You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
shi yanzun
idan sun iso kafin su isa gidsn malamin ya sauke
yashige daki. Aliyu yakalli malamin. Allah
yagafarta malam naga jama'ar wannan garin
suna alhinin rabuwa dakai shin bazamu dan kara
kwanakiba? Malam yakalli Aliyu ina da dalilin
barin garinnan asubahin gobe.Aliyu yace Allah
yasa haka shine mafi Alkairi. Malam yace ameen.
Sai dai kai ina mamakin yanda kake son bina ban
cika sakewa da mutaneba amma kai raina ya
kwanta dakai amma daganinka ka taba zaman
cikin birni? Aliy yace e duk cikin gari nayi
rayuwata ban zauna gidaba, Malam yayi
murmushi toh Aliyu sai dai kayi hakuri ina zaton
bazanje dakaiba. Aliyu yace saboda me malam?
Malam ya gyara tsayuwar wato malam Ali an
sanar dani cewa duk inda zan shiga kada in shiga
da mutumin cikin gari domin shine zai zamemin
hadari cikin rayuwata. Aliyu yace Allah gafarta
malam an fada maka kamannin shine munyi
kama? Yace ko kusa an dai ce min zai shiga jikina
sosai kuma zai cutar dani a rana irin ta gobe
shiyasa duk lokacin dazan bar gari nakan barshi
tun asubahi. Aliyu wanda ya kosa yaga isowar
jami'an tsaro yace toh Alagafarta yaya zaka yarda
da irin wannan kila ba gaskiya bane. Malam
yadafa kafadar Aliyu inayimaka fata nagari Allah
yasa zamu hadu wata rana amma wanda yafada
min zancen nan yasha fadamin zantuka suna
tabbata ina ji ajikina zamu sake haduwa da.....
Jiniyar motar 'Yansanda ce tasa malam bai karasa
zancenba sai Aliyu yaga malam ya daga kafada
yasa gudu cikin azama da kwarewa Aliyu yaciro
bindiga daga bayan wandasa ya harbi malam a
kafa take malam yafadi amma burinshi yakai daki
dan haka ya yunkura Aliyu yayi azama yacafkeshi.
Mutanan gurin sun cika da mamaki harma suka
taso da nufin jin ba'asi sai dai kafin suji dalili tuni
yan sanda sunyi zobe a gurin sun kuma cafke
wasu daga cikin makarraban malamin sannan an
samu muggan makamai cikin kayan malamin da
kudin kasar Amuruka(Dollar) da irin namu na
gida. Mutanan unguwar suna ta al'ajabin lamarin
yayinda wasu ke mamakin Aliyun wanda suka
zata shima yana cikin mukarraban malam. Ta
gidan lima suka bi mai masaukinsa,Aliyu yayi
musu sallama yadauki yan kayan shi tare dayi
masa alheri haka ma yen majalirarsu yatafi yabar
su da labarinshi tare da jinjinawa aykin shi.
Cikin wata hudu da aka damka aykin hannun
Aliyu ya samu nasara ya fara bibiyar malamin
tundaga maiduguri har kawo Kaduna sannan
Zaria inda yayi nasara sakamakon haka ya samu
lambar yabo tare da karin girma zuwa
mataimakin kwamishina na can Abuja haka nan
nasarar taja masa farin jini inda akayi ta haskashi
gidajen talabijin. Ina kallon Iya tunda Aliyu yazo
da batun aykin nan kullum cikin yimasa addu'a
take tare dayawaita sadaka. Araina nace da da
mahaifi sai Allah. Dubi duk haushinsa datakeji be
hanata yimasa addu'ab. Inzanje aiki yanzu gida
nake barin Sadiq sabida yana shan kamu. Iya
tasani gaba tana min fada wata ranar Litinin na
shirya zantapi aiki. Sadiya! Dan Allah shekarunki
nawa? Nace me yafaru Iya? Tace fadamin. Nace
26 Tace dubi duk yanda kika koma ba wani ado
ba kwalliyar da kikeyi ada, ki dage ko dan ki ba
Gadanga haushi,amma kullum sai kina yawo
kamar me takaba,Nace ni banima da kayan
kwalliyar,tace inzaki dawo ki tsaya kasuwa ki saya
in ma baki da kudi in baki,nace ina dashi a cikin
account dina,tace to.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ina zaune bayan na sallami daliban ajina sun fita
break nazabga tagumu ina tunanin zancen Iya
gaskiya ta fadamin bazan tsaya in tsufar da
kainaba tilas in nafita in shiga banki sannan in
shiga kasuwa. Shigowar alert ne ya tsaida
tunanina na dauka na duba kudi ne naira dubu
saba'in sannan yaya ne ya turo min. Haushi da
bakin ciki kamar inyi kuka don haushi. Dakyar
nabari aka tashi na nufi banki na ciri kudin daya
turomin naira dubu 70 na maida masa cikin
account dinsa sannan naciri dubu 20 dan yin
siyayyata acikin account dina. Nashiga cikin
kasuwa nasiyo mai na perpect nasiya duk kayan
shafawa, sannan nasai turaruka na har da kayan
humra dan dakaina nake hada humrata nasai
mayafai da takalma har atamfa na kara. Iya na
gani tace ko kefa. Nanfa nashiga gayuna kafin
wata daya na komo da farina da gayuna, sai dai
ban maida kibata sosaiba, ba wanda zai ganni
yazata ina da yara har 4. Wani abin dariya sai ga
mutane sun soma yin sallama dani.
Ranar wata juma'a ne sunan wata malamar da
muke koyarwa tare nayi kyau cikin leshi mai
ruwan madara ni kaina nasan nayi kyau taku dai
dai nake yi na tsallaka titi zan hau abin hawa sai
mota ta tsaya a gabana na waiwaya zanyi masifa
sainaga yaya Usman ne cikin dariya na isa gurin
shi. Yaya ashe kaine? Yace to na tsaya kafin inyi
magana sai naga za'syi min masifa nayi dariya ka
san mutane wai dasunga mutum ya tsaya sai
suce zasu dauki mutum. Yace hakane sai ina?
Nace nan Askulaye zani suna watace da muke
koyarwa tare ta haihu. Yace muje. Nace a'a
dakaje kada in batamaka lokaci yace hanya tace
ni gaba naci don kurmin mashi zanje. Nace ok.
Nashiga muka hau titi nace ina su Auntyna da su
Ummul? Yace duk suna lfy shine bakya son fita
da Sadiq koh? Nace shima ya saba da Iya baya
son bina. Yace ya huta da shan rana. Nace
wallahi. Naji cewa abokina yasamu karin girma
kwanaki? Nabata rai ina ruwana. Yayi dariya da
ruwanki mana koba dangantaka akwai su Kausar
nace harsu duk na barmasa na yafesu. Yace
bacin raine. Nace wai ya batun binciken? Yace
ina kan binciken kiris yarage in kammala. Murna
ta cikani cikin zakuwa nace kun gano kowane ne?
Yace eh toh na dai yi nasarar gano cewa mutum
dayane a abu uku Sulaiman din daya kawowa
aboki gulma shine malamin makarantarku kuma
shine Sadiya Abubakar mun gano hakan ne ta
hanyar lambar MTN Din dayayi amfani da ita
gurin cike form na account din da ya bude. Nace
a'a duk lamba daya yayi amfani? Yace a'a daban
daban ne sa'ar da muka ci duka na MTN ne
kuma duk yayi musu rijista taimakon dayayi
mana kenan. Nace Alhamdulillah. Muka danyi
shiru nawasu yan dakiku sai Usman yayi gyaran
murya yace, Sadiya! Nadube shi irin kallon
dayayimin yasa gabana faduwa nayi ta maza
nadauke kaina. In tambayeki mana? Nace
eh...ina...jinka. Nafada cikin in ina yace in
abokina yaji gaskiyar batun nasan zaku sasanta
koh? Nakalleshi da sauri nan take raina yabaci na
sunkuyar da kaina yaya Usman dan Allah na roke
ka kadaina yimin zancen yaya nayi rantsuwa
bazanyi kaffara ba,Muka danyi shiru na wani
lokaci,sannna yasake yin 'yar gyaran murya
"Sadiya nasan kisoma tsayawa da masu sonki
ko?"
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Nadubeshi "banajin zan bata lilacina gurin kula
su,domin al'amarinsu sai su."
Yayi dan murmushi "karkiyi kudin goro"
Nan nanunamasa layin muka shiga,gabana yana
ta faduwa sabida irin kallon da yaya Usaman
yake yimin. Nace ga gidannan.ya tsaya ya
dubeni.
"Zan dawo in daukeki"
Nace a'a kayi hakuri daga nan zanwuce wata
unguwar,nagode.
Yace "ina zaki!"
Nadubeshi "Gidan kawata"
Yace "Ok! Shikenan, kila zan dawo nanda anjima
inna zaton zamu tattauna wata magama mai
muhummanci
Nace to sai kazo.
Jiki babu karfi nashiga gidan sunan,duk da irin
shewa da wasa da dariya da abokan aikina keyi
ni nakasa ko murmushi.
Malama Bilkisu ta dubeni tace wai Malaman
sadiya kodai baki da lafiyane?nai dan yake kaina
ciwo yake Sukayimin sannu mai jegon har
dacewa ke kam tunda kika haihu shi kenan kika
zama sarkin ciwo. Nace aykam gashi nan na
kasa maida jikina. Adaddape nayi minti 40
agidan nafito na nufi gidan Ayshata sai taganni
kamar an jeho ni ta tashi tare dapadan lfy?
Nace Uhm wata sabuwace tasamu. Tace kuma,
to zauna kisha ruwa kin taki sa'a yau alalar
gwangwani nayi. Naja tsaki ni wallahi yau ko
nama kikayi zalla bana zaton zan iya ci. Tace
meyafaru? Nan na bata lbrn duk yanda mukayi
da yaya Usman itama dai ta damu amma tace
balallai yace yana sonaba wai kila zuciya tace
kawai ta zargi hakan nace toh shikenan. Sai
bayan magariba na yimata sallama ta rako ni na
hau mashin ina hanya naji wayata na ruri, ina
dagawa iya ta rufe ni da fada ina natsaya ga
Sadiq yana ta ihu? Nace gidan Aysha nawuce
gani nan tafe. Ina shiga yaya naci karo dashi zai
fito dashi a kafada yana ta kuka, duk da darene
na raya cewa fuskar shi a daure take ranshi
kuma a bace yake, nashige nazauna a falo ina
ninke mayafina sai gashi. Kin tafi yawon
banzanki kin bar yaro yana ta kuka ko? Ina
kikaje? Naki ko dubanshi nagama ninke
mayafina na mike zan shiga uwar daki yace baki
amshe shiba yana kuka? Iya ta sallame sallah
tace ki daukeshi mana ya jima yana kuka, nace
to. Saida nakai mayafina na ajiye sannan nafito
fuska daure na isa gurinshi namika hannu cikin
harara yabani shi sannan yayi kwafa. Kisani in
zaki tafi yawon banzanki ki daina ajiye min yaro
a gisa yana kuka banda shashanci me zai sa
mace tafita har magriba. Na zaci acikin zuciya
nake magana ashe tafito fili ina ruwana da
kukan shi zan kiyin harkar gabana ne saboda
shi? Sai muryar Yaya naji yace Iyee haka kikace?
Nayi shiru. Tozan dauki yarona in hada shi da
yan uwansa in yaso ke kije kiyi ta gantalinki.
Nazauna nasoma bashi nono ina jijjiga nace
Tabdi Ay wallahu bazan bada dana ba koh
gaban Alkali Za'a,Iya dai tana jin mu bata
tankaba yace basai Alkaliba ahannunki zan
amshe shi kicika baki kigani. Nakalli iya don na
soma fargabar zantukanshi tsaf zai iya,Nace iya
kifada masa yafitga harkata yadaina cemin ina
gantali. Iya tace ki kyaleshi yazo yadauki dan
nasa gantali kuwa ai kin isa yine. Yatausasa
murya Iya kidena dauremata gindi tanamin
rashin kunya. Yakalleni. Zan targadaki in kika yi
wasa. Namike nashige daki shi kuma
yawuce.......Zandakata a nan, acigaba da hakuri
dani.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Darajar Yayana4-03
Posted by ANaM Dorayi on 10:47 PM, 13-Apr-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
_________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Mama natawasan ruwa a karamin fanfon cikin
bandakin,Khausar ta kalleshi cikin fargaba amma
bata tashi daga inda takeba,jiratake yafara
yimata fada kamar yanda in Mujidat taci Zalinta
sanna tayimata karya gurin Abbanta cewa Tayi
kaza-tayi kaza, yayi mata fada amma sai taga
yamaida kofar ya rufe kuma yamaida
mukullin,dan tajiyo kara,sabon kuka tasoma
Mama ta juyo tan kallonta.
Cikin zafin rai Aliyu Yayi dakin Mujidat,turo kofar
dayayi da karfi shiyasa ta tura wayar a karkashin
pillow sanna ta mike zubur, ya kalli pillon sannan
ya kalleta,rashin gaskiya ya bayyana fuskarta.
Sanna tace, "My Dear sannu da zuwa."
Ya dauke kansa daga kallonta sannnan yace, "ina
yarana?"
Gabanta yabadi sakamakon tinowa datayi ta
kullesu a bandaki,cikin inina tace sun..suna falo
kokuma dakinsu bari inkirasu,yadan kauce ta
wuce shikuma yabi bayanta. Cikin takun isa
tashiga cikin dakin sannna tafito tace, "ina
yarannan suka shiga?" Nahanasu Khausar
yawonnan amma sunki,bari induba gidan maman
Markus,
Aliyu yace,"kinsan inda suke dan haka nunamin"
Tace, "ni bansab inda suka shigabafa a falo na
barsu"
Yace, "yaya basu tafi da yaronkiba sai sukadai"
Tace, "Amma dai kasan Abdul bashi yarda
dakowa"
Yace, "bansaniba, kin rufemin yara a toilet?"
Ta zaro ido "suna Toilet?" Ta nufi bandakin da
sassarfa,Aliyu yabi bayanta,ta bude mukullin
hannunta na rawa,zunmbur Khausar ta mike
hannunta na rawa tana cewa yi hakuri Aunty
nadena kar ki dokeni.
Tace zonan Khausar me kukeyi a nan?
Tadaga Al'amin tana cigaba da cewa, "haba
Khausar"....
Aliyu yana tsaye cikin takaici da bakin ciki, domin
ko karamin yaro zai fahimci cewA kawo yarantayi
ta rufe amma tana nema ta raina masa hankli.
Sai da tayiwa yaran wanka tana cewa haba
yarana karku kara ba'a wasa a toilet. Saida
tagama musu wankan suna fitowa zata fito ya
hankada ciki ta koma da baya tafadi,ya maida
kofar ya kulle sannan ya zare mukullin yabi yaran
zuwa dakinsu, yazauna bakin gado yana
kallonsu.kausar ta dakko musu kaya,hawaye ke
zuba daga idanunshi, yaranshi duk sun lalace ba
wata cikakkiyar tsafta,yaran da mutane ungwa
suke labarinsu a makaranta suke amsar kyautuna
sabida tsafta dubesu duk sunyi baki, gashin su
khausar ya lalace, kayansu duka bakula. A fiili
yace, "Sadiya kin tarwatsamu," yasake kallon
yaran yaga suna kallonshi yamike yaje ya hadasu
ya rungume yana cewa, "Kuyi hakuri yarana, ba
laifina bane laifin mamankune" sunfi minti daya
haka sannan ya sakesu yace, "inkaiku gurin
wasan yar ko?
Skace, "e"
Yace, "to,kokuma kuna jin yunwane."
Nanma sukace, "e"
Yace, "to bari inyi wank"
Yace, "ina sababbin kayan dana siyo muku."
Khausar tace, "suna dakin anty"
Yatafi dakin ya hau bincike har ya binciko kayan
yazo yasamusu,sannan shima yaje yayi wanka
yafito cikin wani yadi mara nauyi me ruwab
siminti, sannan takalmin da hular wadanda suka
dace, har zai wuce sai yaleka dakinta, har yanzun
danta na bacci, yadaga fillon sai ga waya BB ya
dakko ya zura a aljihu yafice ya kwashi
yaran,yanajinta tana buga kofa tanacewa, "My
Dear dan Allah ka budeni."
Yace, "kiji abinda sukaji"
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
yafice yazuba yaranshi a mota suka wuce.
Ranar dai yaran sunji dadi duk da Khausar ta
kasa walwala amma fuskarta a sake alamar taji
dadi, yaymusu siyayya sosai
Basu dawo gidanba sai da yayi sallar isha.
Yasamu Abdul yatashi yayi kashi da fitsari a gado
da kasa, yaje ya budeta tayi kuka ta gaji dan tana
jiyo kukan danta badamar ta je gunsa,
tasakarmasa harara sannan taja tsaki ta wuce,
dariya yayi don turamata haushi.yana ta re da
yaransa har sukai bacci sanna yaciri wayar
yasoma binciki amma hakan ya faskara saboda
security datsa, yamike yatafi dakinta yatara da ita
tana waya da karamar wayar da kullum yake
tsammanin ita kadai ke gareta ya tatsuramata ido
dan son fahimtar da wa take wayar amma sai
tayi sallma tare sa cewa, "momyi sai anjima."
Ya dago ya nuna mata wayarta dake hannunsa
yace, "wannan wayar waye?"
Tace, "tawace" cikin gadara yace, "ina kika samu
kudin siyan wannan wayar dubu sittin?"
Gabanta ya fadi amma sai ta dake tace, "ni ba
haka na siyaba second hand na siya."
Yace, "gurin wa kika siya?"
Tace, "gurin kawata."
"Wacece kawar taki?"
Tace, "Azima"
Nawa kika siya?
Tace, "dubu ashirin"
Yace, "a ina kika samu kudin?"
Cikin kosawa tare da daga murya tace, "Auncle
yabani,
Wai sata nayi da kasani a gaba da wadannan
tanbayoyin?"
Ya mika mata, "ciremin scurity"
Ta amsa ta cire tana kokarin shiga wasu guraren
ta goge wasu abubuwan ya fisge wayar yafita, ta
biyoshi tana cewa ni kabani wayata ba kai
kaseminba,
Afalo yazauna sanna ya kalleta kallon zargi, "karki
karso min nan, inbadan kinsan baki da gaskiyaba
menen dan mijinki yadauki wayarki?"
Tace, "nadamune dan zaka duba wayata meye a
ciki?
Kayi ta dubawa nidai nace kabani a buna tinda
bakaine kaseminba"
Baisake tankamataba, yayi iya bincikensa baiga
wani abu ba amma cikin inbox dinta na message
yaga wani sako da yadauki hankalinsa cewa
akayi,
"Malama ki aikomin da cikon kudin aikina inba
hakaba zanyi miki rashin mutunc daga Jamilu."
Yaduba ranar da aka turo sakon ya lissafa kwana
tara kenan,ya tura sakon zuwa wayarshi sannan
ya aje wayar a hannun kujera tazo ta dauka ta
wuce. sam bata tinanin wannan sakon
damuwarta karyashiga group dinsu yaga abinda
sukeyi,dan in hirar da sukeyi da mazane tasan
bazai ganiba tinda tana gogewa shikuma bai
tsaya wani shiga group ba.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Sunfi kwana uku suna gaba,tafita lamarinshi da
yayanshi,shinma yafita shirginta,sai hidimarsa
yake da yaransa.Nazari tayi taga suke
cutuwa,don haka ta sauke girmankai tare da
samunshi a dakinshi tsakar dare inda tabashi
hakuri,tare da yimasa alkawarin bazata karaba.
Cikin kwanakin da suka biyo baya tana kokarin
dannar zuciyarta dan ta kyutatawa yaran,sabida
ubansu ya yarda ta canja,saidai yaran sunki sakin
jiki da ita, data lura yasaki jikin sai takoma
halinta,yanzu bata rufesu a bandaki saidai duka
kamar jakuna, dan kuskure kadan na yaro sai
takama tayita duka.
Cikin haka wata ranara litinin su Khausar sun
dawo daga makaranta dauke da yunwa,sunfi
minti talatin sannan ta tashi daga chatting din
tabasu abinci,wanda ko Al'amin sai yacinye.
Kausar tace, "Anti Wannan fa bazai ishemuba,"
Ta watso mata wata harara ta nufi dakinta tana
cewa, "Dama ni nace ku koshine?"
Khausar ta Mika musu tace, "kuci," sun cinye
Amma basu koshiba, Don haka khausar tace
kibari in ta dan dade zanje in debo muku nima in
debo nawa,Don ka dayushe dama idan basu
koshiba takan dan lababa ta debomusu.
Kamar kullum ta taka kujera tana cikin zubawa
sai taji kamar motsin Auntynsu ashe
Mamace,tana kokarin sakkowa kujerara ta gurde,
Kausar ta fado, shi kuma plate din yayi sama sai
yafada kan wasu plates din 'yan uwanshi na
tangaran,nanfa kakejin tartsatsi yana tashi,da
gudu Mujidat ta fito.
Khausar ta mike jiki na bari tsoma cewa , "Anty yi
hakuri tana kka."
Mujidat tace, "ok! Allah yakamaki dama kece me
satar abinci kullum inna tanbaya kice bakebace
ko?"
Cikin rawar muraya khausar tace, "zasu karane,ni
ko cima banyiba."
Tace, "Ina ruwana,dole inzaneku yau, kizo ki
gyaramin kitchen bari innemo wayar wuta."
Ai tana juyawa khausar tafita da gudu inda tadau
takalmansu suka gudu,Mujidat tafito bata
gansuba,tace "oh! Kunguduko?zaku dawone."
Duk da cewa barikin 'yan sanda da tsaro amma
sai Allah yakauda idon kowa basu gansuba har
suka fice.
Al'amen yace, "yaya Khausar ina zamuje? Ko
mutafi Office grin Baba?"
Khausar tace, "inmunje zai dawo damune ko Yayi
mata fada,in Yayi tafiyrs Sai ta dakemu,"
Al'amin yace, "emana , kawai mu tafi gurin
Momy."
Khausar tace, "zamu iyane? Kadunafa?"
Mama tace, "nima zanje Momy kinji Yaya
Khausar"
Khausar tace, "to mama zaki iya Zuwa a kasa?"
Mama tace e
Almen yace, "in tagaji sai ki goyata"
Khausar tace, "muje to kila mugane.'
Sunyi ta zagaye cikin garin Abuja har duhun
Magriba yasoma shigowa,inda suka Isa kusa da
wani Store na saida kayan shaye shaye na
zamani, suna son su sha ruwa, ga yunwa,in
mama tayi kuka sai Khausar tace, "yi shiru mun
kusa"
Khausar ta Isa gurin wani mutumi dake tsaye
yana shan kankanar gwangwani, tace, "Baba dan
Allah kasammana ruwa."
Yakalleta ya kalli su Mama yace, "kai inazaku?"
Khausar tace, "Kaduna"
Yace, "Inna zuwa"
Yaje yafito da ruwan gora yabasu suka sha
sannan yakirasu gefe yanayimusu tanbayoyi har
mutane suka taru,nanfa akayi ta shawarwari
wasu suna Cewa akaisu makaranarsu inyaso su
can sai su kira iyayensu,tunda ansan
makarantar,jin haka yasa Khausar tashiga kuka
tana cewa, "Kutaimakamana wallahi antynmu
zata kashemu,kukaimu kadna gurin Momynmu."
Suma su Al'amin kuka sukeyi dan haka sai
sukace, "tinda shi wanna daya saimusu ruwa
direban motane sai yatafi dasu Kadunan indai
sunsan unguwarsu." Dayake daga gurin babu nisa
zuwa tasha dan haka sai suka tafi..
Mujidat bata tina da cewa yarannan basa gidanba
saida Aliyu yakirata a waya yace ta shirya
yarannan zaizo yakaisu Islamiyyar dayayi musu
register,firgigit ta mike tana cewa ai saita dokesu
babu fashi.saidai me?tayi Neman duniya cikin
gidan da makota basanan,nanfa hankalinta ya
tashi,makota suka firfito,kafin wani lokaci
ankarade rukuninsu da neman yaran,amma babu
wanda yagansu, saidai masu cewa tabbas
sungansu da takalman makaranta a
hannusu,wasu kuma suce da kayan makaranta.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Mujidat taci kuka ta koshi,gashi ta kasa kiran
babansu dan tsoro.makotansu kuwa da suka San
abin da takeyi wa yaran cewa suke Allah yakara,
saidai munafukn dake bin bayanta ne ke tayata
damuwa.
Yana shirin zuwa don kaisu sabuwar islamiyyar
da yasasu saiga wayar makocins wai bafa aga
'ya'yansaba, cikin tashin hankali yanufo gidan.Sai
yasamu gida dankam da mutne,ya kalli Mujidat
"Ina Yayana?"
Tace, "bangasuba sunyi barnane a kitchen suka
gudu."
Baice kalaba ya nufi gidan,sannan yafito yakira
"yansanda suzo gidan shi,sanna yace kowa yatafi
yagode.
Kafin wani lokaci "Yansanda sun karaso nan yasa
sukama Mujidat sai ta fadi inda takaimasa yara.
Cikin dare 'yansanda sai faman neman yara suke,
duk inda yakamat asanar an sanar, hanklin Aliyu
yatashi Karshe.karshe yakira Usman yafada
masa,amma yace yabar zancen a tsakaninsu dan
bayason su Iya suji,Usman yace Allah ya
bayyanasu.
Abu kamar wasa har cikindare babu labarin
yaran. Daidai wanna lokacin suna can akan
hanya,inda direban yasasu a bayan Mota yakashe
kujer daya kusa da wata mata inda yace "Don
Allah ta lurar masa dasu," duk da tsare motocin
da 'yansanda sukeyi suna haskawa sam babu
wanda yagano yaran,shiko direban bemasan
yaran ake nemaba balle yayi wani bayani.
Sunyi isowar dare,don haka yagama da fasinger
yanufi gidansa da yaran,wadanda harsunyi bacci,
matarsa tanada fahimta,baisha wahalaba wajen
fahimtar da itaba, nan yaran suka kwana.
Washgri akayi Tayi musu tanbayar Sunan unguwar
ta momynsu Amma suka kasa tunawa,gidan me
unguwarsu ba nisa,don haka sai yaje dasu
gurinsa,suma dai sunyi iya tanbayoyinsu
ba'aganeba,Sai matar me ungwar tabasu
shawara suje gidan TV da yaran,aikuwa basuyi
kasa agwiwaba suka nufi gidan DITV inda ake
gabatar da wani shiri na gari ya waye.
Daidai wanna lokcin inna zaune agaban TV inna
kallon shirin domin dama baya wuceni,innayi
innashan Tea. Iyama na son shirin sosai,don haka
tana ta kokari tafito daga kitchen ta iso.Kamar
daga sama sai akace ga wasu bayinAllah suna
bada Cigiyar iyayen wadannan Yara, mai
sanarwar yafada, ganin an hasko fuskar Khausar
cikin daga Murya nace Iya Iya zo kigani,da
tuntube tafita tana fadin lafiya? Itama nan
tazauna dabar.daidai lokacin ana tanbayrsu
sunayensu suka fada,dan Jaridar ya haska
Khausar
"Yarina yakikace Sunan ki?"
Tace, "Khausar Aliyu Tukur Hadeja"
"Daga ina?"
"Abuja"
"Ina Zaku?"
"Kaduna gurin momynmu"
"To can Abujan gurin wa kuke?"
"Gurin antynmu"
"Ina bbanku?"
"Yana gurin aiki."
"Me akayi muku zaku dawo gurin momynku?"
"Dukanmu Auntynmu keyi,kuma bata bamu
abinci muna kosh,jiyama naje zankaro aboye
batasaniba,zan krawa su Momy dama ni banciba
duka nabarmusu,shine nafadi,dataji karar
fashewar abu tafito,shine taje dakko wayar wuta
sai muka fito Muka kwashi takalmanmu Muka
gudu."
Yace, "to kinsa unguwar da momynku take?"
"Da nasani yanzu namanta."
"To yasunan mamanku?"
"Sadiya"
"Babankufa?"
"Aliyu Tukur Hadeja"
"Meye sana'arsa?"
Tace, "dansadane"
Nantake dan jaridar yace badai Aliyu Tukur din
danasaniba,in shine kuwa ai sanannene,yataba
rike kakakin rindinar yansanda alokacin yana ASP.
Mai unguwa yace shekarun baya ko.
Ai tini na jike shrkaf da gumi da hawaye har da
majina, yaranane wadannna ? Sai ga Habu
yashigo da sauri yace Aunty Ku kunna TV,Sai
yasamemu cikin kuka,yace iya kutaso muje gidan
me unguwa,na dauki lanbar wayar dayabayar,
gidan sa kuma hayine layin yandinki,dakyar
namike wayata tana ta ringi amma nakasa
dagata,nasan kawyenane dasukaga yaran,tin
kafin mutafi mkota dai shigowa suke suna mana
jaje gami da barka da arziki.
Munshiga gidan,sashin matar me unguwar, Mama
tana wasa,khausar da Al'amin suna ta zantuka
kasakasa,mukayi sallama yaran suka dubemu, da
karfi kausar tace Momy! Se rige rigen tahowa
gurina,na hadasu su ukun na rungumesu
jikina,inna kuka suma suna kka, duk mtanen
gurin suma kuka suke.nadauki Mama inna
kallonta,nadubi Iya cikin kunci
Nace, "dubi yarana yanda suka llce,"
Iya tace, "su da Allah sun cuci Kansu,menene
riba don ka cuci karamin yaro?" Nandai akayi abin
dayakamata muka dauki yara muka nufi gida.
Gidan cike da makota Sai barka da arziki
akeyimana,Allah yasa sunfada hannu nagari.har
lanbar direban na karba dan yimasa godiya ta
musamman sabida taimakon dayayimana.
Tini Habu yafesawa Yaya cewa abga su Khausar
anan Kaduna.Habu yabashi labarin komai,shi
kansa yasan tinda yarannna sukazo gurin iya dole
ya hakura dasu,amma yaji dadin ganinsu.yanufi
office dinsu yasa asaki Mujidat,ta fito tayi wujiga
wijiga, yace to bafa gidanshiba sai ta nemi gurin
zuwa,tace ina Abdul? Yace ai ba yaronkibane
yaronane na amshi dana.
Tace, "kana zaton dan ka boyemin Yaro zanki inje
infadawa iyayenka? ai dole su Sani."
Yace, "kekisani,saidai kisani zakikoma Kadunane
bayan kinkoma gidan Ubanki Lagos."
Aikuwa yasa aka kaita har garin da 'yan
kayanta,ko gani Abdul din ya hana tayi,yakaishi
gidan wani abokinsa a Asokoro.Mujidat ta
jinjinawa wulakancin da Aliyu Yayi mata,Amma
tace indai itace yaci Bashi,sannna tinda be
saketaba da sauki.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ya nufo kaduna cikin fargaba. Nikam na tsefe kan
yarana na wanne,akaje akayi musu kitso nayi
musu lalle. Munsha labarin irin wuyar da suka
sha a baki Khausar ni da iya, aikuwa munsha
kuka sabida tausayinsu.
Karfe uku ina zaune da 'Ya'yana cikin farinciki
inna yanke musu farce,Mama nakeyiwa magama
yiwa sauran.Khausar na dauke da Sadiq
tanayimasa wasa tace "Momy Sadiq dinki wallahi
dariya Yake yimin damun hada ido ya sannine?"
Nace, "kullum sainabashi labarinku, yasanku
dukkanku...."Sallamar yayace ya katsemu,sainaga
Khausar ta mike da gudu ta nufi daki Al'amin ma
yabita,Mamace kawai naga ta nufi Yaya tanamai
Oyoyo oyoyo,na hade raina tamkar zan saki
kuka,sanna na kauda kai nadauki wayata inna
latsawa. Yanufi cikin daki gurin iya, su Khausar
duk sun makale a bayanta tana Cewa, "lafiya
kuke boyewa?" Sai kuwa Yaya Yayi sallama,tsaki
Iya taja takasa amsa sallamar, yazauna tare da
sunkuyar dakai yace, "ina yini"
Ta kauda kai tace, "lafiya,"
Yace, "nazone inbada hakuri kan laifin danasan
za'a gani nawa,duk dacewa bansan fitarsuna
tinda ni bama na gida,laifin Mujidat ne kuma
nayi mata hukunci."
Iya tace, "can da matsalarku, sai dai abinda
zanfadamaka yarannan sunzo kenan,kuma abin
da kukayi musu Ku da Allahnku,"
Aliyu yace, "Dama ni bawai zan Koma dasubane."
Iya tace, "ai nazaci takardara sammaci kazo
kawomana." Ya mike yasake fadin aymin afuwa.
Ya dubi Khausar, "bazaku gaisheniba?"
Tace, "ina wuni Abba,"
Almin kuwa cewa Yayi, "mudai bazamu bikaba,"
Yace dama badaku zan tafiba.
Ya iso gurin su Khausar ya dauki Sadiq yafita.
Bai zaci zai samu sauki a guri Iyaba,yasandai
damuwar dama kar yakuma daukan yaran, kuma
dama ya yanke hukuncin barinsu fishintama na
yaune.
Yakira Usaman a waya suka gaisa samasama yace
,"Aboki kana gidane in iso ? Yunwa nake ji,gidan
su Iya kuma babu fuska."
Usaman yayi 'yar Dariya sannnan yace, "ka isa
gidan zan sameka a can."
Aliyu yace, "kayi nisane?"
"Inna Office din 'yansanda na nan unguwar."
Aliyu yace, "lafiya me kake a gurin?"
Usam yace, "wani dan case ne."
Aliyu yace, "shine bazaka sanar daniba, bari
inzo."
Ciki yakoma yamaida Sadiq, a cinyata ya ajiyeshi
ya fita,yana Isa office yansanda suka soma
kamewa suna sara masa, Oga yana ciki.
Agaban DPO yasmu yaron tare da Usama, DPO
ya mike ya kame sannan suka gaisa. Aliyu ya kalli
Usman, "Yaya, me yafaru aboki,"
Usaman yace, "irin yarannanne masu bude
account da Sunan mutane su kullamusu sharri."
Aliyu yace, "to shi wa yayi?"
Usma yace, "shine yayiwa Sadiya,"
Aliyu yace cikin sauri, "wace Sadiya,"
Usman yace,"wadda nake neman aurenta."
Kan Aliyu ya kulle yace, "dama zakayi aure?"
Yace, "Eh,bamuyi zancen dakaiba ko?"
Ya kalli yaron, "kasan Wannan?"Yanuna masa
Aliyu, yaron yace, "a'a,"
Daga nan Usman ya kalli DPO; "yanzu ni zan tafi "
Aliyu ya zauna, "bangane zaka tafiba, wai yaya
case din yafaru?"Nan aka umarci Jamilu yayi
bayani kamar yanda Yayi dazu.
Jamilu yace, "nidai wani yarone kanin Aunty
Ramatu ya kirani inzo zanyiwa wata Auntynsu
wani aiki,dama yana zuwa Cafe dinmu yana
Browsing, danazo sai tace inbudemata wasu
account guda biyu,zata yiwa kishiyarta sharri,
kawai Sai na yarda sabida ta yarda zata bani
Dubu5,nikuma dama inna neman dubu 5 din
sabida zanse JAMB Form dan shiga Jami'a.shine
nayi mata har yau kuma bata cikamin dubu
biyunba,sunma tashi daga garin."
Aliyu ya dinga kallon Jamilu tamkar yanason Yayi
tajin labarin kokuma labarin ya burgeshi. Usman
yace Jamilu sakamakon wanna hada Chat din
danayi nafada maka kasan aure yarabu? karaba
uwa da 'Ya'yanta? yanuna Aliyu Kaga mijinsu
nan,wadda kayiwa sharrin da wadda tasaka kayi
aikin."
Mamaki Yakama DOP yace, "Dama abin yafaru ne
a gidan Oga?"
Aliyu dai hannu a cikin aljihunsa yarasa me zaice,
Jamilu kuwa zubewa Yayi gban Aliyu yana
rokonshi cewa a yafemasa, shi dama wannanne
karo na farko da yasoma kuma bazai karba.Aliyu
yamike yakalli Jamilu, "Ayimaka hukunci daidai da
lefinka sabida masu hali irin naka." Har waje DPO
ya rako Aliyu, sam Yakasa magana sai zufa
yakeyi, zuciyarshi