Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ikonsa da kwarjininsa na attajiri sun fara
dawowa gare shi.
Abinda nake nufi shine ina neman kayi min alfarma guda
biyu bawan Allah.
Ni kuwa zan saka ma da abinda baka taba zato ba.
Numfashina ya dauke abinda ban taba zato ba? Indai ba
kuskuren fahimtarsa nayi ba nasan abinda kalmar ke nufi
muddin ta fito daga bakin ATTAJIRI.
Wa.... Wacce alfarma kake so? Ya dubeni na tsawon lokaci
kana yace.
So nake ka rufa min asiri maganar jaririn nan ta zama
daga kai samu don Allah na rokeka ka rufa min asiri
domin idan ta fito fili nagama yawo... Kaga shekara mai
zuwa nake son tsayawa takarar GWAMNA zuciyata ta
harba tsakanin hakarkarina. Bakina na rawa nace dashi.
Indai don wannan ne Alhaji kada ka damu in Allah yaso
babu wanda zai kara jin ta abakina. Nayi tsammanin zai
saki fuska cikin jin dadi amma sainaga haryanzu dai tana
nan yadda take babu yabo babu fallasa.
Sai kuma alfarma ta biyu bawan Allah yace. Lokaci guda
kuma naga akwai alamar razana a fuskarsa.
Fadi muji ranka ya dade. Nace dashi ina dada kwantar da
murya domin kalaman dayayi ne zaiyi min abinda ban
taba tsammani ba yasa zuciyata lissafe-lissafe,,,, na tuna
da dimbin bashin da ake bina.
.
Bawan Allaj me ye sunan?
Sunana Hilal.
Yawwa hilal.
Alfarmar danake nema tanada nauyi amma kamar yanda
nace dakai abaya zan saka ma. Ya danyi shiru sannan
saiyace,
Zaka iya hilal? Na dubeshi cikin mamaki nace to ai bansan
me zanyi ba Alhaji.
Ya dada saurarawa lokaci guda kuma saiya daga kansa ya
dubeni ido da ido yace.
SO NAKE KA AURI 'YA TA FADILA.

.
************ ************** *************
*****
.
Ba karamar girgiza nayi da kalamansa ba. Kaduwar
danayi ita ta sani zaune nayi mutuwar tsohuwa na kasa
cewa dashi komai domin bansan me zance dashi ba. Na
auri fadila? Chab babbar magana.
Yaya kayi shiru Hilal ko baka sonta ne? Na girgiza kaina
cikin kaduwa.
Bahaka bane Alhaji... Kaga dai yan sa'o'in da suka wuce
na santa kuma.... Ya daga min hannu.
Hilal basai ka fada ba nasan abinda kake tunani. Auren
yarinyar banza kamar fadila ko?
Yarinyar data yi cikin shege ko? Ya danyi shiru sannan
yaci gaba.
Abinda yasa na baka duk tarihinta abaya shine so nake ka
aure ta da halinta. Kuma ko da yake baka dade da saninta
ba kai kasan fadila kyakkyawa ce bata da wani aibu in ya
wuce na dabi'unta na banza.
Hilal inason ka sani cewa in dai kana sonta zaka aureta da
halinta to zan saka maka da babban alheri domin tuntuni
na gaji da zamanta agidan nan. Ganin sharrin dataso ta
dora ma shi yasani tunanin babu wanda yadace ya aureta
sai Kai.
Na gama rudewa zuciyata sai dum dum dum takeyi duk
abubuwan dake faruwa ji nake kamar amafarki.
Mecece sana'ar ka hilal? Mutumin ya tambayeni hakan
dayace shi ya sani dada gyara zama.
Harkar shirin fim nakeyi... Nace dashi cikin gaggawa
mutumin ya shafi kansa da tafin hannunsa na dama yace.
Saurareni da kyau hilal zan baka lokaci kayi shawara zan
kuma sami Fadila nayi mata maganar.
Ya danyi shiru sannan yaci gaba. In dai zaka yarda zaka
aureta da halinta nayi maka alkawarin zan sayo maka duk
abubuwan da kake bukata na harkar shirin fim idan
nafita kasashen ketare. Ko gobe ka amince kazo ka
sameni ka fada min zan aika cikin sati guda a sayo maka
duk abinda kake bukata inason kuma ka nemi gida mai
girman gaske a ko ina ne zansa arugujeshi agina maka
kamfanin fina finanka zan kuma zuba maka jarin naira
Milliyan biyar kyauta. Na shiga uku nace cikin zuciyata.
Milliyan biyar?
.
Alhaji zanyi shawara.... Abubuwan sunyi yawa akaro na
farko sai ya saki wata tattausar dariya yace.
Ai kadan ma ka gani ya mike tsaye sosai zo muje in
rakaka. Jikina na rawa na bishi abaya.
Ruwan saman ya tsaya cak. Tuni gari har yafara haske
naji sa'ar da agogo ya buga karfe shida na safe. Muka bi
ta wata yar kofar sai na ga mun bulla a filin ajiye motoci.
Motovi bakwai ne ejere kusan duk sababbi ne akwai jeep

guda biyu Lexux daya marsandi biyu da honda shudiya
da ja. Ga mamakina sai naga ya tsaya ajikin motocin.
Alokacin ne fa nayi masa kyakkyawan kallo dogo ne siriri
fari mai gashi irin na buzaye yalo yako me yiwuwa
bafilatani ne kokuma mutumin Mali. Allah masani. Sa'ar
daya dubeni yayi dariya sainaga hakorinsa na sama guda
daya a bantare.
.
Zan baka sati guda kayi shawara hilal abinda ka yanke
saika zo ka fada min ni da kaina zan sami iyayenka.
A ina kake ne? Ya tambayeni hannunsa na dama akan
rufin motar lexux.
Anan unguwar nake can ciki nake (No 106)
Af ashe ma makwabvina ne. Ya fadada murmushinsa ya
laluba aljihun doguwar jallabiyar shudiya dake jikinsa ya
dauko dan makullin mota sannan ya nufi shudiyar motar
honda.
Alha..... Alhaji bama sai.... Ka bari kawai saina karasa ma
akasa. Murmushinsa ya fadada.
Uhm hilal kenan kaifa nace dakai yanzu ka dan ma ka
gani. Ungo rike wannan. Ya miko min dan makullin mota
ya nuna shudiyar motar da baki yace.
Gata nan nabaka kyauta. Wannan kyautar bata cikin
wancan yarjejeniyar tamu koda baka amince ba wannan
motar dai taka ce... Na bude baki cikin kaduwa da
mamaki chab. Dan saurayi hilal anya kuwa ba mafarki
kake ba?
Bansan irin godiyar da zanyi maka ba alhaji na gode
Allah... Ya katse ni ta hanyar daga min hannunsa a fuska..
Kada ka gode min Domin asirin dakayi alkawarin zaka
rufa min yafi dahaka. Da'ace ciniki zamuyi.
Ya dan saurara yana dan dukan saman motar da yan
yatsunsa.
Shikenan hilal sainaji daga gareka kana iya shiga motarka
Allah yabamu alheri nakuma gode domin nine da godiya.
Yana gama fadi saiya juya yayi ciki da sauri. Yakoma cikin
gidan ta inda muka fito.
.
Na dade anan saroro a rude domin abin kamar a mafarki
awani bangare kuma na zuciyata sai cewa akayi dani
wannan yaudarar ce irin na aljanu.
Amma sa'ar dana bude hondar na lume acikin kujerar
direba sai na gaskata faruwar dukkan al'amarin.
Ada na dauka dana shiga motar zan ga ta bace saina tsinci
kaina kwance akan tsohon gadona. Amma tabbas ko
shakka babu duk abinda nagani tun daga dare har zuwa
wayewar gari gaskiyane babu zancen aikin aljanu KAMAR
A FIM.
.
Nayiwa motar key na tashi sannan na fara tukata ahankali
na nufi kofar gidan azuciyata nace Allah mai yadda yaso
yan sa'o'i kadan nine ke yawo da mataccen jariri ina

neman inda zan jefar dashi sannan lokaci guda kuma na
tsinci kaina amatsayin barawo sai gashi akarshe cikin ikon
Rabbana motovina da bashi ya cinye daya ta dawo daga
cikinsu.
Koda na fara tuka motar sai na juyo da nufin na yiwa
ginin gidan kallon karshe gabana yayi RAS. Sa'ar dana
hangi.....
ALAKAKAI-10
.
Gabana ya fadi ras sa'ar dana hangi FADILA tsaye agindin
taga tana daga min hannu ba ganin nata ne yasa zuciyata
ninkaya ba sai tunanin cewa ayanzu abinda ke tsakanina
da zama miloniya shine kawai na yarda zan aureta.
LAURIYYA ta fado min arai.
Ga koshi ga kwanan yunwa nace araina.
Koda masu gadin suka hangoni tafe sai sukayi sauri suka
bude min kofa atunaninsu ubangidansu ne koda suka
fahimci nine sai suka bi ni da kallo bakunansu a bude
cikin kaduwa. Dankareren katon daya kamoni amatsayin
barawo idanunsa suka firfito cikin kaduwa kamar idanun
kwado. Na daga masa hannu harda murmushi na take
sabuwar motata abina na nufi gida.
.
********** ********* *********
.
Tun daga nesa na hangesu tsaye akofar gidana motoci
biyu da mutane biyar kowannensu nata waige waige suna
ta duban hanya akwai alamar damuwa a fuskokinsu.
Nayi fakin da dalleliyar hondar adaf dasu ina ganin
alhajiji ta cikin gilashin motar yana duban agogo baiko
damu daya kalli motar data tsaya afad dasu ba domin
nasan babu wanda acikinsu yake tsammanin nine na
bude kofar motar ahankali.
Sannunku da zuwa furodusa. Nace dasu da faffadan
murmushi. Duk su biyar din suka juyo acikin mamaki
ganin nine sai fuskokinsu suka washe.
Dan Banza daga ina a ina ka kwana? Tun dazu karfe biyar
da rabi muke nan muna jiranka duk sauran yan wasan
sunyi gaba kai kawai ake jira na dubeshi bayana jingine
da motar ina karkada dan makulli.
Kun aika gidan kawuna ne nemana? Na tambayesu
gabana na faduwa.
A'a bamu aika ba daman USMAN ne ma yace mu aika
nikuwa nasan da wahala in kana ciki. Nayi ajiyar zuciya
da sun aika gidan kawuna nemana da sun janyo min jaf'i.
Bari in shiga gida in dan wasa ruwa sai mu tafi ko? Usman
dake ta kallona tun zuwana yasaka magana saboda
kullewa sai kawai safa da marwa yake.
Kaga malam tun dazu da muke jiranka fa anan sai zamuyi
ta jira har rana tayi mana dubi fa karfe shida da rabi. Na

fashe da dariya.
Dubi rigata fa usman ka gani gaba dayansu suka zubo
min idanu sabodar tsabar kaguwa da sukayi basu ko kula
da yanayin da rigar ruwan dake jikina take ba.
Me ya sami rigarka haka naga duk a yayyage... A'a kaima
ai duk a jike kake da chabi. Duk jikinka tun kafin suyi
tambayar nagama tsara amsar da zan basu cikin zuciyata.
Ai jiya muna rabuwa dakai lokacin daka bar mu da
Lauriyya sai wasu suka daukeni muka tafi daukar wani
fim. Da Allah da Annabi suka janyeni domin wai jarumin
da sukayi niyyar fim din dashi baya gari kuma daukar da
zasuyi suna bukatar ruwan sama. Shiyasa suka takura sai
mun tafi acan na kwana. Kai jiya munyi fim da wuya. Don
nasha dukan ruwa....
To indararo.... Don Allah alhajiji barshi yaje ya shirya
yafito mu tafi inka biye tashi sai yayita zuba kenan daga
nan har azahar. Kasan ba gajiya yake da magana ba....
Usman yace cikin fada. Na dube shi nayi masa gwalo...
Sannan da gudu gudu na shige cikin gidan.
.
Bayan mintuna ashirin nafito nayi wanka na sanya kayana
tsaf dani inka dauke zunzurutun tunanin dake raina. In
banda na amsa musu tun jiya da ba zanje fim din ba
milliyan biyar.
.
Mu tafi nace dashi cikin sauri na nufi sabuwar motata.
Hilal mota ka sake ne? Alhajiji ya tambaya na san gatse
yake son yi min ya dauka arota nayi domin duk fadin
duniyar fim babu inda labari bai watsu ba cewa
taurarona ya daina haske.
Daman ai chanji zanyi shine yasa na saida wadancan nan
da sati guda ma za'a kawo min marsandi daga kwatona.
Alhajiji ya dubeni cikin kaduwa akwai alamun hassada
karara a fuskarsa. Hakanan kuma na lura da cewa kamar
dai na barshi cikin wasi wasin gaskiyar abinda nafada.
Ganin ya kasa magana saina ce dash.
Ina lauriyya? Fuskarsa ta washe nan da nan. Ai ka fini
kusa da ita.
.
BIYAR 5
.
Ina ganinta tsaye sa'ar dana nufo ofishin ta raba
hannuwanta ajikin kofar tana ta hange hange ko shakka
banayi ni lauriyya take hange taga ta inda zan bullo to
amma har sa'ar danayi fakin da sabuwar honda akofar
foshin Allah bai nuna mata ni ba domin atsammaninta
akasa zata ganni na bullo.
Nayiwa kaina murmushi sa'ar dana fara rufe gilashin
tagogin motar duk yadda akayi masu karbar bashine cike
suke jirana. Don na lura da yanayin fuskar lauriyya
hankalinta atashe yake. Babu mamaki ma duk hange
hange da take kokari take taga ta inda zan bullo tayi min

inkiya na gudu batareda masu karbat bashin dake ciki
sun sani ba.
Na dubi bakar jakar dake ajiye akan kujerar motar. Kudin
da kamfanin Sinad produtions ne suka biyani na fim din
danayi musu aranar. Naira dubu talatin da biye ne cif cif.
Fim din da muka dauka aranar ya burge duk ma'aikatan
amfanin musamman ma alhajiji. Domin ya yaba da
kwazona. Da wannan ne ma tasa sa'ar da aka kammala
saiya kirani yace.
Hilal akwai sauran kusan gurare hudu da zakayi mana sati
mai zuwa amma zan biyaka kudinka yanzun nan baki
daya.
Godiya nake furodusa. Nace dashi.
A'a ai ni nake da godiya domin Wallahi Hilal na dauka ka
gama mutuwa domin tuni ake yawo da labarin wai
tauraronka ya daina haske sai yanzu ne na lura da cewa
ashe duk hassada ce. Ya danyi shiru. na yan dakiku
sannan ya ci gaba.
Dubu ashirin da takwas mukayi da kai ko?
Na gyara kai sai yace
Toh ga dubu talatin da biyar nan saura kyauta ce ta
musamman daga kamfanin sinad production domin
baka taba yi mana fim ba sai yau ina kuma dada tabbatar
maka in Allah ya yarda wannan fim din sai ya dada
haskaka ka domin mu muna da labarai masu kyau sauran
kuwa duk shirme ne dahaka ai suke so su kashe ka.
Har na baro gurin alhajiji bai daina Yabona ba da zan
baro gurin ma har kyautar shadda mai tsada yadi goma
yayi min Don haka sa'ar dana gama rufe gilasan motar sai
na dauki kudin da jakar yadin shaddar na nufi kofar
ofishina.
Lauriyya bata tashi ganina ba sai dana zo daf da ita sai
tace cikin rada.
Lahh ta Ina ka biyo? Na kalli motar ina murmushi acikin
wannan motar nazo lauriyya ta waiga bayanta a tsorace
bayan ta tabbata babu mai ganina daga cikin ofishin saita
kifta min idanu akan na gudu
Wanene aciki? Na tambaye ta a tausashe.
Emeka ne tun safe yake nan har yafara fada yana cewa
yau ko zai kwana nan sai ya same ka in kuwa bai ganka ba
toh gobe da yan sanda zai zo lauriyya ta dada waigawa
tana dubana.
Mu shiga daga ciki kada ki damu ai yau a shirye nake da
zuwansa hakan dana ce shiyasa lauriyya ta kalli jakar
ledar dake hannuna nan da nan sainaga fuskarta ta washe
cikin mutanen murmushi ta matso inda jakar take ta
karbi jakankunan guda biyu daya ta kudi daya kuma ta
shadda.
Har naji dan dadi Wallahi Hilal.
Tun dazu gabana ke ta faduwa Wallahi bana son naga
kana ta guje guje akan bashi. Allah sarki lauriyya nace
cikin zuciyata irin wannan kulawa tata ita take dada rura

wutar begen ta cikin zuciyata. A da can ban dauketa a
komai ba amma a Yan kwanakin nan dana shiga masifa
lauriyya ba karamin tallafi bace agare ni.
Tana gaba ina binta Abaya har muka shiga cikin ofishin.
Hello Emeka barka da zuwa ya juyo firgigit kamar an
tsikare shi da kibiya.
Kada ka karya min kujera a banza da wacce kazo naji
ance kusan kullum sai kazo nemana ko? Emeka ya
Harareni.
Ai kafi kowa sanin abunda yakawo ni tun yaushe ne
alkawarin cikon kudin kaset din mu ya cika? Kasa sai
kashe kudin mota Nakeyi a banza duk ribar ta tafi ga
masu mashin da mota.
Huta da nunfashin ka kada hauhawar jini ta hau ka a
banza. Nace dashi ina murmushi Lauriyya ta ajiye kullin
jakankunan daga can bayan teburina sannan ta fice cikin
sauri ta koma can dakin karbar baki.
Nawa ne cikon kudin naka? Emeka yabata rai dubu
ashirin da biyar.
Na bude baki cikin mamaki kai kace da man can bansan
yawan kudin ba.
Dubu ashirin da biyar? Ashe dai kudin naka Emeka da
yawa. Ya Harare ni.
Kaga Hilal ni kada ka bata min lokaci in banda lalacewar
ka nawa ne dubu ashirin da biyar agurin ka. Na dube shi
gamida girgiza kai.
Sanin da kayi min yanzu abubuwa ne sai a hankali. Ina
gama fadin haka saina sunkuya kasan teburina na zaro
naira dubu goma sha biyar na Riga nasan teburin yakare
Emeka bazai ga daga inda nake zaro kudin ba
Nawa ne nan? Emeka ya Kalleni fuska a yatsine sa'ar daya
ga kudin basu cika ba.
Nawa ka gani?
Dubu goma sha biyar.
To ka godewa Allah daka sami wannan kayi min hakurin
dubu goma sai bayan sati guda.
Tsawon lokaci Emeka na nan zaune yayi jim kamar ruwa
ya cinye shi can saiya nisa yace ba jiran sati guda ne aiki
ba cika alkawarin ka
Kada ka damu zama sami cikon kudin ka.
A haka na lallaba shi muka rabu a zuciyata nace
shashasha baisan ba a yanzu tsakanina da miloniya kalma
daya ce tak kawai.
.
Bayan na raka Emeka saina dawo kan kujerata na zauna
sannan sannu ahankali kamar a hoton majigi sai
abubuwan da suka faru adaren jiya har zuwa asuba suka
fara dawowa garai garai a faifan zuciyata.
Fadila ta zame min ALAKAKAI.
hakika ga dama ta sameni nace cikin zuciyata na farko dai
idan na amince zan auri Fadila saina rabu da duk bashi da
ake Bina saina zama gagara gasa acikin duk kamfanonin

shirya Fina finan hausa. Na dubi hannun rigata sainaga
har yafara kodewa sainayi tsaki fitaccen jarumi kamata
yana bukatar kayan sawa akalla kala dari biyu a talauce.
.
Zan saya maka duk abin da kake bukata na harkar fim.
Kalamansa suka Fado min a zuciya.
To amma duk wannan da zarar na tuna da halayarta sai
inji duk al'amarin Yafita daga raina hakika ina matukar
son kudi a halin danake ciki a yanzu domin basussukan
da ake Bina sun kusan miliyan guda to amma acan cikin
zuciyata ni nasan auren fadila ba daidai bane na farko dai
ba dole bane tace tana sona in kuma ma ta amince Dani
ba itace irin uwar daya kyautatu na samarwa 'ya' yana ba
domin ayanda ubanta ya bani labarin halin ta ko na aure
ta zaiyi wuya in zata daina bin maza.
A dacan kuma wani bangare na zuciyata nasan duk
kwane kwanen da nake na abu daya ne hakika na kamu
da son lauriyya tabbas in har zan auri wata mace a
duniya toh lauriyya ya kamata na aura nace da kaina.......
ALAKAKAI-11
.
Idan har zan auri mace a duniyar nan toh lauriyya ce
nace da kaina.
.
To sai dai fa ga fadila ga miliyan biyar. Wani zazzafan
gumi yafara sartu akan goshina acan wani bangare na
ofishin agogon bango ya fara buga kararrawa karfe biyar
da rabi na yamma.
Zuciyata tagama shiga rudani abubuwa uku agabana.
Lauriyya
Miliyan biyar da fadila
Biyu nafi son na mallaka daga ciki to Saidai kuma daya
daga cikinsu yashiga tsakanina da guda daya tabbas in
har Inason lauriyya to sai dai in hakura da miliyan biyar.
In kuwa kudin nake so dole ne saina hada da Fadila. Allah
kiyaye nace cikin zuciyata. A can wani bangare kuma
wata zuciya sai cewa takeyi dani kai shashashan banza
saikace ba wayayye ba ka manta kawai da lauriyya ka auri
fadila ko ka rabu da talauci da wulakancin Abokan harkar
ka na shirin fim yanzu in banda shirmen ka har akwai
wani abun kunya da aibu da miliyan biyar bazata iya
lullubewa ba?
Hilal..... Naji muryar lauriyya ta daki dodon kunnena na
dago kaina firgigit ina shafar fuskata da hannu.
Tunanin me kake yi? Ta tambaya lokaci guda kuma ta
matsa kusa dani ta zauna akan teburin dake gaban
kujerar danake zaune kadan ya rage gwiwarta ta gogi
tawa.
Akwai alamun damuwa karara a fuskar ta.
Uhm.. Bawani tunani nake ba gajiya kawai nayi lauriyya ta

zuba min idanu na tsawon lokaci na lura karyar dana
shirya bata samu matsugunni ba.
Mintunan ka ashirin fa kenan kana zaune cikin ofishin
nan kai kadai kuma kace ba tunani kake ba? Sai fa dana
kira sunan ka har sau hudu kafin kaji ni... Ban amsa mata
ba dan banida abin cewa Gaskiyar ta tabbas tunani nake.
Lauriyya ta ci gaba da wasa da Biron dake hannun ta tana
kida dashi a tausashe akan teburin.
Da wata shawara nazo da ita Hilal... Kokuma ince neman
alfarma. Nan da nan na juya na kalle ta cikin mamaki sai
a lokacin ne na lura ashe akwai jaka rataye a kafadarta.
Ina zaki tafi ne naga kin dauko jaka? Lauriyya ta girgiza
kai.
Babu inda zani muka sake yin shiru.
Ni Nafara magana. Wacce shawara ce.... Kokuma ince
wacce alfarma kike nema? Na tambaye ta zuciyata na
harbawa abin na da rudarwa. Yan sa'o'i kadan fa kenan
da attajirin ya nemi alfarmar na Auri 'yarsa to ko itama
alfarmar na aure ta zata nema?
.
Hilal nasan ana binka basusuka dayawa wadanda na
tabbata bazaka iya biya ba a kwana kusa.
Lauriyya ta dago kanta ta dube ni sainaga kwalla ta taru
cikin idanun ta.
SHI Yasa nazo neman alfarma. Alfarmar itace zanyi Maka
kyauta ta musamman da wani abu wanda zai taimaka
maka ka rage mafi yawan bashi da ake binka.
Idan na baka so nake ka karɓa kada ka juya hannun
kyauta baya shine kawai alfarmar..... Wani abu mai kamar
gare gare yafara zaryar cikin kwakwalwata.
Me kike son ki bani? Na tambaye ta a iya tunanina
lauriyya bata da wani abu da zai iya biyan koda rabin
bashin da ake Bina.
Jikinta na rawa ta sauke yar madaidaiciyar jakar dake
makale a kafadarta ta dorata akan bencin dake gabana
sannan saita daga jakar sama ta zazzage abubuwan dake
ciki akan teburin. Alokacin sa al'amarin ke faruwa duhu
ya gauraye dakin domin tuni har an fara kiran Sallar
magariba kuma bamu kunna kwan lantarkin dake cikin
ofishin ba. Amma duk da hakanan sai kyalkyalin
abubuwan ya haskake dakin sarkokine yan kunnaye da
sauran tarkacen kayan karau na kwalliyar mata duk
dayake bansan darajar su ba amma nasan sunada tsadar
gaske bakina na rawa na girgiza kai.
Lauriyya.... Baza ta yiwu ba bazan iya raba ki da kayanki
ba... Kuma ina kika same su ban taba ganinsu ajikin ki ba
dan abin da kike samu kuwa a kamfanin nan bai isa ko iya
tarawa kike balle har ya sayi wannan ba. Lauriyya ta
matso gareni ta dafa kafadata tace.
Kayiwa Allah Hilal kayiwa Annabi ka karɓa tunda nake ban
taba neman alfarma agurinka ba sai wannan idan kaki
karɓa ka gama bata min rai ka konan zuciya.

Toh amma dai lauriyya bai kyautu ba ace in har ni ban yi
miki ba ke ki..... Ta katse ni ta hanyar daga hannayen ta.
Kada ma kafara wannan zancen Hilal tunda nazo garin
nan wake wahala dani in ba kai ba Kaine uwata Kaine
ubana Kaine abin kaunata ka kadai ne ka iya sani dariya
har cikin zuciyata. Ta danyi shiru tana kokarin share
hawaye.
Farin cikin ka shine farin ciki na tunda nazo garin nan
baka taba sanin tarihina ba baka kuma takura min saina
fada maka sirrina ba amma kake taimaka min iya karfin
ka yau juyi nane na taimake ka don Allah kwashe su Hilal
ko a kasuwar barayi ka sayar dasu akalla zasu kai dubu
dari shida. Ta dafa hannuna ta kankame.
Kaji Hilal don Allah kwashe su Narasa abin da zance da
ita. Wata zuciyar nacewa dani kada ka yarda ta rudeka
dubu dari shida basu kai miliyan biyar ba.
Karkari dai su biya ma bashin amma zata kare babu
komai a hannun ka
Nayi fatali da kururuwar zuciyar. Hakika abunda lauriyya
tayi min bazan taba mantawa da ita ba har iya rayuwata
nasan cewa a yadda take da Matsalar ta sa komai tabani
kadarar ta cancak ta makudan kudi zata iya bani naira
miliyan dari inda ita tana da shi.
Hilal... Hilal kayi magana mana ka zura min idanu in kuma
banida matsayin da zan nemi alfarma kayi min saika fada
na kwashe kayana na tafi.
Kada kice haka lauriyya ki kuma daina cewa alfarma kike
nema ai nine kika yiwa alfarmar bakisan wani abu ba
lauriyya nace da ita ina duban ta ido da ido.
DUK duniya a yanzu banida wadda tafiki in babu ke
lauriyya bansan inda zan sa kaina ba kece garkuwa ta mai
tallafa min na yarda zan karɓa amma ki ajiye min su
agurin ki daga nan zuwa sati guda kawai.
Lauriyya ta dada kankame hannuna saita fashe da wani
tattausan KUKA.
Ban taba farin ciki irin na yau ba Hilal kuma.....
Kwankwasa kofar da aka yi shine ya katseta nan da nan ta
Mike tsaye cikin sauri ta share hawayen dake idanun ta
muka dubi kofar lokaci guda aka dada Kwankwasawa.
Bari in je in gano tace dani a tausashe. Na gyada mata kai
sannan nayi sauri na boye sauran kudin dubu ashirin da
suka rage me yiwuwa wani mai karbar bashin ne nace
cikin Raina.
Bata dade da fita ba sai ga lauriyya ta dawo ta tsaya
gabana ta rike tsantsa akwai alamun damuwa a fuskarta.
Wata ce wai take son ganin Ka nayi ajiyar zuciya nasan
aduk masu Bina bashi babu mace ko daya.
Kice da ita ta shigo nace da ita... Ina Nan zaune sai Naji
motsi ina daga kaina sainagan ta tsaye agabana. Nan da
nan dakin ya hade da kamshi doguwa ce sanye da
doguwar riga ruwan Hoda kanta lullube dan kyalle irin
launin rigar. Baba iya ganin fuskar ta Sosai domin

haryanzu ban kunna kwan lantarkin dad ofishin ba.
Sannun ki da zuwa malama ga mamakina sainaga ta
matso ta zauna a bakin teburina daidai da inda Lauriyya
ta zauna.
A'a MALAMA ga kujera nan koma can ki zauna mana ta
fashe da dariya cikin wata zazzakar murya.
Hilal Wallahi kabani mamaki daka kasa gane ni.
Ko na kara kyau ne? Naji gabana ya fadi rasss nan da nan
sai ta girgiza kanta lullubin dake kanta yafado kan
kafadarta siraran gashin ta suka bayyana suna sheki.
Me yiwuwa kafi gane ni ahaka ko haryanzu baka Gane ni
ba JARUMIN JARUMAI.
Ta sake fashewa da dariya.
NICE FA FADILA......
.
SHIDA 6
.
Fadila nakira sunan ta a sanyaye ko shakka babu ta sani
bala'in kaduwa domin ban taba tsammanin zan sake
ganin ta kwana kusa ba Hilal kenan manyan gari ta tashi
daga kan teburin ta nufi kujerar dake fuskantar teburina
ta zauna.
Babu wuta a ofishin ne ko kafi son zama acikin duhu ne?
Na muskuta akan kujerar na fara farfadowa daga cikin
kaduwar danayi.
Akwai..... Wuta ban kunna bane ga makunnar nan a
bayan ki Fadila ta Mike tsaye ta lalubi makunnar lantarkin
ta kunna dakin ya gauraye da haske numfashina ya dauke
yawun bakina ya kafe. Nashiga uku nace cikin Zuciyata
ashe kyakkyawace ta gaske kamar ta karanta abin da ke
zuciyata saita kashe min idanu tace.
BAKA dauka na kai haka ba ko? Kallon tsoro kayi min jiya
ta matso kusa da bakin teburin tana tafiya tana girgiza
jikinta da gangan kusan ko ina a jikinta rawa yake ta dafa
kan teburin da hamnayen ta na dubi yan yatsunta sirara
ne farare sol babu wani alamar tabo ko kwarzane atare
dasu kamar jikin maciji.
Tsawon lokaci tana tsaye akaina ta lullube ni da kamshin
turare da man dake jikinta bansan sa'ar data dauke
hannaye ta daga kan teburin ta Mike tsaye ba.
Hilal yaya naga kayi shiru ko bakaji dadin zuwana bane?
Nayi kokarin na tattare hankalina guri guda nace.
Da wacce yau kika zo kuma? Wata sabuwar kyautar kika
kawo Min?
Fadila ta bata rai
KA cika rikon magana wannan zancen ya fita daga bakin
ka Hilal.
Abinda ya wuce ya riga ya wuce jariri dai tuni an gama
binne shi an riga an binne shi tun da safe. Tayi shiru tana
tsuke baki muka sake yin shiru.
Amma.... Dai kinsan ai abunda kikayi baki kyauta ba ko?
Ko kina ganin daidai ne Abinda kikayi? Fadila ta dauke kai

gefe guda.
Da zamu bar zancen nan dai

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment