Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara
kallon kallo tsakanin yarima Uzaima da Sadauki
Kularu ya zamana cewa kowannensu yaji a jikinsa
cewa ya gamu da gamonsa domin alamar karfi
tana ga mai kiba.Sarki Garzub ya bushe da dariya
sannan ya hade fuska yace ni nafi karfin na
sakeyin fada dakai saidai nayi da ubangidanka
sarki Madarus tunda mun gwabza a baya mun
gama fitar da raini.Koda jin wannan batu sai sarki
Madarus yayi murmushin mugunta sannan yace ai
haka za'ayi.Yanzu ni,Sharkas da Sadauki Kularu
zamu fara bude fagen yaki daku ku ukun.Bayan
mun sami nasara akanku ko kuma kun samu sai
acigaba da yaki.Sarki Garzub yace mun amince da
hakan.Nan take Sarki Madarus ya sauko daga kan
dokinsa ya cire alkyabbar dake jikinsa saiga
damatsansa sun firfito fili.Koda yarima Uzaima
yaga irin siffar jikin sarki Madarus yaga kuma da
mahaifinsa zai gwabza yaki saiya firgita ainun ya
matsa daf da sarki Garzub yace yakai Abbana ka
kyaleni na tari sarki Madarus kai ka tari
Sharkas,sarkin Yaki Zamud ya tari Kularu.Dajin
haka sai sarki Garzub yayi murmushi sannan yace
ai nafi shakkar Kularu kan sarki Madarus domin
shi sarki Madarus ya fara manyanta kamar yadda
nima na manyanta.Ko shakka banayi akwai iyakar
lokacin da zai gaji.Zahiri nasan cewa sarki
Madarus yafi ni sadaukantaka kuma yafi Kularu to
amma zaifi kyau yaro ya tari yaro tsoho ya tari
tsoho.Gama fadin hakan keda wuya sai shima
Sarki Madarus ya sauko daga kan dokinsa yana
mai zare takobinsa ya matsa daf da Garzub aka
fara kallon kallo.Shima Zamud ya sauko daga kan
nasa dokin saboda kasancewarsa musaki mai
Hannu daya da kafa daya.Sarkin yaki Zamud ya
zare takobinsa ya tari Sharkas.Koda yazo daf dashi
sai Sharkas ya dubeshi yayi murmushin mugunta
yace sarkinku ya tsorata da dana ya kasa tararsa
yaje ya tari sarkinmu bai san cewa ajalinsa ya
kirawo kusa ba domin masifar sarki Madaru ta
ninka ta Kularu sau dari.Ina mai tabbatar maka
dacewa a cikin dakika dari da tamanin zan maida
kai abincin ungulu.Koda jin haka sai Zamud ya
dakawa Sharkas tsawa yace kai wawa karyarka
tasha karya domin ka hadu da daidai da
kai.Tabbas zan baka mamaki zan nuna maka
tsantsar kwarewata da sanin makama irin wacce
kake takama da ita.A bangaren Yarima Uzaima da
sadauki Kularu kuwa har suka zo daf da juna
dayansu bai zare makaminsa ba.Sai kawai suka
cigaba da kallon juna kowannensu zuciyarsa cike
da sake sake da tunani kai da gani kasan cewa
KAR TA SAN KAR ce.Babu abinda zai baiwa
mutum mamaki face yadda tsawo,kaurin jiki da
murdewarsu yazo daidai tamkar Hassan da Husaini
tsakanin Yarima Uzaima da Sadauki Kularu.Hatta
kwarjininsu iri dayane inda suka bambanta kawai
shine a kamannin fuska.Shima Sadauki Kularu
saurayi ne kyakyawa abin misali amma bai kai
Yarima Uzaima ba kuma shekarunsa daidai dana
Uzaima suke domin rana daya aka haifesu.Tun
Kularu yana yaro karami dan shekara takwas yake
tsananin son gimbiya Zarilaf har suka girma tare
amma daidai da rana daya bai taba samun ganin
murmushinta ba bare ya sami nasarar da zai iya
furta mata abinda ke ransa.Saida takai cewa kowa
a kasar yasan cewa Sadauki Kularu yana matukar
son Gimbiya Zarilaf amma ita ko kadan bata
sonsa.Kai ko sunansa bata son taji an ambata.comments TSIRA DA HALAKA!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part D
.
REAL RAYYANU SAEEd
.
Kai ko sunansa ma bata son taji an ambata.Babu
irin abinda Kularu baiyi ba domin Zarilat ta so shi
amma abu ya gagara har saida ta kaishi ga kai
ziyara ga bokaye a kasashen nahiyar su amma
duk
wajen bokan da yaje sai yace dashi babu abinda
zai iyayi masa yasa Zarilat ta soshi.Da kyar ya
sadu da wani takadirin boka wanda ya gaya masa
cewa idan har yana son ya sami karbuwa a wajen
gimbiya Zarilat dole ne yayi gagarumar bajinta a
yakin da za'aje ayi a can nahiyar bakaken fata ya
zamana cewa tafi kowa jarumtaka.Lallai idan
yayi
haka Zarilat zata soshi ainun harma ta
aureshi.Bisa
ga wannan dalili ne Sadauki Kularu ya ZAGE
DAMTSE wajen baiwa kansa horon yaki dare da
rana har tsawon shekaru bakwai ya zamana cewa
yaji a jikinsa cewa zai iya tarar kowanne sadauki
a
duniya komai kwarjininsa da KARFIN
DAMTSENSA.A bangaren tsafi kuwa sadauki
Kularu
ya tafi yayi nisa domin masu bincike sun gano
cewa a gaba dayan nahiyarsu sarki Madarus ne
kawai akan gabansa.A halin yanzu sadauki Kularu
bashi da fargabar komai a zuciyarsa duk daya
karewa Uzaima kallo ya fuskanci cewa sadauki ne
shi na gaske wanda za'a fafata amma aby daya
ne
ya karya masa zuciya.Ba kuma wani abu bane
face
ya lura da lokacin da gimbiya Zarilat tayi arba da
Uzaima tayi masa wani irin kallo mai dauke da
ALAMAR TAMBAYA kuma ta kura masa idanu ko
kiftawa batayi.Abinda Kularu ya tambayi kansa
shine shin kwarjini Uzaima ne yasa Zarilat ta
kura
masa idanu ko kuwa kyawunsa ne ya ribaceta
har
ya burgeta?Nanfa Kularu ya kasa baiwa kansa
amsar wannan tambaya.Abinda ya kudurce a
ransa
shine duk wuya duk rintsi saiya siye zuciyar
gimbiya Zarilat a wannan yaki da za'ayi don haka
yanzu zai fara wannan yaki ne da mugun nufi
wato
yana son duk wanda ya fara haduwa dashi yayi
masa kisan gilla farat daya.Bayan jaruman shida
sun tsaya daf da juna anyi kallon kallo na tsawon
dan lokaci sai aka buga gangar yaki.Nan take aka
ruguntsume da azababben yaki a tsakanin
jaruman
shida.Sadauki Sharkas ne kadai akan doki.Babu
fadan da ya zama mafi ban tsoro face fadan
manyan zakuna biyu,wato fadan sarki Madarus
da
sarki Garzub domin bambancin a baiyane yake
wato karfin sarki Madarus da zafin namansa ya
ninka na sarki Garzub sau uku.Tunda suka fara
gumurzun ko sau daya sarki Garzub bai maida
martani ba in ba don ma yana da matukar juriya
da naci ba da tuni sarki Madarus yayi masa kisan
farat daya.Babu abinda ya tsorata sarki Garzub
sama da azababbiyar takobin dake hannun sarki
Madarus wacce ta kasance sihirtacciya domin duk
sa'adda sarki Madarus ya kawo masa sara da ita
ya goce tofa ko kasa ya samu sai kaga ta dare
kuma ko dutse ya samu sai ya rabashi gida biyu
kuma ko dakushewa takobin batayi.Al'amarin
daya
dugunzuma hankalin sarki Garzub kenan domin
yasan cewa idan aka sami koda tsawon rabin
sa'a
ne a haka sarki Madarus zai iya galabaitar dashi
ya gaji da zarar ya gaji kuwa take zaiyi masa
kisan
farat daya.A bangaren Sarki Madarus kuwa shima
yayi tsananin mamaki bisa ganin yadda ya kasa
kashe sarki Garzub nan da nan domin a tarihin
sadaukantakarsa da yake yaken da yayi bai taba
haduwa da wani jarumi ba wanda ya kasa
kasheshi
a tsawon dakika sittin ba sai yau.Nanfa zuciyarsa
ta kama tafarfasa ya kara zage damtse wajen
kaiwa
Garzub sara da suka cikin tsananin zafin
nama.Shi
kuwa Sarki Garzun zage damtse yayi waken kare
kansa.A bangaren su Sharkas kuwa da sarkin
Yaki
Zamud yaki yayi tsamari a tsakaninsu.Shidai
sadauki Sharkas dama yana kan doki.Sadauki
