Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗauko min ruwan gora, ta buɗe wani bokiti ta ɗibo min cincin da ta ajiyemin a gaban wani tabur dake gabana, har yanzu bata zauna ba naga ta wuce ciki, bata jima ba sai gashi ta fito hannunta riƙe da plet na abinci, mai ɗauke da shinkafa da miya da vegetable, ta ajiye a gabana.
"Kici ƴata nasan ba lallai kinci abinci ba "
"To "kawai nace na fara cakular abincin kamar wacce take koyo,
Ban wani ci da yawa ba na ajiye cokalin nasha ruwa, ina jira inji musabbabin kawoni gidannan amma har yanzu banji tace "komai ba ",
Sai da muka ɗau tsawon lokuta a zaune kafin naji tace "kece Ilham ko ?"
Na amsa da "eh hajiya nice "good babanki ne yasa a taho dake a bisa yardarsa akan cewar zaki fara aiki a gidannan, da kuɗin da za'a biyaki a kaishi ayi masa magani ",
Gabana na tsanannta faɗuwa idona ya kaɗa yayi jajir nace "eh na sani ina Abban nawa ?"
Hajiyar tace "yana hospital ana yi masa aikin ƙafar ",
"Wato har Abba yakai kansa batare da ƙara shawartata akan ko na amince da aikin na ko ?hmm lallai Abba ",
Na faɗa ina ce mata "to Hajiya ko zan iya ganinsa ?",
"Eh zaki iya ganinsa sai dai ba'a gidannan yake ba yana asibitin Murtala ", a razane na dafe ƙirji tare da cewa "asibitin Murtala kuma ashe abin yayi yawa, nida akace yana asibitin gidannan "na faɗa ina share hawayen da suke ambaliya a fuskata, Hajiyar ta ɗaga waya ta danna number driver, bai jima ba yazo ya durƙusa a gabanta, cikin bada Umarni Hajiya tace "ka kai Ilham asibitin da aka kwantar da babanta, driver yace "an gama hajiya taso muje "na miƙe jiki a sanyaye, dole nabar kayan anan na wuce muka shiga mota muka lula asibitin.
Muna isa, driver yayi parking tare da cewa "kiyi sauri lokacin ziyara ya kusa ƙurewa "nayi azamar fitowa, yana gaba ina binsa a baya, har muka shiga wani ɗaki mai lamba 5, muna shiga na hango Abbana a kwance an naɗe ƙafarsa da bandeji , iya yau ya rame sosai, nikam na rasa ganewa shin ciwon ne ya tashi ko kuma shine ya kawo kansa har yanzu ban sami mai bani amsa ba, tarin da naji yanayi ne ya sani ƙarasawa kusa dashi ina cewa "Abba sannu ya jikin "
Cikin murya irin ta marasa lafiya Abba yacemin "jiki da sauƙi na warke yau akayi aikin zuwa jibi idan sunga jikin ya warke sunce zasu sallamemu ",nace to alhmdulilh Abba yanzu gidan aikin kenan zan koma ?"Abba yacemin eh man ai sai kinyi na wata bakwai ",na zaro ido, saboda kar in tayarwa da Abbana hankali yasani ɓoye damuwata nace masa karka damu Abba, lafiyarka ta fiyemin komai a duniya, farinciinka shine nawa, samun lafiyarka itace farinciki na "Abba ya shafi kaina yana sanyamin Albarka, shigowar likitan dake dubashi ne yasa na koma kan kujera, sai yanzu driver yace "baba ya jikin dai ?" Abba ya amsa fuska a sake, "na sami sauƙi alhmdulilh ",
Driver yace "zamu wuce toh "babu inda na iya haka muka dawo gidan su Hajiyar, wannan karon na sameta ita da wani saurayi wanda nake tunanin kamar na san fuskar, nazari na shigayi tare da tinanin a ina na taɓa ganinsa ?",
Kyakkyawan saurayi ne dogo fari tass ɗan shekara 32yrs fuskarsa masha Allah, a taƙaice dai shiɗin ba mummuna bane,
Kansa na kan cinyar hajiyar yayinda gangar jikinsa ke kan kujera 3 sitter, da sallama na ƙarasa kafin nace "hajiya mun dawo "Hajiyar na faɗaɗa fara'arta tace "ƴata zoki zauna ", ta nuna min kujera mai zaman mutum ɗaya, yaron nata da naji ta kira da my son naji yace "momy wannan kuma wacece ?",hajiyar ta shafi kwantaccen gashin kansa kafin tace ",ka mance maganar da akayi da dadynka jiya akan ƴar aiki da kuma rashin lafiyar mahaifinta ?"gani nayi ya taɓe baki haɗi da galla min harara, nikuma sunan data kirani dashi ne yai mugun ɓatamin rai, wai ƴar aiki mtsw.
"Oh momy yanzu taje ta gyaramin part ɗina Ibrahim na nan zuwa anjima "waro ido nayi, sbda a halin yanzu na ganoshi sarai, ga kuma yanayin maganarsa kamar ta mace, wato shine ko ?"lallai zan gasa maka aya a hannu " na faɗa ina kawar dakai daga kallonsu.
Nasan shikam bai ganeni ba, amma ni na ganesa, sbda wannan ƙaton gilashin danasa wanda ya mamaye ilahirin fuskata, jira kawai nake inji hajiyar tace "tashi ki tafi ", amma shiru ina zaune kamar gunki, ganin hajiyar bata sake wai-wayata ba, yasani kallon TV badan ina fahimtar abinda akeyi ba, kawai dai mutanen dake drama nake kallo a tashar arewa24.
Bayan wasu sa'oi,
Najiyo muryar hajiyar na cewa "ke Ilham jeki gyara part ɗin my son anjima yanada baƙo "na amsa da toh "dama burina inbar gurin nagaji da zama agurinsu,
"Ina ne part ɗin?"
"My son oya jeka nuna mata yau tazo fa ",
Fuska a yamutse haɗi da kallon ƙyama da wulaƙanci, ya yaso bai cemin komai ba ya fita a ƙofar shigowa palon Hajiyar nima na bishi,
Mun ɗanyi tafiya sannan naga mun iso wata ƙofa mai ɗauke da mudubi, yana zuwa ya danna wani abu a jikin bango naga ƙofar ta buɗe, ya shiga nima na shiga, irin haɗuwar palon hajiya kusan iri, ɗaya da nasa, amma a nashi palon akwai wani tangamemen Frame mai ɗauke da photonsa wanda ya baiyanar da kyawun fuskarsa, gashi gunin ban sha'awa murmishi yake, niko nace "duk wannan cin maganin da yakeyi dama yana dariya ?",
"Inkin gama nuna ƙauyancin kizo ki wanke min toilet ki gyaramin ko ina nabaki 30mins "rai a ɓace na kallesa sai kuma na sunkuyar da kai, banason in nuna raina ya ɓaci ya sami damar turamin haushi, batare daya nunamin toilet ɗin ba ya fice yana waƙa ƙasa-ƙasa.
Zubewa nayi akan kujera tare da zuba tagumi nace "shikenan na ƙanantar da kaina na shiga uku, koma zagina mutan gidan sukayi haka zan daure Allah ka wadatamu ",
Cikin azama na miƙe na buɗe wata ƙofa wacce nake da tabbacin nan ne bedroom ɗinsa, sbda gado dana gani da mudubi da drowa, gadon na fara gyarawa kafin nace na wanke toilet nama rasa ya zanyi in tsara abinda zanfara, duk abinda yazo min shi nakeyi, tashi ɗaya na gama gyara komai cikin hanzari na kunna burner nasa turaren wuta ƙamshi ya game ɗakunan duka..!


*💥GUNTUN GORO..!💥*


_Zainab habib(Mom Islam_


Domin samun complete a arewa books danna wannan links ɗin👇
https://arewabooks.com/u/momislam22

_Zainab habib(Mom Islam_

Free page 5-6

Ina shirin ficewa naji yace "kee..! ",
Tsayawa nayi cak ba tare dana juyo ba, kewai me kike taƙama dashi ?"naga alamun kinada girman kai, oya shiga ki dafamin indomie ",
Wannan maganar da yayi ne ta sani juyowa na kallesa naga ko a jikinsa, so yake yi ma yaci gaba, karo na farko da na fara yi masa magana kenan nace ",bawai dan nazo gidanku aiki shi zaisa ka dinga wulaƙantani ba, ni bana ɗaukar raini so ka kiyaye ?"
Duk wannan maganar da nakeyi a tsorace nake yinta saboda cikin ƙarfin hali nake yinta,
Tashi ɗaya na ga fuskarsa ta rikiɗe kamar ta mahaukacin zaki ya fara tunkaroni, yunƙurun guduwa na farayi, amma ina sai naga ƙofar ta rufe ruf na kasa buɗewa, fitsari ne kawai bai zubomin ba, nashiga tashin hankali, da kuma nadamar gargaɗin da nayi masa,
Nayi tsammanin zai yimin duka har in kasa tashi, sai kuma naga ya shareni ya koma kan kujera ya zauna, tare da dakamin tsawa yace "ficemin a ɗaki tunda bana ubanki bane, ni bazaki kawomin rainin wayo ba, karki manta mahaifinki na asibiti kuma muke da ikon yi masa komai, wallahi kinji na rantse sai kinyi nadamar wannan rashin kyautawarda kika yimin" nocking ɗin da akayi ne yasa shi cewa "yess waye ?"batare da mai nocking ɗin yace komai ba ya shigo yana cewa "Mubin..."
Mubin ya faɗaɗa murmishinsa kamar ba shine mai surfamin ruwan masifa ba, ni na rigada na ganeshi har shima Ibrahim ɗin na ganeshi amma ban nunar musu da hakan ba, jira kawai nake suɗan kauce daga bakin ƙofar in wuce,
"Mubin kace ka kamo mutuniyar a hannu.."
Cikin rashin fahimta Mubin yace "kaifa ɗan iska ne banaso kajamin rini wannan ƴar aikina ce ",
Ibrahim na dariya yaja hannun Mubin ina tsaye ina kallonsu, suka zube akan kujera ni kuma nayi hanyar fita, abin mamaki banji yayi yunƙurin hanani ba na fice da sauri,
"Mubin wato ni zaka rainawa hankali ko?, masifar ma bata bar kaina ba, kai kenan kullum cikin faɗa, naga inda matarka zatayi "Ibrahim ya faɗa yana tuntsirewa da dariya,
"Kaga idan ba maganar arziƙi bace ta kawoka kaficemin banason sakarci "
"Ya kuma zaka miƙe ?",
Ibarahim ya faɗa yana kallon Mubin,
"Waccar banzar ce ta ɗora indomie kaga ta fice tunda bata da asara ",
"To jeka duba nidai ina jiranka kasan jibi nefa ya kamata ace daga yau mun kammala komai "
Ba tare da Mubin ya sake magana ba, ya wuce kitchen ya juyo indomie a plet yasa fork ya kawo gaban Ibrahim ya ajiye akan wani kyakkyawan table,
"Bismillah "
Mubin yace yana yiwa Ibarahim nuni da hannu.
A tare suka fara ci, ba wani sosai sukaci ba, Mubin ya buɗe fridge ɗin dake gefensa ya fiddo musu da Chivita ya zuba musu a glass cup suka sha,
Hamdala sukayi kana aka ture table ɗin gefe, Mubin ya miƙe, Ibrahim na kallon ikon Allah, dinning yaje ya buɗe flaks ya tsiyaya ruwan zafi a ƙaramin cup ya jefa lifton tare da buɗe gwangwanin madara ya zuba da milo da zuma, yana shirin sake zubawa a wani cup ɗin Ibrahim yace "mr acici nidai na ƙoshi kasha kai dai "hararasa Mubin yayi yasa ƙaramin cokali a cup ɗin ya taho yana juya tea ɗin ya zauna a kujera mai kallon ta Ibrahim,
Sai da ya gama yangar shan tea ɗin sannan ya ajiye cup ɗin, duk da bai shanye duka ba, ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya kafin yace "ina sauraronka ?",
Ibrahim ya fara magana kamar haka...
M .M CHICKEN REPUBLIC.Na buƙatar sabbin ma'aikata, kasani nasani wannan taron da zamu sakeyi shine zai sake ƙaro mana dubban masoya suso abincin mu, mu muna Kano su kuma suna Legos gashi dady yana egypt kuma dole jibi taron zai kasance tunda anriga anyi sharing ɗin invitation cards tun tuni ".
Mubin yayi gyaran murya kafin ya shafi gefen fuskarsa kafin yace "Da farko zamu haɗa taronne akan inda suke gudanar da al'adunsu, na biyu kuma zamu gudanar da taron dan samun ɗaukakar company ɗinmu, abinda nakeso dakai shine, ka binciko mana yanayin bikin yankin nasu da inda suke gudanar da aiyukansu, da kyaututtukan da sukafi jin daɗi da so idan anyi musu ",
Cikin farinciki Ibrahim yace "Insha Allah, kasan inda naji daɗi kuwa?",
Yana maganar yana kunna data ya hau whtsapp na wayarsa yana magana da wani abokinsa mai suna Muhammad Alfa,
Sai da suka jima suna tattaunawa kafin naji yace "Alhmdulilah an wuce gurin saura wani kuma "ya ajiye wayar yana murmishi.
Kallonsa Mubin yayi yana sauraron abinda Ibrahim zaice,
Fuskar Ibrahim wasai yace "a al'adarsu, idan mutum na neman ɗaukaka ta hanyar kasuwanci ko wani abun to sai yanada mata ",
Waro ido Mubin yayi kana yace "aiko ban shirya aure yanzu ba, inaga zamu ɗaga taron har sai dady ya dawo sai suje da momy "
Ibrahim ya murtuke fuska kafin yace "kasan daraja da girman cika alƙawari kuwa ?kanaso a mayar damu ƙananun mutane? kanaso su mayar damu masu karya alƙawari ko ?",
Mubin ya buga table ɗin gabansa kafin yace "mtsw wannan ka'idojin sunyi yawa ni bazan ɗauki iskanci ba just a fasa kawai bazan iya ba "
Ya miƙe yana mita, shima Ibrahim ɗin miƙewa yayi ya riƙe hannunsa suka fice suka je part ɗin momy,
Momy na ganinsu tahau murmishi tana cewa "Ah yarana kun fito kenan ?"
Ganin Fuskar Mubin babu wal-wala yasa momy cewa "my son mekuma ya faru ?" Ibrahim ya kama hannunsa ya zaunar dashi kana yace "momy akan maganar taron da zamuyi na M.M CHICKEN REPUBLIC shine yasawa kansa damuwa, alhalin abun ba wani mai wuya....
Kafin Ibrahim ya rufe baki Mubin ya karɓe da cewa "kai wawan ina ne, nacema an fasa taron ko ana dole ne, nifa babu wani taro da zani da mace sai kace bunsuru, wallahi zan koma india dama zamana a Nigera tsautsayi ne "
Mubin ya faɗa yana dafe kansa sbda bai iya zuciyaba ko kaɗan,
Zama momy tayi kafin tace "Ilham ki kula da abinci a kitchen "
"To "nace kafin naci gaba da haɗa miyar stew dake kan gas,
Cikin lallashi momy tace "my son bakason ci gaban dadynka ne?" karka manta fa, Ibrahim ba ɗan gidannan bane kawai dai yana sonka ne har yake taimaka maka"
"Ibrahim yace" Momy an kusa kiran sallahar la'asar nakusa tafiya",
Mubin da sai yanzu yayi magana yace "naji zanje amma bada wata mace ba, to idanma da macen ne ai babu wacce zamuje da ita "momy tace "gaskiya yanzu yawanci sunakaratu amma akwai shawara guda ɗaya bansan yazaku ɗauketa ba, sun mayar da hankalinsu ga momy suna jira suji abinda zatace,
Sai da momy ta jinjina maganar sannan tace "mezai hana Ilham ta shirya a zuwan matarka, da zarar kun gama hidimrku sai kudawo gida, ko ya kagani Ibrahim?"
A zuciye Mubin ya miƙe yana huci cikin ɗaga murya yace"bazan lamunta ba, bana son raini bana ƙaunar talaka ya raɓu dani ",
Momy tayi murmishin takaici kafin tace "Mubin babu wanda ake haifarsa da arziƙi haka kowa da abinda Allah ya tsaga masa yake zuwa duniya, talakawa kuwa dole ka sosu tunda harkar kasuwancin ku sai kun sakosu, yakamata ka sani Allah baya ban banta talaka da mai kuɗi, dan me zaka dinga yiwa Allah haka, sbda kana ganin kai ya wadataka su ya barsu a talaucinsu ko? to kar in sakeji ".
Shidai wannan taron da za'ayi akansa an gama ɓata masa rai, kuka ne kawai beyi ba, tsabar takaici.
An kaɗa an rawa anyi lallashin akan ya amince su tafi da Ilham amma yaƙi amincewa sam,
Gashi jibi ne taron .
Momy ce ta janyo system ɗinta ta hau whatsapp bayan kuna data da tayi cikin sa'a taga dady yana online, batare da sunyi tsammanin dady zatayiwa magana ba, kai tsaye ta danna video call, sukaji momy na cewa "habiby barka da hutawa, gaban Mubin ne ya bada rass yaja baya dan kar dadyn ya hangoshi, momy tace "habiby kana aiki ne ko kana free naga tulin files a gabanka" dady yayi murmishi kafin yace "ko ina aiki ai dole in ture file sbda nasan akwai important thin" sassanyar ajiyar zuciya momy ta sauke kana ta juya da system ɗin gurin fuskar Mubin da Ibrahm kafin tace", ka gansu ko inata fama akan maganar taron da ka sanar Mubin zai wakilta a madadinka, shi da kansa yasa Ibrahim ya dubo abinda sukafi so da abinda ke kawo ɗaukakar mutum lokaci ɗaya, to alhmdulilh an binciko Mubin yace shi bazai amince ba" inaga sai ka dawo ne ko kuma me kake ganin za'ayi ?",
Dafe kai dady yayi kafin yace "to shiba aure ba dawa zai tafi?, yayi gaggawar zaɓo budurwa nan da yamma su tafi tare 😂niko nace idan kaƙi sharar masallaci...
Ibrahim yana daga gefe sai da dariya taso kufce masa.
Dady yaci gaba da cewa" ina Mubin ɗin?"
Mubin ya taho kamar wanda ƙawai ya fashewa a ciki ya zauna gaban system ɗin kafin ya ƙaƙalo fara'ar dole yace "barka da wannan lokacin dady ya aiki ..,
Dady ya amsa da "kaji saƙona ko..?
Mubin yahau sosa kansa kafin ya shagwaɓe fuska yace" dady bani da budurwa.., batare da jin nauyi ko wani abu ba dady yace "aiko zaka yita dan wannan taron shine karo na farko munaso sunan gidan abincinmu ya zagaye duniya amma kana ɗaukar abin wasa ko ?",
Mubin da hankalinsa ya gama tashi ya juya ya kalli momy ko zatace wani abu, sai yaga ta janyo system ɗin tayiwa dady murmishi dan ta kwantar masa da hankali kana tace" Habiby akwai yarinyar da aka kawo aiki in baka mance ba, kunyi magana da mahaifinta, to ta riga da tafara zuwa aikin dan a halin yanzu ma tana gidannan kuma budurw ce mai kyau inaga su tafi da ita kawai, a zabure Mubin ya kalli momy, taci gaba da cewa "habiby ya kake gani ?",
Dady ya washe baki kana yace "wow kin kawo tunani mai kyau, eh yakamata ayi mata magana muji ko nawa take buƙata sai mu bata just na rana ɗaya ne "Ibrahim yace "shawara tayi masha Allah, momy ni zan tafi, my man abinda kukayi anjima zan kiraka ",
Mubin ya zabgawa Ibrahim harara kafin yace "to muna fuki ",
Momy tace "Mubin bana son sakarci jeka rakashi"
Mubin ya miƙe yabar momy tana magana da dady,
"Ki lallaɓa Mubin fa, dan akan rashin gabatar da taron nan wallahi zan saɓa masa garama ya halarci gurin"
"Insha Allah zaije ai ansamo yarinyar akwai buƙatar dai kuɗi wanda za'a bawa ita yarinyar da kuma dressing ɗin da zatayi "
Dady ya amsa da toh zakiji alart zuwa dare kushirya komai nima ina gabatar da aiyuka ne amma on monday ina hanya"
Momy tace "okay ubangiji ya dawo mana dakai lafiya.
Bayan Mubin ya raka Ibrahim, sai da akayi faɗa sannan ya juyo.
Ilham- niko ina laɓe ina jin duk shirye-shiryen da sukeyi, a zuciyata nace "aiko bazan amince ba, aiba BASAJA nazo yiba dan haka su samamin lafiya, na koma kitchen,
Washe gari, da asbha bayan nayi sallaha na ɗauko al'qur ani dana gani akan loka, na daɗe ina karatu daga ƙarshe nayi adu'oi na na ajiye shi a inda na gansa,
Wanka na shiga, ina fitowa na shafa mai wanda na gani an jere a gaban dressing mirror, simple makeup nayi kana na fito da doguwar rigata abaya baƙa mai adon golden stone gabanta kuma anyi adon fulawoyi,
Na ɗauki ɗankwalinta na ɗaura a kaina kafin na fito, lokacin ƙarfe takwas, kasancewar yau Asabar ne yasa ban wani damu da sai na fito da wuri ba, tunda momy ta bani time table na lokuta da ranakun abincin su,
Da sallama na shiga parlon ban sami kowa ba, hakan yasa na wuce kitchen, na share na goge na gyara gidan cikin ƙan ƙanin lokaci, kasancewar dama bawai yayi datti bane,
Ruwan shayi na ɗora wanda yaji kayan ƙamshi, yana tafasa na juye a flask nakai dinning na ajiye ina shirin juyawa naji momy tace "ƴata kin tashi lafiya ..."
Zubewa ƙasa nayi kafin nace "Hajiya barka da safiya.."
Momy tace "barka ya aiki har kin fito kenan..?
Nida ba wata magana mai tsayi ke haɗamu da ita ba , amma yau naga tana son jana da hira,
"Eh nace kafin na juya zuwa kitchen na, fara fere dankali na soya na fasa ƙwai shima na soya daga nan na sassaka a plet na rurrufe, na kawo dinning na ajiye kafin na koma kitchen a karo na uku na ɗauki nawa abin karin na wuce ɗakin da aka bani in dinga kwana,
Ina zama na saka abincin a gaba na zabga uban tagumi, a fili nace "koya Abbana yake oho, banji ana cewa in kai masa abinci ba, ko sun bashi ne? gani ina shirin cin abinda nakusa shekara rabona daci, Allah sarki Abbana ",
Na ƙarashe maganar hawaye na wankemin fuska,
Ada ina murna zanci abinda nake sha'awarci, saboda ina mugun son cin dankali soyayye da ƙawai uwa uba shari mai marada gashi mai kauri, a halin yanzu tunda na tuno halin da Abbana yake ciki sai naji komai nawa ya sauya, haka na tuttura abincin,
Ina zaune na faɗa kogin tunani, wani lokacin in tuno Basma wani lokacin in tuno watsamin ruwan taɓo da wancan sokon yayi, dan bazance masa wani Mubin ba, kamar inda naji abokinsa na kiransa,
Kiran da aka ƙwalamin ne ya sani amsawa ina miƙewa, dan muryar Hajiya naji,
Ina fitowa na sameta zaune akan ɗaya daga cikin kujerun mai cin mutum biyu, na zauna a ƙasa,
"Tashi ki zauna anan"
Ta nunamin kusa da ita,
Batare da nayi mata musu ba na zauna ina wasa da hannun rigata,
Muryarsa da bata ɓuya muka jiyo tun kafin zuwansa, muka ji yana cewa "momy breakfast ɗinafa" momy na murmishi tace "my son yau an mance da gaisuwar ne ? fuskarsa babu walwalah saboda ganina da yayi tare da momynsa, yace "momy barka da safiya, sai naga ya gallamin harara,
Bayan momy ta amsa yaje yayi breakfast ɗinsa, yana ganawa ya miƙe zai fice momy tace ",inason magana dakai "batare da yayi tsammanin maganar da momyn zata faɗa masa ba, ya dawo da baya kana ya zauna yana kalonta,
"Ka mance maganar da mukayi dakai akan tare da Ilham zaku tafi? kuma ko shiri banga kunayi ba daga kai har ita "
Momy tayi wannan maganar ne kawai dan tasha cikinsa sbda ta sani sarai bawai kulani yakeyi ba, duk da yau kwana na biyu a gidansu..!


*💥GUNTUN GORO..!💥*


_Zainab habib(Mom Islam_


Domin samun complete a arewa books danna wannan links ɗin👇
https://arewabooks.com/u/momislam22

*TEAM GAWURTATTU BIYAR*

Free page 7-8

Yamutsa fuska yayi kamar bai san da zancen ba,
Na kawar da maganar tare da cewa "Hajiya dan Allah inason zuwa gurin Abbana"
"Bari driver yazo ya kaiki "
"To "
Nace ina ɗan faɗaɗa fuska da murmishi nabar gurin dama na gaji da harara.
Hijab ɗina na ɗauko kana na fito ina shirin fita naji Hajiya tace "bari drivern yazo mana "
Na tsaya cak tare da rungume hannuwana a cikin hijab,
Ina nan a tsaye suna magana da Mubin, amma bansan me suke cewa ba sbda ƙasa-ƙasa suke maganar,
"Aslamu alaikum hajiya barka da safiya gani "
"Gurin Babanta zaka kaita "
Driver yace "to angama Hajiya ",
Hajiyar ta miƙa masa kuɗi tace ya tsaya ya siya fruits,
Daga nan muka fice zuwa parking space, motar danaga drivern ya shiga ita na shiga muka lula zuwa asibitin Murtala.
A bakin titi muka tsaya, driver ya fita ya siyo fruits ya dawo muka ƙarasa ciki,
A gurin da aka tanadar dan ajiye motoci driver yayi parkin, ya miƙamin ledojin kafin na fito na nufi ɗakin da Abbana yake,
Ina shiga na sameshi shida malam Ahmad suna hira, da sallama na shiga na nemi kujera na zauna ina gaishesu, bayan sun amsa, nace Abba ya jikin ?"
Ya amsa da "alhmdulilh ƴar Abba ya gidan aikin naki ?"
Na ce" lafiya lau "ban sanar dashi abinda ke wakana a gidan ba,
Fitar da malam Ahmad yayi ne ta bani damar ƙarewa ƙafar Abba kallo na ɗago kaina ina ɗora idanuwana akan fuskarsa kafin nace "Abba amma kaji sauƙi koh? naji kace za'a sallameka yau kuma na ganka a kwance "Abba yayi murmishi kafin yace "eh da yau za'a sallameni, to anyi gyaran wallahi har yanzu ƙafar taci gaba da zubar ruwa ana tunanin fitar dani ƙasar waje ne, dan jiya wani yaron Alhjin mai suna Mubin ne yazo yake sanarmin zai nemi transfer zuwa asibitin India,
Wasu zafafan hawaye ne suka wanke min fuska nace "Abba wai ciwo sosai ƙafar take maka ?"
Naga Abba yayi murmishin yaƙe sai kuma yace "da sauƙi karki damu ai yaron yanada kirki jiya ma ya kawomin abinci,
"Dama wannan Mubin ɗin nada mutunci ko kuma dai yanada wani nufinne akan Abbana, amma zan zuba ido ",
"Ilham! Ilham!..."
Muryar Abba ta dawo dani daga dogon tunanin dana tafi,
"Na'am "
Nace tare da kawar da idona ga kallon Abba,
"Ilham ki kwantar da hankalinki babu abinda yake damuna face ciwon ƙafar nan, itama ɗin ina kyautata zaton zatayi sauƙi insha Allah tunda ba kamar daba "
"Hmm "
Nace ina mamakin inda Abba yake ƙoƙarin ɓoyemin damuwarsa,
"Abba kenan kace ka sami sauƙi to nidai maganar fita ƙasar wajan nan ne ke damuna"
"Ilham banason musa musu ne ki kwantar da hankalinki"
Da mamaki na baro asibitin muka dawo gida,
Tun a mota nake tunanin anya babu abinda Abba ya ɓoyemin kuwa ?, ina tunanin akwai lauje a cikin naɗi ",
Dan rabona da ganin ya taka tun a gida,
1:40pm Nayi alwalah na kabbara sallah, ina idarwa na fito parlo na fara gyara dinning sbda jere abincin rana, Allah ya taimakeni Hajiya ta gama abincin kasancewarta mace mai kirki, da Mubin ne yayi halinta daya more wallahi.
Bayan na gama kawo komai ina shirin ajiye juyawa zuwa ɗakina naji sallamar su Ibrahim,
Da fara'arsa ya ƙaraso shi kum Mubin ɗin naga yayi room ɗin momy,
"Sister Ilham ya aiki..?"
Cikin jin nauyi nace "alhmdulilh"
"Masha Allah dan Allah inaso muyi magana mai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment