Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka?Mahfuz jiya baka san a ya na kwana ba amma ka kira wacce ba matarka ba dan kaji lafiyarta Kuma har zaka biya ka ganta kafin kaje wajen aiki, Mahfuz Kaine kamin laifi Ina gefenka ka fita Palo dan kayi waya da mace dan na tambayeka da wa kake waya ka rufeni da fada ka kirani wawiya mara hankali laifine dan nayi kishin ka har yaushe muka yi auren da zaka min haka?Ina duk alkawarikan da kayi min a baya Koda zaka kula mace mahfuz bazaka kwantar min da hankali ko dan cikin jikina ba? kayimin adalci kenan"?

Na karashe hawaye na zubomin

"Lubna kina da matsala shikenan dan kinji.ina waya da mace sai ta zama budurwa ta,kinsan ya muke da ita da zaki zageta ne?wajen aikinmu daya da ita kuma ba komai a tsakanina da ita sai Yar tsokana amma sabida balai kin dorawa kanki kishi,har kina Neman zagina,wane bayani kikeso na miki?

Mamakin maganar sa ya sa na kasa motsawa na zuba Masa Ido har ni zai cewa ba budurwarsa bace shi kuwa ganin ban magana ba yace "ba wani abu a tsakanina da ita ke kikesan ki dorawa kanki abinda ba haka ba,abinda yasa jiya ban waiwayeki ba naji Haushin karyatani da kikayi bai dace na miki magana ki karyatani ba har kina neman zagina kina nufin baki yarda dani ba kenan,nidai zanje wajen aikii dan na makara daga haka ya ratsa ta gefena nabishi da ido har ya shige ko minti biyar baiyi ba ya fito daga d'akin ganin Ina hawaye Ina Kuma tsaye ban motsa ba ya iso wajen da nake tsaye yana "Kina nan a matsayin da Kika sanki a zuciyata ba Wanda ya Isa ya kwaceni a wajenki gwara ki kwantar da hankalinki daga haka ya sunkuyo yamin kiss a kumatu ya juya Yana "Sai na dawo"

Lumshe idona nayi Dana shaki kamshin turarensa kukan da nake dannewa ya kwacemin har ga Allah ni nasan Mahfuz soyayya yake yi da wata amma yake San raina min hankali Ina balain San mijina dama yarinya nan ta barni da mijina ta nemo wani nayi nadama da ban dauki lambarta a wayarsa ba.

Ban tab'a tunanin mahfuz zaimin haka ba

A daddafe nayi Sallah na dumama abincin da mahfuz baici ba naci dan yunwa nakeji.

Sai da na gyara ko'ina nayi wanka na zauna Ina tunanin hanyar da zan bi na raba mijina da SR dinan da take neman d'auke min hankalin Miji.

Kiran aminiyata farinciki rayuwata abokiyar sirrina ce ta katse min tunanin da nake mahaifiyata banida wacce tafita duk duniyar nan ba abinda nake boye mata a haka na taso sabida yanda take jana a jikinta ba Kuma Ni kadai ba haka duk kannena,koda na tashi aure ajiye kunya tayi a gefe ta karantar dani rayuwar aure da yanda zan kula da mijina.

Mahaifiyata a waye take dan nurse ce bama na iya boye mata komai.

Ina sallama na hau gaisheta bata amsa ba tace "Mai yake damunki Lubna"?

Kamar Mai jiran kiris na fashe mata da kuka.

Sai da naci kuka na na koshi bata hanani ba ba ta kashe wayar ta ba Jin na tsagaita tace "Ina jinki lubna mai yake faruwa"

Tiryan tiryan na kwashe komai na gaya mata ba abinda na cire har yanda mukayi da Sr din da bansan sunanta ba sai da na gama tsaf ta sauke ajiyar zuciya tana "Wlh bansan bakida wayo da tunani ba sai yau,Lubna waye ya gaya miki ana yiwa namiji haka,waye ya gaya miki ana fada da budurwa Miji a waje,salon ki jawowa kanki raini,daga lokacin da Kika d'auko wanan hanyar kin kashe kanki da kanki ai komai dan wayo ne da dabara wlh na raina wa wayon ki Lubna,ai kiyi fushi da mijinki ko kiyi gaba dashi dan kin gano Yana da budurwa ba shine mafita ba dan kin nisanta kanki daga wajensa ne kin kusanta shi da budurwar tasa dan su maza haka suke Abu kad'an ka d'auke musu hankali,daga lokacin da Kika fara wanan haukar fita zaki nayi a zuciyarsa ya fara ganin aibunki,waccen kuwa dama burinta ta samu ta kwace shi, karki sake wanan gangancin yanzu damara zaki daura ki jawo mijinki jikinki cikin kirsa ki rabashi da wancan yarinya cikin ruwan sanyi,ki rubanya kyautatawarki a gare shi.