Sharkas ya zaburo dokinsa da gudu yayi kan
Zamud da niyar da danneshi.Wohoho!Hakika karfi
yana da ranarsa domin in badon Zamud ya kasan
kakkarfan gaske ba da tuni dokin ya
danneshi.Idan
mutu yaga yadda kwanjin Zamud ya kumbura
dole
ne yasan cewa ya cika Sadauki.Ba zato ba
tsammani sai akaga Zamud yayi jifa da dokin
Sharkas,take Sharkas ya wantsulo kasa suka baje
a
kasan tare da dokin nasa.Cikin zafin nama
Sharkas
ya dogara sandarsa ya mike tsaye da kafarsa
daya
ya sake daga takobin tasa ya fuskanci
Zamud.Koda
Zamud yaga zaiyi yaki da mai kafa daya da
hannu
daya saiya bushe da dariya uace ai dama dokin
kane ya ceceka a dazu don haka yanzu karyarka
tasha karya mutuwarka tazo.Sharkas ya dubi
Zamud cikin murmushi da raini sannan yace ai
fada ba cikawa bane lallai sai an gwada akan san
na kwarai.Ina sauraron ka nuna mini iyakar
jarumtakarka da kwarewarka na gani.Ka sani
cewa
sarkinka ma baiji da dadi ba a wancan karon da
muka gwabza tsananin sa'a ce tasa ya sami
nasara a kaina kawai.Gama fadin hakan keda
wuya
sai Zamud ya daga takobinsa sama ya kwarara
uban ihu ya ruga izuwa kan Sharkas.Sharkas ya
tsaya cak a inda yake ko motsawa baiyi ba suka
kacame da sabon azababben yaki.A bangaren
sarki
Garzub kuwa da sarki Madarus al'amura sun
sauya
salo domin tuni sa'a daya ta shafe da fara
gumurzunsu,a sannan nefa ido ya raina fata a
wajen sarki Garzub domin ya fara gajiya har takai
cewa da kyar yake iya tare mugayen hare haren
sarki Madarus.Suna cikin haka ne sarki Madarus
ya shammaceshi ya dankara masa sara a saman
cibiyarsa.Duk da Garzub yayi kokarin kare saran
saida takobin Madarus ta yankeshi wajen ya dare
jini yai tsartuwa.Sarki Garzub bai san sa'adda ya
kurma ihu ba yai tsalle ya fadi kasa.Madarus ya
kawo masa wawar suka a ciki da tsinin takobinsa
ya goce takobin ta nutse a cikin kasa gaba
dayanta.Kafin ya zaro takobin ne Garzub ya dage
iya karfinsa ya kirba masa naushi a fuska.Saboda
karfin naushin saida Madarus yayi taga taga da
baya kamar zai fadi.Take idonsa guda ya lunkume
fuskar ta kumbura.Wannan shine karon
farko da sarki Garzub ya sami nasarar taba jikin
Madarus tunda suka fara yaki.Shi kuwa Madarus
dama tuni ya hadawa Garzub jini da majina
saboda
yawan naushi.Cikin tsananin fusata sarki
Madarus
ya sake zaro wadansu gajerun adduna guda biyu
dake jikin cinyoyinsa a daure ya ruga inda Garzub
ke kwance da nufin ya daddatsashi tunda ya
kaishi
kasa.Yayin daya rage saura taku uku kacal ya iso
kansa sai kawai yaga Garzub ya yunkura cikin
bakin zafin nama ya mike tsaye zumbur tamkar
sifirin sannan ya yagi suturar jikinsa yayi gammo
da ita a zagayen cikinsa wato ya daure raunin da
ita don tsaida jini ya tari Madarus suka cigaba da
bakin artabu.Wannan karon dai sai gashi
kowannensu yana iya kare hari da maida
martani.A bangaren zaratan matasa biyu kuwa
wato yarima Uzaima da Sadauki Kularu abin ya
zama ba kyan gani.Hatta sauran dakaru na
kowannen bangare dake tsaitsaye suna kallon
abinda ke faruwa kowa hankalinsa ya dugunzuma
ainun domin kare jini biri jini suke saboda karfi
yazo daya.Da farko saida suma suka shafe sa'a
guda cur suna kaiwa juna sara da suka cikin
tsananin zafin nama,juriya da bajinta,ya zamana
cewa dayansu bai sami nasarar koda lakutar jinin
abokin gwaminsa ba.Da kansu suka ja da baya
sukayi cirko cirko suna kallon juna suna
haki.Daga
can sai suka rugo da gudu suka sake kacamewa
da yaki amma a cikin sabon salo na tsalle tsalle
da kwance kwance.Abinda ya baiwa kowannensu
mamaki shine salo iri daya sukeyi.A wannan
karon
ne Kularu ya sami nasarar yankar Uzaima a
gadon
baya wani irin dogon yanka.Uzaima ya kurma ihu
saboda mugun zafi da zogin da yaji amma
saboda
juriya da naci irin na Uzaima bai fadi kasa ba sai
ya daka wawan tsalle sama bayan ya dafa kasar
da
tafin hannunsa tamkar an cillashi daga cikin
baka.Kularu bai ankara ba sai ganin Uzaima yayi
a
sama ya shallakeshi.Kularu ya juya da sauri
domin
ya kawo masa wani harin amma sai yaji tuni
Uzaima ya dankara masa dogon sara a
kirji.Kularu
ya kwalla ihu sakamakon jini da yai tsartuwa a
kirjin nasa yayi baya taga taga kamar zai fadi
amma saiya tsaya cak.Kawai sai ya rike
takobinsa
da hannayensa biyu a lokacin da jiri ke dibarsu su
biyu.Koda suka fahimci halin da suke ciki sai
kowannensu ya tsaya ya daure raunin jikinsa don
tsaida jini sannan suka sake ruguntsumewa da
masifaffen yaki.Saida suka sake shafe rabin sa'a
a
haka sannan Kularu ya sami nasara a karo na
biyu
ya sari Uzaima a gefen cikinsa.Kafin Kularu ya
dauke takobinsa tuni Shima Uzaima ya rama
saran
da yayi masa kuma shima a gefen ciki.Lokaci
guda
suka fadi kasa tare kowannensu ya kasa
tashi.Adaidai wannan lokaci ne Uzaima ya juya
ya
dubi bayansa inda ake fafatawa tsakanin sarki
Garzub da sarki Madarus,kawai sai ya hango
Madarus ya lumawa Garzub takobi a cinya ta
hudo
ta baya.Yana zare takobin Jini yayi
tsartuwa.Garzub ya kurma uban ihu.Madarusi bai
kyale Garzub ba sai yasa kafa ya doki kirjinsa yai
tsalle sama ya fado kasa ya baje a cikin mugun
hali,Madarus ya ruga izuwa kan Garzub yana
kururuwa cikin mugun nufi.Yana isowa daf dashi
ya daga wannan sihirtacciyar takobi tasa da nufin
ya tsargeshi gida biyu kawai sai akaga Uzaima
ya
sake dako tsalle daga inda yake ya doki kirjin
sarki
Madarus da kafafunsa biyu.Saboda karfin dukan
saida Sarki Madarus yai sama sosai sannan ya
rikito kasa a matukar galabaice.Kofa dakarun
sarki
Madarus sukaga abinda ya faru ga sarkinsu sai
suka yunkura gaba dayansu suka afkawa dakarun
sarki Garzub.Nanfa filin yakin gaba daya ya
hautsine aka bar batun fidda raini a tsakanin
sadaukan shida.Aka ruguntsume da azababben
yaki cikin zafin nama.Uzaima ya suri mahaifinsa
Sarki Garzub ya goyashi a bayansa sannan ya
cigaba da yaki a haka yana ragargazar maza
yana
kutsawa ta cikinsu da karfin tsiya yana sare na
sarewa kuma yana banke na bankewa,kokarinsa
kawai shine ya koma can baya inda farkon
dakarunsu suke wato inda tantin sarki yake
domin
ayi masa magani a ceci rayuwarsa daga hallaka
sakamakon jinin dake ta zuba a jikinsa mai
yawa.Tunda Uzaima yazo duniya hankalinsa bai
taba dugunzuma ba sama da na wannan rana
kuma ransa bai taba baci ba kamar haka domin
yana yakin ne da dukkan karfinsa a lokacin da
zuciyarsa ke tafarfasa.Gaba dayan dakarun dake
filin yaki saida suka cika da mamakin irin wannan
gagarumar jarumtaka da Uzaima keyi musamman
da akaga an rasa wanda zai sha gabansa ya
tsaidashi.Duk ta inda aka kawo masa hari walau
gabas da yamma ko kudu da arewa sai aga ya
tare
harin.Wanda zai iya tarar tasa a wannan lokaci
mutum biyu ne kacal daga sarki Madaru sai
Sadauki Kularu.Su kuwa duk sun haukace akan
daukar rayukan dakarun sarki Garzub duk inda
suka ratsa saidai kaga mazaje na zubewa.Shima
sarkin yaki Zamud haka ya rinka ragargazar
dakarun Madarus.Kuma duk sa'adda ya hango
Sharkas na kokarin hawa kan dokinsa saiya ruga
inda yake ya kashe dokin su cigaba da artabu.Ba
abinda zai baiwa mutum mamaki a wannan yaki
face yadda sadaukai ke nuna tsantsar jarumtaka
domin sai kaga sadauki da raunika manya a
jikinsa
yana ta zubar da jini amma yaki zuwa kasa yana
dada ragargazar maza.Kaico!Yau fa ranar cinikin
rayuka,ga inda aka baje kolin gawa kuma ga inda
kogin jini yake ambaliya.Kowa ka gani a filin yaki
sai kaga anyi masa wankan jini.Hatta fuskokin
jamaa sun shafe da jini saidai kaga suna share
idanunsu don kada jini ya hanasu gani.Duk
wannan jarumtaka da Uzaima keyi ashe gimbiya
Zarilat na hangowa daga can karshen baya inda
tantin sarkinsu yake.Koda Zarilat taga irin
gagarumar bajintar da Uzaima yayi sai nan take
taji
yayi matukar burgeta.Nan take Sonsa ya shiga
zuciyarta ya mamaye amma data tuna
cewa makiyi ne a gareta sai ta fara tunanin
yakice
shi daga cikin zuciyarta.Kularu na cikin
ragargazar
dakarun Garzub sai ya hango can tsakiyar filin
yakin inda Uzaima keta tsala gudu yana dauke da
mahaifinsa a baya yana kutaswa ta cikin
miliyoyin
abokan gaba har yaje tsakiyar.Tabbas nan da
wasu
dakiku kamar dari uku da doriya zai iya zuwa
inda
tantin sarki Garzub yake a sami damar yi masa
magani cikin gaggawa.Koda ganin haka sai
Kularu
ya daka tsalle sama ya rinka gudu akan kawunan
mutane ya durfafi inda Uzaima yake.A wannan
lokaci ne Kularu ya nuna tsantsar zafin namansa
domin duk sa'adda ya taka kan Abokan gaba sai
kaga sun kawowa kafafunsa sara amma babu
wanda ya tabashi har ya dira a gaban Uzaima
yasha gabansa.Bisa dole Uzaima ya tsaya cak a
waje daya yana mai sara abokan gaba masu afko
masa kuma suka fara kallon kallo shida
Kularu.Shima Kularu bai fasa saran dakarun su
Uzaima ba tunda filin yakin a yamutse yake gaba
daya.Duk mai tsautsayin da yazo ta gabansu ko
ta
bayansu ko ta gefe take yake zama gawa.Bisa
dole
akatarwatse daga kusa dasu aka cigaba da yaki
a
nesa kadan dasu domin sun zama dodanni a fili
dagar.A sannan ne Kularu ya dubi Uzaima ya
kyalkyale da dariyar mugunta sannan yace kana
zaton zaka sami nasarar kai mahaifinka can
tantinsa ne alhalin ina nan a filin wannan yaki?
Tabbas kayi babban kuskure da kake tunanin
zaka
sami nasarar yin hakan.Tabbas kayi dabara daka
ceci rayuwar mahaifinka daga sharrin Sarki
Madarus saidai kayi gudu ne na banza wanda
babu
wajen zuwa.Ko shakka banayi yanzu zan kashe
mahaifinka nayi masa KISAN GILLAH a gaban
idanunka sannan kaima na kasheka.Hakika idan
nayi haka na gama cika burina domin na gama
siye zuciyar abar begena.Cikin tsananin mamaki
Uzaima ya dubi Kularu yace wace kuma abar
begenka?Maimakon Kularu yace wani abu sai
yayi
nuni da takobinsa izuwa can inda sansaninsu
yake
wato inda suka kafa tantuna.Uzaima ya dubi can
wajen saiya hango Gimbiya Zarilat tsaye akan
wani
dogon dutse ta rufe fuskarta da farin kyalle mai
shara shara kuma ta kura masa idanu.Kularu ua
dubi Uzaima yana mai cigaba da bayani yace kai
kadai ne sadaukin da yayi gagarumar jarumtaka a
bangaren abokan gabarmu.Lallai idan na kasheka
a yanzu na nuna cewa jarumtakata tafi
taka.Adaidai
wannan lokaci ne sarki Garzub ya budi baki da
kyar yace yakai dana ka ajiyeni ka tari wannan
yaro domin ni tawa ta kare bazan iya tsinana
komai ba a wannan yaki.Koda jin haka Sai
Uzaima
ya girgiza kai yace Yakai Abbana kayi sani cewa
ba
zan iya ajiyeka ba makiya su hallaka.Lallai ta
kowane hali sai na kaika tantinka.Kularu bai isa
ya
hanani ba.Kafin Uzaima ya gama rufe bakinsa
tuni
Kularu ya daka tsalle ya dira a gabansa ya kawo
