Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gine-ginen cikin masarautar.
   Ba mota daya suka shigo daga airport din dashi ba, shiyasa ma bata ganshi ha a sanda suke fitowa daga mota. Cikin rakiyar hadiman shashen Ammi da na gidan ma baki daya suka isa babban falon nata, da aka kawata shi matuka ana jiran isowar su. Kamar yadda suka samu tarba ta musamman a Kano haka aka karbe su anan dinma. Hakan ya kara bawa su Mamma nutsuwa da tunanin irin yadda Iman din zata samu kanta a gida irin wannan wanda yake cike da abubuwan da ba lallai ta iya dauka ba.
   Bayan sun huta an gabatar musu da abinci ne Ammi ta saka aka rakasu masaukin su, wanda aka ware musu tun kafin isowar su. A gajiya kowa yake dan haka suna zuwa kowa ya mike aka shiga maida maganar yadda aka karbe su da irin sa'ar da Iman din tayi.
   Tana jin su bata tanka ba, hankalin ta ya tafi sosai wajensa tana son jin yadda yake dan ta tabbata da akwai wani abu da ya rage masa walwala.

***Tun isowar su ta samu labari wanda dama abinda take jira kenan, ta shirya tsaf babu Kuma abinda zai hanata aiwatar da abinda tayi niyya shiyasa ma bata bari Kilishi ta sani ba balle har ta hanata.
   Shigar sa shashen nasa bayan ya bar wajen Bubu hadimar ta, ta sanar mata wanda dama ta saka ta ne ta saka ido tana ganin ya shiga ta fad'a mata.
   Tashi tayi tana gyara gashin kanta da ta saka ribbon din tayi sako-sako dashi, ta daura babbar Alkyabba akan kayan da suke jikin ta da ya kasance karamar riga ce mara hannu iyakar ta guiwa kawai, sai dogon wando a k'asan da ta saka saboda yadda zai zama ko ina na jikinta ya rufe.
   Turaren da yake cikin Jakarta ta ciro, ta dunkule shi a hannun ta, ta fita ta kofar bayan cikin rakiyar amintacciyar hadimar ta. Tafiyar dake tsakanin bangaren Moh din da nasu da akwai tazara dan haka yasa suka bi ta baya har suka isa. Idon ta, ta daga ta dubi bangaren bedroom dinsa amma sai taga dakin babu haske sai sauran dakunan. Zagayo wa sukayi zuwa gaban ginin masu kula da kofar suka tashi ganin ta, da ido sukayi magana da daya, ya girgiza mata kai alamar eh sannan yace

"Yarima na jiranki gimbiya Lailah."

Jin haka ya saka dayan saurin bud'e mata kofar, ta kutsa kanta ciki kai tsaye tana jin kamar anyi an gama ta samu cikar burin ta.
   Tafiya ta ke a cikin falon tana kallon komai, yadda aka sauya komai kamar ba part din da take shigowa a duk sanda ta ga dama ba, babban hoton da ke manne a jikin bangon dakin ta kurawa ido tana matsawa gaban sa. Iman ce a jiki, ita da Moh ranar da aka daura aure, sunyi masifar kyau kamar kayi musu magana su amsa. Wani bakin ciki ne yazo ya tokare mata a makoshi, taji kamar tayi wurgi da hoton ya tarwatse a wajen amma sai ta daure, ta maida hannun ta baya tana nufar bedroom din nasa in da tasan zata same shi.
   Kafin ta karasa ta hango glass cup a k'asa a farfashe, ta durkusa ta dauki ragowar tana kaiwa hancin ta, murmushi tayi tana da yakinin komai ya zama daidai, everything is in order kamar yadda ta tsara. Hakan ya saka ta wucewa Kai tsaye ta murda kofar dakin ta kutsa kanta ciki tana zare alkyabbar da take jikin ta, ta zame a wajen ta fadi.
   Muryar sa da ta soma bacewa yayi kokarin cewa

"Waye!"

Yadda yayi maganar ya saka ta sake tabbatar da komai yayi daidai, basu yi mata shirme ko shiririta ba. Karasawa tayi jikin gadon, ta kai hannu ta taba shi ta hasken bedside lamp da ke kunne, take kallon sa, idon sa yayi masifar komawa ciki yana lumshe su tamkar wanda yake shirin yin bacci irin baccin da yafi karfin sa yake neman kai shi k'asa.

"Waye?" Ya sake maimaitawa da k'yar kansa da yake juya masa ya shiga kai masa sakon mayen kamshin da yaji ya karad'e dakin,kamshin da ya dauke shi zuwa wata duniya ta daban, a take yaji komai ya hargitse masa, ya mike da k'yar yana duban ta cikin ido, gaba daya komai ya chanja masa,ta juye masa Iman dinsa gaba daya. Hannu ya kai zai taba ta, ta saka karbi ta tura shi baya ya fad'a saman gadon!

***Text message ne ya shigo wayar ta, ta bud'e da sauri tana fatan ya kasance daga shi, kamar yadda tayi tsammani, shi din ne kuwa,

_"A rako ki shashe na."_

Haka kawai sakon ya kunsa, kifa wayar tayi tunanin yadda zata fara fadawa Mamma yace a rakota bangaren sa. Da kunya sosai bata kuma jin zata iya,shiru tayi tana wassafa abun a ranta, zuciyar ta na ce mata kawai ta kira mamma ta fad'a mata ai ba wani abu bane, wata zuciyar kuma na ce mata a ah. Ta na nan zaune har aka dau tsahon wani lokaci, sakon ya sake shigowa irin na dazu a karo na biyu, sai dai banbancin lokaci. Amaani ta kira suna zaune suna cin snacks da juice, ta bata wayar tace ta kaiwa Mamma. Sai ta kifa kanta tana jin nauyin Mamma. Tana jin sanda Mamman tazo kanta, tana sababi

"Yanzu haka ake gaya miki anayi Iman? Mijinki yana kiranki tun dazu kika yi shiru. Kunyar me? Zamani ya chanja kinji? Tashi maza ki gyara jikin ki, ga masu kula dake nan da yawa daya sai ta rakaki, tashi maza kina kara bata lokaci."

Tashi tayi kunya na nukurkusar ta,ta dinga sunne kai taki yarda su hada ido da Mamman, tana kallon ta, ta fito mata da wasu kayan tace ta sauya, sannan ta kawo mata wani abu a cup da madara ta bata ta shanye, ta faffesa mata turarurruka masu kamshi sannan suka fito in da yan matan ke zaune, da sauri suka tashi su biyu, suka sakata a tsakiya suka nufin bangaren Moh din da yake da dan tazara da wanda aka sauke su.
   Babu kowa a kofar, kai tsaye ta shiga su kuma suka samu waje daga wajen suna jiran ta dan tace musu ba jimawa zatayi ba, babu kowa a falon babu motsin komai, dakin farko ta bud'e da sallamar ta, baya ciki, sallama take amma ba da karfi sosai ba, a tunanin ta ko ya shiga toilet ta zauna jiran shi, shiru shiru babu alamar sa, ta kasa kunne ko zata ji karar ruwa a toilet sai taji kamar shesshekar kuka, sake kasa kunnen tayi sosai ta tabbatar da abinda taji, sai ta fara tunanin aina take ji, dakin da yake karshen falon ta kalla, babu alamun haske a ciki amma kuma tabbas da ga nan ne sound din yake fitowa. Tashi tayi ta nufi dakin tana taraddadin abinda zata tarar. A hankali ta tura kofar, ta leka da kanta kafin ta shiga da jikin ta gaba daya, tana gama shiga wutar dakin ta kawo, kwakwalwarta ta dauke kamar yadda ake dauke wutar nepa, idanun ta suka sauka akan Moh yayi ruf da ciki a saman gado yana bacci cikin kwanciyar hankali, boxer ne kawai ajikin sa dgaa shi babu komai. Da sauri ta maida kallon ta kan matar dake zaune a kasan tiles din dakin, kanta babu dankwali gashin kan nata da ya hargitse ya barbazu har zuwa saman fuskar ta, shigar jikin ta kawai ta kalla tayi saurin dauke kanta tana kokarin barin dakin, sai dai bata kai ga barin wajen ba dan ko taku biyu batayi ba, taji sanarwa shigowar Maimartaba, bayan sanarwa ne taji shigowar sa.
   Karuwar kukan Laila ya sake sakata cikin yanayin da ta shiga, har Maimartaba ya karaso bakin dakin tana tsaye kamar an dasa ta, bata san me zatayi ba. kallon ta yayi kafin ya maida kallon sa cikin dakin, yayi musu kallo daya wani abu me dacin gaske yana tokare shi a goshi. Juyawa yayi sai a lokacin kwakwalwarta ta kai mata sakon waye wanda ya shigo din, da sauri ta zube a wajen ta gaishe shi cikin muryar ta da take rawa sosai.
   Be amsa mata ba, sai daga mata kai da yayi ya juya ya fice yan rakiyar sa suka bi bayan sa cikin tunanin dalilin zuwan Bubun shashen Moh.
    Kasa daga kafarta tayi daga wajen, ta jingina da bangon dakin tana karanto duk addu'ar da tazo bakin ta, ji tayi kamar ana mata magana, ta dago tana kallon cikin dakin

