Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko dai bakaji dadin zuwana bane"

Mahfuz keya ya sosa ya hau dube dube dan bayaso Yan unguwar suyi Masa wani fassarar,

"Kinsan Yan unguwar tamu suna da sa Ido"

"Tab Kai kake tsoron Yan unguwa ma muje"

Tace a daidai lokacin da ta bawa Mai machine d'in kudinsa

Mahfuz Kamar Wawa yayi gaba da sauri ya shige gidan.

Yana dan mamakin Hadeeza da tazo masa har gida.

Hadeeza kuwa ko a jikinta da biyu tazo gidan so take taga ya gidan ma mahfuz din yake ta dade tana Neman wanan damar daya ce Mata lubnar ta koma gida.


Suna Shiga palon ta ajiye basket din ta hau kalle kalle tana "Masha Allah gidan namu yayi kyau sai dai ya Mana kad'an nida Auntyna"

Murmushi ya sakar mata Yana "ki zauna na d'auko Miki ruwa ya nufi wajen da fridge ke,Yana d'auko ruwan yaga ta cire mayafi ta d'auko mopstick ta hau mopping....

LUBNA...



*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀️

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee


Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166
[6/29, 7:53 AM] Khadija Candy: *BUDURWAR MIJINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F.*

*PAID BOOK*

*PAGE 4*

Runtse idona kawai nayi jikina na rawa badan nayi da gaske ba ba abinda zai hanani faduwa.

Tamkar a handsfree ya saka haka nake jiyo maganar ta Cikin shagwaba da kuka

"Dan kaga Ina sanka da kaunarka kake wulakantani mahfuz mai yasa kake min haka"?

"Wlh ba haka bane haba sweetyna ya za'ayi na wulakantaki ban isa ba cajina ne ya d'auke Kuma wani uzuri ya tasomin naje gidanmu ban baro can bama sai goma na dare wlh "

"Wlh ban yarda ba kace matarka dai ta kwace wayarka ta kashe ta hana ka zuwa wajena na dade da sanin tsoranta kakeji ka sa na sha wahalar dafa maka abinci har konewa nayi a hannu"

"Ya salam dan Allah kiyi hakuri wlh ba da gangan naki zuwa ba ki hakura Mana karki sa na kasa bacci"
"Um um bazan hakura ba sai ka goyani Kuma wlh sai ka biyo gobe kacinye abincin Nan shine kawai zan hakura"

Dariya mahfuz ya kyalkyake dashi Yana "Angama sarauniyar mata idan na fara goyaki sai kin gaji gobe weekend bana fitowa da wuri wajen 10 zanzo a dumama min abincina,kinyi kitso da kunshin"?

"Emana har kwalliya nayi fa da sabon Kaya kak'i zuwa"

"Haha karki damu gobe idan nazo zan ma biya kudin kunshi da kitso amaryata kifita wajen haske na kiraki video call"


Iya abinda na iya jure ji kenan zuciyata kamar ta fado sabida tsananin bakin ciki mutumin daya gama tumurmusheni san ransa da tsohon cikina shine yanzu ya baroni a daki yake zuba soyayya da wata.

Wutar kishi kawai ke ruruwa a raina Ina Jin kamar na rufe kofar na kulle ya kwana a waje ko yaje wajenta ya kwana da bakin ciki da takaici ace kina iya k'ok'arinki akan ki kyautatawa namiji amma shi ba take yake ba zuciyarsa na wani wajen.

So nake na bar gurin amma.kafafuna sunki bani hadin kai,haka na zubawa mijina Ido,dake ta murmushi kamar an Masa bushara da gidan Aljanna har Mai nayi Masa haka,dame na rage shi da zai min irin wannan sakayyar bana ma iya gani sosai sabida hawayen daya cikemin idona.

Nasihar mahaifiyata kawai ke dawo min kaina da kyar na iya danne abinda nake ji da shaidan daya ke ingizani akan na kulle k'ofar ya kwana a waje ko naje na cakumu wuyan rigarsa na dadana Masa ashar.

Dak'yar na koma ciki Ina Shiga daki na kwanta naja bargo har saman kaina hawaye na cigaba da zubarmin zuciyata na suya,daga yanda Mahfuz ke magana da yarinya nan ba karamin so yake Mata ba har baya iya bacci idan baiji muryarta ba, wato shiyasa yanzu bai damu da yaci abincina ba? wacece yarinya nan,da take San kwace min miji,.har tana Masa shagwaba da sai ya goyata,tunani na tafi mai zurfi naga ko dai akwai ta inda na gaza har wnan yarinya ta dauke masa hankali Ina matarsa ta sunna ya baroni a daki ya fita waje dan kawai yayi waya da ita,tsafta, girki mai dadi, uwa uba iya gado,daga samun cikina na zama raguwa,Ina da kunya amma sabida kawai na faranta masa, duk da ni ba jarababiya bace har nemamsa nake da kaina,dan naji matan da suke neman miji da kansu daban suke a wajen mazajensu.

Ganin ya dade bai shigo ba yasa na daga kaina na kalli agogo karfe biyu saura minti goma,wasu matan na can rungume a kirjin mazajensu ni gani a kwance nikadai mijina na waje Yana Shan soyayya.

Motsin rufe k'ofar Palo yasa na d'ad'a Jan bargon kaina.

Ina jinsa ya shigo cikin sand'a har da lekani kafin ya kwanta a gefena a hankali ko minti goma baiyi da kwanciya ba naji Yana sakin munshari.

Haka na kwanta zuciyata kamar tayi bindiga har aka Kira sallah na Mik'e naje na daura alwala na tada Sallah.

Har na iddar bai tashi daga bacci ba ta Ina zai tashi ya kwana Yana waya.

Ko ganinsa bana so nayi hakane yasa na koma Palo, so nake na taushi zuciyata na daure Kar na nuna Masa komai a fuska nabi shawarar mahaifiyata dan tunda na taso duk shawarar da ta bani idan har nabi Ina ganin haske.

Yanda nakejin jikina nasan ko tsinke bazan iya dagawa ba nama wahalar da kaina dafa Masa abinci shi da zaije wajen budurwarsa yaci dumame.

Haka nayi kwanciya ta a dogon kujera wajen tara sai gashi ya fito Palo Yana "Uwar biyu shine yau baki tasheni nayi Sallah ba ko wlh bansan ya akayi na makara haka ba,A'a lubna lafiya kuwa ya Naga idonki a kumbure ko bakida lafiya"?

Duk maganar da yake ban daga kaina na kalleshi ba,ban tabbatar idan na Budi baki dan na masa magana ba magana zan gaya Masa ba hakane yasa ban magana ba na ja bakina na tsuke Kai kawai na gyada masa da Sunan banida lafiyar"

Kamar gaske ya nufoni da sauri ya zauna tare da jawoni jikinsa Yana tattab'a jikina.

Na janye na koma na kwanta sam bana San ganinsa duk abinan da yake na munafircine Yana da wacce yake so da kauna.

"Jiya Kuma kalau kika kwanta fa,Allah dai ya saukemin ke lafiya sannu kinji"

Yace tare da manna min kiss a goshi,nidai lumshe idona nayi, ba'a zagin miji amma na danna masa Ashar a zuciyata.

"Bari na dan gyara gidan mai zakici na dafa miki"?

Ganin ban bashi amsa ba yasa ya kara yimin sannu ya fita waje nabishi da mugun harara inajin Kamar na jawo shi na rufe shi da duka,sabida me zai nuna min kulawa alhalin Yana da wacce yake so da idan baiji muryarta ba baya iya bacci,a yanzu Kuma banida burin daya wuce na san wacce yarinya ce wanan da har ta d'auke masa hankali.

Bai dade ba ya dawo da leda a hannunsa daga kamshin nasan kosai ya siyo Ina balain san kosai da kunu,Yana cikin abincin dana fiso na karya dashi da safe kitchen ya wuce dama muna da garin kunu,da alama shi yake damawa.

Yanda yake nuna damuwarsa a kaina yasa wani bakin cikin Kara turnikeni duk abinan da yake min da wata a zuciyarsa.

Motsinsa da naji yasa nayi saurin maida idona na rufe Ina jinsa ya ajiye kofin daya damo kunun a ciki ya ajiye Yana "Lubna tashi ki karya kinji ga magungunan ki nan sai ki sha.

Ya jawo kafafuna kasa.

"Bana Jin cin komai"

"Ki daure mana kinsan baaso mace Mai ciki ta ringa wasa da abinci ko dan abin cikinta"

yace Yana kawo kosai bakina na d'auke kaina Ina "zanci anjima"

Tilasta min ya ringa yi naci nasan nacinsa akan dole nasaka hannu na fara cin kosai na karbe kofin a hannunsa dan bana San munafircin wani bani a baki.

Dadin daya min yasa na zage naci kosai baifi biyar ba na bari, na Sha maganguna na, ya dauki flasks din ya Kai kitchen,ya fito da tsintsiya ta share palon har da mopping mahfuz ba dai baya ba wajen aikin gida idan dai Yana nan, wanke wanke ne kawai bayamin.

Mai Mahfuz yake nema a wajen wata ya mace dan Allah mai na rage shi dashi daga kaina nayi na kalli agogo tara da rabi karfe goma sukayi da budurwarsa akan zaije wajenta bari naga ko zai hakura da fitar na ayyana a raina a daidai lokacin daya gama goge kayan kallon ya fara k'ok'arin nufar d'akin da a raina nasan wanka yakeso yayi ya fita.

"Kai mai zakaci"?

Na jefa mishi tambaya tare da zuba Masa Ido

"Ai zanje gida yanzu inaje can sai na karya na taho Miki da abincin rana ba sai kin wahalar da kanki wajen girki ba kiyi kwanciyarki ki huta kawai"

"Indai har dan abincin zaka fita yau weekends daya Kamata ka zauna a gida na samu kulawarka Zan daure na maka girkin ba sai kaje ko'ina ba"


"Ba iya dan na karya zan fita ba,Hajiya tace tana san ganina Yau bansan neman da take min ba"

Ko kunyar yanko karya baiyi ba na gyada kaina kawai ina Jin wani irin zafi a zuciyata bai kara cemin komai ba ya shige daki na fara tunanin.hanyar da zan bi na hana shi fita.

Tunanin daya darsu a raina yasa ni mikewa na nufi d'akin nawa Ina k'ok'arin.murda.kofar naji muryarsa Yana "Nan da minti goma Zaki gani wlh na shirya"

Murda k'ofar nayi na Shiga yaya saurin sauke wayar daga kunnesa ya cigaba da goge jikinsa murmushin da bai Kai har zuci ba na sakar Masa Ina "bari na saka Kaya nabika dama na kwana biyu banje gidan ba"


"Keda bakida lafiya Lubna Kika je can ma hayaniya kawai ta isheki kiyi kwanciyarki ki huta kawai bazan dade ba Zan dawo"

"Aaa nima inaso na dan fita na Sha iska bana san na zauna Ni kadai a gida kamar mayya"

Take naga fuskarsa ta sauya ya Kuma kasa min magana na wuce shi na nufi wajen wadrobe na bud'e dan yau zanga iya gudun ruwansa.


Bakar doguwar Riga na jawo na fara k'ok'arin sakawa a daidai lokacin da wayarsa ta hau vibrating na juya na kalleshi Ina "Kila hajiyar ce ke kiranka ka fada Mata tare zamu Zo"

"Lubna ba dadewa zanyi ba wlh yanzu zan dawo bai dace ma ki hau machine da tsohon ciki ba"


Ban ce masa komai ba na saka hijabina na fita Palo dan wlh yau kafata kafarsa inyasan wata bai San wata ba.


Mahfuz kuwa rasa yanda zaiyi da lubna yayi,ga Hadeeza sai kiransa take,bazai so yau ma yayi wa Hadeeza laifi ba, dabarar da ta fado masa hakane yasa ya shirya tsaf ya fito Kamar waya yake Yana "Wai da da Lubna ma zamu zo ok to shikenan sai kun dawo"

Ya sauke wayar daga kunnesa ya nufi wajen lubna Yana "Kinga ma hajiyar ce ta kira Wai sunje gaisuwar mutuwa sai anjima zasu dawo idan sun dawo sai muje,tunda kin hanani fita bari na fita waje na siyo abu na dawo yace da sauri Yana k'ok'arin yin waje ga wayarsa na vibrating.

Yana faramin bayani nima na shirya karyar da zanyi Yana zuwa bakin k'ofa na kwalla ihu tare da dafe cikina Ina wayyo Allah cikina Zan mutu"

A guje yayo wajena ni kuwa na cigaba da zunduma ihu.

Mahfuz ba karamin rikicewa yayi ba hakane yasa ya ajiye wayarsa akan kujera duk ya dauka da gaske ne banida lafiya

Yayi waje da gudu wai zai nemo.mana machine Mai kafa uku Yana fita tsinaniyar na kiransa a waya


Aikuwa da sauri na dauki wayar Ina dauka tace cikin shagwaba "Nagaji da jiranka fa haba Mana Nima fa ban karya ba yunwa nakeji Kai nake jira ka karaso muci tare"


"Tunda nake ban taba ganin jaka balagaza irinki ba,tom jiya mahfuz ya bani labarin irin nacin da kike Masa yace kuma.ba kaunarki yake ba dan haka kije ki nemi wani, shegiya asarariya ko kunya bakiji ba mutum da matarsa kina wahalar da rayuwarki wajen.masa girki har da sai ya goyaki yazo yaci abinci da Kika girki kamar mijinki"

Kit naji ta kashe wayar nayi saurin ajiye wayar na cigaba da zunduma ihu danaji Mahfuz ya shigo.



HADEEZA

Hawaye ne ya hau wanke Mata fuska ta zubawa wayarta ido......




*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀️

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee


Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166
[6/29, 7:53 AM] Khadija Candy: *BUDURWAR MIJINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F.*

*PAID BOOK*

*PAGE 2*


Bansan tsawon lokacin dana d'auka a durk'ushe a kasa ba,zuciyata Kamar an cinna Mata wuta ban tab'a sanin haka nake da tsananin kishi ba kawai Ina hararo irin so da kaunar da mahfuz yake gwadamin ya fara gwada wa wata,har ta d'auke Masa hankali a kaina akanta ya cemin wawiya Mara hankali waya sani ma ko zance yake zuwa wajen tsininiyar yarinya da ta Kira mahfuz da sugar,har san da yake Mata ya Kai Muna kwance ya baroni a daki ya fito Palo dan kawai yayi waya da ita.

Ko dan na samu ciki hallitar jikina ya canza yasa mahfuz ya fara ganin munina

Tunanin daya darsu a raina yasa na m'ike a hankali na nufi wajen da mudubi yake na fara karewa kaina kallo tunda ga saman goshina tare da shafa fuskata.

Tunda na samu ciki wani irin kananan pimples suka feso a fuska ta suka Sakani Muni,siririn lebbena yayi kauri.

Haka hancina da bai fiye tsini ba ya doke nasan cikin nan yasani muni ba kadan ba fari dai na Kara tunda ni fara ce.

Baza'a sakani a sahun masu tsayi da kyau sosai ba akan dai mahfuz za'a sakani a sahun masu kyau duk da mace sai ta dan yi kwalliya kyaunta ke Kara fitowa.

Kwalliya da nake yi yasa ake ganin kyauna sosai.

mutum tara yake bai cika goma ba abinda na rasa shine nono banida cikar kirji Sam idan na ga mace mai kirji sai naji Kamar na sace ko dan mahfuz da sai da muka yi aure na fahimci Yana balain san no-no,kafin na samu ciki indai Muna zaune hannunsa na saman kirjina Yana shafawa wai idan ana yawan shafa shi Yana fitowa.

Bansan Yana san nono ba sai da naga ya fara siyomin duk wani cream ko supplement akan na ringa Sha zai taimaka wajen fitomin da nono.

Ba abinda banyi amfani dashi dan nono ya girma ko dan na farantawa mahfuz rai amma abin ya gagara daya ga na fara matsawa kaina ya ce min na daina takura kaina duk da haka burina na samu nono na ya girma idan na d'auke nonon ba wani abu a jikina da baya burge mahfuz.

Idan ya dawo bashida wajen kwanciya sai a jikina ya gwadamin kaunar daya narkar dani a kogin Sansa burina bai wuce nayi abinda zan faranta Masa ba Koda bana so har na samu ciki banga canji a wajensa ba duk da mitar da nake akan cikin ya sani muni hakan na iya sawa mahfuz ya rage ji dani.

Idan na ce masa nayi muni dariya yakemin yace shi bai gani ba ai cikin nan yasa kirjina ya ciciko,bamu tab'a fushi da juna ba,bamu taba sa'insa ba,bai tab'a gaya min bak'ar magana ba sai gashi wata Yar iska tana neman juyar min da kwakwalwar miji bansan adadin tsinuwar da nayiwa macen da ta Kira shi ba.

Gajiya nayi da tsayuwa agaban mudubin na koma Kan gado na kwanta Ina sak'e sak'en yanda zan biyowa mahfuz ni nasan idan ya dawo dole ya bani hakuri dan baya iya dogon fushi dani dole na nuna Masa bacin raina na Kuma jawo shi jikina na binciki wayarsa nayi blocking din Yar iskar yarinya da take kiransa,da Wanan tunanin na samu nayi wanka abincin ma da kyar naci sabida b'acin rai,sai duba wayata nake naga ko zai kirani ko zaimin text,har watsapp na hau naga ko ya ajiyemin sako duk shiru,hakan kuwa ya Kara saka min Jin haushinsa na tanadi masifar da zan Masa idan ya dawo.

Kamar bazan yi girkin dare ba na daure na dafa jollof din shinkafa na hada Masa zobo.

Nayi kwalliya kamar yanda na Saba na zauna zaman jiransa raina a had'e.

Mahfuz bai dawo gidan ba sai goma da rabi na dare Ina Jin sa ya shigo da machine dinsa.

Ciki ciki yayi sallamar ya hade rai da leda a hannunsa bai Kuma Kalli inda nake ba.

Baki sake nabi shi da kallo har ya shige daki mamaki da bakin cikin halin ko inkular da ya nuna min ya rufeni,Mai mahfuz yake nufi dani yamin laifi ya nade tabarma da kunya a zuciye na tashi zan bishi har d'akin.

Kafin na isa d'akin na tsaya Ina bin umarnin zuciyata dana watsar dashi zai nemeni da kansa.

Da wanan tunanin na nufi daya d'akin da idan ba baki muka yi ba ba Mai kwana a ciki.

Nan na shige zuciyata na balain tafasa

Duk abinda nayi dan na samu zuciyata tayi sanyi duk a banza kofa kawai nake kallo ko zanga shigowarsa yazo bani hakuri ga yunwa da nakeji amma bana jin cin abincin.

Watsapp na hau sabida na samu nayi hira da Yan uwana da muke grp daya ko zan samu na rage bakin ciki dake Raina sai dai Ina hawa na duba mahfuz naga Yana online,wato ba abinda ya dame shi ni nasan da Yar iskar yarinya yake hira.

Ban iya hakuri ba na rubuta "Mahfuz yanzu nice abar wulakantawa a wajenka ko,"?

Bai bud'e sakon da wuri ba na fara k'ok'arin Kara rubutu naga ya bude ya turo "hmmmmm"

Bakin cikin bazai iya bani hakuri ko ya biyoni daki ba yasa na kashe data na wurgar da wayar,

Idona akan agogo har karfe daya na dare sai juyi nake ba alamar bacci zai daukeni sai tunani daya cike min zuciya tunda mukayi Aure bamu taba raba shimfida da mahfuz ba sai gashi a sanadin haduwa da wata nayi fushi dashi bai ma kalleni ba.

Hawaye kawai ke zubomin Ina tsinewa macen da ke san Shiga tsakanina da mahfuz har ta samu matsayi haka a wajen mahfuz da zai k'i nemana a kanta sai da cikina ya tsufa mahfuz ya fara daga min kafa amma ko yayane sai ya nemeni ko period nake sai na Masa dabaru har hirar na tab'a yi da wata aminiyata take cemin namijin da baya iya daga ma kafa ba karamin gamsar dashi ake ba.

Amma mahfuz yamin laifi akan Ina kishinsa bai iya bani hakuri ba,nifa yayi wa laifin nan amma shine ya kasa bani hakuri.

Har tunani na Kara yi a tsanake dan naga ko dai zaginsa nayi cikin fushi batare da nasani ba sai dai banda karya tashi da nayi na zagi tsinaniyar da ta kira ban Masa komai ba.

Zuciyata raya min kawai yake akan naje d'akin na sameshi wani b'ari na zuciyata na hanani akan shi yamin laifi shi ya Kamata ya nemeni.

Haka na kwanta zuciyata kamar tayi bindiga dan bakin ciki sai biyu da wajen rabi na dare bacci yayi awon gaba dani.

Ban tashi bude Idona ba sai wajen bakwai da minti goma Sha biyar.

Na Mik'e da sauri Ina sallati na tsani naga sallah asuba ta kubcemin.

Da balain sauri na fada bandakin na daura alwala na fito.

Sai dai banida hijabi a dakin bana san zuwa dakina naga mahfuz sai dai ya zama dole tunda ba hijabi a d'akin.

Fuskata a had'e na nufi dakina a hankali na tura k'ofar na shiga.

Bangan shi a dakin ba na dai jiyo motsinsa a bandakin da alama wanka yake.

A madadin na d'auko hijabi na wajen da na hango wayar sa a saman bedside drawer na nufa da sauri na dauki wayarsa na fita daga dakin na koma daya d'akin na saka key na zauna a saman gado hannuna sai rawa yake.

Ko da na bud'e wayar ajiyar zuciya na sauke da naga ba password.

Message dinsa na fara shiga SR da na gani ta turo message da bai bud'e ba yasa na bud'e message din jikina na balain rawa

Message ta turo.masa wajen biyar na asuba da alama reply ta Masa "Kayi hakuri sugar banga kiranka ba sai yanzu kasan jiya ban kwanta da wuri ba how was your night my love zaka biyo d'in I missed you"

Hannuna rawa kawai yake kirjina Kamar ya fado ji nake ma dakin na juya min

"Lubna ki bud'e min k'ofar nan sabida Mai zaki zo ki dauki wayata?Wai me yake damunki ne"

Najiyo mahfuz a bakin k'ofa Yana jijjiga k'ofar.

Rawar da jikina keyi yasa ban ma iya mik'ewa ba na nemo lambar SR na fara kiranta a wayarsa bugu daya ta d'auka murya can kasa tace "Sugar ka iso ne"?

"Kutumar bura ubanki tsinanniya ya iso wajen ubanki shegiya laananiya"

Kit naji ta kashe wayar na Kara kiranta bata d'auka ba,ban hakura ba na cigaba da kiranta

Mahfuz kuwa sai jijjiga kofa yake Yana kwalla min Kira akan nazo na bud'e k'ofar na bashi wayarsa

Ganin tak'i d'aukar wayata yasa na m'ike jikina na rawa naje na bud'e k'ofar mahfuz ya fado dakin da sauri ya fusge wayarsa daga hannuna idonsa ya Kada yayi jajjur cikin k'ak'ausar murya yace "Daga yau karki Kara tab'a min waya lubna wlh Kika Kara sai ranki ya b'aci kinji na fada miki"

Ya fara k'ok'arin juyawa ya bar dakin na Sha gabansa da sauri hawaye na zubomin

"mahfuz mai na maka da na cancanci haka daga wajen

Please Login or Register in order to submit comment