Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa, ta dago tana kallon kasa tace

" Naga wata Laila a nan."

Ta nuna wajen da Lailan ta zauna

" Lailah!? "

"Eh."

"Ehen, sai me?"

"Tana zaune a wajen tana kuka sosai, daga nan sai Maimartaba ya shigo, sannan ya tafi sai kuma wata mata ta shigo ta daga ta suka fita

   Abu ya hadiye me karfi, ya yi kokarin ganin be yi wani abu ba, a hankali yaji kamar ana masa rad'a

_Be calm Moh, be calm."_

Kamar wanda aka saka abu aka bubbuge ma guiwa haka ya zube a wajen, zai tolerating komai amma banda fushin Bubu, shi za'a wa wannan kazafin? Abinda be taba tunani ko shaawar aikatawa ba, Zina? Shi Muhammad shi aka yiwa wannan sharrin? Saboda yayi kamar be san wani abu yana faruwa ba, shine har aka samu damar yi masa wannan kullin?
  Tana ankare da yadda ya shiga kaduwa, tana kuma ganin yadda Adam apple dinsa ke hawa da sauka tsakanin makogwaron sa, idon sa kadai zaka kalla ka tabbatar da ransa yayi masifar baci.
   Sai da yayi kusan minti goma be ce komai ba, ba dan bashi da abinda zai ce din ba, sai dan yadda mamakin Iman din ya hanashi komai, be zaci haka daga gareta ba, idan wata ce, ba zata iya daukar abinda ta gani ba, har ta tsaya jiran shi, ya ga kokarin ta sosai kuma ya jinjina mata, hakan ya kara mata matsayi a zuciyar sa.
  Girgiza mata kai yayi yana kama hannun ta

"Kin yarda dani?"

" I don't know." Tace tsakanin ta da Allah

"Bansan yadda zan dauki abun na ajiye ba, all I know shine I'm hurt, more than yadda nayi tunanin I ll be."

Folding hannun nata yayi a cikin nasa ya damke.

"I promise to make everything right, koma menene we will over come it, in sha Allah, together we will build tomorrow, I promise you that!"

Shiru sukayi babu wanda ya sake magana, ko be ce ba, ko be ba ita zata gano komai, zata gane kafin ma ya gane, tana da kaifin tunani, sannan tana karantar komai kafin tayi judging din mutum.
   Kwanciya tayi ganin suna zaune kowa da abinda yake tunani, ganin ta kwanta sai ya mike ya fita, ya nufi part din Ammi duk da lokacin garin ke karasa yin haske. Ya san tana zaune har lokacin tana azkar kamar yadda ta saba a ko da yaushe.
   Yadda ta ganshi ya shigo jikin ta, ya bata babu lafiya, katse abinda take tayi ta mike tana kallon sa har ya karaso

"Lafiya Babana?"

"Ina kwana Ammi?" Ya duk'a k'asa ya gaishe ta, kafin ya amsa mata tambayar ta

"Ba lafiya ba Ammi, yarinyar nan Laila tayi abinda zan nuna mata ko ni waye, ganin kamar ban san me take ba ya bata damar aikata abinda ta aikata wanda zai zame mata dana sani, dama chan Ammi kece kike hanani, saboda zumunci amma not anymore."

"Me ya faru?!"

"Bubu be sanar dake komai ba?"

"Be ba, me ya faru?"

Iyakar abinda ya sani ya sanar da ita, jikinta yayi sanyi, ta kuma san Bubu zai iya daukar kowanne mataki akan muhammad din, tun da be taba sanin wani abu daya danganci Laila din ba da shi, ita kawai da Muhamamd din ne suka sani sai Kilishi.

"Babu abinda zai faru, kai dai ka rike gaskiya, zatayi halin ta."

"Shikenan, zanje naga Bubu, zanji me zaice."

"Allah ya taimaka, zanyi magana dashi nima in sha Allah."

Fita yayi ita kuma ta zauna a wajen tana hango abinda zai je ya dawo.