"Amarya! Kinyi farin gani ko?"

Me zata ce? Shiru tayi tana maida idonta ta rufe shi ruf tana kokarin ajiye abinda ta gani din da kuma abinda zuciyar ta take haska mata waje daya.

"Anya? Anya kuwa? Muhammad? Me ya faru? Me yake shirin faruwa? Wacece wannan din?"

"Karki wahalar da kanki tunanin wacece ni, sunana Laila, gimbiya Lailah."

Yawu me karfi ta hadiye, ta hau kokarin daidaita kanta waje daya, shigowa taji an sake yi, ta daga idonta da sauri wannan karon wata babbar mata ce ta shigo a hargitse, tayi saurin yin kan wadda ta kira sunan ta da Laila tana rik'e ta, tana kallon yadda Lailan ta cigaba da rusa kuka kamar Allah ya Aiko ta, matar na bata baki jikin ta na rawa sosai. Daga ta tayi da sauri, ta yafa mata mayafi ta rik'e hannun ta, suka zo daidai in da Iman din take tsaye, matar tayi mata wani mugun kallo, ita kuma Laila tayi mata murmushin da ta tsaya mata a rai. Fita sukayi tayi saurin zuwa ta sakawa kofar key, ta dawo ta durkusa a k'asan falon ta shiga kuka, kukan da take ta kokarin rikewa dan bata son su ga weakness dinta, dama chan ita mutum ce me taurin zuciya da wuya kaga weakness dinta, shiyasa yanzun ma ta daure har suka fita.
   Sai da tayi kuka sosai sannan ta tashi ta share hawayenta, a kalla zata so taji ta bakin shi, kar ta yi judging dinsa da abinda ko a musulunci babu hujja, dan bata gansu suna aikata wani abu mara kyau ba. Duk da ta na kokarin karfafa jikinta da zuciyar ta akan ta bari taji komai, amma kuma jiki da zuciyar ta ta sunyi sanyi, sanyin da take jin kamar komai ya kare mata, kasan zuciyar ta tana jin zafin sa, tana jin haushin sa amma kuma bata da damar yanke masa hukunci.
   A yan awannin da tayi a cikin gidan nasu ta fuskanci akwai wani Babban al'amari da ya shafi Moh dinta. Tana jin kamar gadar zare aka hada masa har ma da ita. A nutse take duk da abin ya kadata, dan babu matar da zata ga wata mace a dakin mijinta cikin yanayin da taga Laila ba tare da taji komai ba, sai dai ta yarda da addu'a dan haka ta dage sosai har ta soma jin nutsuwa na saukar mata.
   Bata san dadewar da tayi a wajen ba, taji kamar motsi a dakin, ta tashi ta dubo cikin rashin sa'a ta cire takalmin ta, ta taka glass din da yake fashe a wajen, kara tayi hakan ya farkar da Moh gaba daya, ya mike da sauri kansa yayi wani irin sarawa da be taba jin irin sa ba, jiri yaji yana neman kayar dashi yayi saurin komawa ya zauna yana dafe kan, bayan kamar sakan goma ya mike a hankali ya fito.
   A durkushe ya ganta tana rik'e kafarta da har ta fara jini, da sauri ya karaso ya durkusa a gabanta yana kama kafar

"Me ya same ki? Me kika taka."

Kokarin janye kafarta tayi, ya sake kama kafar ya rik'e yana kallon kafar cikin tausayawa.

"Cika min kafata."

Tace ba tare da tasan me yasa ba, kawai ganin sa ya sakata jin haushin sa. Kin cika mata kafar yayi, sai ma daukar ta da yayi gaba daya duk da yadda yake jin sa babu kwari, ya ajiye a gefen gadon ya dauko first aid box din sa yazo ya durkusa a gabanta ya gyara mata kafar Allah ya taimaka kwalbar bata shige ba.

"Yaushe kika zo nan? Ya akayi nayi bacci? Me ya faru aina aka samu kwalba a wajen nan har kika taka? Ina masu kula da wajen?"

Ya jero mata tambayoyin cikin son tuna wani abu, da Ido kawai yake bin sa kamar me son karantar sa, sai dai bata ga komai ba sai tsantar gaskiyar sa a yadda yake maganar. Janye kafarta tayi ta mikar da ita a saman gadon, ya dawo ssman gadon ya zauna yana jan kafar ya dora akan cinyar sa.

"Bacci ne ya dauke ni bayan na sha juice daga nan kuma bansan me ya faru ba, kin dade kina jirana? Da baki tashe ni ba?"

"Bana so na katse maka barci ne." Tace ganin duk ya damu, ajiyar zuciya ya sauke yana matsowa ya gyara mata kafar yadda zata ji dadi, ya mannu a jikinta.

" Kiyi hakuri, kaina ne naji yana min ciwo sosai shine kawai nazo na dan huta bansan zanyi bacci ba."

" Ba komai."

Tace tana rufe idon ta

" Bacci?"

" Umm."

Tace a gajarce dan bata son doguwar magana tana son tattara bayanan da ta samu ta hade su waje daya kafin wayewar gari.

Tashi yayi ya fita bayan ya maida rigar sa,  ya hau k'wala kiran ma'aikatan wajen, da sauri ya shigo yana raba ido, masifa ya fara yi masa akan dalilin barin kwalba a hanya, hakuri yayi ta bashi yayi saurin gyara wajen sannan ya fita.
   Ji yayi duk jikin sa yana masa ciwo, chan k'asan zuciyar sa kuma wani irin feeling ne da be san dalili ba, ji yake kamar idan har be samu abinda yake so ba zai iya rasa ransa, yana wanka yana tunani har ya kammala ya fito daure da towel iya ka guiwar sa, kallon in da take kwance yayi, ta dunkule waje daya kamar me jin sanyi.
   Kaya ya saka sannan yayi sallah ya duba wayar sa yaga misscalls da yawa, ganin dare yayi ya saka shi ajiye wayar ya hawo gadon yana juyo da ita tana kallon shi. Hawaye ya gani a saman kuncin ta, ya saka hannu cikin mamaki yace

"Kuka?"

Kamar wadda take jiran kiris ta shiga rera shi sai dai babu sauti, rikicewa yayi ya hau tambayar ta menene, bata amsa masa ba, ta cigaba da kukan ta wanda ita kanta bata san me yake sake tunzura ta take kukan ba, da farko ta zata zata iya daurewa sai daga baya ta gane duk dauriyar ta wannan ya wuce in da take tunani, kishin mijinta ne ya sakata kuka. Magiya ya cigaba da yi mata akan ta fad'a masa dalilin kukan ta amma taki, rungume ta yayi a jikinsa yana lallashin ta amma kamar kara ingizata yake, ya rasa yadda zai, ga wani irin abu da yake jin yana taso masa. Kasa daurewa yayi ya hade bakin su waje daya, da karfi tayi kokarin turashi ta amma ta kasa!



Rano💕

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)  s_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 
1/31/22, 19:15 - Buhainat: Halin Girma
      23

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

*******
A hankali ya shiga bin ko ina na jikinta yana aika mata da sakonnin shi, kukan da take na taba shi, yana jin har cikin kansa, sai dai ba zai iya controlling kansa ba, abinda yake ji yafi karfin ikon sa, ba kuma zai iya tsere masa ba.
   Da fari ta dauka babu wani abu da zai mata sai son ganin ya rarrashe ta, amma daga baya sai taga abin yana chanja salo. Jikinta ne ya hau rawa ta ko ina, ta sauya akalar kukan nata zuwa magiya da rokon sa, baya jin ta, idan ma yaji ta baya tunanin zai iya yi mata abinda take so din.
   Juyo ta yayi ta zama a saman sa, ya sake hautsina ta zuwa kasansa , ya ajiye mata dukkan karfin sa, ji tayi kamar numfashin ta na janye wa daga jikin ta, ta dinga jansa tana kuka tana kiran sunan sa, yadda yake kissing dinta kamar mayaunwacin zaki ya sake tsorata ta,shi kansa jikin sa rawa yake,ga wani karfi da yake ji ya zo masa wanda be taba jin irin shi ba. Kayan jikin ta ya shiga janyewa yana wurgi dasu ta kowanne angle, har yayi nasarar rabata da komai. Idanun sa da suka rine sosai ya zuba mata yana kallon ta, wani abu yana kaiwa da komowa a tsakanin wuyansa.

"I'm so sorry."

Ya furta mata da k'yar kafin ya shiga aiwatar da abinda yayi niyya.

   Sama sama yake jin ta, cikin muryar da ta shige ciki saboda kukan da ta sha,  kamar mafarki haka yake jin abun, juyowa yayi da k'yar ya dune ta, tana kwance agefen sa taci kuka har ta gode Allah.

"Subhanallah!"

Ya furta yana tashi, abinda ya faru ya shiga dawo masa akai, ya akayi haka? Bayan yayi ma kansa alkawarin zama so gentle, yadda yasan ba zai bata wahala sosai ba, what has gotten in to him? Me yayi mata?
  Rik'e ta yayi yana kokarin daidaita kansa ya samu damar kwantar mata da hankali

"I'm so sorry dan Allah, dan Allah kiyi hakuri ki yafe min, bansan me ya hau kai na ba, this is not me, bani bane ba."

Bata da karfin da zata kwaci kanta, sai kawai ta lafe a jikin sa tana jan numfashi. Kanta ya dinga shafawa a hankali a hankali, yana jin wani irin son ta, na saka shigar sa. Idan har abinda kwakwalwar sa ta dawo mata dashi gaskiya ne, toh lallai sai yaci uban Lailah, dole ne yayi mata abinda ko a hanya ta hadu dashi ba zata nuna ta sanshi ba.
  Idonsa a rufe yana tariyo abinda ya faru, tabbas ya ganta a tsaye a kansa, lokacin da baccin da be san na menene ba dauke shi da sauri. Tunanin sa ne ya koma baya, zuwa sanda ya shigo ya tarar da juice akan table din da ake ajiye masa, a gajiya yace amma ya tsaya ya sha daga nan ne ya fara jin wani abu me karfin gask yana taso masa, sai wani irin bacci me nauyi da be taba jin irin sa ba.

"Desire pills?"

Ya furta yana kokarin tashi, k'ara tayi mara sauti ya tuna tana jikin shi, yayi saurin komawa ya zauna yana sake gyara ta.

" I'm sorry."

Ya saka hannu ya goge mata hawayen da suke sauka a fuskar ta. Tsawon minti talatin yana a haka yana tunanin abubuwan da suka faru a daren, tabbas koma menene an shirya masa abu ne, be san ya akayi ya bada kafa ba, har aka yi galaba akansa. Tashi yayi bayan ya gyara mata kwanciya, ya shiga toilet ya gyara jikin sa, sannan ya fito, ya taimaka mata, ta tashi tana ciccijewa sai dai taki yarda su hada ido, ta hade fuska sosai a dole haushin sa take ji, haushi biyu ne suka hadu waje daya, ta kasa manta abinda ya faru farko da na karshen.
  Toilet din ta shiga sai taga ya biyo ta, ta dube shi tana tsaye gaban bathtub din, ta marairaice fuska, yi yayi kamar be ganta ba, ya rufe kofar ya karaso ya durkusa yana taba ruwan.

"Ka fita."

Ta fad'a muryar ta babu karfi, banza yayi kamar be ji ta ba, ya ciro towel a cikin jerin sabbin towels din dake jere a cikin wata drawer, sannan ya dauko brush da toothpaste ya saka mata a jiki ya ajiye a gefe ya hau nannade hannun rigar sa. Kamar ta rusa ihu haka taji, ta rasa yadda zatayi ta hanashi, bata ga alamar ma zai hanun ba, sai kawai ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido, bata san rashin kunyar namiji ta kai haka ba. Sai da ya gama abinda yayi niyya ya tabbatar yayi mata yadda zata ji dadin  jikin ta sannan ya kyale ta ya fito yana jawo mata kofar.
   Kwanciya ta sake yi a cikin tub din ruwan na ratsa ta, gefe tana tuna abinda ya wakana tsakanin su. Murmushi tayi, duk kalaman sa na dawo mata daki daki, abu daya ne ya tsaya mata har take kokarin alakanta shi da abinda ya faru kafin nan, idan har shi din ba mutumin kirki bane, idan har wani abu ya faru tsakanin sa da Lailah, ba zai sha wahala wajen neman hanya ba.
   Saurin kawar da tunanin tayi kunyar kanta na kamata kamar yana wajen, da wanne idon zata koma wajensu Mamma ma wai tukunna, da wanne idon? Kwankwasa mata kofar yayi ganin ta dade, sai ta tashi tana karfafa jikin ta, ta dauro towel din bayan ta goge jikinta ta fito kanta a k'asa. Ajiyar zuciya taji ya sauke bayan ya kare mata kallo, hankalin sa yaki kwanciya tunanin sa ko yayi mata illa ne, sai yaga akasin haka, be sani ba ko duk cikin dauriyar da ya gane tana da ita bane. Lokacin sallah ake kira a cikin masallacin cikin Masarautar, daga jikin kofar ya tsaya be fita ba, yana kallon ta har ta gama ta saka doguwar jallabiyar sa daya ajiye mata a gefen gadon, murmushi yayi ya fice kansa sanye da farar hula da ake kira da tashi ka fiya naci ya dora doguwar riga irin wadda ya dauko mata.
   A sahun farko ya samu Kamal, daga liman sai shi, hakan ya bashi mamaki amma ya share, bayan an idar suka gaisa a tsattsaye ya fice yana son komawa ya ga halin da take ciki. Sun hadu da Bubu amma be masa magana ba, ya dai ce masa ya sameshi idan garin ya gama wayewa, sai dai yanayin fuskar Bubun ta saka shi tunanin akwai wani abu me girma.
   A saman sallayar ya tarar da ita, ta kwanta akan hannun ta ta mik'ar dashi, karasawa yayi ya daga ta, ya maida ta saman gadon yana zama a gefen ta. Rufe idon ta tayi da sauri jin ya matso da fuskar sa daidai saitin tata. Iska ya fitar me zafi, ya tashi ya kashe wutar dakin ta dawo ya hawo gadon ya kwanta.

"Me ya faru?"

Yayi mata tambayar kai tsaye, yadda yayi sounding zaka gane daga muryar sa, maganar yake so suyi, shiru tayi bata ce komai ba, dan bata san me zata ce ba, tace masa ta same shi da wata a daki ko me? Ta yaya ma zata fara?

"A lokacin da kika zo dakin part din nan, wani ya shigo? Ko kinga wani a ciki?"

Nan din ma shiru ta sake yi masa, kasan zuciyar ta na ce mata kar ta yarda,kawai zai yi amfani da innocent dinta ne ya nuna mata kamar be san komai, daga gefe kuma wata zuciyar na ce mata ta fad'a masa watakila be sani ba, watakila so ake a hada su, tunda har yanxu bata san komai akan sa ba, ba zata iya dorar da wani abu ba balle har ta iya judging dinsa, kawai dai a matsayin ta na mutum me tunani , tana kyautata masa zato.
   Birkitota yayi da karfi muryar sa na fita da dan karfi akan dazu yace

"Tell me, me ya faru? Wani abu ya faru? Kin samu wata ko wani da kika zo? Wani ya fad'a miki wani abu ne? Me ya faru!"

Kuka ta samu kanta da fashewa da, ya tashi da sauri yana kunna wutar dakin, ya dawo ya tashe ta zaune suna fuskantar juna, zuwa lokacin ya ji yana neman loosing temper dinshi.

"Kalle ni, look at me! Menene? Me ya faru da ban sanshi ba? Tell me, waye yazo?

" Maimartaba ne yazo."

" Maimartaba!?" Ya furta da dan karfi cikin yanayin dake nuna tsantsar mamakin sa

"Me yazo yi a part dina? Me yace? Me ya faru? Wani abu ne ya faru while i'm sleeping?"

" Eh." Ta daga masa kai, tsugunawa yayi a wajen yana tattaro dukkan nutsuwar sa, gabansa na faduwa da abinda zata ce dan yasan ba karamin abu bane zai kawo Bubu part din sa.

" Believe me, bansan komai ba, kamar yadda babu alkalami akan me bacci, na rantse miki bansan me ya faru ba."

Goge fuskar ta, tayi da hancin ta a jikin

Please Login or Register in order to submit comment