Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yake nuna iya idanun ta da girar ta haɗe da shatin tsinin hancin ta..
  Hatta da takobin ta daban ne ba irin waɗanda ta saba riƙewa bane shi yasa da ta nufo su kowa sai ya miƙe a shirye za'a kawo mata hari  sai ita abin ma ya bata dariya dan haka tayi saurin ɗaga masu hannu tana faɗin
  "Ni ce fah baku gane ni bane"?sai a sannan Berenice ta gano ta ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce
  "Juda ce fah ba wata ba"!sai a sannan suka maida makaman yaƙin nasu suka nufo ta cikin mamaki suna faɗin
  "Lafiya kika sauya shigar ki ina kika samo waannan kayan"!?ɗan ɗage gira ɗaya tayi sama tana faɗin
  "Sato su nayi"sai suka dara gabaɗayan su kafin ta ɗan gutsira masu labarin kayan kaɗan sannan ta ce da su
  "Mu tafi ko dan na ɓata maku lokaci kuma duk ni na fi kowa zaƙuwar shiga masarautar nan"ɗan murmushi suka yi kafin Agneta ta ce
  "Amma da na so baku wata labari da ban sani ba ko zata amfane mu kafin mu shiga masarautar nan,sai dai na ga kamar a hanzarce kuke duk cikin hanzari kuke"da sauri Juda tace
  "Ba matsala faɗa muna sauraron ki in har kin san zai kawo mana mafita mai kyau"!!zama suka yi a gefe suka maido hankalin su ga Agneta da ta fara magana kamar haka
  _"A masarautar sarki Malik akwai wata addini da suke yi wanda ya kasance a ɓoye suke yin ta dan kuwa sarkin Ottoman ɗin nan wato sarki Sultan Baal-Hamon a bai san ana yin ta ba sakamakon dokar da ya saka ya kuma kafa akan babu wanda ya isa yayi wannan bautar da ake gudanarwa cikin addinin,toh mutum na fari da ya bijirewa wannan doka tasa shine yarima Ziyan,wanda ya kasance ɗa ɗaya tilo ga sarki Malik kuma yarima mai jiran gado,dalilin gano wannan addinin da yake gudanarwa a ɓoye kuwa shine,yana karatu ne a wata ƙasa karatun da shi sarki Sultan Baal-Hamon ya haramta dai wato karatun zamani dan ya ce bai yarda da wannan karatu ba shi yasa wannan yarima ya bar ƙasar baki ɗaya yayi tafiyar sa wata ƙasar daban yana gudanar da rayuwar sa haɗe da addinin da sarki Sultan Baal-Hamon ya haramta ba tare da sanin sarki Sultan ba"_
  _"Sai daga baya da yarima Ziyan ya dawo gida kasancewar ya ɗau shekaru tara baya gidan haka baya ƙasar sai aka haɗa mai shagulgula na tarbar sa,toh a ƙa'idar wannan masarauta akan hole da mata duk lokacin da sha'ani ya taso sai aka tara mai mata masu kyawun diri da kyawun fuska amma sai ya ba mahaifin sa sarki mamaki dan bai ma halarci shagalin ba sai ma bayan an gama jiran sa ya zo ya fara faɗar kowa ya fita yayi tafiyar sa baya buƙatar wannan haramtacciyar shagali,wannan abin ya ɗaga hankalin sarki Malik ganin ɗan sa na son ɓallo mai liƙin da ya daɗe yana liƙewa wato rashin yaɗuwar wannan addini a ƙasar sa dan saɓo ne ga sarku Sultan Baal-Hamon"_
  _"Ko da ya tuntuɓi ɗan sa da batun sai yarima Ziyan ya amsa mai da shi fah kan sa ya waye kuma ilimi ne cike a kan sa dan haka ya tara ilimi sama da biyu a kan sa ga na masarautar da ya taso ciki wato na jahilci ga na zamani da ya samo sannan ga na addini da ya samo dan haka baya buƙatar komai daga wannan masarautar a cewar sa abu ɗaya zai faru cikin biyu ko mahaifin sa sarki da mutanin sa symu karɓi addinin da ya taho da shi su tsira tare ko kuma ya bar masarautar kuma ba ƙara dawowa zai yi ba sannan sai ya fallasawa duniya jahilci da duhun kan da masarautu ukun nan ke dulmiye ciki wato masarautar su ta Oman da ta Ottoman da kuma ta Jordan"_
  _"Wannan abin ya ɗaga hankalin sarki Malik ganin zai fah iya rasa ɗan sa tilo gashi matar sa sarauniya har ta amince da ɗan ta akan ita zata karɓi ilimin da ya zo da shi dan ba zata yarda ta rasa sa ba sai kawai sarki Malik ya amince amma da sharaɗin a ɓoye za'a na gudanar da wannan addini ni ko Islam naji suna faɗi  ko Islamic i can't recall but something related to that wor.toh tun lokacin ake gudanar da wannan addini a ɓoye sai dai bayan komawar yarima Ziyan aka yi fatali da wannan addini kowa ya koma yin abin da ya mai daɗi amma na zamani da yarima Ziyan ya saka a masarautar ana kan koyar da shi dan har na baro masarautar nan ana kan koyar da su sai dai ban sani ba ko an cigaba yanzu ko an daina but na ji sarki Malik na faɗin da wannan dabara zai ƙwace kundin da sarki Sultan Baal-Hamon a ke kaiwa hari toh ni dai bayan sihirin da yake yi ban san ta yaya zai yi amfani da wannan ilimin addinin ba wurin ƙwace kundin nan shi yasa da na ga har mun tunkari masarautar na ce zan sanar da ku ƙila ku san wata hanya da mu ma zamu iya bi dan dai mu sami damar fiddo ƙanwar ki cikin sauƙi amma me kuka gani"!?dukkan su murmushi suka yi sai Juda kaɗai da ta shiga wani yanayi sakamakon jin abin da bata taɓa yin karo da shi ba cikin karatun ta da take yi a kundin ta amma yana iya yiwuwa da gaske addini irin wanda Agneta ta faɗi na nan a doron ƙasar"_

"Kika ce sunan addinin islam"?tayi tambayar tana mai kallo Agneta,amsa ta bata ta hanyar ɗaga mata kai alamar eh sai Juda ta jinjina kai ta barwa kan ta sirrin da ta ji a shekarun baya.
Berenice ce tayi caraf ta cafe zancen ta hanyar faɗin
"Nima dai kamar na so jin sunan wannan addini sai dai ban saka kai na ba dan baya gaba na"!!dukkan su jinjina kai suka yi daga haka sai Juda ta masu magana tana miƙewa tsaye
"Mu tafi bamu da lokaci,amma ina waɗannan mutanin na jiya"?sai Agneta ta amsa mata da
"Sun tafi ai tun ɗazu da safe"a nan dai ta mayar mata da saƙon da aka bar mata sai abin ya ɗan taɓa Juda kaɗan sai dai bata ce ƙala ba daga haka dai suka ɗau hanyar su ta zuwa masarautar Ottoman..

★★★★★
Tafiya tayi tafiya sun kusa kawo bakin masarautar nan dan suna hango hasken ƙwayayen da ya haskaka masarautar ya fito da kyawun sa na masarautar da ba'a taɓa samin kamar sa ko makamancin sa ba tun a baya,tun daga nesan suke hango masu tsaro manya manyan majiya ƙarfi ne da su kamar mazan da aka yi zamanin farkon ƙarni da su..
Babu wanda bai jinjina ma wannan masarauta ba cikin su sai dai ba ta yaba kyawun sa suke ba abin da ya kawo su suke son aiwatarwa ba tare da an sami akasi ko mishkila ba..
Tun da suka doshi masarautar suka fara jin wani irin mugun gilmawar abu mai raɗaɗi na shigar su tun suna iya resisting har abin ya faskara ya girmewa tunanin su dan haka suka kasa jurewa dole suka ja da baya wanda yayi daidai da jin saukar takubba biyu a wuyoyin su ɗaya takobin a wuyar Juda yayi landing ɗayan kuma a wuyar Balik dan suna a ƙarshe ita Juda a ƙarshen dama Balik kuma a ƙarshen hagu yayin da Agneta da Berenice ke tsakiyar su..
Ɗago kawunan su suka yi suka ga fuskokin mutani biyun nan duk a rufe take kuma daga ganin su ka ga siffar mata dan komai ya nuna sai dai abin ɗaurewar kan a nan shine su ɗin waye su..
Kallon kallo suka yi exchanging ma junan su a tsakanin su kafin su juyo su kalli waɗannan mutani biyun kafin a ce me har sun juya takubban ya koma kan masu takobin....


*_IS SIYAMAIBRAHIM_*
[3/29, 08:59] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:39&40*

"Waye ku kuma wa ya saka ku biyo mu a baya har inda muka zo"?tambayar da Agneta ta aikowa ɗaya daga cikin matan nan kenan wacce sanadiyar faɗuwar su ƙasa mayanin fuskar ta ya ɗaga..
  Kasa bata amsa suka yi sai suka yunƙura suka taso a take faɗa ya kaure wurin sai dambe ake ta yi wanda ya saka su yada makaman yaƙin ma gabaɗaya suka shiga yi da hannuwan su da jikin su,faɗa sosai suka yi kasamcewar four against two ne sai suka rinjayi mata biyun suka yi faɗa da su sosai sai da abin ya kai masu yadda suke so sannan suka tsagaita ba dan an kai matakin tsagaitawar ba..

  Cikin zafin nama Juda ta tambaye su babu alamar wasa ko shirme cikin batun ta
"Mun san juna yanzu kuma alamu sun nuna min da manufa kuka dumfari masarautar nan dan haka muna sauraron ku ku yj gaggawar fallasa dalilin ku tun kafin rai na bai ɓaci ba in kasa dakatar da kai na daga aiwatar da abin da zuciya ta ke kwaɗaiyin aikatawa"duk sun gaji tsabar ɗaukar abin da suka yi da zafi da yadda suka ci da zuci wun yaƙin.
  Kamar dai ba zasu furta kai ba sai daga baya suka amsa maganar wacce ɗaya daga cikin su ne ta bada amsar kamar haka
  _"Ni sunana Callee kamar yadda kuka gan mu mu biyu ne tare da abokiyar tafiya ta kuma ba wani abin ya kawo mu nan ba sai son cikar burikan mu biyu wanda muka gano muna buƙatar wani littafi kafin komai ya wakana,ko da muka taho nan bamu da masaniya akan komai amma mun san ba zamu koma gida haka ba sai da wannan abin da muka fito nema"_.
Kallon ta suka yi sai suka kuma kallon ɗayar haɗe da yi mata alamar ke kuma fah dan haka itama ta gabatar da kan ta
_"Sunana Fianna kuma aiko ni aka yi sakamakon kasa aiwatar da aikin da sarkin ƙasa ta ya sa ayi aka dawo mai da sakamako mararar gamsarwa dan haka aka buƙace ni da in cika wannan ragowar aikin kuma kamar yadda abokiyar tafiya ta ta faɗi,a hanya muka haɗu kuma bamu taɓa mafarkin zamu haɗu da ku ba hasalima abin da ya kawo mu nan muka zo aiwatarwa sai dai hakan bai samu ba,yau kimanin kwanakin mu huɗu kenan muna zuwa da komawa akan rashin nasarar da muke samu dan a duk lokacin da muka zo nan masarautar haka muke komawa babu nasara sakamakon mugun baƙin dafin asirin da mamallakin masarautar ya sa aka mai wanda in ba ƴan cikin masarautar bane toh babu mai shiga cikin dare wannan dalili ya sa muka daidaici lokacin da muka ga zuwan ku a tunanin mu ku ɗin ƴan cikin gidan ne dan muyi amfani da ku wurin shiga gidan sai dai muka ga akasin haka kuma da kuka gan mu muka yaƙe ku dan kar ku shaida mu amma bamu san abin zai zamo haka ba"_.
Kallon mamaki suka bi ta da shi kenan in nutshell suma dai mayaƙa ne kamar su sai dai kowa da abin da ya fitar da shi daga masarautar sa..
  Wani idea ne ya zo wa Berenice akan me zai hana su masu wayo exactly yadda suka wa Agneta a haɗuwar su ta fari in ya so bayan sun yi nasarar fiddo ƙanwae Juda sai su rabu da su ita a nata ganin hakan zai yi sosai..  
  Kafin wata ta furta wani abu cikin su Judan sai Berenice tayi karaf ta riƙo hannun Juda ta fara jan ta wanda abim ya zo mata cikin shammaci..
  Sai da auka yi ɗan nesa da su sannan ta rage muryar ta ƙasa ta fara magana
  "Juda ni gani nake kamar mutanin nan biyu Callee da Fianna wannan kundin suka fito nema kuma ko basu sanar da mu ƙasar su ba na san abin da ya kawo su kenan dan haka ni a tunani na me zai hana mu janyo su jiki tun kafin su gano cewa kundin nan na tare da mu su yaƙe mu ba tare da mun ribatu da komai ba mu nuna masu cewa muma abu ne ya fiddo mu daga ƙasashen mu daban daban kuma muna son komawa gida cikin farinciki da jin daɗi dan haka su haɗa hannu da mu mu taimaki junan mu dan samin komai cikin sauƙi kamar dai yadda muka wa Agneta a haɗuwar mu ta fari da ita,ya kika gani ke a naki tunanin"?tambayar tayi tana kallon idanun Juda dake rufe cikin mask ɗin nan..
  Sosai Juda tayi na'am da shawarar Berenice ko ba komai Berenice ta koyi dabarar ta dan haka sai kawai ta rungune Berenice tana ɗan bubbuga bayan ta tana faɗin
  "Kin kawo shawarar da na kasa kawowa kuma kin birge ni ba kaɗan ba  kuma hakan za'a yi amma Balik kaɗai za'a yi revealing ma sirrin banda Agneta ko"?da sigar zolaya tayi tambayar wanda ya saka Berenice darawa kaɗan dan ta san zolayar ta Juda ke yi..
  "Oh come on ai mun zamo ɗaya mu da Agneta komai ma ana iya sako ta ciki"!murmushi suka yi sannan suka koma can inda suka baro su Agneta da Balik haɗe da sauran mata biyun..
  Balik Berenice ta jawo yayin da Juda ta ja Agneta gefe suka mayar masu da shirin da suka yi dan ƙaruwa da su Callee da Fianna..
  Duk sun yi na'am da tsarin sai dai shakkar su kar su gano gaskiya su zo su guje su sai dai Juda da Berenice sun yi ƙoƙarin fahimtar da su..
Komawa suka yi Balik ya jagoranci zance ta hanyar yi masu bayanin abin dake tafe da su dan haɗa hannu su sami abin da suke so..
  Bayani sosai Balik ya ɗau lokaci yana masu amma sai da suka so janyewa kafin su yarda akan zasu haɗa kai da su.
  "Sharaɗin mu kar abin nan ya tafi ba bisa tsarin da kuka zo da shi ba dan in hakan ya faru toh ba zamu maku ƙarya ba sai mun raba ku da kawunan ku wannan ajiyayyen zance ne kun yarda"!!gyaɗa kai suka yi kafin duk su koma gefe dan sanin abin yi..
  Agneta ce ta fara magana dangane da shirin da ya kamata su fara yi akan tunkarar wannan masarauta
  "Ni a gani na me zai hana mu samo wanda ya san kan sihiri a cikin garin nan wanda zai iya bamu sirrin sihirin masarautar nan dan dai ba za'a ce babu wanda ya san sirrin masarautar nan ba dangane da irin tsaface sa da aka yi ba sai dai in bamu nema ba, dan haka ni a nawa tunanin kafin mu samowa kan mu mafita game da sihirin da aka wa masarautar nan dole sai mun samo wanda ya ƙware a fannin sihiri dan ya taimaka mana in ba haka ba bana jin abin nan zai mana sauƙi ya kuka gani"?ta juyo tana kallon su ɗaya bayan ɗaya sai Fianna ta karɓe zancen da
  "Ni tun kafin in zo sarkin da ya aiko ni ya shaida min cewa an tsaface masarautar kuma da mugun tsafi dan haka zai ba ni sirrin warware tsafin amma in tabbatar ni kaɗai nayi amfani da wannan sirrin dan in ba haka nayi ba toh lallai shirin mu da shi zai lalace toh ni dai ina da sirri ɗaya da zan iya shigar masarautar nan da shi sai dai ban sani ba ko zamu iya amfani da wata hanyar dan ganin dukkan mu mun shiga".
  Girgiza kai Juda tayi dan ta gama nazarin zantukar su kaf kuma ta gano kamar shawarar Agneta ne yafi dacewa da halin da suke ciki yanzu da haka dan  haka sai ta ɗan rage murya tana faɗin
  "Shawarar Agneta ya fi dacewa da yanayin nan da muke ciki dan samo mafi sanin kan sihiri shine zai kawo mana sauƙin lamarin nan amma me kuka gani"?amsa Balik ya bayar da
  "Eh mun amince sai dai shawarar Fianna ma na kan hanya me zai hana in mun samo mai sanin sirrin sihirin daga baya mu ɗabbaƙa shawarar Fianna duk da ma ita kaɗai ce ke da ikon amfana da sirrin amma dole za'a sami hanyar da zamu iya amfana da shi".jinjina kai suka yi baki ɗayan su cikin amincewa da shawarar ta Balik a ƙarshe dai sun yanke shawarar komawa masaukin su Juda na jiya dan su yada zango har zuwa washegari in yaso sai su bazama cikin gari dan nemar masanin wannan sihirin.

★★★★
A wun kwanciya kuwa Fianna da Callee duk a waje suka kwanta sai da Balik ya ga kamar bai kamata a nuna masu _Bambanci_ ba sai ya fito ya zo yayi joining nasu suka kwana a wajen bayan daɗa cusa masu son kasancewa tare da su da abokan tafiyar sa sannan ya tabbatar sun yi hira sosai sannan ya bar su suka runtsa su kuma a cikin duk kusan ɗaya ne dan dai tunani ake yi akan hanyar ɓullowa lamarin washegarin..
★★★★★★
  Da safiyar fari suka farka dukkan su haka suka tsara yanayin ranar akan duk dare sai sun binciko wannan mutumin da ya san kan sihirin dan ya taimaka masu duk da sun san abin da kamar wuya kai tsaye a aminta da su a basu haɗin kai amma sun sakawa ran su zasu sami haɗin kan..
  Abu na farko da suka yi shine raba kan su da suka yi suka bazu cikin kasuwar garin dan samo wannan mutumi duk da basu da tabbacin samo sa a sauƙaƙe ko a wahale.
  Yawo suka yi a kasuwar amma basu yi sa'a da samin kowa ba haka suka haƙura suka koma sansanin su..
A ƙalla sun shafe kwanaki biyar masu kyau suna zaga kasuwar garin nan amma basu taɓa katari da wannan mutumin ba haka suka kwashi kwanakin suna zama tare amma babu wanda ya san ya kalar fuskar Juda yake cikin su du biyun wannan kuma wani hikima ce ta Juda dan gani take wataran tana iya gwada amincin su dan tabbatar da eh su ɗin masu amana ne..
  Wani yammaci haka bayan fitar su sun dawo babu nasara still sai abin ya fusata Juda ta kama hanyar rafi ta faɗa ciki tana tsaye wuri ɗaya kuma ba komai take yi ba face kuka dan ƙunci da takaicin abin dake faruwa da su gani take kamar ba zata sami cigaba cikin wannan buri nata ba dan alamu sun nuna ta ko ina babu nasara a tafiyar ta..
Ju ta rinƙa yi kamar ta ja baya akan wannan ƙudiri nata kawai ta koma gida ko kuma ta natsu ta karance kundin nan tsaf dan gano sirrikan sihirin nan da aka saka aka lulluɓe masarautar Ottoman ɗin nan da shi..
  Kwata kwata bata jin daɗin jikin ta dan haka ta cigaba da zaman cikin ruwan tana ɗan watso ruwan a fuskar ta.
  Can kamar ta tuno wani abin ta fara fitowa daga cikin ruwar tana ɗan dakatawa kaɗan kaɗan kafin ta fito baki ɗaya ta zauna a gefe ta ɗau jakar ta ta buɗe.
  Ciro kundin tayi ta ajiye a gaban ta ta fara buɗo shafukan baya da ta karanta ta saka a gaba tana bi da idanun ta,ƙura ido tayi akan wata tambari da aka yi a shafin wanda a baya in tana karatun bata cika maida hankalin ta akan sa ba.
  Cikin sauri ta buɗe shafi na gaba nan ma ta ga irin tambarin sai ta kuma buɗo wani shafin still ta gani,abin sai ya bata mamaki dan haka ta cigaba da buɗe shafukan tana duba tambarin duk kundin na ɗauke da wannan tambari alamar wani abu ne a wurin..
  Komawa tayi shafin farko ta kai hannun ta kan tambarin ta shafa sai ta ga kamar abu ya gilma daga cikin kundin sai ta kuma kai hannun ta saman tambarin sai ta kuma ganin haske fiye da na da dan haka sai ta natsu tayi nazari hala wannan shine dalilin da ya sa sarakan nan ke harin wannan kundin tunda dai ita ba gama sanin sa tayi ba zai mata wuya ta tantance ma'anar wannan hasken sannan ba zata san ya ake amfani da sihirin ba..
  Sai dai dole ta saka kai ta koya dan gani take zata iya ko babu taimakon mutumin da suke wahal da kan su akai dan yanzu take samin ƙwarin gwiwar komai fiye da ɗazu da abin ya zamo mata a rufe duk ta rasa madafa..
Da murnar ta ta ƙarasa inda ta bar su tun safe sakamakon ɓacin ran da ta riski kan ta ciki ɗazu..
Babu wanda bai yi mamakin ganin ta cikin wannan halin ta farin cikin dan rabon da a gan ta tana walwala har sun manta.
Jawo Berenice tayi gefe tana mai cire face mask ɗin ta sai ta rage murya ƙasa tana magana
"Berenice kin san me na samo"?saurin girgiza mata kai Berenice tayi sai ta ce
"Na samo mana mafita sai dai matsalar shine ban san ya zan juyar da wannan mafitar zuwa dai dai abin da muke nema ba",saurin tambayar ta Berenice tayi
"Amma me yasa kika ce haka kuma a ina kika samo mafitar"?riƙo hannun ta tayi tana yin ƙasa da murya ta ce
"Cikin kundin nan,cikin kundin nan na samo sa,kuma yanzu na gano sirrikan da yake ciki kuma na gano dalilin da ya sa ake kawowa wannan kundin hari daga ƙasashe daban daban sai dai ko da na gano sirrin ban san ya zan amfana da shi ba kuma kin san me"?girgiza kai Berenice tayi sai Juda ta ɗora
"Ban yarda da Fianna ba"!?da mamaki Berenice ta ce
"Ban fahimce ki ba kamar ya baki yarda da Fianna ba"?sai Juda ta gyaɗa kai ta ce
"Kin san ta taɓa ce mana sarkin ƙasar su ya bata sirrin wani sihiri da zata yi amfani da shi ita kaɗai dan shiga masarautar Ottoman"?sai ta gyaɗa kai sai ta cigaba
"Toh ƙarya take yi kuma yanzu zaki gani kawai ki tsaya ki min wani taimako"!cike da alhini Berenice ta ce
"Meye wannan kuma"?sai Juda ta rage murya ƙasa ta ce
"Faɗa zamu yi da ke sosai har mu ƙarasa gare su"!ja da baya Berenice tayi tana girgiza kai alamun ba zata yi ba
"Dakata Berenice,ni fah mafita nake nema mana dan na san yaran nan Fianna da Callee ba gaskiya suke faɗi ba kuma yau zaku gani dan har yanzu basu yarda da mu ba kawai duk abin da maƙiya kewa mai harin su zamu yi kin fahimta"?gyaɗa kai kawai Berenice tayi tana mamakin hauka irin na Juda mutum da kan sa ya janyowa kan sa yaƙi bata taɓa gani ba sai akan Juda..

★★
Can bayan wasu lokuta su Agneta basu ga dawowar su Berenice ba sai kawai suka yanke hukuncin nemo su.
Tashin Agneta kenan da nufin dumfarar inda ta ga sun shige sai kawai ta ji ƙarar takubba da numfarfashin mutani.
Tuni tayi masu alama akan su shirya ai kuwa aka shirya aka tsaya jiran masu zuwa ai kuwa ba jimawa sai ga Berenice da Juda sun fito sarari suna faman dambe kamar me sai da suka zo gab da su Agneta suka ƙara ƙaimin yaƙi ai kuwa sauran ma suka rufo suna son taya Berenice..
Ganin haka kuma za'a iya cutar da Juda dan sun fi ta yawa sai Berenice tayi hikima ta hanyar yaye mask ɗin fuskar Juda tana faɗin
"She lied to us,she is not the person we have been thinking she was,she deceived us,this isn't Juda she is a traitor wearing Juda's outfit"maganar ta na ƙarshe tayi sa ne tana ma sauran alama da ido alamar kar su nuna sun gane Juda dan haka sai suka ɗago

Please Login or Register in order to submit comment