Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna yimin, momy dady Kakus da Ibrahim duk sun hallara a hospital ɗin,
Murya kamar ta mai koyon magana nace "yauwa ina Abbana"
Dady ya matso kusa dani ya kamo hannuwana yana mammatsawa yana yimi sannu, fuskarsa cike da damuwa, Kakus ma ta matso tana ta jeramin sannu.
Kwananmu huɗu nida momy aka sallamemu muka dawo gida, cikin ikon Allah Abba bai zoba koda akace muɗin ƴan uwa ne, Mubin ma babu labari dan ko leƙowa beyi ba, ran momy da Kakus kai harma da dady in yayi subu ya ɓaci, Ibrahim kuwa kusan kullum yana hanyar zuwa gidan momy dubani,
Bayan one week naji sauƙi sosai, na fara shiga kitchen taya momy aiki,
Wata ranar lahadi muna zaune a parlo nida momy da Kakus muna kallo, dady ya shigo yana cewa "Hajiya tare da baban Iham muke" na miƙe da sauri Kakus da momy suka washe haƙora, Abba yayi sallama muka amsa masa, ina ganinsa na fashe da kuka tare da toshe bakina,
Mirmishi Abba yayi kafin yanemi guri ya zauna, nima na zauna, ina bin dady da ke cewa "yaya ka ƙaraso mana, "waye" nace ina kallon ƙofar ɗakin, Alhji Bashir ne ya shigo tare da durƙusawa ya gaishe da Kakus,
Ƙin amsawa tayi cikin ɓacin rai tace "ka ficemin bana son sake ganinka a tare dani"
Tambayar da nayiwa kaina shin wannan kuma "waye a cikin family?"
Sakkowa yayi daga kan kujerar da yake zaune ya durƙusa gaban Kakus yana cewa "dan Allah kiyi haƙuri ki yafemin hajiya, nasan haƙƙin uwa akan ɗanta kana da kuma haƙƙin ɗa akan mahaifiyarsa, dan darajar fiyayyen halitta (s.a.w) ki yafemin wallahi hajya bazan sake nuna rashin kulawa a gareki ba"
Wani irin kuka Ahji Bashir yake mai wuyar fassarawa, wanda komi rashin imaninka dole ka tausaya masa kuma ka tayashi bawa mahaifiyarsa haƙuri.
Dady da momy da Abbana dukkansu naga sun zamo ƙasa suna roƙon Hajiya ta yafewa Alhji Bashir, sai da Kakus ta share hawayen daya fara sintiri a fuskarta sannan tayi musu alama da hannu su koma gurin zamansu, bayan sun zauna kowa ka kalla fuskarsa babu walwala, ta fara magana kamar haka "Ɗan Tala (Kasancewarsa ɗan fari bata kiran sunansa) kasan tun bayan mutuwar mahaifinku na kasance cikin kewa, gashi duk kunyi aure, koda nake cikin garin Kano ai bai wuce kazo ka gaisheni ka koma ba, bance sai ka bani wani abu ba, ga Abdullahi nan kullum yana cikin hidima dani, kuma ka fishi arziƙi nesa ba kusa ba"
Alhj Bashir ya kuma cewa "ki yafemin"
Kakus tace "na yafe muku ubangiji ya abarkaci rayuwarku, ta nuna masa Abba tace "yaron ɗan uwa nane, ta bashi labarin inda suke, da sauri Alhji Bashir yaje ya rungume Abba kafin yace "kutashi muje muga gidansa dan mu dunga zukunci da matarsa" bansan lokacin da hawaye ya zubomin ba, Abba yace "kaga ƴar tawa nan, ai mahaifiyarta ta daɗe da rasuwa tun tana ƙarama"
Alhji Bashir yace "bakayi wani auran ba kuma ?" Abba yayi murmishi kafin yace "sai na aurar da Ilham"
Da sauri Kakus ta amshe da ku haɗe dukiyar aure zamu tafi ƙauye asan halin da ake ciki, tunda shi marar kirkin yayi mana ƙaura"
Alhj Bashir yace "meya sami ɗan nawa?"
Kakus tace "wooo ai ɗannan naka halinsa sai shi, kaga inda ya..sai Dady yai saurin tarar numfashin Kakus sbda Abba, dady yace "akan maganar auranan nefa kawai shine yaketa fushi"
Alhj Bashir ya miƙe tare da cewa yana ta inane?" Momy tai saurin tashi tace "ai ya fice tuntuni" sbda bata ƙaunar Dady ko wani hatta Kakus suje suga halinda yake cikin bayanni da ita da muka gani,
Washe gari aka shirya zuwa ƙauye gurin manya akan maganar aurena da Mubin, ban isa ince bana sonsa ba, tunda har Abbana ya amince.
Ya rage nida momy sai Mubin da yanzu ya shigo,
Ina ganinsa na ruga ɗakina da uban gudu,
Zama yayi kusa da Momy kana yace "momy yunwa nakeji"
Ko uffan momy batace masa ba, ya gama maganarsa ya miƙe, momy ta dakatar dashi ta hanyar cewa "Mubin ni zaka tozarta ashe shaye-shaye ka farayi ko ince kakeyi ban sani ba?"
Mubin ya durƙusa gaban momy tare da kamo hannayenta yace "momy dalilin dayasa na faɗa wannan halin abu ɗaya ne, "ni banason Ilham auran dole kukeson yimin, bawai ina baƙincikin kasancewarta ƴar uwata ba, kawai dai bani da ra'ayin...! "dalla rufemin baki an gaya maka Ilham ɗin ajinka ce? da zaka dinga kusheta, karkaji ance ƴan mata na layi a kanka itama samari wani na doke wani haka akeyi mata layi"
A gigice Mubin ya ɗago idanuwansa da suka sauya yana kallon momy, bansan ashe faɗa takeyi masa ba, na fito ina cewa "Yaya Mubin ga abincin, na miƙa masa soyayyar doya da dankalin turawa, da miya a gefe, zai ɓarar da tiran momy ta daka masa tsawa ta shiga surfa masa ruwan masifa kamar bazata dena ba, ta ƙara da cewa "idan akayi masa auran yafi hankali, niko na koma ɗaki da suri na zauna naci dankalin, sai yanzu na tuna dukkanmu dagani har momy babu wanda yayi karin kumallo.
Sai dasu Abba sukayi kwana uku sannan suka dawo gida,
Suna isowa naje da gudu gurin motarsu ina cewa "sannunku, kowannensu kallona yake cike da kulawa, naɗan matsa tare da buɗe musu ƙofa suka fito suna sanyamin albarka.
Kai tsaye muka ɗunguma zuwa cikin gidan,
Bayan dady da Alhji Bashir sun zauna da Kakus da Abba, momy da Mubin sukayi musu sannu, dady ko kallon Mubin beyi ba,
Bayan an kawo musu abin taɓawa kowa yaci,
Aka baje kolin hira, Kakus ta fara bamu labari, tana cewa "ƙarshen tuka tuki tukkk Hama dai ta haukace ashe ko aihuwa bata taɓayi ba gashi ta tsufa tukuf, liman kuwa yayi shekaru da rasuwa, munje mun sami ƙannen Liman da ƴan uwanmu na gurin uwa an yanke dukiyar aure har ansa rana wata biyu masu zuwa, muna fatan Allah ya nuna mana"
Alhaji Bashir yace "malam Abubakar na baka gidana dake Jambulo" dady yace "nikuma na ɗauke komai na game da maganar aurannan kome ake buƙata a tambayeni ko nawa ne"
Abba da Kakus suka fashe da kukan farinciki, Mubin kuwa ya koma kamar gunki, kiran sallahar magrib da akeyi ne ya tashesu daga hirar zumunci da sukeyi, sukaje kabbara sallah.
Washe gari Dani da momy da Kakus da Dady da Alhji Bashir muka ɗunguma a motar dady zuwa gidan da Alhj Bashir yaba Abba,
Gida ne haɗaɗɗe madai-daici harda get, da muka shiga ciki kuma ɗakuna ne manya-manya zan iya ce muku mu haɗu a parlo, daga can gefe kitchenne babu abinda babu a ciki, Kakus tayi matuƙar farinciki, Abba kam ya rasa ta cewa sai cewa yake "Allah ya daɗa arziƙi"
Anan muka bar Abba muka dawo gida,
After 2weeks, Safiyar ranar Assabar ta kasance safiya mai ɗimbin darasi a rayuwata, sbda a ranar ne momy ta zaunar dani a bedroom ɗinta, wanda tunda nazo gidan zan iya ƙirga shigata, zaune muke aman bed nida ita,
"Ilham.."
Momy ta kira sunana "na'am" na amsa tare da sunkuyar da kaina ƙasa, sbda inajinta kamar mahaifiyata wacce ta haifeni,
"Inaso ki koyawa Mubin soyayyarki a zuciyarsa, ina so ki zamo masa jigo ko ince wani ɓangare na rayuwarsa, inaso ki zamo masa mai saita shi ta hanyar kula dashi, kafin ku kasance a matsayin ma'aurata, nasan abin da yayi miki tabbas bai kyauta ba nasan ko kaɗan baiyi miki adalci ba, inada manufata shiyasa na faɗa miki hakan pls ƴata karkice a'a"
Momy ta ɗaureni da jijiyar jikina, a ganina mai zata nema a gurina ta rasa kash dole inyi mata biyayya sbda ko farkon zuwana bata ƙyamaceni ba balle ta nunamin bambanci,
Ranar haka na wuni jiki babu ƙwari.
Washe gari da asbha bayan munyi sallah, ƙarfe 7:pm muka fito kitchen muka dafa yam balls da Ajoke rice da charcolit chicken, sai farfesun kifi wanda Kakus tasa ayi mata, muna gamawa mukayi kunun aya da carrot juice, jere abincin a babban tirai nayi naje dinning na jeresu, na dawo kitchen muka wanke kayayyakin da muka ɓata, momy ta koma ɗakinta yin wanka nima na koma nawa ɗakin nayi brush na watsa ruwa, na shirya cikin shadda mai ruwan ƙwai tasha stone work ɗinkin doguwar riga ta zauna a jikina sosai, bansan nayi kyauba sai dana kalli kaina a mudubi, na feshe jikina da turare na fito hannuna riƙe da wayata, ina dosowa parlo naji momy na tafi, ƙarasawa nayi ina dariya, dady ya fara tsokanata wai ina zanje nasha kwalliya hak? Kakus ta taɓe baki tana cewa "nifa kishina ya motsa nima kwaliyar zani sbda tsaro"
Janyo kujera nayi na zauna, kallon warmrs ɗin nayi kafin nace "momy an kaiwa Yah Mubin nasa ne?" momy tayi murmishi kafin tace "ƴata ke nake jira" rufe fuska nayi na ɗauki wani haɗaɗɗen foodflaks mai hannu da juice na fice...!

Wayoo masoyana anan zan dakata hilis, me kuke tunanin zai faru, idan taje a karo na biyu? tofa auran yana yiwuwa kuwa? kai in taƙaice muku bayani akwai cakwakiya a gidan Mubin, Abban Ilham na auro masifaffiya, Kakus taci ubanta 😂barin ƙyaleku anan.

Masu comments sai mun haɗu a paid group much love 😘

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*



1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*
_Miss Hajo_


Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*


Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.


Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144


Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎....

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224



*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment