana cikin yanayi na matukar rashin lafiya?
Ina ganin cewa bazaka iya yin yaki a haka
ba.Dajin
wannan batu sai sarki Garzub yayi murmushi
sannan ya hade fuska yace ai duk NAMIJIN
KWARAI ba'a sanshi da karayar zuciya ba.Idan
har abokan gaba zasu fito wannan yaki lallai
nima zan
fita yanzu muyi sauri mu koma can sansanin yaki
don kada a fara yakin muna nan.Koda jin haka
sai
daya daga cikin dakarun ya baiwa Sarki Garzub
nasa dokin.Cikin hanzari gimbiya Sulaira ta hau
kan dokin sannan ta mikawa Garzub hannunta ya
rike ta janyoshi shima yahau kan dokin ya zauna
a
bayanta.Zamansa keda wuya sai Sulaira ta saki
linzamin dokin ya fita da gudu,ai kuwa sai
wannan
saniya tata tabi bayansu da gudu sannan dakaru
suka rufa musu baya wanda ya baiwa Sarki
Garzub
dokinsa kuwa a kasa ya falfalo da gudun tsiya
bisa kafafunsa.Lokacin dasu sarki Garzub suka
isa nasu
sansanin yakin inda jama'arsu suke sai suka iske
mutane a zazzaune suna hutawa babu wani yaki
da akayi.Al'amarin dayayi matukar basu mamaki
kenan.Kawai sai sukaga an harbo wata wasika a
jikin KIBIYA.Kibiyar tazo ta cake a gaban dokin
sarki Garzub.Cikin hanzari sarkin yaki Zamud ya
sunkuya ya zare kibiyar daga cikin kasa sannan
ya
warware wasikar ya soma karantawa a fili kamar
haka:-Takarda daga sadauki Sharkas sarkin yakin
birnin Darul Nusur zuwa ga sarki Garzbu na birnin
Hirtoliya.Ykaia wannan sarki ka sani cewa mun
fafata yaki nida kai a karo na farko bakaji dadi ba
kuma ka tabbatar da cewa ruwa ba sa'an
kwando
bane.In badon kayi sa'a ba mun rikito kasa tare
daga kan tsauni duk mun suma ba da tuni na cire
maka kai.Ina maiyi maka mugun albishir da cewa
gobe da safe zamu cigaba da wannan yaki na
ganin ido,a sannan ne zanyi maka KISAN GILLAH
a
gaban jama'rka.Dama na sani cewa kai mai
kishin
jama'arka ne da kasarka don haka dole ne ka fito
daga cikin wannan kogon dutse da kuka buya kai
da sabuwar matarka Sulaira.Lallai a gobe bayan
na
kashe ka zan yiwa matar taka fyade sannan
itama na sassarata gunduwa gunduwa.Koda jin
wannan
jawabi sai zuciyar sarki Garzub ta kama tafarfasa
kamar zata kone saboda fishi.Gaba dayan jikinsa
ya kama tsuma ya yunkura da nufin ya zare
takobinsa ya ruga izuwa sansanin su Sharkas sai
su Zamud sukayi sauri suka rirrikeshi suna masu
bashi hakuri da tausasa zuciyarsa.
Da kyar da sidin
goshi suka shawo kansa in badan ma Sulaira ta
rungumeshi ta fashe da kuka da basu isa su
hanashi zuwa inda sadauki Sharkas yake
ba.
Lokacin da Sarki Garzub ya shiga cikin tantinsa
sai ya iske Sulaira a zaune ta kifa kanta bisa
guiwoyinta tana ta faman rusa kuka.Al'amarin
daya
matukar DUGUNZUMA hankalinsa kenan ya
karasa
gareta da sauri ya durkusa a gabanta ya dago da
habarta da hannunsa suka dubi juna sa'adda
hawaye ke shatata bisa kumatunta ya dubeta
cikin
alamun matukar damuwa yace yake matata ina
dalilin wannan kuka naki?
Dajin wannan tambaya
sai Sulaira ta rungume
sarki Garzub ta sake fashea da matsanancin
kuka
kamar bazata daina ba.Daga can sai tayi ajiyar
zuciya cikin shasshekar kuka tace yakai mijina
kayi sani cewa ba wani abu bane yasa kaga nake
wannan kuka ba face sanin daga gobe shike nan
mun rabu har abada ba zamu sake saduwa
ba.Ina
ji a jikina cewa bamu da nasara a wannan yaki
da
za'ayi gobe.kai kanka ka sani cewa Sharkas
yafika
karfi,jarumtaka da zafin nama.Tabbas ba zaka
iya hallaka shi ba.Idan kuwa har baka hallakashi
ba
lallai sai ya hallakamu da dukkan mayakanka
sannan ya cika mugun nufinsa a kaina.Daga nan
kuma ya wuce izuwa birninka ya cika babban
burinsa.Kaga kenan ni da kai duk bamu cika
wasiyayyar iyayenmu ba.Sa'adda Sulaira tazo
nan a zancenta sai sarki Garzub yasa hannunsa
ya
share mata hawaye sannan yace yake matata ina
son ki sani cewa takin dake tsakanin TSIRA DA
HALAKA dan kankani ne.Mai rai baya cire
tsammanin samun rabo koda kuwa a bakin kura
yake.
Na sani cewa kin karaya bisa yakin da za'ayi
gobe kuma kin tsorata ainun,Abinda nakeso dake
shine idan har kinyi imani da son da kikeyi min a
cikin zuciyarki na gaskiya ne to ki dauka cewa
tabbas sai na sami nasara akan wannan yaki
koda
kuwa bayn nasarar zan hallaka.Inason ki sani
cewa tun kafin na fito wannan yaki na gana da
abin dogarona ubangiji Laruta ya tabbatar mini
da
cewa bazan hallaka ba wannan yaki amma akwai
wani abu wanda zai sameni wanda yaki sanar
dani
ko menene.Ni kam naji a jikina cewa bazan
mutum ba'a wanna yaki kuma ke ma ba zaki
mutu
ba kuma da izinin Larruta sai mun cika burin
iyayenmu.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya
lullube Sulaira ta kara kankame Sarki Garzub a
cikin kirjinta ta shiga Shasshafa jikinsa.Nan dai
suka wanzu a cikin SOYAYYA irin ta ma'aurata
har
suka gusar da bukatar juna.
Washe gari da sassafe
sa'adda hasken rana ya hudo aka buga tambarin
cigaba da yaki aka rinka busa algaita.Nan da nan
dakarun yaki suka fito filin daga bisa dawakai a
sahu sahu.
Bangaren sarki Garzub suna sanye da
bakaken tufafi gaba dayansu.Su kuwa bangaren
su
Sharkas fararen tufafo suke sanya.Idan daga
nesa mutum ya hango wannan dandazo guda
biyu na
mayaka sai yayi tsammnin cewa fari ne da
tururuwai sukayi cinkoso.Nan take sarki Garzub
ya
tsaya a gaban tasa rundunar sanye da bakin
sulke
a jikinsa na karfe sama da kasa hatta kansa ya
rufeshi da hular karfe kuma yana rike da zabga
zabgan takubba guda biyu bisa farin ingarman
doki.
Tsayuwar sarki Garzub keda wuya sai akaga
dakarun Sharkas sun buda hanya a tsakiyarsu
saiga Sharkas ya ratsa ko riga babu a jikinsa
daga
sai wani dogon wanda na fata sai kuma dogon
takalimi karfe yana rike da wannan tafkekiyar
takobi tasa.Hakika duk inda kato yakai Sharkas
ya
cika abin misali domin ya kasance dogo kuma
kakkaura wanda duk jikinsa a murde yake tamkar
dutwasu aka jera.Kallo daya mutum zaiyi masa
yasan cewa sadauki ne shi na gaban
kwatance.Idan yana tafiya ita kanta kasa rawa
takeyi saboda nauyinsa,shi kadai sai kaji yana
wani
huci kamar na rikakken zaki.Koda Sharkas ya iso
gaban dakarunsa sarki Garzub yayi arba dashi
kuma ya kare masa kallo sama da kasa sai yaji
zuciyarsa ta buga da karfi domin bai san cewa
haka surar jikin sharkas take,domin wancan
karon ba'a tube ya ganshi ba.Nanfa ya gane
kurensa ya
tabbatar da cewa yau fa ya taro abinda yafi
karfinsa.Nan da nan aka fara kallon kallo
tsakanin
Sharkas da sarki Garzub.A wannan lokaci Sulaira
nacan baya cikin tsakoyar dakarun Garzub tana
hango filin yakin zuciyarta na ta daka tamkar
zata faso kirjinta ta fado kasa don tsananin
firgita.Ba
zato ba tsammani sai akaji Sharkas ya bushe da
mahaukaciyar dariya wacce kararta ta cika dajin
gaba daya da amsa kuwa.
Lokaci guda Sharkas ya
murtuke fuskarsa ya nuna Garzub da dan
yatsansa
yace yakai wannan sarki Mai Taurin Kai kayi sani
cewa yaune ranar kure karya,kuma yau ne ranar
da za'a bambance tsakanin aya da
tsakuwa.Tabbas kayi ganganci da rayuwarka
data
jama'arka domin inda kabi umarninmu da tun
farko kai da jam'arka kun tsira daga masifarmu
amma yanzu lokaci ya kure dole ne ku fada cikin
hallaka.Ka yi sani cewa nida kai ne zamu fara
bude
fagen wan yaki.Da zarar na gama hallaka ka sai
mu fadawa jama'arka na kamo matarka da
hannuna na idda bakin burina a kanta.Kafin
Sharkas ya gama rufe bakinsa sai aka ga sarki
Garzub ya diro daga kan dokinsa cikin zafin
nama da kunan rai ya falfalo da matsanancin
azababben
gudu izuwa inda Sharkas yake tsaye yana mai
daga takubbansa biyu sama yana tsala ihu da
kururuwa.
Ai kuwa yana riskarsa suka kacame da
azababben yaki wanda ya dugunzuma hankalin
kowa wajen domin yaki ne irin wanda ba'a taba
ganin kamarsa ba.
Sharkas da Garzub suka rinka
kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin
nama,juriya da mugun nufi.
Nima ganin wannan azababben yaki da ake
gabzawa yasa na tsaya
cak domin na kalla.
TSIRA DA HALAKA!!!
Littafi Na Daya (1)
Part F
Cikin tsananin zafin nama,juriya da mugun
nufi.
Duk sa'adda takubbansu suka hadu sai kaga har
tarwatsin wuta ne ke tashi.Wannan karon dai
saida
suka shafe sa'a guda suna gumurzu dayansu bai
sami nasarar koda lakutar jikin daya ba duk da
cewa karfin saran Sharkas da kaifin takobinsa
ya
ninka na Garzub sau uku.Shi kansa Sharkas yayi
matukar mamaki bisa ganin irin kokarin da
Garzub
yayi a wannan lokaci ya rinka kare hare
harensa
yana jure karfinsa.Koda Sharkas yaga Garzub
na
bata masa lokaci saiya fusata yayi jifa da
takobinsa
ya tsaya cak a waje daya ya dunkule
hannayensa
kawai.Koda Garzub yaga haka sai ya cika da
murna ya ruga garesho cikin mugun nufin ya
daddatsa shi da wadannan takubba nasa guda
biyu.Tun daga nesa tazarar taku shida Garzub
ya
dako tsalle sama ya kaiwa Sharkas mugayen
sara
guda biyu da nufin ya fille masa kai kuma ya
raba
masa allon Kafadarsa gida biyu.Kawai sai akaga
shima Sharkas ya daka tsalle sama tamkar an
harbashi da kibiya kuma ya gocewa dukkan
harin
Garzub ya danki makoshinsa sai gashi Garzub
yana wutsil wutsil a sama da kafafunsa kamar
yaro
ya rike jelar dan tamilo.Suna durowa kasa
Sharkas
ya dunkule hannunsa ya gabzwa Garzub naushi
aka.Saboda karfin naushin saida hular karfen
dake
kan Garzub ta tarwatse ta kakkarye tayi filla
filla.Garzub ya sulale kasa zai fadi cikin mugun
hali
mai kama da suma,sai Sharkas ya sake cafo
makoshinsa ya cigaba da gabza masa naushi a
ciki da fuska yayi ta jera masa naushin sai
gashi
Garzub na aman jini ta baki da hanci.Koda
Sulaira
ta hango wannan al'amari dake faruwa sai ta
kwala
ihu ta sulale kasa sumammiya.Gaba dayan
dakarun
Garzub sai dukkaninsu suka kama koke koke
suka
fara tunanin neman hanyar gudu.Kamar
dakarun
Sharkas sunsan abinda ke shirin faruwa sai
suka
ruga da gudu izuwa kansu filin ya hautsine aka
ruguntsume da azababben yaki.Lokacin da
Sharkas
yaga ya luguiguita Garzub matuka sai ya sakeshi
ya fadi kasa ya take kirjinsa da kafarsa
gudu.Nan
take ya zaro wata sharbebiyat wuka ya cakata
akan
tsohon raunin Garzub.Garzub ya kwala ihu
sakamakon mugun zafi da yaji kuma jini

1 Comments On TSIRA DA HALAKA 1 and 2
avatar
hafeez-dalhatu

10 months ago

Reply

Godiya

Please Login or Register in order to submit comment