Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaske, idan ba haka ba ya rasa unguwar da zai samo ya siya gida sai irin wannan unguwar. A daidai wani kofar gida karamin gaske suka tsaya, suka fito a tare wanda zasu gani yana tsaye yana jiran su, yana ganin su ya karaso bakin sa cike da murna ya gaishe su, sannan ya bud'e musu gidan yace su shigo.
   Siminti ne gaba daya tsakar gidan sabo yana ta kamshi, bashi da girma tsakar gidan sosai dan be fi yaci tabarma days da rabi ba, a gefe yar karamar rijiya ce saboda rashin ruwan unguwar.
   Dakunan guda biyu da suka kasance falle-falle ya bud'e musu suka shiga nan ma ko ina an masa fenti yana ta kamshi, babu abinda ba'a saka ba hatta karamin gado da kujeru an saka,da yar karamar tv babu batun fridge ko cooker gas balle azo maganar su AC da sauran kayan more rayuwa, kitchen din babu komai dama sunyi da nufin daga gida sai a kawo mata kayan kitchen suyi amfani dashi. Kitchen din karamin gaske ne dan mutum biyu ba zasu iya aiki a ciki ba saboda kankantar sa, balle a samu sukunin cika shi da kaya.
   Fitowa sukayi ya rufe gidan yana sake washe baki

"Ranka ya dade gidan yayi ko?"

"Yayi sosai yadda nake so, sai ka sanar musu ba sai an kawo kayan gida ba ,iya kitchen ya isa shima karsu matsawa kansu duk abinda babu zaka saka musu."

"An gama ranka ya dade, sai maganar lefe."

"Ana gobe daurin aure za'a kai, an gama hada komai ina tunani."

" Nagode Allah ya kara arziki."

Be amsa ba, yayi gaba ya fad'a motar yana kallon tsarin gidan, murmushi ne ya kwace masa, ya girgiza kansa yana ayyana yadda zuciyar Mama zata buga ko kuma ta kusan bugawa,yayi alkawarin shayar da ita mamaki irin wanda bata taba tunani ko hasashe ba.

  Kai tsaye wajen gym suka wuce, ya kwana biyu be motsa jikin sa ba, yana bukatar hakan saboda tafiyar da sukayi be samu lokaci ba. Dariyar shakiyanci Musaddik ya dinga yi masa, ya tsaya daga abinda yake yana hararar sa

"wai dariyar menene haka? Uhum?"

" Naga yadda ka dage kake ta faman daga karafu nan nan ne wallahi, kar dai ka illata musu yarinya wallahi, kasan dai kai din tsohon tuzuru ne da yaki auruwa. "

Robar ruwan da ya gama sha ya jefe shi dashi, ya goce ta fadi kasa yana sake tuntsurewa

" Ka kiyaye ni wallahi. "

" Anki din, daga fadar gaskiya?"

" Zan kamaka ne, naga kafarka a gida na wallahi. "

" Gidanmu dai. "

Towel ya ja ya goge gumin fuskar sa, ya biye wa Musaddik zai dauke hankalin sa ne ga abinda yake shirin yi. Wayar sa ya dauka akan dan table din wajen yayi dialing number ta, sai da ta kusan katsewa sannan ta daga.


"Huh!" Ya furzar da iska yana jan numfashin

"Ranki ya dade an gama jamin ajin ne?"

"Ina wuni?" Ta kautar da maganar ta hanyar gaishe shi

"Lafiya lou, ya gida ya kowa da kowa?"

"Alhamdulillah."

"Masha ALLAH, yaushe Abba yace zaki dawo?"

"Be fad'a ba, amma naji Mummy tace ba zan dawo ba sai ranar."

"Ranar? Yaushe kenan?"

" Ka cika tsokana wallahi, nima ban sani ba."

"Ke kuma kin cika kunya ba, sai kici sai ranar auren mu kawai."

" Allah zan kashe wayar." Ta fad'a tana turo baki, dariya yayi yace da sauri

" Allah ya baki hakuri Matata."

Shiru tayi tana wasa da album din hotunan da Mamma ta bata bayan ta mata bayanin kowa da yake jiki.

"In sha Allah ana gobe za'a kai lefe, kinsan sha'anin rayuwar, Allah yasa be makara ba."

" Be makara ba, Allah ya saka musu albarka."

"Amin Matata, nagode sosai da bani dama da kikayi, in sha Allah ba zaki yi Dana sani ba."

"Kullum godiya? Ni me nayi?"

"Ai wai kinga dai yanayin yadda abubuwan suke."

"Babu komai Allah ya tabbatar mana da alkhairi."

"Amin Amin amarya ta."

Yar karamar dariya tayi, shima ya tayata kafin suyi sallama. Mamma ce ta shigo dakin rik'e da jaka babba, sai me aikin gidan dake biye da ita da wasu kayan suma da yawa, ajiye su sukayi a gefe me aikin ta fita kafin ta sake dawowa ciki dauke da tray da aka doro chicken pepper soup da wani cup shima cike da abu kamar kunu, sai wani da akayi ma hadin fruits aka saka madara. Dora shi tayi a saman drawer ta fita ta barsu.
Da hannu Mamma tayi mata alamar ta taso, ta taso ta zauna a k'asa in da Mamma din ta nuna mata, tray din ta sakko mata dashi tace maza ta cinye naman tas, idan ta gama akwai bakuwar da zata shigo wajenta, Itace me jakar chan. Tun zuwan ta gidan take faman shan abubuwa, a dan lokacin tayi masifar chanjawa, tayi kara fari da kiba jikinta ya sake murjewa sosai. Ita kanta tana jin da gaske ta kai mace, tana jin zata iya karawa da ko ma wace amma a dah, bata da wannan confidence din.
Bata kyuwar cin duk abinda aka bata dan da bata samu wanda zai dubeta ba balle har ya bata abinda yasan zai amfane ta. Shiyasa ta bada himma take yin duk abinda za'a sata.

***A bangaren gidan su Iman kuwa, bayan dawowar Abba sai da suka sake wani rikicin da Mama, wanda ya saka kowa ji har aka dinga ganin baiken Maman, amma kishi ya rufe mata ido matar Abba Musa na zugata tayi masa tijara son ranta, be kula ta ba don a yanzu baya sakata cikin jerin masu hankali, yana mata uzurin kishi ne ya sakata yin wasu abubuwan. Bayan kamar kwana biyu da dawowar sa ta same shi har daki ta bashi hakuri abinda ya bashi mamaki sosai, hakura yayi ya sakko amma ba wai don ya hakura da maganar Iman ba, yana nan sai ya yi mata hukunci daida abinda ta aikatawa yar sa.
Shirye shirye ya kankama sosai, mama babu zama kullum tana hanyar kasuwa tun da ta samu labarin cewa Bashir yace iya kitchen kawai zasuyi, hakan yayi mata dadi shine ta maida hankalinta sosai wajen kawata kitchen din dan ta tabbata gidan ba karamin gida bane, dole ne su fita kunya ta hanyar hada mata kitchen din yayi sosai.
Duk abinda ta tambaya Abba bata yake dan baya son wata doguwar magana, hankalin sa gaba daya yana kan maganar auren Iman, da yadda daurin auren zai kasance domin yasan za'a yi taro ne irin wanda ba'a taba yi ba, manyan mutane zasu halarta da yan siyasa da manyan sarakunan k'asar nan da ma na ketare. Duk abin nan Mama bata san komai akai ba, bata taba tambayar shi game da Iman din ba ko yadda nata tsarin yake, shiyasa kawai shima ya rufe ta ruf ya barta da abinda take yi.
A yadda tsarin bikin yake, alhamis za'a yi kamu, juma'a a daura aure sai asabar dinner kamar yadda Zeenat din suka zauna suka tsara ita da Bashir bayan ya sanarwa Moh da tsarin ya kuma bashi go ahead.
Tsarin bikin da su kuma chan masarauta suke shirya wa biki ne gagarumi za'a yi a Kano da Adamawa, kowanne kuma kwanaki za'a dauka anayi tun daga asabar din washegarin bikin, na Kano za'a fara kafin a koma adamawa in da za'a kai amarya.
Kamar yadda yake a tsari, ranar alhamis za'a karbi lefe, lefen Zeenat da Iman, wanda Mama tayi gayya, gayya irin ta ban mamaki, tana Kuma sanarwa mutane suzo suga lfen Zeenat dan ta tabbatar za'a ga kayan da baa taba gani ba.
Yan uwa da abokkan arzikin Mama su suka cika gidan, aka shirya kaya na mamaki, aka gyara gidan. Wata sister Mama ce tazo ta sameta tana zaune cikin kawayenta ana shewa, ta jata gefe hankali a tashe tace

"Yaya, wani labari naji fa, dangin mijinki na hirar basu san Ina wajen ba, naji suna cewa Iman tayi goshi ta samo jinin sarauta, ana ma tunanin dan sarki ne duk da Basu tabbatar ba ana boye zancen ne amma kamar hakan ne."

Wata irin dariya Maman ta saka, har da hawaye

" Kinji ki Fatima da wani zance, su fa basu san kan zancen ba, maganar Zeenat ake ba Iman ba, na ji wannan zancen tun bayan zu ba ai, kawai na kyale mutane ne yadda abun zai kada su, ba dai anjima kadan zasu iso ba? Zamu gani ai."

" Allah yaya? Kin Kuma tabbatar da hakan ne?"

" Zaki gani ai."

Tayi gaba tana murmushin mugunta, ba karamar kunya tasan za'a sha ba a lefen Iman din ba.


Hmmm






***Assalamu alaikum sisters fatan alkhairi ga kowa da kowa. In Sha Allah hutun mu zai kama asabar da lahadi, domin kowa ya samu damar aiwatar da wani abu me muhimmanci a rayuwar sa, sannan mu kula da gidajen mu da iyalan mu dukka, mu bawa yaranmu da mazajenmu lokacin da suke bukata daga garemu. In Sha Allah Monday to Friday za'a samu posting in sha Allah, sai dai wani uzurin ya gifta. Sannan masu korafin ba'a basu page biyu ko uku a rana, wani page dayan yayi wasu pages din guda biyu, so idan hakan ne gwara dayan me tsawo mu tafi a hankali har Allah ya bamu ikon kammalawa.
Zafafa biyar na godiya da zabin su da kuke a kowanne lokaci, dan Allah mu cigaba da yi ma juna uzuri kuma mu kyautata lafazi a tsakanin mu domin magana me kyau ma sadaka ce.


Masu sharing novels group group una weldone kunji? Dan Allah ku daina babu kyau, ka sowa dan uwan ka abinda kake sowa kanka hakan na cikin cikar imanin mumini.

Rano
1/18/22, 19:58 - Buhainat: Halin Girma
14


_*Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

_________________________

*_MACE SAI DA GYARA_*💃🏻💃🏻
_GYARAN MA NA KAMFANIN TURAREN:_
    *YERWA INCENSE AND MORE*

*Ƴar uwa ta hanyar gyara ne kawai zaki cigaba da amsa sunanki mace hamshaƙiya a wajen miji ba tare da ya ga kin tsufa masa ba.*

_Maza garzayo ki gyara jikinki da kayan ƙawatattu kuma nagartattu irin namu na gida da suka sami haɗi na musamman da babu cutarwa a ciki. hadin bornu/chadian na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE_

*_Muna da haɗin_*

_Turaren wuta kala kala na gidah_
_khumrahs_
_Kullaccham_
_Turaren wanka_
_Turaren Kaya_
_Turaren wanki_
_turaren mopping_
_Dukkanil al’ajab (Turaren tsugunno na Matan aure kad’ai)_
_khumratul al’ajab (khumrah ta jiki ta matan aure_

_Muna Gyaran jiki_
_Na amare_
_Da masu jego_
_Da sabulai masu gyara fata_
_Turaren tsugunno_
_zumar goran tula_
_Scented hair cream and spray (man kamshin gashi da gyara gashi_

_Akwaisu kujeran tsugunno
_Dilke and halwa set_
_Burners da igniters da tong_
_turaren fesawa dana ruwa._
_wardrobe balls_
_scented pebbles_
_cotton wooly oudi incense_
_kabbasas_

_Da sauran kayayyaki da yawa da bamu ambata ba_

_Akwai ragi na musanman ga yan zafafa fans❤️_

_Muna bada sari, Ko sayi ‘dai ‘dai akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan 👇🏼_*

_EMAIL:[email protected] ko INSTAGRAM PAGE d’inmu:yerwaincense_and_more dama nambR mu:08095215215_

_MUNA TURAWA KAYAN MU KO’INA A FADIN NIJERIYA DAMA KASASHEN KETARE.
100% TESTED AND TRUSTED_

•••••••••�?



*****
Azahar sosai ya tashi, ya mike yana salati, daga curtains din dakin yayi yana mamakin tsawon lokacin da ya dauka yana baccin, wayar sa dake saman gadon ya dawo ya dauka ya bud'e ta, misscalls ya gani ya duba sannan ya ajiye ya fito zuwa falo in da yatar da abincin sa a jere cikin manyan warmers sai kuma wani dan basket da aka rufe shi da jan kyalle me kyau dake dauke da hoton heart, matsawa yayi gabansa yana kallo,

"Menene wannan?" Yayi maganar yana rik'e kugun sa da sauri wani bafade ya shigo, ya rissina yace

"Sako ne daga shashen Kilishi, inji gimbiya Laila."

"Laila?" Ya furta cike da mamaki

"Yaushe ta zo?"

"Tun da safe, lokacin baka nan."

"Dauke shi a kai sashen Ammi, ace ta ajiye."

Sake dukawa yayi cikin girmamawa yace

"An gama ranka ya dade."

Juyawa yayi ya koma ciki, yayi wanka sannan ya shirya yana tunanin dawowar Laila a irin wannan lokacin da yasan suna tsakiyar karatu ne. Fitowa yayi ya tsattsakuri abincin ya fita wajen ammi dan be samu ganin ta da safe ba.

A gabanta ya tarar da sakon nasa, ta bishi da kallo sannan ta kalli kwandon da yake na Kaba. Sai da ya zauna ya gaishe ta sannan ya saka aka miko masa basket din

"Ammi kinga ko? Menene ma'anar haka?"

"Ni kaina nayi mamaki, amma kuma kasan dama hakan zata faru idan har ta samu labarin auren ka."

" Bana son wata matsala gaskiya, zan aika da sako wajen Kilishin dan ba zan dauki rainin hankali ba."

" Ka rabu dasu, karka yarda su bata maka rai har kayi tunanin biye musu, ka cigaba da addu'a nima kuma ina tayaka mahaifin ka ma,.ba zasu taba samun nasarar abinda suke so ba."

" Shikenan Ammi, dan Allah aje a kona basket din nan dan bana son ko ganin sa."

" Shikenan, ka cigaba da walwalar ka karka yarda makiyinka ya gane weakness dinka."

" In Sha Allah Ammi."

" Allah yayi maka albarka."

" Amin." Ya amsa yana jin tamkar dawowar Laila akwai wani babban dalili

" Yawwa na kira Fatima akan lefen ka, zata hada komai in sha Allah, idan yaso sai su tafi ita da kai da wata dai cikin su, Takawa ma yace shi zaiyi komai, amma duk da haka Fulani tace yayi nasa itama zatayi nata mu ma nan sai muyi namu."

"Wayyo ni dan gata." Yace yana murmushi

"Ammi gatan kar yayi min yawa ai."

"Ba zai ba, Allah yasa ayi damu kawai, amma dole sirikata taga gata."

"Uhm.. Allah sa idan tazo karta kwace min wajena."

" Dole ne ai, kasan dai yadda nake son ya mace ko?"

" Shikenan sunana sorry wallahi."

Dariya Ammi ta saka

" Aikam ka shirya tun yanzu."

" Shikenan, Muhammad kana ji? Kayi hakuri da duk abinda zaka gani."

Ya fad'a cikin yanayin kalar tausayi, dariya sosai ya bawa Ammi tayi sosai, kallon ta ya dinga yi cikin tsantsar son ta, yana son Ammi da duk wasu halayenta, babu abinda yake so irin yaga tana farin ciki sosai, hakan yake sashi jin zai iya komai dan ganin ya faranta mata, ya dawwamar da farin ciki a kan fsukar ta, hakan kuma ba zai yiwu ba sai dole yaki karbar muradin Bubu, dole ya hakura da mulkin ko da yana so, saboda farin cikin Ammin Sa!

***Satin Mama daya cif a Katsina, ranar da zasu dawo ranar Bashir ya iske su a chan da dalleliyar mota da sha tara ta arziki, murna wajen Mama da Zeenat ba'a magana aka dinga turashi gida gida na dangi dan aga irin mijin da zeenatun ta samo, aikuwa nan da nan magana ta karade ko ina cikin family din Maman, anan wasu da yawa suka samu labarin bikin Zeenat din wanda aka saka wata daya kachal bayan Bashir din ya tabbatar musu da zaiyi komai basa bukatar komai hatta da kayan gida duk shi zai zuba, hakan ya sake fasawa Mama kai ta dinga hura hanci a lallai zeenatun ta ta dallo miji na kere sa'a, tausayi da farin cikin halin da ta tabbata Iman zata shiga idan har ta auri fakirin nan take, gashi dai su kam Allah yayi musu gam da katar dan yadda aka dinga maganar Bashir din a dangi kadai ya ishi Mama tutiya da alfahari.
A motar ya kwaso su Zeenat na gaba gida na tashi cikin taken soyayya Mama da Marwan na baya har Kano, Zeenat ji take kamar tafi kowa sa'a a duniya dan da gaske take jin wani irin son Bashir din na ratsa ta.
Sanda suka isa gida magriba tayi saboda basu taho da wuri ba yana faman zaga dangi, alwala aka kawo masa ruwa yayi, ya zauna Zeenat din ta shiga ta fito suka dasa sabuwar hira irin ta yaushe rabo. Cikin hirar ne yake fad'a mata lefe in sha Allah za'a kawo cikin upper week, zai sanar mata da ranar sai ta fadawa Mama, hakan yayi mata dadi har tana hasashen uban kayan da za'a kawo mata dan taga Bashir din me bajin ta ne sosai.
Ranta fes ta koma ciki bayan ya tafi, ta labartawa Maman lokacin Matar Abba Musa ta shigo wajen Maman yi mata sannu da zuwa.

"Haba ni nayi mamakin da aka ce manyan mutane ne suka zo neman aure gidan nan na tabbata dama wajen Zeenat ne, yarinya kakarki ta yanke saka wallahi."

Tace tana dariya, murmushi mama tayi

" Kice manyan mutane ne suka zo? Bani labari Binta."

" Ai Maman Habib baki gani ba, wallahi manyan mutane ne kamar ma daga wata babbar masarauta, yadda naga mazan gidan nan sun rikice kadai zaka gane ba kananun mutane bane, na zata ma na Iman ne ashe na Zeenatu ne, Baban Walid be min bayanin da zan gane ba kinsan wajen lokaci daya suka zo dukka."

" Aikuwa sune, kai kice dai manyan mutane ne, masarauta fa? Kai masha ALLAH abu yayi kyau wallahi."

" Ai Maman Habib ba karamin dace Zeenat tayi ba wallahi, Allah dai ya kaimu bikin nasan za'a ga lefe na ban mamaki."

" Bari kawaii, sai muzo mu tanadi kyautar girma da zamu fita kunya, na gode da kika sanar dani dan Dr ba lallai ya fad'a min ba muna yar tsama dashi."

" Ai haka suke, basa fadar cikin su wallahi, itama kuma Gajin ba zaka ji daga bakin ta ba tunda komai suna fad'a mata ai."

Tabe baki Mama tayi

" Ai ni baki sani ba, so akayi a yi min bakin ciki."

Sai ta rage murya

" So akayi fa a hana Zeenat auren Bashir din nan, kuma ina kyautata zaton akwai saka hannun Gajin a ciki, toh in ba haka ba yadda Dr ya rikice akan maganar lokaci daya zaki gane zugashi akayi."

Kama baki Matar Abba Musa tayi

" Allah? Tab ashe an so yi miki tsakiyar da ba ruwa."

" Ke dai bari, shiyasa na tsaya kai da fata, kinsan mutane basa son ka cigaba ko aga danka ya cigaba ko zai huta."

" Zahiri, toh Allah ya kyauta, ban yi zaton hakan daga gareta ba."

" Ai ba laifin ta bane, itama yadda aka dora ta haka zata tafi akai."

" Eh kuma gaskiya, tunda kinga ai bata cika saka ido akan al'amuran mu ba."

" Shine, koma waye kansa yayi wa, aure kam babu fashi."

" Assalamu alaikum."

Iman tayi sallama ta shigo, gimtse fuska Maman tayi,ta gaishe su matar Abba musa ta amsa a sake tana tsokanar ta da amarya amarya, murmushin yake kawai tayi tana satar kallon yanayin fsukar Maman, zuwa tayi ta fad'a mata anjima zata tafi wajen dangin Mamanta amma ganin Matar Abba Musa ya saka ta fasa ta wuce kawai daki ta karasa hade koman ta waje daya.
Bayan tafiyar Matar Abba Musa ne ta fito ta samu Maman a kitchen tana rarrabe kayan da tazo dasu dangin su kuka kubewa da daddawa waje daya

"Mama dama yau zan tafi gidan su Mamana."

Tsayawa da abinda tayi, tayi ta kalle ta a mamakance tace

"Yau? Yaushe aka yanke maganar tafiyar taki ban sani?"

"Dama tun ranar da na dawo daga gidan Ya Maryam Abba yayi min maganar."

"Toh! Shi zai kaiki kenan? Ko turowa za'a yi kije? Ko da yake mutanen da basu damu dake ba yaushe zasu turo? Wannan din ma nasan dan Dr yayi magana ne."

"A ah tare da Abban zamu je."

"Kutmar Uba!" Da sauri Iman din ta ja baya dan yadda ta ga Maman ta birkice lokaci daya

" Ni za'a yiwa munafurci? Wato yace zai ganki saboda yaga tsohuwar matar sa ko? Dan an raina min wayo an maida ni wata sakarai. "

" Dama... "

" Dallah rufe min baki, wato gani shashasha an dauko raino an bani shine yanzu za'a nuna min bariki ko? Toh wallahi ba zata sabu ba wallahi kinji na rantse, ko ya barki ki tafi ke kadai ko ya hada ki da wani cikin yan uwansa ko Hafiz ne ma. "

Shiru Iman tayi kamar ruwa ya cinye ta, tana jin sababin da Maman take kanta na kasa ita dai bata ce komai ba,me zata ce ma?

" Bari yazo naji abinda yasa zai munafurce ni wallahi, bayan duk kokaarin da nayi wajen rik'e ki amma sam yanzu baya gani, dan kawai yar matsala ta ratsa tsakanin mu shikenan sai ya rufe ni. "

" Uwata zo ki wuce, kije waje kina da bako. " Abba da yazo a lokacin yace yana kallon Maman, sum sum Iman ta fice kafin Abban ya dubi Maman cikin bacin rai yace

" Kin bani mamaki Hajara, ban zaci haka daga gareki ba."

" Dama ai haka ne, duk abinda mutum yayi ba gani za'a yi ba musamman aka ce da ba naka bane, amma ai Allah ya gani. "

" Bakya tsoron Allah kuwa in dai haka ne, har kece zaki ce Allah yana gani? Kina tsoron haduwar ku kuwa? Bayan wahalar da kika bawa yarinyar nan har kina da bakin magana? "

" Wahala? Ita tace maka na bata wahala kenan ? Oh shine ka shirya zaka kaita wajen uwarta kenan bayan na gama cin wahalar ta, duk abinda nayi baka gani ba. "

" Kiki tsoron Allah, na gano duk irin rikon da kika yi wa Ummi, kinci amanata kin ha'ince ni, Ashe ke din fuska biyu ce dake ban taba sani ba."

" Da yake yanzu hankalin ka ya koma wajen tsohuwar matar ko, ko nace tsohuwar karu... "

A wani irin bacin rai ya daga hannu zai Kai mata mari, fasawa yayi yaji kamar an rik'e hannun zuciyar sa na tafasa, ba ya cikin mazan da zasu daki matar su,baya kuma fatan hakan duk da irin yadda Maman ta bata mishi rai.

"Dukana zakayi Ibrahim? Dukana? Akan na fadi gaskiya, waya san auren da kukayi na gaske ne ko kuwa? Tunda mu dai babu wanda ya shaida, shine zaka dauki hannu ka dake ni akanta ko?"

Ji yayi kansa yana sarawa, be taba tunanin tashin hankalin mAman ya kai haka ba, juyawa yayi da nufin barin kitchen din amma sai yaji ta rik'e masa riga ta baya

"Wallahi ba zaka je wajen ta ba, wallahi ba zan yarda ba."

Tsoro ne ya kamashi jin ta daga murya sosai, da sauri ya fizge rigar sa ya daga kafarsa wajen ficewa daga gidan ma gaba daya, ba zai biye mata ba, har a jisu a gidan abinda zai zamar masa abun kunya a wajen yan uwan sa .
Shashen Gaji ya wuce da ya hango Iman tsaye da Musaddik a chan wajen gate din. Sako ya kawo mata daga Muhammad ya juya ita kuma ta koma cikin gidan.
Tana shiga Mama dake tsaye a falo tana huci ta fisgota, saura kad'an ta fadi amma ta tsaya akan kafarta, kallon Maman take a tsorace dan bata dauka abin nata ya kai haka ba

"Zan ga uban da ya isa ya fita daga gidan nan wallahi, wato kece munafukar kina so ki hada uwarki da ubanki ko? Toh wallahi baki isa ba na gama cin wahalar ki."

Matsawa baya tayi ganin kamar dukanta Maman zatayi, kamar daga sama sai ga Habib kaamr an jeho shi, yayi saurin shiga tsakani yana wa Maman magana,

" Lafiya Mama? Me tayi?"

Bata jira amsar Maman ba ta yi saurin ficewa.
Abinda Abba ya guda sai da ya faru, magana har gaban gaji, mama ta dage ba zai tafi ba shi kuma yace bata isa ta hana shi ba, haka sukayi ta kai ruwa rana karshe ya je da kansa ya dauko kayan Iman din ya bawa Habib ya saka masa a mota sannan suka tafi tana kallo ta cigaba da haukanta.



***Jingina tayi ta rufe idonta a lokacin da suka shiga jirgin, karon ta na farko kenan shiyasa take jin tsoro tsoro amma ta dake dan da wuya kaga abinda zai sa kaga weakness dinta, rashin tsaron da ake fama dashi a k'asar ya saka Affan yi musu booking flight kawai zuwa Abujan dan ba zai yi risking tafiya da Iman din a hanya irin wannan ba. Lokacin ma da Moh yaji labarin tafiyar tata sai da yaji tsoro Allah yasa ba a mota zasu ba, dan har ya gama shirya yadda zai siya musu ticket din kawai ya aikawa abba amma kuma baya so a san shine sai kuma tace masa a jirgin zasu, hakan ya

Please Login or Register in order to submit comment