Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karo sun taso cikin bacci sun fito daga dakinsu sakamakon ihun dasuka ji na mace, atare sukace "Ya Marwan wacece tai ihu" alamu yamusu da surabu dashi kawai ya sauka downstairs ya kwanta akan dogon kujera zuciyar shi na wani irin tafarfasa, da sauri Omari da Abdallah sukai dakinshi ahankali suka bude kofan batare dasun shiga ba, kara ware ido Abdallah yayi yana kallon wicked Nurse dan bazai taba mance fuskarta ba yanda ta takure a kwance ta kankame jikinta tana kuka sosai idanunta a rufe tana pisipispisspis da baki basujin metake cewa, fuskarta da gefen bakinta yay jajir, da sauri Omari ya rufo kofan daga shi har Abdallah suka juyo zuciyarsu namusu wani irin zafi suka sauko kasa akanshi suka tsaya atare sukace "meya sameta?" tashi yayi ahankali ya zauna yana dafe kanshi kafin ahankali ya finciko Omari ya zaunar dashi gefenshi ya finciko Abdallah ma ya zaunar dashi gefenshi, kaman wani wanda ya bugu yace "wa..waya ce yataba ta? How dare he try to molest her? Wlh wlh every single pain that she's going through now saina rama mata double" yay shiru tareda daura hannunshi akanshi sai kuma ya janye ya mike tsaye wani irin ball yay da center table din palon na glass jikake rugugugu, wani irin ihu yayi ya daki kujeran one sitter da kafa da sauri Omari yatashi ya rikeshi yace "calm down Ya Marwan, calm down please" fizge kanshi yayi yay wani irin ihu. "leave me Omar" sai kuma yahau kan stair case da gudu, binshi sukayi bude kofar dakin yayi azuciye yana magana yace "who was dat man?" gani yayi tayi bacci atakure hakan yasa duk suka tsaya suna kallonta, ahankali Abdallah ya shiga dakin yaja bargo ya lullubeta ganin yanda ta takure kaman maijin sanyi, sai ajiyan zuciyan kuka take uhhu'uhm take, tsayawa yayi ya kafe fuskarta da kallo yanda yay luhu luhu wani irin kuka ne yazo mishi hakan yasa yajuya da sauri zai fita dakin hanunshi Marwan yarike da sauri ya fada jikinshi ya saki kuka ahankali yana shesheka, "Ya Marwan waya mata haka? Wanan ai zalinci ne, abun namin wani irin ciwo Ya Marwan wlh am not going to spare that man we will not spare him" shafa kanshi Omari yayi shima heart dinshi namai zafi sosai yace "we will not spare him Abdallah, stop crying" daga kai yayi ya kalli Marwan da ya rike Abdallah ne kawai amma kanshi najikin bango yay wani kala, ahankali yace "Ya Marwan calm down please" gyadamai kai yayi kafin yabude kofa yaja Abdallah suka fita Omari na binsu abaya.

*Idan kika karanta baki biyaba keda Allah*!!!



*Maman Abd Shakur*

Da sauri suke tafiya har suka kai gida, wani dan daki dake nan kwara daya gaban part dinsu sukayi bude dakin sukayi suka shiga desktop guda biyu ne akan table da sauri Muhsin ya zagaya ya zauna akan kujeran roban wajen, Ya Ahmad ya zagayo ya tsaya ta bayanshi ya dafashi yana kallon system din, da keyboard ya Muhsin ya dinga operating computer sanu dawo da footage din baya har suka kai daidai inda Nadeera tafito daga barander dakinsu da gudu ya danna play tare da daura yatsunshi akan baki yana kallo kirjinshi na bugawa sosai, aguje tafito tanajan rigan baccin ta kasa tana kuka sosai tana kallon baya tana waigen baya tayo shashinsu, saiga Abba shima yafito aguje gaban rigan shi a mike da sauri Muhsin ya kawad da fuska zuciyarshi kaman ta tarwatse, sake juyo dakai yayi idanunshi sunyi mugun ja daidai takawo kofar dakinsu tanaso ta buga saiga Abba magana Abba yafara hakan yasa Muhsin yay pursing ya danna kara sanan ya komar dashi baya yay playing, Abba yana kawo wurin yace zai tsine mata inta buga kofan, har zai tsine saikuma tazo da sauri yawani jata yasa ajikinshi yana shafa mata baya, da sauri ya Muhsin yasake kawad dakai ya kai hannu ya goge kwallar daya zubomai yasake juyo dakai ya kalla daidai inda tafara tutturjewa Abba naso ya shiga da ita ciki kafin yasaketa yafara gyara hannun riga itakuma ta juya da gudu tana kuka tabude gate tafice Abba ma yabita da gudu saiga gateman yafito ya leko ya rufe gate din da kyau yakoma daki.
Sosai Muhsin ke goge hawayen dake zubo mai yama rasa mai zaice, ahankali ya mike tsaye ya kalli Ahmad da shima jikinshi yay wani irin sanyi kanshi ya kwance baima san mezaiyiba yajuya yafita daga dakin yabar Ahmad kadai a wurin a tsaye, fadawa kan kujeran Ahmad yayi ya wani irin zama kaman wanda akama mutuwa da sauri ya tura hannunshi cikin aljihun jallabiyar shi ya ciro wayarshi cikin kunan rai yay dailing number Mum, ringing uku ta dauka da dan dariya tace "Ahmadudu dont tell me kai mafarkina ne dan nasan yanzu naija kaman uku da hamsin ne ko na dare, ya kake my boy" cikin wani irin kunan rai yace "ki kira mijinki ki tambayeshi ina ya kai mana kanwar mu Mum" da sauri Mum tace "Ahmadudu wat is it? Me haka kake maganan baban ka kaman wani mate dinka, wat is going on?" akufule yace "Mum!" da sauri tace "Naam Ahmad dina menene?" "Nadeera ta bace ki shigo hanya kidawo gidan nan" da sauri Mum ta buga salati tace "innalillahi ta bace, garin yaya? How? Na shiga uku na lalace, Ahmad kun sanar da police? Ina Muhsin? Gashi wlh I have one last meeting to attend yau nai finalizing deal dina da burj al arab in sha Allah next tommorow zan dawo" akufule Ahmad yace "ki mutu achan ma mtsww" ya katse wayar tareda wurgar da wayan akasa ta tarwatse, yay wani ihu, wanan wani irin iyaye Allah ya bashi ne, Uwa business tasani tun suna yara nani ke kula dasu, tun basu sababa harsunzo sun saba ma da rashin ta, Uba kuma yanzu ya dawo dan iska, bama dole ya dawo haka ba, all Mum does is travel, business, business, ko Micheal Zuckerberg bazai nunama matarnan tafiye tafiyen business ba, meeting, meeting kaman itace ta hallici meeting a duniya, wani irin ihu yayi yace "i hate dem" fita yayi ya banko kofar ko takan shashin su baibi ba yawuce masallaci, anan ya zauna oo har akai asuba ana idarwa tareda Ya Muhsin da idanunshi sukai jajir suka dawo gida kaman an musu mutuwa inda ace Abba ba Abba bane ayanda zukeji zasu iya kasheshi, wanan ranan shine bakin rana a rayuwan su. Koda suka shigo Abba suka gani sanye da white jallabiyar yana magana da wani ma'aikacin gidan talabijin din AIT yana mika hoton Nadeera, wuce su sukayi batare da sun kalli uban nasu ba sukai shashin su, duk wanka sukayi suka shirya cikin suit bakake, ko wanan su jiyake kaman yamutu, suka fito tsakar gida lokacin gari yay haske sosai suka fito atare, Abba suka gani sanye da fararen shadda riga da wando ya rako Dr Bello dayazo duba shi rike da cikinshi yanadan murmushi, bin yaran nashi yay da kallo yanda sukai kyau sunci bakaken suit gwanin ban sha'awa, Muhsin yakafa bakar glass a ido, suka dumfaro wajen, wucesu sukayi batare da sun gaida Abban ko abokin nashiba kowanen su ya shiga motar shi suka danna wani uban horn mai gadi ya bude musu gate suka fita, bakaramin tsinkewa zuciyar Abba yayiba all he sees a fuskar yaranshi is tsantsar tsana dawani irin mugun hatred, sosai yaji he's heart broken dan yana mugun son yaranshi, he's 3 children are his life. Maganan Dr Bello ne yadawo dashi daga dogon tunanin dayaje yace "nabarka lpy Alhaji, please ka kula da kanka fa, banda yawan tunani karka sami hawan jini, sanan kasha magungunan sosai nan da kwana biyu cikin zai sakeka da izinin Allah" murmushin yake yayi yace "thank you Dr, agaida iyali" jan Motar Dr yayi yabar gidan, Abba yajuya yakoma cikin gida yana dan duka wa jikinshi yay sanyi sosai, akan kujera ya zauna yana dan kara ya jawo wayarshi daga kan table yay dailing number commissioner.




***
Afirgice ta farka daga baccin datake yi sakamakon wani irin haske bau dataji akan fuskarta tana kallon dakin cikin shirin yin kuka, yana tsaye jikin window ya yaye labulen dan ta farka, juyo da kai yayi ya kalleta yanda take kokarin tashi daga gadon jikinta na rawa amma takasa sabida kafarta dayay mata tsami sosai, ahankali yafara tafiya ya zagayo wajen ta gaban gadon, kulle idanunta tayi gam kirjinta nawani irin bugawa jin mutum akanta gawani irin kamshi dayake yi mai shegen dadi, daukanta da akayi yasa tasaki kukan datake ji sosai batare data bude idanunta ba jikinta narawa sosai, abayi ya zaunar da ita da sauri ta kifa kanta akan kafafunta tana kama jikinta, juyawa yayi yay wajen kofa yace "15 minutes nabaki, rana tafito u need to pray" yabude kofa yafice yarufo mata, saida taci kukanta ta koshi sanan ta dago kanta ahankali tana kallon inda ya ijiyeta kasan shower ne kaman jiya saita chan gefe kadan kuma babban leda ne da aka rubuta 24 hours super market ajiki ga towel sai toothbrush da toothpaste akai, da kyar ta cire jallabiyar jikinta tai wanka a zaunen tai brush kafin tai alwala, ta share jikinta tana kallon ledan, kaya ta gani ciki yasa tasake fashewa da kuka Mum kawai takeso tagani, wani doguwan riga data gani nasama baki mai stones taja tasaka aiko ya mata kyau ba kadan ba, bakin dan kwalin ta yafa akanta, ahankali ta dafa bango dantaga ko zata iya mikewa da sauri ta koma ta zauna dan kaman kafan ya balle sabida azaban dayake mata, knocking kofan akayi hakan yasa ta kara makurewa a zaunen, bude kofa yayi ya shigo yana tafiya wani irin nishi tayi tanaji kaman tai fitsari ajiki yanda yake tafiya ko ina na jikinta takeji gawani irin sanyi da takeji yana siga kasusuwan ta, daukanta taji kawai anyi hakan yasa tasake fashewa dawani kukan shikenan ita tadawo kaya adauka a ijiye, akan dadduma ya ijiyeta ga hijabi pink akai dake a linke yakoma kan dogon kujeran ya zauna yana danna agogon hanunshi, ahankali tadau hijabin ta saka, azaunen tai sallan ta idar ta daura kanta akan kafafunta, kaman daga sama taji saukan maganan shi. "hey! look up" yafada adake, da sauri ta dago kai takasa kallonshi, "look at me" kaman wata yarinya ta juyo dakai tana wani irin pikipiki da ido ta kalleshi tana sauke ajiyan zuciya ajejjere, yanda yaga tanayi yasa yadan sassauta murya yace "what's your name?" ahankali bakinta na rawa sosai tace "N..a...Nad..Nadeera" tai maganan tana goge kwallan daya zubo mata da bakin hijabin jikinta, innocent face dinta ya kafe da ido sanyi na ratsa jikinshi sosai, murya chan kasa yace "meke miki ciwo yanzu?" gwuiwanta ta nuna mai da yatsa, hakan yasa ya mike daga kan kujeran yazo inda take, wani irin kwalalo ido tayi kaman wacce za'a kashe kirjinta na bugawa tana kallon kafafun shi, hannunshi dake cikin safan hannu ya mika mata yace "give me d leg" wani irin rawa hanunta keyi tadan yaye doguwan rigan da hijabin tabashi kafar jikinta narawa sosai, karban kafan yay ahankali yadan ja rigan ta yanda gwuiwan yafito ya kalli yanda ya kumbura sai shining yake, ahankali yakai hannu zai taba da sauri ta rike hanunshi tana kuka sosai tana kallon gwuiwan cikin kuka tace "dan Allah ka barshi, zai warke ahaka am scareddd" sosai yake kallonta yanda take kukan wani irin abu na fizgarshi, jiyayi kaman butterfly namai yawo aciki, ahankali yace "leave my hand" da sauri ta sakeshi tana hawaye sosai, calmly yace "close your eyes" kulle idanunta tayi gam tana numfarfashi, itadai batasan meyama kafar ba amma wani irin azaba dataji lokaci daya takusa suma ihu tayi sosai tayi tana ture hanunshi da karfi cikin azaba tana kuka, saida yagama sanan ya saki kafar yana kallonta yanda take kukan dayakeji har ranshi, ahankali yace "waye wanan mutumin na jiya?" da sauri ta dago kai ta kalleshi saikuma ta dauke kai da sauri kirjinta na bugawa sosai tana goge hawayen datake yi. "who is he?" da sauri ta matsa baya dan yanda yay maganan kaman zai kasheta, data tonama Abba asiri awaje gwara taga yayyinta ko Mum tafada musu, akaro na uku yasake cewa "waye mutumin nan?" girgiza mai kai tai da sauri tana share kwalla, hannu yasa abayan wandonshi yaciro karaman bindiga, ihu tayi cikin kuka tana kallon bindigar cikin tsoro, saita mata bindigar yayi akai hakan yasa taja wani irin numfashi kaman zata suma tana kwalalo ido, cikin tsananin fushi yace "waye mutumin nan dat was trying to rape you?" a mugun tsorace tace "A..a..Abba na ne" da sauri yace "what? Abba? U mean Ur dad?" gyadamai kai tayi ahankali hawaye nabin kuncinta, ahankali ya maida bindigar bayan wandonshi ya dagata ya daurata kan gado, wani irin tsayuwa yayi agabanta ya daura kafa daya kan gadon yay folding hanunshi a kirji yace "Abban ki?" gyadamai kai tayi ahankali wasu hawaye masu ciwo na zubo mata. "and where is your Mum?" girgiza mai kai tayi tana kokarin hana kanta kuka, muryan ta na rawa sosai tace "bata nan" "ina taje?" yatambayeta da sauri, cikin sheshekan kuka tace "Dubai for business" wani irin fuzar da iska yayi kafin yasake daga kai ya kalleta yanda take kuka mara sauti yace "jiya yafara miki hakan?" dago jajayen idanunta tayi ta kallai saikuma ta girgixa mai kai alamun a'a hakan yasa yace "yaushe yafara?" sosai kuka yaci karfinta, shiru yayi yana kallonta zuciyarshi namai zafi da kyar tace "3days ago" wani irin ajiyan zuciya yayi murya chan kasa yace "yamiki wani abu d first time?" girgiza mai kai tasake yi tana goge kwallan datake yi tace "i ran na shiga toilet na kulle da key" sosai jikinshi yafara rawa hakan yasa ya janye kafarshi ya zauna yana facing dinta yace "kinada siblings?" gyadamai kai tayi tace "Ya Muhsin da Ya Ahmad" cikin fushi yace "to maisa baki fada musu ba?" fashewa tasakeyi da kuka sosai tana goge fuskarta da hijabi da kyar ta iya magana tsabagen yanda kuka yaci karfinta tace "yace zai yankani da wuka inna fada, and zai tsinemin" wani irin juya kanshi yayi with so much anger kafin yasake juyowa ya kalleta yace "ba a compound dinku brothers dinki ke zama ba?" gyadamai kai tayi tace "suna side dinsu, side dinmu is just me Abba and Mum muke a wurin" cikin tsananin kunan rai yace "inane gidan ku, wani anguwa kuke?" cikin kuka tace "Cresent Street no. 16" "ya sunan Abban ki?" batare data kawo komiba tace "Alhaji Naseer Aluminum" tashi yayi yafita daga dakin yana tafiya kaman zaki, saka kanta tai akafafu ta fashe da sabon kuka dan yasa ta sake tuna abubuwan da Abba yamata ne da ko kadan batason tunawa.


Yakai kusan 30min sanan ya shigo dakin dauke da tray kulan abinci da plates da spoon ga ledan magunguna agefe, tunda ya bude kofar fuskarta yake kallo yanda ta dukunkune tana bacci da hijabi ajikinta fuskarnan hawaye duksun bushe, gefen bakinta har yanzu da tabon ciwo wurin marin ne kawai ya sace, ajiye tray din yayi akan side drawer ya juya ya zauna akan dogon kujeran dakin yadau MacBook dinshi yana aiki, kusan every second yake dago kai yana kallonta.

Wuraren sha biyun rana wayarshi yay kara hakan yasa ya ijiye MacBook din yadau wayar wani sako ya karanta hakan yasa ya mike tsaye ya fita daga dakin yana tafiya kaman wani dan daba, sauka yay kasa ya fita daga part dinsu zagayawa bayan gidan yayi saiga wani part yakarasa ya bude kofa ya shiga, babban falo ne da aka ijiye wani mutum dake sanye da fararen kaya akan kujera a tsakiyar dakin an kulle mishi hannu sanan an rufemai fuska dawani bakin kyalle, kallon su Abdallah, Omari da Kamal yayi dasuka zagaye shi, alamu yamusu da sufice hakan yasan yasa suka fice suka rufo musu kofan, zama yayi akan wani kujera dake swinging haka ya daura kafa daya kan daya yana kallon yanda mutumin ke motsi yana uhmm uhmmm, yakai kusan 10min yana kallonshi kafin ya tashi daga kan kujeran yay inda mutumin yake daure akan kujera, bakin kyallen kan mutumin ya zare ya yar fuska Abba ya bayyana an taushe mai baki dawani irin salatef mai ruwan toka, wani irin kallon tsoro Abba kemai jikinshi na rawa, hanunshi yakai kan salatef din bakin Abba ya bare hakan yabama Abba daman magana arude yace "dan Allah kumin rai, mena muku, kuyakuri dan Allah inada yara uku karkusa su dawo marayu, ku fadi ko nawa kukeso zan baku wlh, kungama banda lpy, wlh cikina ba lpy, dan Allah kuyakuri bawan Allah kaji" yadade tsaye kanshi yana kallonshi jiyake kaman ya kasheshi hakan yasa ya juya ahankali yakoma kan kujeran dayake ya zauna ya daura kafa daya kan daya yanadan swinging ahankali ahankali, kallon shi Abba yayi a rude yace "dan Allah bawan Allah kumin rai, wlh banida lpy, konawa kukeso zan baku i promise" cikin wani irin fushi Marwan yace "kana ganin kanada kudin bamune?" arude Abba ya girgiza kai dan muryan mutumin saida yasa gabanshi yawani irin mummunar fadi, saukar da kafanshi yayi kasa yawani irin bubbuga takalmin akasa kafin ya dena ya sake dago kai ya kalli Abba cikin wani irin murya mai kama dana rikakken dan ta'addan nan yace "Kai! Kaine Naseer Aluminum ko" da sauri Abba ya gyada kai yace "bawan Allah nine, mina muku wlh banda makiya bana cuta, aluminum din danake saidawa a kamfanina original ce, bana saida jabu, dan Allah kumin rai yarana uku da mata daya karku illata ubans..." hannu Marwan ya dagamai azafafe, hakan yasa maganar Abba ta tsaya kyam yana zazzare ido yana kallon boyayyen mutun dinan dayaji yana wani irin shakkan shi, sake kallonshi yayi cikin wani irin murya dake girgiza zuciya yace "I will be straight, yarka Nadeera Naseer na hannuna, nasa a daukomin kaine sabida inaso kabani aurenta, inaso kabani auren yarka Nadeera!" wani irin kallonshi Abba yakeyi kirjinshi nawani irin dukan biyar biyar, sake kallon Abban yayi daya kasa koda motsin kirki yace "inada waliyyi na, inada shaidu, munada masallaci anan, so Naseer Aluminum inaso kabani auren yarka Nadeera Naseer mecece amsar ka?".

[9/13, 11:52 PM] Lady: 🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳




*Maman Abd Shakur*


Ahankali ya tsugunna agabanta yana kallonta batare dayace mata komiba, harde kafafunta tayi sosai tana kara daure hannayenta a kirji tana goge hawayen datake yi da bayan hannu kanta akasa tana kallon cinyoyinta da takeso taja towel ta rufesu amma ba halin hakan, dan fuzar da iska yayi dan kukan nan datake yi na mugun tabashi bayaso ko kadan, murya chan kasa yace "kinsan inda Mumyn ki takene?" juyo dakanta tayi ta kalleshi kafin ta kawad da kai da sauri bakaramin cika mata ido yayiba cikin manyan fararen kayan data ganshi gabanta na faduwa, girgiza mai kai tayi muryanta na rawa sosai tace "t..ana D..dubai" shirun dataji yasa tadan juyo dakai ta kalleshi ahankali ganin fuskarshi na saitin tane yasa tasake kawad dakai da sauri tace "please zan kirata ne ince tazo ta tafi dani kaji" mikewa tsaye yayi yana kallon agogon hanunshi kafin ya kalleta yace "you are not going anywhere, bazaki kara barin gidan nanba" fashewa tai da kuka sosai tana makemai kafada alamun a'a takasa magana sabida tsoro da shakkan shi, tsayawa yayi yana kallonta kafin yasa hannu yawani irin fizgota ta tashi tafado jikinshi arude takoma baya tana kuka tana kara rike towel din jikinta da kyau, sake jawota yayi ya sakala hanunshi daya ta bayanta ya riketa da kyau yana kallon yanda gashin gaban kanta ya kwanta lub ata goshinta, hadiye kukan tayi gum tana zaro ido kirjinta nawani irin bugawa tana kokarin ture hanunshi daga bayanta amma takasa, ta saukar da kanta kasa tana rera kuka ahankali, ahankali yasa yatsan shi yadago habarta kin kallonshi tayi saima hawayen dake gangarowa, dawani irin calm voice yace "ke yarinya ce? Don't you get tired of crying? Clean those tears" ya nuna mata hawayen daya gama wanke fuskarta, da sauri tasa bayan hannu jikinta na rawa sosai ta share hawayen batare daya saketa ba ta saukar da hanun kasa tana sauke ajiyan zuciya, janye hanunshi yayi daga waist dinta ahankali jin yanajin wani abu da tunda yake bai tabaji ba ya maida hannun cikin aljihu murya chan kasa data dan dishe yace "go and get dress am waiting for you" yay maganan yana nuna mata kofar bathroom din da kai, da sauri hartana neman turgudewa tanadan dingishi tai wajen kofar, bude kofar tayi ta shiga da sauri yana binta da kallo.
Wajen kayan ta taje tana share hawayen ta bude ledan super market din wani dinkakken atampa English da aka mata riga da skirt kayan kalansu brown and milk ne anyi musu stone work daya kara karama kayan kyau sosai ta ciro, saka kayan tayi tana kuka kaman ta shide wanan wani irin rayuwa Abba yasata aciki, bakaramin kyau kayan suka mataba tadau dankwalin su ta yafa dan hijabin ta na falo kuma kayan sundan matseta tafito ahankali tabude kofan batare data kalleshiba tai wurin gadon tana dan dingishi tadau pink hijabin ta dake kan gado da sauri ta saka ta zare dan kwalin sanan tq zauna a bakin gadon tana wasa da yatsun ta batare data dago kaiba, yakai kusan 2min yana kallonta kafin ya mike tsaye yace "let's go" da sauri ta tashi tsaye murmushi da tunda tazo batayi shiba ya lullube fuskarta tace "gida zaka maidani?" wani irin juyowa yayi yazo gab da ita ya daure hannayen shi ta baya hakan yasa tadan matsa baya da sauri tana kallon fuskarshi dake cikin mask, ahankali yace "gida?" gyadamai batare datai magana ba murmushi mai kama dana tsoro akan fuskarta, juyawa yayi yay wurin kofa ya bude kofan yace "lets go" ahankali take tafiya hartazo wajen ta tsaya nesa dashi hannu ya mika mata alamun ta bashi hanunta, hannu dake cikin safan hannu tabi da kallo kafin ahankali hanunta na rawa ta mikamai nata tadaura akan nashi wani irin shock taji harsaida tasaki ajiyan zuciya tana kallon hannayen, shima kusan hakan yaji yadaure ya rike hanun nata dakeda taushi yajata suka fice daga dakin ya rufe kofan tana gefenshi saibin babban gidan take da kallo yanda ko ina yake tsaf tsaf kaman ba mutane aciki, stairs sukayi suka fara sauka, ahankali yake binta sabida kafarta har suka sauka babu kowa afalon sai babban tv dake aiki, sai kallon ko ina take, bude kofar falon yayi suka fita compound, nanma babu kowa sai kallon compound din takeyi da uban motoci kusan shida ke ciki, sukai baya tana bin ko ina da kallo wani white yar babban mage ta gani tana wasanta tana hawa bango da sauri ta rirrikeshi ta tsaya batare data kalleshiba tace "kunada mage i don't like it" kallon magen yayi kafin ya kalleta yanda duka hankalin ta na wajen magen yace "is Abdallah's, muje bazai miki komiba" dago kai tayi ta kalleshi kaman zatai kuka saikuma ta kalli magen tace "are you sure?" matso da kanshi yayi ta wurin kunenta yace "yes muje kona kira miki ita ne?" da sauri takara rike hanunshi tabishi suka bar wajen, gaban wani part suka tsaya kafe kofar tayi da ido hakanan gabanta taji yana faduwa bude kofan yayi ya shiga hanunshi rike da nata tana biye dashi abaya itama ta shigo, ido da ido sukayi da Abba dake zaune kan kujera yana kallon su hakan yasa kirjinta yawani irin buga dum! tafara nishi kaman zata sume tana komawa baya sosai tanaso ta fizge hanunta tafice yaki sakinta.

Juyowa tayi ta kalleshi a mugun rude ta fashe da kuka sosai tanaso ta fizge hanunta ta gudu waje tsabagen yanda ta tsorata kaman taga dodo ya riketa gam yaki sakinta, da karfi tsiya ta shiga tureshi tana bubbuga kafanta akasa. "sakeniii" tana ture kirjinshi tana kokarin bude kofa, tare kofan yayi ya rungumota jikinshi da kyau yana bubbuga bayanta yana kallon fuskar Abba tacikin mask yanda Abba ke wani irin kallon bayanta idanunshi sun chanza kala, ahankali yacirota daga jikinshi ya shafo gefen fuskarta yace "shiiii" fashewa tai

Please Login or Register in order to submit comment