Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aiko a tafi dasu, ba'a dade ba kuwa sai ga wani saurayi yazo a golf irin ta hayar nan, dole suka saka Habib bin bayan su da wasu kayan bayan ya dauko yar kurkura dan yawan kayan kadai sun isa a yiwa wasu amaren biyu amfani dasu bayan Zeenatun.
   Sanda suka shigo unguwar gaban kowa ya hau faduwa, basu gama shiga masifa ba sai da suka ga kofar gidan da aka tsaida, katuwar kwatar dake kwance a kofar gidan ce ta fara tsorata su. Haka suka daure suka fito ya bud'e musu gidan suka shiga.
   Babban tashin hankali sanda suka shiga gidan suka tarar da kayan da suke gidan da Bashir din yace ya saka mata kaya kar ayi komai, su kansu kujerun bayan yadda aka daina yayin su, ba set bane dan babu three seater ko kankantar falon ya hanata shiga ko kuma ba'a yi da ita ba oho.
   Sanda suka shiga kitchen din sai da suka kusa kurma ihu, kwatan kwatan abinda Maman ta siya ba zai shiga kitchen din ba. Babu wanda yake wa wani magana a cikin su, suka saka abinda zai iya shiga kitchen din da ko kitchen cabinets babu, sauran na amfanin suka saka mata a cikin sip dan wannan ba za'a kirashi da wardrobe ba sai da sip😢😂 ragowar kayan suka juya dasu cike da tunanin yadda za'a kare da Mama. Babu maganar uban kayan turaren wutar da ta siya wajen hadaddiyar me turaren wutar nan*yerwa incense and more.*
     Shigowar su kenan suka tarar ana ta hotuna da Iman, jiki a sanyaye suka wuce bangaren Maman suna taraddadin yadda za'a kwashe. Mama ma jin ance sun dawo ta yi zumbur ta tashi, sai dai tun kan su gama zama ta san da matsala.
   Aunty Maimuna ce ta jata daki tayi mata bayanin komai sai ragowar kayan da tace an loda su a motar Aunty Muhibba dan kar a shigo dasu saboda yan saka ido.
   A k'asa dirshan ta zauna, ta cire dan kwalin ta da take jin yayi mata nauyin gaske saboda yadda kanta ke masifar sarawa

"Amma Bashir ya cuce mu, ya cuci rayuwata, yanxu dan Allah wannan abun kunya da me yayi kama? Na shiga uku."

Ta jefar da hannun ta gefe,

"Be kyauta ba gaskiya, ha'inci ne wannan kuma, sam be kyauta ba."

Aunty Maimuna dake kokarin bata baki ta fad'a duk babu dadi

" Allah ya isa ban yafe ba wallahi,shege macuci. "

"Kiyi hakuri Yaya Hajara, cuta dai Bashir ya riga yayi mana ita sai dai muyi hakuri, mu lallaba a kai ta idan yaso daga baya idan hankalin kowa ya dauke sai musan abinda ya kamata. "

Wani kallo tayi mata, kamar ma ta rufe ta da duka take ji

" Sai bayan an kai ta ya gark'ama mata ciki sannan ne kike tunanin zai rabu da ita? "

" A ah Yaya, kinga wai ai dai yanzu daga daure aure yau ai ba za'a ce ya saketa ba, kinga hakan ai kema zai iya baki matsala da Dr. "

" Matsala ta nawa kuma? Ni yanzu ya riga ya fita daga kaina, ta yata kawai nake, dole na bata farin ciki ko ta halin Kaka. "

Shiru kawai Aunty Maimuna tayi dan ba kuma tasan yadda zatayi ta bawa Maman hakuri ba. Aunty Muhibba ce ta shigo, tace maman ta tashi ta gyara jikinta Iman da mijinta zasu shigo. Kamar ta danna ma Aunty Muhibban ashar taji dan dai akwai kunya tsakanin su kasancewar ta matar babban wansu, dole ta tashi ta wanko fuskar ta a bathroom ta shafa mai da yar hoda ta saka kwalli sannan ta fito.

***A zaune take ta tankwashe kafar ta akan dan carpet din da yake jikin gadon dakin, ranta a bace yake tun bayan da ta samu labarin auren da Yarima Muhammad zai, taso ta tada hankalin ta amma Kilishi ta hanata, yanzu gashi tana ji tana gani an daura.
 
"Laila!"

Ta kira sunanta tana daga zaune a gefen makeken gadon ta, da ido ta kalle ta ba tare da ta amsa ba, ta mike tsaye. Sanye take da doguwar gown ja, sai gashin ta da yake a tattare a waje daya da yasha gyara na musamman.

"Yaushe zaki koma?" Ta ta da tambayar bayan tasan amsar da zata bata. Da ido ta sake dubanta, ranta na sake baci tace

"Na dawo kenan."

Da sauri ta mike daga gishingid'ar da tayi, ta dauka zata ce mata soon zata koma kamar yadda take bata amsa a ko da yaushe idan tayi mata maganar komawar.

"Kinsan me kike cewa? Ba zaki koma ba? Me yasa?"

"Ba zan koma ba har sai na samu cikar burina. Ni ce na chanchanta da zama a wajen da aka bawa yar talakawa, wadda bata da komai da kowa. Yarima nawa ne ni kadai babu kuma wanda ya isa ya dakatar dani."

"Har ni?" Tace tana zaro ido cikin mamaki

"Duk wanda yayi kokarin shiga hanya ta, ko waye kuwa, ko da Bubu ne!"

Tsam kilishi tayi a in da take tsaye ta kasa cewa komai. Tana son Laila tamkar yadda take son Kamal,sai da tafi son Kamal ya gaji ubansa akan yadda ita Lailan take so. Sai dai idan taga da gaske Kamal ba zai samu sarautar ba, toh zatayi duk yadda zatayi ta samu Laila ta shiga rayuwar Muhammad din.
   Juyawa Lailan tayi cikin takun ta na isa, ta bar dakin. Da kallo Kilishi ta bita ta girgiza kai

"Ba zan taba barin ki da tsarin ki ba har sai na ga da gaske plan dina ba zai yiwu ba, wanda bani da shakku, Kamal shine zai gaji  ubansa a ranar da suka shirya bawa dan gatan dan nasu. Maimartaba da kansa zai yi fushi dashi, fushi irin wanda be taba yi ba!"

Dariya ta saki ta koma ta zauna tana harda kafarta, indai tana numfashi Muhammad ba zai taba sarauta ba wannan alkawari ne da tayi wa kanta.

****
    A gajiya Bubu ya dawo, shiyasa be samu ganin kowa ba ya shige turakarsa. Tun da wuri Ammi ta shirya tana jiran sa dama,aiko yana dawowa ta tafi dan tana so su karasa maganar da ya fara yi mata ranar basu samu damar gamawa ba
   Har ta karaso ta zauna be bar kallon ta ba, babu wani babban chanji akan sanin da yayi mata a dah da nayi yanzu, jikin ta me kyau ne zaka rantse bata ajiye garkamemen saurayi kamar Muhammad din ba.

"Barka da zuwa gimbiya a fad'ar Ahmadu."

Yayi mata kirarin da ya saba mata tun zamanin kuruciyar su. Dariya tayi ta zauna tana dora tray din da ta shigo dashi a saman table.

"Sannu da zuwa, kun sha gajiya. An rabu da taro lafiya da kowa?"

"Lafiya Alhamdulillah, Takawa yayi matukar kokari sai dai muci Allah ya saka masa da alkhairi."

"Ai dama yace shine uba, kuma shine kuma kaka, mu yan kallo ne kawai."

Murmushi Bubu yayi yace

"Gaskiya kam ga zahiri nan mun gani ai."

"Allah ya basu zaman lafiya, har na matsu su tawo nan wallahi."

Hannu ya kai saman hancin ta ya lakace mata fuska yace

"Ko kunya, dan farin."

"Kuma dan auta ba."

Sai suka saka dariya a tare.

"Allah dai ya basu zaman lafiya da zuria dayyiba, kwanan nan zaki ga yan duguiw duguiw suna yawo a tsakiyar masarautar nan, lokacin na dawo gida nima na huta kamar Aji, kinga sai kawai na dinga kallon su ina jin dadi." 

" Allahu ya sa, Allah ya nuna mana. "

" Amin. " Yace yana hasaso lokacin idan da rai da lafiya

" Ka gama yanke shawarar nad'in ranar juma'a din? "

" Haka muka tsara da Aji kuma na sanar da Takawa shima yayi na'am da hakan. "

" Kana ganin babu matsala? "

Rik'e ta yayi a jikin sa, yasan me take tsoro take gudu kuma

" Babu komai in sha Allah, babu abinda zai faru. "

" Aikin sa fa? "

" Ajiye shi zai kinga ba zai yiwu a hada ba ai. "

" Amma... "

" Ki tayashi da addu'a har ma dani din ma, idan ban ajiye mulkin nan ba hankali na ba zai taba kwanciya ba. "

" Allah ya nuna mana, Allah yasa ayi lafiya a gama lafiya. "

" Yawwa ko kefa, addu'ar kenan. "



#Rano💕



*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)  s_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107
1/25/22, 10:41 - Buhainat: Halin Girma
      19

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

**************
Ta cikin ido Moh ya kalli Mama da ya lura kamar tsaiwar na neman gagarar ta tunda aka fara daukar hotunan, gashi sai dauka ake an ki dainawa itama a cikin yanayi take da saura kad'an ta zube a wajen idan aka cigaba da daukar hotunan. Sai da ya tabbatar da tayi masifar kaiwa karshe har tana neman fito da abinda yake zuciyar ta ne sannan yace ya isa haka, tayi saurin fadawa daki babu ko magana, hannun Iman din ya kama a gaban kowa, suka juya suka bar part din yana jin a kalla Mama zata yi hankali, a kalla zata san rayuwa da yadda take juya wa bawa.
    Tafiya sukayi bayan sun yi sallama akan zuwa magriba za'a zo a dauki Iman din. Sake chanja kaya tayi zuwa wasu kayan na daban, suka zauna cikin yan mata da sauran yayan da aka ma aure a family aka dinga hira cikin farin ciki. Bata saka musu baki sai dai tayi murmushi musamamn da ya zama kusan rabin maganar akan zaman aure ne wanda take jin kamar wasu maganganun sun girmi kanta.
   Gabatowar la'asar ya sake saka Iman din a cikin yanayi fargaba, irin wanda ake ji idan za'a rabu da gida. Tashi tayi ta ja Khadija suka fita zuwa shashen su, tana son ganin Zeenat sannan tana son daukar wasu abubuwan a dakin su.
   Shigowar su ya saka kowa na falon bin su da kallo, kai tsaye dakin Mama ta wuce Khadija na binta a babu yadda zatayi. Kusan zabura mama tayi ganin ta, ta tamke fuska tamau tana jin haushin shigo mata da tayi a halin da take ciki. Har kasa ta duk'a, ta gaida Maman sannan ta gaida su Aunty Maimuna. Duk sun amsa banda Maman da tayi kamar bata ji ba, tashi tayi bayan nan ba tare da wata magana ba ta wuce zuwa dakin su. Tayi mugun mamakin ganin Zeenat din, sai taji tausayin ta ya kama ta, ta durkusa a gabanta tana tuna lokacin da ta taimaka mata da bata jin dadi.

"Zeenat?"

Ta kira sunan ta, sai a lokacin ta san sun shigo dakin ma. Da ido tabi Iman din kamar taga sabuwar halitta,

"Iman?"

"Na'am, baki da lafiya ne? Kin ganki kuwa Zeenat?"

"Bani da lafiya Iman, bana jin dadin komai, wallahi bana son auren nan gashi an riga an daura, tsoro ma nake ji kar naje na aikata wani abu mara kyau."

" Me ya faru? Me yasa bakya so?"

" Bashir karya yayi min, babu gaskiya a maganar sa, bashi da komai fakiri ne wallahi."

Shiru Iman din tayi dan bata san me zata ce ba, tunanin yadda akayi hakan ta faru take, sai dai bata san yadda zata dauki maganar ta kuma ajiye ta ba. Kuka Zeenat din ta sake fashewa dah, kuka dacin da take jin sa a chunkushe a makoshin ta. Baki Iman din ta dinga bata, ta samu da k'yar tana maida numfashi. Tashi Iman din tayi ta duba wajen da ta ajiye jakar islamiyyar ta, ta dauka sannan ta sauki abubuwan da tasan zata bukata ba kaya ba. Khadija ta bawa ta tafi kai mata wajen Mamma sannan ta dawo ta cigaba da kwantar wa da Zeenat din hankali.
   Kamar ba Zeenat ba da take taka Iman din tayi mata duk wulakancin da ta ga dama, tayi laushi sosai,har tana dora kanta a kafar Iman din.
   Wayar hannun ta ce tayi k'ara,  Moh ne yake kira, dagawa tayi tana tashi daga gaban Zeenat din

"Amaryata."

"Umm." Ta turo baki, dariya yayi sosai kafin yace

"Ki cigaba da turo bakin nan, babu ruwana aka samu matsala wallahi"

Murmushi ta samu kanta da yi, ta jujjuya kanta tace

"Kaiko?"

"Me nayi?"

"Ba komai."

"Sharri kawai zaki min dan kin ganni bawan Allah."

"Nima ai baiwar Allah ce."

" Na yarda kuwa, are you ready?"

" Mefa?"

" Shigowa fadar Moh."

" Ummm."

" Get ready kinji? Yanzu zasu zo, kwana biyu zuwa uku zamuyi anan sai mu wuce adamawa."

" Adamawa?" Tace tana zaro ido

" Calm down, zan miki bayanin komai."

" Shikenan." Tace a sanyaye

" That's my wife, Allah yayi miki albarka."

" Amin." Ta amsa tana sakin murmushi a hankali.

Kashe kiran yayi, Zeenat ta bita da kallon sha'awa, tana hango tsantsar dacewar da Iman din tayi, gashi ita ta tashi a tutar babu.

"Zeenat bari na tafi, zamuyi waya in sha Allah, kiyi hakuri dan Allah ki kwantar da hankalin ki."

Jumbur ta mike, ta rik'e jikin rigar ta tana goge kwallar da ta zubo mata

" Dan Allah Iman karki tafi ki barni, wallahi ba zan iya zama da Bashir ba."

" Me yasa? Bakya son sa ne wai dama?"

" Wallahi bana son shi, ko kad'an wallahi laifin Mama ne."

" Iman!" Taji muryar Mamma a kofar dakin tana kiran ta, juyawa tayi ta fita tana kallon Zeenat din cikin tausayawa

" Ke kuma daga zuwa daukar abu sai ki zauna? Kinga ai lokaci yayi ko?".

Bata ce komai ba sai kawai tabi Mamman suka bar bangaren, ranta babu dadi ko kad'an.

   Wanka mamma ta sake sata tayi, kayan da zata chanja ta tarar a dakin, an turara mata su da turarurruka masu dadin kamshi. Tana shiryawa tana tunanin halin da Zeenat din take ciki, yadda ta firgice ta shiga tashin hankali zaka gane akwai wani abun a k'asa, ba wai kawai dan Bashir din bashi da hali bane kamar yadda ya Maryam ta bata labari.
   Duk shirin da tayi da taimakon su Harira, aka kuma kawo wata sabuwar alkyabbar aka dora mata, tayi kyau ainun, babu make-up babu komai amma yadda fuskar ta take sheki kadai zaka gane ba karamin gyara tasha ba.
 
   La'asar likis sai ga jama'ar gidan su Bashir, motoci goma ne gaba daya har data amarya , yadda za'a samu kowa ya je har mutanen unguwa, a lokacin babu irin kiran da be yiwa Zeenat din ba akan gasu nan amma bata dagawa, shiyasa kawai ya kyale ta domin shi a yanzu ba ta ita yake ba, yadda zasu kwashe da hajiyar ce kadai matsalar sa, labari ya riga ya kai mata ya kuma san gamon su bazai taba yin kyau ba, gashi akwai wasu kudade da ya ta bashi da nufin zai mata wani aiki ya bi ta kansu.
   Hankalin Mama ne ya kara tashi sanda suka iso, ta tabbatar da gaske Zeenat dai sai ta tare gidan Bashir, kiran Abba tayi, kafin ma ta fadi komai yace

"Ina falon Yaya idan kun gama ki turo min Zeenatun."

Daga haka ya kashe kiran, cikin sanyin jiki Mama ta nufi dakin su Zeenat din, ta tarar da Aunty Maimuna na ta fama da ita akan ta tashi ta shirya, ganin shigowar Mama ta saka ta saurin tashi ta nufi wajen Maman.

"Jeki shirya Zeenat, kiyi sauri Mahaifin ku yana kiranki."

"Mama?"

"Ya zanyi? Ya zanyi? Aure an riga an daura ba kuma zan je na chakumi wuyan Bashir nace lallai sai ya sake ki ba, tunda kuma an daura ai dole ki tafi, dole ki bishi shine mijinki, ya zanyi."

Fashewa tayi da kuka, tayi saurin fadawa toilet din ta rufo kofar, danne zuciyar ta sosai Mama tayi, ta juya ta bar Aunty Maimuna a dakin ta kuma jaddada mata kar su bata lokaci. Mamaki sosai Aunty Maimuna tayi da yadda Maman ta dake, amma kuma ta hango tsantsar tashin hankali a tattare da ita.
   Da k'yar ta taimaka mata ta fito ta shirya har lokacin kuka take, kaya kawai ta saka sai turare babu batun powder ko makeup. Lullube mata fuska Aunty Maimuna tayi suka fito, kai tsaye aka wuce da ita wajen Abba. Su uku ne a dakin daga shi sai Abba kabiru sai Abba (Babba) nasiha suka soma mata, me shiga ciki akan rayuwar da zata shiga sabuwa, yawanci magana daya ce hakuri wanda Zeenat din ta kasa fahimtar su, bata gane me suke cewa balle ta san a wanne mazauni zata ajiye maganganun nasu ba, har suka gama bata fuskanci komai ba, hankalin ta ma baki daya baya wajen su ta tafi tunanin kalar rayuwar da zata fara a gidan Bashir din. Sadakin ta Abba ya dauko a aljihun ta ya mik'a mata

"Gashi zeenatu,Allah ubangiji yayi miki albarka ya baku zaman lafiya."

K'asa karba tayi, ta fashe da kukan da take ta rikewa, mikewa Abba yayi ya fice daga dakin zuciyar sa na tabuwa, yana jin kamar ya dawo da hannun agogo baya a lokaci da ya dinga nunawa Zeenat din illar abinda take shirin aikatawa. 
   Abba Kabiru ne ya karbi kudin a hannu Abba yace

"Barshi Yaya, bari wani cikin yaran nan sai yaje ya saka mata shi a account, idan yaso bayan komai ya lafa sai ta ciro tayi amfani da abinta."

"Hakan ma yayi, shikenan zeenatu kudin ki za'a saka miki shi a account kinji? Ki daina kuka."

Tashi tayi da k'yar tana gid'a kai kamar gadangaruwa ta fita, daga nan ne kuma kowa ya firfita dan zuwa kai ta gidan Ango Bashir. Sai dai duk mutane suka gama shiga mota sannan aka fito da ita aka sakata a mota, tana kuka Mama na yi haka aka tura ta a motar. Dangin Bashir din sukayi ta mamakin abinda yake faruwa dan kowa ya ga kukan yasan ba kawai na rabuwa bane akwai wani abu daban.
    Shiru kake ji a motar babu motsin kowa kamar ba ma mutane a ciki. Wata Yayar su Abba ce da Aunty Maimuna suka sakata a tsakiya, hannun ta na damke ana Aunty Maimuna tana cigaba da kukan ta a ciki ciki. Har suka karaso bata daina kukan ba. Sauran jama'ar motar ne suka fiffito, kowa tayi cirko cirko suna jiran a nuna musu gidan Zeenat.
  
***Text message ne ya shigo wayar Bashir din, ya duba yana sauri sauri dan yana so yaga Moh kafin tafiyar da zai yi,

_"Ina jiran ka kaida kanwar tawa a gida, na saka an gyara muku daya daga cikin dakunan nan. Sai kunzo." _

Gaban sa ne yayi mummunar faduwa, yayi sakale rik'e da wayar yana tunanin mafita, be shi da niyyar hada Zeenat da Hajiya Layuza gida daya, amma kuma be isa ya ki kai ta ba dan komai zai iya faruwa. Kiran ganin sa Ghali yayi ya tabbatar da sun karasa, yace idan kafa ta dauke ya kirashi ya sanar masa. Yana kashewa yayi mata reply da an gama hajjaju sannan ya saka wayar a aljihu ya fita yana sauri
    Yadda dakunan suke kananu ya saka gidan ya chunkushe, kowa so yake yaga abinda zai samu na dorarwa a gaba, masu bud'e kitchen masu bud'e toilet har da masu bud'e rijiya dan tabbatar wa.
    Aunty Maimuna ce tace kowa ya fita za'a koma gida saboda zuwa kai Iman, mutane suka hau saurin fita dan kowa ta kama motar da taxo amma suna fita suka ga wayam babu ko mota daya duk sun gudu,. Nan fa waje ya rude kowa ya hau tofa albarkacin bakin sa, yan uwan Mama suka shiga tashin hankali dan babu abinda yafi ciwo a debo mata a kawo su gidan amarya a watsar dasu, komawa cikin sukayi aka tilastawa Zeenat kiran Bashir din, be daga ba har aka gaji da kiran sa suka hakura suka fita, aka fara tunanin yadda za'a yi kowa ya koma gida.. saukin ta ma dama duk cikn garin ne dan tuni wasu ma sun dade da tafiya sun tari napep. Wanda suka rage ne dole su Aunty Maimuna suka san yadda sukayi kowa ta samu abin hawa. Sai yada habaici da bakar magana suke musamman yan uwan Abba da Mama ta bata wa rai tun a farkon fara bikin.
   Sanda suka gama dawowa gida magriba ta kawo kai, a lokacin ne kuma motocin masarauta suke jere kansu a cikin layin wanda ya kasance tun daga farkon layin har karshen sa. Motar da za'a dau amarya daban take ta gaji da haduwa, anyi decorating dinta tayi kyau.
  

Gashi nan na biya bashin na ranar Friday.

  

#Rano💕

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)  s_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107
1/25/22, 10:41 - Buhainat: Halin Girma
      20

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

**************
Gaban Iman din ne ya dinga faduwa sanda taji tashin algaita da bud'a a lokaci daya, rik'e hannun Mamma tayi tamau bayan sun dawo daga wajen su Abba da wajen Gaji. Zaunar da ita Mamman tayi tace tana zuwa Amaani tayi saurin dawowa ta manne kusa da ita hakan ya saka ta dan ji dama dama. Mukullin motar da Abba ya damka mata a hannun ta da wasu abubuwan ya sakata shiga yanayin da ta shiga, har yanzu bata bar mamakin yadda abubuwan suka sauya salo ba, wanda bata taba tunani ko hasashen hakan zai faru da ita ba.

    Bayan kamar minti biyar sai ga Mamma nan ta dawo ta kalli sauran tace

"Matar nan bata da kirki sam, bansan me yake damunta ba, amma ni dai na fad'a mata lallai ta shirya tazo ta kai Iman dakin ta, idan ma wani abun ne yake damun ta ko hassadace ita ta sani, na dai bata girmanta."

"Toh ai Mamma kina gani kinsan bakin ciki take, dama kin kyale ta kawai mu kadai mun isa."

"Ai ba haka ake ba, mu muka zo muka same ta kuma duk tsiya dai itace marikiyar Iman din."

" Toh yanzu zata je din ko yaya?"

" Ban san mata ba wallahi, na dai fita ai ni dai,ruwanta taje ruwanta taki zuwa, babu abinda za'a fasa."

" Wallahi kuwa, Allah ya kyauta."

" Amin." Tace tana zama.

     Kayan Iman din aka gama fitarwa, aka saka a booth din motocin, sannan suka shigo da kansu su uku, suka ce sun zo daukar amaryar su, akayi barkwanci dai tsakanin su da su Mamma sannan suka fita su kuma su Mamma suka fito da Iman din.
    A harabar gidan suka hadu da Mama, ta yafa mayafi ita da Aunty Muhibba, kallo daya Mamma tayi mata ta dauke kai suka fice, bayan su suka bi, suka tarar an gama tsara mutanen kowa ta samu mota ta shiga, kowacce mota da kayyadadden mutanen da za'a saka kuma kowa ya samu an shirya komai yadda ya kamata.
   Motar amarya ce kawai ta rage sai guda daya da tazo a karshe, wasu ne suka shiga dayar tare da Aunty Muhibban sai Mamma da Mama suka shiga ta amarya suka sakata a tsakiya kamar yadda ake yi. Chan jikin kofar motar Mama ta makale taki yarda ta rabi Iman din, jawo ta sosai Mamma tayi jikin ta ta dora kan Iman din a saman kafadarta ta kwanta sosai.
    Lamido Crescent suka nufa in da nan ne ainihin gidan Iman din, sojojin da ke zube birjik a gaban gidan ya saka mutane sake jinjina lallai Babba ne Muhammad din, gida ne hadadden gaske wanda dama chan a nan Muhammad din yake amma an masa gyara sosai da ba zaka taba cewa ba a lokacin aka gina shi ba. Tsaruwar gidan da yadda aka kawata faluka da dakunan gidan da kaya na alfarma ya kusan saka Mama shan k'asa, ta rik'e hannun Aunty Muhibba dan da gaske ta tsorata da yadda taga gidan. Falo biyu ne daya sama daya k'asa sai dakuna biyu a sama, uku a k'asa kuma kowanne Masha Allah kaya ne aka zuba na alfarma, kar Azo batun kitchen wanda duk yadda Mama ta kai ga kure siyayyar ta sai taga ta raina kanta, komai na ciki unique ne ga wasu shegun electronics wasu ma bata san menene amfanin su ba. A daddafe ta daure ta shiga ko ina dan yadda kowa ya zura ido a kanta kowa so yake ya ga yadda zata shiga dimuwa ko ma ta kasa

Please Login or Register in order to submit comment