Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a ciki"
Dady yace "Ilham ai kyauta aka baki so ki koma dasu"
Har ƙasa na durƙusa inayi musu godiya, nace zanje gaida Abbana.
"Ki turawa momy da account number zanyi miki transfer zuwa anjima"
Nace "Dady bani da account ai"
"To bari Mubin yazo idan da kuɗi a hannunsa sai yabaki"
"A'a dady na gode"
Da mamaki dadyn ke kallona har zan fice momy ta tsayar dani,
"Nawa za'a bata?"
Dady yace "100k"
Gabana ne ya bada rass sai kuma na daure ban nuna tsoron da nakeji ba,
Momy ta miƙe, kai tsaye part ɗin Mubin ta wuce, zaune ta sameshi yana shan black tea a ɗan ƙaramin cup,
Bayan tayi sallama ta kalleshi kamar baya cikin farinciki,
Cikin nuna kulawa tace "my son meya faru kamar akwai abinda ke danunka?"
"Momy inhar yarinyar nan bata bar gidannan ba wallahi ni sai nabar gidannan tunda ta zageni"
Waro ido momy tayi cike da mamaki shin anya Ilham zata iya zagin wani na gaba da ita kuwa?"
Momy tayi murmishin yaƙe, batare data tsaya saurarasa ba tace "to zan ɗauki mataki, dan Allah zoka ciromin kuɗi wani uzuri ne ya tasomin yanzu"
Rai a ɓace ya miƙe yabi bayan momy, ta ƙofar baya yabi ya ƙarɓi ATM ya fice,
Yaɗan jima bai dawo ba, dan saida na zauna dady nata kallona, ko kallon meye oho.
Zuwa wani lokaci ya dawo a mota kana ya shigo ta ƙofar da zata sadaka da parlon ya miƙawa momy wata ƴar jaka, yayiwa dady sannu ya koma part ɗinsa.
Tun kafin ya shigo momy taji alart ancire 100k,
Ta miƙawa dady kuɗin ya miƙa min na ƙarɓa hannu biyu ina godiya, zuciyata cike da tsoro dan tunda nake ko dubu ashirin nawa ban taɓa riƙewa ba.
Zuciyata na sharaɗamin in miƙa musu kuɗin duka a mai-makon aikin da nake in koma gida in huta, wata zuciyar kuma na cemin to "idan akazo kuɗin yafi haka fa? zasuga kamar kin wulaƙantasu ne"
"Kisa a cikin hand bag ɗinki tunda tanada girma"
To nace tare da fito da kuɗin adai-daita sahu nayi musu sallama na fice, cike da tsoron kuɗin hannuna.
Ina fitowa drivern gidan ya taso yana cewa "Ilham ina zaki?"
"Gidanmu an sallamo Abbana"
Na bashi amsa a taƙaice.
Nuni yayimin da in shiga mota, babu musu na shiga shima ya shiga muka lula titi.
Muna tafe yana ɗan jana da hira har muka iso gurin wasu masu siyar da kayan marmari, ina shirin buɗe murfin mota in fita, drivern yace "barinje ina zuwa"
"Gaskiya drivern nan yana da matuƙar kirki wallahi samun irinshi sai an tona"
Yana dawowa ya shiga mazauninsa kana ya miƙomin leda bag mai ruwan ƙwai cike da lemu da kankana da ayaba da abarba,
"Mungode Allah ya ƙara buɗi"
"Amin" yace
Mukaci gaba da tafiya,
Cikin ikon Allah muka iso anguwarnu, a dai-dai ƙofar gidanmu yayi parking, muka fito kai tsaye muka shiga gidan da sallama.
A tsakar gida na sami Abba yana kishingiɗe akan tabarma, abu na farko dana fara kallo ƙafarsa, Abba na ganinmu yahau washe haƙora yana cewa "yanzu nake zancenki a zuciyata"
Driver ya gaishe da Abba, kana ya miƙe yana cewa "toni zan tafi Allah ya ƙara lafiya"
Ya ajiyewa Abba ɗari biyar,
Godiya nayi masa kana na rakashi har gurin mota muka kuma sallama na dawo gida,
Kasancewar tabarmar nada girma yasa na zauna a gefe ina cewa "wash Abba kwana zanyi"
Abba yayi murmishi, wanda sai yanzu yake baƙincikin turani aiki, amma alhamdulilh tunda ƙafar ta gyaru.
Miƙa masa ledar nayi kafin nace "Abba yanzu kana iya tafiya ba tare da kayi ɗingishi ba?" Abba yace min "Eh sosai ma ai yanzu ƙafa ta warke Ilham"
Na miƙe ina rawa alamun farinciki,
Ganin Abba nayi yana dariya, sai nakuma tsintar kaina cikin farinciki, fuskarsa wasai sai dariya yake ni kuma ina ci gaba da rawa.
Dawowa nayi na zauna kafin nace "Abba tashi muje ɗaki akwai sabon albishir"
Na riƙe hannun Abba muka wuce ɗakinsa, kasancewar akwai wata doguwar kujera 3sitter da 1sitter yasa na zauna a 1 Abba kuma ya zauna a 3 ɗin yana cewa "ina jiran albishir"
Nace "Abba rufe idonka"
Abba ya rufe idonsa kamar inda na buƙata nafice.
Ina dawowa nace "Abba buɗe idonka"
Bayan na ɗora masa a cinyarsa.
Yana buɗe ido ya waresu kamar zasu fito, jikinsa na rawa yace "Ilham wannan kuma fa?" Ilham a ina kika samo?"
Shiru nayi sbda jeromin tambayoyi da ya dingayi,
Sai da yayi tsit sannan nace Abba bari kaga video ɗin momy ta turamin jiya.
Yana karɓa na fice da gudu, sbda na tuno da baɗalar da akayi na riƙe hannu,
Bayan Abba ya gama kallon videon ya ajiye wayar gefe rai a ɓace ya ƙwalamin kira a fusace "Ilham.!!"
Jiki a sanyaye na fito nazo gabansa na durƙusa, kafin yayi magana na karɓe da cewa "Abba kaifa kace inje taron"
Tass!! tass!!
Abba ya zabgamin mari, wanda yasa na fara ganin wasu fararen taurari, ina riƙe da kumatu na ɗago idona daya fara sauya launi izuwa kalar ja, na kalli Abba na sunkuyar da kaina ƙasa, har na miƙe zan tafi, Abba ya dakamin tsawa tare da cewa "Dawo ki zauna"
Na dawo sum-sum na zauna tare da sadda kaina ƙasa.
"Ilham ki faɗamin gaskiyar lamari akan kuɗaɗen nan, ban turaki aiki dan ki zubar da mutuncinki ba"
"Ina kuka na ɗaga ɗan yatsana wanda ake nuni dashi nasa a saman bakina, kana nace "wallahi Abba ban aikata komai ba, idan kuma kana tan tama barin kira maka momy"
Kafin yayi magana, na ɗauki wayata cikin sauri na danna number momy, ring ɗaya kamar jira take ta ɗaga, a speakout nasa inda Abba zaiji duk abinda zatace, ina kuka nace "momy dan Allah baku kuka bani wannan kuɗin ba? Abba yace wai baku bane"
Na ƙarashe maganar in ƙara sakin kuka mai tsuma zuciya,
"Ilham haɗani da mahaifin naki"
"Abba ga waya"
Na miƙa masa,
Bayan sun gaisa da momy tayi masa bayanin taron da mukaje da kuma nasarori da suka samu, ta ƙara da cewa bawai mun gama yi mata alkairi bane, dadyn Mubin ya ajiye mata 50k kyauta yace sai end of this month zai bata so karka zargi komai"
Jiki a sanyaye Abba ya ɗago ya kalleni kafin ya yace "hajiya kinsan yaran yanzu ba wayanka ba, bakuma dabararka ba dole ka tsananta bincike waɗannan maƙudan kuɗaɗe ai dole sai da tuhuma, mun gode ubangiji ya saka muku da alkairi dan Allah kiyiwa Alhji godiya"
Momy tace "insha Allah ai mune da godiya Ilham yarinyace mai nutsuwa bugu da ƙari tanada hankali".
Daga nan sukayi sallama.
Da kallon tausayi Abba ya bini kafin ya dafa kaina abin mamaki naji yana sheshekar kuka, yana cemin "Ilham ki yafewa Abbanki, nasan nayi miki ingantacciyar tarbiya wacce nake da yaƙinin koda ƙasar waje na turaki kai koma ina ne a faɗin duniya bazaki zubar da mutuncinki ba"
Na sanya hannuna ina sharewa Abbana hawaye nace "Abba duk abinda kayi, dai-daine"
Bayan yasa albarka a kuɗin ya kuma ji daɗin wayar da suka barmin da kayan da momy ta siyamin nakai ɗaki, kuɗin kuma na barshi a gurinsa.
Abin farinciki ƙafar Abba ta koma normal sai ɗaurin bandejin da ba'a kunce ba,
Munsha fira nida Abbana, har nake ce masa nagaji da aikin nan a ɗauki kuɗinnan a basu a madadin aikin da zanyi na watannin,
Abba yayimin kallon baki da hankali kafin yace "Ilham ina sane da komai, wannan kuɗin da kike gani inhar biyansu zamuyi sai mun daɗo wasu dan sunyi kaɗan"
Shiru nayi kamar ruwa ya cinyeni, ya ƙara da cewa "Ilham karo na farko kuma na ƙarshe da zan kuma ganinki rungume a jikin saurayi ki kiyaye",
"Tashi kije kiyi alwalah ana kiran la'asar, ni zan fita sallah me zaki dafa zuwa dare?"
"Abba kawai tunda munyi kuɗi a soya ƙwai da tea"
Na faɗa ina dariya,
"Hmm" kawai Abba yace, ya fice.
Yana fita naje nayo alwalah na kabbara sallah, ina idarwa na fito tsakar gida na ɗauki tsintsiya nayi shara na gyara gidan tsaf, ina haɗa wuta Abba ya shigo hannunsa riƙe da ledar gawayi ɗayan hannun kuma ƙwai ya siyo da kayan shayi da buredi,
Wato dai munci kalar abincin gidansu momy muma.
Washe gari bayan anyi sallahar asbha na koma bacci bani na tashi ba sai wajen ƙarfe tara, lokacin dana fito har Abba ya haɗa wuta ruwa yayi zafi,
"Sannu da aiki Abba"
"Yauwwa sannu ƴar Abba kin tashi lafiya"
Nace "lafiya lau Abba, yadai yau na ga sai fara'a kake?"
Abba ya kuma faɗaɗa fara'arsa kafin yace "kedai jekiyi karin kumallo ganinan zuwa in baki labari"
Bayan mun gama karyawa na kalli Abba da har yanzu fuskarsa na ɗauke da fara'a nace "Abba mun kammala ina jinka"
Shiru naga Abba yayi, fara'ar ma ta ƙaurace daga fuskar tashi sai naga ya kawar da kai gefe,
"Abba lafiya kuwa?"
Na tambayeshi cikin damuwa,
"Lafiya Ilham bansan inda zaki ɗauki abin ba, amma kisa a ranki akwai maganar da zan sanar dake insha Allah kinji koh?"
Banji daɗin ƙin sanar dani da Abba yayi ba, babu inda na iya dole na ƙyaleahi.
Yana fita na shiga wanka, ina fitowa nayi kwalliya ba wata mai yawa ba, simple makeup nayi, na sanya riga da wando na pakistan, na janyo wayata na fara latsawa "to wazan kira ma? bani da lambar kowa"
Na faɗa ina tunani.
Sallamar da naji ne ta sani ajiye wayar akan katifa na ruga da gudu ina cewa "oyoyo Basma na, yaushe rabonmu da haɗuwa?"
Muka ƙarasa ciki,
Bayan na kawo mata ruwa nace mata ta jirani ina zuwa, kai tsaye shagon Dauda naje na siyo mata 5alive da cincin ɗan kanti na kawo mata inata murna,
"Kai Ilham kinyi kuɗi ne haka? harda wata ɗawainiya",
"Ke bani son surutu kici dan Allah"
"Ke kinga wani haske da murjewa da fatarki tayi sai kace wacce takecin tufa kullum?"
"Murmishi kawai nayi kafin nace "ke Basma abin harda zolaya wallahi kin cika tsokana"
Wayar hannuna data hango ne ya sata ƙin mayar min da maganar da takeson yi ta karɓa tana cewa "ƙawata wane gaye muka samu ne?"
"Uhm"
Kawai nace, sbda a ganina idan na faɗi ai aikatau nake zuwa kamar na tonawa kaina asiri ne,
Sai na ƙirƙiro ƙarya nace mata "ai in baki labari biki akayi a anguwarnan shine Allah ya haɗani da wani gaye, shinefa harda bani waya ga kuɗi da yake kashemin"
Abinka da ban saba ƙarya ba, sai nake ganin kamar zata ce nayi ƙarya.
"Lallai Ilahm kice kin kusa shiga daga ciki muna tafiya kema zakibi bayanmu, dan Allah idan da gaske yakeyi karki yaudareshi, Ilham ƴam mata yanzu neman samari suke, wasu sun samu suna wulaƙantawa, wasu kuma samarin basu mazo ba balle su wulaƙanta ɗin"
Banji daɗin ƙaryar da nayi mata ba, sbda bata can canci hakan ba, amma ina yin hakan shine mafita a gareni,
Ashe Abba yana tsaye yanajin nasihar da Basma takemin da kuma ƙaryar danayi mata,
Ya ƙaraso da sallama, Basma ta fito suka gaisa ya ƙwalamin kira,
Kasancewar yana ɗakinsa, yasa na bata haƙuri naje.
"Me kika bawa baƙuwar taki?"
"Nasiyo mata lemu da cin-cin"
Abba yace "idan bata ƙoshi ba ki tashi ki ɗora abinci"
Nace "toh"
Koda naje tambayota na sameta ta buɗe gallery na wayata tana ta kallon videos ɗin da akayi na gurin taron su Mubin,
Tashi ɗaya jikina ya fara karkarwa, Allah yasa bata fahimci hakan ba.
"Ilham wannan hotunan fa?"
Cike da ƙarfin guwaiwa na zan kaɗo mata ƙarya nace "ai shine saurayin"
Ɗagowa tayi ta kalleni kafin ta kalli Mubin dake riƙe da hannuna tace "kinsan ko waye wannan kuwa?"
"A'a nace"
Basma taci gaba da cewa "to wannan da kike gani ɗane ga Alhaji Abdullahi Zakin naira, shahararren mai kuɗinnan wanda ake damawa dasu a ƙasaranan dama ƙasar waje"
Ta ƙarashe maganar tana kuma kallona.
"Basma bani labarinsa ya mutu a soyayyata dole ta sani kulashi saboda tausayi daya bani"
Na faɗi maganar ina kashe mata ido,
Basma tace "Mubin yaro ɗan ƙwalisa, gashi da jiji da kai ga rashin son magana, ga gaye bugu da ƙari baya harka da ƴa'ƴan talakawa, ke in taƙaice miki bayani ƴanmata ma tururuwa suke akansa amma baya saurarasu, ai abinne ya bani mamaki, shiyasa"
Murmishin yaƙe nayi, a zuciyata kuwa murna nake na gano halayansa,
"Basma kina mamaki kenan ham wato sai da ya dinga haɗani da Allah akan in sosa shine na karɓi soyayarsa amma fa bawai ya sami gurin zama bane"
"Basma ta waro ido kafin tace "ke kinada hankali kuwa?"
"yesss"
Na faɗa ina dariya,
Kallon recording ɗin da nake a wayata nayi cikin hikima, dan tunda ta miƙomin wayar na danna record nasan koba komai zai yimin amfani.
Munsha hira kamar bazamu rabu ba har akayi sallah sannan Basma tace min zata tafi, bayan na karɓi numberta na rakata bakin titi ta tari napep, na bata kuɗin da Abba ya bani dubu ɗaya..!
*💥GUNTUN GORO..!💥*

_Zainab habib(Mom Islam_


Domin samun complete a arewa books danna wannan links ɗin👇
https://arewabooks.com/u/momislam22


13-14

Washe gari da asbha bayan anyi sallah na ɗora mana abinci, ina kamalawa naje ɗakin Abba da sallama na ajiye masa,
"Ilham yanzu fa ƙarfe shida ne, harkin gama kalaci?"
"Abba yau zan koma jiya da daddare momy ta kirani wai za'ayi baƙuwa aiki yayi mata yawa"
"To shikenan ki shirya da wuri sai ki tari adai-daita sahu ko?"
"Abba driver ne zai zo"
Na faɗa ina shigewa ɗakina.
Sai da na gyara komai na gidan, har girkin abincin dare nayiwa Abba nakai masa ɗaki, mota na zuwa na shige muka tafi.
Cikin hukuncin ubangiji muka iso lafiya,
Bayan yayi parking nayi masa godiya na fito, kai tsaye na shige part ɗin momy, na fara nocking, na daɗe a tsaye banji ance shigo ko kuma in koma ba, a zuciyata nace "kodai ta tafi anguwa ne?" bani da zaɓi na murɗa handle ɗin na kutsa kai ciki bakina ɗauke da sallama, batare da na lura da mutum a parlon ba na wuce, na kusa kaiwa baƙin ƙofar ɗakina naji an dakamin tsawa,
"Keee..! ubanwa ya baki izinin shigowa?"
Maganarsa ta tsoratani matuƙa, sbda banyi tunanin yanada irin muryarnan ba,
Sai kuma na dake nace "aiba gurinka nazo ba gurin momy nazo"
"Munafuka inma kinada wani nufinne akaina wallahi zakisha wahala dan bazan ƙyaleki ba"
"Nidai ba munafuka bace mugu kawai"
Da sauri ya miƙe daga zaman da yake, nikuma na zuba da gudu, na shige ɗakina da gudu na danna key.
Daga can ƙofar ɗakina naji yana cewa "zaki fito wallahi saina koya miki hankali.
Mubin na faɗar haka ya koma kan 2sitter ya zauna dafe da kansa, a fili ya furta meyasa zan dinga biye mata, wannan ai zubar da class ne".

11:am Ina zaune a ɗaki ina latsa wayata, naji maganar momy a parlo,
Nama mance da laifin da nayiwa Mubin na taho da sauri ina cewa "sannu da dawowa momy" wannan karon nasamu harda Ibrahim,
Cikin sakin fuska momy ta amsa da "yawwa ƴata kin dawo lafiya?"
"Lapy lou Abba na gaisheki"
"Ina amsawa zauna man"
Zama nayi ina satar kallon Mubin dake yiwa Ibrahim magana,
Ji nayi bazan iya zama a cikinsu ba, na miƙe tare da cewa "momy akwai aiki ne?"
"Eh yau kakarsu Mubin tana hanya tuwon shinkafa da miyar Efo riro da coconut rice zamuyi sai kunun aya da zoɓo".
"To" nace kana na wuce kitchen.
Tuwon shinkafa muka farayi, sai miya da shinkafa da juice muka saka ice,
Lokacin da muka kammala ana kiran sallar azhar,
Dinning naje na duba abubuwan da aka ajiye, na duba abinda babu nakai nasa, kasancewar momy taje sallah,
Ina gamawa nima naje nayi alwalah na kabbara sallah.
Ina ninke sallahya naji an kurma ihu ana cewa "oyoyo Kakus"
Sai da na tsaya ina nazarin,
"Shin zata daɗe ne ko kuma tazo ta wuce ne,
Firgit nayi waje inayiwa kaina dariya, sbda katoɓarar danayi.
Da zuwana na samesu zaune a parlo Momy Mubin da Kakus kamar inda naji suna faɗa, Ibrahim baya nan.
Har ƙasa na durƙusa na gaisheta, cikin sakin fuska ta amsa tana cewa "Saudart kunyi baƙuwa ne?"
Momy tace "ai ƴar aiki ce Hajiya",
Washe baki Kakus tayi kana tace "gata kyakkyawa Allah ya baki miji na gari",
Momy ta amsa da amin.
Gogan naku na zaune idonsa nakan TV ya ɗora ƙafarsa akan table ɗin dake kusadashi ya kishingiɗe, kai kace wani basarake,
Zuciyata har wani zafi take, duk ƙaunata da mutum banaso a kirani da wannan sunan, na mai-maita a zuciyata wai "ƴar aiki..!" innalilahi wa'inna ilaihi raji'un, na ambata, kafin na miƙe tsaye ina dariyar yaƙe naban gurin.
Tundana tafi ɗaki nayi kukana na share hawaye, sai wajen ƙarfe 4:11pm na fito,
Kai tsaye dinning na wuce naga sunci abincin wanda suka rage kaɗan ne, kuwashe plets da foodflaks ɗin gurin nayi nakai kitchen, kana na ɗibi nawa abincin na zauna a kitchen ɗin inaci.
Washe gari kamar kullum sai dana gama gyara ko ina sannan naje nayi wanka na shirya cikin gwn na doguwar rigar lace pink yanada fararen flowers na ɗaura ɗankwalin rigar a kaina,
Ring ɗin da wayata keyi ne yasani juyawa na ɗaukota kafin na duba mai kiran,
"momy"
Nace ina maiyin sallama.
"Ilham kije ki gyarawa Mubin ɗaki Ibrahim da abokansu zasuzo"
Badan raina yaso ba na amsa da "toh" koba komai ya sami damar yimin wulaƙanci san ransa.
Kallon fuskata nayi a mirror, ba wata kwalliya nayi ba, powder da man baki nasa sai tozali, na ajiye wayar, harnakai bakin ƙofa na dawo da baya na ɗauki wayata na danna number Abbana, saida na danna sannan na fara tunanin anya akwai kuɗi a cikima kuwa? cikin sa'a ta shiga, Abba ya ɗaga muka gaisa ya tambayeni ina lafiya nace masa "eh",
Daga nan na fito zuwa part ɗin Masifaffe sunan dazan dinga kiransa kenan.
Koda na iso bakin ƙofar na daɗe ban motsa ba, ina tsoro da jimamin wulaƙancin dazaiyi min, Doorbell na danna, na jima a tsaye ba'a buɗemin ba, tunani na fara ko babu kowa ne?
Alamu za'a buɗe ƙofar naji,
Naja baya gabana na tsananta faɗuwa,
Mubin ne ya buɗe door ɗin jikinsa ba wasu kayan kirki daga shi sai gajeren wando iya cinya sai farar ves, waro ido nayi tare da sauke kaina ƙasa,
"Dalla malama wuce ki gyaramin parlo"
Mubin ya faɗa yana wani murmishin mugunta,
Batare danayi masa musu ba na raɓa ta gefensa na wuce zuciyata fal tsoro,
Tsayawa nayi a haɗaɗɗen parlon nasa, shirin da ake a TV na arewa 24 ne yaja hankalina, cikin rashin tsammani naji an watso min ruwa, zan kuma magana ya tako har inda nake ya ƙuramin idanu kafin yace "karkiyi tunanin ƙwaɗayin da kikazo yi zaki samu ne, indai ina nan bazan barki ki huta ba"
Gudun kar inyi gautsin baki yayi min tijara yasa nayi hiru har yanzu jikina yana kyarma, remote ya ɗauka ya kashe kallon kafin yace "gida babu sai ki kalli glass"

Raina a ɓace na juya zan koma bana kallon gabana naci karo da table na faɗi, ji kake Timm! Mubin me zaiyi banda dariya har yana riƙe ciki.
Da sauri na miƙe ina ɗingishi har na fice baice min komai ba,
Inaga dama dan ya wulaƙantani yasa a kirani.
After 5 days mun fara sabawa da Kakus, dan har yawo nake rakata, a cewarta zama guri ɗaya tsautsayi ne,
Wata ranar Juma'a, su Kakus anata shirin zuwa masallacin Juma'a, Mubin ya fito cikin wata shadda milk color tasha aiki ya ɗora hula akansa da takalmi fari, wanda ya ƙarawa zara zaran yatsun ƙafarsa kyau, gyara zaman dardumar dake ratauye a kafaɗarsa yayi kana ya wuce ɗakin momy, ya sameta tana waya da Abba, dan yau satinsa ɗaya a Legos,
"Momy ƙaramin turare zan wuce"
Momy tayi murmishi kafin tace "Allah ya baka mata mai iya jure shagwaɓarka mai son"
Ta daɗa fesa masa turare tare dayi masa adu'ar Allah ya dawo dashi lafiya.
Yana fitowa palo yaga Kakus zaune hannunta riƙe da sallahya, tana ganinsa ta miƙe tare da cewa "Mubin muje ko?"
Harara ya galla mata kafin yace "ni wallahi takuramin zakiyi"
Kakus ta riƙe baki tace "wato dan kar inga budurwar taka shine zakayi min rashin ɗa'a ko?"
"Haba budurwa, ni basa gabana dan Allah kibar wannan maganar ki wuce mu tafi".
Yana gaba tana binsa a baya har suka iso parking space, "muje ko?"
Mubin yace yana kallon Kakus, "Ko a ƴar motar bazaka tuƙani ba zaka wani ce muje?"
Sai da Mubin ya kuma sakar mata da harara sannan ya muɗe mata mota gidan gaba, ya shiga mazaunin driver itama ta shiga suka fice.
Ba wani tafiya mai tsayi sukayi ba, suka iso, bayan yayi parking ta wuce gurin mata tsofaff da yara, shi kuma ya shiga can cikin masallacin kasancewar duk da alwalarsu.
Bayan an sakko daga sallah sun shiga mota, sun fara tafiya Kakus tayi gyaran murya, tace "Yaron kirki akwai wata muhimmiyar magana da nakeso muyi dan Allah nasanka da hankali"
Hankalin Mubin na titi dan bai bi dasu ta anguwarsu ba, ya ƙarawa tafiyar tasu nisa sosai ko ina zai kaisu oho,
Juyowa yayi a hankali kafin yace "ina jinki"
Ya mayar da hankalinsa ga titi.
"Yauwwa irin albarka, wannan yarinyar wato Ilhamatu ita nakeso ka aura tanada hankali ga nutsuwa, gashi kullum ita keyi min wanki da guga har ƙasa take durƙusawa ta gaisheni"
Ƙiii..!!! kakeji Mubin ya taka burki kamar zasu kifa, Kakus tahau salati tana ihu tana cewa "nashiga uku ni ƴar Ali da Ahmadu zai kassarani ko uwarka ta tsufa banajin zatayi ƙarko na"
Maganarta ta bashi dariya, dayake zancen na maƙiyarsa ne wato ni, yasa shi cin magani.
Suna isowa bakin get ya dannawa ƙofar motar saƙata tare da juyowa ya yace "Hajiya Kakus wallahi tallahi na rantse miki da girman Allah, idan kika sake yunƙurin maganar Ilham a kaina saina mayar dake gida insa miki maganin bacci, kuma kika sanarwa dasu momy kuji jiki keda Ilham ɗin zan wahalaku, garama kija baki kiyi shiru".
Baki a hangame Kakus ke kallon Mubin wai harda gargaɗi yake mata, abin mamaki.
"Wato birni ya saka fitsara ko? nizaka duba kace zaka yi mana rashin kyautawa ka ci ƙwallo yaro"
Suna shigowa gidan Kakus ta fice tana kuka.
Ina durƙushe a parlo ina goge TV da sauran kayan parlon naji shigowarta tana kuka, Momy dake jere abinci a dining ta ƙaraso da sauri tana cewa "hajiya lafiya?"
Mubin daya shigo yanzu yai saurin karɓewa da "Momy cewa fa tayi in siya mata ƙuli-ƙuli nace mata ta bari zan aika waccar ya nuno ni, ta siyo shine take kuka"
Kakus dai takasa magana tsabar mamakin ƙaryar da Mubin ya lafta mata.
Washe gari Dady ya dawo daga tafiya, ya dawo da tsarabar kayayyaki su atamfofi da lace da hijabai kai harda kayan abinci irin na company ɗinsu, kasancewar suna sarrafa abinci kuma su girkawa,
Washe gari Kakus da kanta ta kawomin lace pink color mai masifar kyau da mayafi milk color wato kalar flowers ɗin jikin leshin,
Nayi tsalle sosai na durƙusa har ƙasa ina cemata nagode Allah ya ƙara nisan kwana Allah ya albarkaci rayuwar danginmu baki ɗaya Allah ya buɗawa dady"
Cike da farincikin ɗimbin adu'oi da Ilham tayiwa Kakus ta nemi guri a wata kujerar roba dake can gefe ta zauna kafin tace "wato nayi miki sha'awar auran wannan makirin yaron wato Mubin, amma bashi da kyakkyawan hali sam baiyo gadon ubansa ba, ƙila a dangin nono ya gado wata ne"
Ilham ta waro ido, kafin tace "Hajiya aure fa kikace mufa talakawa ne kinsan Allah bamu da fili namu na kanmu"
Kakus ta dakatar da Ilham ta hanyar cewa "talaka da mai kuɗi duk Allah ne yayi su dan haka ki dena tunanin talaka zaki aura, inaji a jikina zaki auri wannan makirin"
"Taɓɓ bana sonsa"
Nace ina taɓe baki.
"Ƙarya kike yarinya, babu macen da zataga santalelen saurayi irin Mubin tace beyi mata ba dan haka sha kuruminki inhar ina raye kin zamo matarsa an gama, kinada hankali, girmama na gaba dake ga ilimi, dama Allah yace ka zaɓawa ƴa'ƴanka uwa ta gari gashi ya samu"
Kunyace ta rufeni na rufe idona ina cewa "Hajiya anyimin miji"
Na fice da gudu.
Ina zuwa parlo na tarar da Mubin shida momy da dady, bayan na gaishesu shikam bai amsa ba, dama nasan bazai amsa ɗinba,
Kitchen na wuce na ɗora girki dama lokacin 12:pm abincin rana, shinkafa da taliya nayi mai miya, sai vegetable daya wadata a ciki da yankakken dafaffen ƙwai,
Ina gamawa na jere a dining zan koma kitchen inyi wanke-wanke dady ya kirani,
Na ɗauka maganar ɗazu Hajiya ta faɗa masa har ina zufa na durƙusa nace "gani Alhaji"
"Gashi wannan ki kaiwa babanki ga 5k kuɗin ɗinki, idan kin tashi tafiya ki tafi masa dashi"
Tsabar farinciki na fashe da kuka, nace "Allah ya faranta muku Allah ya saka da alkairi",
Dukkansu suka amsa da Amin banda Mubin dake zaune yana kallon TV.
Tashi nayi hannuna riƙe da shaddar da kuɗin nabar parlon Hajiya na tayani godiya.

Kwanci tashi babu wuya yau kwanan Hajiya wato Kakus goma a gidannan, munyi sabo sosai gashi jininmu ya haɗu, zaune muke a parlo ni da ita muna hira momy ta tafi kasuwa, na bata labarin taron da akayi

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment