Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

daka fito da abunka kana
ganin ya maka tsufa sabo kake so, lokacin wani
kuma zai ga cewa na kannan shine sabo agurinsa
Allah yayi miki zabin Alkairi, nace amin.
Daren ranar su Yaya Sulaiman suka zo da shi su
hudu wai iya tayi hakuri tayafe masa sannan
suka matsa masa cewa ya maido da matarsa
kuma ya yarda amma da sharadin zata daina
koyarwa. Ina kwance kan gado a uwar daka ina
jin su tamkar in taso in fito in ce bazan koma ba
amma sai na tsaya inji me iya zatace? Ay kuwa
sai naji Iya tace da farko dai kamar yanda na
shaida masa dazun ni bai min laifi ba bare ya
bani hakuri in da ace ni wata ce lokacin da
rigimar tafaru yaneme ni mana sai kurum yatafi
ya aikata son ransa yanzun yazo yana ban
hakuri,ni a wa? Batun kome kuwa ga matarsa
nan adaki tazo in zata koma bazan sata ba kuma
bazan hanata ba, Tadaga murya Sadiya na'amsa
tace zo nafito da dana akafada na zauna
gefe.tace nasan kinji komai dan haka in zaki
koma sai ki fada musu, shidai sun bashi baki ya
yarda,Budar bakin da nayi sai kuka nace yaya
kuyi Hakuri da abinda zance in Yaya Aliyu ne ya
rage namiji a doron duniya wallahi tallahi bazan
aure shiba bana kosan ganin shi ya fita a raina
sam.Iya tace tashi ki koma ciki sannan tace kunji
koh? To kuma na roke ku da kar ku sake
zuwamin da wannan zance ko gaba an rufe
wannan babi in dansa ya isa yaye yazo ya
dauka,bansan lokacin da nace Iya harda wannan
ma za'a rabani tace Allah ya baki wani mijin na
gari ki haifi wasu yayan Sadiya,sai lokacin Aliyu ya
dago ya dubi Iya sabida yaji zafin kalmarta
sannan ya sake sunkuyar da kai Aliyu yaba yaya
Sulaiman kudin yadan matsa yace iya ayita hakuri
shin ina Sadiyarne? Na fito ya miko mini nace a, a
yaya muna da komai na koma ciki yace ke Sadiya
zoki karba hakkinkine da danki Iya tace tunda
tace bata so saiku barta ko ku tashi kuje zamu
kwanta...zamudakata anan,fatan zamuyi sallar
juma'a lafiya
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

Darajar Yayana4-02
Posted by ANaM Dorayi on 12:11 AM, 12-Apr-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
_________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Haka suka fita jiki babu karfikowa ya nufi gidan
shi suka nufi nasu da safe na gama yiwa yarona
wanka kenan sai gashi ya shigo sanye da
kananan kaya sai yaune ma na kalleshi yadan
rame yayi duhu natabe baki sannan na bata rai
Iya ta fita siyo mana biredi na gama na kwantar
dashi kan kujera zan fita da ruwan sai naga yakai
hannu zai dauke shi da sauri na dauki yarona na
sashi a bayana na kwance zanin jikina wanda
dama na dora ne a saman dogon wando na
goyeshi sannan na dauki ruwan, yako ji haushi
cikin zafin rai yace me kike nufi? Nace duk
abinda kake nufi ,na kalleshi sama da kasa yace
nufinki bazan dauki yarona ba? Nace au shima
danka ne? Na zata inda nake zuwa na yoshi yace
karfa kiga Iya na daure miki gindi ki zata har kin
kai matsayin da zakiyi min rashin kunya dan
kinga na kyaleki ban dauki mataki a kankiba, nace
don Allah kaini kotun musulunci yace bani yarona
in ganshi? bazan bayarba,Sallamar Iya tasa
yazauna kan kujera nima nazauna, na kwantoshi
nasoma shafa masa mai Iya tashigo dakin
ganinshi sai ta daure fuska tace lafiya me kuma
yakawoka? Yace Iya gurinki in gaisheki tsaki taja
sannan tafita zuwa kicin Yakalleni Nan gidan
ubanane ba mai hana ni zuwa. Nima na
harareshi ina ruwana Allah yasa nima ina da
gidan uban. Kafin yayi magana sai ga Iya ta shigo
da ruwan zafi takalle ni zo ki karya cikin jego,
kawo shi in sa masa kayan. Nace to, bayan na
karasa sa masa pampers din na mika mata shi.
