Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na lafiya,sai na ce da shi ai abin da sarauniya Bayarma ta haifa ne ya koma,kasancewar duk cikin masu yi mata hidima tun da ta fara naƙudar nan an dakatar da su dan kar su cutar da ita sai ni kaɗai ke shigi da fici a sashen nata"_
_"Shiru Sultan yayi a tsaye yayin da ni kuma na ke kukan munafurci da kirsa,can kuma sai na ga Sultan ya fita,jim kaɗan sai ya dawo ya ce da ni ɗau jinjirar mu fito tare,hakan na yi sai muka nufi sashen sa inda ya ce da ni in ɗau jinjirar in kai ta in binne ta a kusa da maƙabartun kakannin ta kuma in bar maganar daga ni sai shi"_
_"Amsa mai na yi sai na fita na nufi inda ya aike ni ɗin sai dai fah ba binne jinjirar na yi ba binne banza kawai nayi na ɗau jinjirar na bi dare da ita na saci jiki na kai ta fannin da ake ajiye jarirai in an sato su,ban bar wurin ba sai da na tabbatar jinjiran ta farka sannan na saci jiki na bar wurin na dawo cikin gida"_
_"Abin mamaki shine,wai bayan na dawo sai na ga sarauniya Bayarma ta farka,hannun ta riƙe da jaririya tana ta murmushi,gefe ɗaya Sultan ne yake ta zuzuta kyawun jinjirar,sai abin ya ɗaure min kai amma na dai yi shiru na rinƙa farincikin ƙarya da yaƙe dan kar a gano ni,"_
_"Da Sultan zai fita ne ya kirawo ni ya sanar da ni komai sannan ya ɗora da cewa jaririyar zata zamo masa kariya a rayuwar sa ta yadda duk wani wanda zai yi galaba akan sa toh fah ba zai yi nasara ba sai dai ya rasa ran sa,muddin jinjirar ta rayu,ko da ya sanar da ni wannan labari sai nayi shiru ina kasaƙe amma na barwa zuciya ta abin yi da wannan shawara da tunani na Sultan"_
_"A haka Sultan ya kai jinjirar nan wun mai masa duba wato Aberald dan ya wanke ta tas da sihiri sannan ya raɗa mata sunar da babu wanda aka taɓa raɗawa a tarihin masarautar,nan dai aka raɗawa jaririyar Acenath a inda tun daga lokacin ake kiran ta da gimbiya Acenath kuma sunan ya bi ta"_
_"Shekaru da yawa ya shuɗe,nakan tafi in kaiwa ɗiyar Sultan ziyara a ɗakin bursinar nan,sosai yarinyar ta saba da ni a kullum in nayi tunanin hallaka ta sai in fasa dan so nake Sultan ya gani da idanun sa bayan ya gano ainihin ɗiyar sa na da rai sai in raba sa da ita,duk rayuwar da tayi ban taɓa yarda an mata fyaɗe ba dan ba shi ne ƙudiri na ba saboda ko ni babu wanda ya min a lokacin da ya turo a watsa yankin mu"_
_"Da haka rayuwa ta cigaba annamimanci na na yau daban nna gobe daban har aka gama yarda da ni a masarautar nan baki ɗaya,sirrin dake tsakani na da Sultan kuwa yana nan a ɓoye,yau da gobe bai bar komai ba,matsaloli ya ishi Sultan har dai ya kawo wannan mayaƙin wato Irad daga ƙasar Iran dan ya magance mai shi dai nashi matsalar,ya mulki duniya,toh da munafurci na na janyo ra'ayin Irad har ya biye min na rinƙa warware mai komai har dai shima ya sanar da ni cewa ga dalilin sa na karɓar gayyatar Sultan kuma ya ce da ni shi ɗin sahihin amimi ne ga ɗan sarkin Oman wato yarima Ziyan Aman"_
_"Shi ya sanar da ni yadda zan yi komai kuma ya sanar da ni cewa a yau wannan abin zai faru kuma kar in ɓoye komai in faɗi duk abin da za a yi a yi sa dan yau sai am ga bayan Sultan Baal-Hamon sannan ya ce da ni da hannu na zan raba kan Sultan da jikin sa,toh dama abin da nake muradi kenan kuma na samu,dan haka na ce zuwar Irad masarautar nan haske ne a gare ni kuma baƙin duhu ne ga Sultan sai dai bai sani ba"_..

A yayin da ta dire wannan labari nata sarauniya Bayarma ta daɗe da sandarewa a zaune suma masu zaman fadar duk sun yi shiru,Sultan na zaune kamar sakarai babu magana,gimbiya Acenath na kallon bakin Calva kamar tana kallon wani abin al'ajabin da bata taɓa gani ba,ayarin su Berenice da su Cahal kam abin ba'a cewa komai sai shiru,Juda kam tun ɗazu take tuno irin abubuwan da suka faru a shekarun baya da wannan yaƙi ya kaure,dama ƙanwar ta suka taɓa yunƙurin sacewa a shekarar da ta gabata dama,amma saboda ƙarfin jini da nufin Allah sai hakan bai faru ba..
Kuka ne ya so cin ƙarfin ta amma ta danne tana ta son controlling kan ta amma ta kasa haka kawai ta fizge takobin hannun Irad ta kaiwa Sultan wani wawan soƙi a inda ta san ba lallai bane ya daɗe a raye in yayi wuta mintuna ashirin....


*_SIYAIBRAHIM_*
[4/1, 07:45] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
   WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_

*EPISODE:67&68*

Wani ƙara gimbiya Acenath ta saki da sai da ya karaɗe faɗin masarautar nan sannan ta haukace ta faɗo gaban mahaifin nata tana ihu kamar zararriya,ko sarauniya Bayarma dake a matsayin matar sa bata yi wannan haukacewar ba kamar yadda gimbiya Acenath ta haukace,.
"Ƙarya ne,ƙarya Calva ke yi,Sultan ne mahaifi na,shine mahaifi na,ni ce ainihin ɗiyar sa,ban yarda ba,ban yarda da wannan ƙaryar ba,ina kuke,ina kukee,,ina kuke nee,,,ku zo ku tafi da Calva,,,ku ɗauke ta,,,ku mata ɗaurin talala,,,na yi rantsuwa Calva ƙarya take yi,,,Sultan..Sultan,,,shine mahaifi na,,,ban yarda ba,Mama na ki zo ana so a raba ni da ke"...
Kowa shiru yayi yana sauraron ta dan an san raɗaɗi ne da zafi haɗe da firgici su suka saka ta jin hakan amma kuma an san dole ta karɓi gaskiya dan in ha Sultan ya iya yin shiru akan abu irin wannan ba tare da ya dakatar da Calva ba,toh hakan na nufin eh da gaske fah gimbiya Acenath ba ɗiyar sa ba ce...
Haukacewa gimbiya Acenath tayi kamar zata kashe rai,yayin da Sultan ke ƙaƙarin mutuwa amma yana ta ƙoƙarin samin hankalin ta dan ya tabbatar mata da gaskiyar maganar akan cewa eh zancen Calva gaskiya ne dan ba shi bane ya haife ta,amma ina ta burge bata cikin hayyacin ta...
Yarima Ziyan dake cikin firgici ganin irin yankar da aka yiwa Sultan Baal-Hamon sai ya ji jikin sa ya wani yi laƙwas kamar baya cikin hayyacin sa sai dai mare image nasa dake zaune a wurin babu motsi...
Irad ne dake tsaye yana ƙarewa Juda kallon mamaki ganin irin yadda tayi ma Sultan yankar wulaƙanci sai ya kawar da kan sa gefe dan bai so aka yi irin hakan ba ya so ne a ce sun bar komai ya tafi a zamanance an yi yadda ya kamata amma ta ɗau hukunci da kan ta..
Gimbiya Ondrea kuwa kamar an ce kar tayi witnessing wannan yankar,tuni ta birkicewa Cahal ta fara yi kamar bata hayyacin ta ta fara juye juye ko kafin ya ankara har ta sume,abin da ya ɗaga mai hankali kenan,duk yadda ya so abin ya ci tura haka ya kinkime ta suka fito ya shiga nemar inda zai sami ruwa dan yayyafa,da ƙyar ya samu ya zo ya rinƙa watsa mata har dai ta farka ta kuka akan ya ɗauke ta daga nan ita bata son cigaba da zama a nan ita dai ya raba ta da nan wurin..
Da ƙyar da lallashi da lallami ya samu ta natsu sannan suka koma ciki amma bata yarda ta ɗaga kan ta ta kalli abin dake faruwa ba...
Dama tun bayan fitar su faɗa ta kaure tsakanin gimbiya Acenath da yayar ta wato Juda a inda ta rantse sai ta hallaka Juda ita kuma Juda ta ƙyale ta dan ta san ko mutuwa zata yi tohta bar zaman gidan nan kenan,ƙafar ta ƙafar gimbiya Acenath,Calva ce ta janyo wannan budurwar har gaban Sultan dan haka yarinyar take kamar mai matsalar ƙwakwalwa babu uhm babu uhmuhm,...
Durƙusar da ita tayi a gaban Sultan tana mai ce da shi
"Sultan nayi baƙin ciki da ba ni na ɗau hanyar kashe ka ba kuma na so in yi hakan amma abin ya shammace ni,but,duk da hakan,,here is your daughter you can bless her and wish her farewell before you go"!!kallon yarinyar yayi wacce tayi kama da sarauniya Bayarma tsab,a yayin da ya kai hannun sa kan yarinyar yana shafawa gimbiya Acenath kuwa ji tayi kamar ta kashe yarinyar dan haka cikin fushi ta fara magana
"Baba na,ka yarda wannan ce ɗiyar taka kenan?eyye?baka yarda ni ce ɗiyar ka ba?kana so ka yarda da maganar Calva kenan?kana so ka ce ni ba ƴar ka ba ce"?..
Riƙo hannun ta Sultan yayi yana haɗa gumi kafin daga bisani ya ce
"My princess,ni ba mahaifin ki bane,ba ni na haife ki ba,ke ba ɗiya ta bane,maganar Calva gaskiya ne,sato ki nayi kuma na cinma buri na sai dai bai gama cika ba matsaloli suka saka ni gaba,,my princess...na ƙi yarda in binne mahaifi na dan Aberald ya sanar da ni cewa in har na bar sa a cikin masarautar nan kuma kema kina cikin ta toh duk abin da nake so a duniyar nan zan same shi,wannan dalili ya sa na ɗauke ki a matsayin ɗiyar da na haifa duk da na san wataran,rana irin mai kamar ta yau zata zo,ki yafe ni princess akan abin da na maki na raba ki da iyaten ki na ainihi,amma ba ni na haife ki ba,,kin ga wannan yarinyar...ita ce ɗiya ta dan ga kamannin ta nan da na matata ta,sarauniya Bayarma,princess you have to leave this Empire with your sister before the worst comes"!!!!

Girgiza kai ta hau yi tana faɗin
"No...no father,,i can't leave you,i won't...i will...not...leave you father...you are my only father i don't know them i don't know her she is a terrorist i can't follow her"!!kuka sosai take yi wanda ya saka mutanin fadar tausaya mata dan da wuya mutum ya ji irin wannan abin daga sama sannan ya yarda,sai an ɗau lokaci...
Fianna dake zaune kusa Balik ne ta kalle sa ta ce
"Juda isa a witch,she almost killed him,and her sister is trying to deny her,we need to take her away ot else she will surely create another scene or even destroy her sister"!!gyaɗa kai Balik yayi kafin ya miƙe tsaye ya zo kusa da Juda da nufin yi mata magana amma tayi saurin dakatar da shi dan ta san hala tunani suka yi da ya sa suka yanke hukuncin zuwa su dakatar da ita,sai dai ta san ba zata bari hakan ya faru ba sai ta gama abin da ya kawo ta..
Wuce Balik tayi ta ɗau jakar ta ta buɗe ta ciro kundin ta dawo ta hau kan matakalar ƙarshe na kujerar mulkin Sultan ta ja ta tsaya ta ɗaga murya tana magana
"Ina buƙatar hankulan ku a tare da ni har da kai kan ka Sultan Baal-Hamon"!!da zafin rai tayi maganar wanda ya saka Sultan Baal-Hamon ɗaga idanun sa ya sauke su a kan ta..
Cikin fushi take faɗin
"All our lives were lost and ended or destroyed because of this,,because of this stupid prophecy,,,i killed alot of people because of this stupid prophecy,so many people were killed because of this stupid prophecy,so many atrocities and believes were committed all because of this stupid prophecy,bloodlines were destroyed all because of this stupid prophecy,illusions,delusions,hallucinations and obsessions occurred all because of this,this stupid prophecy,challenges and lost occurred all because of this stupid prophecy isn't it?all the kings are after this stupid prophecy,they wanna make stories that has never been told,they wanna be fame and rulers who will rule the world right?the are ever ready to cross their limitations just to get what they want,,fine,i..am..the owner of this stupid prophecy,it was handed over to me by my own mother who inherited it from my grandfather and he,inherited it from our ancestors,today,,in front of you,i want to bring an end to all these calamities,i want to vanish this believes and atrocities amongst people,,from today hence,you all have to believe that there is only one God,and that is the God that is capable enough to handle this whole world it is that only God who can do and undo,it is that same God who have the total control of our lives and not some cheap and unworthy creature called man,that God is called _*ALLAH*_,he is the only one who is worthy of worship"..
Dakatawa tayi ta hau buɗe kundin tana yayyaga su cikin fushi da baƙin ciki tana magana
"A yau na kawo ƙarshen wannan jaraba da bala'i dake addabar mu take addabar al'umar mu take janyo mana rigima da masifa a yau na kawo ƙarshen sa kuma an share tarihin sa a duniya,i was out for a battle,a _Battle to reach_ and the battle just ended because i have seen the reason why i left my home"!!haka tayi fata fata da kundin nan ta watsa shi sannan ta sauko ƙasa tana tafe tana kallon gimbiya Acenath dake tsugune tana kallon Juda,wani irin mutuwar tsaye ɗumbin jama'ar wurin suka yi suna kallon Juda da ta gama raga raga da zancen kundin da ake haukacewa kan sa...
Da zuwar ta bata tsaya jin komai ba ta saka hannu ta ɗago gimbiya Acenath dake kukan cin rai tana ta fincikewa akan Juda ta rabu da ita amma sam haka ta ƙi ta cigaba da jan ta...
Da ta ga kamar zata mata gardama sai kawai ta ɗauke ta da wani razanannen mari da sai da ya saka gimbiya Acenath daskarewa a tsaye ta natsu tana kallon mutani a yayin da Juda ke jan ta..
Kallon su mutani suka rinƙa yi suna mamakin abin da Juda ta yi sai dai babu wanda ya iya cewa komai..
Tana zuwa daidai inda abokan tafiyar ta suke,ta ja ta tsaya ta ce da su su zo su tafi..
Haka suka tashi suka fita suka bar masarautar ana so su tsaya a ƙarasa abin dake faruwa amma ko ta kan su basu bi ba haka suka shige motar da suka taho da shi suka yi gaba leaving the palace in dispute...

A haka aka rinƙa fallashe fallashe ana kwasar rahoto ana ɗaukar hotuna ana kwasar video,ba a gama aiwatar da wannan judgment ba har sai cikin dare a inda zuwa lokacin kuma kowa yayi Allah wadai da halayyar Sultan Baal-Hamon wanda ya kawo ma mutani naƙasu a sannu ba tare da sun sani ba..
Zuwa dare kuwa bayan dogon ƙananun kace na ce da aka yi aka rinƙa barin masarautar nan ɗaya bayan ɗaya,zuwa cikin dare masarautar kaf ya share kamara ba a taɓa dasa rayuka a cikin masarautar nan ba,haka ya dawo shiru kamar maƙabarta hatta da Dacey dake iƙirarin in ba Sultan bazata iya cigaba da rayuwa ba,toh ita kan ta haka ta lallaɓa ta bar gidan dan ta san Sultan kam ba amfanuwa zai yi ba haka ma Calva ta bar masarautar Ottoman tana mai jin farinciki cikin ran ta na ganin ta cika burin ta haka ta kama hanya ta bar yankin,..
Ɗiyar Sultan Baal-Hamon kuwa haka ta zamo wata baƙuwa cikin masarautar tana kalle kalle ga sarauniya Bayarma da ta ƙulle kan ta cikin ɗakin ta tana ta rusa kuka tana kewar gimbiya Acenath da ta raina da hannun ta tun tana jaririyar ta har girmar ta yau kawai a ce an raba ta da ita,abin da ciwo....
Sashen Sultan da masu bin sa na ainihi wanda suke ganin kamar zai farka kuma ya dawo masu da farincikin su da suka rasa a yau..
A washegarin safiyar ne aka wayi gari aka tarar da gawar Sultan Baal-Hamon wanda sai da ɗumbin al'umar masarautar nan suka tabbatar rai ba a bakin komai yake ba haka kuma in mai iko da ran ya so,yana iya ƙwace sa a sadda ya ga dama...
Haka aminin sa sarki Malik ya taho masarautar nan aka samu aka ma Sultan Baal-Hamon wanka aka mai addu'ar dacewa sannan aka dangana sa da gidan sa na gaskiya dan dama yarima Ziyan tare suka kwana da aminin sa Irad inda suka rinƙa tunanin ta yadda zasu ɓullowa lamarin a sauran masarautu ukun da suka rage,,..
Su da ƴan jaridun su ne suka kwashi komai dangane da jana'izar Sultan Baal-Hamon wanda tun a ranar sauran mabiyan Sultan Baal-Hamon suka rinƙa fita suna barin masarautar Ottoman a ƙarshe dai zuwa yamma fadar ta kuma dawowa wani iri kamar ba'a taɓa dasa tarihin wani sarki mai suna Sultan Baal-Hamon ba...
A washegari su yarima Ziyan suka bar ƙasar Ottoman suka nufi hanyar Mughal Empire dan nunawa sarauniya Zinaida ishara dan an san labari bai isa gare ta ba...

★★★
A motar da su Juda suka shiga tare da gimbiya Acenath kuma abin ba'a cewa komai dan hauka muraran gimbiya Acenath ta rinƙa yi masu sai da ya kai ya kawo Juda ta kuma sauke mata wani marin da ya birkita mata lissafi kana ta natsu tana ta kukar zuciya mai ban tausayi da taɓa zuciyar mai sauraro..
Su kan su sun so komawa Mughal Empire amma haka Berenice da ɗan uwan ta Habilah Balik Habaccus suka nuna sam basu son wani abin da kuma haɗa su da wannan ƙasa sai dai haka dan dole Cahal ya nuna masu dacewar komawar su dan gimbiya Ondrea ta gana da mahaifiyar ta ko zata sami sukuni a ran ta,a haka suka yarda bayan sun raba dare sun huta washegari suka kama hanya suka nufi masarautar Mughal amma fah tun a daren har wayewar gari haka suka yi sa gimbiya Acenath na kukan zuci,tun Callee na rarrashin ta har ta rabu da ita dan kaf ta zauna tana ta labarta mata tarihin su akan su ɗin zuri'a daya ne kuma in ta koma gida haka za a karɓe ta da hannu bibbiyu amma haka ta toshe kunnuwar ta ita ita sam ba zata yarda ba,abin da ya harzuƙa Callee kenan ta fita harkar gimbiya Acenath..
Dama Juda bata saurare ta ba tun jiyan burin ta kawai ta ga sun koma gida dan a yi duk abin da za a yi..

A washegarin suka nufi hanyar masarautar Mughal ta sarauniya Zinaida inda suka yi kusan zuwa tare da su yarima Ziyan Aman dan da awowi suka riga su yarima Ziyan..
Toh a nan fadar sarauniya Zinaida abin ya so ya sha bamban dan cewa ta rinƙa yi ai akwai _Bambancin ƙasa_ tsakanin ta da Sultan..
Dama so take ya mutu kuma ya mutu dan haka su bar mata ƴar ta su rabu da ita amma haka ƙememe gimbiya Acenath ta ce sam ita ba zata taba zama a masarautar nan ba..
Wannan abin ya daure masu kai ganin da gaske sarauniya Zinaida bata shirya sauka ba,abin haushin ma shine yadda ta dage akan bata yarda da auren Cahal da gimbiya Ondrea ba ita dole sace mata ɗiya aka yi kuma an mata fyaɗe,abun ya ƙanƙama har sai da agent ɗin investigation committee na nan wurin ya zo ya shiga lamarin wato prosecutor Khabeer Ateeq..
Kaca kaca aka ma sarauniya Zinaida a masarautar ta tun tana gudun bayar da wuya har ta shiga hankalin ta amma still tana da burin son mallakar duniya,a ranar ne ana tsaka da wannan rigimar naƙuda ta kama gimbiya Ondrea..
Wannan dalili ya janyo hankulan su inda naƙudar ta fi ƙarfin gimbiya Ondrea mijin ta Cahal ya rasa abin yi hankalin sa a tashe tun yana iya ɓoyewa har abin ya girme mai ya rinƙa sharar hawaye har dai Agneta ta kasa cigaba da kallon sa a hakan dan bayan mugunta irin ta sarauniya Zinaida har da zalunci cikin al'amarin ta tana ganin ɗiyar ta cikin matsala amma haka ta dage akan wannan naƙudar tsinuwa ce a gare ta sam ba zata yarda gimbiya Ondrea ta haife ɗan ba..
Wannan abu ya ba mutani mamaki da tsoro ganin har nata da ta haifa tana nuna mata mugun hali toh ina ga sauran mutani..
A ƙalla awanni da dama gimbiya Ondrea ta ɗauka tana naƙuda wanda a ƙarshe tayi nasarar haifar ɗiyar ta mace sai dai farinciki ne ya koma ciki dan bayan haihuwar da wasu mintuna,Allah ya karɓi ran gimbiya Ondrea..
Actually it was a painful lost dan bata ji ba haka bata gani ba laifin mahaifiyar ta ya shafe ta tsinuwa da bakin jama'a ya bi ta..
A fannin mijin ta kuwa,ba a cewa komai dan yayi kuka kamar ba zai daina ba shi da bai ma tsaya cewa sai ya ɗau fansar hallaka masa iyaye da Sultan yayi ba yana ganin kamar matar sa ta ishe sa yin rayuwa ashe ba haka bane,yau ta tafi ta bar sa...
Da ƙyar ya rage sarauniya Zinaida bata yi hauka ba dan ma wasu cewa suka yi ai ta haukace duba da irin ɗabi'un ta da take yi tun da ta ji mutuwar ɗiyar tata...
Sama da sati ɗaya kenan sarauniya Zinaida bata dawo daidai ba su dai sauran sun bar masarautar kuma burin Juda shine ta koma gida,tun gimbiya Acenath na jan jiki da su har ta fara amsa masau magana in sun yi duk da ba ko da yaushe ba amma hakan ya fi zaman shirun da take yi...

★★★★
Tafiya suka shirya dan komawa gida yayin da aka bar Berenice da ɗan uwan ta Habilah Balik a nan Mughal dan ganin sun yaɗa addini da wayar da kai,duk da Fianna ta so bin su Juda amma haka ta danne zuciyar ta akan sam ba zata bi su ba ta nuna masu zata zauna a nan ɗin tare da su Berenice dan su yaɗa addinin,babu wanda ya kawo komai ran sa haka aka bar su..
Juda,Agneta,Callee Cahal da gimbiya Acenath suka ɗau hanyar tafiya duk da Cahal ya so ya koma can Turkey dan cigaba da rayuwar sa dan sun sallami ƴan rahoton da suka dauko,shawar Juda ta bashi akan ya biyo su dan ta nunawa mahaifiyar ta shi a matsayin wanda ya tsaya masu akan al'amarin har kawo yanzu tunda dama ita ke kular mai da ƴar tasa dan bai yarda ya bar ƴar a masarautar Mughal ba...

★★★
After some times masu bincike a yankin Tanzania da Nigeria suka bazama binciko yankunan dake fama da duhun kai,kuma sun sami yankunan and sun shirya gyara sa sosai,again sai da suka binciko tarihin warriors na ƙasashe biyun nan dan su saka su cikin sabon kundin tarihin da zasu fara rubutawa na zamani ba kamar na cikin kundin Juda da ta yayyaga ba...

A yau ne kuma zasu koma zuwa Babylon dan jin ta bakin sarauniyar mayaƙa wato Juda dan kafa tarihi marar saurin mantuwa,kuma shi kan sa yarima Ziyan ya shirya karɓar auren gimbiya Acenath tunda ya san bata da wata alaƙa da Sultan Baal-Hamon kuma a yanzu shi kan sa ya ji yana son ta dan haka ya ma abokan tafiyar sa magana da su shirya zuwa ajiyayyen ranar da suka saka dan su kai ziyara ga Babylon sannan su nemi auren gimbiya Acenath dan da auren nata yarima Ziyan yake so su koma ƙasar Nigeria dan ya natsu ya rubuta kundin tarihin da zai rubuta in hali ya bayar ma ya binciki wasu tarihin duk da mahaifin sa ya so ya ɗan dakata amma ya ce a'a shi so yake ya aure ta dan yana tuno yadda aka raba ta

Please Login or Register in order to submit comment