Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sarkin
karfi,saiya hakura bisa dole ya juya da baya ya
cigaba da yaki.Yana yakin yana dada lura da
yanayin yadda yakin yake kasancewa.Abinda ya
daure masa kai shine duk da cewa mayakansu sun
ninka na sarki Garzub sau uku amma gashi har a
sannan sun kasa karar dasu.Kuma komai zuba
idon mutum bai isa ya iya gane bangaren dake
samun nasara ba domin duk bangaren da ka duba
sai kaga jama'arsu nata zuba a kas tamkar
sharesu akeyi da tsintsiya.Gaba daya filin yakin ya
cika da gawarwaki fululu babu kyan gani.Kofaton
dawakai da kafafun mutane sai taka jini suke yana
dada fantsamuwa.Filin yakin ya yamutse ga ihun
mazaje,ga karafkiyar karafa kuma ga kura da jini
sun gallabi al'umma.Wani lokacin saidai kaga kasa
ta hadu da jini ta hade tamkar kwabar gini za'ayi
da ita.Lokacin da Yarima Uzaima ya sami nasarar
kai sarki Garzub cikin tantinsa sai na da nan
likitocinsa suka taru a kansa suka shiga aikinsu.An
shafe lokaci mai dan tsawo sannan ya farfado.Koda
ya bude idanunsa ya dubi inda yake sai ya yunkura
da nufin ya mike tsaye ya fita daga cikin tantin
yaje ya cigaba da yaki.Cikin hanzari da matukar
damuwa Uzaima ya rike kafadunsa ya dubeshi yace
ya kai Abbana kayi sani cewa idan ka fita yaki a
haka za'a iya hallaka ka cikin kankanin lokaci
domin a halin yanzu babu kuzari a jikinka domin
ka zubar da jini mai yawa.Lallai kana bukatar
isasshen hutu.Cikin fushi sarki Garzub ya dubi
Uzaima yace saboda me ka ceci rayuwata?Me yasa
baka bari sarki Madarus ya hallakani ba in yaso ka
tareshi ku cigaba da yakin ko ka kashe shi ko ya
kasheka?Ka sani cewa yanzu haka yana can yana
dada ragargazar mutanenmu.Shin ka mantane
cewa idan suka gama damu anan can birninmu
zasu karasa suje su kama kowa da kowa a
matsayin bayi su kwashe arzikinmu kuma su kone
birninmu yadda har abada za'a manta da
tarihinmu.Mu ne kadai masu iya taka musu birki
bisa wannan mugun nufi nasu.Idan muna nan su
suna can filin yaki nan da kankanin lokaci zasu
karar da dakarunmu,mene amfanin rayuwarmu da
numfashinmu a yanzu?Uzaima yace yakai Abbana
aini yanzu zan koma filin daga kuma na tabbatar
yanzu haka sarki Rakalu da sarkin Yaki Zamud
suna can sun yiwa abokan gaba mummunar
barna.Haka kuma sauran sadaukanmu,wannan
karon suna yaki ne da DAKAKKIYAR ZUCIYA domin
nayi matukar mamaki bisa ganin irin namijin
kokaron da sukeyi a filin yaki.Sarki Garzub yayi
ajiyar zuciya yace duk na gani da idona amma
inason ka sani cewa ganin irin jarumtakar da
mukeyi ne tasa suma sadaukan namu suka
taso.Baka tunanin cewa rashinmu a filin yaki zai
iya janyo musu karayar zuciya?Shin yanzu menene
tabbacinka cewar sarki Rakalu da sarkin yaki
Zamud har yanzu suna nan a raye?Bazan yi hutun
jaki da kaya ba maza ka tashi mu koma filin daga
tunda dai harka sami nasarar kawoni nan kuma
anyi mini magani kayi babbar jarumtaka.Ka sani
cewa karo da sarki Madarus ba karamin bala'i
bane.Koda mu biyu zamu taru a kansa bana zaton
zamu iya hallakashi.Koda gama fadin haka sai
Sarki Garzub ya diro kasa daga kan gadon karfen
da aka kwantar dashi ya gyara damararsa ya nufi
kofar fita daga cikin tantin.Cikin hanzari babban
likitansa yasha gabansa yace ya shugabana idan
ka fita yaki a haka ba zaka iya koda rabin sa'a ba
zaka yanke jiki ka fadi.Cikin harara da tsawa sarki
yace da likitan kauce ka bani hanya kona sareka
da takobina.Kawai sai ya juyo ya dubi Uzaima yace
koda mutum daya jal zan sami nasarar kashewa a
wannan fita da zanyi nima a kasheni na samu
babbar nasara domin na mutu namiji ba rago
ba.Gama fadin hakan keda wuya sai sarki Garzub
ya fita da sauri daga cikin tantin Uzaima ya
bishi.Lokaci guda aka kawo musu dawakai suka
hau suka zaburesu da gudu izuwa cikin sansanin
yaki.A tsiyace sarki Garzub da Yarima Uzaima
suka afkawa abokan gaba aka cigaba da bakin
gumurzu ya zamana cewa sun haukace kuma basa
ji basa gani face saran mutane saidai kaga sassan
jikin bil'adama na shawagi a sama yana zubowa
kasa.Sarki Madarus ma
yana can bangare guda yana ta ragargazar
maza,kawai sai ya hango gawar sarkin yakinsa
Sharkas data abokin gwaminsa Zamud a waje
daya.Koda ganin wannan gawa sai ya fusata ainun
shima ya haukace akan saran abokan gaba ya
zamana cewa a lokaci guda idan ya kai sara
damansa sai kaga sama da mutum arba'in sun
zube kasa matattu.Haka ma hagunsa,gabansa da
bayansa.Nanfa ya cigaba da mummunar barna
domin duk inda ya durfafa saidai kaga yana
tarwatsa cinkoson dakarun dake wajen suna
bajewa a kas tamkar manoma sunyiwa gona
rubdugu suna yi mata sassabe.Yana cikin wannan
mummunar barnar ne ya dubi bangaren da
Sadauki Kularu yake ya ga shima yana ragargazar
maza saiya cika da farin ciki kuma ya rinka hange
hange da waige domin har a sannan baiga duriyar
su sarki Garzub ba.Kwatsam!Sai ya hangosu a can
nesa dashi suna ta ragargazar dakarunsa kamar
yadda shima yake ragargazar nasu.Nan take
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone ya
sake zaburar dokinsa izuwa inda Kularu yake.Tun
daga nesa Kularu ya hango sarki Madarus yana
mai yi masa nuni da hannu cewar su kai dauki
izuwa can inda su sarki Garzub keyi musu
barna.Nan take kuwa Kulara ya fahimci inkiyar
Madarus ya tarwatsa dakarun dake gabansa ya
sukwani dokinsa izuwa inda sarki Garzub da
Uzaima suke yaki.Tuni sarki Madarus ya rigashi
nufar wajen don haka Uzaima na hango sarki
Madarus ya nufosu saiya yunkura don ya
tareshi.Cikin hanzari sarki Garzub ya rukeshi yace
ai ba abokin gwaminka bane ka kyaleni dashi,ga
sa'anka can a bayana yana tahowa shi zaka tara
nika kyaleni da wannan babban shaidanin.Cikin
alamun tsoro da matukar damuwa Uzaima ya dubi
sarki Garzub yace yakai Abbana shin ka mantane
cewa ka jarraba tarar wannan mutum amma baka
sani nasara ba?Sarki Garzub yace ka kyale ni
dashi.Take sarki Garzub Ya tunkari sarki Madarus
Suka runguntsume da azababben yaki.Shi kuwa
Yarima Uzaima saiya tunkari Sadauki
Kularu.Lokacin da sarki Madarus da sarki Garzub
suka fara wannan gumurzu a karo na biyu sai
labari yasha bamban domin wannan lokacin
kowannensu yana yakine a fusace da dukkan
karfinsa kuma da dacin zuciya.Al'amarin daya
janyo karfinsu da zafin namansu ya kusan zuwa
daya.Suka wanzu suna masu kaiwa junansu sara
da suka cikin tsananin bajinta.Saida suka jima a
haka babu nasara ga kowannensu har ya zamana
cewa takubbansu nata zubar da tartsatsin wuta da
hayaki saboda yawan haduwa.Dukkaninsu sunyi
kokarin amfani da karfin sihirin tsafi wajen ganin
sun hallaka juna amma sai sihirin yaki yayi tasiri
saboda kowannensu sihirin nasa mai karfi ne.Da
kansu suka soke takubban nasu a cikin kufe suka
tsaya suna kallon juna suna haki kamar zakaru ko
sauraron abokan gaba basayi saidai duk wanda
yasha gabansu sai kaga sunyi masa naushi daya
ya kife kasa matacce.Dakaru nata saransu da
takubba suna sukarsu amma kamar duwatsu ake
sara domin makaman basa tasiri a jikinsu saboda
karfin sihiri.Nanfa Madarus da Garzub suka cigaba
da kusantar kuna har ya zamana cewa tsakaninsu
bai wuce taku biyar ba sai gashi sarki Madarus ya
zama shirgege a gaban Garzub tamkar giwa a
gaban kura.Sarki Madarus ya dubi Garzub cikin
tsananin fishi yace yanzu kuma karfin damtsenka
ne zai ceci rayuwarka daga sharrina baby batun
iya yaki ko sihiri.Tabbas yanzu zanyi maka KISAN
GILLAH irin wanda ba'a taba yiwa wani ba domin
yanzu a fusace nake bisa ganin gawar sarkin
yakina wanda sukayi RAGAS da na sarkin
yakin.Koda jin wannan batu sai idanun sarki
Garzub suka ciko da kwalla yace nayi matukar
bakin ciki da ya zamana cewa sarkin yakinka shine
ajalin sarkin yakina domin kusan ya dauki fansa ne
a kansa bisa maisheshi musaki da nayi,so nayi
ace nine na raba sarkin yakinka da ruhinsa.To
amma duk da haka sarkin yakina ya mutu cikakken
namiji ina alfahari da haka.Ina tabbatar maka da
cewa koda zaka sami nasarar hallakini nima saina
bar maka babbar shaida a jikinka wacce harka bar
duniya da bakin cikinta a zuciyarka.Inason ka sani
cewa bani da wata nadama idan na mutu a
wannan yaki domin tun kafin na fito yakin nayi
bincike a hallarar tsafina naga cewa bani da
nasarar a wannan yaki amma kuma kuma koda kun
sami nasara sai kun koma kasarku da bakin
cikinmu da tashin kwanciyar hankali.Kafin Garzub
ya gama rufe bakinsa tuni Madarus ya daka masa
tsawa yace karyarka tasha karya yakai wanna
sarki.Tabbas sai mun biya dukkan bukatarmu dake
kanku.Lallai sai mun sami nasarar yaki daku kuma
sai munje har can birninka Hirtoliya mun kama
matayenku,yayayenku da tsofaffinku kuma mun
kwaso dukkan dukiyarku.Koda gama fadin haka sai
sarki Madarus ya shammaci Garzub ya shaki
wuyansa da hannu daya kuma ya dagashi sama
sai ga kafafun Garzub suna wutsil wutsil yana reto
a sama a lokacin da idanunsa suka kumbura kuma
suka kada sukayi jawur ya fara kokarin
mutuwa.Garzub yayi ta kokarin ya cire hannun
Madarus daga wuyansa amma ya kasa.Nanfa
Madarus ya fara kyalkyal dariyar mugunta domin
ya tabbatar da cewa nan da yan dakiku kadan
Garzub zai sheka Barzahu a hannunsa.A wannan
lokaci ne sauran dakarun Sarki Garzub da suka ga
halin da sarkinsu yake shiga sai suka yanyame
Madarus masu saransa nayi masu sukarsa nayi.Kai
harda ma masu cizonsa amma duk a banza domin
babu wanda ya sami nasarar koda yakusar fatar
jikinsa.Kawai sai ya rinka makesu da daya
hannunsa suna zubewa kasa matattu.Duk wanda
ya cafka da hannunsa kuwa idan yai jifa dashi sai
kaga kamar da takarda yai jifa,domin sai mutum ya
luluka sama sannan kaga ya fado kasa cikin
cinkoson jama'a ana takeshi.Kwatsam!Ba zato ba
tsammani sai sarki Garzub ya naushi Madarus a
al'aurarsa da kafa.Ba shiri Madarus ya saki
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On TSIRA DA HALAKA 1 and 2
avatar
hafeez-dalhatu

10 months ago

Reply

Godiya

Please Login or Register in order to submit comment