Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kirki, Dan bakin munafurci shine kika bani abinda zai konamin yan hanji?”

Nafisa ta kece da dariya, Na mike ina gyara damarar kan zani na, Ji nake tamkar na karairaya ta tsabar haushi. Bello ya yo kai na yana karkada min hannu,

“Kede gaba d’aya baki da hankali, kidahumar banza. Dan tsabar reni lemon kazamin bakin ki kika zubamin a fuska. Ni sa’an ki ne?”

“Wannan ne lemo? Walle ba dai lemo ba. Kawai dai mugunta akeson hadamun.”

Bello da Nafisa mai zasuyi ba dariya ba. Suka shiga kyakyatawa. Na murtuke fuska ina gatsine baki.

Nafisa ta ri’ko hannu na tana murmushi,

“Be lemon wuta bane kawata. Lemo ne na sha, Sunan sa coke. Tsaya kiga ma na sha.”

Tana gama fada ta dauki kwalbar ta kafa a bakinta Sai da ta shanye tas sannan ta ajiye. Ganin dagske ta shanye hakan yasa na danji sanyi a rai na. Murmushi na mayar mata nima na dashare hakora na,

“Ayyo! Lemon yan gayu ne dai. To ai kuwa dai zanba su Larai labarin lemon nan. Tab.”

Bello yai tsaki kafin ya sakar min rankwashi a kwanyar kai na,

“Mugu azzalumi..”

Na fada ina sosa wajen. Har ya fara tafiya ya juyo yana kallo na,

“Me kika ce?”

“Ca nai adawo Lapia”

Na karasa fada hade da mai zunde, ya fice ba Tare da yace komai ba. Nafisa taja hannu na muka koma cikin parlorn su. Maman su ta zuba mana abinci fal da naman kaji. Abincin juya ban su na yan gayu. Muka hadu da sauran k’awayen Nafisa muka cinye tas . Suma mukajajje gidajen su muka ci muka koshi, Daga nan naja zugar yara k’awaye na muka tafi gidan mu. Muna tafe muna neman magana. Kafata tayi busu busu ba silipas.

“Oganniya ta Gajiyalle me yar hakiya.”

Cewar lantana yar gidan rumasa’u me kitso. Na kece da dariya kafin na buga tsakiyar zani na na ja guda,

“Sai ni Dijangala ta mai gari yar Baffan ta..”

“Gajiyalle ai ba babar ki bace ko? Ita bak’ace bata da kyau.”

Nafisa ta tambaye ni tana cigaba da irga duwatsun hannun ta. Na tab’e baki kafin na bata amsa,

“Yarinya Dagaske ba ita ta haife ni ba. Ni baba ta ta mutu dan kiji tun ina karama. Kuma ita kyakkyawa ce yarinya.”

Haka dai mu kai ta shirmen mu akan hanya har muka Karasa gidan mu. A tsakar gidan mu zugar k’awaye na suka zauna muka shiga yin yar carafke, Na lek’a gefen murhu inda Gajiyalle ke girki, cikin sa’a ta kammala tana karkasa shi.

“A zuba mana da kawaye na.”

Harara ta dankara min ta cigaba da karkasa abincin. Komawa nai cikin yara muka shiga hirar mu. Can Gajiyalle ta callarawa sunana kira. Na mike a sukwane har ina bal da robar ruwan dan akuyan Gajiyalle. Ina zuwa ta mikamin wani kwano cike da abinci yasha nama. Yawuna yatsinke, kunnuwa na sai rawar dadi suke.

“Ungo.”

Wayyo Allah na dadi! Yanzu duk namu ne wannan? Nama nasha nasha akai. Gudun kar nayi katobara Hakan yasa na sake tambayar ta namu ne da kawaye na.

“Na mu duka ne?”

Gajiyalle ta daga kai tana mai cigaba da kasa abincin gaban ta.A sukwane na karasa wajen kawaye na da kwanon. Muka hau ci sai da muka cinye tatas muka gyatse Sannan kowacce tatafi gidan su. Haba tsabar yadda yau naci na koshi kasa tashi nai nabi lafiyar tabarmar da nake zaune na kwanta sai bacci. Cikin daddadan baccin da yai awun gaba da ni na jiyo wani azababban dundu da aka sakarwa gadon baya na tamkar zai burma saboda yadda aka duma masa dundu. A firgice Na mike Ina sosa bayan. Ina bud’a idanu na na hango Gajiyalle da Mudi, Sai huci take,

“Dan guzumar uban ki ina abincin dana mika miki ki bawa Mudi?”

Idanuna suka kawo ruwa . Wane abinci taban na Mudi? Girgiza kai nayi Saboda hakikanin gaskiya kenan ni bani ta bawa abincin Mudi ba,

“Ba ni .”

“Zaki shiru ko sai na lakada miki na jiki. Yanzu dai dan guzumar uban ki ina abincin yake.?”

“Wallahi Gajiyalle bani kika bawa abincin Mudi ba. Iya abinci na da kawaye na kawai kika bani. Nace miki na mu duka ne? Ki Kai shiru alamun Eh. Amman bayan haka baki bani abincin Mudi ba”

“Dan guzumar uban ki. Ca ki kai na Mudika ne? Na daga miki kai. Uban wa zan zubawa abinci haka Idan ba Mudikalle naba?”

Na sake girgixa kai cikin hakikanin gaskia nace,

“Sai da na tambaya nace na mu duka ne? Kika daga kai alamun Eh”

Kukan kura Gajiyalle Tai ta shak’o wuya na tana huci.

“Amma wannan yarinya ko yar bankadaddiya. Abincin Mudikallen zan baki ku cinye keda yuyar kawayen ki? Nace abincin Mudikallen? Zaki magana ko sai na lakada miki na jaki?”

Ruwan ciki na ta hau bugu tana yakushi na. Takaici da zugin da ciki na yake yasa na fara kuka mai kara, Cikin haka ‘Dara’ifa makociyar mu ta shigo da alamun kuka na ne ya kawota. Dakyar ta banbare Gajiyalle daga jiki na,

“Haba Gaji! Haba! Kashe ta zaki yi? Yarinya kamar wannen fisabilillahi ya za’ai ki dinga hayewa ruwan cikin ta kina duka? Tsakani fa da Allah. Shi fa da na kowa ne Gajiyalle, Idan ka kyautata wa dan wani sai a kyautatawa naka kai ma. Marainiya c...”

“Ishiru dakata, dakata min ‘Dara’ifa, kefa dama akwai ki da shisshigi da gutsiri tsoma, Ina ruwan ki? Dan tsabar tsagwaran gulma irin ta ki menene na shiga abinda babu ruwan ki? Shysa akeyi dake a garin nan.. Kinsan meta min ne da zakizo kina min wa’azi?”

Dara’ifa ta girgiza kai cikin takaici tace,

“Koma meta miki Gaji sai ki hak’uri, Amma akan me zaki dinga dukan ta kamar kinsamu katako? ‘Ya mace kamar wannan da zaki kyautata mata bafa kisan inda rana zata fa’di ba. Shi maraya kokarin kyautata masa kake ba kuntata masa ba.”

“Yau za’ai tsallen badake. Abincin Mudikalle na fa mumugunciyar yarinyar nan ta kaiwa kawayenta suka cinye. Tafa tambaye ni nasa ne? Na daga mata kai alamun eh amman yarinyar nan dake ba tsoron Allah a ranta sai tai mirsisi takai musu suka cinye.”

Ina daga kwance na mike dakyar saboda yadda jiki na ke tsamin jibgar da tamin.

“Walle ba haka bane, Kina ji Dara’ifa? Sai dana tambaye ta nace na mu duka ne? Ni da kawaye na nake nufi. Saboda tun farko sai dana ce mata tazuba mana ni da su. Bayan ta kirani ta mikomin abincin na tambayeta fa ta daga kai alamun eh”

Gajiyalle taja tsaki tana bubbuga hannu a katangar gidan mu, Har gefen dake lilo ya zubo a kasa.

“Guzuma. Yarinyar nan ko yar makaryaciya. Aina akai haka? Na mudika ne? Kika tambaye ni? Na daga kai alamun Eh. Dara’ifa ki ky’ale ni na kacaccala yarinyar nan”

‘Dara’ifa ta shiga tsakanin mu tana janye Gajiyalle tana bata hak’uri,

“Toh Kiyi hak’uri akasi aka samu. Ke dije ita Gajiyalle na nufin abincin Mudi. (Na Mudika) ke kuma Gajiyalle, Dije na tambayar ki ne (Na mu duka?) ma’ana nasu itafa kawayen ta? To adai Yi hak’uri . Abinci dai anci sai kasayarwar sa. Bazai dawo ba, Duka bashi bane. Ke kuma dije Idan kinyi laifi Ki zama mai bada hak’uri kinji”

Daga kai nayi alamun Toh, haka Dara’ifa tagama maganar ta ta tafi. Tana fita Gajiyalle ta hau rankwashi na ji kake ‘qwas’ gwaf’ Kif’ duk a kwanyar kai na. Da alamun Dara’ifa ta jiyo. Ai kuwa ta sake yo sallama ta kirawo ni wai zan kai mata nik’a. Arcewa nai a guje har yin karo da dan akuyar Mudi. Rike hannu na Dara’ifa tayi muka shiga gidan ta, Koina yasha siminti abun sha’awa wallahi kamar na lashe shi. Zama nayi a gefen kitchen kofar dakin ta Ita kuma ta shiga ciki,

“Dara’ifa ina ku’din aiken?”

“Ki hutawar ki Dije babu abunda zaki siyo min, Kawai kiran ki dai nayi naga yadda take nadar ki.”

Dashe baki nayi kawai na cigaba da shasshafa simintin dake malale a k’ofar dakin. Dara’ifa nada kirki, Ita ba tsohuwa bace irin Gajiyalle, Amarya ce amma bata taba haihuwa ba. Daga kauyen alfindi mijinta ya aurota, Shine dan karkarar mu. Sam batada gulma ko biyewa mata n auren karkarar mu dake yawon gidajen juna suna gulma, Ita kullum tana gida tana harkokin gabanta bata shiga lamuran su. Shiyasa suka tsane ta, Kullum cikin yi da ita suke, Wai tacika girman kai, Takance ba girman kai bane gudun zucia ne.

Ina nan zaune har aka kira sallah, Dara’ifa ta fito tayi alwala tayi sallar ta, Inata bin yadda take Sallah gwanin sha’awa. Ta mike ta cire hijabin jikin ta,

“Dije ta shi kiyi alwala kiyi sallah.”

Baki na na bude kafin na rufe shi Ina mai jinjina kai na,

“Ban iya ba. Daga alwalar har sallar.”

“Wai har yanzu bakya sallah dije? Shin ba’a saki a Islamiyya bane ko allo?”

Na daga kai hade da kafad’a ko ajiki na.

“Tashi kiyi alwala mu gani.”

Mikewa nai dakyar na kamfanci ruwa a buta tamkar yadda naga Baffa yana yi wani lokacin. Na wanke hannu na da k’afa sau dai dai sannan na kuskure baki na na zuba ruwa a gashi na, Na gantsare na mike zan bar wajen Dara’ifa ta hanani,

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Koma ki zauna, Haka ake alwalar? Shikenan har kin kammala? Oh ni Dara’ifa!”

“Shin dije, Gaji bata koya miki? Anya kin iya karatun sallah ma kuwa?”

Na tabe baki kafin nace

“Itama fa battai, Yasin seta kwan nawa batai ba. Yo alhaki akanta tunda bata koyan.”

Dara’ifa ta girgiza kai kawai, Ta sake debo ishasshen ruwa a buta ta mikamin, Na karba na koma na zauna. Ahankali take koyamin tana min bayani tamkar malama da daliba, Ba lefi na fara ganewa gaskiya. Daga nan tace nayi sallah, Nan ma ban iya ba, Na dudduka kawai na mike na jefar da hijabin data bani a gefe, Nan ma sai data sake koyamin yadda zan dinga yi. Na gane wani abun, Wani kuma ban gane ba. Mudi ne ya leko yace gaji tace naje, Na mike dakyar banso zan koma gida ba har ga Allah. Saboda sam Dara’ifa bata da fada ko hantara irin na Gaji. Har na Kai kofa zan fita ta yafito ni da hannu na koma. Wazobiya ta mikomin hade da radamin a kunne,

“Ki sai sabulun wanka kinji? Sai da safe nagode.”

“Nima nagode Dara’ifa. Allah dai ya biya ki da alkhairi.”

Sallama mu kaiwa juna na tafi gidan mu zuciya ta sam ba dadi. Ji nake dama Dara’ifa ce babata dana more. Take ummata ta fadomin arai na. Uwa mai dadi, Da ace tana raye nasan bazan taba tagayyara kmar haka ba. Wasu zafafan hawaye ne suka zubomin, Cikin sarkakiyar murya nace,

“Allah ka jik’an Umma tah..!”

Tun daga zauren gidan mu nake jiyo sautin suratan Innarajo mahaifiyar Balki K’awata itada Gajiyalle. Sam innarajo bata sona batasan kawancen da muke da Balki ‘yarta. Shiyasa nima na dena shiga harkar Balkin. Wai ashe barar (kudin aure) Balkin aka kawo. Mamman mai shayi ne zai aure ta. Gajiyalle sai guda take tana yada magana.

“Ai wallahi innarajo Gwara ka aurar da yar ka tun tana karama kana iya tankwarata. Yanzu ba gashi ba xatai auren ta tabar yuyar su hannu na mai kafada( Wai ni)”

Ta karasa fada tana mun zunde da baki. Yi nayi tamkar Bansan suna tsakar gidan ba na kauda kai na gefe. Band’aki na shige na rage ciki na kafin na fito nai ficewata yar kasuwa siyo sabulu da kayan k’walam da wazobiyar (hamsin/50 Naira) da Dara’ifa ta bani.


ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
[3/4, 9:59 PM] +234 903 234 5899: *KIBIYAR AJALI.....!!!!*
_(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)_
🏹👑👩❤️👨💝


*MALLAKAR:- NANA HAFSAT* 🧕🏼
*(MISS XOXO)*


*©️®️ZAFAFA 5 2021*
(NA KUDI NE! NEMI:+234 903 318 1070 KO +234 903 234 5899 DAN MALLAKAR NA KI!)


*BABI NA 4*
(Free page)


*Cikin* kankanin lokaci aka fara kawo malamai daga cikin birni wadanda zasu koyar da mutanan karkarar mu karatun boko, a cewar mai gari harda na addini duk za'a koyar kuma kyauta, abinda kawai ake bukata shine iyaye su yarda su dinga tura yaransu makaranta. Yaran mai gari dana mai unguwa da liman da sauran masu faɗa aji a kyauyan mu su aka fara sakawa a makarantar saboda ma kar wasu iyayen sunce gashi gashi, su ance su kai yara makaranta amman wadanda suka ce ayi su basu saka nasu can ba, hakan yasa suka fara yiwa tufkar hanci.

Tun daga kan su kuma ba'a kara kai wasu ba, ba wai rashin yaran zuwa makarantar ne babu ba. A'a tsabar su yan garin basu yarda da karatun bokon ba shine ya hana su kai yaran su. Ganin haka ne yasa hakimi da kanshi ya yi magana cewar dole ne kowa ya kai dansa makaranta tun daga kan dan shekara uku zuwa goma sha biyar maza da mata. Amman iyaye mata suka ki barin yaransu mata suyi, a cewar su babu abinda ya kamaci suyi irin talla dan su tara abin da za'a siya musu lokacin aure. Ni kuwa da dama bani da wani mafadi idan ba Baffa na ba, kuma shi ɗin ma ba wani tsoro yake bani ba. Sai ya zamana babu mai cewa Dije shirya na kai ki makaranta, ko kuma Dije zoki je makaranta.

Ranar da aka fara yin karatu naje makarantar amman ba wai shiga nayi ba, lekawa nayi ta taga na hangi su Abu yar gidan mai unguwa zaune a kan benci ta kurawa malamar ido kamar zata hadiye ta, na kwashe da dariya tare da sake yin ɗage yadda zan dinga hangowa sosai nace.

“Kai Abu hekace kin samu talabijin sai kallon matar can kike yi.”

A dai dai lokacin malamar ta juyo da yake rubutu take yi a jikin allo. Ita kam Abu turo baki tayi ko bata fada ba nasan bacin rai ne a zuciyar ta dan itama ba son makarantar take yi ba. Malamar ta saki murmushi cike da tsantsar kulawa ta kalle ni tace.

“Zagayo ki shigo kema.”

Cikin dafe kirji da zaro ido duk a lokaci guda nace mata.

“Wa?” Malamar tace,

“Ke mana, shigo ki zauna a yi karatun dake.”

Budar baki na sai cewa nayi.

“Allah sitiri buƙi, inci tsohowar....”

Ban kai ga karasawa ba naji wani irin abu ya sauka a tsakiyar kai na, babu arziki na yi kasa ina kuka ina ihun a kawo min dauki. Kafafuwa da na gani sanye cikin wani cover sheo shine ya tabbatar min da cewar wani ne ya yi min abu. A hankali na dinga dago ido ina karewa jikin kallo, kafin daga bisani na sauke idanuwa na biyu na dora su kan fuskar shi, gabana ya buga ras! Saboda tsananin tsoro da naji. Sam fuskarshi babu annuri bare kayi tsammanin fara'a a kai, ya kalle ni fuska a murtuke tare da cewa.

“Bar nan gurin ko na babbalaki.”

Sam ban san daga ina furucin ya fito ba, dan ban maji kalmar a baki na ba bare nace ni nayi, kawai saukar furucin nayi a cikin kunnuwa ne ina cewa.

“Saboda me?!”

“Ohh tambaya ta kike yi?”

Cike da gasgata tambayar da ya yi min nace,

“Eh walle talle ban gane mekake nuhi da cewa na bar gurin ba.”

Bacin rai ya kuma ziyartar zuciyar shi, ya dan matsa kusa da bishiyar darbejiyar dake bayan shi, ganin yana niyar tsinko bulala yasa nayi saurin rugawa da gudu tare da yi masa gwalo. Shi kuwa gabaki d'aya haushin yan kauyan namu yake yi, tunda yazo yake faman korar masu zuwa gulma wato iri na kenan, bamu shiga anyi da muba, gashi mun hana wadanda ake koyawa suyi cikin nutsuwa. Malamar ta leko ta taga tana yiwa malamin magana cikin dariya.

“Malam Auwal kana ta fama kaima.”

Yaja dan karamin tsaki,

“Ni anya zamu shirya da yan kauyan nan kuwa? Wallahi malama Mardiyya baki ji yadda rai na yake baci ba, gashi sam basu da tarbiya mazan su da matan su.” Dariya malama Mardiyya tayi.

“Wallahi kuwa malam Auwal sai dai kawai muyi hakuri tunda Allah ya kaddara cewa nan zamu dawo, ni dama mai gida na da kyar ya yarda wallahi dan cewa ya yi sai dai na ajiye aikin saboda nisan dake tsakanin mu da wannan Kauyan.”

“Mtwww! Ni abin da yake bani haushi malama shine, yadda kina ganin yara a kauyan nan maza da mata sunfi dari biyar duk wadanda basa zuwa, dubi ko class d'aya mun kasa samu saboda wulakanci, babu abinda suka sani sai tallah shegun.”

Malama Mardiyya ta kwashe da dariya tana gyara zaman mayafinta tace,

“Lallai malam Auwal kafi mai gida na jin haushin wannan kauyan, kasan shima ya taba zuwa nan yin aikin ƙidaya, nake gaya maka suka ki amincewa a yi musu haka suka tattara suka koma gida ransa a mugun bace. Shi yasa da nake gaya masa anyi min transfer zuwa nan ya fara masifa, da kyar na samu ya amince, tunda gaskiya ni dai albashin da nake karba yana rufa min asiri sosai.”

Malam Auwal ya tabe baki kai kace shi ba da albashin ya dogara ba, mugun dan kwalisa ne dan irin samarin nan ne da suci a cikin su gwara su sanya a jiki ace sunyi abu iri kaza a rayuwar su. Matashi ne dan a shekaru ba zai wuce ashirin da bakwai ba, dogo ne baki irin mai kyau din nan mai dauke da yar siririyar fuska, idanunsa mici-mici kamar wanda aka sauwa, habarsa dauke da d'an guntun gemu wato tabani kasha hadisi da samari ke yi. Ya kuma taɓe baki tare da cewa.

“Ai kuwa ni zanyi maganin su wallahi tallahi, dan babu shege ko shegiyar da zata sanya ministry su zo suyi mana dibar albarka.”

“Da kyau malam Auwal ina bayan ka wallahi dari bisa dari.”

Cewar malama Mardiyya tana ta dariya.

Wucewa ya yi ya tafi ita kuma taci gaba da koyar dasu kamar yadda ta soma yi.

Ina ta gudu ban tsaya ba, duk a zato na yana biye dani ashe bai ma biyo ni ba, sai da naje kofar gidan mu na turo kofa tare da lekawa sannan na tabbatar da cewa gudun banza nayi. Gajiyalle ta damko min wuya na tare da tun kudani cikin gida tana masifa.

“Gantalalliyar yarinya kawai, babu abinda kika sani sai yawo da bin lunguna yin dambe. To zaman banzarki ya kare daga yau, maza dauki gashi nan na soya nayi miki kullin biyar, goma da ashirin. Tun dazu na hangi su Lami sun tafi tallar wainar roga da wainar gero nasan zuwa wannan lokacin ko basu siyar ba toh sun kusa. Amman ke da yake ba ƴar mutunci bace, baki taba yin tunanin abin arziki ba, tashi maza ki tafi yar kasuwa ki sai sa min.”

Wani sassanyan dadi ya mamaye rai na, yau na samu abin da nake so wato damar yin tallah, saboda tan matukar bani sha'awa, musamman idan naga yadda kawaye na suke sha'anin su da kudi. Carab na dauki farantin gyada ina murmushin farin ciki nace da Gajiyalle.

“Daman fa Gaji kece baki sani ba, ina ta so na gaya miki ki dinga yin wani abu ina fita yar kasuwa dashi. Toh sai na yi shiru dan karki doke ni, yanzu kuwa kinga kema zaki zama mai kudi kamar Innarajo, dama har ta fara tarawa Balki kayan aure, nima kinga sai ki fara yi min tanadin nawa.”

Ta sakar min wani banzan kallo wanda ya tabbatar min da cewa taji haushin kalamai na, sai dai bata ce komai ba har na tashi na fice daga gidan. Wayyo ranar jina nake tamkar a gidan aljanna saboda farin ciki, gashi tun kafin na karasa yar kasuwan na fara ciniki a majalisar Sallau mai tsire.

Cas! Suka bani kudin gyadar naira saba'in na dauki farantin na dora a kai na ina digirgine ga kuma kudi a hannu ina kuma lissafawa. Ta kusa da makarantar da aka bude na bi, har zan wuce sai kuma na sake shiga ina mai kulle kudin a gefen mayafi na da nayi damara a kuguna. Wasu malamai suka kira ni suma suka siya, naga na dazu da ya biyo ni amman wannan karon ko kallo na beyi ba, har zan tambaye shi ko zai siya, sai nayi shiru dan na lura kamar bashi da mutunci.

Na tafi yar kasuwa kasan cewar ni sabuwa ce kuma gyadar sabuwar suya ce sai ya zamana ta kare da wuri. Ina kudin Gajiyalle? Na same su ci banza ci wofi tamkar nawa ne, ni har mantawa ma nayi cinikin ba nawa bane saboda rufewar idanuwa. Ban lura cewar kudin sun kusa karewa ba sai da naje siyan kankana kwallo daya aka ce min naira saba'in, jiki na yana bari na zaro ina kirgawa naga arba'in da biyar ne kawai. A lokacin gabana yayi mugun faduwa na dafe kirji na tare da furta.

“Na shiga uku da Gajiyalle.”

Babu shiri na dauki farantin gyadar na tafi gida, sai da na kusa zuwa sannan na fashe da kuka ina tafiya ina yi kamar wacce aka yiwa dukan tsiya. Na shiga zaure na samu kasa duk na zuba a jikina da gurin baki na idan ka gani ba zaka taba kin cewa ba na jaki na sha ba a gurin manyan maza, na shiga ina dora hannu aka. Gajiyalle na zaune tana dinkin hula gani a wujejjige yasa ta saurin mikewa tana tambaya ta.

“Lafiya Dije?”

“Na shiga uku Gaji zasu kashe ne.”

“Suwa ye?”

“Yan sholisho... Wayyo Allah na Gaji sun kwace cinikin na shiga uku.”

“La'ilaha illa lahu ni jikar mutum hudu me kike son sanar dani Dije? Kina nufin kice an siyar da gyadar yan iskan gari sun turmusheki sun kwace cinikin?”

Na gyada kai na ina share maina da bayan hannu, tace.

“Na shiga uku Dije kin cuce ni, dan kaniyarki ina karfinki da har kika bari aka kwace kudin? Shikenan daman gyadar rantowa nayi nace zan yi gwaji gashi nan kin gwadani Dije, wallahi Kedai banza ce sakarai shashasha. Allah ya isa ban yafe ba, gashi dole na biya.”

Tana magana rana duka na ni dai ban da bata hakuri babu abinda nake yi, cikin dashasshiyar murya nace bayan na zaro ragowar kudin.

“Wannan kawai suka bani, suma din sai da suka mare ni da suka ji nace ba tawa bace ta babar mu ce.”

“Uban babar ku, nice babar taki dan malafar gyatuminki? Da ace kin dauke ni uwa ai da ba zaki bari su karbe miki ba bakar munafuka kawai, tashi ki bani waje ko na karya ki, bana son ganin ki Dije na tsane ki.”

Na tashi kamar munafuka na fita, zama nayi a zaure ina tikar dariya ta ganin yau na rainawa Gajiyalle hankali. Tun daga lokacin kuwa bata sake gigin dora min komai ba, duk nacin da nayi mata kin yarda tayi haka na hakura, na koma gidan jiya wato yawace-yawace kwararo-kwararo ina gurin.

*SASHEN MAI GARI JAMILU*

Gaba d’aya kusan duk maza dattawan dake karkarar Durbun suna zazzaune a karkashin bishiyar darbejiyar da mai gari jamilu yake zaune. Yana hakimce akan kujerar sa yasha rawani na masu gari, Sauran mutane na daga kasan taburmi sun yi gurfane suna sauraron mai gari. Malam Bashari (baban Dije) shi ma yana gefe kansa a kasa. Mai gari ya sake jan majina kafin ya cigaba da cewa,

“Toh nagode da abunda wasun ku suka yi min, Wato ina matsayin mai garin nan ban isa na zartar da hukunci ba kenan sai an gayawa magabata na? Saboda an rena ni shine Za’a kai ‘karata wajen hakimi? Kai bara na fito muku a Mutum. Kauyen nan tsatso na ne suka kafa shi, Babu wasu wa’enda suka isa su zartar da hukunci bayan namu. Ku ba farin cikin ku bane ace ‘ya’yayen ku suna boko? Yanzu ‘yayan kansila su biyu ina har alfindi yake kai su kullun suyi bokon? Gata ya samu yanzu za’a zo amana makarantu shine kuke bakin ciki? Wannan

Please Login or Register in order to submit comment