Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kintashi lpy sis cikin shagwa6a tace ”lafiya lau , a d'a rare ya zauna a dining chair d'in yayi karin kumallo ,tunda ya zauna fara'ar fuskar dady ta gushe , shigowar Bash ce yasanya Harun juyawa , sanye yake da gajeren wando iya guwai warsa sai singlet fara a , k'arasowa yayi yace ”good morning dad ,good morning mom, amsawa sukayi cike da kulawa suna yimasa ya aiki ,dady ko janyo Bash yayi kusa dashi yazuba masa farfesun kaza , Fauziya ce tace ”ya Bash inason muyi wata magana saboda is very important to me and yau lol , kashe mata ido yayi yace ”oky yanzu dai kibari na gama sai muje muyi ko , suna had'a ido da momy ta galla mata harara , Harun ne ya dubi gefen da Bash yake zaune yace ”brother babu magana ne , cikin zafin rai Bash yace ”bana magana da y'an iska irinku , yana magana yana nuna Harun , hankalin su momy ne yakoma gurinsu , yacigaba da cewa wlh dady ciki yayiwa wata yarinya yanzu gashinan iyayenta suna nemanshi ido rufe yama samu na rufa masa asiri , a razane ido yai ja Harun ya d'ago yana kallon Bash yace k'iyayyar mu harta kai ga kayimin sharin zina ?"nine fa d'an uwanka , dariyar mugunta Bash yayi yace ”a da kake d'an uwana amma yanzu an sauya bani babu abota da mazinaci !! kalmarnan ba k'aramin dukan Harun tayi ba ,har lokacin idon Momy da dady da Fauziya na kanshi ,wasu hawaye ne masu zafi suka kwaranyo daga idonsa ya had'a hannuwansa biyu yace ”na rantse da Allah dady da momy ku yarda dani ko kula y'ammata banayi walhi , wani mari dady ya wanka masa yana cewa d'an iska dama shiyasa kake shigo mana gida ?"to kull kar in sake ganinka a ginanan kaje can 6angaren ka amma nayi maka iyaka da iyali na so get out ko bakaji ba , Harun na kuka yana cewa dan Allah ku amince da magana ta, haka ya fice zuciyarsa babu dad'i ."



Dady ne ya kalli momy yace ”kinga abinda yaronnan ze janyo mana ko ? sunkuyar da kai momy tayi hawaye na zuba a fuskarta ta d'ago ta dubi Bash tace ”Bashir kaji tsoron Allah kuma kasan zaka mutu kaje ka tarar da Allah shin gaskiya ne ko k'arya ? Bash ne yatashi yana mita , ni dama ai ba'a yarda da maganata ya fice , a hanya ya had'u da Harun ya tsuguna ya dafe kansa , dariya Bash yasa yace ”d'an samari kana lokaci , bai sami damar maidawa Bash martani ba ya mik'e jiki na rawa yanufi part d'inshi , gado ya fad'a tare da sakin kuka mai ban tausayi .



Rurin dayaji wayarsa na yine yasashi cirota a cikin aljihu bai mai number ba 'amma tunda yafara zuwa sabon gurin aiki bari dai ya d'aga ,yana d'agawa yaji ance Malam Harun nine ma manjan ma aikatar ku , kasancewar baisan ko waye manaja ba yasashi gaisheshi cikin ladabi , mutumin da yakira sunanshi a matsayin manaja , yace ”inason mu had'u a gidan Zoo sabo wanda kasani ,hak'ika Harun ya firgita amma tunda umarnin manaja ne dole yabi , haka ya share hawayen fuskarshi ya mik'e yashiga toilet yayi wanka yana fitowa ya shafa mayukansa masu k'amshi ga turaruka ,yasanya ya d'auki k'ananun kayansa ya sa ya d'aura agogo , ya dauki wayarsa da key d'in motarshi ya fice , yana shirin shiga motar yaji wani kiran yasake shigowa , d'agawa Harun yayi cikin rawar jiki yace ”manaja ga ninan zuwa , cikin sauri ya shige motar yatada ta yanufi titi tafiya yakeyi amma gabanshi na fad'uwa ...✍️.



Vote me on wattpad
♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_


*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020


Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk


Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2



________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 9 & 10

____Bash ne shida Fauziya a bedroom d'insa kwance take yana wasa da gashin kanta ,kanta ta d'aga tayi masa rad'a a kunne , mik'ewa naga sunyi ta zura hijab suka fice , Allah ka karemu da rayuwar dabbobi🤦‍♀️,zama yayi a cikin mota yana jiran fitowar Fauziya ,bedroom d'in momy taje ta sameta a zaune tana goge mirror , gefen gadon tasamu ta zauna ta rik'o hanun momy ta shagwa6e fuskar ,momy ce tace ”to shagwa6u ,meyafaru ?" cikin shagwa6a tace ”momy zanbi ya Bash shopping , momy ce ta dubeta tace ”mezakije siyowa , turaruka cewar Fauziya , to Allah ya tsare ki kula da kanki please ,oky momy natafi , tashige mota suka wuce , suna tafiya suna hirarsu wacce ni kaina banajin abinda suke fad'a ."


Umma na fito da abin gwajin cikin taga ya zana mata layi biyu , waro ido tayi cikin tuhuma tace ”Asma'u tsiyar da zaki janyo mana kenan?"shikenan na shiga uku cewar umma ,Asma'u dake zaune ta sunkuyar da kanta k'asa ,idanunta na kan shinkafar da take tsincewa tace ”Umma dan Allah kiyi hak'uri dan girman Allah , wani wawan mari umma tabata yayi dai dai da shigowar Malam , cikin alamun tambaya ya zauna yana ”cewa meyafaru kike dukan budurwa kamar wanan gaskiya bai kamata ba , hawayen da Umma take k'ok'arin 6oyewa ne sukayi nasarar zubo mata , Malam daya kasa gane me yafaru ya dakawa Umma tsawa yace ”bana san sha shanci ina tambayar ku meya faru amma duk cikinku babu mai bani amsa ? juyawa malm baya umma tayi tare dacewa ”to cikin shege Asma'u tayo , mik'ewar da Umma zatayi ta yanke jiki ta fad'i , Asma'u dake cikin tashin hankali ta nufi d'akin umma a d'an madai_daicin fridge d'insu wanda yad'an ji jiki ta d'auko ruwa a gora ta yayafawa Umma , ajiyar zuciya umma ta sauke tare da cewa wlh kinyi asara a rayuwarki duk tarbiyar da muka baki bin mazan waje yafi yemiki komai ko? Malam da zuciyarshi ta hassalo ya mik'e yashiga d'akinsa da yake ajiyar bulalai ya d'auko mai baki biyu yakuma d'auko mai baki d'aya ya had'asu yashiga , zabgawa Asma'u , saida yayi dukan ya gaji dan kansa yaga idanuwanta ne masu k'iftawa alamar taji jiki , zama yayi ta gefenta ya yarfe gumin goshin sa yace ”Asma'u yanzu irin tarbiyar da na baki kenan ?"sakaiyyar da zakiyimin kenan wlh bakiyi mana adlci ba kin cucemu kin 6atawa gidannan suna , saita bulalar yakumayi yana shirin zabga mata yace ”ubanwa yayi miki ciki ?" rufe bakinta tayi tana shirin yin amai , takasa mik'ewa dole ta kwararo amai a gurin , Malm ne yace ”tambayarki nakeyi kokuma kinason ink'ara miki bulalar ne , shiru tayi tak'i magana , Malam ko kamar jira yakeyi tak'iyin mgna ya zuga mata bulalar yana shirin k'ara kaimata na biyu ne tace ”malm kayi hak'uri zan fad'a maka , to ina saurarar ki cewar Malam ,Asma'u ce tayi jimm can kuma tace ”Harun ne , gyara zama Malam yayi yace waye Harun??? ,d'ane ga Alhaji Muntari yayan Alhaji Yusuf mahaifin Bashir ,Malam ne yace ”kina nufin kintsatsen yaronnan dashi kukayi watsewar ?"sunkuyar da kai k'asa tayi Malam ko saida yakuma yimata lilis sanan yafice domin yin sallah la'asr."




Da isar Harun gidan Zoo d'in ya hango wani bak'in mutumi ya rufe fuskarshi , yana shirin ciro waya yakira wanda yace ”yazo aka shak'e masa wuya aka sanyashi a mota sukabar gurin ."



Washe gari malm ta saka Asma'u a gaba wai saita kaishi gidan wanda yayi mata abin kunya , saida suka hau a dai daita sahu ta kaisu har zuwa anguwar , Malam ne yatsa a nesa da get d'in gidan yacewa Asma'u , taje ta k'wan k'wasa , tafiya take cikin sanyin jiki ta nufi get d'in , k'wan k'wasawa tashiga yi , megadi ne yace waye ?"Asma'u dake waje tace ”nice munzo gurin masu gidanne , to bari a sanar musu cewar mai gadi , dawowa yayi yace ”alhajin yana ciki wai kushiga , Malam ne yataso da sanyin jiki , shigewa sukayi tundaga k'ofar dazata sadaka da cikin gidan Malam jikinshi yayi sanyi dubada ganin yanayi dakuma tulin nerar da aka kashewa gidan yasashi tafiya kamar mai k'irga k'asa , suna isa k'ofar da zata sadaka da baban palorn gidan sukaja suka tsaya , jin alamun bud'e k'ofa ne yasa su Malam razana Fauziya ce ta fito cikin riga k'arama mai siririn hannu sai wando gajere fari tass , da ganinsu tasan ko suwaye , cewa tayi gurin dady kukazo ne ?"Malam na rawar jiki yace ”eh jagora tayi musu suka shiga k'ayataccen parlorn da yakuma tsinkawa Malam zuciya dan yana ganin idan yace ”Harun ne yayiwa ,Asma'u ciki tabbas bazasu yarda ba , da shigarsu suka tarar da momy zaune ta pillow a ciyanyarta zama sukayi a k'asa suka gaida momy , amsawa tayi cikin sakin fuska tace ”daga ina kuke ”ban ganeku ba , malm ne yace ”dama nazone akan maganar Harun ,Harun momy ta mai maita cikin fad'uwar gaba , me Harun d'in yayi ,kalon Asma'u Malam yayi yace ”wanan tarinyar ita k'adai Allah yabani a duniya , munbata tarbiyar dai dai gwargwado kuma tayi karatun islama tayi na boko tana sakandire , to ni inacan gurin neman abinda zamusa a bakin salati nadawo nasamu mahaifiyarta tana yimata fad'a yanzuma munbaro ta a gida tayanke jiki ta fad'i , dady dakejin komai yana daga saman step yace ”malm ban gane ba?" Malam ne yace "Harun ne yayiwa y'ar wajena ciki !!momy da taji gabanta yayi mumunan fad'uwa ta nuna Malam da yatsa tace ”kull Harun ba d'an iska bane walhi , Malam ne yace ”to gatanan dai insharri nayimasa Allah yasaka masa ,itace tagayamin , dady ne ya k'arasa saukowa yace is okay , kome akace Harun yayi bazanyi musu ba , amma kuyi hak'uri insha Allah dole ya aureta what!!! momy tace ”hankali a tashe wanan bazai yuwu ba wlh , haka kawai bawan Allah beyi Abu ba ace yayi ?" haka su Malam suka mike ,dady ne yaciro dubu ishirin 20k yabasu suka fice daga gidan."




Mom ce taketa gwada number Harun amma switch of yau kwana biyu kenan , Hajiya ce tace ”ki kwantar da hankalinki tunda yasami aikinnan baicika zuwa a kan kari ba , badan mom tayi na'am da maganar hajiya ba ta sai saita yanayin fuskarta , amma tanajin gabanta na yawan fad'uwa , alwalh tayi tazo ta tayar da sallah , addu'oi tadin kuwararo wa Harun na bud'i dakuma na kariya ta dad'e akan sallahya daga nan ta mik'e tanufi bed ta kwanta da tunani kala kala a cikin ranta."



Basma ce kwance tarasa meke kimata dad'i rabonta da ganin Harun a makaranta harta manta ko muryarshi bataji , momynta ce tazo ta zauna kusa da ita tana rarrashinta akan taci abinci koda ad'anne ,haka dai Momynta ta tilasta mata tutura abincin...✍️.

♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_


*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020


Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk


Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2


*_SALON ALK'ALA MINTA DA BANNE✍️_* 💃



________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


EPISODE 11 & 12


____Wani d'aki aka shiga dashi mai duhu , magunguna kala² mutanen suka d'irka masa dan zasukai su hud'u , kwanciya Harun yayi bacci mai nauyi ya kwashe shi , bayan 30mins ,ya mik'e alamar jikinnasa yana yimasa wani iri sha'awa ce ko kuma buk'atar mace a kusa dashi ne yakasa ganewa , mutanen ne suka shigo jikinshi babu k'wari dan bazai iya magana ba bare har ya ta6uka wani abu , wanka suka masa suka ciro masa wani sabon kaya wando ne iya guwai wa sai riga irinta nigogi , haka harun ya koma kamar d'an arna , wani jan abu suka shafa masa a kansa tare da mik'o masa cup da Vijumilk a ciki da wani abu da suka sanya, jiki na rawa Harun ya kar6a yasha mik'ewa yayi yana layi yana cewa beb kizo gareni man , wata budurwa da alamu ba musulma bace "wani gaye da gefen , Harun yayi mata alamu da ido , tafiya tayi da wasu shegun kayan jikinta da kana ganinsu kasan shed'an yasami mazauni , kwanciya tayi a cinyar Harun tana shafashi had'i da sakar masa zazzafan kiss , daganan lamarin nasu ya k'azanta harta kai ga Harun ya cire kayan jikinshi sun yi zina shida wanan budurwa , nishi yake saukarwa kamar wanda yayi gudu , itako shu'umar cigaba tayi da kwanciya a jikinsa , a lokacin Harun bai dawo hayyacin sa ba , yana kwance a gurin tsirara ,haka suka d'aukeshi suka kaishi toilet suka yimasa wanka , kayansa wanda yazo dasu suka sanya masa ,mik'ar dashi sukayi suka sanyashi a mota , direct gidan su suka nufa dashi ,ganin babu kowa a tsakar gida suka turashi cikin d'akinshi suka kullo k'ofa ."




Zaune Asma'u take tana da ddna wayar da Bash ya siya mata , tuno hud'ubar da bash yayi mata tayi akan cewar ko me za'ayi mata karta sake tace shine yayi mata ciki tace ” Harunne , tausayin Harunne ya kamata , dukda bata sanshi ba amma yanada kya kyawan hali lokaci guda hankalin ta ya tashi tana tunanin anya tayiwa Harun adalci kuwa , amma kuma ai bata isa tace ” ba Harun d'in bane tunda maganar farko da ita ake amfani ,wani hawaye ne yazubo mata mai tattare da nadama ."



Bacci yakeyi ko motsi bayayi , sallamar da akayi ne tasa shi k'ok'arin farkawa , jin idanunsa sunyi masa nauyi yayi dak'yar ya bud'e idon ya d'orasu a kan wacce ta shigo , mom ce fuskarta sha6e sha6e da hawaye , tace ”Harun ina kashiga ?"Harun babu magana sai dai yana binta da ido , kiran drivern daya kawota tayi. yana shigowa tace ”ya temaka mata tasa Harun a mota , babu musu ya kama Harun mom ma ta rik'eshi suka nufi mota , direct hospital suka wuce da azama aka kar6e su sbda nan asibitin su momy ke zuwa kulawa aka fara bashi ta gaggawa , mom banda kuka babu abinda takeyi , wani doctor ne yafito hancinsa sanye da abin rufe hanci yace ”hajiya wanan yaron akwai matsala 'a tattare dashi , yasha abin da zai gusar masa da tunani , bayannan ba a bisa k'a ida yasha ba sbda abubuwan dayasha na maye dakuma na tada sha'awa suna neman salwantar da rayuwarsa, rik'e baki momy tayi tana kallon likitan harya gama jawabinsa ya fice .*




Dady ne yake yiwa Bash shirya shiryen tafiya India karatu komai ya kammala ,gobe insha Allah jirgin zai d'aga , momy ce take cewa dady ,nidai bana son tafiyar shi k'asar waje gaskiya , wlhi tarbiyar y'a y'a watsewa takeyi , dakatar da ita dady yayi tare da cewa inhar bazakiyi masa fatan alkairi ba to kija bakinki kiyi shiru , karki manta shine magaji na kuma inada buk'atar yayi karatu sosai , mik'ewa momy tayi ta wuce bedroom d'inta tafad'a gado tana kuka , Fauziya ce tafito sanye da dogon hijab ta gaida dady washe baki yayi yace ”malama Fauziya ke a wace k'asar kikeson yin karatu ¿ shagwa6e fuska tayi tace ”dad nikam abarni a gurin momyna , dariya dady yasa yace ”to brother'nki gobe zai wuce , fatan alkairi tayi masa tana tayashi murnar cikar burinsa ,dan Bash ba karatu zashi ba , sun shirya shida wata budurwar sa zasuje honeymoon lol ."


🤭an rainawa dady hankali 🤏😎.


Harun kusan awan shi d'aya a hospital ,baiyi mgna ba sai dai bin mutane dayakeyi da idanunsa , doctor ne yace ” Indai yaron nan yakuma kaiwa 1hour bai farka ba idanunsa ne a bud'e to dole zamuyi muku transfer wlh , mom da tunda suka kawo Harun take kuka yanzun ma kukan tasaki tana jijiga shi amma babu magana sai ido ."



Washe gari plane d'in su Bash ya d'aga zuwa India babu wanda yasa budurwar tana cikin jirgin kasancewar bai nuna alamun tare da wata sukazo ba , momy da dady da Fauziya sai d'aga masa hannu sukeyi daganan suka d'aga , dady ne yawuce dasu momy supermarket , kaya suka jido masu tsadar gaske daganan suka wuce gurin shan ice cream , suka dawo gida ."



Kwance yake shi kad'ai a d'akin mom taje gida ta dawo doctor kuma yana office , tuno abubuwan da suka dinga faruwa dashi yayi a club inalilahi yadinga mai _maitawa wayo Allah na garinya gariya wayo mom!!! lokacin mom da hajiya sun taho suka dingajin hayaniyar sa da sauri suka k'arasa , yaci gaba da cewa wlhi sai Allah ya sakamin Allah baya azzalu mai Allah kayimin sakaiyya da gaggawa , hawayen da mom ke k'ok'arin 6oyewa ne suka zubo a fuskar da bata gushewa da zubarda hawaye , kujeru suka samu suka zauna suka fara kwararo masa adu'a, yunk'urin mik'ewa yakeyi yakasa , hajiya ce ta rik'o shi ya mike yana salati , bud'e idanunsa yayi ya saukesu a kan na momy da sukayi ja jawu kamar gauta , tausayin mahaifiyar tashi ne ya kamashi yanajin sonta na dad'uwa a cikin zuciyar shi , doctor ne yashigo d'auke da wata takarda a hanunsa da alamu ta sallama ce "cewa yayi dama tashinsa muke buk'ata to yanzu kubiyoni office saboda ka'idojin shan maganinsa , hajiya ce ta nemi guri ta zauna momy kuma tabi doctor , doctor ne yace ”kullum zai dinga shan maltina da madara sau uku a rana , mom ce tace ”wanan ba matsalar su , okay doctor yace tare da ciro magungunan daya sanyasu a leda , kinga wanan yana shansa zaiyi amai please kukiyaye dokokin insha Allah zai sami sauk'i godiya mom tayiwa doctor suka fice sbda komai mahaifin mom ne zai biya , tattarawa sukayi suka koma gida ."






Da isar Bash shida wata tantiriyar yarinya mai suna Bahijja ,Bahijja yarinya ce y'ar shekara ashirin da biyu ,ta taso cikin gata da nera batasan babu ba a rayuwarta , kasancewar iyayenta y'an boko ne yasa sukace bazatayi aure yanzu ba harsai ta kammala komai , hakan yasata fad'awa harkar karuwanci , kuma a mazan ma ba da kowa take hurd'a ba setaga mutum ya iya d'aukar wanka kuma wayayye ajin k'ar she bugu da k'ari mai bud'a d'en ido wanda kunya bata gabansa ...✍️.



Muje zuwa 🥰karku manta da salon alk'alamin✍️marubuciyar taku kudai kubiyoni karkuce ina jamuku rai a kowanne page 😉hakan shizai sa kudingajin sha'awai bibiyar page d'in gaba ,dafatan kungane ko🤙.

♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_


*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020


Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk


Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2



*_Masu sharhi naga sharhin ku 🤙kuma ina godiya da soyayyar da kuke nunamin👏kuyi hak'uri jiya babu wanda na kula am sorry 🙏wlh kuna raina kuyimin uziri please 🥰.


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


EPISODE 13 & 14


__Wata k'awar Asma'u wace suke watse warsu tare ta shigo gidan su da sauri , Asma'u dake gyara d'aurin zaninta tace lafiya Rumaisa ?infa lafiya cewar Rumaisa , kujera yar tsugunno , Asma'u tabawa Rumaisa , ganin umma batanan yasa Asma'u cewa to wace gulmar kika guntso ?" cikin rad'a Rumaisa tace ”wlh Allah Bash yatafi k'asar waje , eeeh cewar Asma'u data dafe k'irji , k'asar waje fa kikace ?"wato ni yabarni nan ga shegiya ko , kuka ne ya ku6ce mata itako , Rumaisa ficewa tayi tunda tayi abinda ya kawota , zama Asma'u tayi tafara sak'a da war wara ."



Kwance Harun yake da wayarshi a hannunshi , watsapp ya hau yana kunna data sak'onni ne suka fara shigowa , wani video ne yaja hankalin sa ganin number babu suna , bud'e videon yayi , ganin shi aka fara nunowa sai kuma wata budurwa tsirara , haka shima tsirara , gyra zamansa yayi yafara tuno abubuwan da suka faru dashi dakuma fuskar wanda ya daukoshi sai dai ba lallai ya ganeshi ba kasancewar , fuskarsa a rufe take idanunsa da bakinsa ne a bude , a razane ya tsayar da vidion yana tunanin to da yaushe har ya aikata zina!!!?" innalilahi wayo Allah na ,dayake bashida wuyar kuka aikuwa yafara kamar k'aramin yaro , sak'one yakuma shigowa ta number me vidieon dubawa yayi ,yafara karantawa ...

_Barka dai maijin tsoron fad'awa halaka to gashinan yanzu saika nunawa danginka kazamo mazinaci , dan wanan yarinyar tace ”a kawo mata kai yanzu , kuma bazamu sa6awa umarninta ba , zaro ido harun yayi tacigaba da karantawa , waanan video da kake gani kana bijire mana saimun watsashi a social media , blocking number Harun yayi yana tunanin yin hakan shine hanyar datafi dacewa ,yakuma goge sak'onin duka , gaban shi na dukan uku _uku_



Bash ne kwance a gurin shak'atawa na k'asar waje ,k'afafuwan sa sanye suke cikin ruwa swimming pl.. yayin da Bahijja take gefensa ,tana sanye da pant da bra ,kasanceawar babu ruwan kowa da kowa ,kuma kowa kagani shek'e ayarsa kawai yakeyi babu mai kallon shi , kallonta yakeyi tana yimasa wasu abubuwa 'amma bai kulata ba , tasowa tayi ta zauna a kan cinyarsa tana hura masa iska a kunne , kawar da kanta yayi gefe , tunani yakeyi karfa Asma'u ta tona masa asiri sbda batasan ya taho ba , Bahijja ce ta dubeshi itama fuskarta da alamun damuwa tace ”da alama kana cikin damuwa amma inba komai ka fad'amin kozan iya temaka maka , Bash ne yayi dariyar gefen baki , kana yace ”wanan ba matsalar da ta shafeki bane just ki k'yaleni but yanzu bansan mgna okay Bahijja tace ”tare da tashi tabar gurin , tana cikin tafiya tana kar kad'a k'ugu ta bugi wani k'aton mutum , rungumeta yayi , yana murmishi itako Bahijja turarensa ne yasata k'ara ruk'oshi , d'agota yayi yana yimata dariya , ware idanunta tayi tace am sorry... hannu ya d'aga mata yace , zomuje room d'ina , kasa yimasa musu tayi yana rungume da ita suka wuce wani tsararen gida suka shiga , da shigarsu yace ”zo kiyimin wani aiki , tasowa tayi cikin yanga , ganin wani jan zane tare da kan mutum a d'aurin d'an kwali a k'irjinsa yasata mutuwar tsaye ,nunfashinta ne ke barazanar d'aukewa sbda inbazata manta ba.....



Mik'ewa Harun yayi ya shiga wanka bayan ya shirya ne ya nufi part d'in mom , samunta yayi kan sallahya tana adu'a zama yayi nesa , shima ya d'aga hanunsa , a tare suka shafa adu'ar , juyowa tayi tace ”son barka ykk sunkuyar da kai yayi yana gaida mom cikin kulawa ta amsa tare da cewa inason zamuyi wata magna dakai dumm!!! yaji gabansa ya fad'i , cikin zuciyarsa yace ”kardai mom tasan abinda yafaru na shiga uku, k'are masa kallo mom tayi cikin hikima da tausayawa tace ”Harun ? na'am mom ,inason sanin me kasha haryayi sanadiyar rashin maganarka , ka koma kamar me maye ?" karfa ka manta ko kayimin k'arya zan gane , Harun ne ya nutsu yace ”mom wlh Allah ina zaune wani mutum ya kirani yace ”wai yanason ganina shi manajan company d'inmu ne to shine ya yimin kwatancen , gunda zamu had'u , shine naje tun daga lokacin bansan meya faru ba , tausayin shine ya kama momy tasani sarai Harun bayason mai yin k'arya bare har shima yayi k'ok'arin yi , kuma tasan yanada mak'iya gaba da baya , hakan yasa tadage da yimasa adu'a , bayanin WhatsApp da ya hau aka turo masa video yayi wa mom , gumi ne ya wanke mata fuska tace wanan wane irin mutum ne ?"amma babu komai mu had'ashi da Allah kawai, kuka Harun ya fara yana cewa dama ba'a haliceni ba , shiii momy

Please Login or Register in order to submit comment