Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bashi akan yayi hak'uri , malm ko saurararta beyi ba yacigaba , zaki fad'amin gaskiya ko bazaki fad'a ba ?" Beauty ce tace ” kabarni zan yima bayani , malm bai gamsu zata fad'a ba ya watsa mata wani ruwa ,ihu tafara tana ya k'yaleta , tambayarta ya kumayi a karo na biyu ,me bayin Allahn nan sukayi miki kike cutar dasu ?".

Yau ta kama daurin auran Sumaiya , manyan mutane da dama sun halarci bikin , kowa kagani fuskarsa cike take da farinciki , Abbi ma farincinne shimfid'e a fuskar sa , haka Ammi sai albarka suke sanya mata ,gidan ango duk da dai tuwona miyata ne ,sunyi rawar gani sosai akwatuna set goma sha biyu , kuma shak'e da kaya , masha Allah amarya tayi goshi, hango Sumaiya nayi tasha bak'in lalle fuskar nan tasha make-up ga wani tsararen kitso da aka yimata , gaskiya ta had'u abinka da farare abin ba'a cewa komai , wayarta ce tafara ring ,sunan my sweetheart ne ke yawo a screen d'in wayar ,cikin sassanyar murya ta d'aga , kunsan marubuciyar taku da son jin k'wa k'waf hhh , ango ne yace ”my honey dafatan dai baki wahalar min da kanki ba , kukan shagwa6a tayi kamar yana ganinta tace ” sweetheart , bana jin cin komai yanzu ,oh my honey kinason wahalar min da kanki , wata irin dariya tayi da nima na dara hhh my fans dariyar fa ta masoya ce."

Ki fito please muje kici abinci , uhm uhm nikam bazan iya ciba ,okay to bari in aiko Shamsu ya kawo miki ,cewar Khalid salama sukayi kowa ya ajiye waya, k'awayen ta ne keta yimata tsiya wai tafiya shagwa6a Khalid zaiyi , fama ,lol niko nace ai mace babu shagwa6a to ai babu kanta 🙈 kuka tasa tana shure shure , tin tsirewa da dariya suka tafa."...✍️.

👏👏👏👏👏👏👏👏

*GASKIYA MASOYANA*

ina alfahari daku da kuma soyayyar da kuke nunamin wlh ina gani kuyi hakuri yanzu aiyuka ne sukayimin yawa , ina neman Adu'arku please kuyimin adu'a Allah ya rabani da abinda nake tare dashi lpy , kuna rai na, nagode da nuna soyayyar.

Please share👏
Vote me on wattpad

♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_


*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020


Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk


Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


EPISODE 39 & 40


____ Mama da Anty na hango a hospital , suna fitowa daga d'akin da aka kwantar da Bahija , kuka Anty takeyi sosai , juya kai mama tayi tana adu'a a hankali doctors ne suka shigo cikin rashin walwala suka rufe gawar Bahija , kulli nafsin za'ikatul maut Allah ka kar6i tubanmu , Allah yayiwa Bahija rasuwa , da dawowarta daga India , ba k'aramin aikin alkhairi tadinga yiba , itace sadaka dakuma ibada , Allah kaji k'an musulmai Allah ka gafartawa wanda suka rigamu gidan gaskiya ."

Babbar k'awarta ce wacce sukayi primary tare , idanunta a bud'e suke dan haka kowa ke tsoron ta ra6i yaronsa, Umma tayi iya yinta amma abin ya fi k'arfinta , kasancewar yanzu Asma'u tanason fin k'arfin Umma , kusan kullum Umma sai tayi kuka gashi malam ya kwanta ciwo na bak'in cikin Asma'u , Umma takoma abin tausayi ."

K'awar tata mai suna Zubby , duban Asma'u tayi tace ”my sis mai yasa kika bari kika d'auki ciki ,gaskiya bakida wayo sekace bakiyi karatun boko ba , shiru Asma'u tayi tace ”ke nifa ban ma san na sami ciki ba , kawai gani nayi ina amai, Asma'u ce tabawa zubby labarin , abinda ya faru tsakaninta da Bash har lamarin auransu da Harun da za'ayi nanda kwana biyar , Zubby ce ta bugi cinyar , Asma'u tace ”kee!!, kud'in banza , kud'in hofi , ke baki iya bariki bane ?"yanzu fa ragamar komai a hannunki take , dan haka ki janye maganar aure kizo mu fasa bariki , ita kuma , Basma da kikace , Harun zai aura , to inada mafita wlh ,mu watsa musu bala'i kuma mubari sai sunyi auran sanan , zaki godemin k'awata , Asma'u ce ta dubi jaririn hanunta tace ”to wanan yaron ya zanyi dashi , Zubby ce ta karkace ,d'aurin d'an kwali tace ”tambaya ma kikeyi ?"to tsaya tambaya wlh garama ki bud'e idonki , ita wanan tsohuwar aikin me rakeyi ki jefa mata shi kizo muyi tafiyarmu , Asma'u kallon Zubby takeyi , a can k'asan zuciyarta tana tunanin , inhar ta tafi to mahaifinta fa gashi babu lpy baima san waye a kanshi ba ."

Maganar Zubby ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da take , maiyasa zaki tsaya watsar da damar da Allah ya baki , just ki share tausayi da wani abu , kizo mu fasa , zan baki kud'in siyan atamfofi da lass da duk wani kaya na yayi , kingafa harkar nan , wlh bazaki dingayi da k'ananan mutane ba , zaki waye kiyi fresh hmm ,sai kin shigo zaki gane manufata beb , hud'ubar Zubby tasami gurin zama a zuciyar Asma'u , sun shirya nanda kwana biyu zata bar gida , Zubby ko tanata k'ara jaddada mata abubuwa na more rayuwa dakuma wanda zata k'ara fasowa gari. "

Sallama sukayi , Zubby tazo fita sukayi kaci6us da Umma , Allah yasa yanzu ta dawo daga anguwa , har k'asa Zubby ta durk'usa ta gaida Umma , cikin sakin fuska Umma ta amsa ,ta fice , Umma ce ta shige d'akin Asma'u , tafara zuba mata masifa , tace ”wlh Allah ki kiyayeni ke bakida hankali ne , wanan shed'aniyar yarinyar kika k'ulla k'awance da ita , to kifita harkar ta kokuwa ranki ya 6aci dan wlh zakisha mamaki tunda bakida hankali , kukan k'arya da munafurci Asma'u tafara , tace ”umma ba k'awata bace fad'a ma mukayi da ita yanzu , Umma ki yarda dani insha Allah nakoma Asma'un da kika sani a da wlh na tuba Umma."

.
Allah sarki rayuwa , Umma ta rungume Asma'u tana kuka , tace ”nayi farincikin shiryuwarki , Allah yakuma shirya mana ku , amen Asma'u tace tare da nufar d'akin Umma tafara gyra gado ta gyara ko ina ta share ,ta koma kitchen ta share ta dawo tsakar gidan shima ta share tazo kan bayangida shima ta wanke ta share , Umma zuciyarta fal farinciki sosai takejin son y'ar tata ."
Ruwan sanwar abinci Asma'u ta d'ora ta kar6i kayan cefanen hanun Umma ta fara gyarawa tuwon shinkafa za'ayi miyar taushe , cewa Umma tayi ta juye ruwa tayi wanka ita zatayi sauran , cikin farinciki Umma ta juye ruwan wanka ita kuma Asma'u na wanke tumatur zata kai markad'e ."


Yau Alhaji ya dawo daga saudiya murna gurinsu Mom da Hajiya ba'a magana , bayan an d'aukoshi daga airport , yaci abinci yayi wanka yake gaya musu cewar , ya siyawa , Harun gida a rijiyar zaki , mom da Hajiya babu zama suka d'unguma zuwa tsararen gidan , tunda suka hango get d'in gidan sukasan ba k'aramin kud'i ,Alhaji ya kashe ba , bud'e gidan sukayi da key ,suka shige cikin gidan , mom da Hajiya da driver kowa sai santin yanayin tsarin gidan yakeyi , da shigarsu , sukaci karo da shuke shuke na flawoyi masu kyau , daga 6angaren dama kuma bishiyoyi ne na kayan itatuwa , irin na turawa , shigewa cikin gidan sukayi , komai akwai a ciki , kama daga kafet na parlor , dakuma labule , da labulen window ga abin kama labule mai flawoyi , hango kujerun da suke zagaye a k'aton parlorn nayi , gaskiya fad'ar kyawunsu bazai fad'uba , ga kafet mai kwaliya daya malale tsakiyar parlorn , daga yamma kuma , TV ne plasma k'ato a manne jikin bango k'asanshi resrver ce da CD ga remote a kansu , mai karatu ,in natsaya lisafo kayan parlor zamu cinye lokacin anan , daga tsakiyar parlorn bene ne shimafa ya tsaru , gida ya tsaru ,mom seda tayi kukan farinciki."



Hajiya ma tayi farinciki sosai , shiga kowane part sukayi na parlorn , k'asa d'akuna hud'u ne ,da bedroom biyu da kitchen da store dakuma d'akin bak'i , hakama sama shima hud'unne , gida ya birge sosai ,an kashe nera ."


Gidansu Basma shiri sukeyi babu kama hanun yaro , mutane cike a gidan kamar ,ranar ne d'aurin aure , daga masuyin cin cin sai masu suyar nama da masuyi donut da sauransu kuma kowanne ba kad'an akeyi ba , amarya tabar gidansu takoma gidan yayar mahaifiyarta da zama , yau kwananta hud'u a can ."

Harun ne zaune shida abokanan sa kowa sai tsokanarsa yakeyi , da kamar ba shine y'ammata suke rubibi ba, yanzu gashi , Basma ta cafke gasar dariya yasa yace ”nifa banida ra'ayi a soyayya , hasali ma bansan abinda masoya suke jiba ,wlh sai yanzu dana had'u da sarauniyar mata uwar y'a y'a na , abokinshi dake gefenshi a zaune yace ”eyee kace ka waye sosai , wanan small mouth d'inne ke furta wanan kalmomi nice , na jinjina maka shugaban masoya , sukasa dariya , hirarsu sukeyi ,mai cike da barkwanci dakuma nishad'i."


Gidansu Bahija yau akayi sadakar uku , dole dadynsu ya dawo gida dan mutuwar ta girgiza mutane da dama haka shima , saida ya zubar da k'wallah yaji rasuwar Bahija , sauran k'annenta da yayunta da basuyi aure ba ,jikinsu yayi zanyi musaman da sukaga anzo tafiya da Bahija makwancinta , Allah sarki rayuwa mudinga kwatanta aikin alkairi 👏...✍️.



Masu sharhi ina ganinku karku gaji da sambad'omin sharhi nikuma bazan gaji da nishad'antar daku ba I love you my fans ana tare 🤙.

♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_


*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020


Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk


Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


EPISODE 41 & 42


_____Washe gari Asma'u ta tashi da asbha , bayan tayi sallah taje d'akin Umma ta gaisheta , sanya mata albarka Umma tayi tare da yimata fatan gamawa da duniya lafiya , mik'ewa Asma'u tayi taje d'akin mahaifinta ta gaishe shi , Alhmdulilh jikin nashi da sauk'i , dan yanzu ma yana magana ."

Washe gari , wayar Asma'u ce take ring misalin sha biyu na rana , Zuby ce , ke wai ya akayi ne najiki shiru ,ko kin canja shawara ne ?"cikin k'asa da murya Asma'u tace ”no yanzu dai mubar maganar zuwa , gobe , ta ajiye wayar , tunani tafara iri iri amma babu wacce ta gamsu da shawararta irin Zuby."

Bayan su mom da Hajiya sun dawo gida ,ta zauna a parlor , tana santin gidan Harun amma taji dad'i sosai , shigowar Alhaji ne yasata tsugunawa ta gaishe shi , zama yayi a kujera two sitter kana ya dubi mom yace ”ya kukaga gidan ?"fad'ad'a fara'arta mom tayi tace ”wlh Alhaji gidan kamar a turai , dariya Alhaji yasa yace ”masha Allah komai dai yayi ko?"eh yayi Allah ya k'ara bud'i , amen y Allah Alhaji yace ”kinga bikin yau saura 2 days ,mom ce ta sunkuyar da kai tace ” Allah yasa munada rai da lafiya ."

Misalin k'arfe biyar na yamma angon Sumaiya ya rangad'o mata kira , d'agawa tayi cikin sanyin murya tace ”barka da yamma , ywwa yace ”kungama shiryawa ne ?"eh Sumaiya tace ”ku suke jira , waro ido yayi yace ”suwa kenan ?"k'awaye na man , to kekuma fa ?"Sumaiya ce tace ”ni bazan zo ba , a zabure yace ”bar maganar wasa ,Sumaiya ce tace ”da gaske , juyawa tayi taga kowa na shiri , itako kwanciya tayi tare da jan mayafi ."

Sunyi tashin harsun gaji bacci mai nauyi ne yayi awon gaba da ita , k'awayen suka shige mota suka barta , ana cikin gabatar da mutane , kowa yaga gurin zaman amarya da ango wayam babu kowa , mc ne ya tsaya da magana yafara tambayar abokanan sa ko menene dalilin rashin zuwansu ?"suma basu sani ba dan lokacin da zasu taho angon yace ”musu zashi d'auko amaryarsa , mc ne ya d'aga abin magana yace ”to kowa yayi hak'uri iyayen gayya basu iso ba kuyimana afuwa mu jirasu ."

A gidan su , Sumaiya ango Imran ne ya shigo a sukwane dan bayason kowa ya ganshi ,direct d'akin Sumaiyan ya nufa da babu kowa a cikinsa , samunta yayi tana bacci , hankalin ta kwance ,rasa inda zai ya tasheta yayi , gashi yanayi yana duba lokaci , zama yayi gefen gadon yafara hura mata iskar bakinsa a fuskarta , wani juyi tayi ,da alamu baccin ma yanzu yafara dad'i , Imran ne , ya d'agata tare da ruk'o mata hannu , kaya yagani a kan gadon da alamu natane, kunyace ta kama sumaiya tak'i had'a ido dashi sai shigewa toilet tayi , a gurguje ta watsa ruwa ta sanya kayan a toilet , duk yana zaune yana jiran fitowarta , shagwa6e fuska tayi tace ”to ina sukayi , suntafi man , cewar Imran , rau rau tayi da idanu kamar zatayi kuka ,tunaninta shine yaya zatayi kwaliya banda mai da powder da man baki babu abinda ta iya sawa , gani tayi Imran ya rik'o mata hannu ya zaunar da ita a stool d'in dake gaban dressing mirror ."

Itadai batace komai ba kallonsa kawai takeyi , mai ya shafa mata , a k'afa da hannnu dakuma fuska , kasancewar sauri yakeyi , powder ,ya shafa mata tare da yimata jagira da janya mata purple d'in janbaki ya zagaye gefen bakin da kalar maroon , wow nimafa naga wankan kyau hatta d'ankwalin shiya d'aura mata ya d'auketa suka fita ta k'ofar baya hand bag d'inta da gylenta da d'ankune da sark'a dakuma warwaro da sauransu duk a mota aka saka , ango dai ya iya kwaliya lol amafa an 6atawa y'an taro lokaci ."
Ba' a d'auki lokaci mai tsayi ba suka iso katafaren hall d'in da yacika da masoya , da shigowar su aka fara tafi masu video nayi masu camera nayi masu wayoyi nayi , samun guri sukayi hanunsu sak'ale a na juna, adu'oi akayi tare da sake zazzafan kid'a mai gigita masoya , kowafa ya tashi ya taka ango da amarya ma ansha rawa , umartar su akayi da yanka cake , hanunta tafara sawa shima ya d'ora nashi suka yanka jikakeyi raf raf anata tafi , suna gamawa aka sanya musu wak'ar bikinsu , an zubar da nera kurin manni kuma kowa yayi farinciki , sai misalin k'arfe bakwai aka tashi, kutt. sai anje gida ayita ramakon sallah ,nidai ina gefe yasin ."

Kai tsaye gidanta aka wuce da ita , wani katafaren gidane mai cike da kayan more rayuwa , tsayawa misata kyawunsa ma babban aiki ne , saboda gidan ya tsaru iya tsaruwa , amma ba gidan sama bane , bedroom d'inta aka wuce da ita , color d'in sa kuwa wait and purple ne , komai ya tsaru , angawaye kam tuna suka kawo amarya suka fice , bayan iyaye da k'awaye da amarya sunyi saloli ne aka fara yiwa , Sumaiya nasiha tare da koyar da ita laduban zaman aure , kuka tafara , kowa na gurin yana kallonta k'awaye na shirin dariya iyaye na tausaya mata , wata k'anwar mahaifiyarta ce ta rik'o mata hannu suka fice., d'akin dake jikin na amaryar suka shiga , shimadai kala d'aya ne komai akwai a cikinsa , zaunar da Sumaiya tayi ,tace ”daughter , yakama kisani nasanma an fad'a miki amma zan kuma jaddada miki, aure ya wuce tunaninki kuma ya wuce zatonki , aure ba abin wasa bane ,shi miji da kika ganshi to yanzu karatunki zai d'auka haka kema karatunshi zaki d'auka."

Kizamo mai yiwa mijinki biyayya, karkice zaki diga yimasa rowar hak'k'insa , saboda Allah yace kibi mijinki ,karkiso 6acin ransa kiyi masa biyayya banda yimasa gardama , kiso abinda yakeso , kuma babban abinda yake , taka muhimiyar rawa shine k'amshi , ki kasance mai son k'mshi mai sanyi , ki guji k'azanta , 6angaren gyran jiki shima nazo miki da kayan gyaran jiki ba kizauna bakya gyara jikinki ba kuma yana k'arewa kiyimin magana , inaso kisani maganin wayo kunyar fad'e nakeyi riders kun bazo ido da kunne to yasin ku gane nikam inada kunya wayo 🤏😎...

Karkiyi wasa da cin aya da dabino da rake da kankana da gwanda da cucumber da karas , da farfesu musaman ma na kifi ko farfesun kaza wlh babu ruwanki da cacar kud'i gurin siyan kayan k'arin ni'ima ,lol nimafa nad'au darasi yasin 💃 , jikin Asma'u ne yayi sanyi , kuma karki dinga bari kayanki suna datti yakamata , ki kula da ado da kwaliya saboda namiji d'an ado ne, batun shagwa6a kuma karkizamo kina yimasa murya kamar ta maza ,kidinga tausasa kalamanki kafin ki fad'esu , janyo hanunta anty tayi suka koma bedroom d'inta, anty ce ta shiga toilet ta had'a mata ruwan wanka wanda yaji turaruka masu k'amshi kuma masu zama a jiki , cire kaya Asma'u tayi tashige toilet tafara wanka , ga wani ruwan shima mai k'amshi an tarashi a bahon wanka , tana gama wankan tashige tayi luf a ciki , kamar mai shirin yin bacci ..✍️.




Please share👏
Vote me on wattpad

♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_


*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020


Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk


Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


EPISODE 43 & 44


____ Malm yasha artabu da beauty ,tun asbha ake abu d'aya har azhar , beauty tace ”zata fasa k'wai , anyi nasarar samun dady da Bash sun dawo normal , saidai beauty tace kota tafi bazata k'yale Bash da dady ba , sundai yi farinciki , da haka ta fice daga gidan ,domin ayar Allah bata fad'i k'asa banza , ammafa hankalin dady a tashe yake ,da magan ganun da beauty take cewa ,Bash ya rame sosai kamar wanda yayi sati yana ciwo."

Su Anty ne suka mik'e dan lokacin k'arfe tara ne na dare , bayan sun gama yiwa asma'u kwaliya da wata nasihar , suka yimata fatan zaman lafiya , haka tadinga kuka kamar wace za'a zare ranta."

Ana gobe biki , da misalin k'arfe hud'u na asbha , asma'u na hango da akwati a hannu tasa dogon hijab , ficewa tayi cikin hikima da dabara , da fitarta ta shige wata mota da tatsaya a k'ofar gidansu , tana shiga motar tayi gaba ,Zuby ce a cikin motar ,tasha bak'in glass ,wanda ya rufe har saman kumatunta , duban Asma'u tayi cikin farinciki tace ”barka da fara shigowa sabuwar rayuwa , hak'ik'a na tayaki murna yanzu kinzamo mai y'ancin kanki bakida matsala please ki saki jikinki man , Asma'u batace komai ba sai tunanin da ya addabi zuciyarta , shin tayi adlci kuwa ?"tayiwa mahaifiyarta da mahaifinta adlci ?"ga jinjirin yaro data bari yana bacci , to inya taso wace irin rayuwa zaiyi , can kuma wata zuciyar tace ”ke ga daula zaki shiga ,yanzu kinzamo free babu mai takura miki karki bari tausayinki ya rinjayi dukiyar da zaki samu so ki manta da iyayenki...

Murmishi tayi cikin samun k'warin guwaiwa ,ta goge guntun hawayenta , sunyi tafiya mai nisa , nisa sosai dan harsun fita a garin kano sun nufi Kaduna , suna tafiya suna hira , abinci mai rai da lafiya Zuby ta mik'o mata tare da abin sha ."

Wayar Zuby ce ta fara ruri , d'agawa tayi tare da cewa my man ya akayi ne nakusa zuwa fa ,kasan a kano na kwana ,ta kashe wayar , Asma'u dai na gefe bata magana ."

*GIDAN SU AMARYA BASMA*

Yau akeyin walima y'an uwa da abokan arzik'i sun taru anata fad'akarwa , an raraba kyautu tuka sosai , kuma anyi taro lafiya , daganan aka kowa ya watse , washe gari ,aka saka amarya a lalle , kowa sai sambarka , washe gari Assabar d'aurin aure ,gidan su mom da Hajiya da Alhaji wanan rana suna cikin farinciki , Alhaji da dady da abokan Alhaji suka cika gurin masha Allah , an d'aura auran Basma da Harun akan sadaki mafi albarka , dubu d'ari , d'aurin auran yasami halartar manyan bak'i ta 6angarori da dama ,anci kuma ansha an godewa Allah ,ango na hango yana sanye cikin wata shadda gezna mai azabar kyau ga gashinan yasha gyara bakinan kamar ansa masa janbaki , ni a ganina ma sai naga kamar yayi haske , zaune yake a gidansu Mom d'inshi sunata yimasa nasiha dakuma sanin hakkin aure a musulunci , Alhaji ne ya kirashi lokacin yana shirin tafiya gidansu Asma'u , kasancewar ya kira ance masa an fasa suzo su kar6i kud'in su , Harun ne yashiga da sallama , samun Alhaji yayi a zaune yana waya, yana gamawa yace ”Harun ya fito da mota zasuje wani guri , cikin bin umarni ya fito da mota suka shige shida Alhaji sukabar gidan , wani katafaren company na Alhaji suka nufa , wanda ake sauke kayan sa na saudiya , turaruka da jallabiya da sauransu , katafaren shago ne mai girma ga tsari ,da shigarsu kowa yahau durk'usawa yana gaida Alhaji da Harun , Alhaji ne ya amsa tare da cewa ga sabon shugaba na kawo shine zai dinga kula da komai na shigar kud'i , kai kuma Bala kazo muje sabon company na zaka koma can da aiki."


Cikin zumud'i da godiya , Bala yabi su Harun ,shimadai sabon company d'in ya tsaru sosai , bayan sun koma gida ne Alhaji ya cewa Harun yanzu kabar aiki a waccan ma'ikatar zaka dawo tawa , kuma maganar auranka da ,wanan yarinyar iyayenta sunce basusan inda ta nufa ba , shikuma yaro nanda wata biyu inya kuma wayau Allah zai baiyana kamanninsa da ubansa , cikin farinciki Harun ya kalli Alhaji yana godiya , lokacin k'arfe biyar na yamma dayake ranar Asabar akayi d'aurin auran ,

Wayarshi ce tafara ruri , ganin number abokinsa yasashi fitowa , jinayi yace ”ganinan zuwa yanzu , ya kashe wayar , parking spice ya d'auki motarshi ya fice daga gidan , gurin abokan nashi ya nufa , hak'ik'a ,sunyi rawar gani kud'ad'e masu yawa suka had'awa Harun , shima yayi farinciki kuma yak'ara sonsu a zuciyarshi."

Kukan jariri ne ya karad'e gidan , Umma na idar da sallah ta nufo d'akin Asma'u , ganin babu kowa sai yaro da wata k'atuwar takarda yasata dogon tunani , kodai Asma'u ta shiga band'aki ne ?"to ina ma zataje da sanyin safiyar nnan?" tunani iri iri Umma tafara , goya yaron tayi ta lek'a bayi babu Asma'u ko ina ta lek'e batanan , d'aukar takardar mai cike da rubutu tayi , bata iya karatun boko ba ko hausa yasata nannad'e takardar ta kaita d'akinta ta 6oye , tunaninta shine ina Asma'u tayi ?"batada mai bata amsa yasa ta fito ta koma d'akin Asma'u , ganin kud'i turus a zube yasa Umma tsorata tafara ja baya cikin tsoro."

Cikin sanyin jiki

Please Login or Register in order to submit comment