Ina zama yayi caraf ya mika hannu ya dauke shi
a hannun Iya na kalleshi cikin tsana nazauna
shima yaharareni sannan yazauna yana kallon
yaron, banzaci ya san sunan shiba sai naji ya ce
Iya Sadiq ma dani yake kama sosai yanda ban
tankaba itama bata tankaba. Yarungumeshi tsam
a kirjinshi, sai kurum nafita tsakar gida ina
karyawa. Ashe Iya ma ta shige uwar daka dan
haka yadauki kayan yana sa masa yagama
yamike yafito da shi ganin zai yi waje nabishi da
gudu a ganina zai tafi da shine, ina fadin Iya
zaitafi dashi nasha gabanshi,bani yarona dasauri
Iya tace kyaleshi yatafi dashi din seme? Nasoma
kuka shikuma sai hararata yake yi yaja tsaki
yawuce nace Yaya inka tafi dashi saina tona
asirinka tsam yatsaya sannan yawaiwayo yakalli
Iya itama shi take kallo sannan takalleni na isa
gabanshi namika hannu Bani yarona.Sai yamiko
minshi sannan yafita da sauri naje kan kujera
nazauna ina cika,Iya ta iso gabana wane irin
asirene zaki tona masa?yaken dariya na kakaro
birgace kawai nayi masa babu komai Iya. Tayi yar
dariya haba Sadiya shi mahaukacikane bayan ba
wani sirri jikinsa yayi sanyi haka? In dai da wani
abu kifadamin,Nace ba komai iya tace oho miki in
ma dashi, shiyasa wani lokacin banasan shiga
shirginku.Ni dai sim sim nayi daki.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Hudu da ashirin ina kwashe tuwo naji sallamar
shi ciki ciki na amsa, banyi tsammanin ma zaijiba
na dago nadubeshi cikin tsana, sai naga
hankalinshi yana kan yarona wanda nashimfida a
tabarma akan katifar shi nakwantar dashi akofar
daki Iya tana zaune kusa dashi. Dagudu na aje
tuwon dake hannuna nafito har ina tsallaka iya
nasuri dana nasa a baya naja zanina a igiyar
shanya nagoye shi sannan nakoma kicin ina jin
tsakinshi a raina nace kadai karata can.Daga inda
nake ina jiyo shi yana gaida Iya, dakyar ta amsa.
Yace zantafi zaria dama wani ayki nazoyi Kaduna
akwai wani malami ne da ake zaton kasurgumin
dan fashine to kan shi nake aiki,rahotanni sun
same mu cewa ya koma Zaria acikin satin nan
kafin inzo dan wata na biyu kenan ina nemanshi
tun daga Maiduguri nake biye dashi har zuwa
nan ina son Iya kitaya ni da addu'a Allah
yataimake ni. Iya tace Allah yabada sa'a. Yace
amin. Tace malami kuma dan fashi in banda son
duniya? Ay irinsu suna da yawa Iya kuma yana
siffatuwa ne da malai manyan malamai yana da
ilimin, sai dai shi dan fashine ga tsafi ,sama da
shekaru goma ankasa kamashi,kingako kamashi
nasarace. Iya tace Allah yataimaka yace amin
yaciro kudi gashi Iya. Tace a'a ai na fada maka
bamu da bukatar komai,yasake tausasa murya
Iya wannan fa tsakanin mune ni dake in baki
amsaba sai inga tamkar kin cire ni a tsatsonki,
Ya'ajiye gefenta. Iya kiyafemin natafi.,Bata ce
komaiba kuma bata dauki kudinba yazo bakin
kicin yajeho min wasu mukullai ga mukullin
gidanki nan kije ki dauki motarki aciki. Nadubeshi
fuska daure cikin harara nace bani da gida bare
mota in kana nufin motarka to bana so,tsaki yaja
sannan ya wuce batare daya dauki mukullanba.
Nafito gurin Iya rai a bace nace Iya naga har
kulashifa kikayi kuna hira har yana wani baki kudi
kina karba? Iya tace kin san shi naci zai tayimin
shiyasa narabu da shi ya aje kudin dan yatafi
yabamu guri sannan ina zulumin yanayin aykin
nan nashi wannan malamin kuwa dan fashi
tunkararsa hadarine ina tsoron karya halakashi.
Gadanga shiba mutumbane mai son neman tsarin
kai, da kaikayi koma kan mashekiya,da kai
magana zaice yana addu'a an san dai ita ce
dama kan gaba. Don haka itama Iya ban tanka
mataba wato ma tausayin shi takeji.

Aliyu yayi masauki unguwar Mazan Gudu gidsn
limamin unguwar da sunan cewa shi bakone
matafiyi ne. Hannu 2 aka karbeshi kwanansa 2
yace a nema masa daki na haya yana son yadan
kama sana'a yafada musu cewa rani yake Zuwa
garin Kaduna daga Hadeja yake,Liman har yayi
masa tambaya game da wasu unguwanni a can
Hajejan Allah yasa garuruwan da Aliyu yasani ne
ya kuma fada masa cewa ya sani. Liman yace sun
zauna sun danyi karatu a garin shekarun baya
lokacin suna yawon neman ilimi. Liman yace Aliyu
yazauna ga daki nan a zaure a gidansa na
dansane dake karatun boko a jihar sokoto a
jami'ar shehu dan fodio. Cikin sati daya yasaba
da makota. Akwai wani dan dandali da mazan
unguwar ke zama ko in ce majalisa. Tuni Aliyu ya
saba da yan majalisar in da ake zama ayi ta
labarin wane da wane ko duk wanda yagifta.
Anan yasamu labarin wannan malami daya sauka
gidan sarkin malaman kusfa ance yanda ilimi
sosai kuma yana bada fatawa. Aliyu yace dan
Allah wanda yasan gurin yayimasa rakiya don
yana son daukan karatu. Kullum 'yan majalisar
nan suna mamakin Aliyu duk irin shigar dayakeyi
ta kaya marasa kyau amma fatar jikinsa bata
nuna cewa daga kyauyen hadeja yakeba kamar
yanda yafadamusu. Akwaima wanda yakecewa
shifa yana wa fuskar Ali kallon sani.
Cikin sati 2 sukayi sabo da Malamin wanda yasaki
jiki da Aliyun amma sai dai Malamin ya fadawa
Aliyu shifa malamine mai yawon yada da'awa
don haka daga nan zai wuce Katsina ne tafi tafi
har Nijar. Aliyu yace in ba damuwa zaibi shi,Aliyu
ya lura da yanda malamin ke daga waya akai-
akai sannan ya lura da irin kudin da malamin ke
rabawa jama'a sadaka. Duk binciken dayayi ya
gano cewa malanin ne wanda yake nema sai dai
dama yana da labarin matsawar malamin yana
cikin daki bazai kamuba. Ana gobe zasu bar garin
kamar yanda suka shirya har da shi Aliyu
shikuma ya daura aniyar kama shine aranar
jajiberen tafiyar. Karfe 2 sun taso daga sallar
Azahar Aliyu hankalinshi tashe burin shi yanzun
idan sun iso kafin su isa gidsn malamin ya sauke
yashige daki. Aliyu yakalli malamin. Allah
yagafarta malam naga jama'ar wannan garin
suna alhinin rabuwa dakai shin bazamu dan kara
kwanakiba? Malam yakalli Aliyu ina da dalilin
barin garinnan asubahin gobe.Aliyu yace Allah
yasa haka shine mafi Alkairi. Malam yace ameen.
Sai dai kai ina mamakin yanda kake son bina ban
cika sakewa da mutaneba amma kai raina ya
kwanta dakai amma daganinka ka taba zaman
cikin birni? Aliy yace e duk cikin gari nayi
rayuwata ban zauna gidaba, Malam yayi
murmushi toh Aliyu sai dai kayi hakuri ina zaton
bazanje dakaiba. Aliyu yace saboda me malam?
