Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun"tambayeni dalilina nayin hakan to xansar dasu komai kuma kushirya amsar tambayeni daxaki fuskanta"" yana Gama fadar haka yatashi yafige daga gidan gabadaya.Ranshi yana kuna iokn Allah ne kawai yakaishi gida Saboda jiri da yake dibarsa
Jiyake kamar xuciyan sa xaitsage saboda kuna da bacinrai.


A,BANGARANSU JAMILA DA
KUMA YARATA UBAIDA.
tunda suka dawo daga mishirikin bokannasu. Suka shige daki tana bawa yar tata kulawa saboda boka bakaramin barna yayimata ba saida ta harhada Mata wasu mugun guna na Hausa ta gasa Mata jikin ta sosai sannan ta ji'dama dama tunda suka dawo bata fito wajaba Saiyanxu da taji sallamar Yusip a parlour Tai taurin durowa daga Kan gadan tayi hanyar fita daga dakin ke inkuma xaki kike sauri haka keda bakida cikakiyar lpy? Babarta jamila ce take tambayar ta. Mm Yusip ne yadawo xanje na ganshi. Tana fadar tafice batare da ta jime mahaifiyar.ta xatasa kuma cewa ba.Adai.dai lokacin Yusip yakarasa shigowa cikin parlour'n tafiya yake kamarxai kifa Ajikinshi yaji ana kallan Shi gurin da yake tunanin tanan ake kallansa.
Aiko yana dagowa sukai Ido hudu da halitta da yafitsana aduniya itako takafe shi da manyan idanunta.masu kamada na mujiya injishi da fada..tsaki yaja sanan yauce abinshi
Dik Wannan abinda yayi mata Bai bata matarai ko kadanba saima wani fatin ciki. da'taji


Daddare yasami mahaifinshi da ajanye maganar aurenasa da ummi.koxan iya' dajin dalilinka nayin hakan?shiru yayi ba amsa.s annan yakuma cewa Yusip meke damun ka naganka cikin damuwa sunkuyar da kanshi kasa yayi. abba bakomai. Yusip inaso kasani baxan iya tunkarar dan uwana da wannan wancan ba amma xankirashi awaya nacemai. Muhadu gobe da safe agidansa inyaso saika sanardashi dalilanka nafasa auren tunda kagiso ka kunyata Ni agurin Dan uwana.wanda shine yaxamemin uwa"da uba. Wllh kabani kunya yanxu dawani idon kakeson na kalleshi? A'tunanina ko wata yadakko canbare yabaka xaka amsa hannu bibbyu Ashe ba hakabane.
Abba Dan Allah dakata yakatsesh banasan Jin wata kalma daga bakinka, abinda xanfada shine kanemi hujjojinka yau daddare kamin waye war gari Dan haka tashi kabani gurin.


Daran"ranar Yusip bairintsa ba ko kadan Allah.allah yake gari yawaye yaji irin hukuncin da Iyayannasu xasu yanke akansu sannan waca hujja ummi xata bayar idan aka tirkesu shidai yasan bashida wata kalma daxai kare kanshi.shiyasa ma yace tanemi abinda xata gayamusu
Haka ya kwana yana tunani kafin bacci barawo yayi a wangaba da shi.


Kiran sallar farko shi.yatsheshi daga dogon baccin daya keyi Acikin baccinne kuma yayi wani mummunan" mafarki wasu mutane subiyu sunbiyo ummi da gudu ga, kuma"wuka A'hannun.su"suna kokarin kasheta,,,
A daidai nan yafar ka yajike share kaf dagumi duk yabi yarude addu.o'i neman tsaki yashiga karan towa da rokon Allah yabayyana mai abinda ke Tun karosu. sannan yaji dama dama..tunda yayi mafar kinnan jikinshi yayi sanyi sosai yamakasa tabuka komai.
Tofa
gabadayasu sun"hallaraa babban falon,gida Al"haji Abubakar.


“To Yusip munajinka meye dalilinka na fasa auran yar uwarka Wanda abaya kafikowa murna amma yanxu kadawo kace ba hakaba to muna sanjin dalilinka na yin hakan? Abbansa ne yake fadar hakan yakuma kafeshi da Ido yana jiran amsa. Topa Yusip bashida amsar da xaibayar gashi dik dakin shisuka xubawa Ido danjin mexai ce.


Itama Ummi shitake kallo Dan batasan mexaiceba ko xai tona asiri yace itace ta ce yafadi hakan kirjinta yahau dukan hamsin hamsin. Waiyooo Allah na inaxansa kaina idan yatabbatar musu da nice silar fasawar shi yaxanyi?


Tayiwa kanta tambayar da bata dame bata, amsar ta.
Malam kayi shiru kai muke saurare? gaskiya abba banida hujja ko dalili da xance su.sukasani fasawa A.a kwai dai Naga yin hakan shi yafi mana alkairi dani da ita dakuma kuu.wannan maganar banxa ce kakeyi kaibara kaji koxaka mutu sai anyi auran nan inyaso akai gawarka gidannaka. Kema abinda xance miki ko xaki mutu sai anyi auran tunda bakinka daya sokuke kumaidamu kanan yara. Alhaji muktar ke.fadar haka cikin mugun bacinrai.
Gaba,daya farlon bawanda yayi maga Saboda sun.san halinshi inranshi yabaci be iya fishiba hatta da Alhaji Abubakar beyi maganaba..saidai yayi mai isarsa tareda jadda da musu aure bafashi Sannan sujirayi hukuncin da xai yanke akansu,,

sannan yabar gidan cikin bacinrai..
Ai"jitayi kamar taxauna taita kurma ihu sabida tsana'nin firgici bawai maganar auran ba A.a hukuncin da abba xai yanke akansu tasan halinshi bashida wasa kokadan idan yace haka to bawan,da ya isa yace ba hakaba..


Ai.dik muna funcin yana gurin ki in bake bace kika kullashi to meye xaisa Yusip cewa yafasa. Muna fukar banxa Aliyu ne ke.magana kamar xaikai mata duka tDasauri tajabaya ta cono baki kamar na tsunsu tashi yayi xaikai mata duka momy ta hanashi kya leta dik abinta dai aurene bafashi tunda iyayennan naku suka Riga furta to bama kawa sai sun daura auran Dan haka kima dena wahalar da kanki wajan tirsasa shi yace yafasa.domin nasan Yusip yana da ladabi da biyayya ba irinkiba da bata Jin Bari wadda bata San mutun cin iyakanta ba yo Allah natuba ummi ko wani daddyn ki yace xai hadaku aure da shi ai kyauimai biyayya amatsa'yin shi na mahaifi.agareki,, amma kuma sai akasin haka.nan fa mommy"itama ta rufeta danata fadan itama ta tashi tabar farlon sai akabarta daga ita sai Aliyu.dayake ta.huci jiyake kamar yayi gunduwa gunduwa da naman jikin ta dandai kawai momy ta hanashi amma dayau saita kasa bambace aduniya take ko alahira. Itakam jitake kamar tasaki fitsari a wando saboda tsa bar fargaba tasan halinshi tsaf xai iya yima ta duka tunda yaga bakowa agurin.. tashi yayi xaibar farlon.ai.ganintai kamar xai daketa aguje tayi dakinta tana haki tanashiga ta,da tsekofar tana maida nummfashi,,


“Yauda asuba bayan an I'dar sallah Alhaji muktar yafadawa limamin masallah cin da a"kawai daurin auranda daxa,A"yi dama maki Alhaji Abubakar yake dubanshi datarin tambayoyi. Nasan xakace auran waxa ayi.kabari idan mun I'dar da sainayima bayanin komai haka kuwa akayi suna idarwa.yafara yimai bayini..nayanke hukunci
Dau ra auran yarannan batare da sanin suba nafison sai bayan an"daura sai a gayamusu amma bayan xuba dafatan dai ranka Bai baciba da irin hukuncin Dana xartar akan yaranmuba?.


In.banda abinka da Ummi da Yusip ai dik "ya "yan Kane kuma kanada Iko akansu kobayan Ba Idona Duk abinda kaxar tar ai basrda saninaba.kuma ai hakanma dakai Ni yamin daidai wllh kaga sai xancan biki..aini inagama bikinan ma basai anyiba kawai in lokacin da xasu sani yayi kawai saisu tatra yanasu yanasu .sutafi can"sukara,ta.
Cewar Alhaji muktar.to and aura auren Yusip Muktar da kuma amarya bilkisu Abubakar akan sadaki dubu hamsin Wanda Alhaji Abubakar ne yabiya kudin sadakin..
Alhaji muktar yaba'yar da Goran Darin aure akabawa jama'ar dasuka samu halartar daurin auran.bayan angama komai kowanne Yakama hanyar gidansa..Kai tsaye hanyar dakin matar"sa..


Yana shiga yasa meta ta I'dar da sallah tana karatun al.kur'ani megirma saida takai Aya sannan suka shafa tare saida ta linke salla.yar sannan taxo kusada shi taxauna.ya akayine baban yara Naga saifara A.kake kowani abin. farin cikine yasamemu?bebata amasar tambayar taba sai yaminko mata goro Aa wannan Goran nameye kedai kinfiya tambaya..to wannan Goran daurin auran yarkine aure kuma Alhaji Eyy anriga da an'daura ama salla ci nikaina ban sanda maganar auran ba sai akoxo daurawa yake sanrmin kinga kuwa banida tacewa.

gaskiya ne to yanxu suyaran gayamusu xa ayi A.a karki sanarda kowanne"su..toshikenan Allah yasanya alkairi. gabadaya suka amsa da Amen nima mmn hibba nace amen..




By
MMN HIBBAT...✍🏻

MATAR YARO!!!



page (15/16)


__________________Acikin su, Babu Wanda yasan da. Maganar daurin Auren mommy ma batayi gangancin sanar"da Umme ba saboda haka Babu Wanda yasani ko Aliyu baisaniba...
Abba wato Alhaji Muktar yagama shirin sa tsaf batareda yasanar wa.kowaba
domin"kuwa yasiya musu saban gida Wanda xasu tare sannan yahada kayan lepe nagani nafada Dan A.kwati doxin yayi.Hatta da kayan abinci yaxuba musu..

To bangaran mommy ma tashiga gyara amarya Ummu baji bagani magun guna na Mata kamtashasu na matsine kawai bata, bataba,,tofa..wajan Shan magani ma sai anyi daru da ita kantasha saboda a kwai masu bauri da daci.wani xubinma saita.

tambaya.momy wannan nameye kotace mommy nifa naga,jida Shan magun guna na. Kai har.kuka takeyi wai ita ancuceta ana bata maganin da suke sa.ta tashin xuciya.wani lokacin mommy.dariya abin yake bata hummmm lallai yaro yarone.
Bakomai bane yasa mommy ta Fara bata mgn da,wuriba saboda ta fuskanci Idanun Yusip abude suke tar shiyasa ma bata hada Dana matsiba,, Jikifa yasha gyara sosai sai sheki take fatarnan tayi laushi da santsi kamar ta jarirai..ita kanta tasan ta canxa bakadanba,

Wllh koxan mutu saina auri Yusip mama kiga fa abinda yayimin akan wacca shegiyar wllh intaiwasa saina sa an haukata ko nasa asaceta Yusip nawane ni kadai Duk macan da ta kuskura ta auri mijina to karshanta mutuwa UBAIDA ce. take fadar wannan mugayan kalman...


Keyy haryanxu baki gane abinda nake man...


Keyy haryanxu baki gane abinda nake hango mikiba su maxan yanxu bakasafai asiri ke.kamasuba.dola saikina hadawa da kissa bare Yusip dake yaro mejini ajika.wanda kowace mace xata so yaxama miji A.gareta.. yanxudai bawannan ba,ma.Ina maganin da boka yabada asamai A abinci yanan na ajiye shi to yanxudai ki,tashi kiyi wanka kiyi kwalliya mekyau nikuma xanshiga kicin nadora abinci.. To Inna,,yi kwalliya mexa"ayi?

"kedai kije kiyi abinda nace miki.. tashi tayi tashiga wanka tashirya sannan taxauna xaman kwalliya. Ta kusa awa daya tana shafe shafe da goge goge..wasu kaya ta dakko riga,da wando
Kocibi Rigar berife mataba.dik ana ganin na.shanunta.."Haka,shima wandan iyakarsa guywa ko dan kwali bata dauraba gashin dokinnan yasha gyara. wani shegen takalmi me tsini ta dakko tasa Sannan takuma goga fauda..

"Kai tsaye farlo tanufa adaidai nan itama mahaifi yarta jamila tafito daga kicint tana ganinta tahau koda,ta tana kara fasa Mata kai.kaga amarya kuma uwar gida agidan Yusip.ko anso ko anki saikin xama matar Yusip India ina raye.nan danan takuma Jin kanta yakara fasuwa..gani take baya ita dik cikin Matan duniya.
"Kinga yisauri kidakko min kullin maganin gurin boka maxaki sauri fa dan lokacin dawo Warshi"yakusa..dakko maganin tai Tamika Mata kowanne filas saida ta barbade,shida maganin..suna sheka dariyar mugun ta,, hardacewa.. wllh dik randa Yusip yaxama miji na wllh saina rabashi"da ita..
"Tare suka jera Abincin akan dainin"table tana kara "ga yamata yanda xata janyo hankalinshi gareta..

7:00).yadawo daga,,Office agajiye.ko mgn ba"yasan ayimasa dan yau yasha aiki sosai ko abin cin rana baiciba. "Ya "yan cikinsa sai ihu suke.suna neman agajin gaggwa..

"Tunda ga harabar gidan"Yake jiyo wani irin kamshin Abinci aituni,yawunshi yafara tsinkewa yàna hadewa. Alla. alla yake yakarasa cikin gidan.)

"Yana shiga cikin farlon kamshin yakuma kaimai xiyara.
"Itako gwanar tana hakimce bisa kan. kujera tana ganin shigo warsa ta tashi da sauri tanamai sannu da xuwa.tareda ko karin karbar jakar hannunshi tana sakin murmushin kissa ..yayi niyyar hanata amma kuma sai yakasa.karba tai ta ajiyeta

"Tana wani karkada jiki shiko binta kawai yake da kallo mamaki..wannan waca iriyar maca,,ce dabata da kamun kai.saiwani kar"kada jiki take kamar wata yar bebi..muryarta ce tadawo da shi daga duniyar tunanin da ya. lula kaxauna mana naganka agajiye bara na xuba ma. abin,ci kaci.saika yi wanka kahuta. In kuma wan kan xakafara yi.saina hadama Ruwan.wanka.tafada"tana kashemai ido daya".shidai baice mata kanxil ba.. to tunda ka kasa mgn..
nibara na
fara xuba abin cin saika yi wanka.. nanma bai tan kamataba. Abincin tafara xubamai..mutum sai miskilan"cin tsiya hum wllh dik Randa kashigo hannuna saika dena wannan shan kamshin da kakemin. Inda waccan shegi yarce saikaita washe mata baki amma in nice saika wani hade rai. nidai fatana kaci abin cinnan.
Indai kaci shi ai an Rigada angama sai yacca nai dakai. Dik acikin ranta take wannan maganar.


Abincin taxuba mai ta sannan tajanyo kukera tadawo kusa dashi.taxauna tana wani karai raya ita daole sai taja hankalinshi. tunda ta nufoshi da filet din Abincin ayji wani irin abu yadaki kokan kanshi,dik yinwar daya kwaso ji. yayi yanemeta yarasa.. cokali tadauka danufin tabashi abin cin da kanta ai jiyayi amai ya antayomai lokaci guda."Aguje yayi hanyar dakinshi. baixame ko inaba sai toilet'Yanaxuwa. yafara ka'karin Amai.amma aman yaki fitowa saboda bakomai acikinsa... Kankaceme yagalabaita sosai. Wanka yayi sannan yaxo kwanta.yana numfar fashi sama²kamar numfashinsa xaifita.bakomai bane ya janyo hakan sai yunwar da take da wainiya da shi. gashi yakasa ta.shi. xaxxabi shima yace gashinan tafe.. nan jikinshi yahau rawar sanyi hakoransa sai gwaruwa suke. Dakyar yajan yo bargo ya lil'liba.



"Tunda yatashi yabar gurin.takasa ko motsa dan"ya tsanta saboda tsana'nin takaici bawai kincin abin"cin bane yabata mataraiba A.a"maganin'da taxuba kenan yatashi abanxa Saita rasa mexatayi. kukane ya kufce mata. meyasa banida sa'a ne Akan Yusuf. kowanne.Irin Abu na shirya masa sai"ya tsalla'ke ta meyasa.Jamila na daki tajiyo kukan yar' ta"ta daya tilo aduniya, Mekuma yafaru kike kuka ina shi Yusif din yake.?"shuritai mata dan yan"xu haushin mahai fiyar ta, ta takeji gani take dik ita taja mata da tayi abinda xatq mallakeshi ai datuni yaxama nata.. katse mata tunani tayi dacewa haba Ubaida kinaji ina magana amma kika shareni..nanama bata kalleta ba saima ta tashi tabar mata gun dakinta tawuce tana,,


kara cin al'washin ko xatayi yawo tsirara saita mallaki Yusip wllh koda mahai. fiyaarta baxata yakiba to ita xata nemi mafita da kanta..xata nemi shawarar kawarta ASMA'U tanema mata duk hanyar daxata sata shiga gidan Yusip kota halin ka, kane``kai ko kisan kaine xata aikata indai Yusip xaixama nata.. tanan wayarta ta dauka takira kawar ta,ta


Hello kina inane kixo gidanmu dan allah inanemanki Ina cikin matsala wllh"maya faru najiki haka humm kedai bari wllh ina cikin tashin hankali.nan ta kwashe"komai ta fada mata Tabdi waca me tsau tsayince wannan.. yar wacece kuma waye U"banta A'kasarnan..wace inban da


Ummi waca ummi kikenufi Ummidai yar uwasa dinnan.Wllh bana kaunar "yarin yarnan ko kadan. nandai tasanar mata irin sanda Yusip yake yiwa Ummu da irin kulawar da yake bata..A. lallai kina cikin ca kwakiya tunda kike san maso wani.. Yanxuda bana nan nayi tafiya Amma inna dawo gidanku xanfara xuwa dan wannan saikin yi. da gaske.Wllh ko ciki daya suka fito saita


rabuda.shi"karkidamu kanki' kijirayi dawo wata kawai A'kwai wani book da yakemin aiki'.aikinshi kamar yankan wuka kedai kaWai kitanadikudade masu yawa wanda xasu isa'
karki damu indai kudine
kin"san banida matsala dasu.


Okay. shikenan saina dawo din. nansukai slm. takashe wayar tana murmushin farin ciki gani take kamar tasamu Yusip A hannu.ta.

Tana ajiye wayar jamila tashigo kusa da ita taxauna batai magana"ba ita Ubaida bata cemata uffa ba.. canda dai taga bata niyyar yin magana..saitace yanxu Ubaida Akan namiji kike min haka karki manta fa ni mahai fiyarkice Kuma baxanso abinda xai cutar dake ba.. sannan ke kadai gareni.nasan kinsanda haka..


Eyy nasan da haka amma mama kina ganin Nakasa samun farin cikina Yusip shine rayuwata. Wllh indai kina sona to kinemo hanyar da xata sanya Yusip yaxama mijina inba hakaba Wllh xan barmiki gidan xamshiga duniya dan yafiyemin xaman gidannan da inxauna Inaganin Yusip da wata A'matsayin matarsa..


Jamila tagir"gixa dajin furucin "yar ta'ta sosai.saboda tasan halin kayanta tsaf.xata aikata abin da tayi niyya.. Ki kwantar da hankalinki indai Yusip ne kamar yaxama naki koda abinda na mallaka xai kare.. amma kijanye maganar barin gidannan kinji.

Nidai nagaya miki indai kinasan naxauna to ki sanyanda xakiyi dani Wllh.tana kaiwanan ta kwanta. tareda juya mata baya. To shikenan karki damu indai wannan ne.. tagama fadar haka ta fice daga dakin. Ranta bace saboda maganganunda Ubaida ta gaya mata. taji haushi sosai amma saboda gudun bacin ranta yasa bata nuna taji haushiba..


"Ban garan Ummu. kuwa.
Yau ta"tashida sanganin Yusip rabanda ta ganshi tun randa abba ya musu.fata²
bata kara ganinshiba. Haka kurum. ta tsinci kanta da san xuwa taga halin da yake ciki. jikinta yabata ba lpy. Yau kusan sati amma ace bexoba kai gaskiya da marsala..

Hijab dinta tasa dakin mommy ta shiga ta sanar mata xataje gidan su Yusip taji ko lpy kallanta kawai mommy tayi tace Adawo lpy.


Tindaga farlo farko take slm amma babu wanda ya amsa hakan yasa ta kutsa kai ciki dai dai lokacin Ubaida ta fito daga kicin daukeda filet din abin ci..jikake tasss tatass. karar fashewar abu kuma abun ma na karas.. Ashe"filet din abincin dake hannnun Ubaida neyafadi kasa yafashe. Saka makon ganin wacca take slm...

Ummu dake kokarin shigowa. taji fashewar abu.dubanta takai.. gurin. Ubaidace tsaye tana binta dawani mugun kallo mai cike da ma"a. Noni da dama..

Karasa shigowa tayi tana kokarin yin sashin Yusip. Dasauri Ubaida tasha gabanta..malama meye haka xaki wani xo kitaremin. Hanya?Ummi ce magana cikin kwanciyar hankali dan talura ubaida bata mutunci shiyasa taimata haka saboda a rabu lpy..

Ke malama dakata ya isheki haka Abinda xan gaya miki shine kifita harkar mijina in kuma ba hakaba Wllh saina sa an batar dake kinji dai na fada miki..

Cikin rashin fahimta Ummu tace waye kuma mijinki da har xanshiga harkarahi da halla malam kina batamin lokaci kiban hanya na wuce..
"Anki abaki tunda gidan bana tso honki bane dariya Ummu ta kwashe da ita..tana"yin datiyar tana nunata da yatsa..

Iya kuluwa Ubaida takulu jitake kamar ta shake ta mutu. Kowama ya huta..xagi kala² tasha shi..
Hardacewa mata waitana bin maxa Itadai tayo cikin shege shiyasa xa A'likawa Yusip ace nashine.. Ummu bata kuma bi ta kantaba tayi dakin Yusip saboda intacegaba da tsayuwa to xa'ayi batacciya shiyasa kawai ta kyaleta"

Tunda ta shiga farlon nashi tasan ba lpy ba saboda farlon A hargi"tsa yake. To ina yashiga mutumin da bayasan kaxanta ki kadan indai kanaso kaga Yusip bai rabekaba to kaxamine amma ki A"ya yaya kake shibaru wansa tab di lallai a kwai matsala. Tajima A'tsaye tana tunani kala kala'kafin ta yanke"shawarar shiga cikin dakin..
Ai saita kuma cika da mamaki saboda bedroom din ma haryafi farlon hargitsewa. Hartayi niyyar tajuya saikuma tafasa dakin tariga xagawa tana karemai kallo taxo daidai bakin bakin gadon saitaga kamar mutum ne a kwamce dqsauri takara ware Idanunta tabbas mutunne A'kwace hawa tayi ta yaye bargon Yusip tagani kwance cikin mawuya cin hali hakoran sa sai gwaruwa suke. taraxana sosai.Yusip meya sameka bakada lfy meyasa baka gayaminba?

Shida Yusip yakasa komai domin
Tunda tshigo yaji motsinta amma yakasa koda motsa danya tsansa bare yasamu yayi magana.. dan axaba"ma ko idanunsa baya iya budewa.

Dasauri ta tashi tashiga toilet ta debo ruwa tafara shafamai A fuska tanayi tana hawayan tausayinshi shafamai tayi sosai harsaida xafin xaxxabin yaragu sannan ta barshi. "Durowar dake jikin gadon tajanyo maganin xaxxabi ta ballo xatasa mai abaki ya kawar da kansa.kasha maganinnan dan Allah ko kasamu lpy tafada Idinta cikeda hawaye. kai ya kuma girgixa. Saita bata rai saboda me baxaka sha maganiba tafada fuska"a daure..
Cikin muryar marasa lpy yace banci abinciba rabona da ci abinci tunjiya da safe

"Tashitayi ta nufi farlo bakowa kicin tashiga ta kunna gas iga ta kunna gas ta ta dora maishayi. cikin mintuna kalilan tagama tafito..gafda xatashige dakinnashi..

Taji muryar jamila nacewa uban wa yabaki ixinin shigarmin kicin harkisamu damar yin girki.?Ummu taji xafin xagin mahaifinta da tayi. kuma baxata kyaleta"ba saita rama domin iyaye ba abin wasa bane.dik da a haife ta haifeta amma ita taja. Karki kuma xagarmin iya yena saboda sunfi karfin axagesu inaji inagani axagesu inyi shiru ki kiyaye hakan domin dik randa kika kuma hummm..

to mexakiyi in anxagesu. Bakomai amma xaki gani. kuma da kikecewa nashigar miki kicinn.. ko kin manta nan gidan kanin mahaifinane.yanda nake iko da gidanmu haka nanma. Kuma babu wanda ya isa yayimin iyaka da gidannan dik inda nakeso xanshiga. ttangama fadin haka ta wuce tabarta nantsaye.


"Iya kuluwa jamila ta kulu wannan yar ficiciyar yarin yarce take gaya mata wa innan bakaken magan ganun eyyy lallai sata tashi tsaye inba hakaba tanaji nata gani Xata xama yar kallo.saboda in alhaji yafadi ya mutu tofa shikenan baxata samu dukiyar da tadade tana mafarkin samuba.inaaa dolama nasan abinyi..


Shayin ta hada tamikai kin karbayayi pls kasha dan Allah ko kaji karfn jikinka kaji.tayi"juyin duniya yasha amma takisha. itama da haushi ya isheta setai xuciya ta dauki hijab dinta tayi hantar fita.
"Muryarshi taji yanacewa Ummu kiyi hakuri dan Allah karki tafi kibarni. in kikatafi yaxanyi.banida kowa bawanda xan kalla naji dadi. mahai fiyata ta tarasu. tun ina cikin tsummana. sai kuka ya kwacemai.. da gudu taxo tahaye gadon ta rungumeshi tana kuka shima yana yi.akarasa me lallashin wani acikinsu".Yusip kadena fadin haka dan allah kaji. kana da gata tunda kana da allah gamu. Kuma in momy taji wannan maganar kasa baxa taji dadiba pls kadena.. kai yadaga mata Alamun to.

"To nabaka shayin Abaki. nanma kai yadaga mata.. hannutasa tana sharemai hawaye. shima share mata nata hawayan"yake..


Saida yasha rabi sannan yace yakoshi.. sannan tabashi. maganin yasha dakinta tashiga gyaramai lungu da sako"kankaceme daki yayi fes saikamshi yake.
Ruwan wanka ta hadamai yashiga "yayi.kanya fito. taiwuf takoma farlo taxauna tana jiran fito warshi.




BAY
MMN HIBBAT..
.✍🏻




MATAR YARO!!!






page (17)



“Yana fitowa yaga batanan yasan"meyasa ta barin dakin,kai gaskiya Ummu badai kunyaba.shiyasa yake karasanta. baya gajiya da tunaninta.."Bataji motsin fitowarshiba.saidai ganinshi tayi yaxauna a kujerar da take kai.

"Yana sakar mata murmushi.itama murumshin tayi. sannan takara yimai yajiki. Dasauki tunda kinxauna dani.kallanshi tayi Emana daxu" ba guduwa kikaso"yi ba.saboda na"ki shan.shayi ko.. sunkuyar da kai tayi saboda yanda yake maganar kamar wani karamin yaro. yaron ma wanda yake bukatar shan. nono"..meye najin kunya kuma. danna fadi gaskiya. Eyyy din ta fada tana murguda dan karamin"bakinta.
Waini intambayeki mana?inajinka Allah yasa inda amsar tam"bayarka.tafa tareda kawar da kanta gefe saboda irin kallan da yake binta dashi.


Meyasameki naga kinkoma haka.Yafada yana karewa jikinta kallo?"kaifa.kafiya rainin wayo Wllh sainai tafiya tama.. ai yana jin ta ambaci tafiya sai yashiga taitai yinsa..tashitai tayi.kamar xata nan yashiga bata hakuri,tareda cewa yadena,, to dama,Itama dawasa takemai.kawai dan tasamu yadena, saboda.tunda yafara fadar haka to saidai Allah yakiyaye.. amma tsafa xai" aikata.abinda itakuma bata son yafaru.tasan indai be gadama ba yanxunnan xai iya yin komai.

To naji amma karka kara. in kuma ka'kara to baxan sakee xuwaba. Ai baxanma kuma. nansuka shiga firarsu ta "yan uwantaka Yusip dai daurewa kawai yake. dan kar Ummu tagane halin da yake ciki..


Baya son tashiga damuwa ta dalilinshi. amma harga allah.xaxxabin ya kuma dawomai kuma wannan karan ma. Jiyake kamar kashin shi xai tsage..jiyake kamar ana kwada mai guduma.


Karfe (5:00)"nayamma'dai Ummu.taimai slm ta koma gida".tana"tasanar da mommy Yusip ne ba lpy shiyasa taga.tajima bata dawo.dawuriba. To" meyasame shi Yusuf din?wllh momy.bayacin Abinci kinga yanda yakoma kuwa gaskiya yana jin jiki sosai."toAllan yabashi lfy gaba dayansu suka amsa da amen..
"Washegari da sassafe tadauki hanyar xuwa"gidan su. Yusip'tana shiga"bata tarar da kowa a farlon"ba. Da alamuma mutan gidan basu tashi daga barciba"bare ayi xan can'dora abin kari. "Karasawa tayi ta kwan kwasa kofar tasa.amma ba"a budeba. hakan yasa takara dukan kofar a karo nabiyu..
shima dai shiru.To koyafita"ne.A'a gaskiya babu inda xashi.

Da karfi takuma dukan" kofar saigashi ta bude".
wata ra'xananniyar.kara tasaki. saboda firgici bata sanda ta saki kayan A'bincin da taxo da. shiba..jijjihashi take tana kiransu nansa. Yusip dan allah

5 Comments On MATAR YARO
avatar
maryam-musa

1 year ago

Reply

Pls matar yaro complete

avatar
maryam-musa

1 year ago

Reply

Pls matar yaro complete

avatar
maryam-musa

1 year ago

Reply

Pls matar yaro complete

avatar
jamiu

1 year ago

Reply

Cikon littafin fa dan gaskiya yayi dado sosai Allah ya kara basira

avatar
munirat

1 year ago

Reply

Wow cigaban shi

Please Login or Register in order to submit comment