Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake kwankwasa kofar awannan karon da karfi. jin
haka shiyasani tunanin komai bugun kofar kafadarsa ya
jingina ajikin kofar yake kokarin balle kofar dakin. Nan da
nan nayi wuf na zare sakatar dakin na janyo kofar da
karfi.
Sai naji sakayau kamar na janyo gadon kara babu abin da
yabiyo baya.
.
Ashe dai ko agaske jarumi ne wata zazzakar murya tace
dani Nayi sororo ina duban abin haushin dake tsaye
akofar dakin cikin mamaki daya sani wangame baki fayau
ina dubanta
Atsaye abakin kofar sanye da bakar riga doguwa da jan
lullubi jikinta na digar ruwan saman daya doke ta, wata
mace ce ajin farko a jerin kyawawa.
Shin ko na iya shigowa, sanyi nakeji gaskiya, gashi kuma
duk kayana sun jike
Na sake kallon katuwar akwatin mai taya dake hannunta
na dama Nace
Malama Lafiya? Daga ina kike Meya kawo ki gidana cikin
wannan daren?
Ta dubeni sannan ta jefeni da wani lallausan murmushin
Allah
kashemu dan dadi, tace Lafiya kalau HILAL ,daga wata
nisan duniya na

tawo domin kawai na ganka, na dade ina ganin
finafinanka ina kaunarka raina na Begen ganinka. Shine
naga bazan iya jurewa ba sai nazo naganka tun daga
maiduguri Nake motar mu ce ta lalace ahanya shine
mukayi dare yanzun ma direban motar ne yaga nayi dare
shine na roke shi yakawoni nan , Tayi shiru tana dubana.
Jarumi Hilal, Ina fatan yanzu dai ka gamsu Shin na iya
shigowa, sanyi nakeji wallahi Hilal. Na matsa gefe guda ta
shigo cikin dakin zuciyata cike da tunane tunane ta ajje
akwatin atsakar
dakin sannan tajuyo ta dubeni.
In bazaka damu ba dan Allah nunamin inda bandaki yake
so nake na shanya kayana duk sun jike jagaf. To ke kuma
ki zauna dame Ina dubanta baki bude Tayi murmushi Sai
na zauna aciki idan sun
sha iska saina mai dasu jikina nafito, Sannan fa takura
min idanu tana dubana ko kiftawa batayi
Oh Hilal yau dai Allah ya nunamin kai wallahi kada kaga
irin son danake ma duk cikin yan wasan hausa babu
wanda nake kauna kamar ka zakayi mamaki idan nacema
acan maiduguri
akwai kawayena da suke kirana da suna HILAL tayi shiru
tana dubana me yuyuwa koh dan ganin duk surutun da
takeyi ban tanka mata ba Hilal yaya kake yimin irin
wannan kallo ne, koh haryanzu baka amince dani ba?
Bahaka bane malama amma abin dake bani mamaki
shine zuwanki cikin wannan tala-tainin daren kuma...... Ta
katseni.
Nace dakai motar muce ta lalace, Haba Hilal nifa bakuwar
kace.
To naji na yarda amma kuma yaya akayi kika san gidana.
Haba hilal Mutane nawane suke ziyartarka arana daga
jihohi daban daban kawayena nawa ne suka zo gurinka ai
kwatancen gidanku ba wuya tunda agidajen gwamnati
kake ga kuma lamba daman kuma ance kai kadaine
abangarenka daban amma kada ka zargeni agurin
maziyartanka naji.
Mukayi shuru muna duban juna sannan sai tasake cewa
Nunamin bandakin Hilal kada mura ta kamani da wannan
jikakken kayan jikin nawa. zo muje nace da ita na shiga
gaba tana bina abaya Bandakin gidan acan baya babban
falon yake saidai kuma zaka iya shiga bandakin tacikin
falon akwai kofar dazata kaika ciki
Ga kofar nan Nace da ita ina duban yala-yalan gashin
kanta Hakika kyakkyawace ajin farko ta dubeni sannan ta
sake jifana da murmushi ta
shige bandakin ta rufo kofar gararamm a daidai lokacin
ne toh aka saki wata aradu Rugugugu..
