Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zaifi.
Don me yasa kika ce haka?
Saboda tone tone bashida dadi. Na Mike tsaye daga kan
kujerar na jingina da bang.
Fadila Gaskiya al'amarin ki sun dame ni kin.... Ta katse ni.
Hilal Inason ka sani cewa duk abin da nayi adaren jiya
nayi ne saboda mahaifina in baka sani ba kasani duk da
cewa kuwa mahaifiyata tafi kaunata da shagwaba ni duk
duniya babu wanda nake kauna kamar sa.
A zuciyata nace duk yadda akayi yarinyar nan tanada
tabin hankali babu mamaki Hakan ne yasa ake kokarin
bani auren ta.
Nasan Abinda kake tunani banida hankali ko? Ta dubeni.
Na girgiza kai.
Kada ka boye min jarumi Hilal naga alamu a idanunka
amma yana da kyau ka yi tambaya kafin ka yanke
hukunci.
Toh..... Amma saiki kashe jariri kice wai saboda kaunar
mahaifin ki kikayi? Ta kada min idanu tace.
....... Nan da wata bakwai mahaifina zai bayyana aniyarsa
ta tsayawa takarar gwamna babu abin da nake buri irin
ace yau mahaifina ne Gwamnan garin nan. Tayi shiru
tana rangaji agabana kamar bishiya.
Ina Fatan yanzu ka fara fahimtar hoton da nake kokarin
zana ma? Kaga Hilal ciki dai nariga nayi Munso mu zubar
da cikin nida mahaifiyata tun yana ƙarami mahaifina ya
hana lokacin Dana haihu sainaga in har na bari dan ya
girma nagama kunyata mahaifina kuma idan zancen
yafito Abokan hamayyar siyasar sa na iya yin amfani da
damar su bata mahaifina.
Amma kuma bakya ganin yanzun ma bata sauya sani ba
tunda dai ai jama'a da dama sun sani kinada cikin shege?
Jama'a kamar su wa? Ta tambaye ni gamida daga girar
idanunta sama.
In banda kai dakuma likitan mu da ya auna ni ya tabbatar
ina da cikin duk duniya babu wanda yasan inada cikin kai
ko wanda yayi min cikin baisan inada shi ba domin tin
yana dan wata daya aka hanani fita ko ina aka sa masu
gadina har sai dana haife dan.
Kawaye na da Abokan Arziki idan sun zo ne mana sai ace
dasu bana Kasar.
.
Nayi shiru ina sauraron shashashan zancen ga mamakina
sianaji duk da kyawunta nafara tsanarta ko kadan bata da
kunya.
Ina ganin idan babu sauran wani abu da zaki fada ni zan
fita nayi sallah kinga har an idar sa sallah a masallaci
nafara yar tafiya a cikin ofishin.
Au harma korata kake yi? Ta bata fuska.
Babu zancen kora kora in kina iyawa jirani nayi sallah sai
muci gaba da hirar daga nan zuwa asuba.

Muga abunda Allah zaiyi nasaki Murmushi nafara Jin
dadin badakalar.
Wai dan Allah da gaske kike yi baki kawo min kyautar
komai ba? Ta kawo min duka cikin wasa na kauce.
Ya ishe ka haka kaga bana so.
Ta juya ta fara tafiya akwai alamun farin ciki a fuskar ta.
Muje to ka rakani.
Muka ratsa ta cikin dakin karbar baki.
Ban iya yarda na kalli inda lauriyya ke zaune ba.
Toh amma na lura zaune take ta kifa kanta akan teburin
dake gabanta.
Nayi tsammanin zata biyo bayan mu da man Ga al'ada
duk bakon da ya zo tare da ita muke raka shi amma Sam
Sam bata biyo mu ba tun kafin mu Gama fita na hangi
katuwar marsandin tana kyalkyali acikin hasken farin
kwan lantarkin daya haskaka kofar ofishin
ALAKAKAI-12
.
Tana kyalkyali acikin hasken farin kwan lantarkin daya
haskake kofar ofishina.
.
Muka karasa gindin motar babu magana muna tafe
kafada da kafada da muka isa gindin motar ta fuskanceni
yaushe zaka zo? Tambayar tayi matukar girgizani.
Ina kike nufi? Fadila ta dafe kirji cikin razana ta harareni a
fusace.
Au baka san zancen ba?
Wane zance? Fadila ta girgiza kai tace shikenan tunda
baka sani ba daman babane yace nazo na sameka amma
tunda kace baka san komai ba shikenan. Tana gama fadi
saita juya cikin fushi ta shige motar.
Shashashan banza sakarai. Wata zuciya tafara yi min
kururuwa idan ka bari ta tafi baka lallasheta ba kamar
kayi sallama ne da miliyan biyar. Mafarkinka duk ya zama
shirme.
Fadila Fadila na kira sunanta cikin gaggawa ta sauke
gilashin tagar motar na sunkuya nace.
Kiyi hakuri dan Allah Fadila... Idan kin kula duk ba'a
ahankalina nake ba a rude nake... Fadila ta dubeni ta tabe
baki sannan tayi tsaki tace.
Yi sauri ka koma gurinta tana can tana kukan kishi kada ta
mutu... Gabana yayi das das.
Wa kenane kike nufi? Na tambaya baki bude.
Kafini saninta... Wancan baiwar taka dake jiranka a ofis.
Tasawa motarta giya ta firzgeta aguje tabarni anan tsaye
ina hangen kurarta.
SAI WATA RANA MILIYAN BIYAR.
Nace da kaina kamar na fashe da kuka koda na nufi
ofishina sainaji wani zazzafan zazzabi yana neman rufeni.
.

*********** ****** **********
.
Har sa'ar dana dawo dakin karbar bakin lauriyya tana nan
kamar yadda nabarta kanta kife akan teburina na tsaya
akanta.
Lauriyya na kira sunanta akwai alamar rawa a muryata.
Ta dago kai ta kalleni da wani fatalwan murmushi. Ba sai
an fada ba duk wanda ya kalli idanunta yasan taci uban
kuka duk kuwa da matukar kokarin datayi wajen share
hawaye.
Har ta tafi? Ta tambayeni hannunta rungume a kirjinta.
Ta.... Tafi na fadi muryata na sarkewa.
Mukayi shiru babu wanda ya sake cewa kala har aka kira
sallar isha. Sai lauriyya ta mike ta sakala jakarta akafada.
Hilal zan tafi gida... Na danyi shiru na farko saikuma nace
Gida? Haka da wurwuri... Ta danyi tsaki sai gabana yafadi
tunda nake da ita bata tabayin tsaki a gabana ba.
Banajin dadi ne... Shiyasa nake son tafiya yau da wuri
muka dan sake shiru na tsawon lokaci.
Dan dakata to ina da sauran magana dake.. Ta hade fuska.
Maganar me kuma zakayi min na dauka mun gama
komai tun dazu? Ga kayan ai acikin jakata. Ta nuna jakar
da hannunta.
Duk lokacin daka shirya saika karba in kuma kana so ma
yanzu sainaba ajiye ce agurina.
Akwai sauran magana lauriyya... A ina kika samosu? Naji
ta rike numfashi cikin kaduwa.
Hilal me kake nufi da a ina na samo su kana nufin kace ni
barauniya ce?
Dan girman Allah kada ki bata zancen nan lauriyya ni
bahaka nake nufi ba. Ki tuna fa kyauta zakiyimin da
kararki ta makudan kudi a iya sanina kuma ban taba
ganinki dasu ba kinga kuwa ashe banida laifi danna
tambaya.
Ta sunkuyar dakai cikin takaici. Tambayar ta kona mata
rai ta daga kai.
Tunda ka dage saika san inda na samesu bari yo na fada
ma MIJINA NE ya saya min su.
Mijinki? Ta gyada kai.
Kwarai kuwa baka san na taba aure ba kafin nazo nan
garin ba? Nayi ajiyar zuciya.
Ina fatan yanzu ka gamsu. Lauriyya tace sannan ta matso
daf dani kusa dani har takai ina iya jinhucinta akan
fuskata.
ITACE TA BATA MAKA RAI ?
Na kalleta a rude.
Wa..wa kenan kike nufi? Lauriyya ta dafa kafadata tace.
Nasan daman kafi karfina Hilal na dade ina kwana ina
tashi da fargabar cewa watarana sai anzo har ofishin nan
an kwace min kai!
Gabana yafadi nayi sauri na dauke hannunta daga kan
kafadata.

Lauriyya nataba fada miki kuwa wata kalma kwaya daya?
Wacce kalma ce wannan? Ga mamakina sai naji ina mai
kunyar hada idanu da ita.
Adacan Lauriyya ban dauki amatsayin komai ba fiyeda
kawai sakatariya na. Nayi sa'a danaga ta kura min idanu
kamar zata hadiyeni.
Yau lauriyya na wayi gari duk fadin duniya babu wata 'ya
mace datafiki agurina. Lauriyya ta dada matsowa daf
dani.
Na Gode Allah Hilal tun ranar dana dora idanuna akanka
nake kaunarka.
Zan baki wani labari lauriyya ki saurareni da kunnen
basira lauriyya ta dubeni dakyau. Labarin me kuma?
Nakama hannunta muka wuce cikin ofishina. Wannan
shine karo na farko dana taaba yi mata haka. Na zaunar
da lauriyya akusa dani.
Lauriyya jiya da daddare wasu al'amura masu kama da
shirin fim sun faru akaina. Abubuwan na da matukar
rikirtarwa to ahaka dai ni gama yanke shawara azcuiayata
cewa ni dai KE NA ZABA LAURIYYA.
Dan Amina Muhammadu.
Lauriyya tace tana tafa hannu. Ban fahimce ka ba hilal.....
Me kake fadi ne kace ni ka zaba ban gane ba.
Me yiwuwa idan nabaki labarin ki fahimce ni ke dai
saurara da kyau.
.
Nafara zubo mata labarin al'amarun kyautar jaririn da
akayi min tun daga farko har zuwa kan zuwan fadila ofis.
Karfe tara saura kwata nagama bata labarin.
Lauriyya tayi shiru bata ko motsi kamar ruwa ya cinyeta
ga mamakina akaro na farko sainaji da gama fada mata
labarin damuwar zuciyata ta ragu.
.
Lauriyya ta Mike tsaye tabar kusa dani sannan saita fara
safa da marwa acikin ofishin akwai wani yanayi dake
fuskanta daya hanani na katse mata hanzari don haka
sainayi zamana ina jiran naji ta inda zata bullo inada
kwarin gwiwar cewa indai har akwai mafita to lauriyya ce
zata kawota na yarda da kwakwalwarta akan hakan.
.
Hilal! Nayi firgigit sa'ar danaji ta kira sunana.
Mecece shawarar Ki akai. Lauriyya ta dawo kusa dani ta
zauna sannan tace
Zancen gaskiya Hilal indai kabar miliyan biyar ta wuce ka
kayi shashanci. Na zabura cikin kaduwa.
Me kike nufi? Lauriyya tayi dariya miliyan biyar tafi karfin
wasa Hilal Amatsayina na mai kaunarka bazan so ka rasa
naira miliyan biyar saboda ni ba.
Tunanina ya kure na rasa abin da zance da ita.
Ni shawara ta ta Hilal kaje ka aure ta.
Lauriyya meke damunki ne ta girgiza kai.
Lafiya ta Kalau babu abin da ke damuna ni har kullum

babu abin da ke faranta min rai irin cigaban ka
Da miliyan biyar kana iya wa duk Abokan hamayyar nisa.
Lauriyya kibar zancen nan tuni nagama fada miki in har
akwai wacce zan aura yanzu a duniya to kece. Idan kuwa
na Auri fadila bansan da idon zan Kalle ki ba ta daga kai
muka hada idanu tace.
Ko?
Kwarai kuwa na Mike tsaye.
Ko sallah banyi ba yakamata naje nayi sallah lauriyya ta
biyo ni Abaya.
Kayi tunani Hilal tunda dai sati daya suka baka amma ni
ina ganin gara ka aure ta Hilal.
Ban juyo na kalleta ba sa'ar da take maganar domin na
lura ita kanta akwai wani sirri datake kokarin boyewa
daga gareni. Wata zuciyar ta ci gaba da yi min kururuwa.
Duk kabi ka zama wawa Hilal haka kawai kabari matan
zamani suna neman su zauta ka.
Daya kasan yadda take dayar kuwa baka ma san koda
tarihin taba.
Zan tafi gida Hilal sai goben lauriyya tace.
Mamakin abin da yasa ta firgicewa haka take sauri sauri
ta tafi gida.
Toh shikenan sai goben kenan. Ahaka muka rabu da
lauriyya ta tsallake bakin titi tana sauri sauri na bita da
kallo cikin mamaki meke faruwa ne? Yanzun nan fa take
nuna tsananin kishin ta a gareni take nuna cewa duk
duniya ni take kauna lokaci guda kuma tana cewa naje na
Auri fadila... Tabbas akwai wani abu murdadde acikin
al'amarin.. Bi a hankali dan samari kada ka bari matan
zamani su haukata ka a banza nace da kaina....
.
*********** *********** *************
.
Karfe tara da rabi agogon mota ta ya nuna nayi kokari
tun sa'ar dana baro ofis na fitar da komai daga cikin
zuciyata abunda nafi kauna yanzu a duniya shine
isashshen barci domin rabona da barci sa'o'i kusan
ashirin da hudu kenan.
Nayi fakin da motar a kofar gidana na rufe gilasan sannan
na fito zan kulle kofar kenan sai Naji kamar motsi
abayana na juya cikin sauri sainaga wata sura ta fito daga
cikin duhu ta nufo inda nake.
Tun dazun nake jiran zuwan ka JARUMIN JARUMAI.
.
BAKWAI 7
.
Da wacce kuma kika zo? Na tambayi fadila lokaci guda
kuma na jingina ajikin motar barcin dake idanuna ya
zama tarihi a halin yanzu domin tuni nagama fahimtar
fadila ta zama kamar tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba.
Nazo maka ne da wani babban labari domin dazun na
fahimci wani gani gani kake yi min ka daukeni kamar

wata yar iska fadila tace tana tabe baki.
Fadila abin har Yakai da bakaken maganganu.
Yama wuce da haka Hilal duk abin da nake yi ni ba
mahaukaciya bace nasan abunda Nakeyi tayi shiru tana
maida numfashi
Babana yayi min bayanin duk abubuwan da kuka
tattauna dashi jiya banyi mamaki ba sa'ar da nazo ofishin
ka naga kana neman ka wulakanta ni ashe tallata maka ni
akayi.
Cool down fadila nace da ita rabi da turanci rabi hausa.
Anki ayi cool down din da asama nake ta ci gaba da huci
agabana.
Ka dubi da kyau Hilal tun daga sama har kasa kaga
makusa ajikina?
Maganganun ta sun fara bani haushi dan haka sainace.
Azahiri dai kam ko shakka babu baki da makusa amma a
badini kuma fa...
Ta yamutse fuska.
Abar kaza cikin gashinta Hilal a kare wanne ne ba bare ba
ku yanzu yan fim har kuna da bakin da zaku bude kuce
wa wani dan iska? Kai yanzun nan Hilal kana tsammanin
kai waliyi ne? Yan mata nawa kuka bata a harkar shirin
fim
ALAKAKAI-13
.
KARSHE
Yan mata nawa kuka bata a harkar shirin fim?
Kada kice haka fadila ba duka aka taru aka zama daya ba.
Fadila ta zabura cikin fushi kamar zata hau ni da duka
Kasani Hilal na kasance daga cikin dubban yan matan da
Allah ya jaraba da son karance karance da kallon Fina
finan hausa wannan ne ma tasa duk inda akayi wani
gangami na yan shirin fim sainaje gurin ba don komai ba
sai kawai don na ganku Abin da baka sani ba shine ba
dade da sanin ka abin da yasa ban taba tunkarar ka nayi
ma magana ba shine girman kanka musamman ma a
lokacin da kake kan ganiyar tashen ka..... Na katse ta.
Fadila duk naji kiyi hakuri don Allah kibar zancen nan mu
rabu lafiya Wallahi barci ne a idanuna kamar na fadi
nakeji. Tsaho lokaci tana nan tsaye tana ta kokarin
dannan bakar zuciyar ta dake ingizota akan dokan
danasani.
Dole ne na fada maka tarihina Hilal dole ne na fada maka.
Domin ka daukeni wata tambadaddiyar yar iska bayan
kuma dan uwan ku ne dan shirin fim ya batani...... Bazan
taba yafe masa ba har abada tafara kuka.
Aure Kam ko zan rasa miji a duniya bazan aure ka ba
domin nasan har abada bazaka taba yarda dani ba.
Natafi Hilal ka huta lafiya.... Ta juya aguje ta nufi bayan
gidan.
Na bita da gudu gudu adaidai lokacin da take kokarin

shigewa mota.
Fadila..... Dan Allah tsaya ki saurare ni ta tsaya cak kafarta
daya acikin motar daya kuma awaje.
Babu wani abu kuma da zakace dani Hilal.... Me kake son
fada? Zancen naira miliyan biyar?
BAZAKA SAMI KO KWABO BA. tunda ka nuna min cewa
kudin kafi so dani tayi tsaki agabana ta tsartar da yawu.
Dubi idanun ka kiri kiri babu tsoro babu kunya.
Kai yanzu har kana da bakin magana?
Aure ne bazan aure ka ba tuni nafadawa mahaifina dazun
bayan nabaro ofishin ka..... Jeka ka tsira da mota
matsiyaci.
Na yi taku biyu da niyyar kifa mata mari sai wata zuciyar
tace dani..
Uhm. Uhm dan samari yi hankali da tangaran.
Fadila ta lura da niyya ta.
Au dukana zakayi? To Bismillah zo doki nayi tsaye kamar
gunki duk kwakwalwata a yamutse.
.
Fadila ta shige motarta ta rufe kofar gararam sannan ta
fizgi motar ta fice da gudu.
Jikina na rawa na nufi kofar dakina na lalubi dan makullin
dakin dake aljihuna sannan nafara kokarin bude kofar
sannan ne to wata takarda ta Fado daga jikin kwadon.
Na dubi takardar data Fado akan takalmina da farko na
dauka shirme ce amma daga karshe sai zuciyata tace dani
Kai duba dai...
INA shiga dakin saina lalubo makunnar lantarkin na
kunna lokaci guda kuma na bude takardar dan Sako ne
kamar haka.....
.
HILAL.
Me yiwuwa zaka so kasan wanda yayi min ciki zan fada
Ma sunan sa domin abin yazama wa'azi a gareka ka kuma
yi hankali kada abin da ya faru tsakanina dashi ya faru
tsakanin ka da sakatariyar ka na lura ita tafi dacewa ka
aura. Sannan wanda yayi min ciki sunan sa (ALHAJIJI)
FADILA.
.
************ ********** *************
.
Ban isa ofishina ba sai kusan karfe goma sha biyu na rana
wannan ya samo asali ne sakamakon nannuyan barcin
daya daukeni
Ahanya sa'ar dana nufi ofishina zuciyata cike take da
tunane tunanen abubuwan da suke ta faruwa a gareni
tun a daren jiya. Alokacin ne na yanke shawarar zuwa a
ranar nasami mahaifin fadila mu gama kashe magana
yanzu kam nagama saduda dacewa nayi sallama da zama
miloniya tun da dai na tabbata fadila bazata aure ni ba.
Haka ma yafi kwanciyar hankali akalla ka tsira da mota
dan samari.

Toh amma sa'ar da tunanin lauriyya ya Fado min duk sai
Naji hankalina ya tashi bansan inane alkiblata ba. Abu
daya dai dana dada tabbatarwa da zuciyata tun adaren
jiya shine na share su baki daya daga cikin zuciyata
domin ita kanta lauriyya na lura akwai wani abu na rashin
gaskiya dake tattare da ita.
Ina kokarin fahimtar ko wanne abu ne har har na isa
ofishin.
Nayi mamakin da ban ga lauriyya a kofar tana hange
hangen ta inda zan bullo ba.
Nasan ga al'ada ko goma na safe nakai banzo ofis ba zan
Harare ta tana ta leke leke to ballantana kuma karfe goma
sha biyu cikin gaggawa nayi fakin da motar na nufi
ofishin cikin sauri gabana ya fadi sa'ar dana shiga gurin
karbar bakin banga lauriyya ba nayi tsaye cak a tsakiyar
dakin jikina Yabani cewa lallai ba lafiya ba.
LAURIYYA. Nakira sunanta murya a sarkake shiru ta gaida
kunnuwana to amma naji kamar motsin mutane acikin
ofishina. Nayi taku biyu gaba da niyyar nashiga sai Naji
motsin tafiya an nufo dakin saukar bakin.
Sannu ahankali naji takun sawu taf taf taf har ta bayyana
idonta sharkaf da hawaye tana ganina saita taho gareni ta
fashe da kuka.
Dan Allah Hilal ka yafe ni.... Ka yafe ni Hilal.
Ta sake fashewa da kuka.
Yi Shiru lauriyya menene kum? Kuma meke faruwa?
Banyi mamakin jin muryata ko rawa batayi domin
Daman tuni jikina Yabani cewa ba lafiya ba lauriyya taci
gaba da kuka.
KA yafe ni Hilal yau zamu rabu dakai......
Bazan taba mantawa da abun dakayi min.... Ta sake
fashewa da kuka iko sai Allah nace cikin zuciyata.
Wai me ke faruwa ne lauriyya kin ki ki fada min komai
sai........ Maganar ta makale a fatar bakina sakamakon
wani kwakkwauran motsi danaji acan cikin ofishina.
Na juyo na dubi lauriyya nace.
SU wanene aciki? Ta dubeni a tsorace ta kasa cewa komai
adaidai lokacin ne to sauran mutanen dake ofishin suka
fito nayi tsaye ina duban su cikin kaduwa.
Mutanen su biyu ne daya namiji ne Kato mai doguwar
kasumba yana sanye da shakwara da jamfa da wando na
shudiyar shadda kai da ka ganshi kasan akwai kudi zai kai
kimanin shekaru hamsin da biyu a duniya dayar kuma
mace ce dattijuwa zatayi kimanin shekaru kusan hamsin.
Kallo daya nayi nata na gane ta na fahimci ko wacece ita
da lauriyya kamar an tsaga kara.
Sannunka da kokari bawan Allah.
Munji duk taimakon dakayi mata. Nayi saroro ina kallon
su banida bakin magana matar taci gaba da cewa.
Yau shekara uku kenan muna neman yar banzar yarinyar
nan.... Kwana uku ka da daura mata aure ta gudo.
Naji zuciyata ta harba akaro na farko saina kalli lauriyya

nace.... KINA NUFIN KICE KINA DA AURE?
Lauriyya ta fashe da kuka sannan ta nuna katon mutumin
da dan yatsa tace cikin kuka... Ka ga mijina nan....... Wai
wannan katon za'a aura min katon mutumin ya kamo
kafadarta ya hankadata waje tsohuwar da nake tsammani
mahaifiyata ce tabi su Abaya.
.
Jikina na rawa na rufa musu baya tun kafin na karasa
waje na hango wata mota daga can baya Kirar Toyota
Coralla mutumin ya tura lauriyya aciki tana ta kuka tuni
har yara sun fara taruwa suna kallon fim din. Cikin sauri
na karasa gindin motar nace.
Lauriyya..... Allah ya kiyaye kinji Allah taimake ki katon
mutumin ya Harare ni alamun tsana karara suka bayyana
a fuskar sa ban zarge shi ba ban kuma ga laifinsa ba
shekara ta uku tare da matar sa nasan duk duniya babu
wanda ya isa ya fitar dani daga zargin sa.
Kaga malam ya isa Jeka kawai abin da kayi da ma ya isa..
Lauriyya ta yunkura acikin motar ta leko da kanta tace.
Watarana zamu sake haduwa Hilal.... Nayi maka alkawari.
Nagode Allah ya saka maka.
Mutumin ya tashi motar sannan ya dubi Mahaifiyar
lauriyya yace.
GATA DAI YANZU AI MUN GANTA KIN YARDA DAI YANZU
BA SAYAR DA ITA NAYI BA KO?
Yana gama fadin haka sai ya sawa motar giya suka harba
aguje.
Koda suka tafi sai cincirindon yaran dake kallon diramar
suka rufa musu baya aguje suna shewa me yiwuwa da
yake sun saba ganin jaruman shirin fim na taruwa agurin
sun dauko ko wani sabon fim din aka shirya musu.
.
Kusan mintuna biyar ina nan tsaye sannan sai na juya na
nufo cikin ofishina koda na shiga sai Naji shiru kamar
makabarta zuciyata tayi kuna bakin ciki da takaici suka
lullube Ni hakika rashin lauriyya kusa dani ba karamin
rashi bane.
Ba'a dade ba sai Naji kafafuna duk sunyi rauni kamar
bazasu iya daukata ba dan haka sai na nufi kujerar da
lauriyya take zama a tunani wai ko zata dauke min kewa
na zauna a kai ina zama sai Naji duk kasala ta lullube ni
dan haka saina dauki kafafuna na dora su akan teburin
sannan na lumshe idanuna na fara tunanin matsayina a
yanzu.
TA LEKO TA KOMA. Nace da kaina babu Fadila na rasa
lauriyya ga shi kuma nayi sallama da zama Miloniya.
Ina Nan zauna sai nafara kiyashin kudaden da ake Bina
bashi. Cikin zuciyata a iya sanina ana Bina kudi kusan
dubu dari shida da hamsin wani zazzafan gumi yafara
sartu akan goshina.
Dole ne nasan duk yanda zanyi na biya su kudin su tun da
dai wacce ke tarairayata da kwantar min da hankalin ma

an dauke ta.
.
Daga inda nake zaune ina iya hangen sabuwar motar da
mahaifin fadila Yabani tana sheki acikin rana nasan
banida wani zabi daya wuce na sayar da motar na biya
mutane basussukan su zuciyata tayi kuna tuni labari ya ya
fara yada duniyar fim cewa na sake shigowa gari domin
duk cikin JARUMAI maza babu mai shiga motar da takai
tawa a yanzu dan haka sayar da ita ba karamar faduwa
bace.
To amma banida zabi. Na lumshe idanuna sannan nace
da kaina dan samari Hilal sayar da motar ka biya mutane
bashin su ai zama lafiya yafi zama dan sarki ina yanke
shawarar sai Naji nafara samun saukin rayuwa cikin
zuciyata.
Naji wani dadi ya lullube ni sa'ar dana tuna da cewa
motar zatayi tsada idan na sayar da ita dole ne na samu
rarar kudin da zanci gaba da juyawa acikin harkar fim.
.
Can kuma sai wani tunani ya Fado min nan da nan na
zabura ai kuwa da zan maida duk abubuwan da suka faru
akaina tun daga daren shekaran jiya zuwa yau fim. Ba
karamar karbuwa zanyi ba murna ta cika ni sai nafara
tunanin sunan da ya kamata na sa masa. Sai kuma
tunanin wahalar dana sha kafin na jefar da JARIRIN nan
tafado min tabbas ALAKAKAI zan Sawa fim din
.
Kwarai kuwa cikin zumudi saina tuma kafata da karfi
akan teburin sannan ne to naji wani abu ya Fado daga
karkashin teburin. Cikin sauri saina sunkuya na dauka.
JAKA ne ya Fado.
Yawun bakina ya kafe zuciyata tafara harbawa cikin sauri
a kwance a tsakar dakin jakar lauriyya ce data kawo min
adaren jiya dauke da sarkokin nan masu tsada jikina na
rawa na bude jakar.
Suna nan kamar yadda suke suna daukar idanu.
.
Lauriyya!! Nakira sunan ta cikin murna da farin ciki yanzu
kam nasan bana bukatar saina sayar da motata dan biyan
bashi.
.
Jikina na rawa na Mike tsaye ni kadai kamar mahaukaci
nafara juya jakar dake kyalkyali a hannuna kawai sai Naji
na fashe da dariya sannan Nace da kaina...
HILAL DAN DUNIYA ALLAH KE SON KA BA MUTANEN
DUNIYAR FIM BA..
.
KARSHE.....
.
Nazir Adam Salih (NAS)


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment