Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba my king da na sani ba meke faruwa"..kallon sa ya mayar gare ta yana nazari da tantance yiwuwar abin shin ya yarda da ita ne ya bar ta ta tafi ɗauko ɗan sa kuma ta wuce da shi izuwa masarautar Ottoman ne dan aiwatar mai da abin da ya daɗe yana tunanin me aiwatar mai da shi?tunda ita dai ta kasance amintacciyar karuwar sa ce mai riƙe mai amana da sirrin sa duk ƙwaƙwar ka kayi ƙarya ka ce zaka bugi cikin Daina ta faɗa maka sirrin mai martaba sarki Malik.. 

  Ɗan tasowa yayi daga kishingiɗar da yayi yana kallon ta kafin ya ce da ita wani abin
  "Daina,,na yarda da ke dan sam baki son ɓacin rai na,kina min abubuwan da suka dace suka kuma kamata,dan haka sakamakon yarda da amince maki da na yi zan yi assigning naki ki min wani duty da zai tafi a matsayin assignment ne,in kika yi komai neatly and clean toh zan maki kyauta babba ba kaɗan ba dan haka in kin shirya ina jiran jin ra'ayin ki"..
  Tunda take tare da sarki Malik bai taɓa biɗar wani alfarma daga gare ta ba sai wanda ba za'a rasa ba na cikin masarauta amma yau yana nemar alfarmar ta da taimakon ta sannan har bata dama yayi dan tayi tunani,toh lallai ya kamata tayi abin da ya dace. 
  Kallon sa tayi ido cikin ido ta ce da shi cikin muryar ƙasƙan da kai
  "My king,am your mistress,my king am your pleasure,my king am your loyal servant,my king you are forbidden from seeking for a favour from a mere chip mistress and a servant,my king,what ever the favour is,consider it done and cleared please,you shouldn't and should not seek for any favour from me again my king"!!..
  Ƙasa tayi da kan ta tana ƙasƙantar da kan ta dan ta san dai tun a tarihi a zamanin da ba'a taɓa yin sarki mai daraja da iko da yake nemar alfarmar mere mistress ba sai a yau dan haka ita kam bata ga dalilin da zai sa ta kasa cika mai wannan nufi nasa ba ko ba komai ya ɗaukaka ta fiye da yadda yake treating bayin sa ya bata gurbi a rayuwar sa mai girma wanda ko matar sa bai ba wannan gurbi ba,toh dan me zata kasa yi mai abin da yake so...

  A ko da yaushe ire iren kalaman bakin Daina da take furta sa kan saka sa jin yana da muhimmanci da ƙima a idanun ta dan bata duba cewa wai yana haɗa shimfiɗa da ita shikenan barumi ta rinƙa mai abu son ran ta..
  Shi ko yayi alkawari matuƙar ta iya ladaftar da yarima Ziyan ya bi ta suka tafi masarautar Ottoman toh zai bata kyautar da bai taɓa yin sa ba a rayuwar sa wannan alƙawari ne ya barwa kan sa..

  Tasowa yayi ya zo daf da ita ya tsuguna ya ɗago ta tsaye suna kallon juna ya ce da ita
  "Yarima Ziyan zaki tafi ki ɗauko min sannan ki yanki hanyar ƙasar Ottoman da shi ku fasa masarautar Ottoman ku ɗauko min kundi da kambun dake ɓoye cikin ma'adanar masarautar Ottoman sannan ku raba kan sarki Sultan Baal-Hamon da jikin sa ku taho min da kan nasa nan dan nayi rantsuwa babu wanda ya isa ya mulki duniyar nan sama da ni ni na dace ba Sultan Baal-Hamon ba,ina so ki kama hanya ke da karagar ki kuyi ayari zuwa ƙasar da yarima Ziyan ymke karatu ku ɗauke sa in ya kawo maku ja ku hukunta sa daidai misali"..
  _Kasancewar yarima Ziyan ba ƙwarewa yayi a fannin yaƙe yaƙe ba sai bai taɓa mai da hankalin sa a wannan fannin ba iyakar sa ya kalli masu yi dan shi ba yaƙin da mulkin bane a gaban sa shi bincike da ƙwaf ƙwaf ne a gaban sa dan ya rantse da Allah da yake bautawa sai ya tono asirin sarakunan nan huɗu babu abin da ya shafe shi wato sarki Sultan Baal-Hamon,sarkin Jordan,sarkin Cyprus da sarkin Oman mahaifin sa wato sarki Malik,sam bai shakkar ko ta kwana dan so yake ayi ta ta ƙare ya fallasa sirrikan da suke ta ɓoyewa ya tono su da aƙidar da suke kai na hana jama'a moruwa da ilimin zamani da na addini da aka daɗe ana gabatar da su a ƙasashe daban daban ciki har da ƙasar Ottoman amma saboda son zuciya irin ta sarkin masarautar Ottoman ɗin dake kai yanzu wato Sultan Baal-Hamon sai aka shafe komai aka nemi dasa sa a matsayin tarihi ba cigaba na alkhairi ba,wannan shine burin yarima Ziyan Aman wato ɗa ga sarki Malik jika ga sarki mai rasuwa sarki Aman Al-Riaz_.

  Kallon sarkin tayi sai tayi ƙasa da idanun ta ta fara magana
  "Na maka alƙawari sarki na,duk yadda kake so haka zan maka baka da shakku ko damuwa dangane da hakan sarki na,na maka alƙawari kuma yau ɗin nan a yanzu zan tafi in shirya su mu ɗau hanya"!!daga haka suka yi abin da suka saba yi na haramci sannan ya bar ta ta bar sashen nasa ta nufi nata sashen dan shirya tafiya..

★★★★
_MUGHAL EMPIRE_

  Kishingiɗe take bisa gadon mulkin ta tana ƙarewa ɗan saurayin kallo tana sauraron ƙarar da ake koro mata dangane da fyaɗen da wasu maza suka ma wasu ƴan mata ba tare da yardar ƴan matan da amincewar su ba suka masu kaca kaca suka keta masu haddi kuma ita a ƙa'idar ta bata karɓar wannan ƙara ba tare da ta aiwatar da hukuncin ƙarar ba..
  Kamar daga bacci aka mare ta ta fizgo maganar ta ce
  "A yanke masu martabar su sannan a kawo a nuna min a nunawa masarautar nan kaf sannan a kaiwa dabbobi su yi abincin yamma da shi"tana gama faɗin hakan ta miƙe aka mimmiƙe ana bin ta a baya suka biyo bayan ta yayin da ita kuma ta nufi hanyar sashen ta tana mai aikawa wannan saurayin kallo irin kallon ka biyo ɗin nan..
   Saurayin jiki na ɓari ya bada mintuna kaɗan tana gama shigewa ya bi bayan ta..
  Tun daga bakin ƙofar ɗakin suka fara shirmen su har sai da suka yi abin da ya masu daɗi sannan suka tsagaita ta sallame sa ta wuce ɗakin wanken jikin ta da gyaran jikin ta dan sati ya zo ƙarshe lokacin hutun ta ya gabato..

  Tana cikin bahun wankan tana faman tunanin ɗiyar ta ganin har yanzu bata ji daga gare ta ba kuma abubuwa na nemar kiɗime mata bai tafiya a yadda ta tsara sa..
  Matuƙar tana da burin mulkar duniyar nan toh fah dole ta zage damtse ta saka a binciko mata ɗiyar ta ko ta ko ina dan sam bata son rasa wannan mulki kuma ba zata taɓa samin wannan mulki ba sai da presence na gimbiya Ondrea....
 
  Ta daɗe cikin abin wankan sannan ta fito ta koma cikin ɗakin ta ta kwanta bisa gadon ta tana tunanin mafitar ta dan tana tsananin buƙatar ɗiyar ta kusa da ita dan in babu ita sam abin nan ba zai mata daɗi ba gashi ta ɗora buri sosai akan son mulkar duniyar nan dan haka dole ta sake takun saboda ba zata taɓa yarda Sultan Baal-Hamon yayi nasarar mulkar duniyar ba sai dai ij bata raye..

Aike tayi akan a tafi a binciko mata faɗin Mughal a gano mata inda ɗiyar ta da bawa mayaƙi Cahal suke dan abin ya fara ɗaga mata hankali matuƙa,jiya jiyan nan aka sanar da ita gagarumin asarar da zata riske ta nan ba da jimawa ba..

★★★★★
Kaf suka karaɗe gidan nan amma babu wanda suka yi katarin gani bare kamowa dan haka suka haƙura suka kuma komawa matattarar su suka yi shawarar barin masarautar kafin a gano su dan still suna da chance na biyu har na uku kafin damar ta ƙulle masu..
Kallon gimbiya Acenath suka yi sai Balik yayi tambayar ko a ya zasu yi da ita..
"Barin ta kawai zamu yi mu tafi next time,,when we return back,i swear i will not spare this Empire and the ruler of the Empire".daga haka suka nemi hanyar fitar su suka fita ba tare da an san fitar nasu ba..

★★★
Bayan wasu kwanaki daga ranar da su Juda suka shiga masarautar Sultan Baal-Hamon,sun yanke hukuncin barin sa sai bayan komai ya lafa dan kar a gano takun su tunda sun rigada sun gama tsarin su toh in suka koma yanzu sun san dole za'a gano su shi yasa Baccus ya ce da su su ƙara jimiri har zuwa wani lokacin dan kar a gano takun su..

Juye juye take yi cikin ruwan tana tunane tunane,son sani take shin menene wannan addinin da ake ma kirari haka kuma ta ya ma aka yi aka gano sa ita dai ta san bata taɓa yin katari da wannan shafin ba cikin karance karancen ta toh ko dai kundin bai gama cika bane har sai an ƙara mai wasu tarihin?toh wa zai ƙara tarihin?zuciyar ta ne ya bata amsa da "Ke mana,ai ke zaki rubuta mai wani tarihin"..
Da sauri ta fito daga ruwan tana mai naɗe suman ta ta saka rigar cikin ta riƙo ɗaya na wajen a hannu tana tafe tana fatar kar tayi rashin sa'a tana fatar tayi katari da Baccus dan ya bata labarin wannan addini dan ta ƙara sa cikin kundin ta tunda tunanin ta ya bata kamar ita ce mutum na gaba da zata nemi wani wuri cikin kundin ta saka tarihin wannan addini..

Ko da ta zo zata wuce su Fianna sai Callee ta tare ta da faɗin
"Akwai labarin da nake son baki tun ɗazu ban gan ki ba ina ta jiran ki"...bata sami damar ƙai ƙarshen ayar zancen ba Juda ta dakatar da ita ta hanyar faɗin
"Zan saurare ki in na dawo Callee yanzu ban da lokaci sai na dawo"..daga haka ta haye dokin ta taba mai yi masu sallama akan zata dawo zuwa dare..
Duk abin ya ɗaure masu kai ta yaya zata zaɓi tafiya ita kaɗai cikin wannan lokaci babu rakiya babu wani dogon tunani...

★★★
Ko da ta ɗauko hanya bata yi karo da komai ba haka bata yi karo da kowa ba sayau ta yi tafiyar ta har ta nufi hanyar kasuwa zuwa mashayar Baccus dan yi mai tambayoyin da take son ƙarin haske akan sa..
Da fari kamar ba za'a bar ta ta shiga ba ganin irin suturar dake jikin ta irin ta mayaƙa sai sai da ta nuna masu ta fah san Baccus kuma shima ya san ta da kyau sannan suka bar ta ta shiga har ɗakin sirtin Baccus ɗin..

Bayan gaisuwa da ƴar taƙaitacciyar hira da suka yi sai ta mai bayanin abin da ya taho da ita..
Murmushin manya yayi mata sannan ya zauna bisa kujerar saai ɗan faɗi yana mai nuna mata wurin zama haɗe da faɗin
"Na so in fayyace maku komai tun ranar farko amma abin mamakin shine na rasa ta ya zan maku bayanin dan ban san mutum mawa zasu yarda da maganar ba sai dai ban cire rai ba na san nan ba da jimawa ba wani cikin ku zai zo da wannan buƙatar sai dai ban san ke ce ba"..shiru tayi tana kallon sa har ya ɗora daga inda ya tsaya
"Zan sanar da ke amma kar ki yarda wasu su sani bayan abokan tafiyar ki dan hakan daidai yake da barazana ga rayukan ku muddin aka gano kafin mu aiwatar da abin da muke son aiwatarwa"..gyaɗa mai kai tayi shi kuma ya miƙe ya nufi hanyar ajiyar litattafan sa ya ɗauko wata babbar littafi ya hura da bakin sa ƙura ya tashi sai ya dawo ya zauna yana mai buɗe littafin..
"Kina ji na"?gyaɗa mai kai tayi sai ya ce da ita
"Ta ya kike son jin labarin wannan tarihi?shin rubutawa zaki yi ko ko sauraro zaki yi kawai"?sai ta girgiza kai tana faɗin
"Ina son in rubuta shi ne cikin kundin nan dan na san shine mafi amfanuwa gare mu kuma zai kawo cigaba a rayuwar mu dan ina son sanin meke faruwa me kuma ya faru da bamu sami damar sani ba"jinjina kai yayi cikin gamsuwa yana faɗin
"Toh yanzu zaki ji tarihin da kyau".

_HISTORY OF RELIGIONS IN THE WORLD(Tarihin addinai a duniya)_

_Tarihin addinai ya faro ne tun shekarun baya kusan shekaru dubu biyar da ɗari biyu(5,200 years ago),a ƙarnin da suka shuɗe kusan ƙarni ƙarni har dubu uku da ɗari biyu(3200 BCE)..,_
_Tarihin addinai an faro shi ne ta hanyar rubutu,dan sauƙaƙawa da ajiye abin da baya zasu zo su tsinta su ƙaru da shi dan cigaban rayuwar su_.
_A lokacin ƙarni ta ashirin da ɗaya(21st century)akwai wani masani da ya laƙanci abin da addini ke nufi ya kuma kunsa mai suna_ *Daniel Dubussion* _wanda shine ya rubuta manufar addini_
_A nasa fahimtar ya ce addini wani abu ne wanda ya kasance unique kuma sai da yarda a zuciyar mutum kuma mutum ke iya yin sa daidai gasgantawar sa da yardar sa akan wannan addini_..
_Akwai wani lokaci da aka yi ƙarni wato ƙarni ta goma sha tara(19th century)da aka ƙirƙiro makarantar koyar da addini wanda ya faro ne a ƙasar jamani(Germany)inda a nan aka hmga dacewar addini a rayuwar bil adama_
_A lokacin an ɗaukaka addini sosai dan an gano addini na tafiya ne akan turba daban daban mai kyau kamar yadda yake tafiya da tsarin doka,rayuwar ɗan adam da mutanin da ke tare da shi,kamilancin mutum,duk an gano addini na saita waɗannan abubuwan_.
_Still a wannan ƙarni ta sha tara(19th century)an kuma gano muhimmancin addini a duniya duba da yadda yake tafiya daidai da tsarin tattalin arziƙi na ƙasa da haramci ga almunbazaranci da abubuwa masu amfani ga ƙasa a haka ne aka sake gano ana gabatar da addini ne daga matakai tun daga kaɗan har zuwa babba wato daga mai sauƙi har zuwa mai wuya ta yadda har aka gano ana iya canza addini daga wannan zuwa wannan duk dan a tafiyantar da komai bisa tsari_..
_Ana haka ne ilimi ya kuma faɗaɗa aka gano cewa addini ya sami karɓuwa har aka yi wasu ajiyayyun theorise akan sa daga wun masana daban daban kamar Edward Burnett Tylor a shekara ta alif dubu ɗaya da casa'in dda talatin da biyu zuwa shekara ta alif dubu ɗaya da tamanin da sha bakwai(1832-1917),haka masana kamar su Hebert Spencer da John Lubbock duk sun ƙara haske akan addini da muhimmancin sa_..
_A waɗannan shekaru ne kuma aka fara tantance masu bautawa abubuwa daban daban kama daga masu bautawa duwatsu,masu bautawa shanaye,masu bautawa rana,masu bautawa dutse,masu bautawa wuta,masu bautawa wasu koyarwar daban daban da masu bautawa dabbobi_

_A haka aka kuma samin cigaba a ilimin addini dan ko wani addini na ƙoƙarin ganin bai ɓata ran wani ɗan adam ba wanda ba addinin su guda ba,an ƙara kusanci da juna ana kafa kafa da ɓacin ran wani da yake bautawa wani abu daban da ya yarda da shi,da haka ne aka sami sauƙi da zaman lumana a duniya baki ɗaya_
_Daga haka aka kuma bambance addinai da ƙasashe da dama ke yi kamar ƙasar india da suka fi mai da hankali akan bautar gumaka dan sun yarda da shi har zuciyar su sai wasu ƙasashen da kusan hakan ne,daga haka aka rarraba addinai ta yadda christianity ya bambanta da wasu addinai har aka kuma kafa tarihin wani addini da ake kira da Islam wanda shima a tarihi addini ne mai ɗumbin tarihi in aka yi duba ta wani fuskar dangane da asalin sa_..
_Wannan addini mai suna Islam,ya karaɗe wurare da dama kama daga Asia ta tsakiya,Africa ta tsakiya da wasu gefe a Europe da India_
_A lokacin da addinin islama ya kafu ne aka yi wani yaƙi da faɗa mai tsamari tsakanin mutanin addinin islama da mutanin Zoroastrian lokacin da aka yi wani yaƙi a ƙasar Persia a shekara ta ɗari shida da talatin da uku zuwa shekara ta ɗari shida da hamsin da huɗu(633-654)..a inda mabiya addini kirista(christianity)suka zage suka yaƙi musulmai lokacin yaƙin larabawan Byzantine a ƙarnibta bakwai zuwa sha ɗaya(7th to 11rh century)da kuma yaƙin ottoman a ƙasar Europia(Europe) a ƙarni ta sha uku(13th century)har wa yau,wanda a yaƙe yaƙen ne tsakanin musulmai da kirista musulmai suka haɗu da mutanin ƙasar india(Hindustani)_
_Bayan yaƙin ne aka sami haɗuwar kawunan waɗannan mutani biyu wato musulmai da mabiya Hindu a inda wasu suka amince suka karɓi addinin islama a ƙarnin kuma suka cigaba da bin addinin ƙarƙashin koyarwar Adi Shankara a shekar ta ɗari bakwai da casa'in da takwas zuwa shekara ta casa'in da ashirin(788-820)..

_Daga wannan lokaci wani ƙarni ya zo a inda mabiya addinin kirista suka baza addinin su a wurare daban daban kamar su ƙasashen phillipines,America,wasu wurare sahara dake Africa da ƙasar Australia.._
_Tun wannan lokaci ake cigaba da yaƙi akan addini haɗe da ɓangaranci wanda bai kwanta ba har ƙarni ta sha takwas izuwa ƙarni ta sha tara wanda sai bayan faransa(France)ta tsayar da nata zaɓin ɓangaren bautar sannan aka sami sauƙi har zuwa ƙarnu ta ashirin_
_A ƙarni ta ashirin(20th century)aka yi ƙiyasti inda aka gano ƙasar china basu da addini bin addinin da ta masu kaɗai suke yi yau suna wannan gobe suna wannan basu da takamammen addini guda ɗaya,yet aka kuma ƙiyasti akan sabbin addinai da aka rinƙa kawowa daga baya wai dan ya tafi da zamanin da ake ciki,sai dai ga masana addini da ƙimar addinai suka yi fatali da waɗannan sabbin addinai ba'a saka su a ka ba aka cigaba da tacewa da tantancewa har ya kai aka gano adadi(%)na mabiya addinai kamar haka:mabiya addinai da aka kawo su daga baya kashi biyu ne kawai(2%) a faɗin duniya a shekara ta dubu biyu zuwa dubu biyu da tara(2000-2009,sai mabiya addinin da zamani ke tafe da shi daidai misali inda aka samo kashi saba'in da biyar(75%)sai kuma waɗanda ke biyewa addinin gargajiyanci waɗanda kason su kaɗan ne(4%),sai kuma a shekara ta dubu biyu da biyar(2005)inda aka gano kaso goma sha huɗu(14%)basu bin ko wani irin addinai kenan basu bautawa komai(Non religion)_..

Numfasawa Baccus yayi yana share zufar fuskar sa sannan ya ɗago ya kalli Juda yana mai ce da ita
"Kin ga kenan ba ƙaramin cutarwar sarki Sultan Baal-Hamon ya ma ƙasashen da yake mulka ba dan sam basu cikin masu bautawa komai tun ma kafin zuwar sbekarat da aka ce an gano kason marasa addini a duniya,ya hana su bautawa komai duk da a zamanin kakannin kakannin sa kin ji an ce sun yaƙi kirisyoci dan kafa addinin islama kuma har mahaifin sa ya bar duniya yana kan turbar wannan addini ce wato ta islama sai dai shi a nashi mulkin,ba wannan ne a gaban sa ba abin dake gaban sa shine ya mulki duniya da mutanin cikin sa hakan ne ya sa ya zamo mai son zuciya da son kan sa"..
Numfaswa Juda tayi kafin ta kalli Baccus ta ce da shi
"Toh kai kawu Baccus wani addinin kake bi"??ɗan murmusawa yayi kafin ya ce
"Zan sanar da ke im lokaci yayi amma ba yanzu ba abin da ya dace da ke shine ki je ki ilimantar da abokan tafiyar ki dangane da wannan tarihi da na baki sannan ku sake shiri dan yaƙi ne babba a gaban mu,ni da ku kar ki yadda wani ya san da wannan sirri cikin kundin ki"!!gyaɗa mai kai Juda tayi tana mai tashi tsaye ta mai sallama ta fita abin ta..
Har ta hau dokin ta tana tafe bata daina tuno tarihin nan ba toh a ina ne ake gudanar da wannan addinin a duniya dan dai su basu yin sa a ƙasar su haka bata taso da shi ba a rayuwar ta all she knows shine war and battle,she was trained on a battle to reach out for something and right now she is on a _Battle To Reach_ out for her sister dan haka bata san ta yaya zata ɗorawa kan ta so da sanin wannan addinai ba haka bata san wa zai ƙara koyar da ita ba game da addinin amma ta san ko ba koma akwai _Bambanci Ƙasa_ albarkar wannan _Bambancin Ƙasar_,zata sami mai nuna mata daidai da akasin sa..
Da haka ta dawo wun abokan tafiyar ta suna mata barka da zuwa ita kuma tana tunanin yadda zata masu bayanin abin da ya fitar da ita...


*_IS SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 09:04] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
   WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_

*EPISODE:49&50*

Sai da Balik ya gaji da shirun Juda yayi magana ta hanyar kallon ta yana faɗin
  "Wai ke kam me kika tafi kika samo ne a tafiyar nan taki?tun dawowar ki kike bin mu da wasu irin kallon sannan kin kasa cewa ko da a ne kin bar mu cikin duhu"..
  Numfasawa tayi sannan ta fuskance su kana ta warware masu komai haɗe da ɗorawa da
  "Ni fah hankali na ya tashi game da addinin nan mai suna Islam ban san me ke cikin ta ba amma ina ji a jiki na akwai wani gagarumin abu tattare da wannan sunan kuma ina ji a jiki na kamar shi zai zame mana next option ɗin mu na tunkarar masarautar Ottoman but ban san ta yaya hakan zai faru ba,ni tun tasowa ta ban taso na ga ana wani bauta ba hasalima ban san wani abu bauta ba kuma ban san ya zamu yi amfani da wannan adadi wurin ganin mun naƙasa wannan azzalumin Sultan ɗin ba,i don't know but there is something special about this religious believes"!!a dame ta ida maganar wanda tana sauka karaf Agneta ta cafe ta hanyae faɗin
  "Wannan same addini nake maki magana akai lokacin da na ce da ku ɗan sarki Malik wato yarima Ziyan ya dawo ya ce sai an yi abu biyu,karatun zamani da kuma bauta,toh wannan shine sunan irin bautar da ya ce za'a yi a masarautar mahaifin sa"!!..
  Maida kallo aka yi gare ta sai Fianna ta amshe zancen
  "Kenan hakan na nufin yarima Ziyan na bautawa ubangijin wannan addini kenan"?gyaɗa kai duk suka yi sai suka yi shiru can kuma suka ɗago same time sai Berenice ta ce
  "But in haka ne kenan shi zai san komai kuma shi ya kamata mu nema ya taimaka mana,tunda shi kan sa ba son ɗabi'ar mahaifin nasa yake ba a gani na kamar muna iya amfani da wannan damar wun durƙusar da Sultan Baal-Hamon amma ya kuka ce"?..
  Kasaƙe Juda tayi sannan ta ce da su su duka
  "Shawarar Berenice daidai ne sai dai ba a nan gizo ke saƙar ba,ina zamu gano sa kuma ta ya ma shi zai yarda ya aminta ya biyo mu kuma anya ma zai iya juyawa mahaifin sa baya kamar yadda muke hasashe kuwa?ya tabbacin mu akan hakan yake"?shiru suka kuma yi kafin Callee ta amsa ta ta hanyar ɗage gira ɗaya sama
  "In bai yarda ya biyo mu ta salama ba toh ai ga ki sarauniyar mayaƙa,kina iya tanƙwara mana shi"!!dariya ce ta kufce ma Juda yayin da sauran suka murmusa kawai dan maganar nata cikin tune ɗin zolaya ne sai ta ce
  "Callee,ba lokacin fah wasa muke ba mafita muke nema ki kawo reasonable idea kin ji"?sai Callee ta murmusa itama daga haka suka natsu suna nemar mafita..

  Har kusan rabin dare basu samo mafita mai sauƙi ba duk mafitar sun cika tsauri da risky amma sun tsara plans uku,option A,B and C..
  Option A shine Fianna da Agneta su tafi har can ƙasar da yarima Ziyan ke karatu su mai bayanin abin dake tafe da su in

Please Login or Register in order to submit comment