Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk jikinshi a sanyayye yana kallonta, tashi omari yayi tare da mata peck a goshi ya amshi car key yafita daga dakin da dan sauri gabaki daya ya shiga damuwa daurewa kawai yake yanzu shine babba dole shizai kula dasu.


Ahankali Abdallah ya zauna abakin gadon bayan yadau tray daga kan stool ya ajiye tray din agabanta tare da kai hannunshi ya daura a forehead dinta yay feeling tempreture dinta wani irin tausayinta yaji yake ji kaman zai mata kuka, ahankali bakinshi nadan rawa yace "My shagwabatu sis" kallonshi tayi tana wani irin sauke ajiyan zuciyan kuka, ahankali yace "zakici abinci yanzu?" girgiza mai kai tayi, dan saita kanshi yayi dan bayaso yafashe mata da kuka, ahankali yace "tashi kaje kiyi alwala kiyi sallah to, shower as well ko kyaji dadin jikinki, i..will be back in the next 20mints okey..oya clean those tears and cheer up, ya marwan will be fine ok..ey?" yay maganan muryanshi na breaking sosai, gyada mishi kai tayi tare dasa hannu tashare hawayen daya zubo mata murmushi yayi yana hadiye kukan dake zuwan mai yahau mata tafi yace "that's my lil sis, my shagwababbiya" murmushi yasake mata yatashi da sauri ya fita daga dakin yana waigenta, rufo mata kofan yayi ya tsaya a wurin yana kuka mara kara yana share hawaye da bayan hannu, bayason anything yasami Ya Marwan, he can give his life for Ya Marwan, Ya Marwan shine gatansu, ya kasance uwa agaresu, uba agaresu, yaya agaresu, kani agaresu, Ya Marwan has been everything to me, ahankali yace "Ya Allah please don't let dat man die kodan Ya Marwan ya kubuta please Ya Allah" yay maganan yana goge kwalla.



Yana fita daga dakin takara fashewa da sabon kuka, ta rasa meke mata dadi, tarasa ina zata sa kanta taji dadi, kawai shes not just her self and so many thought are running over her head, she's regretting, dana sani take sosai na chakama Abban ta fork, gashi yanzu tasa Ya Marwan in trouble, gashi yanzu an kamashi, takai kusan 10min tana kuka dakyar ta mike tana takawa ahankali dakyar ta shiga bathroom, cire kayanta tayi tasa a washing machine tasakin ma kanta shower bayan tagama tashiga cikin warm water kamar yanda tagan ya marwan na mata, da kyar ta daure ta zauna sanan tafito, ba karamin dadi ruwan ya mata ba, dauro Alwala tayi tadaura towel tafito daga toilet tana tafiya kaman zata fadi dan tsananin jiri ga yunwa, cikinta sai kuka yake da kyar taja mai tashafa tasaka gown kafin ta dauko hijab da praying mat tahau kai ta tayar da sallah.

Zama tayi akan dadduma tana ma ya Marwan addua na Allah ya kubutar dashi, kuma Allah yasa kar Abbanta ya mutu, bataso chakamai fork ba, sosai take kuka ba kakkautawa data tuna abinda daya faru some hours ago. Tana danasanin abinda yasa tadauki fork harta chaka ma Abbanta,haka tacigaba da kuka har Abdullah yayi knocking kofa ya shigo jin sautin kukanta.


Da sauri yakaraso cikin dakin ya dagota daga kan dadduma tare da hugging dinta yana patting bayanta murya chan kasa yace "its okey, stop crying kinji, ya Marwan nothing will happen to him, kinsan mesa? Because ya Marwan is strong and bold ga juriya, he will be fine I promise" gyada mishi kai tayi ahankali wani irin bakin ciki ne yatokare mata zuciya sosai, hannunta yarike yace "Oya zoki sha tea" girgiza mai kai tayi bakinta na rawa sosai tace "am not hungry" bai sauraretaba yaja hannunanta yazaunar da a edge din gado ya hada mata tea a mug mai kauri sosai ya mika mata, ahankali ta mika hannu ta karba, kadan tasha ta ijiye tana girgiza mai kai hawaye na fitowa daga idanunta tace "ni banaso, please Ya Abdallah I don't feel like eating" tafashe da kuka sosai, kafeta yay da ido danji yake kaman shima yataya ta kukan, ahankali yasa hannu ya dauki ragowar tea da tray ya mike tsaye yana kallonta yace "i will be right back, stop crying pls" gyadamai kai tayi tana share fuskanta da bayan hannu.

Agaban tap ya tsaya a kitchen yana dauraye cup din tea yaji alamun bude kofa, da sauri ya ajiye cup din yafita daga kitchen din dan ganin ko waye ya shigo gidan su, Ya Omari yagani da wata nurse biye dashi that will be in her late 30's. Bismillah yama matar sukai sama suka shigar da ita cikin dakin da Nadeera dake kwance ta lumshe ido, ahankali ta bude ido hoping aranta taga Ya Marwan, ganin su Abdallah ne da Omari ne yasa ta mayar da idanunta ta lumshe tana sakin ajiyan zuciya, Ya Omari ne yakaraso jikin gadon yace "Lil she's here to check u, feel free kifada mata abunda ke damunki, okay?" gyada mai kai tayi yajuya suka bar dakin shida Abdallah tareda rufo musu kofa. Kafeta da ido nurse din tayi kafin ta karaso tazauna gefen ta abakin gadon takai hannu ta taba goshinta da wuyanta zafin dataji saita taji tsoro da sauri tace "meke miki ciwo haka?" shiru tayi tana kallonta sai kuma tai mata bayani abinda ke damunta alokacin ne ma ta tuna she's a nurse itama fa, gyada mata kai nurse din tayi tace "kina zama ai cikin ruwan dumi?" ahankali tace "eh" "good kidage da zama cikin ruwan zafin zai warke, yanzu kawai pain relief zan miki prescribing da kuma pcm sabida wanan temperature dakike running" gyada mata kai tayi ta juya ta fita daga dakin ta sauka kasa, da sauri Omari da Abdallah dake zaune a palour suka mike suna kallonta, karasowa tayi ta mika musu prescription na magani tace "kusiyan mata maganin nan in shaa Allah she will be fine, and idan akwai anyproblem dont hesitate to call me, will come back nanda 3days to check on her, na barku lafiya". Godiya suka mata sosai Abdullah ya amshi key daga hannun Omari to drop her and from there yayi branching pharmacy ya siyan ma rahma drug nata, suka fice.


Shigowa gidan Abdallah yayi dauke da ledar magani, direct dakin Nadeera yayi daddan sauri, sallama ya tsaya yayi jin shiru yasa yatura kofan ahankali bacci tanata sauke ajiyar zuciya irin na wanda tasha kuka tagaji dinnan. Tashinta yayi ya bata magani da kyar tayarda tashanya ta koma barci, juyawa yayi yafice bayan yaja mata kofa yay dakin palo duk hankalin shi yaki kwanciya da halin da ya Marwan ke ciki.


Bayan kwana biyu.

Sosai jikinta yay sauki, bata wasa da zaman ruwan zafin, saidai bata iyacin abinci ko kadan, idan yayyinta basu takurata ba bazataci ba, so kawai take taga Ya Marwan amma sunki zuwa sa ita station din, ga wani irin kewan shi datakeji, gashi batada waya balle takira tafadima Mum ko hankalin ta ya kwanta, duk tunanin yaja ta rame idanunta suka fito sosai.


***
"Kin ganta shar shar da ita, give me head haba mana Princess, haba baby girl nidai head nikeso princess..." wani irin ihu yayi yatashi yana salati arude yakai hannu zai taba abunshi yaji wani irin zafi awurin, da sauri yacire hannun daga wurin yasaki wani irin wahalallen kara hawaye na fita daga idanunshi. Police guda biyu daaka sa su tsareshi dake bakin kofan dakin ne suka shigo sabida jin ihun dasukayi Abba ne suke gani dake kokarin cire drip daaka sa mishi yana cizon lebe saboda azabar dayake ji, sai kiciniya yake kaman wanda yasami tabin hankali, da sauri suka karaso wurin gadon daya daga cikinsu ya dafa Abba yace "calm down sir everything is under control"wani irin kallonsu Abba yayi kafin yace "where is my daughter? Where is my princess?" "she is with the commission" daya daga cikin police din ya amsa mishi ataikaice ganinshi a birkice da sauri ya mika musu hanun shi yace "now get this off me I want to go and see my babygirl" Kallon Abba sukayi batare dasunce mai komiba, wani irin ihu daya musu akai yasa Dr yashigo dakin da gudu. "nace kuciremin ko" da sauri Dr dayake Christian yakaraso yana kallonshi yana murmushi yana cewa"ahhh! Thank God you made it, kana da taurin rai Alhaji, kanada taurin rai gaskiya, we thought we were going to loose you fa, all you need now is to relax bara inyi alerting nurse taxo mu duba maka ciwon ka, kai am so happy Alhaji kanada taurin rai" Wani kallon Abba kema Dr din yace "kaikuma daga ina?" dan murmushi yayi yace " am your Dr, so how are you feeling?" Abba dai binshi yake da kallo kafin ya bude baki yace "Dr please take this drip off me inada important abunda zanyi, yanxun like its really really urgent" "But sir bazamu iya barinka katafi ahaka ba batare damun duba wound din ba, Its against our profession please, bakai warkewan dazamuyi discharging nakaba" dasauri Abba yace "ciwonka ne? Ajikin ka ne? nace zan tafi, tuge abin nan ku sallame ni, are you trying to tell me what to do, mtsww inda princess dina na nan data ciremin my nurse" yay dan murmushi yana tunanin Nadeera kafin ya dago kai ta Kalli Dr, ganin baida niyyan ciremai yasa ya tuge canlullar daga hannunshi ya yarda yana kokarin sauka daga kan gado shaff ya manta babu komai ajikinshi blanket ne kawai aka rufeshi dashi kadan yarage blanket din yafadi ya rike da sauri yana kallon Dr yace "where is my trousers?" "ba'a kawoka da trouser ba" Dr yafada ataikaice dan yaga rigiman tsohon tafi karfinshi, bai damuba saima tabe baki dayayi yaja katon blanket din yana nannadewa ajikinshi yana cije lips saboda yanda hannunshi da manhood dinshi ke mishi zafi sosai, yana gamawa yace ma police din "kaini wajen commissioner" bai jira amsansu ba yayi gaba yana takawa ahankali yana squeezing face dinshi alamun pains, binshi abaya sukayi ganin alamun dagaske Abba yakeyi bude mishi baya sukayi yashiga sukuma suka shiga gaba suka ja motar tare da barin premises na hospital din.



Direct office na commisioner ya shiga, ko knocking baiyi ba ya shiga kai tsaye. Da mamaki commissioner ya bude ido yana kallonshi ganin Abba agabanshi, zama Abba yayi kan kujera yace "ina Nadeera take? Hope yaron bai kara dauketa ba?" kallonshi kwamissiona yake kafin ahankali yace "ya jikin naka friend? Ya akayi sukai discharging dinka ahaka?" da sauri Abba kaman zaiyi kuka yace "ba wanan ba friend, please tell me how is my baby girl? Where is she now? Hope dat kidnapper bai kara kamata ba?" shiru kwamissiona yayi yana kallon Abba dan sosai yaji Abba nawani irin bashi tausayi ayanzu, gyaran murya kwamissiona yayi yana fuskanta Abba yace "Alhaji harkaji sauki dazaka iya fitowa daga hospital, i thought you still suppose to be on the hospital bed?" Kallonshi Abba yayi kafin yace "where is my daughter?" Sake gyaran murya commissioner yayi yace "Alhaji ashe Nadeera is not your biological daughter? And baka taba fada min ba duk amintanmu? Haba Alhaji? Gaskiya am surprised? How could you hide such a big thing from me?" shuru Abba yayi still no response from him yana kallon commissioner, cigaba da magana commission yayi yace "I've seen all evidence nacewa this girl is not your daughter, and you are trying to rape her? Why friend? Kasan har yanzu bansaka any kara a kotu ba sabida kai nake jiye mawa, and do you know what it means cewa akai kara court sai yaran nan suyi presenting case cewa you are trying to rape there married sister, do you know what that means friend?" katseshi Abba yayi ta hanyar cewa "waye married sister nasu? su waye su? Am not getting you, Nadeera batada kowa aduniyar nan sama dani ubanta ahalin yanxun, babu wanda yakaini iko da ita, namata komi na rayuwa, Yes nasan shez not my daughter, and am sorry for not telling you tun tana 3months lokacin ina aiki a eygpt mukai adopting dinta, friend banda wacce nakeso a duniyan nan kaman Nadeera I swear to you shiyasa nikeso in aureta, I want to marry her and make her mine, mine forever, and for the rape case sharrin shaidan ne, wlh shairin shaidan ne dakuma tsananin son danake mata always make me feel that urge to cuddle her or have her u know" yay shiru yana sauke ajiyan zuciya dan sosai muryanshi tafara rawa kuka na neman kufcemai, murmushi commissioner yayi tare dacewa " i've heard you, koni nasha ganin son Nadeera a idanunka but I always tot irin father and daugtherly love dinan ne, but kasani you are my friend and i can never deceive you, and ba tun yau muka san juna ba, musan juna tun muna samari tun mama nadarai, kagan yaron nan wanda ka aura mata toh dan uwanta ne, kaga yanda Allah ke abu ko, Allah yahada auren su, auren ya kasance kuma auren kaddara, kai kanka bakasan lokacin daka amince kabada auren nataba anan kadai yakamata ya yarda da hukuncin Allah rabbul samawati, kuma yaran nan sunada complete evidence wanda ko ina sukayi presenting this evidence idan nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba sune zasuyi winning case dinan akanka, Saisa am very happy dana ganka I personally want to advice you sincere advice ma kam ka hakura ka janye case dinan u can never win, kai attempting raping yarinyar nan basau dayaba, you hit her, kai alot of things da instead of akamasu saidai kai akamaka aturaka prison, Alhaji Naseer Friend!" yakirashi cikin dan kakkausar murya yace "inaso ka janye kowani irin kara let's free this boy, ya tattara matarshi Nadeera da kananshi subar kasan nan su koma chan kasar su Egypt, ka manta da komi Nadeera ba matarka bace Allah ya riga ya kaddara hakan accept your faith kaji, mekace ka hakura mu saki yaron tun kafin yay involving lauyanshi aciki dan dama ni nace mubar komi on hold harsai anga warkewan ka, kokuwan in barka kai go ahead kaga kaine zaka shiga matsala nan gaba, me kace? Are you giving up or not?" kwamissiona yamai maganan yana kallon fuskarshi.

*masu min posting waje kuda Allah*


*3107021073 first bank aisha Muhammad zaki turo 300 in kinason book dinan, zaki iya turo MTN card ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting*


*BOYAYYEN MUTUN*


Daga mishi kai kawai Abba yayi without saying a thing, hannu yakai ya bude dayan document din kaman mara gaskiya, zaro ido yayi ganin document nasu dasukeyi adopting Nadeera ne da aka basu a eygpt, saboda harda picture da dukkansu suka dauka dasuka je motherless home ranan dasukai adopting nata. "Where did you get this docuuu...m...en..t" abinda ya fito daga bakin Abba kenan da kyar yana numfashi da sauri sauri, murmushi Omari yayi kafin yama Abba bayanin yanda akayi mummy takawo musu document gidansu as an evidence cewa ba ita bace ta haifi Nadeera, coincidentally kuma tazamana itace lil sister dinsu dasuketa nima. Shuru Abba yayi without any word from him again sai zufa yake yana numfashi da sauri da sauri kirjinshi na bugawa sosai, wani irin tausayin shine ya diran ma commissioner a zuciya jiyayi kaman yamai kuka hakika so cuta ce wlh, kallon Abba yayi ahankali yace "friend, am happy yanxun you've seen for yourself, Alhamdulillah, so what did you say now?" Shiru still Abba yayi idonshi cike da kwalla, zuciyarshi namai wani irin zafi da yana ganin tunda yazo duniya bai tabamai irin zafin ba, yanzu wayan nan shikenan yan uwan Nadeera ne, yan uwan Princess dina? Shikenan yanzu, shikenan? Ya shiga can duniyar tunani yay nisa, he just realize cewa shikenan he has lost Princess forever, wa'inda suka fishi iko da ita Allah ya kawuso, wani iri yaji zuciyarshi namai, he just want to cry amma yakasa, nauyi sosai yaji kirjinshi namai, inama ace yanada ikon maida agogo baya dabaiyi kokarin raping princess ba, attempt rape dinta dayayi yasa harta gudu daga gida har yay resulting to yau, dabaiyi yunkurin haike mataba da maybe yanzu ma tana dauke da cikinshi, mesa ya biyema shaidan akan Mum batanan yaje yabi yarshi? Why? why? Shikenan Princess is not mine yanzu? Wani irin hawaye ne ya gangaro mai da sauri ya share ya daura hanunshi kan idanunshi ya matse idanunshi yana wani irin cizon lebe yana kokarin hana kanshi kuka amma hawayen saida suka shiga bulbulowa sunabin hannunshi.


Ayanda commissioner yaga yana kuka mara kara yasa yakira wani sergent ya bashi umarnin afito da Marwan daga cell, yadawo ya zauna kusa da Abba ya dafa kafadarshi alamun lallashi batare dayay magana ba, bayan kamar 7min wani sergent yashigo office din Marwan biye dashi.

Umarni commissioner ya kara bama sergent daya dauko mishi dogon wandonshi da tshirt nashi dasuka amshe, sabida da boxer da kuma singlet kawai suka barshi. Fita sergent din yayi with immediate effect don zuwa aiwatar da maganan commissioner. Kallon Marwan commissioner yayi tare da cewa "you are freed, sannan on behalf of my friend" yanuna Abba da har lokacin hanunshi kekan idanunshi hawaye nabin hanun yace "we are sorry for all the pains we have cursed you. Allah ya baku zaman lafiya, we are really very very sorry, you guys can leave now"
Har sun juya zasu fita commissioner yace "Marwan please i want you to do me a favour idan ba damuwa" kallon Abba Marwan yayi dahar lokacin yana yanda yake kafin ya kalli kwamissiona ya gyadamai kai, ahankali kwamissiona yace "i want you to leave this country da kai da family dinka don Allah" kallonshi Marwan yayi adake babu alamun wasa ko tsoro for like 5sec kafin yace "if i may ask why?" murmushi commissioner yayi tare da yadan fuzar da iska yace "its just a request, and hope it will be considered" dan tabe baki yayi yace "Actually, munada intention na barin nigeria dama tun ba yau ba, But tunda haka things yayi turning around we have no other option, we are going back to our father's land" wani irin dadi ne ya lullube zuciyar commissioner yay murmushi yace" thank you Marwan".

Fita sukayi dukkansu daga office din suka rufo musu kofan, har aka gama dukka wannan conversation din suka fita Abba bai dago kai ya kallesu ba, sosai yake kuka, bayan fitansu ne commissioner ya matso da kujeran shi sosai kusa dana Abba dafashi yayi ya fuzar da iska yace "friend please take heart, I did wat I did because I love you friend, because I care for you, nasan idan nabarma komi bazakai taking d right choice ba, I do wat is best for you, am ur bro your friend I have to guide you, had it been I knew everything tundaga farko trust me non of this would have happened, everything daya faru yanxun kaddara ne, just take it as your destiny, haka Allah ya kaddara, kafara tuba ka nemi gafarar ubangijin ka dana family dinka da ita Nadeera, but before then u have to start healing, u have a long way to go my friend, you've made mistake but I can never hate you for that, a true friend shine friend that will love support you and stood by your side regardless, so am with you zamuyi fighting this battle together, love is a disease, love is poison, and love can be the most sweetest and cutest thing to someone's life, forget Nadeera ka kaddara hakan Allah ya tsara, ba komi mukeso musamu ba, Allah na karban tuban Bawan shi matukar baikai gargara ba, kasan abinda kama Allah ka tuba sanan kai alkawari bazaka karaba, lemme tell you something sef, Wlh Billahi Allah ma na nemanka da shiriya ne inda ba hakaba daya barka kai raping yarinyar nan and kasan hukunci wanda yakeda aure dayay Zina ko? Jifan shi za'ayi harya mutu, kayakuri forget Nadeera nasan is not going to be easy yarinyar daka shaku da itane tun tana yar jaririyan ta kayakuri kaji friend, Allah maganin komi ne once ka mika wuya gareshi ka fawwalamai al'amuran ka toya isar maka kaji" dago kai Abba yayi fuskarshi duk ya jike da hawaye, idanunshi sunyi jajir kaman wuta, heart dinshi na suya kaman ana soya gari, fashewa yayi da kuka sosai kaman yaro yace "I love my baby girl so much friend bazaka ganeba, I love baby girl, I admit I've made alot of mistakes amma wlh nai nadama, I love my baby girl dan Allah kadawo min da baby girl, I promise bazan kara abubuwan danayi ba, am sorry, am so sorry princess forgive ur Abba, babygirl, my little princess please come back to your Abba mukoma gida da Mum da yayyinki muyi zaman mu as one happy family, am so so sorry babyna, am so sorry princess, I love you so much so much wlh, friend I love my princess dayawa dayawa, wlh I can die idan na rasata forever, my life will be shattered, shekaran jiya ko yaushene ma I was damn jealous dat was d reason why I wanted to scare her off, but ba raping dinta zanyi ba, I love princess tun tana yarinya, innalillahi wa inna ilahi raji'un, astagafurullahi, Ya Allah natuba, ya Allah am sorry, wayyo Allah na I love you princess so much, my heart is burning Fri.." sosai kuka yaci karfin shi hakan yasa yaja blanket din daya daura yasa a fuska yana share fuska yana kuka uncontrollably gwanin ban tausayi. pathing bayanshi commissioner ya dungayi yana bashi hakuri ahankali kafin yace "tashi let's go inside ka chanza kayan nan" da taimakon shi ya daga Abba ya kaishi dayan dakin ya bashi kaya ya saka kafin ya kaishi asibiti da kanshi dan yakasa daina kuka gwanin ban tausayi jikinshi yay zafi sosai.



Suna fita daga station din direct parking lot sukai, agaban motan suka tsaya yace "Omari inaso kuna isa gida yanxun pls ku shirya kayanku and ku taya Nadeera shirya nata as well, I book any available flight for you guys ku wace airport, i want us to relocate to Egypt" juyowa Abdallah yayi ya kalleshi yace "how about you, inace tare zamu wuce dukkanmu." "No akwai abubuwan dazanyi clearing, so zan biyonku nanda 1-2weeks in shaa Allah, yanxun kukaini can gidanmu dake bwari, idan kun tafi zan dawo gida in shaa Allah. Sannan 1 more thing, pls kar ku fadawa Rahma anyi freeing dina, and ranar da zanzo egypt too please karku fada mata. I want it to be in a form of suprise. And please take good care of her, take very good care of her, none of you should trouble my wife" Gyada mishi kai sukayi both of them, suka shiga motar, saida suka fara ajiyeshi a tsohon gidansu na bwari kafin su wuce gida. Suna isa gida suka taradda Nadeera sai barci takeyi a palour remote na hannunta. Part dinsu suka wuce suka hado kayansu kafin su dawo nata su hada mata nata, Saida suka gama hadawa sannan suka zauna booking tickets dinsu Marwan yafara tura musu ta email sanan suka tasheta tare da mika mata hijab dinta binsu tai da kallo Omari yace "wear your hijab" karba tayi tasaka ba musu tana gama sawa Abdallah ya mika mata takalmin ta "wear it" ahankali ta zura, Abdallah ya ja hannunta suka fita daga gidan bude mata mota yayi yasata aciki Omari yakoma ya rufo gidan ya shiga cikin motar suka bar gidan. "where are we going to?" tai tambayar ahankali tana kallon Ya Omari dake driving, juyowa Abdallah yayi yace mata "we are living nigeria to eg.." batama bari ya karasa ba tace "toh ina ya Marwan? Taya zamu bar nigeria bayan he is still in cell?" Tana kaiwa nan tafashe da kuka sosai Omari ne yakira sunanta. "Rahma dont worry he is fine kinji i assure you" kuka tacigaba dayi har suka isa airport bata bar kuka ba. Ahaka sukayi boarding idonta duk a kumbure jirgin su yadaga sama.

Around 6:30 pm na yamma jirginsu ya sauka a garin egyp, wata babban mota tazo ta daukesu daga airport din takaisu wani babban gida...


2days later.
Marwan yadawo gida ya hada important document daya kamata ya hada duk ya hada, ya nemi masu siyan gidan sunzo sun siya yahada kudin yaraba gida uku kashi daya yakai gidan marayu, daya prison, daya kuma hospital, The following day yaje har gidansu na daji

Please Login or Register in order to submit comment