Kasancewar safiya ce, shiyasa ya shige kai tsaye wajen Bubun, a lokacin ya fito wajen shashen bayan sallah yana duba wasu littattafan sa. Sai dai yau ya kasa yin komai, tunda aka fito masa da littafan ya kasa taba ko guda daya, balle har ya karanta, abinda ya gani jiya yayi masifar girgiza shi, ya kada shi sosai, har yayi furucin da yake jin idan har Muhammad be wanke kansa a tsawon kwanaki biyar ba, ko da yana da gaskiya ya zama dole ya auri Lailah tun kafin maganar ta fito waje, a jita a ko ina.
    Aji ya samu da maganar a lokacin dan ji yayi yana neman faduwa k'asa, sai dai yadda yayi tunanin maganar zata taba Aji sai yaga akasin haka, yana zaune kem fuskar sa bata chanja ba ko kad'an, har sai da Bubun ya kasa daurewa ya tambayi Aji dalilin da be ji abun ba, murmushi yayi yace.

"Ahmadu kenan, da Muhammad da Laila su dukkan su nawa ne, ni na haifi iyayensu na kuma san kowa a cikin su, na san abinda kowa zai aikata da wanda ba zai aikata ba, duk da yanzu ance baa shaidar mutum, amma ni zan shaidi Muhamamd ko aina ne, lallai akwai wani al'amari bayan abinda kai din ka gani."

"Amma kuma komai ya nuna, a yadda na ganshi naga Lailan, bani da hujjar kare shi ko yarda dashi, idan har nayi haka sai naga kamar banyi wa Yaya adalci ba, mutane zasu ce ko dan babu shi. "

" Duk abinda zakayi karka tuna mutane dan dama su baa raba su da abin fad'a, kayi gaskiya kawai. "

" Toh ta yaya zan yarda da Muhamamd be aikata ba? Da wacce hujja zan yarda dashi? "

" Ka bashi lokaci, ya kare kansa, idan har ya amsa laifin sa shikenan, idan kuma ya kawo hujja gamsasshiya toh."

" Idan har muhammad ya kasa kawo hujjar bai aikata abinda ni da mahaifiyar Laila muke tunanin ya aikata ba, nayi alkawarin aura masa ita a tsakanin kwanaki hudu! "

  Dawowa yayi daga tunanin yadda suka kwashe da Aji yayi, ya bata rai sosai sanda Moh ya dire a gabansa, cikin girmamawa ya gaishe shi, amma sai yaki amsawa, ya kausasa murya yace

" Ban kiraka nan dan ka gaishe ni na amsa ba, ban kuma kiraka nan dan muyi doguwar magana ba, me ya faru tsakanin ka da Lailah? "

" Babu komai Bubu. " Yace kai tsaye dan dama ya riga ya shiryawa tambayar

" Babu komai? "

" Eh babu, duk abinda ka gani sharri ne, bansan komai akai ba. "

" Waye shaidar ka? "

" ALLAH! "

Ya fad'a kai tsaye, shiru Bubu yayi, ya dauki wani lokaci kafin yace

" Ka dauki alaka ta da kai ta d'a da mahaifi ka ajiye a gefe, ka kalle ni a matsayin alkali da aka kawo min kara ka, na baka nan da kwana hudu ka kawo min kwakkwarar hujja, idan har kwana hudu ya wuce babu komai, nayi maka alkawarin aura maka Laila! "

" Aure?!!! "

" Aure, tashi ka bani waje."

Jikin sa a sanyaye ya tashi, ya fice cikin sauri sauri ya nufi part din Lailan, yana tafiya yana huci, ji yake kamar ya dauko bindiga ya harbe ta, mutanen da suka fara fitowa wanda suka kasance masu aikace aikace a tsakanin parts din suka hau mamakin ganin Moh a irin lokacin shi kadai babu wani tare dashi. Be same ta a bangaren nata ba, tana bangaren Kilishi,juyawa yayi zuwa bangaren Kilishi yana ayyana kalar rashin mutuncin da zai yi musu.
     Sai da ya kusa zuwa sai kuma zuciyar sa tace yaje yayi musu me? Yafi karfin haka, ba girman sa bane, dan haka sai kawai ya koma nasa part din yana lissafin kwanaki hudun da Bubu yace, yasan zai iya yin komai ba kuma sai karya alkawarin sa ba, idan kwanakin suka cika bashi da wata hujja. Abu na karshe da zai iya shine auren Lailah, gwara ya hakura da komai akan ya aure ta.
    Bacci ya sameta tanayi, baccin da yasan na wahala ne, duk tausayin ta ya kamashi, shi da yaso ta huta sosai kafin ta fara sanin komai amma sai gashi daga shigowar ta gidan ta fara da karo da abinda yafi komai muni. Peacefully take baccin,fiye da wanda tayi jiya, a kalla yanzu ta samu kwanciyar hankali bayan ta sanar masa da abinda yake damun ta, yasan tayi dauriya sosai.
   Kissing goshin ta yayi, ya gyara mata kwanciyar ya koma dayan side din ya kwanta da tunanin kwana hudu

Rano

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)  s_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107
2/1/22, 10:25 - Buhainat: Halin Girma
      24

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

Sai da rana ta daga sosai sannan ta farka, da sauri ta mike tana mamakin dadewar da tayi tana bacci ita da ya kamata ta koma wajen su Mamma. Sakkowa tayi tana jin jikin ta da dama-dama, ta shiga takawa a hankali zuwa toilet din dakin,ta wanko fuskar ta, ta fito ta gyarata sannan ta cire jallabiyar tasa ta maida kayan ta, ta ajiye masa a gefen gadon ta fito zuwa falon. Tunanin yadda zata iya komawa wajen su Mamma take da kuma yadda zatayi da kunyar da take ji daga zuwa ta dawo sai kwana bayan ba haka ya kamata ba a ganinta. Abin takaicin ma bata dauko wayar ta ba balle ta kira, tana tsaye tana tunanin yadda zata fita taji maganganu a kofar part din,wajen window ta isa, ta daga curtains din tana son ganin komai. Gabanta ne ya fadi, tayi saurin cika window din a daidai lokacin da taji suna karasa maganar su. Kyakkyawa ce ajin farko, kana ganin ta kaga bafulatanar adamawa, yau ba kamar jiya da ta soma ganin ta ba, tana cikin shiga me kyau harda Alkyabba, tayi kyau fuskar ta fes alamun tana cikin farin ciki. Kokarin daidaita kanta tayi sanda taji an turo kofar an shigo, idonsu ya hadu lokaci daya, wani banzan kallo Lailan ta watsa mata tana karaso wa ciki a gadarance, ta samu saman daya daga cikin kujerun falon ta hakimce baiwar ta,ta gyara mata k'asan rigar sannan tace ta fita ta basu wuri. Tana fita ta kalli Iman irin kallon sama da k'asa kafin tace

"Barka da rana amaryarmu."

"Sannu." Kawai Iman din tace ta juya zata bar wajen amma sai ta dakatar da ita

"Nace ba, ya kika ji da kwanan bakin ciki? A ranar farkon ki a dakin mijinki?"

"Bakin ciki kuma? Na me kenan?" Ta tambaya Kai tsaye kamar bata gane me Lailan take nufi ba

"Na abinda kika gani mana, bakin gani, kinga true color din so called mijinki ko?."

" Ohh, wannan wasan kwaikwayon wai? Yayi kyau sosai ya kuma tsaru yadda ya kamata, sai dai shi actor din be san kan wasan ba dan be ma san me yake faruwa ba, shine kawai matsalar film din amma yayi kyau."

"Me kike nufi?" Tace a hasale tana mikewa tsaye

" Abinda kika sani shi nake nufi, kin dauka zan yarda da banzan plan dinki? I'm not an illiterate, I can tell when someone is lying, beside mijina ba zai taba aikata abinda kika ikirarin ya aikata, and i trust him yadda bakya tunani."

"Wow! Wow!! Wow!!! Sannu da kokari, I love your confidence, amma wanne irin sani kikayi masa haka? Da har zaki bashi irin wannan yardar? Kinsan waye namiji kuwa?"

" It doesn't matter yaushe na sanshi, all that matters now shine, miji na ne, kuma nayi trusting nashi, dari bisa dari."

" Shikenan, sai muga yadda zakiyi depending mijin naki at this critical condition, let's see how far you can go...."

" Kwana hudu kachal kike da, idan har baki samu way out ba. Ki shirya karba ta a matsayin kishiyar ki, sannan na fitar dake ta karfin gaske, dan baki da waje a gidan nan, captain nawa ne right from the start kuma he will always be mine."

Murmushi Iman tayi mata, tana jin wani irin tsana da haushin Lailan, tana jin zata iya komai, idan tace komai tana nufin komai domin taga ta fitar da shi daga koma menene, akwai babban kalubale a gabanta, amma ba zata karaya ba, duk wanda ya rik'e Allah da addu'a ya gama, da ikon Allah sai tayi galaba akan duk wani makiyin su. Ta daina shiru, duk wanda yace mata kule! Zata ce masa chas! Ita kanta bata san tana da courage din da zata iya maida mata martani ba, sai gashi.

Juyawa tayi ta koma bedroom din dan ba zata cigaba da bata lokaci akan wadda bata tunanin tana da hankali ko kad'an. Wayarta ta gani ajiye a saman chest of drawers ta dauka ta kira Mamma da k'yar, sukayi magana ta ajiye ta zauna tana lissafin rayuwar da zatayi a irin wannan gida, tuna sanda ake mata fad'a irin na bankwana tayi, wata Babar su Abba tana ta jaddada mata hakuri da kuma shirya wa duk wani kalubale na gidan sarauta, karta bari a takata kar kuma ta cuci kowa, akwai makirci sosai wanda zata gamu dashi amma idan ta nutsu tayi hakuri da karfin addu'a Allah zai bud'e mata komai.
   Bata jima a zaune ba taji ana mata knocking, ta tashi ta bud'e ta fito, russunawa tayi har k'asa da sauri ta gaishe ta, kunya ta kama Iman din ganin Matar da zata yi kusan sa'ar Mama tana gaishe ta a haka. Kaya ta mika mata cikin girmamawa tace ta chanja zata rakata bangaren Fulani (Ammi) juyawa tayi ciki, dan dama kayan jikin ta sun dame ta sosai. Sai da ta shirya tsaf  sannan ta fito, ta lura Laila ta jima da barin falon sai dai mayen kamshin da take yana nan a falon. Kai tsaye shashen Ammi suka wuce wanda sai a sannan ne ta sake karewa fadar gani sosai. Anan suka tarar da su Mamma da wasu mutanen wanda da yawan su kana kallo zaka gane alakar su da gidan saboda yanayi na kama da suke da juna. Shigowar su ya saka kowa maida hankali kanta kowa na son ganin amarya, tunda jiya babu wanda ya samu ganin ta saboda dare. Kanta a k'asa taki yarda ta dago saboda yadda take jin kamar ta nutse, a tunanin ta duk sun san daga in da ta taho, bata san Mamma bata fad'a ba sun dai barshi a zuwan sun barota ne tana shiryawa. Sai da duk suka lafa ne aka zazzauna sannan ta gaida Mamma da take kallon ta da murmushi, murmushin da ita kadai ta san ma'anar sa, hakan ya sake saka Iman din cikin jin kunya.
  Sanda ta shigo Ammi bata falon, tana zaune suna magana da Amaani ta dawo, da sauri Iman din ta zamo daga kujerar ta gaishe ta, ta rik'e ta, ta mik'ar da ita tsaye tana amsawa a sake sosai, sannan ta saka a raka Iman din part din Kilishi.
   Hannun ta cikin na Amaani suka shiga, babu kowa a falon farko sai wata baiwa guda tana goge-goge,wadda ta rako su ce tace su zauna sannan ta nufi kofar ciki don sanar da zuwan su. Jim kad'an ta dawo ta tsaya a gefe, zuwa wani lokaci Kilishin ta fito, fuskar ta kadaran kadahan ba zaka gane komai ba, Iman bata kalle ta ba, ta gaishe ta cikin girmamawa ta amsa a yatsine bata ma zauna ba.

"Hari wannan din itace sirikar tamu?"

"Itace ranki ya dade."

"Lallai sannu yarinya, shi ko Muhammad ya rasa wa zai dauko mana sai yar karamar yarinya haka? Ko da yake ra'ayin sa ne ai, ba kuma a san ya akayi ba dai, ko da yake dama dai yaran talakawa sai a hankali, idon su idon me arziki sai in da karfin su ya kare, sannu kinji? Allah ya bada zaman lafiya."

Sai ta juya

" Hari naga amarya, ki gaida uwar dakin naki."

Wani abu ne ya tokare wa Iman a makogwaro, idan har ta fahimci maganganun matar tana nufin asiri tayi ta aure shi kenan, a fakaice ta ci mata mutunci babu gaira babu dalili, bayan bata san ta ba, idan banda jiya sai yau ne karo na biyu da ta taba ganin ta. Ajiye ta tayi a daidai mazaunin da da ajiye Laila, ta kuma kuduri aniyar zama dasu daidai da yadda suka zaba.
  Daga nan sai suka wuce bangaren Aji da Hajja, amma a mota saboda tazarar dake tsakanin bangarorn biyu, sosai taga karamci da girmamawa dan Adam, Hajja kamar ta goye ta saboda murna, ta dinga tsokanar ta da ta kwace mata miji da rana tsaka, murmushi kawai Iman din take, hakan ya janyo suka dade sosai a bangaren har zuwa sanda taji sallamar sa, ta dago suka hada ido sanda yake shigowa ciki, jamfa da wando ne a jikin sa kalar sararin samaniya, ya tsaya iya kar guiwar sa, kansa sanye da hula me kalar duhu, yayi kyau sosai, da sauri ta janye idon ta kunyar abinda ya faru daren jiya na hasko mata, murmushi yayi me kyau ya karaso ya zauna kujerar dake fuskantar ta. Hajja dake nade a saman wani cushion me laushi ta tabe baki tana dubanss

"Saboda rashin kunya shine ka biyo bayanta ko?"

"Toh ya zanyi? Kin rik'e min ita kin hanata tafiya."

"Ah lallai, shine ka biyo baya kazo kaga ni, toh ba zan cinye ta ba ai."

"Kai yar tsohuwar nan kin fiye rikici wallahi, kishi ne nasan yake damunki ba wani abu ba."

Dariya tayi tace

" Ai na bar mata kai tuntuni, kuje ku karata nima Amadu na ya ishen."

A tare duk suka yi dariya, ya kashe mata ido daya tayi saurin dauke kai kamar bata ganshi ba.

" My wife!"

Yayi kiranta a hankali karaf sai a kunnen Hajja, ta banka masa harara ya sosa kai

"Dan nema, kin hadu da aiki kinji Fatima, mijin nan naki bashi da kunya sam, bari kiga na tashi, taso yan mata muje na baki wani abu ki bar wadannan."

Tashi Amaani tayi tabi Hajjan, suna shigewa yayi saurin komawa kusa da ita.

"Ka ganka ko?"

"Me nayi?" Ya tsare ta da ido yana marairaice fuska

"Gashi nan ka kori Hajja."

"Rigimar tace kawai fa, mun saba irin haka da ita."

"Toh ka koma chan ka zauna."

" Wai kunya ta kike ji? Ko kunyar Hajja?"

" Both!" Tace tana kauda kanta

Murmushi yayi kawai

" Kinsan me? Bubu ya bani kwana hudu na kawo masa gamsasshiyar hujja, idan ban kawo masa ba, zai aura min Laila."

Sak tayi, duk da Laila ta riga ta fad'a mata amma ji daga bakin sa ya sakata shiga yanayi,

" Karki damu, hakan ba zai faru ba, I promise you that!"

" Allah ya bada sa'a." Tace a sanyaye

" Zan je Abuja anjima ko gobe da safe zanyi kwana biyu, na dawo"

" Tafiyar ba zata bamu matsala ba?"

" In sha Allah."

" Shikenan, Allah ya kaimu ya dawo da kai lafiya."

Tayi shiru tana tunanin yadda zata taimaka masa ta taimaki kanta dan ba zata taba iya zama da Laila ba a yanayin ta.

***Idan tace tayi bacci a ranar tayi karya, tun bayan fitar matar gidan da kawayenta bata sake nutsuwa ba, kuka take tun tana yi da hawaye har ya zama babu hawayen sai suya da zuciyar ta, take kamar zata fito. Da asubar fari taji ana buga kofar dakin amma a hankali, tashi tayi da k'yar tana jin jiri jiri saboda yunwar da ta kwaso ta zare sakatar dakin. Da sauri ya shigo ciki ya maida kofar ya rufe yana kallon ta, matsawa tayi baya tana masa kallon tsana

"Karka matso nan wallahi zan iya illataka, ka maida ni gidan mu wallahi ba zan zauna anan ba."

"Rage muryar ki dan Allah, kar taji, kiyi hakuri zan yi kokari naga na lallabata ta bar mu, mu koma gidan mu dan wallahi a matse nake, kinsan dai mutum da sabuwar amarya."

"Wallahi bazan koma ko wanne gida ba, gidan mu zaka mayar dani ka sake ni kuma, ba zan zauna da kai ba na tsane ka."

Saurin damkota yayi, ya toshe mata baki yana hade jikin su waje daya

"Idan kina daga murya wallahi zamu dade a haka, idan ta gano na sato hanya nazo ni dake duk ba zamu fita ba, yanzu ki kwantar da hankalin ki, ki bita duk yadda tace zan dinga shigowa nan din da asubah tunda bata tashi da asubah sai gari yayi haske sosai."

Fizge kanta tayi tana masa mugun kallo

"Na tsane ka, na tsane ka Bashir har bansan iya adadin tsanar da nayi maka ba, Allah ya isa cutar dani da kayi, kasan dama kana da mata amma shine ka auro ni, wallahi sai ka sake ni ko na jawo maka abinda zaka dade kana dana sani."

"Baby!" Yaji muryar hajjajun tasa tana k'wala masa kira, jikin sa ne ya hau rawa yayi hanyar fita hankalin sa a tashe,kafin ya karasa ta turo kofar cikin shigar kayan bacci masu shegen kyau, tayi musu wani kallo kafin ta kama hannun sa tana murmushi

"Kana nan ashe, toh wuce muje ko?"

"Toh;" yace yana yin gaba.

"Ke kuma, ki fito ki fara min aiki kafin gari ya gama wayewa, akwai menu na kalolin abincin da nake son gani kullum a saman dining bana kuma so ki wuce karfe goma baki gama komai ba."

Ta juya tana karkada mata mazaunanta ta buga kofar. Hawayen bakin ciki ne suka sakko mata, ta share tana shiga dan kurkutaccen bandakin da ke gefen dakin ta dauro alwala da k'yar sboda yadda yake wani shegen wari ta shinfid'a dankwalin ta, tayi sallah akai sannan ta bi ta hanyar zuwa kitchen din dan ta tabbata idan har ta sake muguwar matar ta dawo bata fito ba zata iya nada mata shegen duka babu abinda ya dameta gashi babu me kwatar ta dan shi kansa Bashir din ba abakin komai yake ba.
  Menu din ta dauka tana kallo, babu abu daya daga cikin kalolin girke-girken guda biyar da ta iya a ciki, tasan dai tabbas Iman tana yi musu dukka a gida amma ita bata taba ko da sha'awar gwadawa ba, daga indomie sai tea sune kadai take yi, sai yar taliya ko macaroni shima ba kullum ba, duk wani girki me wahala kamar su tuwo da sauran su.

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)  s_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or

Please Login or Register in order to submit comment