Ai ke mijinki ma Yana shakarki tunda a boye yake Mata waya kinsan akwai mazan da agaban matansu zasu yi wayar sai dai ta hadiyi zuciya ta mutu.

Ki nesanta kanki da tab'a wayarsa ko da Kinga an turo masa text an Kira karki sake ki nuna Masa kingani cikin salo zaki rabashi da ita, kiringa kai zuciyarki nesa kishi hauka yake sawa da tarin nadama, kifita a zuciyarsa yaji ma gwara yayi auren kawai tunda kin k'i ki kwantar masa da hankali,ba dai text take tura masa ba kema sai ki dage wajen tura masa,Yana fita ki kirasa kiji lafiyarsa sau uku kafin ya dawo anan zaki ga hankalinsa ya fara rabuwa gida biyu har kiyi nasarar dauke masa hankali akan wacce yarinya ki fito da salo salo na soyayya da bai sanki dashi ba kiga ikon Allah"

Sai da muka shafe awa daya mahaifiyata na bani shawara na Kuma ji dadin shawarawarin da ta bani duk da ba k'aramin dauriya zanyi ba dan Ina da tsananin kishi bana iya controlling kaina idan ya motsa min.

Koda muka gama waya wacce take min lalle na Kira akan tazo tamin na Sha damara dawo da hankalin mahfuz kaina insha Allahu sai na raba shi da SR dinan


MAHFUZ

Allah Allah yake ya isa gidansu Hadeeza dan ya bata hakuri tunda ya fito daga gida yake kiranta a waya taki d'aukar wayarsa.

Koda ya iso k'ofar gidansu ya cigaba da kiranta a waya bata dauka ba sai da ya mata text akan ya iso Yana waje ta fito Yana jiranta.

Sai da aka kwashi mintuna wajen goma Kafin ya fara shako kamshin turarenta daya saka shi lumshe Ido ya bud'e Idonsa a hankali ya zuba Mata tana daga bakin k'ofa a tsaye ta harde hannayenta a kirjinta ta had'e Rai......



*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀️

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee


Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166
[6/29, 7:54 AM] Khadija Candy: *BUDURWAR MIJINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F.*

*PAID BOOK*

*PAGE 6*

Mahfuz duk kasa sakin jikinsa yayi Kamar Mara gaskiya sai yake Jin Kamar Lubna zata iya fadowa gidan.

Hadeeza kuwa ko a jikinta ta zage ta gama mopping ta fara goge kayan kallon sai ce mata yake ta barshi amma fir tak'i har sai da ta gama tsaf ta koma ta zauna tana "da akwai wuta har guga zan maka"

Murmushi ya sakar mata Yana "haba dai wankin ma bayarwa nake Mai wankin ne baya gari"

Tana k'ok'arin Magana wayarsa ta fara ringing gabansa ne ya Yanke ya fadi daya ga Lubna ke kiransa.

Mikewa yayi da sauri yayi hanyar d'aki ya kalli Hadeeza data kura Masa Ido Yana "Ina zuwa"

Yana shiga d'akin tayi sauri ta mik'e ta leka k'ofar da ta gani,ganin kitchen ne yasa ta tab'e baki ta leka daya d'akin da ke bud'e ta daga labulen nan ma ta tab'e baki tana "ko kayan kirki.ma Babu a gidan da sannu Zan shigo kifita insha Allahu"

Tayi sauri ta koma ta zauna ta cigaba da karewa palon kallo,Sam palon lubnar bai wani burgeta ba kayan lubnar ma duk ba masu tsada bane da zasu daga mata hankali.

Rigar jikinta ta kara gyarawa na fulaninta ya fito ta saman riga sosai,dan so take ta rikita mahfuz yayi ya fito ya aureta.

Da zata samu yanda take so da lubna ma kafin ta dawo daga haihuwa zata zo ta tarar da sunyi aure da mahfuz har ta tare,sai dai ta rasa mai yasa mahfuz ya kasa motsawa duk gani take tsoron lubna yake,so take ma taga hoton lubnar amma babu ko daya data gani a palon,wayar mahfuz Kuma akwai password a wajen hotunan,da alama shegiyar matarsa ce ta kirashi ya wani shige daki,take taji ranta ya fara b'aci ta had'e rai.

LUBNA

Kwalliya nayi sosai na gyara d'akin kanina dan nayi kewar mijina duk da yana zuwa ganina so nake yau idan yazo mu dan keb'e dashi na faranta masa rai dan nasan halin kayana hakuri kawai yake.

Da taimakon kanwata zainab na tuka Masa tuwon semo da miyar wake na jera duk a d'akin kanina.

Karfe biyu muka yi dashi akan zaizo idan ya gama wankin da yake.

Ganin biyu da rabi tayi baizo ba yasa na fara k'ok'arin kiransa a daidai lokacin da kiran makociyata ya shigo Mmn Iman"

Ina dauka tace "Lubna kin dawone"?


"Na dawo Ina"?

Shine tambayar da na mata cikin mamaki

"Ina nufin kin dawo gidanki ne"?

"Aaa Ina gidanmu mmn imam Mai zai dawo dani nida na zo gida haihuwa lafiya kuwa"

"Eee toh lafiya ba lafiya ba wata naga kamar ta Shiga gidanki sai na dauka ko kin dawone"


Kirjina wani irin bugawa yayi nace "wata kika.ga ta Shiga gidana wacce"

"Nima bansani ba wlh ko bakuwa kikayi batasan bakya nan ba"?


"Mmn Iman da idonki Kika ga mace ta shiga gidana Dan Allah jeki dubamin wacece"

Tana k'ok'arin Magana na katse wayar da sauri ko dai budurwa Mahfuz ce taje har gidana dan taga bana nan,? Yanzu mahfuz zai iya cin amanata?


Mikewa nayi da sauri hankalina ma na neman barin jikina sosai zuciyata ke sak'a min kila budurwar mijina ce taje har gidana,

Wayar Mahfuz na Kira jikina sai bari yake sai dube duben mayafi ko hijabi nake akwai tazara daga gidanmu zuwa gidana amma tabbas zanje gidana na indai har naga mace wlh tallahi sai na raba ta da numfashin ta,Yana daga wayar nace "Mahfuz kana Ina"?

"Gani a gida na shirya yanzu zan taho"

"mahfuz karya kakeyi wlh mace ka kawo min har cikin gida sabida kaga bana nan, yanzu cin fuska da cin amanar taka har ta Kai ka kawo min mace gidana Mahfuz innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"

"Kanki daya kuwa wacce mace na kawo gidan kin fara ko"

Mahfuz yace cikin dauriya numfashin sa na Neman daukewa

"Ai gani nan a waje wlh tallahi idona idonta.mahfuz sai na rabata da numfashinta.mahfuz"

Na katse wayar mahfuz yayi waje da sauri a daidai lokacin da ake buga kofar gidan

Hankali a tashe ya d'auka da gaske Lubnar ce hakane yasa yayi Kan Hadeeza aguje baiyi wata wata ba ya rike hannunta ta ya fara janta ya kaita daya d'akin ya tura ta bandakin daya d'akin nasu

"Mai haka mahfuz lafiya kuwa"?

"Shiii kiyi shiru Lubna ce ta dawo"

Cire hannunsa tayi daga bakinta tana "Toh sai me dan ta dawo ai ba wani Abu mukayi ba shine hankalinka ya tashi haka Mahfuz"

"Dan Allah kiyi shiru Hadeeza Ina zuwa karkiyi magana "

Yace tare da jawo kofar yayi waje da sauri

Lubna

Ina katse wayata Kiran makociyata na Kara shigowa wayata a daidai lokacin da na samu na tare abin hawa Ina dauka tace "gani a k'ofar gidan Ina kwankwasa wa"

"Ki taimaka min mmn Iman Ina hanya yanzu dan Allah idan har Kinga mace a gidana ki rikemin ita har sai nazo Dan Allah dan annabi wata kwartuwa yarinya ce take bibiyar mijina"


"Nidai Naga shigar mace banga fitowarta ba,ba lallai Kuma budurwar tasa bace kila bakuwa kikayi amma dai Ina kwankwasa k'ofar ba'a bud'e ba"


Katse wayar tayi adai dai lokacin da Mahfuz ya bud'e kofar ganin mmn Iman ce dan.ya Santa yasa shi sakin ajiyar zuciya take zuciyarsa ta bashi ita ta gayawa Lubna mace tazo gidan,kila taga shigar Hadeeza gidan.

Ko amsa gaisuwar da ta masa baiyi ba yace "Yanzu Mai amfanin abinda kika yi mace da cikinta kin daga mata hankali,daga gidan mu aka aiko min da abinci kanwata ce kuma tsabar munafirci shine Kika Kira lubna kika ce Mata mace tazo gidana dan Allah bakiji kunya ba da kika zo kina kwankwasa wa dan ki tabbatar toh kishigo kigani"

Yace mata a dan tsawace

Ja da baya mmn Iman tayi sam bataji dadin abinda lubna tayi mata ba

"Wlh ba ni nace Mata mace tazo ba ni muciya nazo ara ma wlh"

Tsaki Mahfuz yayi ya rufe k'ofar

Mmn Iman itama ta juya da sauri ta shige gidanta bakin ciki Kamar ya kasheta banda b'atar basira da rashin hankali irin na lubna name zata kira ma mahfuz da zuwan zatayi ai bai dace ta kira mahfuz ba.

Mahfuz kuwa Yana jikin kofa Yana ganin mmn Iman ta shige gida yayi sauri ya koma bandakin da Hadeeza take itama ta cika tayi fam,bata bari yayi magana ba ta fito daga bandakin ta fito palo ta d'auki Jakarta bata saurari mahfuz dake mata magana ba ta fice daga gidan tana zuba sauri mahfuz ya balain Kona Mata rai har mace yake tsoro haka Kamar wata uwarsa,har da kaita wani bandaki ya kulle wlh da ace ma tazo ba abinda zai hana ta fitowa ta ganta sai dai duk abinda zai faru ya faru,taya Mahfuz zai iya Kara aure Yana tsoron matarsa haka,yanzu Yana nufin ma yafi fifita matarsa akanta,duk wahalar nan da take sha akansa shine zai wani kaita bandaki ya b'oyeta sabida Yana tsoron kar matarsa ta ganta,shi daya Kamata ma ya fara gayawa matarsa tun yanzu akan aurenta zaiyi.

Da tsanin bakin ciki ta isa gida tana zuwa ta hau watsapp ta fara zanna Masa ta WhatsApp akan ta gaji da wanan kumbiya kumbiya idan har yasan ya isa da gidansa ba tsoron matarsa yake ba ya turo manya gidansu.


Mahfuz

Wani irin Ajiyar zuciya ya sauke daya ga Hadeeza ta bar gidan,shi baiga abin Jin haushi dan ya b'oyeta ba yanzu da lubna tazo ta ritsa ta mai zai ce Mata har ga Allah bai tab'a tunanin zata zo Masa har gida batare da ko tsoro ba,har mamakin confidence dinta yake,Koda ba wani Abu suke yi ba ai bai dace lubna tazo ta ga ya kawota har gida ba, duk wanan munafikar makociyar tasu ce ta jaza Masa Kuma sai ya rabata da Lubnar baiji dadin fushin da Hadeeza tayi ba ya Kamata ta fahimce shi.

Mahaukacin bugun da aka yiwa k'ofar yasa shi mik'ewa yayi waje ya ma riga da yasan lubnar ce sai daya je bakin k'ofa ya tuna bai d'auke basket din abincin ba

Yana bud'ewa lubnar ta Fada gidan tana hucci Mahfuz kuwa ya hade rai Yana "Lubna daga yau karki sake ki Kara min wanan haukar ke yanzu ko tararki akayi akace miki na kawo mace gidanan sai ki yarda kina nufin zargina kike"?


Ko ta kansa ban bi ba na ratsa gefensa nayi cikin gidan sai da na hau napep naji Kamar na rufe kaina da duka da nasani ban Kira shi a waya ba da tahowa kawai nayi da kila na ritsa Yar iskar yarinya,ai nasan dole ma kafin na dawo yasa ta gudu zuciyata ko gezau batayi ba na yarda dari bisa dari itace ta biyoshi har gida dan taga bana Nan,

Basket din abincin dana gani ya tsakiyar palon ya Kara tabbatar min da zargina abinci ta kawowa mahfuz har gidan Aurena,kila ma har iskanci sun yi,dandaga muryar ta da naji da goyata da tace ayi nasan yarinya Yar duniya ce Yar iska

Basket din na d'auka a daidai lokacin da Mahfuz ya shigo Yana cigaba da bambamin fadan zargin sa da nakeyi.

"Mahfuz yanzu dan bana Nan shine zata kawo maka abinci har gida"?

"Lubna Nagaji da wanan halin naki ni nace Miki macece ta kawo min abinci tunda kika tafi kabiru abokina yasa ake kawo min abinci wai wanan wane irin Hali Kika tsiro dashi ne?kishi hauka ne"?


Ni kadai nasan halin da nake ciki jikina har rawa yake mahfuz na san sakamin hawan jini, palona na fara karewa kallo Ina ganin kamar Zan iya ganinta ma a cikin gidan,

Ban bi ta kan masifar da yake ba na Mik'e da basket din a hannuna na Shiga dakina tamkar zan ganta a ciki Koda na Shiga ciki ma har karkashin gado na tsugunna na duba na kurawa gadona Ido naga ko an kwanta a akai shigowar mahfuz d'akin bai hanani cigaba da dube dubena ba Inda yaja wani dogon tsaki ya nufi wajen kayansa ya fara zurawa

Na zauna a gefen gadon na zuba Masa Ido hawaye na zubo min
"Mahfuz mai na maka dana cancanci haka daga wajenka, mahfuz ko aure zakayi bai Kamata ka kawo budurwar ka har cikin gidanan tazo ta gane min sirrina ba,mahfuz ni nasan ba rageka da komai ba Ina iya kokarina dan naga na faranta maka rai, a yanzu da nake d'auke da cikinka bai Kamata ka daga min hankali ba,wlh Tallahi budurwar ka tazo gidanan,mahfuz palona kamshin turare yake na daban da nida Kai mun San bamu irin wanan turaren har yanzu bamu yi shekara biyu da Aure ba,mahfuz mai kake nema a wajen wata da bani dashi,wlh tallahi yarinya da ta san Mai takeyi bazata ringa dafa maka abinci ba sabida tasan kana da aure, mahfuz bansan yarinya nan ba amma na mugun tsanarta mahfuz na yarda idan ma auren zaka Kara ka kara ka auri koma wacce Banda tsinanniyar yarinya nan da har dan bana nan zata biyoka har gida duk halin da kake ciki da ita nasani mahfuz magana ce kawai banayi,haka zamu kwanta dakai ka fita ka barni kaje kana waya da ita daddare wane irin kallo kake so tayimin shashasha ko wacce bata da matsayi a wajen mijinta?namiji shi yake fara siyawa matarsa mutunci da daraja a wajen budurwarsa,idan har kana min haka kana tunani ko Allah ya kaddara aurenka da ita bazata balain rainani ta ringa min gori ba,Kai kana tunanin idan ka auro mace irin wanan da bata damu da kana da Mata duk abinda ta ga dama shi zatayi da muyi fada da Kar muyi fada ba abinda ya dameta har kana tunanin zamu zauna lafiya idan ka aurota".


"Hmm Ke dai kin d'auko wani banzan halin da bansanki dashi ba ni nace miki Ina neman aure ne,ai ko budurwa ma zan kula kinsan dai ba haramun bane Allah ya hallata Mana mu Kara auren ballantana ni bakiji a bakina nace Miki Zan Kara aure ba,amma tunda kin dorawa kanki balain kishi har dasu zargi ke Kika jiyo kizo muje na maidaki gida"


Wani mugun kallo na watsa masa na kwanta akan gadon dan na dawo gida kenan,tunda abinda yakeso kenan na bar gidan

Ganin na share shi yasa ya fice daga d'akin a daidai lokacin da mahaifiyata ta kirani Ina dagawa na bata labarin duk abinda ya faru na kara da "tunda har dan.bana gidan take kawo Masa abinci har gida gwara na dawo gidana mummy Nagaji yarinya Nan so take ta zautar dani"

"Ke dai ba bazaki bi komai a hankali ba Zaki kuwa dorawa kanki hawan jini yanzu ke da kika je kinganta da idonki,a gaskiya kishin naki ya Miki yawa dole ki daura aure da hawan jini kuwa, nace kiringa bin komai a hankali,idan har namiji ya fara kulle kullen nan, wlh baki Isa ki Hana shi ba ko dafa kanki Zaki ringayi kina bashi Yana ci,wanan haukar kishin da kike sai dai yasa ma kifita a ransa kuyita fada dashi,yaji ya daina ma Jin dadin Zama dake a karshe ma ya fara Shirin auren amma tunda kin k'i bin shawara ta shikenan Anjima zan turo miki zainab ta zauna dake har ki haihun Allah dai ya kyauta"

Daga haka ta kashe wayar

Mahaifiyata bazata Gane halin da nake ciki ba ni nasan wanan yarinya da ta likewa mahfuz idan har banyi dagaske ba idan ni ban hanata shigowa ba fitar dani zatayi.

Badan babu kyau zubar da abinci ba naso na zubar da abincin a karshe na bawa almajirai narasa Ina Iyayenta suke suka barta take aikin dafawa saurayi lafiyayyen abinci haka,waya sani ma ko zaman kanta take Yar iskar.

Idan ferfesun mahfuz keso nima ya ringa siyowa yaga idan ban masa ba,duk bakin ciki da takaici ya cikani.

Koda na Shiga gidan mmn Iman masifa ta hau yi tana "da nasan Zaki Kira mijinki wlh Tallahi da ban kiraki ba,Haka kawai kin zubar min da mutuncina yanzu zai ringa mun kallon munafika,ke sam baki iya ba da so kike ki tabbatar ko ki kamashi,ai da baki kirashi a waya ba da muka gama waya dake sai kizo ki ritsa shi gajen hakurinki ya Miki yawa"


"Hmm mm Iman bazaki gane ba,kisa kaina a matsayin kece na kiraki nace ga budurwa ta shigar Miki gida baban iman na Nan wlh abinda nayi zakiyi"

"Hmmm ai shikenan Allah dai ya kyauta"

"Dan Allah baki ga fitowarta daga gidana ba Naga dai kayan abinci bansameta ba"

"Ya zaayi ma kisameta kiringa da kin kirashi tab a gaisheki ni banga kowa ba dan gida nayi shigowa ta da mijinki ya rufeni da masifa na hada Masa munafirci"
"Na Shiga uku mmn Iman ki kawomin agaji wlh yarinya Nan so take ta kwacemin miji ta k'arfi da yaji"

Shawarwari mmn Iman ta hau bani akan na ringa daurewa Ina danne kishina zuwan zainab kanwata yasa nayi Mata sallama muka koma gida ta dora Mana abincin dare Ina ta tunanin Inda mahfuz yayi.

Mahfuz kuwa Yana barin gidan, gidansu Hadeeza yaje.

Da isar sa ta fito fuskarta a hade

Mahfuz kuwa Sam bai lura da fuskarta ba shigar da tayi ne ya d'auke masa hankali dan indai lafiyayen namiji yaga a yanda yaga Hadeeza dole yaji ya harba

Farar doguwar riga ta sa dayaje mata har kasa kana iya hango duk undies dinta har kalarsu.

Yawu ya hadiye ya daure ya d'auke idonsa daga kirjinta Yana k'ok'arin Magana tace "Mahfuz idan har kasan kana Sona ka tura manya gidan mu ka daina b'ata mun lokaci a gaskiya Nagaji dan bazan zauna na ringa wahalar da kaina akanka alhalin ba Aurena zakayi ba,dan a yau na Kara tabbatar wa da cewar tsoron matarka kake ji bazaka ma iya Kara auren ba Ina kuwa dalili wlh indai dagaske kake.kana sona kazo ka samu babanmu idan Kuma kasan matarka tsoron ta kakeji bazata barka ka Kara aure ba tom sai mu hakura da juna dan a yau ka tsoratani".......


*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa

Please Login or Register in order to submit comment