Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a Lagos na kunna mata videos ɗin da akayi mana, washe haƙora Hajiya tayi tana cewa "gaskiya kun dace babu ƙarya aure babu fashi keda Mubin".
"Aslamu alaikum"
Mubin ya shigo hannunsa riƙe da wata babbar leda ya ajiye a gaban Hajiya,
Bayan mun amsa sallamar ya jefomin harara ya zauna kusada Kakus,
"Nazo miki da mutuniyarki harda abinda kikeso rufe idonki"
Harna tashi zan tafi ɗaki, hajiya ta dakatar dani tahanyar cewa "dawo mana Ilhamatu"
"Wani abun zatayi miki ina zaune itama zama zatayi?"
"Au eyee zamafa kace ita ba mutum bace?"
"Mutum ce mana amma ai ba sa'anta anan dan haka ta wuce taba mutane guri",
Ban kuma tsayawa jin abinda zai kuma cewa ba na wuce ɗaki.
Mubin da Kakus, Buɗe ledar yayi kafin yace "kazace in gaya miki da nono na gora harda kwakwa kisha muyi wata magana yanzu"
Kakus na dariya ta buɗe murfin gorar ta kora ta yagi naman kaza, ta daɗe tanaci tana korawa da nono shi kuma yana dane-danne a waya,
Fitowa nayi na wuce ta gabansu,
Gurin driver naje sbda yanzu momy ta kirani akan, driver yaje ya ɗaukota.
Bayan na dawo na samu sunata ƙyalƙyala dariya, zan wuce Hajiya ta janyo hannuna ..!

*💥GUNTUN GORO..!💥*


_Zainab habib(Mom Islam_


Domin samun complete a arewa books danna wannan links ɗin👇
https://arewabooks.com/u/momislam22


Free page 15-16
Tare da cewa "lafiya naga kin fita?"
"Hajiya ce tace driver yaje ya ɗaukota"
Na wuce ɗaki.
Bayan sun tsagaita da dariyar Mubin ya kamo hannun Kakus kafin yace "ƴar tsohuwa wata magana nakaso muyi dake dan Allah ki fahimceni"
Kakus na washe baki tace "mai gida fahimtarka ta zama dole ina jinka"
"Dan Allah karkisa a haɗani aure da waccar Villager ɗin"
"Ah ai karka damu Mubin, ƴan mata sai wacce ka darje"
Mubin yayi murmishi tare da haɗe hannayensa biyu yana yi mata godiya.
Bayan kwana uku da maganar,
Safiyar Talata, bayan an gama break fast, lokacin ma duk suna zaune a parlo kan kujerun da suka zagaye parlon,
Gyaran murya Kakus tayi kana ta waiga taga babu Mubin, tace "Babana dama akwai maganar da nakeso muyi daku"
Dady yace "Hajiya muna sauraronki"
Momy ma tace "muna jinki"
"Dama akan maganar Mubin ne, yakamata ace yanzu yana da yara fa, kuma kai Abdullahi girma na daɗa ziyartarka, a ganina tunda jininsu ya haɗu da yarinyar nan Ilham jiya ma har kiranta a waya yayi, shine nace mezai hana a haɗasu aure tunda yarinyar tanada hankali ga nutsuwa"
Tunda Kakus ta fara magana suke ta faman murmishi da alamu suma hakanne a zuciyarsu,
"Wato Hajiya kamar kin shiga zuciyarmu, sbda mun daɗe muna hasashen hakan amma muna tunanin inda dukkansu zasu ɗauki abin, zata iya yiwuwa Mubin bawai sonta yake ba, amman dai zan tuntuɓi mahaifinta inhar beyi mata miji ba sai mushiga".
Abba ya faɗa yana murmishi.
Momy ma tace "Allah ya zaɓa mana mafi alkairi,
Bayan kwana biyu da maganar, dady suka shirya shida wani yayansa wanda suke uwa ɗaya uba kowa da nasa, ana ce masa Alhaji Bashir,
Drivern dake kai Ilham gida ne ya kaisu,
Da isarsu suka umarci driver yayi musu sallama da Abba,
Bayan fitowarsa yace "Abban yace su shiga"
Da sallama suka shiga drivern ya koma mota.
Suna shiga suka sami Abba zaune akan ƙatuwar tabarma yayi musu umarni dasu zauna,
Bayan sun zauna suka gaisa Dady yayiwa Abba godiya akan taimakonsu da Ilham tayi,
Abba yace "ai babu komai muma munga abin arziƙi Allah ya saka maka da mafificin alkairi"
"Amin ya rabbi" Abba yace cikin fara'a.
Miƙewa Abba yayi kana yace "dan Allah ina zuwa kuyi haƙuri"
"Babu komai" cewar su dady.
Abba bai jima ba ya dawo hannunsa riƙe da manyan ledoji guda biyu ya ajiye a gaban su dady ya fara firfito da drinks ɗin daya siyo,
Alhji Bashir yace "ah malam harda ɗawainiya ai da munsan abinda ka tafi siyowa kenan da mun dakatar dakai",
Abba na murmushi yana cewa "ah haba dai, dan Allah kusha"
Basuyi musuba suka sha drinks ɗin haɗe da ɗan taɓa snacks da shawarma, sukayi hamdala.
Abba yaji daɗi sosai, bai taɓa tunanin dady zai tako zuwa gidanmu ba, gashi harda cin abinci a gidanmu, a zuciyarsa kuwa cewa yake "ashe dai masu kuɗin ba duka suka taru suka zama ɗaya ba".
Bayan shiru ya biyo baya na ƴan wasu lokuta, Alhaji Bashir yayi gyaran murya kana yace "dama dalilin daya kawomu akan maganar ƴar gurinka ne, munzo mu tambaya kayi mata miji ne?"
Kamar daga sama Abba yaji maganar tasu, shin mafarki yake kokuwa a gaske ne?
"Alhaji Abdullahi Zakin Naira da Alhaji Bashir sun tako har gidansa, da alamu neman auran ƴarsa sukazoyi, in hakan ta kasance sai yafi kowa farinciki"
Cikin sauri yace "banyi mata miji ba amma akwai wata matsala ce? kokuma tayi muku rashin kyautawa?"
Dady da sai yanzu yayi magana, yace "babu abinda tayi mana, munzo neman izini ne Munason a haɗasu aure da ɗan gurina",
Abba ya kasa ce musu a'a, tunaninsa ɗaya, da kuma roƙonsa Allah yasa in amince, sbda burinsa da adu'arsa itace Allah ya bani gidan dazan huta, tunda suɗin mutanen kirki ne,
"To bawai naƙi ta naku ba, zan nemi shawarar ita Ilham ɗin idan ta amince sai asan matsaya"
Su dady sukayi na'am da maganar Abba, sukayi masa sallama tare da ajiye masa 10k suka tafi.
Bayan kwana biyu da maganar Abba ya kirani a waya yace in bana komai yanason ganina, na tsorata dan a tunanina ankai ƙarata gurin Abba ne akan wani abun da bansan nayi ba.
Washe gari na shirya cikin shadda pink batada wani ado sai stone da akayi kwalliya dashi ɗinkin doguwar riga na kafa ɗaurin zara buhari, nayi kyau sosai duk da ba wani makeup nayi mai yawa ba, alrready dama na sanarwa da Momy tun jiya, ina fitowa Kakus ma ta fito riƙe da mayafi tace "harkin fito ne? nima binki zanyi muje inga gari"
Mubin dake waya da Ibrahim ya wani yamutsa fuska kafin yace "haba Hajiya nifa wannan zubar mana da class ɗin da kike yayi yawa"
"Shittt" momy tayiwa Mubin alama da yayi shiru ta rufesa da faɗa tana cewa "inaga wannan ƙiyayya taka da Ilham akwai aure a tsakani"
Mubin ya gimtse fuska yana cewa "haba momy ni kidena yimin haka"
Hannun kakus na kamo ina cewa momy "mun tafi" muka fice.
Muna fita muka tsaya a parking space, driver na ganinmu ya fito da gudu, yana cewa "hajiya an fito ina zamu"
Kakus tace "gidansu Ilhamatu zamu" muka shige mota.
Muna isa akayi parking muka shiga gidan da sallama,
Abba dake tsaye yana waya ya katse wayar yana faɗaɗa fara'arsa kafin yace "ah Ilham sannunku ku shiga mana kin barta a tsaye"
Ɗakina muka shiga na ɗibowa Kakus ruwa, Abba yayi sallama muka amsa, suka gaisa da kakus nima na gaishe shi, kana nace masa "itace mahaifiyar Alhaji Abdullahi"
Godiya Abba ya fara jero mata akan riƙeni da amana da sukayi ya ƙara da cewa "bashi da abinda zai biyasu sai dai adu'a,
Kakus taji daɗin godiya da yabon Alhaji da Abba yayi, har take cewa Abba "dama akwai maganar da nazo muyi shi yasa ma na biyo Ilhamatun muka taho"
"Abba ya tasheni na fice zuwa kitchen dan in samawa Kakus abin taɓawa, kasancewar tun kuɗin da dady ya bani naba Abba ya siyo kayan abinci, ragowar kuma yasa a account ɗinsa.
Kakus ta gyara zama kafin tayi ƙasa da murya tace "dafa arziƙi a gidan wasu gara a gidanku, a gidankun ma a ɗakinku nayiwa ƴarka Ilhamatu sha'awar auran jikana saboda tanada hankali zata kula dashi tunda rayuwar sakalci yayi babu kwaɓa"
Abba ya nisa kafin yace "jiya su Alhajin sunzo akan maganar, dama nace sai na tuntuɓi ita Ilham ɗin"
Ina yanka albasa Abbana ya ƙwalamin kira, da sauri na taho tare da durƙusawa a gabansa nace "Abba gani"
Abba ya kalleni kafin ya jinjina kai sai kuma yace "Ilham inason kisani, nayi miki tarbiya nida mahaifiyarki har Allah ya karɓi abinsa, naci gaba da ƙoƙari gurin ganin kinyi makarantar boko wato jss da ss, ta jami'a ce dai har yanzu Allah bai bani ikon saki ba, kinyimin biyayya akan duk wata buƙatata kuma naji daɗi babu abinda zance miki sai Allah yayi miki albarka"
Abba ze kuma magana nace "Abba wai lafiya kuwa naga kanata yimin nasiha ko wani abun akace maka nayi?"
"Ko ɗaya Ilham, neman auranki akazo yi"
"Dafe da ƙirji na kalli kakus na juya na kalli Abbana kana nace "Abba waye?"
Kakus tace "kaji gulma waye banda Mubin"
Kuma waro ido nayi nace "Mubin kuma shiɗin yace yana sona?"
"Rufawa mutane baki ku yaran zamani gulma tayi muku yawa, kunaso kuna kaiwa kasuwa"
Abba yayi murmishi, tunda naga haka ban sake magana ba, sbda ina ganin Abba ya rigada ya amince zaɓinshi shine nawa.
Kaina a sunkuye naji Abba yace "tashi Allah yayi miki albarka"
Na amsa da "amin" na koma gurin girki.
"Amma naga kamar kanayi min kama da ɗan gidan Liman na ƙauyenmu can Tsaudawa dake hanyar Ƙiru"
Abba yayi murmishi kafin yace "ai ɗansa ne, Sunana Abubakar ana kirana da garba, Kakus ta washe baki kafin tace "amman dai baka sanni ba ko?"
Abba yace "wallahi ban sanki ba"
Kakus tace "ai liman da ubansa da ubanmu uwa ɗaya uba ɗaya, nidai naso in ganeka sbda kama dakayimin da Hama, Abba yace "ai tun bayan rasuwarta nabar garin haryau ban sake komawa ba, tun inada shekara goma sha uku, na dawo cikin Kano ina tallan ruwa da kunun zaƙi"
Kakus tace "wato Mero hatsabibiyar matace, sai da tayi tasan inda ta rabaka da mahaifinka kenan?"
Tabbas naji ana cewa ɗan gidan Hama ya ɓata kuma mune da laifi da bamu cigiyeka ba"
Abba ya share hawayen da suka zubo masa..
FARKON LABARI(Waiwaye)
Malam Sani, mutumin Tsaudawa ne wato ƙauyen Kano, yanada mata mai suna Azumi da yara biyu Hudu da Haruna, sun taso cikin ilimin islama lokacin makarantar boko bata gama ko ina ba, malam Sani babban malami ne mai faɗa aji a garin, yana sana'ar kiwo wato idan ana neman mai siyan dabbobi sai a kirashi ya siya shi kuma ranar kasuwa yaje ya siyar ya ɗora nashi akai, mahaifiyarsu Hudu da Haruna tayi musu tarbiya dai-dai gwargwado, har Allah yasa suka girma, aka malam sani ya fara zuwa dasu gona suna tayashi aiki, daga lokacin da suka san ciwon kansu ma'ana suka kai aure sbda a ƙa'idar garin, daga mazan har matan ba wani girma sukeyi ba, Haruna nada shekaru ashirin da biyu Hudu kuma ashirin da biyar, kasancewar shine babba aka musu aure, malam Sani yayi rawar gani ya gina musu ɗakuna a cikin gidansa, zaman lafiya da ƙaunar juna tare da yiwa mahaifiyarsu biyayya suna yinsa dai-dai gwargwado, Itama Azumi wato mahaifiyarsu bata sanyawa surukan ido ba, suma basu rainata ba.
Kwanci tashi asarar mai rai, anyi wata uku da aure, matar Haruna nada cikin wata ɗaya, ita kuma matar Hudu tana kwance babu lafiya ashe itama cikin ne, Azumi ta dinga kula dasu tana tayasu aikace-aikace, sunan matar Hudu Laure matar Haruna kuma Halima lokacin da cikin Laure yakai wata takwas ta koma gida kasancewarsu fulani, watan aihuwarta na cika ta haifo ƴarta mace mai suna Zulai, yarinya santaleliya fara sol kasancewar Harunan shima farine ga dogon hanci, bayan anyi suna da wata biyu matar Hudu Halima ta haifi ɗanta shima fari kyakkyawa ranar suna yaci sunan Abubakar, suna kiransa da garba, cikin hukuncin ubangiji yara sukayi wayo, bayan aihuwar Laure da wata biyar ta dawo gida sukaci gaba da zamansu cikin amana.
Bayan shuɗewar shekaru kamar biyar, Zulai da Abubakar sunyi wayo, aika babu inda basa zuwa gashi ko irin faɗannan na yara basayi,
Wata ranar laraba mahaifiyarsu Hudu ta tashi da matsanancin ciwon ciki mai tsanani, anyi magani har an gaji, daga Hudu har Haruna babu wanda ya fita gona, malam Liman ya rikice sosai sbda tunda yake bai taɓa ganin ciwon daya gigitashi irin nata ba, washe gari ranar juma'a da safe rai yayi halinsa, Hudu da Haruna da babansu Liman sunsha kuka, kan kace me gida ya cika da al'uma na kusa dana nesa...!

*💥GUNTUN GORO..!💥*


_Zainab habib(Mom Islam_


Domin samun complete a arewa books danna wannan links ɗin👇
https://arewabooks.com/u/momislam22

Free page 17-18

Daga nan rayuwa taci gaba da tafiya musu da daɗi babu daɗi,
Wata ranar Monday Hudu da Haruna suna zaune a gindin bishiyar darbejiya dake ƙofar gidansu, aka fara sanarwar za'a ɗauki mutane magidanta aiki a cikin garin Kano, Haruna ya miƙe da sauri yana cewa "ai ko banyi ilimin boko ba sai naje" Hudu ya riƙe hannunsa yana ce masa "dan me zakace duk shiririta nefa"
Haruna yace "idan bazakaje ba babu lallai babu dole,
Da yake Haruna nada rabo, yana zuwa fadar mai gari ya bada sunansa akasa ya dawo gurin Hudu yace yaje ya bada nasa, harara ma ta bashi amsa dole tasashi yayi shiru,
*******
Yayinda kwana yake shuɗewa haka shekaruma suke shuɗewa, Allah kenan mai tsara abinsa a lokacin da yaga dama kuma yakeso, ta ɓangaren Hudu da Haruna shekaru sunja sosai, Azumi mahaifiyarsu takai shekaru goma da rasuwa, liman kuma ya daɗa tsufa sosai,ba kasafai yake fita ba.
Lokacin Haruna ya koma cikin garin Kano da zama, shi kuma Hudu ya ƙara aure ya auro wata bazawara anan ƙauyen nasu na Tsaudawa, tunda da bazawarar mai suna Hama ta tare, sukayi bankawana da zaman lafiya, wani lokacin Halima ta shiga ɗaki tayi ta kuka, lokacin Abubakar wato Garba yanada shekaru tara a duniya,
Tunda Hama ta shigo gidan Hudu ya juyawa Halima baya, gashi mahaifiyarta ta rasu, kishiyoyin mahaifiyarta kuma sun tsaneta, danginsu ba suda yawa bare ko wani bai kulakaba wani zai kulaka,
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, da yawon gidan bokaye da ƴan bori, Hudu ya dena ambaton sunan Halima bare ɗanta Abubakar,
Washe garin ranar talata, Abubakar ya shigo hannunsa riƙe da sandar rake guda biyu, tun daga tsakar gida yake ƙwalawa mahaifiyarsa da yake ƙwala mata kira amma shiru, da gudu ya ƙarasa ɗakin yana shiga ya zube a gabanta yana kuka yana jijigata, Allahu akbar mai rai ba'abakin komai yake ba, koda Hudu yaji maganar rasuwar ba wani damuwa yayi ba, bayan anyi sadakar uku kowa ya watse, sukaci gaba da ganawa Abubakar azaba, girki shine ɗibo ruwa a rafi shine shara aika wanki duk shi kaɗai, lokacin da yakai shekaru goma sha uku, ya fara hankali yasan samu da rashi gashi Liman ya tsufa bai isa ya tsawatar ba, Abubakar yabar ƙauyen Tsaudawa shida wasu yara sa'anninsa ya dawo cikin garin Kano da rayuwa, farko dai sunsha wuya, sbda duk inda sukaje korarsu akeyi, kwanansu biyu basu sami matsuguni ba, gashi bai san inda Haruna ɗan uwan babansa yake ba.
Wata ranar alhamis su Abubakar sunyi yawon bara wanda sukasa kansu domin samun abinci sun gaji, zaune suke kan a ƙofar shagon wani mutumi dake cikin garejin, wata mata wacce a ƙalla zatayi shekaru 50yrs ta iso gurinsu,
"Sannunku ƴan samari" matar tace tana ƙarewa su Abubakar kallo, binta da ido sukayi har ta kamo hannuwansu duka biyu, ta fita dasu daga garejin, a gidan abincin dake bakin titi ta tsaya, ta siya musu abinci mai rai da lafiya, bayan sunci sun ƙoshi sukayi mata godiya, ta zaunar dasu tare da shawartarsu akan zata sama musu aikin siyarda buredi, duk kansu sunyi na'am, anyi hakan da kwana uku ta nuna musu gidanta da inda zasu fara,
Lokacin da Abubakar yakai shekaru goma sha biyar sun rabu da yaran dasuka taho tare daga ƙauyen Tsaudawa, ya nemesu ya rasa sakamakon faɗace-faɗace da akayi, haka yaci gaba da tallan buredi har yakai munzalin da ya nemo aure, uwar ɗakinsa wacce ta nema masa aikin gaf zaiyi aure ta rasu, yasha kuka kamar ba gobe, ya shafe tsawon sjekaru tun bayan rasuwarta bai ƙara maganar aure ba, daga baya ya tattago maganar aure. bai wani jima dayin aure ba aka koresa daga gidan buredin sbda dama idonta yasa suka barshi, tunda duk cikinsu babu bare duk ƴan Niger ne.
Wata biyu da aurensa yana zaune da matarsa mai suna Maimuna, zaman lafiya da amana iyayenta sun riƙeshi hannu biyu , har aikin kayan gwari suka nema masa wato sun tallafa masa da jari har ya bunƙasa, ya fara yin arziƙi, watansu bakwai da aure, Maimuna ta sami ciki lokacin yanada sati biyar, sun ɗauki burin duniya sun ɗorawa cikin, ga wata tsafta tacciyar soyayya da suke gwadawa junansu.
Bayan wata tara naƙuda takamata gadan-gadan, sukayi asbiti kasancewar naƙudar batayi nisa ba, cikin ikon Allah ta haifo ƴarta mace mai kama da ita , bayan an gama biyan kuɗin asibiti an gyara mai jego, ƴan uwanta sukazo aka dawo da ita gida, ranar suna yarinya taci suna Hauwa'u suna kiranta da Ilham, tun bayan aihuwar Ilham Maimuna ta sami wani ciwo shiba hauka ba shiba lafiya ba, koda yaushe bata cikin hankalinta, shekarar Ilham goma, Maimuna ta rasu Abubakar yayi kamar zautacce sai cewa yake "Bani da kowa bani da dangi ke kaɗai kika ragemin amma kin tafi kin barni, kasancewar tun kafin a haifi Ilham iyayenta suka rasu, zumuncin yanzu ya zamo sai a hankali kowa takansa yakeyi, yasa babu wanda yayi yunƙurin ɗaukar Ilham daga gurin babanta, anan gabansa tayi makarantar islamiya da boko, harta girma ta mallaki hankalin kanta, tanada shekaru goma sha uku, mahaifinta da take kira da Abba ya sami ciwob ƙafa, wacce ta hanashi aikin ƙarfi, lokacin da takai shekaru 17 ta gama Secondary tayi saukar alƙur'ani mai girma, har ila yau bai taɓa sha'awar yin aure ba, yana ganin kamar bazai sami wacce zata kula da Ilham ɗin ba,
A halin yanzu ko marmarin zuwa ƙauyensu bayayi balle yasan waye a raye waye yabar duniya, tunda Hama ta rabashi da garin kwata-kwata.
Gashi Allah ya haɗashi da Zulai ƴar Haruna,
Back to story ina fatan kun fahimci labarin namu 😍
Ina sauke abincin na zubowa Kakus a plet kana na zubawa Abba a samira, sannu Kakus tayimin na amsa na fice,
A kitchen ɗin na zauna naci, kasancewar mutuniyata na dafa wato taliya, mamaki ne ya kamani ashe ma wannan Mubin ɗin ɗan uwanmu ne? taɓɓ.
Bamu muka koma gida ba sai wajen ƙarfe shida, muna shiga gidan ana kiran sallahar magrib,
Momy kawai muka samu a parlo tana ninke kaya, tana ganinmu ta washe baki tana cewa "ni na ɗauka kwana zakuyi ?" Kakus tace "ina Alhaji ƙarami" yau akwai kyakkyawan albishir"
Na gaishe da momy bayan ta amsa na wuce ɗakina.
Bayan anyi magrib anyi isha'i kowa ya hallara a dining, ina zaune a kan kafet Kakus tace "taso kihau kujera ai kema ƴar gidance" ban taso ba tunda banji wanda yasa baki bayan maganarta ba,
"Haba ni wallahi kina bada mutane, duk sawa da kikayi ta raina mutane bai isheki ba har saita zauna a inda muke zama? haba dan Allah"
Mubin ya faɗa yana miƙewa hannunsa riƙe da plet mai ɗauke da soyayyar taliya wacce taji kayan lambu.
"Haba Mubin meyasa kake son wulaƙanta ɗan adam ne dawo ka zauna"
Yana tafe yana buga ƙafafu ya dawo ya zauna,
Dady yasani dole in dawo dining in zauna, bayan kowa ya gama cin abincin, Kakus ta fara bada labarin rayuwarsu ita da Abbana da rayuwar matar babansa dana Ummana kafin ta rasu,
A gigice Mubin ya saƙƙo daga kujera har plet ɗin hannunsa na faɗuwa yace "whatt!! kina nufin wai wannan ƴar uwarmu ce?"
Dady yayi hamdala kafin ya fara magana "wallahi tun da yarinyar nan ta shigo gidannan nake jinta a jikina ashe ƴar uwa ce ta jini Alhmdulilh Allah mun gode maka"
Gumi babu ta inda baya karyowa Mubin a ransa kuwa cewa yake "ashe jinina nake wulaƙantawa ashe ita ɗin ƴar uwarmu ce ta jini ashe muma mahaifinmu a ƙauye ya taso lallai shiyasa babu kyau kaga mutum ka rainasa Allah ka yafemin"
Momy bakinta yaƙi rufuwa sai wani murmishi take, ta kamo hannuna muka dawo kujera mai zaman mutum uku, ta rungumeni kamar ƙaramar yarinya, gawaye ne ya kwaranyomin sbda tunowa da Ummana danayi ashe ɗumin jikin uwa daban yake, Allah sarki rayuwa, rabon da wata uwa ta rungumeni har na mance, na share hawaye na kuma rungume momy, itama hawayen naga tanayi, nasa hannuna ina share mata kafin nace "momy ki dena kuka momy ki taimakeni ki mayemin gurbin Ummana, ashe masu uwa suna jin daɗi, Dady da Mubin da Kakus kowanne share hawaye suke, a parlon bakajin ƙarar komai sai shesheƙar kukan su momy,
Washe gari bayan anyi sallahar asbha dady na dawowa daga masallaci ya kirani ya kira momy yace "daga yau kar a ƙara sani aiki nima na zamo ƴar gida, sai dai abinda ba'a rasa ba wanda zan dinga taya momy,
Daga nan kowa ya wuce ɗakinsa,
Ƙarfe 11:12am mun kammala breakfast mun jere a dinning muna jiran Mubin,
"Jeki part ɗin Mubin ki kirashi na jishi shiru ko lafiya wayarsa ma bata shiga" momy ta faɗa,
"Tom" nace na miƙe na tafi part ɗin nasa,
Nocking nayi haɗe da sallama,
Banji an amsa ba, hakan ya sani shigewa kai tsaye, ina shiga na samesa ya baje akan haɗaɗɗen kafet madai-daici, gabansa kuwa kwalin taba ne gefe kuma ga wasu wanda yasha kamar mahaukaci, daga irin inda yake fitar da hayaƙinta zakasan bawai yanasha dan nishaɗi bane, yanasha ne cikin ɓacin rai, ƙyam na maƙale sbda arba da nayi da abinda yake aikatawa,
"Dama ɗan shaye-shaye ne? ko kuma yanzu ya fara?"
Na tambayi kaina.
"Keee!! ubanme kikeyi anan waye ya baki izinin shigowa?!! me kikazo yi?!!"
Jikina na kyarma na fara ƙoƙarin ƙwatar kaina sbda tunkaroni da yakeyi gashi ya kusa kaini jikin bango, ina tsoron inje buɗe ƙofa ya kamoni, ni kaina na rasa nutsuwata sbda fitsari ne kawai bai zubomin ba, ya tsareni da jajayen idanuwansa, wanda ada nasan fari tarr yake,
Jin nakai bango yasa na zaro idona tare da ɗorawa a fuskarsa murya na rawa nace " dan...dan...All...Allah...ka...ka..ra..bu..bu...dani!!" ina kaiwa nan hawaye masu zafi suka zubomin, sbda zamemin ɗankwali dayayi ya cafki jelar gashin kaina saida na saki ƙara,
Hannunsa yasa dukka biyu ya fincikoni ya wurgar kamar ya sami karya, tashi ɗaya goshina ya fara zubar jini, bai wani damu ba yaci gaba da dukana kamar an aikosa, daga can bakin ƙofa momy ta fara nocking tana cewa "son ka buɗe wai lafiya meke faruwa?" yana jinta yaƙi buɗewa niko sai kuka nake, kukan da ba lallai wanda ke nesa yaji ba, sbda dashewa da muryata tayi nama kasa matsawa daga inda nake..!

Yau ina buƙatar zazzafan comments sbda gobe insha Allah ku sami new update da safe 😍 masu comments ina ƙaunarku ina sanku, alƙalamina bazai iya rubuta yawan soyayyar da nake yi muku ba.


*💥GUNTUN GORO..!💥*


_Zainab habib(Mom Islam_

Domin samun complete a arewa books danna wannan links ɗin👇
https://arewabooks.com/u/momislam22

_💃🏿Masoya Littafin GUNTUN GORO, ayau muka kammala pegin kyauta, ahito a nuna mana soyayya tafiyar na gaba😂_


Free page 19-20

Tsawar da momy ta daka ne yasa Mubin buɗe ƙofar jikinsa na rawa ya maƙale a bayan ƙofar, cikin rashin tsammani ta hango ni kwance jini ya wankemin fuska.
"A you serious?" momy ta faɗa tana mai matsowa kusa da mubin, kafin yayi magana ta wankeshi da mari, yana shirin sake yunƙurin yin magana a karo na biyu ta kuma wankesa da mari,
Ina daga kwance muryata bata fita na ɗago hannuna ina cewa "momy ki taimakamin"
Kasancewar tana kusa dani yasa ta taho da gudu ta rungumeni, abin mamaki bata damu da jinin dake jikina ba, gashi tasha kwalliya ta kurma ihun neman agaji, Mubin da yasha mari sai wani gurnani yake kamar mahaukacin zaki,
"Sakaiyyar da zakayi mana kenan ko Mubin? ka saka mana da shaye-shaye, yayi kyau, ta riƙe hannuna muka fice.
Muna shiga part ɗin momyn ta kawoni gaban Abba tana cewa "Mubin ni zai ciwa mutunci? yayi kyau, kana ganin abinda yayiwa ƴar mutane kuwa?"
Kakus ta rafka salati tashi ɗaya hawaye suka zubo mata tana cewa "Mibin ɗinne zaiyi haka?"
Cikin ɓacin rai Momy tace "kaje kaga abinda yake aikatawa,
Dady da ransa ya gama ɓaci yace "to meya sameshi kodai tayi masa wani abunne?"
Momy bata wani tsaya saurararsa ba ta kamo hannuna muka wuce parking space muka shiga mota driver ya tuƙamu zuwa Asibitin da aka Abbana ya kwanta lokacin yana fama da ciwon ƙafa,
Kai tsaye aka wuce dani emergency room, aka fara bani taimakon gaggawa, tare da allurai na bacci.
Tun ƙarfe 12:11pm na fara bacci bani na tashi ba sai wajen ƙarfe 2:pm,
A hankali na dafe kaina tare da buɗe idanuwana da sukayi min nauyi,
"Sannu Ilham"
Naji bakuna da yawa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment