Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan yadda ta baka shi kaima kaje ka jefar dashi ka
hutawa kanka tonon silili.
Kokuwa na tashi yayana na sanar dashi? To sai dai kuma
haryanzu zuciyat nan nata kururuwa cikin kwakwalwata
kai fa baka rabuwa da sakarci Wallahi mutumin da tuni
mutanen unguwa sun gama zuzzuge kawun naka ana
cewa yan iska ne ku yan shirin fim bakajin cewa idan
yaganka da jariri zai iya tunanin ko naka ne aka kawo
maka shi har gida dan bariki?
Ai kawai ka dauki jaririn nan bakinka alaikum ka jefar
dashi.
Abinda yakama nayi kenan nace da kaina. Nasan dai
yanzu babu jami'an tsaro akan tituna ballantana kuma
mutane na mike tsaye cikin sauri ina mai fargabar kada
gari ya waye min akamani da jariri dumu dumu ahannu.
Wani zazzafan gumi yayi zarya tun daga kan doro wuyana
har zuwa bayana. Kagafa hakane. Nace da kaina. Lallai
kam mafita ta daya ce kawai na hanzarta na dauki jaririn
nan na jefar dashi na huta in yaso daga baya na nemi
uwarsa. Amma tabbas in har maganar ta fito fili to ko
kawuna bai zargeni da komai ba sai mutanen sunyi ta
yawo da zancen me yiwuwa ma wata rana yazama abin
gori ga 'ya'yana.
Akaro na farko tun bayan da akayi min kyautar jaririn sai
naji sanyi sanyi araina. Kwakwalwata kuma tafara tunani
sosai da sosai.
Na nufi kofar dakin ahankali sannan na shiga falon. Na
duba hanyar da zata kaika har bandaki saina girgiza kaina.
Lallai budurwar tayi kyan dan maciji na wuce kai tsaye na

nufi kofar da zata kaini har waje na budeta kadan.
Sassanyar iskar dake ta faman watangarariya da
kwayoyin ruwan dake zubowa adoron kasa daga sararin
Subhanahu Wata'ala ta bugi fuskata yan sa'o'i kadan da
suka wuce bazan iyayin maraba da iskar ba amma ayanzu
saita zame min tamkar na'urar sanyaya daki alokacin zafi.
Na juyo dakin cikin sauri na sunkuya abakin gadon
sannan na tura hannuna na dauko katuwar rigar leda ta
ruwa wacce azamanin danake tashe aharkar fim idan
zamu tafi daukar shirin fim lokacin damina da ita nake
fita.
Koda na dauko rigar na karkadeta saina dorata akan rigar
dake jikina sa'annan na fara balla maballin rigar bugun
zuciyata yafara dawowa daidai ayanzu na sake sunkuya
karkashin gadon akaro na biyu na dauko takalman
ruwana nasa sannan na duba akwatin da mataccen
jaririn ke ciki na tambayi kaina da cewa...
To yanzu kuma ina zaka jefar da akwatin waje na farko
daya fara zuwa zuciyata shine wani katon kango dake
bayan gidan wani attajiri wanda ya saye ginin kwamnatin
gidaje uku ya hadesu ya kera katon gida.
Katon kango ne yadade ahaka an zagaye shi ba'a gina ko
daki daya acikinsu ba. Lokacin damina kamar yanzu
kangon cike yake da dogayen ciyayin tafasa da rai dore
awani lokacin dan daya wuce zamanin muna yara acikin
kangon muke bata lokaci muna wasan boyayyeniya idan
mun taso daga makaranta. Bazan manta ba maciji ya
taba cizon abokina Sani Ayuba acikin kangon. Nayi sauri
na kawar da tunanin hakan daga zuciyata tabbas nan ya
dace nakai akwatin.
Na sunkiya ahankali na dauki akwatin mai tsaya wacce
jaririn ke ciki na nufi kofar dakin cikin sauri.
Koda na bude kofar dakin sainayi murmushin yake cikin
duhun daren kamar awani fim din Daren mutuwa.
Allah sarki jiya ba yau ba nace da kaina.
Na dade akofar tsaye ina duban duhun daren ina
tsammanin ko zanga wani dan motsi. Daga karshe dai
sai......
ALAKAKAI-07
.
Na dade a kofar tsaye ina duban duhun daren ina
tsammanin ko zanga wani dan motsi daga karshe dai sai
na saduda naga tsoro da fargaba basu amfana ta
awannan lokacin sai kawai na jefa kafata waje na shige
cikin ruwan ina mai Addu'ar Allah yasa duk wanda muka
hadu dashi yayi kuskurena a matsayin jami'in tsaro.
Naci gaba da tafiya ruwan saman dake zuba kamar da
bakin indararo sai dukan bayan rigata yake fas fas. Duk
dayake dai nayi sa'a duk kusan bangaren gidajen an
dauke wutar lantarki amma Hakan bai bani kwarin
gwiwar fitowa nayi tafiya kai tsaye cikin takama ba

Ina tafiya ina bin inuwar bango kamar Kadangare wata
sa'ar ko Walkiya akayi sai na rabe kadan kafin naci gaba
da tafiya.
Ina nan tafe lokaci guda kuma duk Addu'ar da Tazo
bakina sai in karanta... Kwatsam sai nafara hango gidan
attijirin tsakanina da gidan akwai yar tazara kafin ka kai
ga kangon dake jikin gidan saikayi tafiya cikin wata yar
farfajiya wacce babu gine gine a cikin ta sai ciyayi haka
nan kuma anan filin wasan kwallon kafa na samarin
Unguwar yake.
Gabana ya fadi sa'ar dana hango fitilun lantarki naci a
kofar gidan dakuma kan katangar reras dasu kamar
taurari tabbas injin wutar lantarki ya kunna.
Ganin hasken ne ya sani sauya shawara na kauce nabi
wata yar siririyar hanya wacce ta ratsa ta cikin filin wasan
kwallon kafar takuma bi ta bayan gidan attijirin zuwa
cikin kangon da nake hari.
A daidai lokacin ne to najiyo sautin abin da ya kusa sa
akwatin dake hannuna ta subuce....
Ko shakka babu mutum ne abayana. Nayi mutuwar
tsohuwa a tsaye tsoro da fargaba suka hanani juyawa.
Wani abu ya dunguri dunduniyar takalmina na dauke
numfashi cak ina kokarin zama gunki har yanzu wanda ke
bayan nawa bai ce Dani uffan ba sannan ne to naji wani
gurnani abayana marar dadin ji
Gashin jikina ya mimmike tsaye kamar gashin bushiya
tuni wani zazzabi zazzabi yafara kokarin rufeni nayi ta yan
maza na juya a hankali na dubi bayana sai mukayi ido
hudu da bawan Allah mai bakaken idanu kamar ifritu
yana gurnani wani dankareren kare ne mai jajayen idanu
da zako zakon hakora kamar tarko babu alamar farin
gashi a jikinsa.
Wani katon kare ne ya kwada min uban haushi WAWWAN Nayi tsallen gefe guda sai yakawo min sura santsi ya
kwashe ni nafada cikin cabin ruwan nagama gigicewa
maimakon na Jefar da jakar saima na sake mikewa tsaye
da ita kankame a kirjina kai kace wasu makudan kudade
ne aciki.
Mukayi tsaye cirko cirko nida karen ya dube ni na dube
shi saina juya da gudu karen kuwa yace da wa Allah ya
hadashi bada ni ba.
Tun kafin tafiya tayi nisa karen ya fara kawowa
dunduniyata sura. Allah ya taimake ni da takalman ruwa
a kafata akaro na biyu ne ya sami Nasarar farka rabin
rigar ruwan dake jikina.
.
Wayyo Allah.
Na kwalla ihu na manta da abun da ke dauke a hannuna
na sake juyowa a firgice na kaiwa karen duka da jakar
dake hannuna Saidai kuma dukan na matsoraci ne domin
bai iya kwantar da ko da yar budurwa ba ballantana
mahaukacin kare alokacin ne to

TAFARU TA KARE. Wani abu mai kamar guduma ya sulalo
ta cikin duhun daren ya daki tsakiyar kaina kafin na gama
warwarewa sai wani abu kuma mai kamar katakon duka
ya daki bayana naji kamar an soke ni da mashi.
Wayyo Allah na kwalla ihu.
Zakayi ihu ma sai agaba shege barawo.
Me ka sato acikin akwatin? Wata kakkausar murya tace
dani daga cikin duhun daren....
.
********* *********** ********
.
Adaidai lokacin dana sulalewa zan fadi acikin cabalin
ruwan ne sai wani busashshen hannu mai kamar iccen
makera ya cafi kwalata ya dagoni sama da karfin tsiya ya
girgizani.
Me ka sato aciki Barawo? Aka sake tambayata akaro na
biyu sannan sai busashshen hannun ya damki
makwogorona.
Idan baka fadi abinda ke cikin akwatin nan ba kasheka
zanyi shege azzalumi kudin wa ka sato?
Wallahi ba kudi bane.. Nace dashi cikin karaji.
Uwarka ce to aciki? Shege Allah ya tona asirinka kananan
barayin unguwa daman jira kakeyi afara ruwa saika biyo
dare ka dauki wannan ka zari wancan kamar mayen karfe
ko?
Haryanzu ba'a daina tsuga uban ruwan saman ba na
hadiye yawu da kyar ba karamin riko yayiwa makoshina
ba dakyar nake numfashi gashi ya daga hancina sama
ruwa sai shiga yakeyi kamar bututu.
Busashshen hannun ya dada girgiza ni zuciyata sai
harbawa takeyi Tam Tam kamar tamaula tsakanin
hakarkarina akwatin kankame akirjina na san idan na
sake ya bude akwatin kashina ya bude.
Daureka zanyi yace dani yau Allah ya toni asirinka bazan
buda akwatin daka sato ba amma da zarar gari ya karasa
wayewa zan mika ka ga hukuma.
Mutumin ya tura ni riki riki da akwatin ahannuna muka
nufi katon gidan attajirin nan mai katanga dauke da
fitilun lantarki burjuk kamar hasken rana.
Mutumin yaci gaba da jana kamar mushe rabi ina tafiya
rabi kuma kafata na jan kasa kamar kafar gawa.
Wani lokacin idan aka kwantsama aradu mai karfin gaske
sai mutumin ya dan dakata da jana yace.
Shege dama ta fado maka azzalumi.
Nayi mamakin ko wanene azzalumin tsakanina dashi.
Bayan wasu yan tsirarrun mintuna muka kawo ga kofar
gidan attajirin nan. Na dubi dankareren gidan kana na
dubi yan mitsi mitsin kwayoyin ruwan dake ta zubowa
bila adadin daga sararin Subhanahu Kamar hazo lokaci
guda kuma na juyo akaro na farko nayiwa mutumin
kyakkyawan kallo.
Banyi kuskuren fasaltashi cikin zuciyata ba.

Domin kamar dai yadda nayi tunaninsa haka nan yake
saima abinda ya dadu kato, baki, jajayen idanu,
fankaceciyar kafada, kamar kofar shagon kasuwa. Abin
dayafi bani mamaki ga halittarsa shine duk da girman
jikin nan nasa kansa dan kankanine haka kuma fuskarsa
tsukakkiya ce fatar bakin siririya kama an tsaga wanda da
tsinin wuka.
Koda ya dada fizgata muka dada matsawa daf da kofar
gidan sai tangamemiyar kofar ta bude wasu dogayen
mutane suka fara fitowa daya bayan daya har suka zama
su uku. Basu damu da ruwan da ake kwararawa ba.
Mutanen uku duk Buzaye ne sirara masu dan rakeken
wuya kamar kasan almakashi ka dauke.
Kowannensu dauke da dakon katon rawani kamar
mushen tunkiya rike da takobi tsirara.
Wa Allah kuma ya hada ka dashi MAMUDA?
Daya daga cikin masu gadin ya tambayi katon mutumin
dake tike da wuyan rigata.
Irin yan kananan barayin unguwannin nan ne dake
damun unguwa da yan sace sace yanzu ma dubunsa ce ta
cika na zagaya cikin ciyayin can sainaji DUNA yana haushi
nakai masa agaji nakamo wannan karamin marar kunyar.
Yana gama fadin haka saiya hankadani gaban buzayen da
karfi na fadi ricaaa agabansu.
.
Wannan akwatin fa dake rungume akirjinsa?
Buzun maigadin ya tambaya
ban budata ba babu ruwana da abinda ya sato ku barshi
kawai idan gari ya waye saimu mika shi ga jami'an tsaro
domin irin kananan barayin nan annoba ce ga al'umma
dan irin su ne idan suka rika sai su zama yan fashi da
makai.
Yasa kafa ya daki Duwawuna da karfin gaske na kwalla
kara.
Au dan dan wannan ma? Ai somin tabi ne kawai na baka
ladan kamu ne saima gobe idan kaje hannun yan sanda
kayi mai dalili Ya fashe da dariyar mugunta.
Ku jefa min shi cikin dakin injin bada wuta yace da
buzayen.
To! Suka amsa baki daya sannan kowa daga cikinsu ya
kama inda yafi rainawa ajikina sukayi sama dani kamar
gadon kara suka nufi cikin gidan dani.
Kada ma ku damu kanku da sai kun daure shi kudai ku
kulle shi kawai aciki karamin barawo ne babu abinda zai
iya yi.
Suka karasa dani kofar wani dan daki dake manne ajikin
bangon gabas na farfajiyar gidan dan dakin kusan duk
akere yake da shuke shuken furannin alfarma haka nan
duk farfajiyar gidan. Nayi bakin ciki domin duk da
mummunan halin danake ciki basu barni na kashe
kwarkwatan idanuna ba.
Muna isa kofar dakin sai suka ajiyeni akasa biyu daga

cikinsu suka rikeni yayinda dayan ya bude dakin
jannaretan nan da nan karar injin dake cikin dakin
gamida hayaki suka gauraye gurin.
Anan zaka kwana in kuma kaso ma to kana iya sace injin
gaba daya duk ribar kafa ce wai giwa ta taka kwado. Suka
jefani cikin dakin kaina ya bugi jikin injin. Sannan na
mirgina gefe guda ina murkususu.
Masu gadin suka mako kofar garam!!! Sannan naji karar
kwadon sun kulle dakin.
.
Na tashi zaune ahankali dodon kunnena kamar zai fice
saboda karajin inji sannan kuma idanuna kamar zasu fito
waje saboda hayakin injin dake shigo min.
To amma fa duk wannan bai sa na jefar da akwatin dake
rungume a kirjina ba
ALAKAKAI-08
.
Na tashi zaune ahankali dodon kunnena kamar zai fice
saboda Karar injin sannan kuma idanuna kamar su fito
waje saboda hayaƙi injin dake shigo min.
Toh amma fa duk da irin wannan wahala baisa na jefar
da akwatin dake rungume a kirjina ba na yunkura Dakyar
sannan na nufi kofar kofar dan karamin dakin injin bada
wutar lantarkin adaf da kofar dakin akwai wasu yan
kananan tagogi ajere reras guda shida don haka ina
Karasawa ga tagogin Saia tura hannuna ta cikin kofar
daya daga cikin yan kananan tagogin hakan danayi shi ya
bani damar shakar tsaftatacciyar iska sannan kuma
sassanyar iskar ruwa ya bugi fuskata nan da nan naji na
dan fara dawowa hayyacina akusa da kofar dakin daga
hannun hagu akwai wai katon duro na mai.
Na matsa kusa da durom din na ajiye akwatin akai na
jingina dashi sannan kuma wani lokaci guda fuskata na
cikin yar Jafar tagar ina shakar iskar tsaftatacciyar iskar
ruwan Saman ahaka ko barcin gajiya ya dauke ni.
Bansan iya sa'o'in dana share ina barci ba Nidai kwatsam
ba zato ba tsammani sai ji na nayi nadaku da kasa.
Sannan naji wani abu ya Fado min awannan sa'ar na tashi
firgigit cikin tsoro sannan ne to na fuskanci ashe barci ne
ya daukeni a tsaye harna ture durom jakar dana ajiye da
kuma akwati.
Na tashi tsaye da kyar jikina na rawa ga mamakina sai
Naji gidan yayi tsit wannan shi ya tabbatar min da cewa
an Dade da dauke ruwan saman acan wani bangare kuma
na Unguwar nasu wani ladan mai zakin muryar gaske
yana kwada kiran sallah asuba tayi nace a zuciyata
kashina kuma ya bushe kenan. Na sake cewa a zuciyata
Daman nasan da gari ya waye marasa imanin masu gadin
nan zasu Mika ni hannun yan sanda shin anya kuwa haka
zata yiwu? Yafa kamata ka motsa ko zaka samu hanyar

tsira wata zuciya tace dani.
Na nufi kofar dakin ahankali kafata kamar zata balle
saboda ciwo nasa hannuna a jikin kofar na dan jijjigata
sannan ne to naga kofar dakin......... Karshen
abubuwan........ Ne.
.
Karfe da gilashi kuma gilashin dake daf da inda nake
masakalin dan makullin yake a daya sakon. Nan da nan
zuciyata tafara harbawa inama ace zan iya murde dan
makullin na ce da kaina. Namika hannu naji hannun ya
taba kwadon dakin kamar wasa sai kawai naji kwadon ga
mamakina ya bude gumi yafara sarara agadon bayana
sannan ne to wata zuciyar tace dani shashasha mai gadin
bai balle kwadon ya shiga daidai ba. Nan da nan na
murde kwadon na tura shi sama sai ya fadi can kasa Tim.
Jikina kamar mazari na rawa na dauki akwatina sannan
na tura kofar ahankali sai ta dan bude nayi shiru ina
saurare ko zanji motsi shiru babu motsin komai sainaga
hanya yakin bishiyoyin gidan da iska ke kadawa banyi
mamakin jin shirun ba domin nasan hankalin masu gadin
a kwance yake tunda dai a tunanin su ina nan a kulle abu
na farko da ya fara zuwa zuciyata shine hanyar da zan bi
na tsere to Saidai kuma tuni na tabbatarwa da kaina cewa
bashi yiwuwa na tsere ta kofar da suka shigo dani idan
nayi gangancin bi ta kofar to kamar na tura kaina ga
halaka ne da gangan.
.
Tsakanina da inda dakin yake dakuma tangamemiyar
kofar gidan yake akwai tazara don haka sai wata zuciya
tace dani tunda dai kofar bata biyuwa me zai hana ka
lallaba ta cikin duhun shuke shuken da suka kare dakin ka
zagaya ta baya? Nan da nan sai na koma ina mai
amincewa da shawarar zuciyata tunanin daya fara zuwa
min shine na zagaya bayan gidan saina haura katangar
indira cikin tsohon kangon dake makwabtaka da gidan
wanda Daman tun farko anan nayi niyyar jefar da
akwatin mai JARIRIN.
Na tura kofar dakin ahankali sannan na fito waje.
Sannan ahankali ina bin lungu lungu sako sako dake cikin
shuke shuken har na kawo ga ginin gidan adaidai lokacin
to naga yar siririyar hanyar data bi ta bayan ginin
dakunan gidan har zuwa katangar arewa wacce itace ke
makwabtaka da gidan.
Fasalin ginin dakunan gidan irin Fasalin nan ne da zaka
iya ginin dakunan su kadai ne a tsakiyar gidan batareda
an jingina koda gini daya da katanga ba wannan shi ya
baiwa rufanin damar yin yado ajikin katangar hakan nan
kuma yan dukur dukur fitilun alfarmar suma suka kai
kusurwar katangar kudu ta gidan abin gwanin ban
sha'awa me yiwuwa hakan ce tasa akayi ginin tsakiyar
gidan batareda an jingina shi da koda katanga daya ba.
.

Na lallaba ahankali kirjina na Dakan shida shida na bi yar
siririyar katangar ta tsakanin shuke shuken na nufi
katangar.
A daidai lokacin ne to sainaga tagar daki ta bude nayi
sauri na sunkuya acikin shuke shuken dake daf da tagar
kadan ya rage tagar dakin ta buge min kai domin jikin
ginin dakin nake bi bantaba zaton za'a bude tagar din ba
haka nan shiyasa ni tunanin ko na koma da baya na sake
hanya domin a baya na akwai jerin wasu tangagogin har
guda biyar kafin nakai ga katangar danake hari. Bangama
shawara ba sai na sake jin abin da yasa zuciyata harbawa
da karfin gaske. Wata shakakkiyar muryar magidancin
mutum tace.....
Ke FADILA tashi munafuka INA KIKA JE DA DADDARE naji
shiru na dan lokaci sai Naji an sake cewa
Ke ba ke Nake yiwa magana ba? Shiru ba'a amsa ba can
sai Naji an amsa
BABA NI WALLAHI BABU INDA NAJE........
Jin muryar shi yasani mikewa zumbur kamar wanda aka
sokawa kibiya na sake saurarawa dakyau
To don iyayen ki ni zakiyiwa karya ina kallon ki fa jiya ana
wannan ruwan kika fice dauke da akwati a hannun ki Ina
Kika kai akwatin ina kuma kika ajiye motar da kika dauka?
Wani abu mai Kamar gizo gizo ya biyo tun daga babban
dan yatsana har zuwa bayana.
Bab...... Don Allah tafara kuka na Mike tsaye ahankali na
leka tagar dakin sannan ne to naji numfashina ya dauke
ko shakka babu yarinyar data bani kyautar JARIRI NE
.
Tana zaune abakin gado ta rufe fuskarta da tafukan
hannayenta gashin kanta awarware wani katon mutum
ne dattijo tsaye akanta sanye da babbar riga bana raba
daya biyu mahifinta ne. Naci gaba da saurarensu jikina
na rawa.
Ina kika kai jaririn munafuka? Mutumin yace sannan ya
matsa kusa da ita ya gaura mata mari tas
ina kuka kai jaririn iye? Wato jefar dashi kukayi ko? To
zakici gidanku.... Yau daga ke har shegiyar uwarki data
bataki sai kun fice min daga gidana ke kuwa ahannun
yanda zan mika ki.
Kai Allah wadaran haihuwar irinku haihuwar bakin ciki.
Adaidai lokacin ne to naji budewar kofar acan cikin
dakin.
Kada ka zageni. Wata sassanyar muryar mace tace duk
abinda yafaru akan FADILA kai ka janyo ai sai da nace
dakai kada ka riga sakarwa fadila kudi tun tana karama
nayi nayi dakai ka ki
kasai mata mota har guda uku don shagwaba har
kasashen turai kake tafiya da ita tokuma shin ayanzu
don.....idonta ya bude da iskanci har ta sami nasarar ba
wa... DAN GWARZO shine kuma zaka zargeni ? Matar tayi
shiru tana maida numfashi ai saida nace dakai a zubar da

cikin ka ki yo kuma yanzu don ta haifi dan ta jefar shine
zaka zo kahauta da duka ka dagata don Allah Alhaji kada
ka kashe min 'ya ba fa taka bace kai kadai.
Mutumin ya dubi matar a fusace yace.
Allah wadaranki Wallahi nima kaddara ce tasa na aure ki
rabon dai in sami wannan tsinanniyar yarinyar da zata
janyo min abin kunya agari kema kafin na aure ki ciki
nawa kikayi aka zubar?
To kace ma fadilar ba 'yar ka bace mana.
Matar tace a fusace nan da nan sai maigidan ya sake
shake yarinyar yahauta da duka.
Wayyo Allah baba na shiga uku fadila ta fada cikin kuka.
Baki shiga uku ba ma tukunna sai ma na dora wuka a
mokogoronki don ubanki. Ina kika jefar da jaririn.
.
Batare da na sake jiran komai ba sai kawai na dauki
akwatin na koma... Da gudu ban damu da ko masu gadin
zasu ganni su sake kamani ba. Ina zuwa saina nemi kofar
shiga babban falon na tura kofa na shiga bayan nayi yan
dube dube saina jiyo hayaniya awani daki. Hakan shi ya
bani damar gane cewa shine dakin da nake nema.
A ina kika jefar da jaririn? Ya sake tambayarta banyi watawata ba saina tura kofar na fada cikin dakin babu
sallama. Gaba daya mutanen uku miji da mata dakuma
'ya suka juyo a firgice suka dubeni kamar wani Aljani.
Kayi hakuri alhaji da shigowata babu sallama.
Nace dashi. Zuwa nayi na ceci ran 'yarka domin ba sai ka
dora wukar a makogoronta ba. Ga Jaririn nan bai yi nisa
ba dazun nan tayi min kyauta dashi amatsayin
kyakkyawan jaruminta na shekara.
Nayi musu murmushin yake su kuma suka dubeni saroro
kamar wadanda suke tunanin na tabu. Na ajiye akwatin
agabansu sannan nace.
Jaririnta yana cikin nan yana barci ni zan koma Alhaji
saidai kuma don Allah kayiwa masu gadin nan magana
domin su Barawo suka kamani jiya da daddare adakin
injin dake baku wuta na kwana. Allah ne ma yasa zan
raba wannan rikici shiyasa na fito.
.
Karya yake Wallahi baba shine ya sace jaririn wallahi shi
ya sace min fadila tace.
Yi min shiru munafuka mutumin ya buga mata tsawa na
dubeta nayi murmushi sannan na lalubi aljihuna na
dauko wasikar datayi min na mikawa mutumin nace.
Duba min nan Alhaji shin wannan rubutuna ne ko nata?
Ni sauri nakeyi domin muna da fim din da zamu fara
idan an jima. Idan kuma kana bukatar karin bayani to
saurareni da kyau.
Mutumin ya amshi wasikar daga hannuna nikuma saina
dubi Fadila itama ta dubeni nayi mata murmushi nace.
Kadan ya rage ki kai labari yan mata to saidai kuma
kyautar da kikayi min tayi girma dayawa. In banda abinci

ina ke ina yi min kyautar Jariri? Ai tayi min yawa ina laifin
ma ki bani Kyautar
KWALBAR TURARE KO FULAWA
Adaidai nan naji sautin sawun masu gadin suna ta guje
guje atsakar gidan.
Lafiya meye haka? Mutumin yace yana dubana nayi masa
murmushi nace dashi
kada ka damu masu gadinka ne suke nemana.
Fadila ta daga kai idanunta cike da kwalla tace.
HILAL nace Na'am FADILA
Tace don Allah ka yafe ni. Na dubeta na tsawon dakiku
sainaji tausayinta ya kamani saina dubeta da tattausan
murmushi nace.
Na yafe miki Fadila saiki nemi kuma gafara agurin
Ubangijinki dakuma mahaifinki.
Fadila ta fashe da kuka.
Adaidai lokacin ne masu gadin suka kwankwasa kofa.
Ku shigo nace dasu.
Waya saka? Mutumin yace dani na dubeshi nayi masa
murmushin ko in kula.
.
BABI NA HUDU 4
.
Kusan minti guda muka share tsaye muna duban kofar
kodayake fadila bata kallon kowa sai ni.
Kofar dakin ta fara budewa ahankali kamar iskace ke
turota sannan sai kakkausar muryar kartin nan tace.
Salamu Alaikum....Alhaji mu shigo ne?
Mahaifiyar fadila wacce ke tsaye rike da tsantsa tana huci
kamar kububuwa.
Mamuda ne? Shigo kai kadai. Maigadin yace bakinsa na
rawa
Garsakeken katon ya shigo dakin cikin sanda yana zuwa
saiya dubeni ya rusuna agaban maigidansa yace.
Kayi hakuri don Allah Alhaji Wallahi adakin injin bada
wuta muka sashi ya gudo.
Bari inyi waje dashi na hada shi da yan sanda. Yana gama
fadi saiya yunkuro ya DAMKE NI............
ALAKAKAI-09
.
Yana gama fada ya yunkro zai Damkeni...
.
Uhm Uhm mamuda kada ka taba shi.
Maigidan yace cikin karaji. Mamuda yayi cak kamar ruwa
ya cinye shi.
Alhaji barawo ne...
Kada ka damu mamuda jeka waje kaci gaba da aikinka
kawai.
Toh yallabai katon yace cikin girmamawa lokaci guda
kuma ya nufi kofa.

Af mamuda... Maigidan ya kira sunansa katon ya juyo
cikin sauri na lura duk a rude yake me yiwuwa tunda
yake gadi agidan bai taba shiga wannan dakin ba.
Wannan maganar daga kai sai mu ka.
Kafadawa abokan aikina ma bana so ta wuce tsakaninku.
Kakuma kawo min akwatin daya bari adakin injin wutar.
Katon ya gyada kai cikin fahimta sannan saiya dubeni.
Kallon dayayi min na iya nufin komai.
Nayi masa murmushi cikin sanda ya juya kamar yadda ya
shigo ya sulale daga dakin.
.
Muka sake yin shiru na tsahon mintuna akaro na biyu
mahaifin fadila na kallon tattausan kilishin dake dakin
yayinda fadila ke kallon. Nikuwa idanuna na kallon
mahaifiyar fadila wacce ta kurawa fadila idanu bata ko
kiftawa. Azuciya na yarda da maganar mahaifin fadila
dayace da mahaifiyarta tun farko itace ta bata fadila
domin na lura da alamun damuwa karara a fuskarta
dakuma kauna ga fadila yarta.
Ku shiga daga ciki RASHIDA. Maigidan ya kira sunan
matarsa akaro na farko. Nayi zaton zata hau masifa
amma maimakon hakan saita dubi Fadila tace. Taho mu
tafi. Fadila tayi min kallon gefe idanu tabi mahaifiyarta
suka bi ta wata yar tsukakkiyar kofa suka shige ciki.
Maigidan ya dubeni gamida sassauta yanayin dake
fuskarsa yace.
Zauna bawan Allah ya nuna min kujera araina sainaji na
kaunace. Hakan shi yasa nayi biyayya na zauna batareda
nayi jayayya ba. Ya danyi shiru gamida sakin wani
tattausan tari kana sai ya dago kansa..
.
Tun tana karama muke fama da ita kadarar yarinya ce ka
ganta nan gashi da babu abinda ta rasa agidan nan na
daga kayan alatu amma bata iya zama sai shegen yawo.
Mahaifiyarta ce ta bata tun tana karama.... Yayi shiru
akwai alamar takaici karara a fuskarsa. Na tausaya masa.
Babu daman nayiwa yar cikina fada sai mahaifiyarta ta
hauni da masifa. Haka kullum nake fama kwatsam ran
nan sai muka fahimci yar banzar yarinyar tayi ciki
mahaifiyarta tayita uzura min sai a zubar da cikin.
Nikuma ina tuna mata yin hakan barna ce domin kisan
kaine saimu bata goma biyar bata gyaru ba. Haka mukayi
ta fama har zuwa ranar data haifu shine yanzu don tsabar
rashin imani suka hada baki ita da mahaifiyarta suka
kashe dan jaririn wata daya kawai da haihuwa....hawaye
ya fara kwarara akan fuskarsa.
Na yunkura akan kujerar cikin damuwa ni duk
maganganun sun fara gundurata duk da dai basu shafeni
ba ni abinda kawai nake so shine yabar ni na tafi dan na
lura tuni har gari yafara haske. Duk da yake banga agogo
ba ina kyautata tsammanin biyar na safe ta wuce. Fita fim
dinsu Alhajiji ne araina.

Alhaji.... Allah ya sawwake.. Nace dashi ina ganin in babu
wani sauran abu to ni zan tafi alhaji domin kaga duk
wannan abubuwan da kake fada bai kamata na sani ba
domin sirrinku ne ku kadai bai shafe ni ba. Mutumin ya
dago kai yana girgiza shi.
Ya shafe ka bawan Allah. Awannan karon ni na dube shi
cikin mamaki.
Tayaya ya shafeni? Mutumin ya sunkuyar da kai na
tsawon lokaci yana girgiza kai. Can saiya dago alamar
damuwa a fuskarsa a fili. Ga mamakina sainaga ya mike
tsaye ya nufo inda nake ya sunkuya akaina ya dafa
kafadata yace.
Bantaba neman alfarma agurin kowa ba tun da nake....
Amma yau zan fara. Abinda yace sai ya daga rudani.
Ban fahimce ka ba. Ya daga girarsa sama kamar biri na
lura karfin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment