Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga, yana kwance kan gado
da waya a hannunsa, da Alamu cht ya ke
yi.Kausar ta dan tsaya nesa dasu kanta a
kasa.Al'amin ya zauna bakin gado,Mama ta
hayekan gado, ya rungume mama da Al'amin
sanan ya tashi zaune.Al'amin ya gaida shi,
Mama ma cikin hausarta mara dadi ta gaida
shi.Ya kalli kausar daga inda take.Zo nan.Ta tafi,
ya janyota zuwa jikinshi, ta ce ina kwana?Ya ce,
ba zan amsa ba Kausar har sai kin fada mun
me mamanku ta ce maku nayi, kuke jin haushi
na?Kausar ta ce ba ko mai Abba, Al'amin ya ce
ta ce ne fa muzo mu gaida kai.Ya kalli Kausar,
yanzu kunfi son mamanku fiye dani ko?Al'amin
ya ce, muma ka daina son mu Abba.Ya ce, ok,
haka mamanku ta fada muku?Kausar tayi saurin
cewa momy bata fada mana haka ba, ta ce ne
kawai muje mu gaida ka.Ya dungurewa Kausar
kai yar karama da ke kin iya munafunci, ba zan
kara yi maki tsaraba ba.Ya kalli Al'amin, in ba
ka daukar maganar mamanku zan sai maka
keke kana so?Al'amin ya kama murna ina so
Abba.Ya kalli mama, mama na ke kuma in se
maki motar ki ta wasa ko?Na juya kicin ina kuka,
mutumin nan zai raba mun kan yara, zai kafa
min jam'iya yan partyn shi da nawa.Jin takun
Kausar yasani share hawaye, cikin sheshekar
kuka ta ce, momy kinji Abba zai sayawa su
Al'amin da mama tsaraba ban dani.Na tsugunna
na rungumota jikina ina shafa mata kai, yi
hakuri Abbanku wasa yake yi miki zai siyo miki
kinji?Ta ce, Allah momy da gaske yake yi ba ya
cein fitar masa daga daki ba?Na ce, yi shiru zai
sai maki.Da kyar tayi shiru.Na bata jug na ce,
kije wajen Iya ki ce mata in ta dama koko ta
baku, karfa ki ce mata wani abu ya faru kinji?Ta
ce to.Ta tafi nikuma na zauna a kicin cikin ta
gumi.Kausar ta sami Iya kwance ta gaida ta, ta
ce kausar menene?Ta ce, wai in kin dama koko
ki bamu, iya ta ce shine aka turoki ba Abbanku
ya dawo jiyaba?Me yasa bai rakoki ba?Tayi shiru
Iya ta ce to muje in se maki koko gidan ladi me
koko dan kulluna jiya ya kare, kice mata na ce a
jika maku gero tunda jifa jifa kuna shan kokon,
ban cika son abin siya ba.Sam iya bata fahimci
bamu da komai a gidan bane, tunda lokaci zuwa
lokaci sukanje su amshi kokon.Ta samu masu
kosai sanan ta rakata har kusa da gida.Tanaji
tana fadan turota ita kadai a wanan safiyar, ta
ce da uwarku tana tattalinku amma yanzu duk
ta canza,na rasa me ke damunta.Suna shan
koko da kosai kausar tana fada min sakon Iya,
na jika gero na ce to za a jika,suka gama na
dauki Mama na nufi kaisu makaranta, kusan
wata guda a kafa nake kaisu makaranta, don
mota tuni nayi fakin dinta gefe na rufe ta don
ba mai ba na da kuma kudin siya.Ina dawowa
na tarar da shi da Usman zaune yana
karantowa Usman laifuka na.Na gaida Usman na
shige daki, na hau gado na kwantawa,bawai don
bacci ba ko don hutu, sai don tsabar ta kaici.Can
na jiyo muryarshi yana kira na, ya kalle ni.Kin
san na fada maki ba zan dauka ba ki rabani da
yara na ba.Jiya na shigo gidan nan wai Kausar
tana yin fushi dani yar karamar yarinyar
nan.Al'amin yana fada mun na daina son su,
tayaya zan yarda wanan tunaninsu ne?Usman
ya daga mishi hannu saurara aboki na, ka barni
in gama magana ta don kada kakatse ni.Usman
ya kalleni,Sadiya me yake faruwa ne?Na runtse
ido don ta kaici, yaya Usman duk abin da ya
faru Abban kausar shine sila.Na koro mishi
komai tun daga farkon rigimar har zuwa
yau.Sanan na ce yaya Usman tsakani da Allah
kullun yaran nan suna kallon muna fada, ko
ince daga yazo sai shiga tashin hankali zasutashi
da tarbiya me kyau?Ya ce, a a.Na fada musu
yanda mukayi da malamansu. Ga rashin abinci
wane laifi na masa, ni dai yanxu tunda gani
gashi kurun ya fada min laifi na, wlh zan bashi
hakuri mu koma kamar da yaran mu suma su
sami natsuwa.Usman ya kalli Aliyu, aboki kaji,
sai ka fada mata laifinta don matsalar tazo
karshe.Aliyu yayi mun wani kallo ke dai kawai
baki son zaman lafiya ne, duk ki dauki damuwa
da bakin ciki kisawa kanki.Sau nawa zan fada
maki baki yi mun komai ba?Usman ya ce, to na
rokeka aboki ko mai ya wuce.Ya runtse ido tare
da fadin shi ke nan.Na dube shi nima in sha
Allahu ko mai ya wuce.Usman ya ce,
Alhamdulilla, yanzu sai ka tashi mushiga kasuwa
don nima abincin gida na ya kare.Nan dai suka
fita.A cikin mota Usman ya kalli Aliyu.Aboki ka
canza fa,Aliyu ya kalleshi wacce irin canzawa
nayi?Usman yayi murmushi sanan ya maida
hankalinshi titi.Kayi kiba sanan dabi'un ka sun
canza.Aliyu ya kure Usman da ido, zaiyi magana
kenan wayarsa ta soma ruri, ya ciro ya kurawa
Screen din ido,sha wara yake ya dauka ko ya
yanke,Usman ya kalle shi, daga mana abokina,
Aliyu ya katse kiran sanan ya kalli Usman,daga
jin kira sai kace in daga ba tare da kasan me
kiran ba?Usman ya ce, jami'in tsaro zai ji
shakkar daga kiran koma wanene.......Kiran
yasake shigowa, sai kurun Aliyu ya dagadan
kada Usman ya dago abinda ke faruwa.Ya ce,
yaya?Mujidat ta ce, muryarka nake sonji, nayi
kewarka da yawa, don Allah ka dawo yau.Tana
magana kamar zata yi kuka, salon dake narkar
masa da zuciya,take ya manta da wa yake tare
har ya furta cewa.Kada ki damu gobe kamar
yanzu muna tare,ta ce, to Zaki na sai mun hadu
a internet.Sai da ya salameta sanan ya tuna
yayi baram barama.Ya dubi Usman wanda bai
ce kala ba, ya soma nade tabarmar kunya.Wata
abokiyar aikina ce, muna gabatar da wani
aikine.Usman yayi murmushi sanan ya ce, sau
da dama in mutun ya shiga aikata rashin
gaskiya sai kaga ya zama makaryaci.Ita ko karya
illar ta da kayi so daya kafin ka fitar da kanka
sai kayi kusan sau goma.Aliyu ya kalle shi, me
ya kawo wanan zancen?Usman yayi dariya, ka
tsargu ne?Aliyu ya kalli gefe, intsargu da me
kuma?Usman ya hade rai, tsayar da halayenka
haka nan Aliyu.Ya gangara gefe titi yayi fakin
dazu nake ce maka dabi'unka sun canza ko?
Aliyu ya kalli titi muje zuwa da maganarka, in
wani zai fada mun aboki ba zan yarda ba,
amma gani ina zar ginka cewa kana hulda da
matan?Aliyu ya kalleshi da sauri, haba aboki,
nasancewa zaka iya bada shaida cewa ban
kasance mai shiga lamarin da mata suke ciki ba,
bare har inyi hulda dasu.Usman ya ce to amsa
min wadan nan tambayoyin.Aliyu ya cire hankici,
ya share zufar fuskarsa sanan ya ce, ina
jinka.Usman ya ce, na kira layinka sau uku wata
macece take dagawa.Na farko da dare ne gurin
karfe dayan dare, don in fada maka rasuwar
kanwata, sai kawai wata mace ta daga wai ka
shiga wanka.Na biyu da safe wata jumma'a don
mu gaisa ta ce ka fita gurin masu gadi, na uku
gargadi tayi mun in san lokacin da zan
dingakiranka yanzu kana cikin halin da bazaka
iya daga waya ba.Sai na soma lissafi giya kake
sha da har ba zaka iya daga waya ba, koko
menene?Sanan ita wanan matar yakuke da ita
har zata kasance a inda kake ciki tsakar daren
nan .In zuciyata ta zargeka sai wata ta shaideka
da cewa ba aikin ka bane, abin da bakayi ba
kana yaro ba na zaton cewa zakayi shi da
girmanka.Amma yau da matarka take fadin
yanda ka kaurace mata, sai na amince kana
neman mata, don kai ba me hakurin zama baka
tare da mata bane.Aliyu ya hade rai tare da
duban Usman, me cece shaidar ka ta zahiri?Duk
abin da kafada bai zama shaidar da zaka
amince ina bin mata ba.Ba zan iya zama ba
mace ba, shekaru nawana dauka can baya babu
auren?Usman ya ce kila lokacin baka san
amfanin matan ba,amma ni shawara daya zan
baka, inma zakayi harkar bariki to bai kamata ka
wulakanta matarka ta sunna ba.Aliyu ya ce, dan
Allah mu rufe wanan firar.Usman ya ce kafin
mu rufe sai nayi maka nasiha duk da cewa bani
da tabbas akan zargin da nake yi maka.Na san
mutun yana canzawa kamar yanda wahainiya
take canzawa zuwa duk kalan dataso.Nasihata
gareka in ka canza daga fari zuwa baki don
Allah ka saki wanan layin ka koma dai dai ko
don gudun zunubi, ko don tsoron azabar
Allah.Ko don kare mutuncin yayan mu, ko don
kare lafiyar ka daga cututukan zamani.Sanan
maganar zubewar daraja da kimarka a idon
wayanda suka san kanayi. Aliyu ya runtse ido
cikin in ina yace, muje aboki don Allah.Suna tafe
yana share zufa, lallai zancen Usman ya shige
shi.
Ko mai na abinci zuwa kayan tea sun hada
muna, lokacin da suka dawo ina kwance
kangado ina karanta littafin gidan zahra.Sau da
yawa in ina karanta littatafan Hausa sukan debe
min kewa halin da nake ciki, har na sha cin karo
da irin matsala ta.Sun ajiye min kayan abinci
suka sake ficewa, na fada kichin na shiga girki,
yarama da suka dawo makaranta sai murna
suke sun sami lafiyayen abinci.Yaushe rabon
muyi girki da kifi ko nama, yau gashi har
farfesun kan rago mukayi.Da daddare na fada
ban daki na sake wankana sheka kwalliya duk
tunanina yau za a shalabari.Sai dai muka
kwanciya ya juyya min baya, na gaji hakurina ya
kare don haka na ajiye kunyata na fada masa
cewa, yau ni ina son a faranta min.Ya ce, shi
gaskiya baya jin zai iya wani abu yanzu don duk
a gajiye yake.Nace, haba yaya, nima fa mutunce
kamar kowa, sama da wata hudu ka juya min
baya.Baka tsoron sharrin shaidan?Ya tashi
zaune a fusace, kina nufin zaki bi maza? Iye?
Fadamin zaki bi maza? Nasauka daga kan gadon,
ban ce zanyi zinaba yay, amma zuciya bata da
kashi, in na kasa jurewa fa?Na durkusa kan
gwiwowina, yaya ka taimake ni ka fiddani wanan
yanayin, ka tuna ni ban taba gudunka ba.Ya
mike ya dauki filo.Sai da ya kai bakin kofa
sanan ya ce, ina ganin kina cikin fitunananun
mata bari naje falo in kwana. Rufda ciki na
kwanta a kan gado ina kuka, wani mai kunci
daga bisani na dangana na fada ban daki na
sakarwa kaina ruwan sanyi yayi ta zuba tundaga
tsakiyar kaina.Ban fito ba sai da naji sanyi yana
ratsani, na fita naje kan gado na dukunkune sai
zazzabi da ciwon kai.Haka na kwana har safe da
kyar nayi Sallah na sha magani, sanan na fita
kicin.Shi kam a ranar ya koma kusan karfe biyu
ina kwance ya tsaya kaina wai ni fa zan tafi.Ba
tare da na dago ba, na ce Allah ya tsare, ya
ajiye kudi a gefe na tare da fadin, motarki an
gyara na ce uhm.
Duk da cewa Aliyu yana kirana a waya mu gaisa
yanzu duk abinda muke bukata yana
kamantawa, sai dai ya barni cikin kewa.Haka
nan ko a waya da mun gaisa shi ke nan sai ya
ce in bashi yaranshi suyi magana,ba wata hirar
soyaya ko ta rayuwa bare in sa rai zamu koma
kamar da.Duk da cewa yanzu yaran nan sun
dan saki jikinsu sai dai duk da haka da sun
ganni cikin takura ko damuwa yanzu zakaga
sunyi mun narai narai tamkar zasuyi kuka.Ni dai
a bisa halin da nake ciki gara ace bukatun ya
dai na yi mun ya bani kulawa da soyayya sunfi
mun duk wani abin duniya da zai sai min.Na
hakura ne saboda DARAJAR YAYA NA, sam bana
so in zube su inyi gaba.In ban rike suba naje
can inyi wahalar yayan wasu.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Wata rana naje kitso inda nake zuwa a can layin
zage-zagi wani gida, gidan haya ne maidauke da
matan aure da dama.A kulun naje gidan ina
karantar abubuwa na rayuwa da dama a gurin
matan gidan.Farko matar dake yi mun kitso, sau
da yawa mijinta in yadawo bata iya sakin kitson
taje gurinsa.Haka zai gaji da zama ya fito ya
dauki bokiti ya ja ruwa yaje yayi wanka.In kuma
da abinci ya ci ya fito in ya ciro kudin cefane ya
bata sai ta amsa a raine, yauma da nazo kitson
hakan ne ta kasance.Ya bata dari biyu ta juyata
sanan ta maida masa tana fadin gaskiya malam
bazata isa ba.Ya ce ba da garin tuwo ba, kuma
naga manja?Ta ce yau kwana uku muna tuwo,
ta kalli yaranta dake gefe suna wasa.Habu kunji
babanku wai yau ma tuwo sai suka rugo da
kansu gaskiya baba yau bazamuci tuwo ba.Ya ce
to me ni dai kudin nan ke nan.Ta ce, ko tuwon
ne ma kudin nan ba isar muzaiyiba, ya ce haba
Tasallah, ba kifi ba nama kice dari biyu baza tayi
miya ba?Ya shura takalminsa yayi gaba.Ta daga
murya sai dai ayi maka ciko kuma kana zuwa
zaka bani kudi na.Yaran suka hau mita, shi
baban nan kullun tuwo.Na kalleta cikin mamaki
sanan na ce, na kusan daina zuwa kitso gurinki,
ta ce zaku tashi ne?Na ce a a na ce nagaji da
yanda kike daukar mijinki ba a bakin ko mai
ba.Dubi yanda kike sa yaranki suna yi ma
mahaifinsu rashin da'a da raini, wanan tarbiya
ke nan?Tayi yar dariya hajiya kenan, Allah hajiya
ba haka bane, ace mutun kullun ba ci gaba, ba
ya neman wata sana'a a caba yake.Na ce, na
lura baki da godiyar Allah ta salla. Ranan fa ina
kallonki da yaranki kuka ce masa kun gaji da
shinkafa, san nan baki sanin mijinki ya dawo ki
bishi daki ba.....
Allah sarki Rayuwar Aure,kowadai da tasa
matsalar,damadai haka Rayuwar take,tanada
manyan matsaloli guda hudu wadanda duka
daya takan haddasa rashin jin dadi daga
bangare daya,Immadai -:
Mijin baya jin dadin zama da matar,misalin
Tasalla me kitso da Mijinta,kokuma...
2:Matar ake zalunta ,Misalin Aliyu da
Sadiya,Kokuma ...
3:Suna zaune lafiya a junansu, Amma dangin
matar ba kaunar mijin,shima Wannan Babbar
matsalace a auratayya,Wacce ke Haifar da Babar
Matsal..kokuma...
4 angin mijine basu son Matar, wanda nasan
da yawanku kunfi sanin wanna matsalar,..
Lallai dukanin gidan auren da suka samu kubuta
daga dukkanin matsalolinnan nazama wajibi Su
godewa Allah,akarshe Dukkani gidan Auren dake
da matsalar makamanciyar wadannan Ya Allah
ka kawo musu agaji,mukuma Ya Allah
kahadamu da abokan zama nagari
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347


Zaharaddeen shomar
Whatsapp 08168575100


Darajar Yayana2-04
Posted by ANaM Dorayi on 06:34 PM, 29-Mar-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
___________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Assalamu'alaikum, fatan kuna cikin koshin
lafiya...
Sagir Ali, Shamsusdden Usman,Fatima
Ahsan,Maman Ummi,Shamsiyya,Ummi
Amal,Aisha and Aisha Kaka Zanna nagode da
kulawarku,sannna inna jin dadin yanda kuke
kulawa da shige da ficena,shirun da kukaji
yafarune sakamakon ayyuka da sukaimin
yawa,fatan zakucikaba da bibiya dakuma hakuri
dani. nagode zamu Dora yanzu.....
Ruwan wanka sai dai ya diba yaje yayi, wanan
rashin dabi'ar har ina?tasake yin dariya, to ni in
nashiga dakin in ya dawo me zan masa?Na ce,
auran kiyayya aka maki?Ta ce, a a ni na kaishi
gidan mu, ta ci gaba kin sani ni gaskiya ko ya
dawo bana shiga, shi yanzunnan zaice zai
rungume ni, niko na tsani haka,ka debo rana ka
wani ce zaka rungume ni, salon su Habu su fado
dakin?na ce menene dan yaranku sun ganku
rungume da juna?Kai ke dai baki da dabi'a,irinku
ne ake kwacewa miji cikin sauki,daga baya kizo
kina ya ci amanar ki,ni dai in baki canza haliba
zan daina zuwa,ta ce;to Hajiya za'a sake, ai ku
hajiya cikin daula kuke baku da matsala.Nayi
murmushi Tasalla kenan.Shiyasa na ce, kina da
hange, ki kalli kasanki mana,Misali waccan
Maman Rashidan kuke ce mata ko wa?Tunda
nake zuwa gidan nan bai fi so nawa naga ta
daura tukunya ba.Kullun in kazo zakaga yaranta
suna cin dumame, ko garin rogo amma ban taba
ganin mijinta ya dawo ta barshi ya dibi ruwan
wanka da kanshi ba, ko ta shareshi taki shiga
daki.Sanan sau biyu na taba ganin mijinta nasan
yayi sa'ar mata, duk cikinku 'yan nan sasan da
na taba ganin shigowar mazajenku da fitarku ita
kadai ke yi wa mijinta sannu da zuwa da yi mashi
addu'a in zai fita.Tasalla tayi yar dariya, hajiya
kenan, ita waccen ai bata san kimarta ta ya mace
ba, in banda haka yaushe zan zauna babu
abincin kirki.Amma kina like da mutun kullum sai
tayi wankan asuba don jaraba.Na ce, tafi ku
godiyar Allah ne da biyayya.Sanan zakuga
cigabanta kuna nan, sanan yaranta sunfi naku
tarbiya da tsafta.Tasalla ta bata rai,Hajiya mu bar
maganar nan, amma ko su maman Auwal zaki
tambaya matarnan tana shiryawa yaranta kinaya
ne don in mutane sunzo su rinka gaidasu don a
ce suna da halin kirki.Na ce, ba wani bayan aike
ma ina kallon naku yaran amma baku aikensu
don kunsan cewa bazasuba, sai dai ku kira
nata.Daga nan Tasalla tayi kus, niko na ce in sha
Allahu duk randa zan kuma zuwa sai nayi wa
yaranta kwalima tunda naga yaranta basu fi
girman su Kausar ba, a raina na raya hakan.Ina
Mota na kusa isa gida da motar dama naje gidan
kitson da mota ne, sai ga kiran Aisha aminiyata,
cikin hanzari na daga ina fadin.Kin haihu kenan?
Tayi dariya yau andace kullun na kiraki zancenki
daya ne kin haihu?To ga yarki nan a gado.Na ce,
Alhamdulillahi ga ni nan.Na kira layin Abban
kausar kamar yanda na zata har ta tsinke bai
dauka ba, na sake kira.Muryar mace naji cikin
harshen turanci tace wakike nema?Sai da sitiyarin
ya kusa kufce min, na samu na tsaya tunda cikin
unguwa ne, na sake yin sallama cikin rawar
murya.Ta ce kina bukatar taimako ne?Na katse
layin zufa ta soma tsatstsafo min.Na rude
matuka, na kifa kaina a kan sitiyarin ina fadin
Allah yasa mafarki nake yi.Na kuma kallon wayar
ina shawaran in sake kira ne ko in barshi, sai ga
kiranshi ya shigo da sauri na daga amman na
kasa magana, Muryarshi ne yanzu ya ce hello!!
Dazun bakiyi magana ba sai wata irin muryanake
ji.A sanyaye na ce dazun ba kai bane wata ce ta
daga.Da sauri ya ce wata wa?A wayata?A'a sai
dai in network ne yasa ki kika ji haka.Ya saki
zancen da cewa, lfy dai?Na ce eh dama ina
dawowa daga gidan kitso ne sai Aisha ta kirani ta
haihu.Ya ce wace Aishan?Na ce, ta mamana.Ya
ce, Allah ya raya, kin cika son yawo.Na ce to yaya
in banje yanzun ba dole in sake fitowa don inyi
gabadaya.Ya ce to shi kenan ina yaran?Na ce
sunje yiwa iya wuni, ya ce ban son fa kina tafiya
ke daya fa.Ko mama bakya iya yawo da ita sai ke
daya tsura?Na ce, to yaya sun kwana biyu ne
basu je sunyi mata yini ba.Ya ce, to shi kenan
kardai kiyi dare don na sanku in kuka sami surutu
na ce to.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Bayan ya kashe wayar ya nufi gurin Mujidat da
ke zaune kan kujera tana dafe da kumatu, inda
Aliyu ya watsa mata mari sakamakon shigowa da
yayi ya ganta ta daga masa waya.Ya kalleta in
kika kara yi min gangancin daga min waya sai na
mugu saba maki, don zaki koma inda kika fito.Ta
mike tsaye kana jin tsoron matarka ne don kar
tasan muna tare ta ce ta fasa aurenka?Cikin
gatse Aliyu ya ce haka ne.Don haka kada ki kara
daga min waya.Ya juya ya shiga dakinsa rai a
bace.Mujidat ta mike tsaye tana kai kawo, wai
mutumin nan yana nufin duk son da nake masa
yafi son matarshi a kaina?In ma yana boye mata
ne sai nayi sanadin da zata sani, in sha Allahu.Sai
dai ta mutu ko ta bar mun shi, don na yi imani
na fita son shi, zanyi komai don naga na rabasu
da makircina kawai,ta hada yatsanta babba da
na tsakiya taja suka yi kara, wanan wata Alama
ce da take yi duk lokacin da ta ma kanta
Alkawarin aikata wani abu cikin izza.Ni kam
kwana nai da motata zuwa gidan Aisha, amma
zuciyata cike take da wasi wasin abin da kunne
na yaji wai netwok ne.Anya kuwa ba binne ni
yaya yayi da rai na ba?Nayi murna da ganin
Aisha cikin koshin lafiya tare da jaririnta.Na dauki
yarainyar ina juyyata, mashaAllahu,Bello ya fiki
karfin jini daga ita har Najib shi suka biyo.Na ce
haka dai su mama suka ce, na ce, ina angon
karnin?Ta ce ya fita na kwantar da yar na kalleta
a Asibiti?A gida kafin ya samo mota har kai ya
fito.Innarsu da mamanmu da ma suka zo sai
kurum suka amshi haihuwar, na ce shi kenan
Allah ya kawo shi cikin sauki.Na nufi wata kula
dake gefe, na ce me suka barararaka miki?Na
bude kular, ta ce tuwo ne, miyar kuka, kinsan
tsaffin nan sai suce wai maijego sai da
tuwo.Muka sa dariya, na ce a ni na horu da tuwo
gurin Iya, haihuwar kausar har wani baki nayi
nayi muni dan uban nan.Muka sa dariya.tace, ai
daga baya Anty Abida ta hada maki sabulu, na ce
ai ta min kokari yanzu ba abin da bana hadawa
da kaina.Ta ce zaki hada min sabulunma nace to,
haka mukai ta fira har shida, sanan mukayi
sallama naje gidan Iya na kwashi yayana muka
tafi gida.
Na kasa bacci cikin dare sai juyyi nake kaso
hamsin da daya na zuciyata, yaya Aley yayi
min.Tabbas zan zama wawiya in ban amince yaya
yana neman mata ba.Yaushe rabon da ya dora
yatsansa kan nawa?Kullun dare ina kwana da
kewa, hawaye na suna kwaranya.Na tashi zaune
in ko haka ne wane mataki zan dauka.Zuciyata ta
dauki zafi ina fidda wani huci, lallai in ya kasance
haka zamuyi rigima ba karama ba, don ba zan
dauki wulakanci a kan matar banza ba.
Washe gari da safe ina ta tunanin yanda zansake
cewa yaya zan sake komawa gidan Aisha, saboda
in na haihu kulun tana hanyar har ayi
suna.Amma ni ko haihuwar Najib dinta banyi
mata wani sintiri ba, yaya hanawa yayi.Kuma
bana son fita batare da izininshi ba.Don nayi
imani shi baya kallona Allah da ya halicceni yana
kallona.Text na tura mashi cewa zanje gidan
Aisha lokacin suna tare da Mujidat suna
karyawa.Ya dauka ya karanta, sai ko ya hade rai
ya soma kiran layi na na daga.Tunkafin in karasa
sallama na ji ya ce, ban amince ba kullum fita,
saboda ki dinga kallon maza ko? Na zaro ido na
mike da sauri na nufi daki dan su Kausar suna
nan gida don anyi musuhutu.Kuma bana so suna
jin matsalar mu.Ya ci gaba da fadan shi, na ce
wacce irin magana kake yi yaya?Don in dinga
kallon mazaje fa ka ce?Kana nufin in na fita haka
nake yi?Ya ce, oho miki, amma ban yafe ba in
kika leko waje, nace naji ai tunda ka hana ba zan
fita ba, amma cewar da kayi wai ina kallon mza
nike son inji hujjar ka.Kana ga don ka shuka
fulawa ta fito kaki kayi mata ban ruwa sai ta
mutu?Na ci gaba, haka ne zata mutu amma
kasani ni nasan DARAJAR YAYA NA.Ko don su zan
kare mutuncina kai shaidane budurwa gar ka
bare ni a leda, ka san haka kuma kullun ina
Adu'a Allah ya kare ni daga sharrin zamani.Ban
jira amsarshi ba na kashe, sanan na fada kan
gado ina kuka.Sai kurum naji hannun kausar a
baya na tana fadin.Momy kiyi hakuri ki kyale
shi.Da sauri na share hawaye na taso kausar
bana ce in ina waya a daki ba ku daina biyo ni?Ta
ce momy ki daina daga wayar Abbanmu, ko ya
kiraki ni bana so yana saki kuka.Na ce naji muje
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Kwana uku da yin sunan yar gidan Aisha ya ta ci
sunan Fateema, sai ga yaya da rana tsaka ina
mamakin yanda yanzu yake son yimin dirar
mikiya.Ko yana zargin ina fita ne?Oho.Nayi masa
sannu da zuwa ya amsa na ce, baka fada ba
gashi banyi abincin rana ba.Jiya sun bar
shinkafar da na dafa da dare, sai kawai nasa a
firiza yau na duma ma, amma bari in maka ko
macroni ce.Ya ce barshi bani da yunwa, in na fita
zan siyo fura.Sai da yayi bacci sanan ya tashi yayi
wanka ya fita.Duk ina dakina ina karanta littatafi
,tinda nalura bai bukatar ganina kusadashi, nima
hakan yafi min sauki don in yana gari nafi jincewa
nima macece in kwana cikin kewa.Washegari ya
fita zuwa gidan su Iya na dauko jakarshi, don
kwashe kayan wanki wanda ya dawo dasu kamar
yanda na saba.Ina daga suit din shi zan rataye
wata takarda ta fado, na dauka har zan maida
masa cikin Aljihun rigar sai wata zuciyar ta ce
bude mana ki gani, na bude.Yar wasika ce aka
rubuta da harshen turanci, ga abin da yake
rubuce.ZUMA NA KA TAFI DA TUNANINA, HAR
KAJE KADAWO KASANI ZA KA BARNI CIKIN KEWAR
LALLAUSAR FATAR JIKINKA.BA ZAN GUSHE BA HAR
SAI KA DAWO KA SAME NI CIKIN KEWAR LEBUNAN
KA MASU SANTSI TARE DA (YAWUN) KA ME
ZAKI.ALLAH YA DAWO MUN DA KAI
LAFIYA.....Kafin na kai karshe tuni na jike da
zufa, ina gamawa na ga gari yana juya min, ban
an kara ba sai dai naji ni a kasa ribin jikina a
gado rabi a kasa.Kusan minti biyar sanan na tashi
zaune sa sake karanta takardar ina kuka wiwi har
da majina tabbas yaya mata yake bi,domin
takardar ta nuna haka, mata ce kawai ya dace
tayiwa mijinta irin rubutun nan, wata zuciyar ta
tambaye ni ko dai ya sake aure ne?Duk da uban
kishi na sai nasami kaina da cewa inda ma auran
yayi zanfi son haka, da bin matan banza.Na soma
kaikawo cikin gidan ina tunanin matakin da zan
dauka.Shawarar wa zan nema?Na shiga dakina
na fada kan gado na dauki wayata na shiga
kiranshi, amma sai wani tunani ya fado min.Bari
kawai in kira Hajiya Baida'u, marubuciyar littafan
da nake karantawa danneman shawara.Dan ita
bata sanni ba balantana inyi zaton zancen zai iya
yaduwa, sanan tana da basira nasan zata sani a
hanya.Ringing na biyu ta daga, ta daga muka
gaisadama na saba kiranta, na ce Anty ina
nemanshawara ne.Leta na gani a jakar me gida
na wanda ke Alamta cewa yana tarraiya da wata
mace.Ta danyi shiru na dan lokaci.sanan ba yan
wanan letar kina da wata shaidar?Sanan can
dama halinsa ne?Na ce, a to a da can ba na
zarginsa, sai da ga baya na soma zarginsa domin
Anty kwata kwata ya kaura ce min kusan wata
shida zuwa bakwai yanzun,kuma Anty shi mutum
ne mai zurfin sha'awa, ba zai iya daukar ko
kwanaki ba ba tare da mace ba bare watanni.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta ce kuma ba gudan sa kike ba har hakan ta
faru?Na ce wlh Anty Allah ya sani ban ta ba juya
masa baya ba, har matsalar nan ta shigo.Ta ce,
kuma kina gyara jikinki ba ji yayi kin zama wata
iri ba?Na soma lissafo mata abubuwan da nake
hadawa, ta ce, lallai kina kula da kanki.Na ce,
anty yanzu in yazo in fada mashi takardar don
yasan na sani?Ta ce, a a tunda

Please Login or Register in order to submit comment