Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daya da rabi na dare kafin mu tafi daki mu kwanta.

Fitsarin da nake ji ne ya farkar dani sai da na wartsake na mike zaune ga mamakina mahfuz baya d'akin har Kara shafawa nayi Naga ko dai lumewa yayi a bargon da muka lulluba sai dai bargone kawai baya d'akin.

Kasa kunnena nayi naji ko dai Yana bandakin a daidai lokacin da na daga kaina Ina kallon agogo d'akin karfe biyu da minti goma Sha biyar na dare.

Mik'ewa nayi a hankali Ina mamakin Inda Mahmud yayi dan nasan baya bandaki tunda banji motsi ba.

Sai dana kunna fitilar d'akin na nufi wajen k'ofar dakin da aka dan bud'e idan har zan tab'a k'ofar ba abinda zai hana yayi Kara daga d'akin Ina Jin maganarsa hakane yasa nake so naji mai yake cewa zuciyata fal da mamaki da wa Mahfuz yake magana a tsakar daren nan ya baroni a daki ni kadai.

A hankali na samu na fito daga d'akin batare da na bari kofar tayi Kara ba, cikin sand'a na fito na nufi palon da yake akwai siririn corridor kafin a iso palon.

Hasken wayarsa kawai nake hango wa yayi rub da ciki fitilar palon a kashe.

"Nifa bana ganinki sosai wai me hakane"?

Abinda ya sauka a kunnena kenan daya bala'in fadar min da gaba har sai dana dafe cikin jikina sabida motsawar da yayi.

Ban motsa ba na tsaya Ina cigaba da Jin hirarsa da macen da nake Jin saukar muryarta a kunnena.

"Bana so na kunna haske na tashi Ameera fa Wai yanzu baka ganina"

"Rowa kawai zaki min Kisani mafarki a banza"

Dariya macen ta kyalkyale dashi Yana shirin magana bansan rike numfashina nayi ba Ina sakin numfashin yayi jifa da wayar da sauri Yana "Lubna"

Duk da jikina balain rawa yake Ina hada gumi bansan ya akayi nayi jarumtaka wajen daidaita kaina Ina "Farkawa nayi zanyi fitsari da ban ganka a d'aki ba shine na fito"

"Ooo e'e'e motsi naji a waje shine na fito naga waye har waje na fita ma"

Yace Yana in'ina ya sunkuya dan ya dauki wayarsa na juya jikina na cigaba da rawa nabi bango na koma d'akin Yana daga bayana Yana fadin Yana tunanin barayi sun adabi unguwar bance Masa komai ba na kwanta tare da Jan bargo dan har wani zazzabi naji Yana neman rufeni.

Yana kwanciya a gefena ya fara k'ok'arin jawoni idan har na hana shi rungumeni zai zargi naji maganar da yake yi da mace.

Halin da nake ciki yasa ban iya jure rungumar da yamin ba dan gani nake kamar ya manna min garwashin wuta na janye jikina banaso nayi magana sabida Zan iya fallasa halin da nake ciki bana so nayi abinda zanzo Ina nadama inaso na samu nutsuwa nayi tunani Mai kyau.

Koda na janye jikina bai Kara jawo ni ba yace tom yau bbyn bayaso a tabaki kenan ya juyamin baya tare da Jan bargo saman kansa.

Ido na zubawa bayansa Ina Jin tashin maganarsa a kunnena nifa bana ganinki sosai wai me hakane
Rowa kawai zakimin kisani mafarki a banza.

Da wa Mahfuz ke video call da tsakar daren nan har ya barni a daki ya tafi palo wacce ce ita,har yaushe Muka yi Aure da mahfuz zai fara kula Yan Mata,Anya ma mahfuz dina ne wanan ko dai mafarki nake yi na mitsini kaina wai dan na tabbatar da ba mafarki nake ba.

Zuciyata wani irin zafi yake min na tsananin kishi mahfuz dama Yana da budurwa duk soyayyar Nan da yake min dama zai iya kula wata, mahfuz makota ma sun shaida irin kaunar da yake min.

Soyayya mai tsafta muka yi a shekara uku da muka hadu dashi,naje banki zan bude acct shi kuma anan yake aiki,tun ban dauki soyayyarsa da wani mahimmanci ba har sai da ya samu matsuguni a zuciyata,ba Wanda baisani dashi ba a cikin dangina haka ma danginsa,kawayena Kan roki Allah ya basu irin Mahfuz sabida yanda baya iya b'oye san da yake min a gaban kowa, nida kawayena mun Sha hada Kai mu siyi layi dan mu gwada shi,Yana Jin muryar mace zai kashe dan kafin muyi aure Ina balain saka kaina a matan da suka yi sa'a da dace samun nagartace kamar mahfuz ban fuskanci wani matsala ba har mukayi aure zan Kuma iya shaidarsa dan ba abinda yake boye min,a gurin mahaifiyarsa Hajiya Ammi kawai nake ganin ban wani samu karbuwa ba duk da da yawa ance haka take bata fiye sakarwa sirikanta fuska ba,da na auri Mahfuz sai na fuskanci idan kina so ta sakar Miki fuska ki bata abin duniya a ranar zata sakar Miki fuska na Kuma ji halayenta a wajen matar yayyen mahfuz Inda Suka ce Kar na sake duk wani abu da zai hadani da Mahfuz nace Zan Kai kararsa wajen mahaifiyarsa tsana zan janyowa kaina dan bata san laifin yayanta ko kad'an.

Daga aurena da mahfuz zuwa yanzu ban wani fuskanci matsala ba duk da kyautata min da yake Yi a waje da bambanci a yanzu da muka yi aure, dama can ba soyayar kudi muka yi ba shiyasa Koda muka yi aure ba wani kudi yake bani ba nima ban damu ba bansani ba ko dan ban Dade bane Zan bukaci kudi a gaba kayan abinci dan abinda bazaa rasa ba ban Kuma damu ba.

Zuciyata suya kawai take bacci ya kauracewa idona zuciyata nata sak'a min na tashe shi na tambaye shi da wa yake waya,wata zuciya.kuma na hanani akan nabi komai a hankali.

Kiran sallah asuba a kunnena dama Ina rigashi tashi sallah ni nake tashinsa.

Haushinsa da nakeji yasa ban tashe shi ba naje.na daura alwala inaga motsin rufe k'ofar bandakin ne ya tashe shi.

Koda ya mike Yana Hamma yace "Da ban tashi ba,bazaki tasheni ba kenan"?

Ban ma iya bashi amsa ba bama naso nayi magana dan wani abu ne ya tokareni a mak'oshi.

Banida burin daya wuce ya tafi massallaci na dan bincike wayarsa dan na tabbatar da zargina.

Sai dai yana fitowa daga bandaki ya zura wayarsa a jallabiyarsa yayi ficewarsa.

Zuwa yanzu zargin mahfuz nada budurwa ya tabbata dan a kwanakin nan yafara haka,amma baya fita da wayarsa har password dinsa nasani dan sunana ne.

Ina zaune ne kawai akan sallaya zuciyata fal da tunanin da mamakin mahfuz dana d'auko so da yarda na dora masa.

Mahfuz ba mutum bane da idan yaje massallaci Yake dadewa sai gashi har gari ya fara haske bai dawo gidan ba.

Tuni wani irin kishi ya turnike ni jikina har rawa Yake.

Har zan fita waje na koma dakina na dauki wayata tare da bin umarnin zuciya ta akan na gwada Kiran wayarsa naji ko dai wayar yake.

Ina kuwa kira ya nuna call waiting Wanda hakan ya kara saka kirjina nauyi sabida kishi ban hakura ba na cigaba da kira dan idan har ya daukeni da mahimmaci ya Kamata ace ya dauki wayata tunda nasan dole zai ga kirana sai dai bai dauka ba nima ban fasa Kira ba nasan bazai wuce layin unguwar ba dan gida uku ne tsakanin mu da massallaci da hijabin jikina na fita waje wayata Kare a kunne na a dakalin gidan makociyata na hangoshi a zaune.

Yana ganina ya katse wayar tare da mik'ewa tsananin bacin rai yasa tun kafin ya iso nace "Mahfuz da wa kake waya"?

Murmushi ya sakar min Yana da Abdul nake waya Mana

Katse shi nayi a dan tsawace Ina "Wlh karyane Mahfuz da mace kake waya bada Abdul kake waya ba"

"Ni nake miki karyar"?

Yace Yana nuna kirjinsa fuskarsa ta sauya daga murmushi zuwa bacin rai

"Ai nasan karyar ne mahfuz dan idan da Abdul zaka yi waya bazaka fito waje kayi wayar ba, jiya ai naji duk hirar da kake yi da budurwar ko zaka rantse ba da budurwa kake wayar ba,Mahfuz wacece ita?dudu yaushe muka yi aure da har wata zata fara d'auke maka hankali jiya har ka barni a daki ka fito Palo Kuna video call har kana ce wa zata saka kayi mafarki a banza"?

Dogon tsaki yaja ya ratsa ta gefena ya Shige ciki na juya da sauri raina na balain suya daki ya nufa nabi bayansa Ina cigaba da tambayar sa da wa yake waya amma ko kallona baiyi.

Takaici yasa na fashe da kuka Ina "Mahfuz wacece ita mai na maka da zaka sakamin da cin Amana"?

Banza ya bawa ajiya ta abinda bai tab'a min ba ya d'auko wayarsa ya fara lalatsawa kamar ba dashi nake magana ba,tun auren mu bamu taba hayaniya dashi ba,bamu taba dogon fada dashi ba,Mahfuz da nasani Ina d'an b'ata rai zai hau rarrashina Yana bani hakuri sai gashi yanzu kuka nake a gabansa amma ko kulani baiyi ba

Yanda ya watsar dani ya bawa banza ajiyata yasa na fusge wayar daga hannunsa a zuciye ya dago da idonsa da suka dan rine sabida b'acin rai ya mik'omin hannu Yana "Bani wayata Lubna kafin na sassab'a miki"

"Bazan bayar ba Mahfuz har sai ka Gaya min da wacce Yar iskar kake waya"

Mik'ewa yayi Yana k'ok'arin Magana naji wayar sa na vibrating a hannuna da alama ya cire ringing tone din a vibrating yasa.

Da sauri na juyo da wayar naga SR ke kira a waya a cikin Sakani na dauki wayar na Kara a kunnena yayo kaina da balain sauri a daidai lokacin dana ji muryar budurwar da bazan tab'a mantawa ba a rayuwata wacce ta watsa min farincikina ta kusa zautar dani.

"Sugar lafiya kuwa naji ka katse wayar"

Maganar daya fito a bakinta kenan

"Allah ya tsine Miki shegiya kwartuwa"


Ihu na saka sakamakon murd'emin hannu da yayi ya fusge wayar a hannuna Yana "Ke wacce irin wawiya ce mara hankali kinsan wacce kike zaginta"?

"Nice wawiya mara hankali sabida na zagi budurwar ka mahfuz"?

Nace Ina nuna kaina hawaye mai zafi ya hau zubomin yaja dogon tsaki ya nufi wajen wadrobe din kayansa ya fito da kanan kaya hawaye kawai nake Ina kallonsa har ya gama canza kayan jikinsa ko kallona baiyi ba ya fice daga d'akin.

Rawar da jikina keyi yasa na zube akan gwiwa ta na cigaba da kuka Ina tunanin ko dai mahfuz ba'a hayyacinsa yake ba har wani dumm na ringa ji a kunnena dana tuna sunan da Yar iskar ta Kira mahfuz dashi Sugar....

*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀️

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee


Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166
[6/29, 7:53 AM] Khadija Candy: *BUDURWAR MIJINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F.*

*PAID BOOK*

*PAGE 5*

HADIZA

Kukanta taci ta koshi,duk zagin da Lubna ta mata ya hau tafasa mata zuciya,ashe dai hasashen da takeyi akan Mahfuz tsoron matarsa yake ji da gaske ne,Karo na uku kenan da Lubna ke zaginta, ta rasa ya ake yi wayar ke zuwa hannunta,duk uban wahalar nan da take sha duk dan ta samu Mahfuz ya aureta,bata San tana San shi ba sai da yayi Aure, duk da sai da Wanda ta kwalafa rai da auren wani saurayinta mustapha ya yaudareta,hakane yasa ta komawa Mahfuz,dak'yar dak'yar ta samu ya fara kulata, shine matarsa take neman hanata rawan gaban hansti, taga alamar idan har batayi da gaske ba,bazata bari Mahfuz ya aureta ba,aikuwa idan ta san wata bata san wata ba ba boka ba Mallam sai ta auri mahfuz ta wulakanta Yar iskar matarsa da sam bata ma san sunanta ba balle tasan kamaninta ta matukar tsanar matar mahfuz Kamar ta kasheta haka takeji,shi Kuma mahfuz bari taga karyar da zai Kara shara mata tun jiya yake raina Mata hankali har ace ya kasa tsawatar wa shegiyar matarsa da take zaginta idan ta kirashi.

Bakin ciki ne yasa ta kashe wayar gabad'aya dan tasan ta kafu a zuciyar mahfuz gwara ta Masa barazana akan zata hakura dashi idan yaga da gaske ne dole ya tura manya gidansu ta gaji so take kawai ta samu ta Shiga daga ciki ta fitar da lubna ma daga gidan ta bar mata mahfuz dinta.


Mahfuz

Gigicewar da yayi yasa Sam bai bi takan wayarsa ba har suka isa asibiti da lubna dake ta zunduma ihun wayo cikinta sai kuka take.

Koda suka isa ihun da lubna ke zubawa taki bari ma likita ya dubata dak'yar dak'yar aka samu tayi shiru.

Likitan ya dudubata,yanda take ihun cikinta yasa likitan yi mata allura.


Ba abinda yafi komai faranta min rai sama da zagin da nayiwa Yar iskar yarinya nan, yanda na zuba drama ba mai yarda ba Ciwon marar nake ba,dan har da kukana awar mu daya a asibiti aka sallame mu ya kashe wajen Dubu biyar a siyan magani sai yaje ya biya kudin kunshi da kitso nagani.

Koda muka isa gida yanda nake langab'ewa Ina matsar kwalla yasa bai motsa daga kusa dani ba sai aikin yimin sannu da yake.

Abincin ma sai shi ya shiga kitchen ya dora da wanan na samu na goge Kiran da tayi dazu so nake nayi ta hadasu fada.

Sai da ya bani abinci naci na koshi Ina yamutsa fuska ya bani magunguna na Sha.

Sanan naga ya dauki wayarsa yayi hanyar palo

Na riga nasan Kiranta zaiyi a waya.

Fitarsa da minti biyar sai gashi ya shigo bansani ba wayar yayi ko baiyi waya ba,Ya zauna a gefen gadon Yana matsamin kafa da hannu daya Yana latsa wayarsa da hannu daya,Sam fuskarsa ba walwala ba Kuma abinda ya shafeni addua ma nake Allah yasa ta sosoka masa Ashar wlh da wayar zai shigo hannuna text zan Mata na zazzageta.

A ranar ma ban bari ya fita waje waya ba dan kwanciya nayi a kirjinsa,ko da bacci ya fara daukana idan na tuna sai nayi sauri na kankame shi.

A ranar dai baiyi waya da ita ba duk da naga alamar idonsa biyu ba bacci yayi ba

MAHFUZ

Tunda suka dawo gida yake gwada lambar Hadeeza yake jinta a kashe,ya dubata ta WhatsApp nan ma Bata hau ba ya rasa duk Mai ke mai dadi,yasan fushi tayi sam bai so yau baije wajenta ba,dan shima ji yayi Kamar ya dade bai ganta ba,burinsa bacci ya dauki lubna ya fita waje ya kirata a waya idan yaji a kashe ya kira Ameera kanwarta,muryrta da zaiji kawai zai saka ya samu nutsuwa sai dai lubna kankame shi tayi taki barin jikinsa abu kadan sai yaga ta bud'e idonta a haka ya kwanta kamar yayi kuka baccin Kuma yak'i daukarsa.

Allah Allah yake gari ya waye idan ya fita massallaci ya kirata a waya.

Wajen tara yaje gidan nasu.

Kiran sallahr asuba a kunnensa hakane yasa ya mik'e da sauri ya fada bandaki ya daura alwala a daidai lokacin da Lubna ta mik'e zaune itama tana yamutsa fuska

"sannu ya jikin naki"?

"Wlh har yanzu ciwo yake min ga kaina Kamar ya rabe gida biyu dan Allah ka zauna kaja mu sallah ba sai kaje massallaci ba"

"Haba Lubna jiya ma fa banje massallaci ba ai ana iddar wa zan dawo bari naje"

Yace da sauri tare da yin waje ya jefa wayarsa a aljihunsa.

Na tabe baki dan nasan Kiranta zaiyi a waya,yau ma bazan bari yaje ko'ina ba

Sai dai mayyar taci kanta,na tsaya ma Ina neman dorawa kaina hawan jini bayan ga hanyoyi nan da Zan bi wajen rabasu,yanzu wayarsa ta kara zuwa hannuna lambarta zan d'auka

Bai dawo gidan ba sai wajen shidda da rabi.

Daga yanda naga fuskarsa ba walwala nasan ko bai samu yin waya da ita ba ko Kuma ta zazzage shi Kamar yanda nake fata da Addu'a.


Ban koma bacci ba na dafe marata na fara wash wash,ya dafe kansa Yana "Lubna wanan wane irin ciwon Mara ne"

Ban bashi amsa ba na hau matsar kwalla.

Mahfuz kamar ya sa kuka dan bakin ciki,dan Yana ta Kiran Hadeeza a waya bata d'auka ba,karshe sai text tayi Masa da Allah ya hada kowa da rabonsa bazata iya ba tunda matarsa ke controlling dinsa.

Ya Kira dan ya bata hakuri Sam taki dagawa,bashida burin daya wuce tara yayi yaje gidan nasu.

Sam bazai iya hakura da Hadeeza ba Yana jinta a ransa ba abinda yake Balain so da ita sama da shagwabarta ko ba'a fada ba yasan idan ya mallaketa zai Sha soyayya sai gashi yau ma Lubna na neman hana shi fita.

magungunan ta ya d'auko mata ya siyo kayan shayi ya hada mata.

Sai dai Koda ta Sha bata fasa ihun ciwo mara ba,Yana ji Yana gani Lubna ta dabaibaye shi bai samu ya fita ba a ranar.

Hadeeza kuwa ta Kara cika tayi fam tana ganin wulakanci mahfuz din ke san yi Mata ta dauka da ta Masa text din zai zo gidansu da sassafe sai dai ko keyarsa bata gani ba.

Sam ba walwala a fuskar mahfuz har wani tsawa tsawa yake min idan zaiyi magana hannunsa manne da wayarsa nima bakin cikin duk wanan abun akan wata can a waje ya keyi dan kawai bai samu fita wajenta ba,har mamaki yake bani wlh bantab'a zaton haka daga wajen sa ba,
banga ta Zama ba ko Ina so ko bana so dole gobe zai fita Kuma yaje gidan nasu sai dai Allah ya kawomin mafita.

Daddaren ma ban bashi space ba haka.na manne Masa banga Kuma alamar zai fita waje waya ba sai tsaki da nakeji yanayi akai akai.


Washegari kuwa da sassafe ya fice daga gidan kamar akan Kaya yake mahfuz da ni nake tilasta.masa fita sabida kar ya makara sai gashi yau wata ta d'auke masa hankali koma wacce yarinya nan ban yafe mata ba na share hawayen daya zubomin na dauki wayata dan na Kira Mahaifiyata ita kawai zan Kira na samu kwanciyar hankali dan nasan zata bani shawarwari masu kyau.

Mahfuz

Dak'yar ya samu Hadeeza ta fito dan sai da yayi ta turawa gidansu Tama k'i d'aukar wayarsa.

Koda ta fito shi kadai ya hau maganar sa Yana bata hakurin dalilin dayasa bata ganshi ba Lubna ce bata da lafiya kwanan su biyu a asibiti bada gangan yak'i zuwa ba

Sai a lokacin Hadeeza ta kalleshi idonta cike da kwalla tana "Mahfuz Ina kaunarka amma ya zama dole na hakura da Kai dan na riga da nasan b'atamin lokaci kake,wlh bazaka iya Aurena ba,bazaka iya rik'e Mata biyu ba,dan kana balain tsoron matarka mahfuz zagi da cin mutunci haka ta zuba min sau uku kenan tana zagina da iyayena har karuwa tace min idan har bata da lafiya zata zageni ne"?

"Wlh da gaske Lubna bata da lafiya ko dai wata ce ta kiraki ta zageki matar da bata da lafiya taya har zata kiraki ta zageki"?

"Hmm Mahfuz kenan karya Zan Mata kenan wlh Azeem bamu dade da waya da kai ba na sake kiranka ta d'auka ta hau zazzagina har da cemin Kai ba sona kake ba,na like ma Ina ta dafa maka abinci Kamar wata matarka"

"Ikon Allah Mahfuz yace tare da d'auko wayarsa ta Shiga call log na ranar asabar din sai dai Sam bai ga Kiran Hadeeza ba dan suna waya yake goge lambar yanzu ya haddace lambar baiyi saving a wayarsa ba har wane lokaci Lubna ta daga wayar tayi zagin bayan yazo fita ta fara ciwon maran

"Wlh Kinga banga Kiran naki ba"


"To na mata karya Mahfuz"

"Ba haka bane bance kinyi karya ba amma kiyi hakuri dan Allah hakan bazata sake faruwa ba insha Allahu"


Dak'yar dak'yar ya samu Hadeeza ta hakura Inda yace Mata ta daina kiransa ta bari ya ringa kiranta da kansa gudun sake faruwan hakan da haka Suka rabu akan zata aika Masa abincin Rana,dan ba karya Yana Jin dadin abincin ta sosai.


Yana isa office Kiran lubna na shigo wa wayarsa sai daya zauna ya daga wayar yana tunanin ko wani matsalar ne ya taso,ga mamakinsa Yana dauka lubna tambayar sa tayi ko yaje office lafiya dalilin dayasa ta Kira kenan.

Murmushi ya saki Suka dan tab'a hira da ita kafin ta Masa sallama.

Yana kashewa ta turo Masa kalamai masu balain Dadi ya hau mamakin Kira da text din da ta masa bata Saba da Masa hakan ba.


LUBNA

Shawarwarin mahaifiyata na dauka,na zage damara wajen San na dawo da hankalin mijina kaina,hakane yasa muna gama waya da ita na kirashi a waya naji ya Isa office d'insa kalau.na Kara da Masa text dan mahaifiyata tace na dage da haka,da rana ma sai da na kirashi na sake Masa text Inda ya hau tsokana ta Wai ko dai soyayayar ce yau ta motsa min.


Murmushi kawai nayi nace Masa ee.

Tunda ga lokacin ban Kara ganin tsinaniyar na kiransa ba,har wayarsa na bincika daya shiga bandaki dan naga ko zan samu lambarta,sai dai na gama dube dubena banga lambarta ba.

Ba karamin danne zuciyata nake ba dan Yana yawan fita wayar daren Koda kuwa a kirjinsa nake zai kwantar dani ya fita.

Na rasa mai yake nema a wajen wata,nasan da kunya yanzu ya ce zai Aure ko shekara biyu ban rufa ba.

A cikin wanan yanayin cikina ya Shiga wata na tara dama mun riga da munyi dashi Ina shiga watan haihuwa na zan koma gida har sai na haihu,dan sai na fi samun kulawa a wajen mahaifiyata tunda haihuwa farine,ji nayi Kamar na fasa tafiya gida dan nasan yanzu mahfuz zai baje kolinsa wajen waya da budurwarsa a baya yakan ce jina kawai yake bazan je gida wanka ba,sai gashi shine Kan gaba wajen hada min kayana.

Ko da nayiwa mahaifiyata magana fada ta rufeni dashi akan na fiye kishi na watsar da komai na ringa kyautata wa mijina zato.

Da haka na tattara na koma gidan mu amma hankalina na wajen mahfuz,haka zuciyata zata tayimin sake sake akan Yana can Yana waya ko ya tafi zance take Zan kirashi a waya tunda bana nan dani.ya Kamata ya ringa hirar.

Muna cikin wayar ba dadewa zaice min zai kwanta bacci yake ji.

Bayan Yan mintina idan na kirashi zanji alamar Yana waya haka.zan cika fam.idan ya biyo Kiran sai yacemin da Wani yake waya.

Mahfuz

Tafiyar lubna gida haihuwa ba karamin Dadi yaji ba dan yanzu kullum Yana gidansu Hadeeza anan yake cin na safe rana da dare,haka ya bude Mata bakin Aljihu.

Waya kuwa idan suka fara kamar bazasu rabu ba.

Duk da yakan ware lokacin da zaiyi waya da lubna gudun zargi.

A haka lubna ta samu sati biyu da komawa gida.

A yau daya kasance weekend ya Yanke ya dan wanke kayansa,ya gyara gidan inyaso yau yaje wa lubnar da ta dage akan yau a gidansu take so ya wuni ta ajiye Mai abinci yau ma zizilewa Hadeeza yake dan baya so tace masa yazo.

Ya gama wanki kenan Yana cikin gyara gidan sai ga Kiran Hadeeza a wayarsa.

Abin mopping din ya ajiye ya daga wayar "lek'o waje"

Shine kawai abinda tace tare da kashe wayar


Wayar yabi da kallo cikin mamaki kafin yayi wajen Yana lekawa waje ya hango ta a machine mai kafa uku taci kwalliya tayi kyau

Wajenta ya Karasa Yana "Kai Ina zakije haka wai dama kin san gidana"


Murmushi ta sakar Masa tana "idan inasan abu dagaske nakesan abun ka gama wankin ne ga abinci na kawo ma kasan bazan bari ka zauna da yunwa ba"

Mahfuz kasa ma magana yayi ta sauko da basket din abincin tana "Wai

Please Login or Register in order to submit comment