Malam ya gyara tsayuwar wato malam Ali an
sanar dani cewa duk inda zan shiga kada in shiga
da mutumin cikin gari domin shine zai zamemin
hadari cikin rayuwata. Aliyu yace Allah gafarta
malam an fada maka kamannin shine munyi
kama? Yace ko kusa an dai ce min zai shiga jikina
sosai kuma zai cutar dani a rana irin ta gobe
shiyasa duk lokacin dazan bar gari nakan barshi
tun asubahi. Aliyu wanda ya kosa yaga isowar
jami'an tsaro yace toh Alagafarta yaya zaka yarda
da irin wannan kila ba gaskiya bane. Malam
yadafa kafadar Aliyu inayimaka fata nagari Allah
yasa zamu hadu wata rana amma wanda yafada
min zancen nan yasha fadamin zantuka suna
tabbata ina ji ajikina zamu sake haduwa da.....
Jiniyar motar 'Yansanda ce tasa malam bai karasa
zancenba sai Aliyu yaga malam ya daga kafada
yasa gudu cikin azama da kwarewa Aliyu yaciro
bindiga daga bayan wandasa ya harbi malam a
kafa take malam yafadi amma burinshi yakai daki
dan haka ya yunkura Aliyu yayi azama yacafkeshi.
Mutanan gurin sun cika da mamaki harma suka
taso da nufin jin ba'asi sai dai kafin suji dalili tuni
yan sanda sunyi zobe a gurin sun kuma cafke
wasu daga cikin makarraban malamin sannan an
samu muggan makamai cikin kayan malamin da
kudin kasar Amuruka(Dollar) da irin namu na
gida. Mutanan unguwar suna ta al'ajabin lamarin
yayinda wasu ke mamakin Aliyun wanda suka
zata shima yana cikin mukarraban malam. Ta
gidan lima suka bi mai masaukinsa,Aliyu yayi
musu sallama yadauki yan kayan shi tare dayi
masa alheri haka ma yen majalirarsu yatafi yabar
su da labarinshi tare da jinjinawa aykin shi.
Cikin wata hudu da aka damka aykin hannun
Aliyu ya samu nasara ya fara bibiyar malamin
tundaga maiduguri har kawo Kaduna sannan
Zaria inda yayi nasara sakamakon haka ya samu
lambar yabo tare da karin girma zuwa
mataimakin kwamishina na can Abuja haka nan
nasarar taja masa farin jini inda akayi ta haskashi
gidajen talabijin. Ina kallon Iya tunda Aliyu yazo
da batun aykin nan kullum cikin yimasa addu'a
take tare dayawaita sadaka. Araina nace da da
mahaifi sai Allah. Dubi duk haushinsa datakeji be
hanata yimasa addu'ab. Inzanje aiki yanzu gida
nake barin Sadiq sabida yana shan kamu. Iya
tasani gaba tana min fada wata ranar Litinin na
shirya zantapi aiki. Sadiya! Dan Allah shekarunki
nawa? Nace me yafaru Iya? Tace fadamin. Nace
26 Tace dubi duk yanda kika koma ba wani ado
ba kwalliyar da kikeyi ada, ki dage ko dan ki ba
Gadanga haushi,amma kullum sai kina yawo
kamar me takaba,Nace ni banima da kayan
kwalliyar,tace inzaki dawo ki tsaya kasuwa ki saya
in ma baki da kudi in baki,nace ina dashi a cikin
account dina,tace to.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ina zaune bayan na sallami daliban ajina sun fita
break nazabga tagumu ina tunanin zancen Iya
gaskiya ta fadamin bazan tsaya in tsufar da
kainaba tilas in nafita in shiga banki sannan in
shiga kasuwa. Shigowar alert ne ya tsaida
tunanina na dauka na duba kudi ne naira dubu
saba'in sannan yaya ne ya turo min. Haushi da
bakin ciki kamar inyi kuka don haushi. Dakyar
nabari aka tashi na nufi banki na ciri kudin daya
turomin naira dubu 70 na maida masa cikin
account dinsa sannan naciri dubu 20 dan yin
siyayyata acikin account dina. Nashiga cikin
kasuwa nasiyo mai na perpect nasiya duk kayan
shafawa, sannan nasai turaruka na har da kayan
humra dan dakaina nake hada humrata nasai
mayafai da takalma har atamfa na kara. Iya na
gani tace ko kefa. Nanfa nashiga gayuna kafin
wata daya na komo da farina da gayuna, sai dai
ban maida kibata sosaiba, ba wanda zai ganni
yazata ina da yara har 4. Wani abin dariya sai ga
mutane sun soma yin sallama dani.