masa wawan sara da nufin ya tsarge kafadarsa
gida biyu,cikin zafin nama ya goce suka ci gaba
da artabu sai gashi Uzaima yana yin gagarumar
jarumta ta gaban kwatance wadda ta shallake
tunanin shi kansa Kularu,domin Uzaima yana yaki
dashi kuma yanayi da sauran dakarun su Kularu
yana kutsawa ta tsakiyarsu da karfin tsiya.Kiri kiri
Kularu ya kasa taba jikin Uzaima duk da cewa
yana
kai masa SARA DA SUKA ta ko ina kuma shima a
hakan yana yakar dakarun su Uzaima.Ba zato ba
tsammani sai Kularu yaga Uzaima ya zabura ya
falfala da azababben gudu ta cikin dakaru yana
bankesu da karfin tsiya yana samarwa da kansa
hanya.Ana saransa jini na tsartuwa amma yaki
ya
fadi kasa kuma gashi yana goye da mahaifinsa
sarki Garzub yaki yarda ya yar dashi.Kularu yabi
Uzaima da gudun tsiya domin ya sake shan
gabansa ya hanashi kaiwa can karshen inda
dakarunsu suke wato inda tantin sarki Garzub
yake,amma sai ya kasa cimmasa domin inda
Uzaima ke shiga wuri ne inda Dakarunsu sukafi
tsananin yawa don tabbatar da tsaro ga tantin
sarki don haka sai dakarun suka rinka lullube
Kularu.Tunda sarkin yawa yafi sarkin karfi dole ya
rinka komawa da baya da karfin tsiya domin ya
ceci rayuwarsa saboda indai ya cigaba da
kutsawa
ta cikinsu tabbas sai ya gaji da yaki sun kaishi
kasa.Ashe duk wannan jarumtaka da Uzaima keyi
Gimbiya Zarilat na kallo domin ta sake sulalowa
daga can inda take ta dawo tsakiyar filin yakin
tana
more idanunta bisa ganin yadda ake
RAGARGAZAR
MAZA.Koda Gimbiya Zarilat taga irin wannan
jarumtaka da Uzaima yayi sai taji duk duniya
babu
mutumin da yafi dacewa da ita face
Uzaima.Kuma
a sannan ne ta tabbatar da cewa Kularu bazai
taba
zama abokin rayuwarta ba domin yau gashi taga
jarumin daya fishi tsananin juriya da
jarumtaka.Nanfa Gimbiya Zarilat ta cigaba da
kutsawa ta cikin turmitstsin mutane ba tare da
fargabar komai ba tana karawa gaba da gudu
domin ta sami damar hango irin jarumtakar da
Uzaima keyi.A iya rayuwar Gimbiya Zarilat bata
taba zuwa filin yaki ba kuma ta kasance mai
tsananin tsoro domin ko yaya taga jini ya zuba a
jikin mutum sai ta kama kuka saboda tausayi da
razana,amma ya gashi ana gididdiba
bil'adama,sassan jikinsa ma take tattakawa tana
wucewa amma bata tsorata ba.Ba komai ne ya
janyo hakan ba face kawao son ta cigaba da
kallon
jarumin daya burgeta a cikin filin yakin wato
yarima Uzaima.Ba komai ne yasa Zarilat ta sami
damar sulalowa ba daga inda ake tsare da ita ba
face yadda filin yakin ya hargitse ya zamana
cewa
yakin yayi tsamari ainun kowanne bangare sun
firgice sun dimauce an koma neman TSIRA.Duk
da
cewa dakarun su sarki Madarus sunfi yawa ainun
amma sai gashi ana KARE JINI,BIRI JINI domin
kowanne bangare yana gane kurensa,mazaje nata
zubewa kasa matattu.A can tsakiyar filin yaki
kuwa
sarki Rakalu ya hakura da bin bayan Uzaima don
bashi tsaro na musamman saboda bala'in yakai
bala'i.A wannan lokaci
comments and like TSIRA DA HALAKA!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part E
Al'amarin Yarima Uzaima da Gimbiya Izaima kuwa
suma kai tsaye suka wuce izuwa nasu sansanin.Da
zuwa sai dakaru suka rugo da gudu suka sauke
sarki Garzub daga kan doki aka shigar dashi cikin
tantinsa aka kwantar dashi akan gado.Wannan
karaya ta yan yatsun hannunsa aka fara gyarawa
sannan aka cigaba da duba sauran jikinsa.Koda
babban likitan nasa yaga wannan kashin baya ya
karye sai hankalinsa ya dugunzuma ainun,domin
yasan cewa kashine wanda koda an dorashi har
abada mutum ba zai iya mikewa ba tsare bare har
yayi tafiya.Saidai ya cigaba da rayuwa a kwance
har izuwa lokacin da rayuwarsa zata kare.Lokacin
da aka fara yiwa sarki Garzub gyaran wannan
karaya ta kashin bayansa saida ya suma sau shida
saboda tsananin zafi da zogin da yakeji.Bayan an
gama gyaran ne aka bashi maganin bacci
yasha.Bai farka ba sai bayan sa'a hudu.Kafin sarki
Garzub ya farka sai Yarima Uzaima yaja babban
likitan gefe daya ya dubeshi yace yaya jikin
mahaifina?Nan da wane lokaci kake ganin zai samu
lafiyar jikinsa sosai ya mike tsaye ya cigaba da
yaki?Sa'adda babban likitan yaji wannan tambaya
sai hankalinsa ya dugunzuma fiye da ko yaushe ya
sunkui da kansa kas ya kasa cewa komai.Cikin
fishi yarima Uzaima ya cakumi rigar likitan yace
maza kayi mini bayani ko yanzun nan na shakeka
ka mutu.Jikin likitan na karkarwa yace ya
shugaban mahaifinka har abada ba zai iya mikewa
tsaye ba bare ya iya cigaba da yaki.Koda jin
wannan batu sai Uzaima ya kurma uban ihu mai
firgitarwa sannan ya durkushe kasa bisa
guiwoyinsa ya fashe da matsanancin kuka.Gimbiya
Izaima dake can nata tantin a zaune tana kuka
tana tunanin nata mahaifin da ta rasa sai ta jiyo
ihun Uzaima,bata san sa'adda ta mike zumbur ba
ta ruga waje da gudu ta nufi inda Uzaima ke
durkuseh.Da zuwa ta tsuguna a gabansa tace
yakai burin zuciyata ina dalilin wannan kuka naka?
Uzaima ya dago kai da kyar ya dubeta a lokacin da
dukkaninsu suke zubar da hawaye yace yake
Izaima kiyi sani cewa har abada mahaifina bazai
mike tsaye ba ya nakasa.Koda jin haka sai Izaima
ta rungume Uzaima suka sake fashewa da kuka a
tare.Ita dai Izaima dalilin kukanta guda biyu
ne.Dalili na farko tsananin bakin ciki ne bisa ganin
cewa mahaifinta ya mutu,kuma shima mahaifin
Uzaima ya shiga mummunan hali don abu ne
mayuwaci aurenta da yarima Uzaima yayiwu.Dalili
na biyu kuwa tsananin farin ciki ne bisa ganin a
yau kuma a karo na farko ta sami damar kusantar
Yarima Uzaima gashi ma harta rungumeshi a
kirjinta.Tsawon yan dakiku Uzaima da Izaima na
rungume da juna,daga can saiya janye jikinsa daga
cikin nata sannan ya mike tsaye ya kira babban
likita yazo gabansa ya tsaya.Uzaima ya dubi
babban likitan yace dashi abinda nake so da kai
shine kada ka kuskura ka gayawa mahaifina cewa
ba zai mike ba.Lallai ka sanar dashi cewa nan da
wani lokaci zai warke sumul ya mike.Idan ka
kuskura ka saba wannan umarni nawa hukuncin
kisa ne a kanka.Koda gama fadin haka sai Uzaima
ya dubi sauran gaba dayan dakarun dake sansanin
yace dasu.Kuma abinda nake so daku shine kada
dayanku ya tona wannan sirri ga mahaifina wanda
duk ya tona kuwa hukuncin kisa ne a kansa.Abu
na biyu ku zuba ido sosai wajen tabbatar da tsaro
a wannan sansani namu domin a ko yaushe
makiya zasu iya kawo mana hari.Yanzu dole ne
mu saurara izuwa lokacin da sarki zai farka daga
bacci domin muji umarnin da zai bamu.Sa'adda
Uzaima yazo nan a zancensa sai wani sadauki mai
suna Ukazu wanda shine mataimakin sarki yaki ya
dubeshi cikin alamun karayar zuci yace ya
shugabana kayi sani cewa zamanmu anan
sansanin yana da matukar hadari domin a halin
yanzu mun rasa dukkan manyan jarumanmu kuma
kaso biyu cikin uku na mayakanmu duk sun mutu
saura kaso daya.A cikin kaso dayanmu da muka
rage rabi sun afka cikin jeji sun buya.Duk da cewa
mun kashe da yawa daga cikin abokan gaba har
yanzu fa sun ninkamu sau uku a yawa,ko a yanzu
idan suka afko mana nan zasu iya murkushemu a
cikin kankanin lokaci.Yayin da Uzaima yaji wannan
batu sai yayi ajiyar zuciya yace tabbas duk abinda
ka fada gaskiya ne yakai Ukazu amma abinda nake
so ka fahimta shine suma abokan gabar tamu
yanzu a cikin mummunan tashin hankali suke
tunda abin dogaron nasu ya zama nakasasshe
tunda ya rasa kafa daya da ido daya.Sun rasa
sarkin yakinsu da kuma manyan sadaukansu
wanda ya rage musu yanzu sadauki Kularu ne
kamar yadda nima na rage a cikin manyan
sadaukanmu.Abune mayuwaci suyi yunkurin kawo
mana farmaki a yanzu dole sai sun tsaya sun yi
tunani da shawara.Na tabbata shima sarki Madarus
bayan likitocinsa sunyi masa magani dole ne su
bashi maganin bacci kuma bazai farka ba sai nan
da tsawon yan sa'o'i kusan lokacin da namu
sarkin zai farka.Ina tabbatar maka da cewa a yau
dai babu wani yaki da za'a cigaba dayi saidai
gobe.Koda gama fadin haka sai Uzaima ya tafi ya
leka cikin tantin sarki Garzub ya ganshi kwance
yana ta shara bacci.Cikin sanyin jiki ya juya da
baya ya tafi izuwa nasa tantin.A wannan lokaci ne
dakaru suka shiga hidimar daga abinci.Yarima
Uzaima ya zauna a cikin tantinsa yayi tagumi
kuma ya fada tunani mai zurfi.Yana cikin wannan
hali ne yaga an shigo cikin tantin nasa koda ya
daga kai sai yaga ashe Gimbiya Izaima ce dauke
da abinci.Jikinta a sanyaye tazo daf dashi ta ajiye
abincin sannan ta koma gefe daya ta zauna tana
mai sunkui da kanta kas.Koda Uzaima ya dago kai
ya dubeta sai yaga hawaye na zuba a
idanunta.Al'amarin dayai matukar dugunzuma
hankalin Uzaima kenan ya dubeta cikin tsananin
mamaki yace yake gimbiya ina dalilin zubar da
wannan hawaye naki? comments and like to be continued TSIRA DA HALAKA!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part F
Alhalin gata a tsaye a gabansa.A sannan ne ya
fahimci cewa tana da tsarin tsafi mai karfin gaske a
jikinta wanda babu mai iya cutar da ita a filin yakin
gaba daya.Koda fahimtar hakan sai sarki Madarus
ya rabu da Izaima ya ruga izuwa cikin abokan
gaba ya cigaba da yaki,Izaima ta fada kan gawar
mahaifinta ta rungume gawar a kirjinta ta fashe da
matsanancin kuka.Abinda ya kara daure mata kai
shine gashi dai mutane suna ta yaki a kanta suna
ta dudufniya amma ko kadan babu wanda ya taba
jikinta.A sannan ne ta tuno da maganar da
mahaifin nata ya gaya mata cewa muddin tana tare
da wannan Kambun tsafi daya bata babu wani
tsautsayi da zai sameta.Koda ta tuno da wannan
batu saita dada kankame gawar sarki Rakalu a
kirjinta ta kuma rushe da kukan bakin domin tasan
cewa son da yakeyi mata yafi wanda yake yiwa
kansa tunda har ya iya bata wannan kambun tsafi
ya sallama rayuwarsa domin tata.A bangaren
sarkin Yaki Zamud da sarkin Yaki Sharkas kuwa
lokacin da yaki ya sake yin nisa sai suka sake
hadewa suka ciga da masifaffen yaki sai gashi
kowa ya baiwa kowa mamaki domin karfi yazo
daya domin dukkaninsu sunsan cewa yaufa sun
gamu da gamonsu.Duk wanda ya sami nasarar
yiwa dan uwansa rauni sai kaga nan take shima
wanda aka yiwa raunin yayi ramuwar gaiya.Kafin
cikar rabin sa'a sun yiwa junasu muggan sara da
suka sunyi fata fata da jikinsu.Lokaci guda duk su
biyun suka zube kasa matattu dayansu bai sake
shurawa ba.Al'amarin Kularu kuwa lokacin daya
fahimci cewar idan ya cigaba da bin yarima
Uzaima izuwa inda tantin sarki Garzub yake zai iya
rasa rayuwarsa tunda sarkin yawa yafi

1 Comments On TSIRA DA HALAKA 1 and 2
avatar
hafeez-dalhatu

10 months ago

Reply

Godiya

Please Login or Register in order to submit comment