Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dawo daga hutu driver ya d'aukota sbda a boarding school take , tana hango Bash yayi shirin fita ta fito daga mata ta rungume shi , suka shige ciki , dady da momy da suka sauko yanzu suka fara dariya suna cewa oyoyo daughter , shiko dady cewa yayi shikuma Bash yaushe ya dawo?" momy ce tace ”jiya nima ko gayamin baiyi ba , dady dake dariya yace ”to muje dining muci abinci , Bash dake rik'e da mukullin mota yace dady nidai zani anguwa yanzu zan dawo , okay to sai ka dawo , momy ma Allah ya tsare tace ”masa , anguwarsu Asma'u ya nufa , da isarsa anguwar ya tsaya can nesa da gidan kiranta yayi a waya , cikin mamaki da sauri ta d'aga , tace ”Bash yaushe a gari number Nigeria nagani , cikin rashin fara'a yace ”in kinada lokaci kizo yanzu gani a waje , to tace ”batare da ya k'ara magana ba ya kashe wayar ."

Yamma ce kuma umma na zaune a tsakar gida , fitowa tayi da abin kwashe shara a hannunta , tana tafiya kamar mara gaskiya , umma ce tace ”bance kidena fitowa ba?" cikin in ina tace ”zan zani zan zubar da shara ne ,ko kallonta umma batayi ba Asma'u ta fice ,da hijab a mara ,tana fitowa ta saka hijab d'in , duk lek'en da takeyi Bash na kallon ta har lokacin da tasa hijab , cikin zuciyarsa kuma ranshi na k'una sosai wanan kucakar yake kulawa jibeta talauci yayi mata yawa kash , gyara zamanshi yayi yana shafa sumar kanshi , ganin bai fito a motar ba yasata bud'e murfin ta shige ,da fara'arta tace ”sanu da dawowa ka dawo lafiya?"lafiya Bash yace "tare da cewa ”nazo gurinki ne akan maganar da mukayi dake dakuma wace dadyna ya gayawa mahaifinki , so yanzu sonakeyi asan inda za'ayi , ki auri Harun , Asma'u ce ta dafe k'irji tace ”Harun!!! eh Bash yace ”alamun babu wasa a tattare dashi , gaskiya bazan iya ba haba ,Bash kamar ba musulmi ba ?" har Bash ya d'aga hannu zai kaimata mari sai kuma ya fasa ya dunk'ule hanunsa , Asma'u ki fahimceni karkiyimin mumunan fahimta indai kud'i ne karki damu ko nawa ne zan baki , Asma'u da jikinta yayi sanyi ta ce zanyi tunani , ta bud'e murfin motar zuciyarta babu dad'i ta fice ...✍️.




Kufayi hakuri da salon alk'alamin nawa sbda duk mai karanta book dina yasan salon sa 🥰 so da sababbi dakuma masu bibiyarsa kuyi hak'uri Ku biyoni insha Allah zanyi kokarin dena Ja muku rai 🤙.



comments and sharhi👌
♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_


*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020


Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk


Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


EPISODE 21 & 22


____Bismillah Harun yayi ya bud'e gat , mai gadi dake zaune a benci ya d'aga masa hannu yana cewa "Allah ya tsare mai gida , cikin fara'a Harun yaciro d'ari biyar ya bashi , Allah ya tsare mai gadi yakuma yimasa ,daganan ya fice batare da yahau mota ba , direct bakin titi ya wuya ya tari napep zuwa gidan su momy , kasancewar gidan babu nisa yasa basu dad'e ba aka iso , a k'ofar gidan mai napep yai parking , ya sauka tareda mik'o masa kud'in sa , bubuga get d'in yayi , mai gadi ne ya bude , yana ganin Harun ya washe baki yana yimasa sannu da zuwa , gaisawa sukayi ya shige ciki , da shigarshi yaci karo da dady da momy da ,fauziya da Bash yana zaune yana danna ,waya sallama Harun yayi cikin nutsuwa , momy ce ta fad'ad'a fara'arta tace ”oyoyo yaron kirki da sauri Harun ya k'araso gurin momy , tana mik'o hannu alamar yazo kusa da ita , yana zuwa zai kwanta a cinyarta ,dady ya daka masa tsawa , tare da cewa " kai d'an iskan ina ne ?"god'ai god'ai dakai kake shirin kwanciya a cinyar matata , to wlh kull kema kika kuma hukuma ce zata rabamu daku , tunda ke bakida hankali kema , momy ko kallon dady batayi ba a zuciyarta tace ”Bash yake hawa cinyata bana hanashi amma shi Harun ne za'a nunawa ban banci , bata bari maganar ta fito fili ba ta ja baki tayi shiru , Harun ne yaje gaban dady ya durk'usa yace ”ina wuni dady , wata uwar harara dady ya galla masa sanan yace ”lafiya , suna had'a ido da Bash ya sakar masa wani killer smile , tare da kashe masa ido d'aya , Harun ya kasa fasara wanan kalo mai cike da abubuwa na rashin kyautawa ."



Emanuel ne yafito sanye da gajeren wando , ganin Bahija na bacci yasashi murmishi ya shige toilet yayi wanka , yana fitowa ya shafa wasu matuka masu tsada da turare , ya sanya farar riga marar nauyi , ya kwanta , matsowa yayi kusada Bahija ya rungumeta yana kissing d'inta , lol duk abinda Emanuel ya keyi tana kallonsa , amma bata bud'e idanunta duka ba , matsota yayi sosai ya d'aga ,y'ar k'aramar rigarta ya fara shafo cikinta , yana jin soyayyar babyn har cikin ransa , yanzu kam tunanishi anya zai iya bawa k'ungiya ,jaririn da Bahija zata haifa ?"ya k'ara rungumo ta yana wasa da gashin kanta , daganan bacci ya d'aukesu , dama ba sallah sukeyi ba dukansu , washe gari Bahija ta tashi da san cin pizza , Emanuel kuwa yau hutu yakeyi kasancewar yau Sunday , haka suka shirya suka nufi wani katafaren shagon kayan k'walama , komai Bahija tace ”tanaso baya yimata musu , ya kashe mata kud'i sosai , bayan sungama da nan ne suka nufi kasuwa , shagon kayan jarirai , sosai ya jido kaya masu kyau ,amma cikin zuciyarsa sam babu dad'i."



Kwance Asma'u take tana bawa jaririnta nono , kira ne ya shigo wayarta , cikin sanyin jiki ta d'aga Umma dake zaune kusa da ita ta kasa kunne dan kwana biyunnan bata gane mata , Umma ce taji Asma'u na cewa ganinan zuwa , ajiye yaron tayi a cinyar Umma tana shirin sa hijab Umma tace ”Asma'u ina zaki?"gabanta ne ya fad'i tace ”zani gurin Bash ne wai ya siyowa yaro madara , hmm Umma tace ”cike da takaici , kafin Umma ta gama tunani , Asma'u ta fice , da fitar ta , ta hango motar Bash sauya tafiya tayi tana yanga , Bash daga cikin mota yaja tsaki yace ”banza marar amfani , tana isowa ta bud'e murfin motar ta zauna a gaba , shagwa6e fuska , Asma'u tayi tare da cewa haba Bash tun lokacin da ka gane inada ciki shikenan ka dena sakarmin fuska ko ?"sake fuskarsa yayi, yace ”no ba haka bane aiyuka ne zukayimin yawa kuma dai yanzu kinsan abinda ya kawoni , Asma'u ce ta d'aga hijab d'inta tare da cewa kaga breast d'ina wlh zafi yake yimin , wata uwar harara Bash ya doka mata tare da cewa wato kin d'auka yanzu zan iya had'a jiki dake ko , to bari kiji ,ko tsautsayi na fishi samako , dan haka karki kuma k'okarin yimin haka , ranta a 6ace tace ”bazan auri Harun d'in ba kai zan aura !!!."



Da fitar Harun daga gidansu momy ya fice ya tari napep zuwa makarantar su ,yana sauka a bakin get yaga makarantar a rufe , ji yayi an rufe masa ido tare da sunkucesa aka turashi cikin mota , tafiya sukeyi cikin wani jeji da bakajin k'arar komai sai na tsuntsaye , wani guri da aka had'ashi da buhu suka ajiyeshi tare da turashi cikin d'akin , suka rufo d'akin da wata sanda da tazamo a jikin buhun Harun ne ya farka daga mutuwar tsayen da yayi sabda tsabar tsoro ya bud'e idanunsa , ya Gandhi cikin wanan d'aki , ya Allah ka dubeni , wani gurnani yaji na namomin daji , cikin tsoro ya had'e hanuwansa duka biyu yana adu'a , neman hanyar fitowa yakeyi amma babu ko alamar gurin fitowa , shin nan ina ne ?".


Juyi yakeyi ko Allah zai bashi ikon ganin hanyar fita amma ina babu hali , Harun tunanin rayuwarsa ya fara tun farkon tashinsa har kawo yanzu bai ji dad'in rayuwa ba , banda wuya babu abinda yake sha , Allah kenan , tuno mom da Hajiya yayi ya fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai karatu , daga jin sauk'i nafito ziyara nakuma cin karo da wani iftila'in , laluba aljihunsa yayi yaga babu wayarsa babu komai a tare dashi , y'an kud'in da ya rik'o dubu goma suma babu su , tsananta kukansa yayi yarasa ihu zai yi ko me wama zai jishi ? ya mimik'e k'afafunsa yana salati ."


*_BAYAN KWANA BIYAR DA 'BATAN HARUN_*.


Mom ce zaune ido ya jeme tsabar kuka ,ga wani bak'i datayi , yau ne Alhaji zai dawo daga saudiya wato mahaifin mom , hidima sukeyi itada Hajiya amma jikinsu duk a sanyaye , komai cikin rashin walwala sukeyi , kira yayi a waya jirginsu ya sauka , Hajiya ce tace ”mom taje ta taho dashi itada driver , gyale mom ta d'auka ta shige mota suka nufi airport, datijon kirki kenan wato Alhaji Ahmad , sakowa yakeyi cikin takun k'asaita ko kwarjininsa ya ishi mitum dai daita nutsuwarsa ,yana gama saukowa ya iso inda momy take tsaye , harya yi mata magana bata sani ba , Aslamu Alaiki Fad'imatu , a razane mom ta ware idanunta tare da kallon fuskar mahaifin nata tace ”barka da zuwa Alhaji dafatan ka iso lafiya , janyo hannunta Alhaji yayi kasancewar ya gane motar gidansu ce yasashi shiga gaba mom kuma ta shiga baya, sunyi tafiya mai nisa sanan suka iso gidan , driver na parking ,mai gadi ya taso da gudu ya bud'ewa Alhaji muffin mota , rik'o hanun mom da itama aka bud'e mata yayi suka shige ciki ."


Sanu da zuwa Hajiya tayi masa ywwa Alhaji yace ”lokacin da ya ga mom ta zauna batare da tace uffan ba.
♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_


*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020


Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk


Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Facebook mom Islam

Bakandamiya mom Islam Habib


*🌹🌷Wanan page nakine shugaba tagari hak'ik'a samun kamarki sai an tona ina alfahari dake a kowane rubutu nawa*💃

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR
RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 23 & 24


_____Alhaji ne ya dubi mom cikin tausayawa dan tausayi take bashi tunda ta rasa mijinta tak'i aure , Zainab a firgice mom ta d'ago tare da kallon Alhaji tace ” na'am na fuskanci , kina cikin matsala ?"sunkuyar da kai mom tayi tace ”Alhaji kaci abinci gashican hajiya ta gama , murmishin su na manya Alhaji yayi yace ”tambayarki fa nakeyi , hawayen da take 6oyewa ne sukayi nasarar zubo mata , Alhaji bayason ganin 6acin ran mom , Yakuma magana cikin sanyin murya meyafaru?" son ,kawai mom ta iya cewa saboda matsanancin kuka , son ? Alhaji yace ”meya faru dashi ?"sun saceshi cewar mom , innalinali Alhaji ne ya kira Hajiya , cikin sauri ta taho tana cewa ai wanan yaron sai dai mutayashi da adu'a ,dan wlh suna son ganin bayanshi , bayan jinya dana gaya maka yayi ,to yanzu rabonmu da ganinshi kwana biyar kenan , Alhaji da ya nutsu yana jin zancen yace ”Allah ya baiyano dashi ,amma yau zan bada cigiya kowace kafa ta sadarwa insha Allah."




Emanuel ne zaune suna breakfast shida , Bahija , kallonta yakeyi cikin so da k'auna , kashe masa ido tayi tace ” haba wanan kallo haka , murmishi kawai yayi dan shikad'ai yasan abin ke cikin zuciyar sa , tasowa tayi ta zauna a kan cinyarsa tare da shafo fuskarshi tace ”my man two days naga komai naka ya canza ne , kodai akwai matsala ne ?" waya gaya miki babu wata matsala burina inga kin aihu lafiya ,my happiness, dariya tasa tana tace ”gobe zan koma hospital zaro ido Emmanuel yayi yace ” gaskiya abar maganar hospital d'innan , sbda kindena fita , cikin mamaki , Bahija ta dubeshi tana cewa "saboda me ?bai kulata ba ya shige bedroom d'inshi , rayuwa Emanuel yakeyi cike da fargaba sosai bayasan abinda zai ta6a lafiyar , Bahija musaman ma babyn dake cikinta dan Allah ya zuba masa san y'a ya'a ."



Bsh ne a mota yana tafiya yana jin kid'a ya k'ure volume sosai , wata budurwa ya gani a hanya , fara kya_kyawa , tana sanye cikin riga doguwa bak'a ,itama budurwar bak'a ce , hannunta sanye suke da tsadadun zobuna masu tsadar gaske , parking d'in motar yayi a gefe ,ya bud'e murfin motar ya fito ,isowa gurin wanan budurwar yayi , tare da cewa aslamu alaikum lol wa/alaikassalm , tace ”tana mumishin da yakuma baiyana kyawun ta , Bash ne yace ”inba komai y'an mata muje na rage miki hanya man , a'a kabarshi tace ”tana gyara zaman d'ankwalin rigarta datayi rolling dashi a kanta , Bash ne ya rik'o mata hannu , yasata back side shikuma yashiga gaba , suna tafiya yana kallonta ta mirror , cikin zuciyarsa cewa "yakeyi zan kwashi rabona dan naga kamar sabuwar budurwa ce , a ina zan saukeki , fashewa da kuka tayi tace ”iyayena sun mutu sakamakon gobara data tashi a gidanmu yanzu ban san ina zansa kaina ba , wani farinciki ne ya mamaye zuciyar Bash , yace ”barin saukeki a gidana matata tayi tafiya ,to nagode cewar budurwar ,menene sunanki , cewa tayi Rahama ,Bash ne yace ”suna mai dad'i nikam sunanan Bash ,ya shiga da motar ya bud'e suka wuce ciki , kallon gidan tafara wasu abubuwa da bata sani ba tafara gani , sbda batasan fridge ba da wasu kayayyakin , ruwan sanyi ya bud'e fridge ya d'auko mata ,kallon Bash kawai takeyi , batasha ruwan ba ta ajiyeshi gefe ,shikuma bayan yagama ciri kayan jikinshi a gabanta daga shi sai gajeren wando ya wuce toilet, wanka yayi da sabulu mai k'amshi yayi brush ,ya fito d'aure da tawul , parlor ya nufo , ganin baiga bak'uwarsa ba yasashi le lek'a gidan hangota yayi a can gurin hutawa a bishiyar lemu ,waro ido yayi , yace ”to ita kuma menene had'inta da bishiyar lemu ?" bashida mai bashi amsa ya wuce gurin da take ."




Tun a kwana na biyu yasamu ya 6alle k'ofar ya fito , jeji ne da babu gidajen mutane a cikinsa , yanzu ko me za'ayi masa baisan hanyar komawa gida ba ,yana tafe yana d'ingishi , hango bishiyar da tazame masa abinci ya yi wato.bishiyar ayaba irin manyan nan ,kullum itace abincin sa , tafiya yakeyi yana dad'a kutsawa cikin jejin ,har yanzu Allah bai had'ashi da mutum ko d'aya ba gashi bashida komai a gurinshi , yana cikin tafiya yaji an k'wala masa kira , juyowa yai yana nazarin mai muryar jiyakeyi kamar ya santa , dawowa ya dingayi saboda tsakanin gurinda yabari da nisa ."



Wa innan mutanen ne zaune da k'ok'on tsafinsu , babban cikinsu ne yace ” a halin yanzu yaronnan baya gidan su , to ina yayi ?"kuzo mushiga gurin dodo , shiga sukayi da baya suna yiwa dodon nasu kirari zan sha jini ,zan sha jini shine abinda dodon ke cewa "kowanne daga cikinsu ya zaro ido ."



Muryar Basma Harun yaji , cikin mamaki , yace ”wai ke dama... yana nunata da yatsa , murmishi tayi ta ciro wata had'a d'iyar kujera daga mota , wareta tayi ta ajiywa , Harun ko kallon kujerar baiyi ba ya fara jero mata tambayoyi , shin menayi miki ?meyasa kika za6i wahalar dani nida iyayena ? dama kece sanadiyar 6atana na farko ?Allah ya isa tsakanina dake , taku takeyi cike da isa da gadara ,ta iso gabanshi tana juya jikinta dayake matsatsun kaya tasa kuma ko ina na jikinta girgiza yakeyi , Harun ne ya kawar da kansa gefe , yana fad'in astagfirullah cikin zuciyarsa ."



"Harun ka tsaya kaji , wlh banida niyar saceka abinda yasa nayima haka ,inasan ganawa dakai ne ,mahaifina ya matsa min akan nafito da mijin aure to nace masa ,kai nakeso ,shida momyna to shine na rasa mafita amma banida burin cutar dakai " turr Harun yace ”cike da tsana ya dubi Basma yace ”karya kikeyi bakya sona wlh meysa baki bani amsar 6atana na farko ba , Basma ce tace ”na rantse da wanda raina yake hanunsa na rantse da Allah banida sa hannu gurin 6atanka na farko wlh , Harun ya yarda dan yaga hakan a k'wayar idanta ,to ki maidani gida inba hakaba wlh zanja miki d'aurin rai da rai , dariya Basma tayi cikin takaici tace ”ko kajamin inhar a kan soyayyarka ne babu damuwa tunda iyayena sunki daukar mataki , bud'e Jakarta tayi ta d'auko masa wayoyinsa da kud'insa ,kar6a yayi yace ”to maidani gida , motar ta bud'e masa suka d'auki hanya , sunyi tafiya mai nisa sanan suka iso cikin gari."



Yau alk'awarin Bash da Asma'u zai kammalu , fitowa tayi da k'aton hijab ,shigewa motar tayi tafara tambayarsa ya maganar auran namu ,gimtse hararar da yake shirin watsa mata saboda yasan wanan shine last na zancensu ,ciro bandir bandir d'in y'an dubu dubu yayi guda biyar , yace ”wanan dubu d'ari biyar ne , inhar kika yarda da auran Harun to wanan kud'in sunzamo mallakinki , kuma bayan hakan kar iyayenki suyi komai na d'aki nizanyi miki ya cire wata rantsatsiyar waya ya mik'a mata tare da sabon layi yace ”duk nakine , Asma'u ce tafara hango wasu taurari masu haske ,shikenan tayi kud'i wow tazo duniya a sa'a , murmishi Bash yayi yace ”kuma duk wata zandiga yimiki transfer na 20k juya kud'in takeyi tana k'ara jujuyasu , sunyi yawa ne ?"cewar Bash zaro ido Asma'u tayi tana yimasa wani irin kallo...✍️.



Vote me on wattpad

♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_


*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020


Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk


Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2


*🌹🤙MASU FARAN TA MIN WANAN PAGE D'IN NAKUNE NABAKU SHI HALAK KUYI YADDA KUKESO SHARHINKU YANA SANI JIN SOYAYYARKU 😘*


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


EPISODE 25 & 26


_____Asma'u ce ta kar6i kud'in tare da shek'ewa da dariya tace ” Bash d'an duniya , bai kalleta ba yace ”Asma'u abokiyar aiki , sukasa dariya , tsayar da dariyar Bash yayi kana ya cewa Asma'u yanzu zakizamo matar Harun kenan ko hhh ai babu matsala ,tanayi tana fifita da kud'in hanunta , ficewa tayi a motar shima ya wuce , tunda ta shiga gida Umma taga yanayin fuskarta cikin farinciki Umma tace ”meyafaru , Asma'u ce tace ”wai Abban Harun zai zo juwa jibi akan maganar , auranmu , tsaki Umma taja tace ”kun gama iskancewar ku keda Harun d'in to uban mezakuyi a gidan auran ?"6ata rai tayi tana sosa kai , mik'owa Umma dubu d'ari tayi ragowar harta je ta turasu cikin kaya , kar6a Umma tayi fuskarta babu wal wala ta fice , tsalle Asma'u ta doka tana wak'a ,juyowa tayi taga jin jirinta na kuka , hawaye ne ya zubo mata tace ”yanzu da wanan yaron zani gidan Harun d'in ?gashi ba nashi bane , share hawayen tayi tafara bashi nono."



Bash ne zaune a gefen dadynsa , dady ne yace ”my son kamar kanada abin cewa , sunkuyar da kansa yayi kamar mutumin kirki yace ”dady dama yarinyar da Harun yayiwa ciki ne ,iyayenta sukeson sa ranar auransu , dady ne ya gyara zama yace ”to su basusanni bane da saikai zasu fad'awa , a'a ba haka bane dady malm d'inne yace ”wai in gaya maka cewar Bash , to babu komai naji ance kakansa yadawo ma, yanzu zani gidan in bashi labarin abinda jikinshi ya aikata , Bash bai ce komai ba yasandai yanzu asirinsa bazai tonu ba , ficewa yayi daga d'akin dady ya koma d'akinshi ya kwanta cikinshi fal farinciki ranshi fess ."


Dady ne yai wanka a toilet d'in d'akinsa ya shafa mai ya sanya kaya ya nufi bedroom d'in momy , samunta yayi tana tsefe kanta , zama yayi kusada ita , ya kamo hanunta tare da cewa , zan fita yanzu zan dawo , momy ce ta kwanta a cinyar dady ta marai raice fauska kamar yarinya , tace ”uhm ina zaka , dady na bala'in san shago6a dan haka yake k'ara son momy , amma in bala'inshi ya tashi baya da mutunci har ita ma bai k'yaleba."


A dai _ dai saitin makaranta ta ajiyeshi , k'in fitowa Harun yayi yace ”wallahi sai kin kaini har gidan iyaye na , dama abinda Basma take sonji kenan ta juya mota ya fad'a mata anguwar suka d'auki hanya , da isarsu tayi Horn mai gadi ya bud'e suka Shiga, Harun ya rigata fitowa itama ta bud'e ta fito , mai gadi ne da drivern su suketa gaida Harun ,amsawa yayi da fara'arsa , yana gaba Basma na baya , da shigarsu parlor sukaji muryar Alhaji na cewa tunda ya zamo d'an iska ai shikenan tunda ta haihu ai babu abinda ya rage gara ya aureta kawai zai gane kuransa , Harun ne yaja ya tsaya dan ya fuskanci dady yazo gidan , tunowa yayi da sharin dasu ,Bash sukayi masa akan yayiwa wata ciki , hawaye masu zafi suka kwaranyo masa daga idanunsa , durk'usawa yayi ya d'aga hanunsa sama cikin murya mai alamun kuka , Basma na gefensa tana tsaye bata gane menene yake faruwa ba , sai dai a yanayin da taga Harun tasan ko maganar tanada alak'a dashi ne oho ."


Harun ne ya d'aga murya sama yana kuka yace ”Allah ka jarabceni da jarabawa iri iri Allah yanzu kuma ka jabceni da wata nadawo daga wata , Allah kaduba maraya Allah ya ceto rayuwata Allah kayi gagfawar baiyana gaskiya Allah narok'eka Allah kasa wanan shine k'arshe wahala ta , ya shafa adu'ar yana kuka mai cin rai , Basma itama kukan takeyi tanata share hawaye , mom da tun d'azu taga shigowar Harun tasa hanunta ta d'agoshi tana kuka tace ”nasan bakai kayi ba ,ba'a shedar d'an yau amma ni wlhi zan shedeka ,nasani ba tun yauba dadynku ba sonka yakeyiba burinshi yaga rayuwarka ta salwanta tunda yasamu ya salwantar da rayuwar mahaifinka , to wlhi wanan karon bazan lamunta ba sam."


Dady da yajiyo surutun mom ya fito yace ”wato kina nufin ni zanyiwa Haruna k'arya kenan ko ? har da yaushe kika haifi d'an da nanunawa tsana kiji tsoron Allah , momy tana kuka tace ”walhi tsakanina daku kaida yaronka da matarka Allah ya.....wani kid'ima mmen mari aka wanketa dashi , jiri na d'ibarta tana shirin fad'uwa Basma ta d'agota tare da shiga da ita ciki , batasan d'akin da zatasa mom ba yasa ta kaita wani parlor da babu komai cikinsa sai lallausan kafet ."


Wasu surutai mom tashiga yi hankalin Basma ya tashi sosai , kasancewar , tasan adu'oi da yawa kuma saukar alqur'anin ta biyu ,tafara yiwa mom adu'oi tana tofa mata tana yimata kabbara a kunnenta , atishwa mom tayi tare da rik'o Hanun Basma tana kuka , jijigata Basma tayi itama hawaye na zuba a fuskarta , Harun ne ya shigo fuskarsa jik'e sharab da hawaye ya durk'usa a gaban mom yana k'ara yimata wasu adu'ion ."



Alhaji da dady suka dawo parlor suka zauna , zuciyar Alhaji sam babu dad'i yana huci yana bawa dady hak'uri, cikin salon yaudara dady yace ”ka haifi d'an ne baka

Please Login or Register in order to submit comment