Ranar wata juma'a ne sunan wata malamar da
muke koyarwa tare nayi kyau cikin leshi mai
ruwan madara ni kaina nasan nayi kyau taku dai
dai nake yi na tsallaka titi zan hau abin hawa sai
mota ta tsaya a gabana na waiwaya zanyi masifa
sainaga yaya Usman ne cikin dariya na isa gurin
shi. Yaya ashe kaine? Yace to na tsaya kafin inyi
magana sai naga za'syi min masifa nayi dariya ka
san mutane wai dasunga mutum ya tsaya sai
suce zasu dauki mutum. Yace hakane sai ina?
Nace nan Askulaye zani suna watace da muke
koyarwa tare ta haihu. Yace muje. Nace a'a
dakaje kada in batamaka lokaci yace hanya tace
ni gaba naci don kurmin mashi zanje. Nace ok.
Nashiga muka hau titi nace ina su Auntyna da su
Ummul? Yace duk suna lfy shine bakya son fita
da Sadiq koh? Nace shima ya saba da Iya baya
son bina. Yace ya huta da shan rana. Nace
wallahi. Naji cewa abokina yasamu karin girma
kwanaki? Nabata rai ina ruwana. Yayi dariya da
ruwanki mana koba dangantaka akwai su Kausar
nace harsu duk na barmasa na yafesu. Yace
bacin raine. Nace wai ya batun binciken? Yace
ina kan binciken kiris yarage in kammala. Murna
ta cikani cikin zakuwa nace kun gano kowane ne?
Yace eh toh na dai yi nasarar gano cewa mutum
dayane a abu uku Sulaiman din daya kawowa
aboki gulma shine malamin makarantarku kuma
shine Sadiya Abubakar mun gano hakan ne ta
hanyar lambar MTN Din dayayi amfani da ita
gurin cike form na account din da ya bude. Nace
a'a duk lamba daya yayi amfani? Yace a'a daban
daban ne sa'ar da muka ci duka na MTN ne
kuma duk yayi musu rijista taimakon dayayi
mana kenan. Nace Alhamdulillah. Muka danyi
shiru nawasu yan dakiku sai Usman yayi gyaran
murya yace, Sadiya! Nadube shi irin kallon
dayayimin yasa gabana faduwa nayi ta maza
nadauke kaina. In tambayeki mana? Nace
eh...ina...jinka. Nafada cikin in ina yace in
abokina yaji gaskiyar batun nasan zaku sasanta
koh? Nakalleshi da sauri nan take raina yabaci na
sunkuyar da kaina yaya Usman dan Allah na roke
ka kadaina yimin zancen yaya nayi rantsuwa
bazanyi kaffara ba,Muka danyi shiru na wani
lokaci,sannna yasake yin 'yar gyaran murya
"Sadiya nasan kisoma tsayawa da masu sonki
ko?"
Nadubeshi "banajin zan bata lilacina gurin kula
su,domin al'amarinsu sai su."
Yayi dan murmushi "karkiyi kudin goro"
Nan nanunamasa layin muka shiga,gabana yana
ta faduwa sabida irin kallon da yaya Usaman
yake yimin. Nace ga gidannan.ya tsaya ya
dubeni.
"Zan dawo in daukeki"
Nace a'a kayi hakuri daga nan zanwuce wata
unguwar,nagode.
Yace "ina zaki!"
Nadubeshi "Gidan kawata"
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Yace "Ok! Shikenan, kila zan dawo nanda anjima
inna zaton zamu tattauna wata magama mai
muhummanci
Nace to sai kazo.
Jiki babu karfi nashiga gidan sunan,duk da irin
shewa da wasa da dariya da abokan aikina keyi
ni nakasa ko murmushi.
Malama Bilkisu ta dubeni tace wai Malaman
sadiya kodai baki da lafiyane?nai dan yake kaina
ciwo yake Sukayimin sannu mai jegon har dacewa
ke kam tunda kika haihu shi kenan kika zama
sarkin ciwo. Nace aykam gashi nan na kasa maida
jikina. Adaddape nayi minti 40 agidan nafito na
nufi gidan Ayshata sai taganni kamar an jeho ni
ta tashi tare dapadan lfy? Nace Uhm wata
sabuwace tasamu. Tace kuma, to zauna kisha
ruwa kin taki sa'a yau alalar gwangwani nayi.
Naja tsaki ni wallahi yau ko nama kikayi zalla
bana zaton zan iya ci. Tace meyafaru? Nan na
bata lbrn duk yanda mukayi da yaya Usman
itama dai ta damu amma tace balallai yace yana
sonaba wai kila zuciya tace kawai ta zargi hakan
nace toh shikenan. Sai bayan magariba na yimata
sallama ta rako ni na hau mashin ina hanya naji
wayata na ruri, ina dagawa iya ta rufe ni da fada
ina natsaya ga Sadiq yana ta ihu? Nace gidan
Aysha nawuce gani nan tafe. Ina shiga yaya naci
karo dashi zai fito dashi a kafada yana ta kuka,
duk da darene na raya cewa fuskar shi a daure
take ranshi kuma a bace yake, nashige nazauna a
falo ina ninke mayafina sai gashi. Kin tafi yawon
banzanki kin bar yaro yana ta kuka ko? Ina
kikaje? Naki ko dubanshi nagama ninke mayafina
na mike zan shiga uwar daki yace baki amshe
shiba yana kuka? Iya ta sallame sallah tace ki
daukeshi mana ya jima yana kuka, nace to. Saida
nakai mayafina na ajiye sannan nafito fuska
daure na isa gurinshi namika hannu cikin harara
yabani shi sannan yayi kwafa. Kisani in zaki tafi
yawon banzanki ki daina ajiye min yaro a gisa
yana kuka banda shashanci me zai sa mace tafita
har magriba. Na zaci acikin zuciya nake magana
ashe tafito fili ina ruwana da kukan shi zan kiyin
harkar gabana ne saboda shi? Sai muryar Yaya
naji yace Iyee haka kikace? Nayi shiru. Tozan
dauki yarona in hada shi da yan uwansa in yaso
ke kije kiyi ta gantalinki. Nazauna nasoma bashi
nono ina jijjiga nace Tabdi Ay wallahu bazan bada
dana ba koh gaban Alkali Za'a,Iya dai tana jin mu
bata tankaba yace basai Alkaliba ahannunki zan
amshe shi kicika baki kigani. Nakalli iya don na
soma fargabar zantukanshi tsaf zai iya,Nace iya
kifada masa yafitga harkata yadaina cemin ina
gantali. Iya tace ki kyaleshi yazo yadauki dan
nasa gantali kuwa ai kin isa yine. Yatausasa
murya Iya kidena dauremata gindi tanamin
rashin kunya. Yakalleni. Zan targadaki in kika yi
wasa. Namike nashige daki shi kuma yawuce.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Haka suka fita jiki babu karfikowa ya nufi gidan
shi suka nufi nasu da safe na gama yiwa yarona
wanka kenan sai gashi ya shigo sanye da
kananan kaya sai yaune ma na kalleshi yadan
rame yayi duhu natabe baki sannan na bata rai
Iya ta fita siyo mana biredi na gama na kwantar
dashi kan kujera zan fita da ruwan sai naga yakai
hannu zai dauke shi da sauri na dauki yarona na
sashi a bayana na kwance zanin jikina wanda
dama na dora ne a saman dogon wando na
goyeshi sannan na dauki ruwan, yako ji haushi
cikin zafin rai yace me kike nufi? Nace duk
abinda kake nufi ,na kalleshi sama da kasa yace
nufinki bazan dauki yarona ba? Nace au shima
danka ne? Na zata inda nake zuwa na yoshi yace
karfa kiga Iya na daure miki gindi ki zata har kin
kai matsayin da zakiyi min rashin kunya dan
kinga na kyaleki ban dauki mataki a kankiba, nace
don Allah kaini kotun musulunci yace bani yarona
in ganshi? bazan bayarba,Sallamar Iya tasa
yazauna kan kujera nima nazauna, na kwantoshi
nasoma shafa masa mai Iya tashigo dakin
ganinshi sai ta daure fuska tace lafiya me kuma
yakawoka? Yace Iya gurinki in gaisheki tsaki taja
sannan tafita zuwa kicin Yakalleni Nan gidan
ubanane ba mai hana ni zuwa. Nima na
harareshi ina ruwana Allah yasa nima ina da
gidan uban. Kafin yayi magana sai ga Iya ta shigo
da ruwan zafi takalle ni zo ki karya cikin jego,
kawo shi in sa masa kayan. Nace to, bayan na
karasa sa masa pampers din na mika mata shi.
Ina zama yayi caraf ya mika hannu ya dauke shi
a hannun Iya na kalleshi cikin tsana nazauna
shima yaharareni sannan yazauna yana kallon
yaron, banzaci ya san sunan shiba sai naji ya ce
Iya Sadiq ma dani yake kama sosai yanda ban
tankaba itama bata tankaba. Yarungumeshi tsam
a kirjinshi, sai kurum nafita tsakar gida ina
karyawa. Ashe Iya ma ta shige uwar daka dan
haka yadauki kayan yana sa masa yagama
yamike yafito da shi ganin zai yi waje nabishi da
gudu a ganina zai tafi da shine, ina fadin Iya
zaitafi dashi nasha gabanshi,bani yarona dasauri
Iya tace kyaleshi yatafi dashi din seme? Nasoma
kuka shikuma sai hararata yake yi yaja tsaki
yawuce nace Yaya inka tafi dashi saina tona
asirinka tsam yatsaya sannan yawaiwayo yakalli
Iya itama shi take kallo sannan takalleni na isa
gabanshi namika hannu Bani yarona.Sai yamiko
minshi sannan yafita da sauri naje kan kujera
nazauna ina cika,Iya ta iso gabana wane irin
asirene zaki tona masa?yaken dariya na kakaro
birgace kawai nayi masa babu komai Iya. Tayi yar
dariya haba Sadiya shi mahaukacikane bayan ba
wani sirri jikinsa yayi sanyi haka? In dai da wani
abu kifadamin,Nace ba komai iya tace oho miki in
ma dashi, shiyasa wani lokacin banasan shiga
shirginku.Ni dai sim sim nayi daki.
Hudu da ashirin ina kwashe tuwo naji sallamar
shi ciki ciki na amsa, banyi tsammanin ma zaijiba
na dago nadubeshi cikin tsana, sai naga
hankalinshi yana kan yarona wanda nashimfida a
tabarma akan katifar shi nakwantar dashi akofar
daki Iya tana zaune kusa dashi. Dagudu na aje
tuwon dake hannuna nafito har ina tsallaka iya
nasuri dana nasa a baya naja zanina a igiyar
shanya nagoye shi sannan nakoma kicin ina jin
tsakinshi a raina nace kadai karata can.Daga inda
nake ina jiyo shi yana gaida Iya, dakyar ta amsa.
Yace zantafi zaria dama wani ayki nazoyi Kaduna
akwai wani malami ne da ake zaton kasurgumin
dan fashine to kan shi nake aiki,rahotanni sun
same mu cewa ya koma Zaria acikin satin nan
kafin inzo dan wata na biyu kenan ina nemanshi
tun daga Maiduguri nake biye dashi har zuwa
nan ina son Iya kitaya ni da addu'a Allah
yataimake ni. Iya tace Allah yabada sa'a. Yace
amin. Tace malami kuma dan fashi in banda son
duniya? Ay irinsu suna da yawa Iya kuma yana
siffatuwa ne da malai manyan malamai yana da
ilimin, sai dai shi dan fashine ga tsafi ,sama da
shekaru goma ankasa kamashi,kingako kamashi
nasarace. Iya tace Allah yataimaka yace amin
yaciro kudi gashi Iya. Tace a'a ai na fada maka
bamu da bukatar komai,yasake tausasa murya
Iya wannan fa tsakanin mune ni dake in baki
amsaba sai inga tamkar kin cire ni a tsatsonki,
Ya'ajiye gefenta. Iya kiyafemin natafi.,Bata ce
komaiba kuma bata dauki kudinba yazo bakin
kicin yajeho min wasu mukullai ga mukullin
gidanki nan kije ki dauki motarki aciki. Nadubeshi
fuska daure cikin harara nace bani da gida bare
mota in kana nufin motarka to bana so,tsaki yaja
sannan ya wuce batare daya dauki mukullanba.
Nafito gurin Iya rai a bace nace Iya naga har
kulashifa kikayi kuna hira har yana wani baki kudi
kina karba? Iya tace kin san shi naci zai tayimin
shiyasa narabu da shi ya aje kudin dan yatafi
yabamu guri sannan ina zulumin yanayin aykin
nan nashi wannan malamin kuwa dan fashi
tunkararsa hadarine ina tsoron karya halakashi.
Gadanga shiba mutumbane mai son neman tsarin
kai, da kaikayi koma kan mashekiya,da kai
magana zaice yana addu'a an san dai ita ce
dama kan gaba. Don haka itama Iya ban tanka
mataba wato ma tausayin shi takeji.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu yayi masauki unguwar Mazan Gudu gidsn
limamin unguwar da sunan cewa shi bakone
matafiyi ne. Hannu 2 aka karbeshi kwanansa 2
yace a nema masa daki na haya yana son yadan
kama sana'a yafada musu cewa rani yake Zuwa
garin Kaduna daga Hadeja yake,Liman har yayi
masa tambaya game da wasu unguwanni a can
Hajejan Allah yasa garuruwan da Aliyu yasani ne
ya kuma fada masa cewa ya sani. Liman yace sun
zauna sun danyi karatu a garin shekarun baya
lokacin suna yawon neman ilimi. Liman yace Aliyu
yazauna ga daki nan a zaure a gidansa na
dansane dake karatun boko a jihar sokoto a
jami'ar shehu dan fodio. Cikin sati daya yasaba
da makota. Akwai wani dan dandali da mazan
unguwar ke zama ko in ce majalisa. Tuni Aliyu ya
saba da yan majalisar in da ake zama ayi ta
labarin wane da wane ko duk wanda yagifta.
Anan yasamu labarin wannan malami daya sauka
gidan sarkin malaman kusfa ance yanda ilimi
sosai kuma yana bada fatawa. Aliyu yace dan
Allah wanda yasan gurin yayimasa rakiya don
yana son daukan karatu. Kullum 'yan majalisar
nan suna mamakin Aliyu duk irin shigar dayakeyi
ta kaya marasa kyau amma fatar jikinsa bata
nuna cewa daga kyauyen hadeja yakeba kamar
yanda yafadamusu. Akwaima wanda yakecewa
shifa yana wa fuskar Ali kallon sani.
Cikin sati 2 sukayi sabo da Malamin wanda yasaki
jiki da Aliyun amma sai dai Malamin ya fadawa
Aliyu shifa malamine mai yawon yada da'awa
don haka daga nan zai wuce Katsina ne tafi tafi
har Nijar. Aliyu yace in ba damuwa zaibi shi,Aliyu
ya lura da yanda malamin ke daga waya akai-
akai sannan ya lura da irin kudin da malamin ke
rabawa jama'a sadaka. Duk binciken dayayi ya
gano cewa malanin ne wanda yake nema sai dai
dama yana da labarin matsawar malamin yana
cikin daki bazai kamuba. Ana gobe zasu bar garin
kamar yanda suka shirya har da shi Aliyu
shikuma ya daura aniyar kama shine aranar
jajiberen tafiyar. Karfe 2 sun taso daga sallar
Azahar Aliyu hankalinshi tashe burin

Please Login or Register in order to submit comment