MASU KARATU KUYI HAKURI DA WASU YAN KURA KURAI
DA ZAKU CI KARO DASU TUN DAGA NA DAYA ZUWA NAN
DAMA GABA KADAN TAYANDA WASU SHAFUKAN ZAKU GA
NA MAIMAITA SU KUMA HAKAN YAFARU NE SABODA

WASU DALILAI NA KUSKUREN RUBUTU DANAYI TUN A
FARKON LABARIN KUMA ZAIYI WAHALAR WARWAREWA
SAI AKASHI NA 5 ZAREN LABARIN ZAI DAWO DAIDAI
NAGODE. AMMA INA NEMAN AFUWAR KU
.
Na sake mikewa tsaye akaro na biyu naci gaba da safa da
marwa cikin dakin. In har ba dauke ruwan akayi na bude
tagar dakin ba zaiyi wuya in zan iya barci.
Banda wannan kuma al'amuran da suka faru ma a
yammacin ranar sun isa su hanani barci na daga kaina na
dubi agogo karfe daya na dare daidai.
.
Sa'ar da muka baro kamfaninsu alhajiji (Sinad
Production) sai Lauriyya tace saita rako ni har gida.
Kiyi hakuri lauriyya kinsan yanzu ba kamar da bane sa'ar
danake agidana yanzu kinga agidan yayana nake kare.
Duk da yake dai bangarena daban ne to amma fa
mutanen unguwa sun gama sa min ido dan sanin kanki
ne duk yan fim yan isa aka daukesu ana son mune ana
kuma kyamar mu. Lauriyya ta fahimci abinda nake nufi.
Toh hilal sai gobe din kenan ma hadu. Kada ka manta fa
da asussuba alhajiji yace zaku fita.... Na dubeta cikin
murmushi ban taba sonta har cikin zuciyata ba kamar
wannan ranar.
Dan haka sa'ar dana fara zirga zirga acikin dakin inata
lissafin dimbin basussukan da suke kaina sainayi
mamakin irin tsabar son da lauriyya takeyimin.
Kafin naci gaba da labarin nan danake baka bari in baka
hoton lauriyya. Dakuma ranar da muka fara haduwa da
ita domin lauriyya tana da matukar muhimmanci acikin
labarin.
.
LAURIYYA doguwa ce launin kofi mararta ashafe siraran
yan yatsun kafarta da na hannu gami da dan madaidaicin
bakinta ma'abocin tattausan murmushi tare da taimakon
dara daran fararen idanunta gamida dogon hancinta mai
kamar kan biro su suka fallasa kyawun da ta gado daga
kakanninta fulani mazauna Gongola.
Haduwar mu da ita tsautsayi ce domin adaren wata
juma'a ne nafito daga ofishina mukayi kicibis da ita
dauke da jaka kallo daya nayi mata ta burgeni.
Sannan naga zatayi daidai da budurwar da muke bukata
acikin fim dina na DAREN MUTUWA.
Kaine Hilal?
Kwarai kuwa nine
Wallahi daga gongola nake masauki nake nema. Hakanan
a saukake don tsabar taren aradu da ka dakuma neman
tsautsayi da rashin tunani sai kyawunta ya rufe min idanu
na samar mata masauki batare da na binciki abinda ya
rabo ta daga gida ba. Yan kwanaki kadan na fahimci ashe
tanada ilmin boko mai dan tsayi domin har diploma ce
da ita abangaren tsimi da tanadi. Haka nan tanada wayo

da hikima hakan ce tasa na maida ita amatsayin
sakatariya lokaci lokaci kuma nakan jefata a fina finai
naso ace duk fim din da zan fito tare zamu fito to amma
saboda acewarta.
Bana son fuskata tayi yawa acikin fina finai sai kawai na
kyaleta ban kuma tambayarta dalili ba.
Har yanzun nan da nake safa da marwa cikin dakin bayan
shekaru biyu cif cif da faruwar al'amarin ina tambayar
kaina shin me ya raba lauriyya daga gaban iyayenta?
Hakika lauriyya ta fara shiga raina sosai.
Adacan sa'ar dana fara ganinta kyawunta ne kawai ke
burgeni babu dadi ba ragi. To amma ayanzu abin ya wuce
haka lauriyya ta zama jinin jikina abin tunaninaba dan
komai ba kuwa sai don na fahimci ita kadai ke damuwa
da fushina ita kadai ke farin ciki da karuwata ita kadaice
komai ke sani dariya ta dauke min kewa aduk lokacin
dana shiga damuwa.
Gobe in Allah yaso saina tambayeta labarinta baki daya.
Nayiwa kaina alkawarin hakan.
.
Haryanzu ruwan saman ake tafkawa kamar da bakin
kwarya na sake nazarin sabon dakin dana dawo cikin
takaici domin baikai ko rabin bandakin da nake wanka ba
atsohon gidana dana sayar na biya bashi.
Dakin danake ciki dan kankani ne kamar dai sauran
dakunan da ake yiwa boyi boyi agidajen gwamnati kujeru
uku ne kacal dakin ya iya dauka. Koda yake dai in ma zaici
fiye da hakan ba samu zaiyi ba domin duk na sayar da
kujeruna sama da talatin na biya bashi ayanzu kam in
kadauke tsohon gadon katakon dake dakin katifar daya
dana tsira da ita gamida talabijin daya mai kala da bidiyo
da rediyon jin labarai mai gidan kaset daya dakin babu
komai sai shegen zafi gamida manya manyan saurayen
dake fizgar rigata ta baya ina kwacewa dakyar.
Dakin danake zaune ayanzu an tanadae shi ne dan yaron
gida dayake kawuna ma'aikacin gwamnati ne ya kuma
san irin yadda mutane ke ta kawo min ziyara sai ya
shawarce ni dana dawo nan na tare tunda da dai karayar
arziki tazo min.
.
Nakoma bakin gadon na zauna sannan na cire rigar dake
jikina na kwanta akan tsohon gadon inajin zazzafar iskar
fankar dake busowa akan fuskata.
Sannan kuma lokaci guda ina mai addu'ar allah sa adauke
ruwan kona sami damar bude kofar nasha tsabtatacciyar
iska.
Ina nan kwance idanuna rufe zuciyata cike da zullumin
basussukan da ake bina gamida tunanin Lauriyya ga
kuma shegen zafi wannan shi ya hana barci ya daukeni.
Nashiga cikin damuwa domin nasan gobe da asusussuba
zan tashi domin tafiya sabon fim din da aka daukeni na
Sinad production. Gashi kuma yanzu ba da ba. Domin

banida ko jaki ballantana mota.
Bansan sa'ar da barci ya daukeni ba adaren.
Acikin barcin ne harna fara mafarki wai anata bubbuga
min kofar dakin danake ciki kuma wai muryar lauriyyace
ke kirana. Nayi firgigit na farka ina mitsitstsika idanuna
sannan ne to ga mamakina sainaji ashe kuwa a gaske
kofar dakin nawa ake ta bugawa.......
ALAKAKAI-05
.
Sannan ne to ga mamakina sainaji ashe kuwa da gaske
kofar dakin nawa ake bubbugawa.
Nayi fakare kamar zakara zuciyata na harbawa cikin
mamakin ganin mafarkin nawa yazama Gaskiya.
To saidai kuma buga kofar yasani cikin damuwa domin
na lura haryanzu sheka uban ruwan ake kamar da bakin
kwarya tabbas nasan ba lauriyya bace.
Toh wanene ? Na tambayi kaina nadubi agogon dake jikin
bangon dakin wanda ke dauke da hoton yan wasan da
mukayi shirin flm din Daren mutuwa dasu.
Karfe biyu da rabi na dare. Domin kuwa banga wanda zai
buga min kofa ba cikin wannan uban daren sai ko
barawo.
Aka sake bugun kofar dakin Das Das Das kamar ana
kugun kwarya da sullen kara. Nayi mamakin jin bugun
kofar dakin babu karfi domin ko wanene ke bugun kofar
to yana tausaya mata.
Aka sake bugawa Raf Raf Raf har sau uku gumi yafara
sartu a goshina hakika amafi yawan fina finan danake
fitowa ni jarumi ne mai zafi marar tsoro to amma azahiri
tsorone dani amar farar kura domin dan karamin yaro
ma na iya tsoratani da bindigar wasan yara saboda
tsorona.
Me yiwuwa lauriyya ce.... Kai ba ita bace babu mamaki
dai kawuna ne nace dakaina. To amma jikina baiyi
amanna da kalaman zuciyata ba domin tun ranar dana
tare agidan kawuna bai taba lekowa bangaren danake ba
in son ganina yake saidai ya turo ayi kirana indai shine to
tabbas ba lafiya ba. Can kuma sai wata zuciyar tace dani
to ai kuwa idan shine kiran sunana zaiyi kai tsaye basai ya
tsaya yanata kwankwashe kwankwashen kofar ba.
Wannan shiyasa cikina ya dada durar ruwa jikina ya
dauki bari nan da nan naji hakorana sun fada haduwa da
juna kaf kaf kaf saboda tsoro.
Najuya ahankali akan tsohon gadon na dubi yan tarkacen
da suke dakin nace da kaina. In dan wannan ne sai na
basu su tafi sun dauka jiya yau ce. Kawai wayannan
barayi da rashin basira suke su basuda labarin na tsiyace
ne ?
Acikin fina finan danayi nasha arangama da barayi da yan
fashi na doddoke su acikin sauki ina hura hanci wasu ma

darakta yasa na kakkama su na daure.
To amma duk wannan daban domin wasa ne yanzu kam
shine azahiri domin gasu akofar dakina.
Na lalubi aljihuna na dauko rubabbiyar naira goman da
mai mashin yabani canji daman naira hamsin ce kadai ta
rage a aljihuna sa'ar da zamu rabu da lauriyya na bata
ashirin ta tafi gida nikuma na hawo acaba naira ashirin
nakaraso gida da goma. Na zargi kaina saboda barin
kofar gidan danayi a bude koda yake kusan ko yaushe ma
ahaka take saboda abokai da maziyartan dake yawan
zuwa gurina cikin dare wasu lokutan ma sai na dawo
daga daukar fim cikin dare zan sami baki suna jirana.
Amman ban taba samun bakin kusan karfe biyu na dare
ba. Raf Raf akaci gaba da buga kofar na yunkura hantar
cikina na rawa na nufi kofar dakin inata salati da
sallallami.
Wai wan....ne ? Nace muryata ashakre ban iya shaida ta
ba amatsayin tawa, maimakon abani amsa sainaji an sake
kwankwasawa.
Wai wanene? Nasake kuga tambayar shiru ba amsa ba.
Haushi yakamani saina tuna da fim din DAREN MUTUWA.
Mun taba yin wani guri mai kamar wannan inda wasu
barayi sukazo suna kokarin balla kofata nikuma nabari
saida suka jingina da kofar suka gama bada karfinsu
akanta sai na bude kofar da karfi suka zubo dakin kamar
an handakosu nikuma na doddoke su. Yau ma zan
maimaita nace cikin zuciyata saidai kuma sabanin
wancan karon yanzu idan Allah yabani sa'a suka fado
cikin dakin tsallake su zanyi na Gudu.
Aka sake kwankwasa kofar awannan karon da karfi jin
hakan shiyasani tunanin me yiwuwa mai bugun kofar
jikinsa ya jingina akofar don haka cikin sauri saina zare
sakata na janyo kofar da karfi sai naji sakayau kamar na
janyo gadon kara babu abinda ya biyo baya.
Ashe dai ko a gaske Jarumi ne. Wata zazzakar murya tace
dani. Nayi sororo ina duban abin haushin dake tsaye
akofar dakin cikin mamaki.
Mace ce tsaye akofar dakin sanye da doguwar riga baka
da jan lullubi akanta jikinta na digar ruwan saman daya
daketa hakika ajin farko ce ajerin kyawawa.
.
******** ********** **********
.
Mun shafe kusan rabin minti muna tsaye muna duban
juna haushi da fargaba da mamaki sun hanani magana.
Shin ko na iya shigowa sanyi nakeji gaskiya kuma duk
kayana ajike suke. Idanuna suka kai ga katuwar akwatin
mai taya dake hannunta sai hakan ya tuno min da farkon
haduwarmu da LAURIYYA.
Malama ina fatan dai lafiya?.... Ma'ana daga ina kike cikin
wannan uban daren? Kuma da wacce kika zo? Yar
budurwar ta dubeni sa'annan t jefeni da lallausan

murmushin Allah kasheni don dadi.
Lafiya kalau Hilal tun daga wata nisan duniya nataho
gareka domin kawai na ganka na dade ina ganin fina
finanka ina kaunar araina da begen ganinka shne naga
bazan iya jurewa ba sainazo na ganka da idanuna. Ta
danyi shiru tana kokarin share ruwan dake sartu daga
cikin gashinta zuwa fuskarta. Gashi dai cikin duhu muke
tsaye dakin babu wuta amma duk dahaka fuskarta har
sheki takeyi idan akayi Walkiya. Ko makaho ya lalubeta
yasan Allah yayi halitta agurin.
Tsarki ya tabbata ga mahaliccin kyawawa.
Haryanzu dai baki gama amsa min tambayata ba nace da
ita ina dubanta. Yar budurwa ta daga girar idanunta sama
cikin rashin fahimta can kuma saita girgiza kai gamida
wani alakaron murmushin.
Oh kana nufin daga inda nake? Daga maiduguri nake
motar mu ce ta baci ahanya shiyasa mukayi dare yanzun
ma direban motar na roka Allah da Annabi shine yakawo
ni har nan tayi shiru tana dubana.
Jarumi Hilal ina fatan dai yanzu ka gamsu.....shin na iya
shigowa?
Sanyi nakeji Wallahi hilal akwai wani abu a tattare da ita
dake damuna fiyeda yawan murmushinta gashi kuma ko
ganina azahiri bata taba yi ba sai yanzu yanzu ma kuma
acikin Duhu.
.
Na matsa gefe guda ta shigo cikin dakin zuciyata cike da
tunane tunane. Ta ajiye akwatin sannan ta juyo ta dubeni.
In baka damu ba don Allah nuna min bandaki yake so
nake na shanya kayana duk sun jike jagaf.
Gabana yafadi ras na bude baki cikin kaduwa nace Ki
shanya kayanki? Na tambayeta adolance. Ta gyada kai. To
ke kuma ki zauna dame? Tayi murmushi lokaci guda tasa
hannu ta yane jikakkken lullubin dake kanta nan da nan
siraran gashin kanta baki sidik suka zubo kan kafadarta
koda walkiya ta hasko cikin dakin sainaji zuciyata na
harbawa da sauri na dade banga gashi da kyawun nata
ba.
Saina zauna aciki idan sun sha iska na maida kayana
nafito. Na sunkuyar dakaina kasa a rude kai yau na gamu
da gamona. Nace cikin zuciyata koda na daga kaina
sainaga ta kura min idanu kamar zata hadiye ni.
Oh hilal yau dai Allah ya nuna min kai. Wallahi kada kaga
irin son danakeyi maka duk cikin yan wasan hausa babu
wanda nake kauna kamar ka zakayi mamaki idan nace
ma acan maiduguri akwai kawayena da yawa da suke
kirana da suna HILAL.
Tayi shiru tana dubana me yiwuwa ko don ganin duk
surutun da takeyi ban tanka mata bane.
Hilal yaya kakeyi min irin wannan kallon ne haryanzu
baka amince dani ba. Akaro na farko sainaga ta dan hade
fuska amma duk da hakan saida idanunta suka nuna

alamun murmushi.
Bahaka bane malama abin da haryanzu ke rudani shine
zuwanki cikin wannan talatainin dare kuma..... Ta katseni.
Nace dakai motar muce ta lalace haba hilal nifa
bakuwarka ce in kuma korata kakeyi shikenan bari natafi
nagode. Ta yi nan tsaye bata dai motsa ba akaro na farko
saina sassauta murya nace da ita a tausashe.
Toh naji na yarda amma kuma yaya akayi kika san
gidana?
Yar budurwar ta dubi akwatin dake kwance atsakar dakin
sannan ta dawo da dara daran idanunta kan fuskata.
Hilal kaga in bakaji dadin zuwana ba simple ce kawai na
fita saina fice ma daga daki ko a tasha na kwana da safe
na koma garinmu yaya zaka sani agaba da irn wadannan
tambayoyi kamar wani tsohon dan sanda. Ta harareni
gamida murguda min baki ta danyi shiru tana maida
numfashi.
In banda abinka hilal mutane nawa ne suke zuwa
ziyartarka arana daga jihohi daban daban ? Kawayena ma
nawa ne suka zo gurin ka? Ai kwatancen gidan fitacce
kamar ka ba wahala bane musamman agidaje irin
wadannan na gwamnati kasan fa kowane gida yanada
lamba...kodayake dai zuwana ne kawai baka so. Ta juya
min baya tana kallon kofar dakin.
Allah baki hakuri nace da ita a tausashe juyo mu fuskanci
juna basai kin juya min baya ba yar budurwar ta juyo da
faffadan murmushi.
Lah hilal menene kuma na bata rai nifa ba fushi nayi ba ai
ko ina fushi da mutane hilal kai ka wuce nayi fushi dakai
idanunta suka kai ga agogon dake makale abangon dakin.
Na dubeta nima karfe biyu da rabi na dare 2:30am
.
Lah wannan ai hotonku ne na fim din Daren Mutuwa.
Budurwar tace cikin karaji sannan cikin hanzari ta matsa
kusa da agogon ta kura masa idanu.
Nikuwa hilal daman inason na tambayeka na dubeta cikin
mamaki.
Me zaki tambayeni? Yar budurwar ta dora dan yatsanta
na hagu akan hoton ta nuna fuskar Lauriyya tace. Amma
wannan yarinyar ko agaske ba'a fim ba budurwar kace
ko? Naji gabana yafadi ras na girgiza kai.
Kokusa kada kiyi tunanin haka fim ne kawai kinsan ku yan
kallo kusan ko yaushe kuna da wannan kuskuren
fahimtar.
Irin kallon datakeyi mane a fim din na lura ya wuce na
wasa..... Na dubeta akaro na farko sainayi mata
murmushin yake..bakya rabuwa da kame kame baiwar
Allah bakisan yan dirama bane yanzun nan sai suyi miki
abu kiga kama da gaske nan kuwa karya suke. Bata juyo
ta kalleni ba haryanzu kallon hoton take amma na lura da
murmushinta ba zato ba tsammani saita juyo ta fuskance
tace.

Ai kuwa kyakkyawa ce. Mukayi shiru na tsahon lokaci
muna duban juna.
.
Nuna min bandaki hilal kada mura ta kamani da wannan
jikakkun kayan dake jikina.
Zo muje nace da ita domin nagaji da jayayya.
Nashiga gaba tana bina abaya kamar bawa da balarabe
bandakin acan bayan falon yake saidai kuma zaka iya
shiga bandakin ta cikin falon batareda k fita waje ba.
Ga kofar nan nace da ita ina duban yala yalan gashin
kanta. Hakika kyakkyawace ajin farko ta dubeni sannan ta
sake jifana da murmushi ta shige bandakin gamida rufo
kofar gararam da karfin gaske karar rufr kofar suka
cakude da rugugin aradun nayi sauri na rufe kunnena.
Akwai lokuta da dama da bana son sautin aradu domin ji
nake kamar ni zata fadowa.........
ALAKAKAI-06
.
Domin ji nake kamar ni zata fadowa..
.
Na juya ahankali na nufi dakin ina shiga saina janyo kofar
dakin amma ban rufe ta gaba daya ba. Na zauna abakin
gado nafara jujjuya batun wannan kyakkyawar budurwa
mai ziyarar tsakar dare cikin zuciyata.
Akwai wani abu atattare da ita dake bani tsoro na lura da
ita ko kusa ko alama batada tsoro haka nan batada kunya
kuma babu alamar bakunta ajikinta bugu da kari kuma
acikin amsoshin tambayoyin danayi mata akwai amsa
daya na tabbata karya takeyi.
.
Shin duka duka wata na nawa da tarewa awannan gidan
da har maziryata na zasu kwatonta mata inda nake? Nidai
a iya tunanina tun dana tare agidan bansamu wani
maziyarci daga bakuwar jiha ba ina nan zaune ina jiran
fitowarta na dubi agogo karfe uku saura kwata 2:45am
nasan ni da sake samun wani isashshen barci kuma sai
abinda hali yayi tunda dai nan sa sa'o'i biyu da motsi
zamu fita sabon fim dinsu Alhajiji. Nayi murmushi sa'ar
dana tuna yaudarar da Lauriyya tayiwa alhajiji kai
wannan al'amari da daure kai yake nace da kaina saikayi
mamakin yadda kudi da mata suke tsananin tasiri
azuciyar Mazaje.
Naji gabana yafadi sa'ar da wani tunani ya fado min nan
da nan naji gumi ya fara sartu agoshina yanzu idan garin
Allah ya waye wani kokuma kawuna yazo ya sameta
adakin nan me zance dashi? Kirjina yafara dakan uku uku
tuni nasan mutanen unguwa sun dade suna zuzzuga
kawuna akan wai dole sai ya hanani harkar wasan
kwaikwayo domin wai duk yan wasan kwaikwayo yan iska
ne marasa mutunci da kyar nasamu na shawo kansa. To

yanzu kuma bayan duk wannan idan yasami mace ta
kwana adakina fa?
Gumi yaci gaba da sartu akan goshina kaga dan samari
wata zuciya tace dani abu mafi sauki shine data fito daga
bandaki katafi da ita gidan kawunka ka kwankwasa masa
kofa nasan in nayi masa dogon bayani yana iya fahimta
sai su kwana tare da matarsa.
Tunanina ya katse adaidai lokacin danaji wani abu kamar
sautin mota wajen gidan na dubi agogo karfe uku harda
kusan rabi 3:30am kai amma dai ta dade cikin bandakin
nan kodana lissafa sainaga kusan sa'arta guda aciki na
mike tsaye cikin sauri na nufi falon ina zuwa saina wuce
kai tsaye zuwa kofar da zata kaini har bandakin ga
mamakina sainaga kofar a bude. Gabana ya ya fadi na
mtsa ahankali na kara kunnena ajikin kofar bandakin ko
zanji motsi shiru sai sautin zubar ruwan sama akan
kwanuka zuciyata na harbawa saina kwankwasa kofar
bandakin. Malama haryanzu kina ciki? Shiru ta gaida
kunnuwana.
Malama ina kike ne? Na sake kiran sunanta to saidai
kuma ni kaina nafara tunanin bazanji amsar komai ba.
Na bude kofar bandakin ahankali sainaga WAYAM. Babu
ita babu alamarta. Nan da nan na ruga aguje zuwa kofar
gidan. Ina kike ne? Adaidai lokacin ne to naji sautin injin
mota an tuka anbar gidan. Nakarasa aguje amma ni kaina
nasan bazan taba samun motar ba na tsaya sororo ruwan
saman na dukana ina hangen danjar motar tana daukar
idona kamar gauta acikin rana.
Sannu ahankali har na daina hangota.
.
BABI NA UKU 3
.
Nadawo cikin dakin jikina na rawa kamar tsohuwar data
sami kwarto karkashin gado. Na zauna jagwaf atsakar
dakin kamar tsohuwar saniya na kurawa akwatin data
bari danu sama da tambayoyi dari suka fara turereniya
cikin zuciyata.
Shin wacece ita? Daga ina take? Menene dalilin zuwanta?
Yanzu kam dana tabbata TA GUDU na tabbata duk abinda
ta fada abaya karya takeyi. Sannan babu zato babu
tsammani saina tuno da akwatin datazo da ita.
Na mike zumbur kamar an sokeni da kibiya na nufi inda
akwatin take jikina na tsuma na daukota na dora akan
gado sannan na fara kokarin budeta. Atunanina acikin
akwatin ina iya samunwata shaida da zata sanar dani ita
wacece. Allah ma ya taimakeni data bar akwatin nace
cikin zuciyata.
Na danna mabudan akwatin ina mai wasi wasin
budurwar ga mamakina sainaga ta bude fayau. Na dubi
cikin akwatin ina mai mamakin ganin babu komai ciki sai
wani dan kyallen yadi fari lullube da wani abu. Jikina ya
dauki rawa kamar mazari. Nasa hannuna kan farin

kyallen sannan na janye farin kyallen.
Numfashina ya kauracewa kirjina yawun bakina ya kafe
kana yar autar cikina ta manne jikin hanjin cikina.
Akwance male male akasan akwatin.
DAN JARIRI NE.
Sabuwar haihuwa kyakkyawa dashi kamar dan larabawa
akusa dashi kuma takarda ce ko liketa ba'ayi ba ajikinta
sakone a rubuce kamar haka........
.
HILAL.
Na dade ina ganin fina finanka kuma kana matukar
burgeni hakan nema yasa begenka yafara mamaye
zuciyata. Hakika tun danake arayuwata ban taba ganin
jarumin danake kauna ba kamar kai ka iya shiri
kwararrene kai mai burge yan kallo to saidai kuma
katsam sai gashi acikin fim dinka na DAREN MUTUWA ka
bani haushi kasa na tsaneka. Lokacin da ka dauki jaririn
nan acikin fim din zaka jefa shi cikin rami sainaji kamar
da gaske zaka jefa ciki.
Baka dade ba da gama fim din sai nima na sami nawa
jaririn abin dai kamar acikin dinka na daren mutuwa
CIKIN SHEGE NE don haka sai naga abinda ya dace shine
na sako shi cikin akwati na kawo maka shi tunda dai ka
saba jefa jarira acikin rami me yiwuwa kana iya rabani da
nawa abin kunyar ka taimaka ka Jefar min da shi. In
kuma kana so to gashi nan nabaka shi kyauta a matsayin
ka na kwararren jarumin fim din
DAREN MUTUWA.
Sai anjima kada ma ka nemeni domin bazaka taba
samuna ba domin GARIN MU DA NISA.....!
.
NA ajiye takardar cikin akwatin jikina na rawa sannan na
dubi jaririn dake kwance cikin akwatin sainaga kamar
yanayi min dariyar kuda. Na dafe kirjinsa da tafin
hannuna na girgiza kai cikin Kaduwa lallai kam kyauta ta
musamman. Hakika kam nayi dace da kyautar
kyakkyawan jariri in da ba don MATACCE BANE.
.
*********** ************ ****************
.
Idanuna suka fara zafi banyi mamaki domin gumin dake
sartu akan fuskata kamar ruwa tuni yafara shigar min
idanu.
Nasake duban kyakkyawan jaririn dake kwance acikin
akwatin na tsahon lokaci sannan sannu ahankali saina
janyo farin kyallen na lullubeshi gami da rufe murfin
akwatin ahankali kaikace tsoro nake kada na tashe shi
daga barcin dayake. To saidaikuma nasan shi da farkawa
sai ranar da aka busa kaho.
Kafin na rufe akwatin saida na dauke wasikar da
budurwar tasa aciki na tura ta cikin aljihuna sannan na
mike tsaye ina muzurai ni kadai kamar tsararraren

kwarto.
Shin wace mata ce wannan? Shin danta ne? In kuma bana
ta bane menene alakata da jaririn menene kuma dalilin
dayasa ta rasa wanda zata kaiwa gawar jaririnin sai Ni?
Kai wannan rashin imani na mutanen duniya da yawa
yake.
Haryanzu ba'adaina tsugu uban ruwan saman ba haka
nan lokaci lokaci saikaji an ruguza aradu kamar ta tsaga
dakin. Ama ni duk wannan ba ita bace agabana babban
abinda yafi tayar min da hankali shine yaya zanyi da
jaririn?
Ka kirawo yan sanda wata zuciya ta shawarce ni. Acan
kuma wani bangaren na zuciyata akace dani.
Kai shashashan banza idan ka sake ka kirawo yan sanda
ka kashe kanka daman tsammani zasuyi sato shi kayi ka
rude shine ka kirasu.
Basai kayi musu bayanin yadda budurwar ta kawo maka
shi ba? Wata zuciyar ta sake kwabata in ka sake ka kira
yan sanda ka karasa rusa kanka a harkar fim domin dole
ne labari ya watsu abokan hamayyarka kuwa sun sami
makamin da zasuyi ta yakarka har sai sun kai ka kasa.
Can kuma sai wata zuciyar tace dani
kai dan samari rufawa kanka asiri tun wuri ka dauki
jaririn

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment