Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ayi hakan...
  Tafi wurin ya kaure da ana ta tafawa haɗe da yin dariya cikin annashuwa da jin daɗi..
  Saukowa tayi daga filin rawar tana mai amsar rigar ta da aka miƙo mata kasancewar ba da wasu suturar arziƙi tayi rawar ba sai aka bata wanda zai rufe mata jikin ta gabaɗaya..
  Tana gama saka rigar ts juya ta kalli masu tsaron ta ta ce da su
  "Ina mama na"?ɗaya daga cikin su tayi gaba ita kuma ta bi ta a baya tana mai gaisawa da mutani tana murmushi..
  Har wurin hutun da mahaifiyar ta ke yawaita tafiya aka kai ta haɗe da nemar mata izinin shigowa kafin a bar su su biyu. 
  Zama tayi a kujerar dake kallon na mahaifiyar nata tana mai aika mata da kallon dake ƙunshe da tambauoyi kala kala wanda ya saka mahaifiyar ajiye abin dake hannun ta ta maido hankalin ta kacokan zuwa ga ɗiyar nata tana faɗin
  "Me kuma aka maki"?cigaba tayi da kallon ta sannan ta amsa mata bayan ɗaukar dogon lokaci da tayi tana nazarin ta
  "Kin fi kowa sanin abin dake dami na dan haka ki amsa min tambaya ta"numfashi ta fitar mai ɗumi sannan ta ce
  "Gimbiya,,in zan fahimce ki da kyau,kamar so kike ki saka min magana a baki alhalin kin san babu wanda ya isa ya fallasa wannan ajiyayyen sirtin sai mahaifin ki da shi ya san aihinin al'amarin"..ɓata fuska tayi ta tashi rai a ɓace tana faɗin
  "Daga rana mai kamar ta yau na daina yi maki tambayar abin nan amma ki sani,zan zare jiki na daga duk wasu harkokin gidan nan a matsayi na na gimbiya dan haka ni na bar ki lafiya sarauniya".kaiwa nan tayi wucewar ta ta koma inda ta fito ta shiga gaisawa da mutani ana raha,...  
  Daga dukkan alamu ma dai kamar wani gagarumin sha'ani ake yi dan taron na manya ne saboda gasu nan ta ko ina sai haye masu jiki mata ke yi suna wani ƙwarƙwasa kamar akan su aka fara halitto rangwaɗar da iyayi sai juye juye suke ta yi ƙarshe ma ɗaga mazajen suka yi suka nufi hanyar da zai fiye masu sirri..
  Dariya ce ta kaure a wurin ganin yadda aka ja wani cikin manyan mazan dake zaune a wurin kamar raƙumi da akala..

  Ɗaya daga cikin waɗanda ke kishingiɗen ne yayi magana wanda ya kasance mai ji da ƙarfi ne haɗe da isa da izza wanda da ganin sa ba sai an yi sharhi ba za'a gane sa da matsayin sa duba da yanayin shigar sa da ƙasaitar sa..
  "Ina Dacey ta shiga tun ɗazu"?wanda yayi tambayar yana kallon sa ne yayi gyaran murya yana faɗin
  "Ran sarki sultan ya daɗe ai Dacey tun rana ta kange kan ta a cewar ta,yau ba zata karɓi gayyatar ka ba,a cewar ta,kai take jira kuma zata yi maraba da ganin ka".murmushin ƙasaita da jin daɗi wanda aka kira da sarki Sultan yayi sannan ya kaɗa kan sa irin na ƴan duniya wayayyyu sai ya gyara kishingiɗar sa yana karkaɗa ƙafa yana zance cikin nuna gadara
  "Dacey sahiba ta,,Dacey abin hutu na,,Dacey mai nishaɗantar da ni..hmm babu damuwa in yau mulki da sarautar ta sun motsa,zan kai mata ziyara in hakan zai faranta mata"da murmushin manya ya ida maganar tasa ta mulki kafin ya gatsa tufa dake hannun sa yana karkaɗa kai..

  A ƙalla sai da suka raba daren suna shagulgulan su da ya zame masu al'ada  sannan kowa ya nemi makwancin sa ya kwanta dan huce gajiya yayin da wannan sarki Sultan kuwa,wani sashe ya nufa inda ya ɗan yi tafiya mai taƙaitaccen zango kafin ya kai inda yake da niyar zuwa..
  Sashe ne mai kyau da faɗi dan tsarin sa ya haɗu iya haɗuwa ko ina haske ne da ƙamshi mai daɗi san shiga rai..
  Cikin ƙasaita ya rinƙa takawa yana shiga gidan har ya kawo sashen da yake son dakatawa sai ya dakata haɗe da tura ƙofar ya buɗe ya ƙarewa wurin kallo yana jinjina kan sa yana murmushi,da gadara ya ƙarasa har turakar da ya san a nan zai same ta..
  Zuwan sa kenan yayi gamdakatar da ita tsaye babu komai a jikin ta tana kallon gefe..
  Ƙarasa shiga ɗakin yayi yana ƙarewa halittar ta kallo yana munafukin murmushi..
  Yana matso ta ya juyo mata da fuskar ta suka fuskanci juna sannan ya ce
"Kika ce yau ba zaki karɓi gayyata ta ba Dacey"?yayi tambayar yana saka idanun sa cikin nata sai ta ƙure sa da idanun ta itama sannan ta gyaɗa mai kai tana faɗin
  "Ka ji saƙon daidai"?dariyar manya yayi daga haka yayi sama da ita kuma daga nan mai wakana ya wakanu...

★★★★★★
Tagumi ta zabga tana tunani kamar dai hankalin ta baya tare da ita dan waɗanda ke tsaye akan ta sun daɗe suna tsaye suna kallon ta amma bata ma san suna nan ba har sai da ɗaya daga cikin su ta ce
  "Hadara"!!sai a sannan tayi firgigit ta dawo duniyar mutani sai ta ɗan lumshe idanun ta tana mai faɗin
  "Ya aka yi,yaushe kuka zo"!?ɗaya ce daga cikin su ta girgiza kai dan in da sabo toh sun saba da halayyar Hadara na zama a duniyar mutani amma tunani da hankalin ta duk yana duniyar tunani ba ma a duniyar bil adama ba..
  "Hadara so kike ki kashewa ƴaƴan ki kan ki?baki tausayawa wannan marainiyar yarinya Juda da ta zaɓi tauye jin daɗin ta ta tafi uwa duniya dan nemo ƙanwar ta kuma abin farincikin ki duk sai a ce a kawai take wannan wahalar da salwantar da rayuwar da tayi?baki fatar wataran ta dawo maki da ƴar ki ku kafa rayuwa mai daɗi sai dai kullum ki zauna kina tunani wanda ke kan ki kin san tunanin nan bai dace ba bai kamata kina yin sa ba amma kika zaɓe sa..yanzu yaushe rabon ki da zuwa wurin bauta?tun shafewar kwanaki goma kika yanke ƙafar ki da zuwa wurin bauta hala kin gaji da yi ma ƴaƴan ki addu'a ne"?da sauri ta ɗago kan ta tana faɗin
  "Ya zaki ce haka Yura,kema kin san ƴaƴa na su ne abin alfahari na su kaɗai gare ni toh akan me zan daina zuwa yi masu addu'a"!!tarar numfashin ta wacce ta kira da Yura tayi tana faɗin
  "Toh in ba dan haka ba menene dalilin ki na ɗauke ƙafa da zuwa wurin bauta"?da saurin ta ta ce
"Abubuwa ne suka kacame min Yuri,na kasa ganewa kai na sam bana cikin hayyaci na,tunani na Juda,,ina take yanzu ya take rayuwar ta a inda ta tsinci kan ta tana lafiya ko a'a,na rasa ina zan kama in ji daɗi da sanyi Yura ki taimake ni"!!da hawaye ta ida maganar yayon da Yura da sauran mata biyun suka rungume ta suna rarrashin ta..

  _YURA aminiya ce kuma kamar ƴar uwa ga Hadara dan tun da ta ganewa gidan bautar da take zuwa ta ƙulla alaƙa da Yura ganin ita ɗin mai tsananin juriya ne in ta fannin bauta ne sai halayyar su ta zo ɗaya suka rinƙa amintaka har dai Yura ta nuna wa Hadara aminan ta da suke bautan tare da haka suka saba har takai ta kawo in aka kwan biyu ba'a ga ɗaya ba sai an biyo an bincika dan sanin abin da ya hana ta zuw,duk zaman nan nasu da suke yi basu taɓa sanin ainihin tarihin Hadara ba saboda ba a cikin garin suke ba kamar dai yadda ita ke tafiya yankin su dan gudanar da bautar ta sai dai wasu lokutan suka biyo ta gida dan sanin matsugunin ta saboda zumunci amma ko da wasa basu san ainihin tarihin ta da ya shafi gidan mahaifin ta ba,iya abin da suka sani shine tana da ƴaƴa biyu mata kuma ɗayar ta ɓace haka kuma ita wacce ke nan ta fita nemo ɗayar sanadin ɓacewar ta kuwa,bata sanar da su ba ta barwa kan ta dan sirri,shine ya BAMBANTA ta da su kamar dai yadda ya kasance a dalilin BAMBANCIN ƘASA take haɗiyar baƙin ciki da ɓacin rai tun tana tare da iyalin ta har kawo yau_..

  Kusan yamma sannan suka tafi suna mai ƙara jaddada mata akan zasu tsumaye ta nan da kwanaki kaɗan,cikin farinciki suka rabu da juna yayin da ta koma cikin gidan ta na ainihi wanda shima bata taɓa bari sun san da shi ba saboda sirri..

★★★★★★
  Kusan ya zame mata al'ada tun bayan rabuwar ta da su bata sake samin kwanciyar hankali ba,ga takurawa daga ko wani ɓangare duk ta kasa natsuwa ta maida hankalin ta ga abin da take burin yi,sannan komai ya tsaya mata cak kamar an yi ruwa ya ɗauke sai dai abu ɗaya ne ta sani ko a jima ko a daɗe sai ta cafko waɗannan ƙananan mutanin da suka yi mata wasa da hankali wai a ce kamar ita har wasu ƙananan mutani sun yi nasarar juya mata tunani ba tare da ta sani ba wai ma ya aka yi bata gane su ba sannan me ya sa hankalin ta bai kai ga cewa ba daga gidan sarauta suka fito ba ya aka yi hakan ma..
  Wannan tunani ya daɗe yana yawo a kan ta sai dai ta ƙarfafa tsaro ta ko ina kuma duk ranar da aka kawo mata waɗannan ƙananan ƙwarin toh fah ba zasu sha ba sai ta hukunta su wannan alƙawari ne..
  Cigaba da sarrafa ta ya rinƙa yi amma madaɗin ta ji daɗi sai ta ji ran ta ya ɓaci dan haka bai yi aune ba ta yaƙice sa daga jikin ta tana mai sauke mai mari a kumatun sa..
  Shi ɗin da bai ji ba bai gani ba sai ya dafe kumatun sa yana kallon ta sai ta nuna mai hanyar waje,second ɗaya bai ƙara ba yayi fitar sa yana waiwayen ta haka yana mamakin ne ke damin Sarauniya Zinaida a kwanakin nan sam duk ƙoƙarin da yake yi bata gani wanda a da da kanta take roƙon sa ya jajirce ya mata yadda take so amma yanzu kafin mai a kai ga yin komai sai ta rinƙa hankaɗa sa sannan zuwa dare zata sake nemar sa shi dai bai san me ke damin ta ba....

★★★★★★

  Yana kwance tana kwance saman ƙirjin sa suna kallon sama daga ƙofar gidan da suke kwancen magana ta mai dan kar ya riga ta kamar yadda ya saba.
  "Masoyi na saura kwana nawa a mana auren ka san na ce da kai bayan auren mu ina son komawa gida dan mahaifiya ta ta san cewa ina da aure dan in ta san hakan toh ba zata tursasa ni in dawo gare ta dole ba dan ba a ƙarƙashin ta nake ba"..rungume ta yayi yana faɗin
  "Gimbiya ta kin san in ta ni ne da tuntuni an yi auren nan amma ke kika hana komai kika ce sai an bi ƙa'idodin mace mai martaba(Virgin)kuma da gaskiyar ki dan ke ɗin mai muhimmanci ce kuma da tsada kike hakan ma ya sa na jajirce ina aiki safe zuwa dare dan in yi mana bikin da ba za'a manta da shi ba a a tarihi ko da kuwa ba a masarautar Mughal aka yi sa ba"daɗa rungume sa tayi tana faɗin
  "Masoyi na ka min alƙawari duk wuya zamu cigaba da zama tare ko da mahaifiya ta ta nemi raba mu"gyaɗa mata kai yayi yana shafa gadon bayan ta..

  Tun rabuwar su da Juda suka kamo hanyar wannan daji da suke ciki presently,tun da suka tsinci kan su a wannan daji Cahal ya nemo kara da ƙirare ya haɗa masu inda zasu na kwana dan yawanci a jeji suke kwana in dare ya masu toh sai yayi fasahar yi masu matsuguni inda suke kwana a haka dai har suka saba da wurin sai ya zamana Cahal na fita nemo masu abinci kamar kayan itatuwa in kuma ya fitan toh ita a nan bukkar zata zauna in ta gaji ta fito waje har sai ya dawo sannan su koma ciki,mutum zai yi mamaki in aka ce duk zaman nan da Cahal da gimbiya Ondrea ke yi babu alaƙar da ya shafi alfasha da suke yi duk iya zaman su baya wuce su yi a zahiri amma kam abin da ya shafi haɗa shimfiɗa basu taɓa yin sa ba dan ta saka a ran ta duk runtse sai an ɗaura auren su sannan zata bar shi ya haɗa shimfiɗa da ita saboda al'adar su ce ta masarautar su akan sai an ɗaura auren gimbiya sannan zata san namiji amma in har ba'a ɗaura ba ta haɗa shimfiɗa da shi toh babbar masifa zata tunkaro ta dan kuwa zata janyo rugujewar mulkin masarautar su, sai dai un ta taɓa aure mijin ya mutu ko ta rabu da shi toh babu laifi ko ƙaddarar da zai same ta,wannan dalili ya sa gimbiya Ondrea bata yarda sun haɗa shimfiɗa ba kuma wannan dalilin ne ya sa sarauniya Zinaida bata wani ɗaga hankalin ta ba ko da aka sanar da ita cewa ba'a samo gimbiya Ondrea da Cahal ba dan ta san duk rashin ta idon su zasu dawo gida dan zasu ce zaau yi aure kuma dole sai da iyaye da ƴanuwa haɗe da shaidu ake aure..
Toh a nata in suka dawo sai ta sa a tsare gimbiya Ondrea sannan shi kuma Cahal a hukunta sa daidai laifin da yayi dan ba zata yarda ta kashe sa ba ta rantse ko zata rasa mulkin ta kamar yadda dodon ta ya sanar da ita toh fah sai ta haɗa shimfiɗa da Cahal dan kwaɗayin sa take ji gani take ba zata iya yafewa ɗiyar ta Cahal ba sai dai duk abin da zai faru ya faru..
Su kuma already sun gama tsarin su dan da daɗewa Cahal yana tattalin sa na auren su yakan fita yin ƙwadago a cikin gari duk abin da zai kawo masu kuɗi yana yin sa da haka ya saba da wasu dattijai har ya bayyana masu matsalar sa da abin da yake da niyar yi suka mara mai baya har da alƙawarin maye masu gurbin iyaye da shaidu a ranar da zasu yi auren toh su suka saka bikin suka cigaba da tsare tsaren su har dai wasu lokutan yake kai ta wun dattijan nan dan su saba kuma ba laifi sun saba sosai suna ɗaukar su a matsayin nasu sun zame masu kamar iyaye dan shima Cahal akwai ƙwazon nema da adalci akan ayyukan sa hakan ya janyo mai martaba a idanun mutani..

Suna kwance a wurin har dare yayi suka koma bukkar su inda nan ne makwancin su,kwanciya suka yi,tun yana mata hira tana amsa mai har ya fara jin shiru alamun bacci tayi dan haka ya daɗa ƙanƙame ta shima baccin ya ɗauke sa...

★★★★★★
Kallon ƙwayar idon ta tayi tana ɗage mata gira ɗaya sama alamar jiran ki nake,sai ta kawar da kai wanda hakan ya ɗan ɓatawa Berenice rai ta ɗan nuna alamar ta hanyar wurgar da wuƙar dake hannun ta wanda ta cire daga gefen rigar ta,sai a sannan ta ɗago ta kuma kallon Juda kafin ta maida idon ta ga Balik da shima ita yake kallo,finally ta maido idanun ta ga Juda da ta ƙagara ta ji amsar Agneta game da wannan shawarar da ta kawo mata..
Buɗe baki tayi kamar mai shakkar yin magana sai ta rage murya ƙasa ta buɗe baki tana mai yin ƙasa da kai ta ce....


*_IS SIYAMAIBRAHIM_*
[3/29, 08:59] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:35&36*

"Ba zan iya yarda da ke ba,ba zan iya yarda da ku ba dan ku ba abin a yarda da bane kawai ku bar ni in yi tafiya ta bana buƙatar agaji ko tausayawar kowa daga cikin ku dan haka ku bar ni kawai"a hasale Berenice ta ture ta ta faɗi daga zaunen da take ta koma da baya ta faɗi itama ta bi ta ta danne ta tana mai bin ta da mugun kallo haɗe da faɗin
  "Ke ɗin har wacece da zaki zauna kina tsara mana yadda ya kamata mu yi har muke sauraron ki bayan taimaka maki da muka yi bamu kashe ki mun aika ma shi sarkin naku da kan ki ba muka baki kundin kika tafi da shi dan ya san ba tafiyar wofi kika yi ba sai kuma yanzu dan ana nemar a taimaka maki a fidda ki daga uƙubar wannan azzalumin kike nema ki gaya mana magana wacece ke ko gani kike har kin kai matakin da zamu ɓata lokaci dake muna nuna maki tausayawar mu ke ɗin wacece"!!!rai a mugun ɓace Berenice ta kai ayar zancen dan kuwa ita ta tsani rainin wayo kawai dan ana sympathising da ita sai ta kawowa mutani rainin hankali..
Balik yayi mamakin ƙarfin hali irin ta ƙanwar tasa dan bai taɓa witnessing nata tana displaying anger ɗin ta ba sai yau ko a baya da suke yara ba kasafai ta cika shiga shirgin peers ɗin ta ba dan bata son raini akwai tsare gida...

Juda kam rasa abin cewa tayi dan tayi iya ƙoƙarin ta wurin ganin bata fusata da halayyar da Agneta ke nuna mata da domin da ta ɗau huɗubar kakan ta toh ta san kuwa da ita kaɗai zata cigaba da tafiya kamar mayya amma ta lura one needs another to keep his self vibrant shi yasa tayi accommodating Berenice right from the start dan ta gane akwai ɓoyayyen sirri tattare da ita sai dai sai a hankali wannan sirri zai warware,..
Yanzu kuma tana fatar ƙulla alaƙa da Agneta dan ta gano yarinyar a duhu take shawagi ga mugun dafin sihirin da aka mata tun bata gama sanin kan ta ba wannan dalili ya sa ta yanke shawarar kawai ta janyo ta cikin su in ya so bayan sun gama nemar abin da suka fito nema sai ta cika mata alƙawarin da ta mata na maida ta kamar ƴar uwar ta..
Ɗagawa Berenice tayi daga jikin Agneta da ta haye tsabar ɓacin rai dan bata ma san ta haye ruwan cikin ta ba ma sai yanzu da ta ji kamar Agneta na son ture ta sannan ta ankara ta fara yunƙurin sauka daga jikin ta..
Tana sauka Agneta ta yunƙura ta taso tana mai kakkaɓe jikin ta haɗe da tofar da yawu tana ƙare ma Berenice kallon haushi..
"Na ce a'a bana son shiga cikin ku an taɓa tursasawa mutum yin abin da bai so ne ko dai wata manufa ce gare ku dangane da ni da ban sani ba?ina sauraron ku ku fara magana in da wata ɓoyayyiyar ce ina son sani"!!matuƙa ran Berenice ya kai ƙololuwar ɓaci amma ta daure ta ƙi yin magana dan kar fushi da ɓacin rai ya saka ta illata Agneta..
Kallo Juda ta bi ta da shi kafin daga bisani ta fara magana a hankali
"Agneta ba zan tursasa maki ba haka ba zan baki shawarar komawa masarautar ku ba sai dai ki sani kamar yadda na sanar da ke ne akan wannan kundi nawa ne ni ƙadai kuma ya dawo hannu na ba zai sake kufce min ba dan haka ko ki yarda ki shigo cikin mu ni kuma in cika maki alƙawarin da na ɗaukar maki na kai ki gidan mu mahaifiya ta ta zamo mahaifiyar ki ko kuma ki cigaba da rayuwa ba tare da kin tsira ba dan kin san sarkin ku bai da imani haka bai da tausayi kuma yana iya aikata maki komai ma in har ya gano kina raye a doron ƙasar nan dan haka zaɓi ya rage ga mai shiga rijiya _Iya ruwa fidda kai_..

Shiru Agneta tayi tana bin Juda da kallo dan tun da ta fara maganganun ta take kallon ta a lokaci guda take nazarin ta da kalaman ta dan ta hango gaskiya in ta bari tayi sake na dafe ita a ciki dan kuwa ba barin ta sarki zai yi ba gani tayi kawai ta yarda ta bi shadow na su dan ta san duk yadda aka yi ba kawai Juda take ba duba da tarihin ta da ta sha ji a wun sarki in suna hira da aminin sa sarki Sultan Baal-Hamon a wasu lokuta da suka wuce game da tsaurin idon ta da hikimar ta ko ba komai ta san zata shaƙi wannan sirri na Juda kuma zata kasance cikin kariya dan Juda na ɗauke da kariyar ta a tare da ita...
Mugun kallo Berenice ke aikawa Agneta da shi dan ita kwata kwata bata son yarinyar kuma bata wani yarda da ita ba haka kawai ta ji Agneta bata mata ba a rayuwa...
"Na ji,na yarda zan shigo cikin ku sai dai fah ku sani,kuskure ɗaya da zai janyo min gane cewa shigar da ni kuka yi a loko toh fah babu wanda zai sha da sauƙi"ɗan scoff na mamakin ta Berenice tayi sannan ta kallo ta har ta buɗe baki da nufin yin magana sai kuma ta fasa tayi shiru ba dan hakan ta so ba sai dan hakan shine mafi alheri a gare ta dan ta san tana buɗe bakin ta toh mummunar abu ne zai biyo baya dan haka kawai ta juyar da kan ta gefe tana sauraron maganganun ta har ta gama..
"Kin tabbata da zuciya ɗaya kika yarda ko kuma da wani dalilin ki"?wani haushin Juda ne ya tasowa Berenice in ba rashin tunani ba ta yaya ma zata fara yarda da ita alhalin ta san ba son su take ba tun haɗuwar su ta fari bata tunkare su da arziƙi ba toh dan me su zasu ƙarbe ta,sai dai in ta san wata ai bata san wata dan haka ta cigaba da yin shirun har dai zuwa lokacin da ta jiyo muryar Agneta na va Juda amsa
"Na ce maki na yarda kuma ai na yardar sai dai in jiye maki ranar da zan gano tarko kika ɗana min dan kuwa ba barin ki zan yi da ran ki ba"sai ta juya zuwa ga Berenice da Balik ta kalle su kana ta ɗora da
"Hatta su ma ba barin su zan yi in na gano wata gaskiyar"sai a sannan Balik ya kuma kallo ta ya ga eh da gaske fah da su take yi dan haka shima cikin hasala ya bata amsa da
"Ko kuma mu mu kamo tsintacciyar mage mai son yi mana maƙarƙashiya ba"!!?sarai Juda ta gano inda zancen sa ta nufa haka Agneta da Berenice dan haka yana gama faɗin haka ya ɗau jakar sa ya juya ya fara tafiya dan haka sauran ma suka biyo sa a baya sai dai fah tsakanin Berenice da Agneta kallon tankaɗen dusa suke aikawa junan su da ka gan su ka ga masu ƙulafucin juna dan ba sauƙi Berenice akwai zafin kai haka Agneta ma akwai zafin kai..
Yayin da suke wannan budiri Juda da Balik na kallon su daga bayan su dan dai Juda ta gano babu jituwa mai kyau tsakanin Agneta da Berenice dan haka tayi tunanin haskawa Berenice abin da ta gano tattare da Agneta da ya sa ta yarda da tarayyar su a tare,haka dai aka cigaba da tafiya kamar kurame marasa ji bare maida magana...

★★★★★

A haka dai tafiyar su Juda ya cigaba da kasancewa har tsawon kwanaki uku haka zalika tsanar dake zukatan Agneta da Berenice babu abin da ya ragu sai ƙaruwa da yake yi kuma a hakan Juda da Balik ke kallon su ba su ce da su kanzil ba bare ku ci kan ku iyaka in abin yayi yawa har ya kusa kaiwa da faɗa sai a shiga tsakanin su dan ko abinci Berenice ta nemo masu ko kuma ta sato ta kawo toh Agneta bata ci sai dai

Please Login or Register in order to submit comment