Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita daga ajin, ni kuma nayi tsalle na koma gurin Siyama dan na kwashi rabona, da yake tasan hali na komai guda-guda ta bani sauran kuma ta gutsiran musu ta basu ana ta hira. Mun dade a makarantar saboda idan wannan malamin ya shigo ya fita sai wani ya shigo shima ya yi surutunsa ya gama bana fahimta har aka tashi, ina komawa gida na tarar Mudi ya dauki akuyar Gajiyalle hannunsa rike da doguwar wuka yana jan akuyar yana fadin.

“Wallahi sai na siyar da ita, nace miki bani da kudin da zan kama sana'a ki bani jari kinki. Nace ki samomin sana'a shima kin shafawa idanunki kwali dan haka dole ne yau na siyar da wannan abar dan nima na dogara da kai na.”

Dariya ta kusa kamani ganin yadda Gajiyalle take bin Mudi tana rokonsa tamkar wani mijin ta ko mahaifinta, yadda take riko shi yana ture ta zaka yi tunanin ko laifi tayi masa yaki yafewa.

“Dan Allah Mudi kabar min abubuwan nan suci gaba da girma suna hayayyafar wasu, idan kana min zari day-d'aya ai zasu kare. Kabari yau din nan zanje wajan mahaifinka na karbo ma jari mai yawa.”

“Naji, idan kin karbo ki rike kudin a bakacin wannan akuyar da na dauka.”

Ya yi tafiyarsa hankali kwance, babu abinda ya damesa da yadda yaji Gajiyalle tana kuka tana ihu kamar wata tababbiya. Ni kuma na karasa kusa da ita wai zan lallashe ta tunda naga babu mai bata hakuri, makota ma basu shigo ba bare asa ran zasu bata hakuri su taushi zuciyarta. Nasa hannu zan kamo nata tayi saurin sanya kafa tare da ture ni na buge da bango, dai dai lokacin Baffa ya shigo kuma yaga yadda ta ture ni. Ya kalle ni ya kalli Gajiyalle daga karshe yace dani.

“Ummina me ya faru?”

Na tashi tsaye ina karkade jiki na tare da turo baki.

“Ba Mudikalle ne ya daukar mata a....” Ban karasa ba tayo kai na tana cewa,

“Munafuka yiwa mutane shiru, daman kallon mu kike kina sauraro dan ki dinga zuwa kina gayawa mutane? Ina ruwanki yar jakar uba? Mudikalle dai nawa ne dan haka ba komai ɗan ya dauki kayan uwarsa. Ke yanzu ba hanyar lalacewa kika dauka ba? Yanzu daga bokoko kike shegiya, shi sana'a zaije ya fara ya zauna da mutuncinsa.”

Na kalli Baffa naga ko zai ce wani abu amman ya yi shiru sai hula ma da ya gyara tare da wucewa dakinsa yana cewa.

“Toh shikenan Allah ya kyauta.”

Haushi ya kamani, Ban taba ganin miji irin Baffa na ba. Duk gidan da nake shiga matan suna tsoran mazajen su amman banda Gajiyalle da Baffa na, gabaki d'aya rayuwarsu ta banbanta da ta sauran ma'aurata. Gaji ta kuma kai min doka na goce hannunta ya sauka jikin bango ta kuma sakin wani ihun tana zagi na.

Waje nayi dan nasan ranar ko kanzo bazan samu ba dan haka gwara naje na nemo abincin da zanci. Karatu kuwa gabaki d'aya na manta dashi bare na tuna da kyautar da malam Auwalu ya bawa Siyama, ko kuma dan be karfafa min gwiwar cewa zai bani ba shi yasa na manta oho. Haka dai na yini a waje sai dare na sake komawa gida, da nayi sallama ma bata amsa ba ko haushi take ji har lokacin oho mata. Na samu waje na kwanta ina ta uban nishi saboda naci tuwo a gidan su Nafisa ci na hauka saboda sai da kowa ya tashi ya barni a wajan kwanon.

Gajiyar wasan jiya da kuma haushi na da Gajiyalle kiyi yasa na makara da tashi, sai kusan karfe takwas da kwata na farka. Ina ta hamma na shiga bandaki na fito ina kallon kofar dakin ta naganshi a kulle tasa tsumma ta kulle kofar alamar ta fita unguwa. Na shiga dakin Baffa yana kishingid'e yana sauraron radio ya kalle ni cike da mamaki yace.

“Ummina baki tafi makaranta ba daman?”

“Makaranta kuma Baffa! Wacce?” Ina turo baki ina maganar dan sam na manta da ita.

“Boko da kika fara zuwa mana jiya, ina nan ina murna kina can kina ta zuba karatu ashe kina cikin gidan nan Ummi na.”

Nayi saurin bubbuga kai na jin yana motsi wanda bana raba d'aya biyu kwarkwata ce ko amosanin ka, nace.

“Aradu na manta da ita, yo nifa yanzu na tahi Gajiyalle ko tahi na bata yi ba kuma yunwa nake ji Baffa.”

Gefansa ya duba ya dakko wani kofin sulba ya miko min, nasa hannu na karba. Koko ne ya sake miko min kaushi mai dauke da danwake yace naci. Ina ci muna hira yana cewa nayi sauri na tafi makarantar.

“Baffa har kyauta ake ba yarwa a ajin mu.”

“Masha Allah, kema ki samu ki ciwo babba kinji Ummina?”

“Yanzun nan ma kuwa Baffa, dan ma dai malamin ba hi da mutunci walle. Baya sona he ya yi ta zagi na yana kira na da yar tallah.”

Baffa ya girgiza kai dan shima yaji babu dadi yadda naga fuskarsa ta bayyana. Ina gamawa ya bani naira biya na dauki hijabi na da yaci uban dauda na tafi ina wake-wake na. Kai tsaye ajin mu na jiya na shiga, ganin ba malam Auwal bane yasa nayi saurin fitowa na kuma lekawa d'aya ajin nan kuma malama Mardiyya ce, na kuma fitowa da gudu, tana ta kira na amman nayi mata banza saboda yau ajin da malam Auwal yake nan nake son zama.

Can na hangoshi a ajin yara wato ecc yana ta raba musu alawa suna ta murna, ba zato kawai yaga ana miƙa masa hanu, girman hannun yasa shi saurin kallon mai shi muka hada ido na sakar masa dariya shi kuma yana hararata yace.

“Ke kuma daga ina kamar wata aljanna?”

“A bani nima.”

“Me?”

“Alawar da kake rabawa.”

“Ke wai me yasa baki da hankali ne? Kinga sa'anninki a nan wajan?” Kamar ban san abin da yake yi ba, idanuwana suna kan alayoyin yaran ina ta hadiyar yawu.

Ni gaba d’aya ba damuwa nayi da gasamin maganganun da yake yi nayi ba. Fatana dai ya dankamin alewar da yake rarrabawa yan yara. Na sake matsawa kamar zan shiga jikin sa, Ya tsula min tsumangiya ko zafi ma babu. Na kwashe da dariya ina karkade inda ya dake nin, Ma’ana dai na mayar masa da kayan sa domin ba zafi tai min ba. Cike da mamaki yake duba na,

“Zaki matsa ko sai na kara zuba miki wata?”

“A hayye nanaye! Malam Lauwali kenan. Yo dan wannan dukan naka shine me zafi? Yo ko gajiyalle takan dau lokaci tana kirbata kafin nayi kuka. Nide yanzu dan bani guda d’aya ko rabi ce Malam Lauwali.”

Zubamin wata shaudar yayi yana huci,

“Ke waye Malam Lauwalin? Ni sa’an wasan ki ne. Naga alamun tsantsar reni a tattare dake. Kneel down!”

“Lid-dawun? Me kenan! Ayyo. Tab! Yasin na mance sunan kane Malam.”

“Kneel down! Bush girl!”

“Lid-dawun! Bushgyas. Nifa kayi da yaran hausawa bana arna ba. Dan bansan me kake nufi ba.”

“Zaki sani yanzu kuwa. Jeki tsakiyar ranar can ki tsugunna awajen akan gwiwoyin ki, Duk malamin daya ce ki tashi kice nace a’a.”

“Tafi nono fari.. a hayye sha madarar lilo..”

“Ke me kika cewa.?”

Ko kallon sa banyi ba, Na kwaye rigata na zuba gwiwoyina a kasa, Inata sauke masa kwandon tsinan taka.

“Matsiyaci, akan ya bani alewar yana bakin cikin zan da zanyi. Allah ka saka min.”

Ina daga nesa ina zabga masa harara, Da sauri ya taho ko duka na zai yi sai kuwa ya bige da kyauren kofar ajin, Me zanyi inba dariya ba? Na shjga kyakyatawa kuwa ina nuna shi. Cikin haka Malama Mardiyya tazo ta same ni,

“Khadija me kike anan!”

“Malam Lauwali ne nasan, Ya hanani alewa, Ya shasshauda min tsumangiya, Shine nan kuma yace nazo na zuba gwiwoyina a kasa. Ai kuwa gahi can ya doke gohin sa a kyaure.”

Na karasa ina babbaka daria, Malama Mardiyya ta girgiza kai kawai,

“Malam Auwal sunan sa ba Lauwali ba. Kuma ki dena yin abunda Za’a dake ki. Sannan malamai tamkar iyayen ka suke kinji? Domin daka baro gida kazo hannun su, Duk wani abu da zasu saka dole kayi. Sai yanzu kikazo makarantar?”

“Yasin Gajiyalle ce bata tahe ni ba, Jia da na koma Mudi ya janyo dan akuyar ta zai sayar. Taita ife-ife tana rokan sa ya bari ai kuwa yaki yadda ya tafi da akuyar nan, Yace ai yace ta bahi kudin jari tak’i. Hi nefa naje rabiyar fadan ta tattake ta doke ni da hyarbebiyar k’afarta a salansar kirji na. Ai kuwa inaga tun duhun safiya ta fice. Hi ne fa motsin ta da ban jiba ya makarar dani, He ba dad’ewa na zo.”

“Oh ni Mardiyya! Kayan jiya kika sako, Kinyi wanka kuwa Khadija? Sallah fa kinyi da asuba?”

Girgiza kai nayi,

“Yasin da asubah ina ta narkar bacci na, daman masifar Gajiyalle ce ke tahi na, toh kuma ba tayi ba shi yasa ban san sanda akai asuhabin ba. Wanka kuma dame zanyi hi Malama? Ba kayan wankan fa.”

Na karasa fada ina sosa kai na.

“Ko dai qudubus ko kwarkwata ce a kan nan billahil lazi. Gidan d'an wanzan zanje ya yahe gahin gaba d’aya.”

“Subhan’Allah! Allah ya shiga lamarin ki Khadija. Kan naki zaki je a yashe gashin? Saboda me Khadija? Ki dena fad’ar haka. Mace yar gyara ce. Ana gyare miki kan ki dama sauran gurare zaki ji kinyi fyes abin ki. Gaki da yalwar gashi tubarkAllah.”

“Tab Malama ai gahin kayi na ya hya sharba Malama, Na takwas kenan. Domin da ya iheni da kaikayi zan je a saisaye hi, Hima dan anacen ba’a runtse hekara zai kara cika fiye da na baya.”

“Wasu na nema wasu na aske nasu. Toh anyi an gama ba zaki sake aske kanki ba Khadija. Yanzu dai bara na rokar mana Malam Auwal ya kyale ki ki koma aji. .”

Tafiya tayi ta ta nufi wajen Malam Auwal, Yana tsaye yana mulmula goshin sa inda ya bige, Ya kumburo yayi suntum. Yana kallon kansa ta wayar salula,

“Sannu Malam Auwal.”

“Sannu Malama. A gaskiya ki san yadda zaki kiwa headmaster magana ya canzamin ballagazar yarinyar can a ajina. Gaba d’aya na tsaneta tsana mai wuyar fassarawa, Sam batada kamun kai. Yadda kikasan tababbiya haka take abubuwan ta.”

“Kayi hak’uri Malam Auwal. Sha’anin Khadija sai ahankali, Yarinya ce data taso da rashin uwa, Tun tana kankanuwa mahaifiyar ta tarasu, Rikon ta ya koma hannun kakarta, Ka kuma san wani goyon kakar yadda yake, Ballantana nan kauye. And still wahalar bata k’are ba Malam, Babanta ya Kara aure, Na takaita maka zance dai a hannun kishiyar uwa take. Kishiyar uwar kuma tazo da agola. And baban ta bashi da say. Tamkar ba shi ya haife taba, Matar tagama dashi. So Khadija tana yin wata irin rayuwa ne mai ban tausayi, Shi ‘da na kowa ne, Shysa nakeson na temaka mata wallahi, Ko Allah zai dube ni ya bani nima mai jin kai. Banason wannan abun ya shafi kwakwalwar ta yasamata psychological trauma Idan ta manyanta.

“Saboda she’s depressed. Ina tausayin kai na ina tausayin baiwar Allahn nan. Gaba d’aya banda neman abinci da shiga ruguntsumi ba abunda ta sani, Ba sallah bare sanun fannin islama. Kawai rayuwa take tamkar mutum mutumi. So please Malam Auwal.. please ka temaka kai ma mu temaki Khadija daga fadawa kogin halaka, Ka temaka da karfin ka da karfin iliminka ka nunar da ita rayuwa, ‘Ya mace ce dake bukatar tattali. Kuma kalle ta mana, She’s young. Kai ina tausayin Khadija.. Na cika ka da surutu taje aji? Kaji?”

Malam Auwal ya daga kafada yana furzar da iskar bakin sa,

“Tsabar duhun kai ce kauye ta ba kauye, Ta zauna ta sharara miki karya kin yadda. Ni ban yadda ba gaskia. Ina ban yadda ba. Irin wa’innan Yaran gasunan acikin gari, plan suke had’awa da iyayen su fa suyi ta samun kudi haka. Look Malama Mardiyya shine your eyes, Yarinyar can muguwar makaryaciya ce. Crook ce da kike ganin ta haka. Hum Uhm”

“Au baka yadda ba kenan Malam? Baka yadda ba? Duk wannan dogon zancen dana maka. Ai shikenan yayi kyau. Toh ni zan tsayawa Khadija, Kuma na yadda da ita..”

INA can ina yar carafke Malama Mardiyya ta dawo tana yak’e,

“Tashi muje aji Khadija, Sannu! Karkad’e jikin naki kinji?”

Karkade rigata nayi, Na mike muka tafi har aji ta raka ni. Yau uwande ma kafu kaza ta kawo, Na lashe lebe na na koma wajen ta kafin Malam Auwal ya shigo,

“Uwande uwar kirki.”

Uwande ta sheke da dariya tana buga k’afarta,

“Kai Dije, Yau kuma ni ce uwar kirki.”

Na kada kai ina murmushi,

“Walle Uwande kinada kirki sosai, Kefa abunki be rufe miki ido ba irin na munafukar can.”

Na karasa fada ina mai nuna Siyama. Uwande ta sheke da dariya,

“To ai kuwa nagode, Me Za’a baki?”

“Kafu tsire zaki bani na biyar..”

Na ciro biyar din da Baffa ya bani na mika mata. Karba tayi, Ta bani har kulli uku, Ta kyautamin ne saboda nace mata uwar kirki. Mik’ewa nai na koma waje na na zauna. A hankali na dinga dangala ina sha ina lumshe idanu na, Hekace tsire nake ci, Kafu tsire naman talaka.

Cikin haka Malam Auwal ya shigo yana kwambo, Yan ajin suka mike suna gaishe shi,

“Gudu moni ankul..”

Zare idanu na shiga yi ina cigaba da bincikar Kafu tsire ina afawa a baka.

“Ke.. Taso Ki zauna anan. Ki kuma wullar da duk abunda kike ci”

“Ni ba abunda nake ci Malam.”

“Ni zaki wa k’arya? Kai jeka ka dau koma Meye ka wullar.”

Ya ce da Usainin Marka dake gaban sa, Na zabgawa Usaini harara Ina kudindine ledar a kayi na,

“Walle ka taba ni sai na yi gunduwa gunduwa da kai, Kasan hali na dai, Oganniya ‘kaya batasan na gida ba. Babu ruwana da Marka kawar Ladingo ce, Yanzun sai na caskala ka, Na casaka nayi kutubal da kai.”

“Ke me kike cewa, Dalla Kai kwace koma menene ka wullar, Ki tabashi kiga yanda ake sauya halitta.”

Damara naci na damke hannu na, Amma dake Usaini ba shi da kirki yana kuma tsoron Malam Auwal haka ya wafce ledar ya jefa a kwata ta kofar taga,

“Kutumelesin kan babban balain dirimin durbun, Walle yau ba Malam Auwal ba, Ko Hakimi ne zai zo daga birni sai na lakada maka na jaki. Zaka san ka taba mallaki na yau.”

Raina a bace na koma gaban Malam Auwal na zauna, Gaba d’aya hankali na baya wajen jira kawai nake a tashi na tisa keyar Usaini mu dambatu. Malam Auwal ya fara mana darasi. Ranar kwata kwata ban kara shiga harkar sa ba, Duk neman yadda zai ya dake ni yake sam naki bashi hadin kai, Usaini kuwa yayi tsuru tsuru yana raba idanu, Ana kada kararrawar tashi na dubi Malam Auwal Sai da naga ya gama hada kayan sa ya fita nima na fice, A bayan makarantar na zakulo Usaini yana ta gumi shi kadai, Na mikawa Uwande jakar bayan sa kafin na ja kafar sa na shatale shi ji kake tim.

“Tahi dan kundin uban ka mu tafi ‘filin kaci uwa ka’, Yau anan zan lakada maka na jaki, Kuma mu tafi wajen mai gari ya mana shari’ah. Banza mai bajajjen hanci.”

Muna tafe da zugar yara ana min kirari har muka karasa ‘Filin kaci uwa ka’ A filin ake dambatuwa musanman Idan mashahurin fada za’ai.

“Dije-Dijangala Oganniya ta Gajiyalle mai yar hakiya, Yar baffan ta. ‘Kaya baki san na gida ba.”

Haka zugar yara keta fada, Na shata layi tsakanin mu da Usainin Marka,

“Alo tsiya, Alo danja, Hege ka fasa, Dan halak sai yanka. Ho ni Dije, Yar gala ta baffan ta.. Tahi mu dambatu Usaini, Har ni zaka wullar wa abu na a kwata. Ko ka Kanta fada uku na taba tare maka, Ba ma siya kayi ba, Kawai mutinci na maka na shigar maka. Wai ni? Ni Usaini zaka yiwa haka. Yau zan nuna maka menene halacci.”

Kafar sa na janyo yanata kuka yana rok’o na, Na shiga kirbar sa ina sake tamaula dashi, yara sai ihu suke suna tafamin. Cikin haka sai ga Galin mai gari ya iso, Yana zuwa ya raba mu ya tisa k’eyar mu wajen mai gari, Dadi kashe ni dama abinda nake so kenan. Na zube akan taburma gaban mai gari,

“Alhamdulillahi, Mai gari dama daga can wajen ka zan yo walle.”

“Dijangala kawo k’arar ki wajen nan ba’adadi. Yau kuma me kika yi?”

Mai gari Jamilu ya tambaye ni yana mai cigaba da jan carbin hannun sa, Na gyara murya ina nuna Usainin Marka.

“Kanaji mai gari? Usainin Marka, Wai Usainin Marka ni zai wa butulci?”

Mai gari yayi murmushi yana kallo na, Sauran manya dake wajen suka shiga keta daria,

“Billahil lazi, Na tare masa fa’da ba adadi mai gari. Amma dan bakin munafurci da kinibibi da tsagwaran mugun ta, Kanaji mai gari?”

Mai gari ya kada kai yana sake dubana da kyau,

“Yauwa, Don Allah mai gari ya dace abunda Usaini ya min? Baffa na ya bani nera biyar, Ai kasan Baffa na dai. Toh ya bani biyar. Mugun Malam Auwal d’innan dama tunda naje makarantar ya tsane ni, Domin yau ma yasa na zube gwiwoyi na kasa Wai Lid-dawun. Toh nayi! Da biyar din da Baffa ya bani na sai Kafu tsire awajen Uwande, Ko Uwande?”

Uwande ta kada kai alamun ba Karya nayi ba. Na sake gurfane na cigaba da cewa,

“Hikenan sai na sai na biyar. Na koma waje na na zauna, Haka kawai Malamin nan yana higowa sai ca yai wa Usaini Wai ya kwace koma menene nake ci ya wullar, Fisabilillahi mai gari Kud’i na ne fa, Na saya. Kuma sanda na saya babu malami a ajin. Nafa boye a gahi na. Amman mai gari walle sai da Usaini ya zaro hi ya wullar a kwata. Shine nace daman bayan na gama narkar sa dole ne muzo kama shari’a. Dan banci nanin ba, Nanin ba zata cini ba ehe.”

Mai gari ya sauke k’atuwar ajiyar zuciya ya dube ni ya dubi Usaini kafin yace,

“Usaini! Wai haka akayi?”

“Haka akai mai gari.”

Mai gari ya girgiza kai kawai, Ya zaro nera goma a aljihun sa ya miko min,

“Shikenan haka yayi?”

Nai saurin kada kai ina tuno dankalin Asiya da zan siyo a bakin kasuwa,

“Toh madalla! Amma dan Allah karku sake fada kunji? Ku basu kunya su wadannan malaman, ku tsaya kuyi karatu. Muyi alfahari daku, Muma ya zamto ana damawa da karkarar mu a birni a dena renamu, Domin kune manyan gobe, Mu lokacin mu ya wuce.”

“In Sha Allah mai gari za kai alfahari damu, Ni dinnan nan da wasu hekaru zaka ganni a gidan talabijin ko radiyo ina kwarara bayani..”

“Allah yasa Dije! Allah ya nuna mana..”

Mik’ewa nai nayi gaba abuna, Ko takan su Uwande ban kara bi ba, Na nufi Y’ar kasuwa sawo dankalin Asiya. Sai da nayi kwanaki hudu daga hutun asabar da lahadi na zarce litinin da talata, sam na manta da makaranta sai ranar labara naje kallon wasan kauraye da aka yi a bayan gari kawai na hadu da malama Mardiyya zata tafi gida dan lokacin an tashi daga makaranta. Ta kalleni fuskarta babu yabo ba fallasa ta kira ni naje da sauri ganin tana saka hannu cikin jakar ta, a tsaye ina dashe baki nace da ita......
...
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
[3/10, 7:27 PM] +234 903 234 5899: _ZAFAFA 5 (2021) NA KUDI NE, DUKA BIYAR DIN AKAN FARASHIN NERA 700 KACAL! KA/KI DUBI GIRMAN ALLAH KI SIYA DA KUDIN KI KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI, KA/KI/KU GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA DAMA MASU SIYARWAR!!! DOMIN SIYAN NAKI TUNTUBI: +234 903 318 1070 KO +234 903 234 5899, AKWAI ‘KARUWA SOSAI ACIKIN WADAN NAN LITTATTAFAN😍MUNA FARIN CIKIN KASANCEWAR KU A TATTARE DAMU😘 MASOYAN MU ABUN ALFAHARIN MU🙌🏻_


_*KIBIYAR AJALI..!!!*_
_(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_
🥰❤️👑🏹

_(PAID STORIES/ZAFAFA 5 BOOKS DIN KUDI NE..)_


_*MALLAKAR: NANA HAFSAT_*
_(MISS XOXO)🧕🏼_


_*BABI NA: 8_*


_*Wattpad:missxoxo00_*


***

“Hannu malama Mardiyya.”

“Yauwa Dije gwara da Allah ya had'a ni dake yanzu. Me ya sa bakya zuwa makaranta kwana biyu, na bincika ance min kina nan lafiya lau kawai ganin dama ne baki zo na.”

Na tafa hannaye ina dariya,

“Malama tawa!”

Maganar tawa ta fito cike da sauki dan ina son matar nan saboda tana sona.

“Ina jinki gaya min meke faruwa?”

“Babu komai wallahi, mantawa nayi ma da makarantar.”

“Innalillahi! Dije daman baki saka son zuwa makarantar nan a zuciyar ki ba?”

Na zaro ido waje,

“Kai! Malama ai bazan iya sata a zuciya ta ba, kinga girman makarantar kuwa?”

Ta girgiza kai,

“Ni ba haka nake nufi ba, ina nufin kiji kina son zuwa koyan karatu a cikin ranki. Haba Khadija ya za'a yi kina girma amman baki dena wasu abubuwan na shirme ba? Yanzu ina zaki je?”

“Oho, ni daga wajan kallon wasan kauraye nake.”

Ta girgiza kai tare da gyara jakarta a kafadarta. Kallo na tayi sosai sannan tace.

“Muje ki nuna min gidan ku”

Babu musu na amsa mata muka tafi muna hirar mu har muka hadu da malam Auwal zai tafi gidan liman, yana kallan mu amman yaki kula mu itama malama Mardiyya bata yi masa magana ba har muka wuce. Da sallama a baki na muka shiga ciki, Gajiyalle tana tankaden garin dawa da zata yi tuwo. Taki amsa min tayi tunanin ni kadai ce, sai da taji muryar malama Mardiyya cikin sallamarta da dole ne duk wanda yake cikin gidan ya jiyo.

“Sannuki da zuwa bakuwa, shigo mana.”

Gajiyalle ta fada tana janyo tabarmar dake bayan ta, naje na karba ina ta faman rawar kafa saboda malama tazo gidan mu. Malama Mardiyya ta zauna tana bin gidan mu da kallo ta ko ina, muryar Gaji ta katse mata tunanin ta inda tace mata.

“Ina wuni?”

“Lafiya lau, ya gidan?”

“Ƙalau muke, sai dai ban wanyeki ba.”

Gajiyalle tayi maganar tana ajiye rariyar da take tankade da ita sai kallon malama take yi kamar wacce aka kafewa idanuwa a kanta.

“Allah sarki daman ba zaki sanni ba gaskiya. Ni malama ce a wannan makarantar da aka bude. Kwana biyu naga Dije bata zuwa, shine na hadu da ita a hanya nace dan Allah ta kawo ni gidan su.”

Tunda Gajiyalle taji tace malamar mu ce shikenan ta sauya fuska tayi kicin-kicin da fuska da alama bata so hakan ba. Malama Mardiyya ta ce na zauna na samu guri a bayan ta na zauna dan ban san me zata fada mata ba, kar naje Gajiyallen ta kawo min naushi.

“Maman Khadija dan Allah me yasa baki tursasata akan zuwa makaranta? Gashi duk tayi wani yarbatsai kamar wata marar mafadi. Dube ta ɗan Allah kamar ba mace ba sai tsami take, ilimi fa yana da dadi Maman Dije, dan Allah kiyi kokari ki canza ta. Ni ban zo dan na gyara miki wani abun ba, amman dan Allah kisa ido akan ta koda wajan kula da ibada ne, ace kamar Dije amman bata san meye sallah ba bare tayi? Muna so muga an samu manya a cikin kauyan nan, amman burin mu ba zai cika ba sai da taimakon ku iyaye, musamman ku mata.”

Gajiyalle tasa kafarta ta buga a kasa tare da kankance idanuwa tana mai nuna malama Mardiyya da yatsa tare da cewa.

“Ke! Dakata min da wannan surutun naki haba, cacacaca kamar wata mai rubabban baki. Yo haka ne mana kinzo sai barin zance kike kamar wadda aka budewa makogwaro. A hayye na naye yau na ga ikon Allah, kizo har gida na kice zaki tsara min yacce zan dinga yin rayuwa ta? To ko hi mai gidan be isa ba ballantana wata ke fankan fayau.

Please Login or Register in order to submit comment