Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"In sha Allahu wannan takadirin ba mijin ki bane Jiddah..." ta gyada masa kai tana gyara masa kwanciyar kansa, ya lumshe ido yace "Tashi ki je kiyi wanke wanken da ta sa ki kar ta dawo kin ji" Ta goge idonta cikin sanyin murya tace "To Abbana Allah ya baka lafiya" Yace "Ameen Jiddah" Mikewa tayi ta tafi gun uban kwanukan da Hansai ta tula bakin kwararo k'uda sai fareti suke a kai, sbda yawan kwanukan sai kusan la'asar ta gama ta mike ta dau buta ta xuba ruwa jin ana kiran sllh ta ajiye inda Abbanta ke alwala ta koma kusa da shi ta durkusa tace "Abba ka daure ka tashi kayi alwala" Jin yyi shiru ta kai hannu jikinsa tace "Abba la'asar yyi...." hannunsa taga ya xamo kasa daga jikinsa, ta kamo hannun tace "Abba...." Shiru bai amsa ba, komin bacci ko rashin lafiya shi din ba me nauyin bacci bane, hakan yasa ta sake kiransa nan ma shiru, jijjigasa tayi taga dayan hannun ma ya xame, bata san lkcn da ta kwala wani ihu da karfi ba kan kace me mutane suka shigo gidan da sauri jikinta na rawa tace "Ku taimakeni Abbana yaki tashi" Wani makocinsu wanda har da shi ya shigo ya kai hannu jikinsa lkci daya ya saki salati yace "Isuhu ai rai yyi halinsa" Daga wnn Jiddah bata sake jin komai ba ta dai bude ido ta ganta kwance saman tabarma dare yyi ga mutane cike tsakar gidan. Bayan kwana uku, Jiddah na xaune tsakar gida da idonta da yyi bulu bulu ga wani rama da tayi don har sannan bata iya cin komai, Hansai sai faman yankan awara take tana cewa "Ke kadai aka ma mutuwa idan ba munafurci ba, Ita Bibalo ba ubanta ne ya rasu ba halan, munafuka kawai me neman suna, kin taso kin fita da kayan awara bakin titi ko sai na taso na nakada maki shegen duka, idan bamu yi awara ba yau ubanki xa mu kwakulo a kabari mu ci?" Hawaye kawai Jiddah take ta mike ta dau kaskon awara da coal pot da wasu kananun kayan ta fita xuwa bakin titi, Hansai tace "Ni wllh idan ba binsa kabarin kika yi ba bansan kina yi ba, bayan mutuwan da yyi ya bar ni da wahalan yi maki kayan aure duk da dai katifa da robobin kitchen kadai Allah xai hore min inyi maki, to ince me wnn wahalan da ya bar ni da shi, ina ta sintirin xuwa gidan Saude xaman makoki miji ya rasu ashe nima nawa na kan hanya xai tafi ya bar ni da wahala, to banda dai dama ya gaji da duniyar daga tashin hawan jini sai mutuwa Allah na tuba, shi dai yaji da munafurcinsa kawai dama ya gaji da duniyar ne, to ba dai ya mutun ba dai ai shkkn, yanxu ga aurenki dake ta karatowa ya gudu ya bar ni da wahala" A haka jiddah ta dawo ta sameta tana ta kumfar baki ta dau robon awaran ta fita, har sannan jiddah taki dawowa dai dai, gani take kamar mafarki take xata farka taga Abbanta bai rasu ba, har yau da aka yi uku abincin kirki ta kasa ci, don ma Iyah na tsareta sai ta sha kunu, banda tsine ma Hansai babu abinda yan anguwan ke yi ganin Jiddah bakin titi tana tuyan awara, daga mutuwar miji da kwana uku har ta ci gaba da awaranta wnn wani irin xuciya gareta, yawanci duk Jiddah ake tausayi don shkkn ta xama marainiya gaba da baya yanxu.... Abuturrab na kallon Ramlah dake yankan ma Umma Fruits yace "Umma ta ci abinci kuwa?" Ramlah tace "Aa bata wani ci ba, Amma Aunty Zainab taje gida xata yi mata tuwo yanxu" Ummi dake xaune kan farin kujera a ward din tace "Ga farfesun hanta ma da nayi mata bata ci ba" Abuturrab ya kalli Umma dake kwance da drip a hannunta yace "Umma ko a siyo maki awara?" Ta d'an yi shiru kafin a hankali tace "Toh Allah ya sa in iya ci, bana jin dadin komai a bakina" Ummi tace "Toh wannan ai dole ne Ramlah... Kawai daurewa xaki yi kici ko kadan sai kiji jikin ya maki kwari" Abuturrab yace "Toh bari in je in siyo maki yanxu" Daga haka ya fita, Slowly yake driving din har ya karasa hayi, dai dai u turn din wajen ya juya ya nemi waje yyi parking yana kallonta ta glass din motar, kanta a kasa tana juya awaran cikin man kaskon a hankali, ya sauke glass din motar yace "Ki bani awaran dari biyar" Dago kai tayi tana kallonsa, kallon idanuwanta da suka kumbura yyi, bata ce komai ba ta saka masa awaran yanda yace snn ta mike ta isa gun motar tana mika masa ledan, bai amsa ba yace "Kukan me kika yi haka??" Ta sauke idonta kasa, lkci daya xuciyarta yayi mata rauni wasu sabbin hawayen suka cika idonta, da mamaki yake kallonta, bata san lkcn da ta fashe da kuka sosai ba tace "Abbana ne ya rasu" Daga nan kuma kamar warce aka tunxura ta jingina da motar ta dinga rera masa kuka, a hankali underneath his breathe yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Kuka kawai take so painfully, ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya bude motar ya sakko ya xagayo yace "Yaushe ya rasu?" Cikin kuka sosai tace "Yau aka yi uku" Da mamaki yace "Shine kika fito suyan wannan abun" Cikin rauni tace "Baabarmu ce tace sai na fito" Dauke kansa yyi, can yace "Awaran na nawa ne gaba daya?" Ta juya ta kalli roban awaran cikin shessheka tace, wai na dubu biyar tace min" Ya girgixa kai bai ce komai ba, can ya juya ya bude motarsa, kudin da ya ciro xa ayi masa delivering eye glasses da yyi ordering online ya dauko a motar, kamar wanda ya tuna wani abu ya fasa fito da kudin a haka sai da ya saka a wani ledan turare snn ya juyo yana kallonta, har sannan kuka take sosai, ya mika mata ledan kudin yace "Gashi ki kai mata kice ance kada ki sake fitowa sai an kwana biyu" Kallon ledan ta dinga yi da yyi mata dishi dishi sbda hawayen idonta ya kamo hannunta ya mika mata ledan ya amshi ledan awaran ya saka a mota yace "Allah ya gafarta masa" daga haka ya xaga ya shiga motarsa ya tada ya bar wajen, share hawayen idonta tayi ta leka ledan taga dari biyar sababbi dal a rafe, sosai gabanta ya fadi, ta kasa kwakkwaran motsi, wani almajiri ne yace "Awaran ki na konewa" Da sauri ta juya ta sauke awaran, ta xauna xuciyarta na bugawa da karfi, muryar Hansai taji a bayanta, Hansai ta ajiye bokitin wani awaran tana cewa "Ta dari biyar ce wnn, gaba daya ya kama dubu biyar da dari biyar...." ganin awara ya kone a mai tayi tsit tana xare ido, lkci daya ta saki salati da karfi tace "Na shiga uku awaran kika kona min Jiddah???" A mugun tsorace Jiddah ta mika mata ledan kudin tace "Baabarmu wllh wani ne ya xo ya kawo min wnn wai in kai maki kar mu sake fitowa sai bayan kwana biyu...." Hansai ta karbi ledan tana duba ciki da sauri, xaro ido tayi tana kallon tulin kudin cikin ledan, lkci daya ta dinga bin anguwan da kallo, murya can kasa tace "Daga ina yake?" Jiddah ta buda hannu har sannan jikinta na rawa tace "Wllh ban sani ba" Hansai tace "Dauko jarkar man da roban awaran mu wuce gida ai ya kare ma" A haka Jiddah ta kwashi kayan awaran ta bi bayan Hansai dake tafiya da sauri da sauri, A bakin kofar dakin Hansai Jiddah ta makale tana kallonta tana ta faman kirgan kudi duk ta hada xufa, har ta gama kirgen tana xaro ido tace "Dubu dari a wannan marran ni Hansatu, Allah yyi ma bawan Allahn nan albarka, yanda ya taimaki marayu Allah ya taimakesa haka shi ma, kaiii a duniyar nan ma dai xaman wasu toshe hanyar alkhairi kawai yake, banda haka daga rasuwan Isuhu kamar daga sama Allah ya jefo bawan Allah ya bamu dubu dari cif cif, yaushe rabon inga dubu ashirin da idona ni Hansatu" Jiddah dai ta sunkuyar da kanta xuciyarta na mata xafi bata ce komai ba, Hansai tace "Maxa ki sa ruwa kiyi wanka kema ko kya ji dadin jikin ki, kinga dai mutuwar nan alkhairi ne garemu sai kiga Allah yyi ta bude mana hanyoyi iri iri, aa ni dai wllh gwara da ya bamu hanya mu san me muke ciki a duniyar, to da ya baki kudin sai yace maki me?" Cikin sanyin murya tace "Yace kar in sake fitowa sae bayan kwana biyu" Hansai ta fashe da kuka tace "To dama banda talauci me xai sa mijina ya mutu in fara awara a ranan da aka yi sadakan uku, ai sai dai talaucin dama" Ta kara rushewa da kuka tana matsar kwalla da bakin xaninta, juyawa jiddah tayi a hankali ta bar bakin kofar tana dada jin mutuwar mahaifinta kamar a mafarki wanda hakan yasa hawaye kawowa idonta.


*Still on free pages kar labari ya dauko maku dadi ku ga an datse don free pages din ba yawa ehee, u can proceed with payment sbda kawai a ci gaba ba sai an tsaya ba after free pages din, that is idan kunyi payment kenan fahh....*👌🏻
Tunda dai littafin me sunana ne wannan kunsan baxan gantalar da littafin ba, don haka kar kuyi fargaban komai ku ma baxan gantalar da xuciyoyin ku ba a gaskiya😹😹

Ping 07087865788 for payment details.💖💖 Jiddatul Khair💖💖




_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻





5.....


Alhaji Usman ne xaune parlonsa tare da Hajiya Hauwa, ya ajiye wayar hannunsa yace "Toh ke ya kika ga Madam?" Ummi tace "Aa in dai tana so babu wani matsala daga gareni sai yanda kace" Ya jinjina kai yace "Toh shi Ahmad din ne yace yana sonta?" Ummi tayi murmushi tace "Toh wannan kuma gaskiya i can't say Alhaji" Abba yace "Toh sai na fara magana da shi Ahmad din da Ramlah, don ke da kanwar nan taki na lura kanku kadai ku ka sani" Yana murmushi ya kare maganar, tayi 'yar dariya tace "Aa ai baxa ayi masu dole ba dama" Yace "Toh Allah yayi xabi mafi alkhairi dai" Ta amsa da Ameen. Bayan sati daya aka saka ranan bikin Ahmad da Ramlah wanda xa ayi bayan wata uku. Abuturrab na gidansa na Abuja tare da Ahmad da shigowarsa gidan kenan, banda kamshi bbu abinda ke tashi a gidan, ko ina so very neat and tidy kai kace da mace a gidan, Ahmad ya fito daga kitchen rike da cup din coffee yana juyawa da spoon yace "Matar gidan bata iso ba har yanxu kenan" Wani kallo Abuturrab ya jefa masa, Ahmad yyi wani dariya yace "Ka gama yaudaran yar mutane daga karshe ka samu yar sweet sixteen ka aura abun ka" Abuturrab yace "Sai ince na auri me? Ashe xaka sha mamaki kenan idan kaga na auri Aneesah" Ahmad yace "Gaskiya don ban ta6a sawa a rai cewar xaka auri Aneesan nan ba, ku dai gama holewan ku tayi auren ta kayi naka" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba ya maida hankalinsa kan TV dake aiki, Ahmad ya nemi kujera ya xauna yace "To in har da gaske sonta kake da aure kayi magana mana a saka mana rana daya gaba daya" Abuturrab that is already getting pissed up yace "You dont have to tell me what to do with my life dude..." Dariya Ahmad yyi yace "Of course, especially in a case like this" Tsaki Abuturrab yayi ya mike ya dau wayarsa ya wuce daki ya bar masa parlon... Ahmad na gama shan coffee din ya mike ya bisa xuwa dakin, xaune ya samesa da wayarsa yana magana alamar video call yake, Abuturrab ya kallesa sannan yace "Toh gashi nan ya shigo sai ku gaisa" Ahmad yace "Waye?" Abuturrab ya mika masa wayar, amsa yayi yana kallon screen din, suna hada ido ya buda baki yace "Mutanen Egypt ne dama" Bai rufe baki ba tace "Waye wannan???" Dariya yayi yana kallon uban glass da ta saka a ido fuskarta duk ya cika screen din wayar yace "To glass din kuma da kika maka haka wa ya ara maki?" Ji yayi tana cewa "Farida xo ki mayar min da fuskar Aliyu don Allah, kamar ya shiga wani kiran fuskar wani nake gani" Wata yar budurwa ce ta leko wayar ta xaro ido tace "Lahh Hajja ai Yaya Ahmad ne" Warce ta kira da Hajja tace "Kaji wani xance to ni ina ruwana da shi xa a sako min fuskarsa, ki mayar min da fuskar Aliyu nace, idan kuma baxai yiwu ba ki kashe kawai, waye kuma wani Ahmad, ni na san shi" Ahmad dake ta dariya yace "Nima ae ba saninki nayi ba kawai miko min wayar aka yi" Hajja ta sake wayar ya fadi tace "Ni dai na shiga uku, A gaskiya wannan ai walakanci ne da cin fuska, ya xan dinga magana da Aliyu fuskar wani kato ya fito, wayar taki ce ta lalace ko wa'adin da aka debar mana na magana da Aliyun ne ya kare aka sako min fuskar wani can" Farida ta ma rasa abun cewa sai dariya take, Ahmad ya katse wayar ya jefa gefen Abuturrab shi ma yana dariya, Abuturrab yyi murmushi yace "Yanxu fa take tambayar ka shine ka shigo na baka fa...."

Iyah ce tsaye kan jiddah dake ta kuka kamar an aikota, A fusace tace "Toh meye amfanin wnn shegen kukan da kike ne wai, nace ki hado tsummokaranki in sa ki mota tunda da kudin ki a hannuna ki tafi legas wajen Salame kawai" Jiddah na kuka tace "Toh Iyah idan iliyan ya hadu da ni a legas din fa? Shi ma fa a can yake aiki ai" Iyah tace "Legas din bai fi Najeriya girma ba aka ce maki, ta ina xai ganki a gari me girma haka" Shiru Jiddah tayi tana kallonta wasu hawayen na sauka fuskarta, Iyah tace "Ni dai ba ruwana ina kokarin ganin na rufa maki asiri kar a aura maki takadiri kina min gardama, hakkin makotaka fa nake son in fita, banda haka me na hada dake Jiddah?? Sannan ni ce mutum ta karshe da Allah ya ba iko nayi hirar karshe da mahaifinki kafin ya mutu, to sai in xuba ido ki tagayyara ya kullace ni duk inda yake?" Jiddah ta sauke idonta dake xuban hawaye xuciyarta yyi rauni, Iyah tace "Atoh babu ruwana wllh, ba dai gobe xata tafi kasuwar tasha siyo kayan sana'arta ba, sai ki shirya tana fita in kai ki tasha kawai, ko da tirela ne sai ki bi xuwa legas din, amma idan ba haka ba shkkn rayuwarki ta lalace idan aka aura maki Iliyasu" Iyah na kai wa nan ta tafi gun tuwonta dake kan murhu tana cewa "Na fita hakkin ki duk da ba dangin iya ba na baba, amma hakkin makotaka fa??" Jiddah dai gaba daya jikinta yyi sanyi, she is too young to even think straight for her age, hakan yasa taji gwara kawai ta gudun don gashi har an xo an sa mata rana wata daya dai dai da Iliyasu a yau.

Aunty na kallon Nafisa, cike da fada tace "Tashi ki fita ki ban waje" Ba musu Nafisar ta mike ta fita kamar xata yi kuka, Aunty ta dubi Abuturrab dake dakin yana kallonta tace "Wllh baka gansa ba Captain, ni dai ban ta6a ganin haka ba, banda yarinta da dolanci me xata yi da shi don Allah??" Abuturrab na cin Apple din hannunsa yace "Meye da shi wai Aunty?" Cike da takaici Aunty tace "Don dai sai da yamma ka dawo jiya da ka gane ma idonka...." Yace "Aa ni a garin nan ma nayi sllhn juma'ah, private jet muka biyo daga kano, sha biyu da rabi ina kaduna..." tace "To a ina ka tsaya sai bayan la'asar ka dawo gida?" Yace "Muna tare da wasu abokanmu" Aunty tace "Shi yasa, ai da ka gansa wllh... Muna xaune fa jiya da safe kamar abun arxiki tace mana wai Salis yace xai xo bayan an sakko juma'ah mu gaisa, na xata abun arxiki ne har da sa masu aiki su tayata yi masa snacks iri iri wai ashe gantalalle xata kawo mana..." Abuturrab dake ta kallonta yace "Toh meye da shi baki fada min ba har yanxu" Tace "Toh kaga Captain tun daga bakin titi da kafa ya tako har nan, ashe ko motar ma bashi da, sai kaga wani yakunannen yadin da ya sa bbu gugan arxiki, kana ganinsa dai kaga 'ya yan ya ku bayi, ni ko a raina nace ko ina wannan yarinyar ta samo mutumin nan haka, ni wllh a bakin stairs na tsaya amsa gaisuwarsa ban yarda na karaso parlon ba" Abuturrab yyi murmushi ya kai Apple dinsa baki yace "Wani sana'a yake yi?" Wani kallo ta jefa masa tace "Sana'a, wa ke ta wani sana'arsa banda abun ka, ko ka mance da wannan saying din that goes thus... The way u dress will be the way u will be addressed??" Abuturrab ya gyada kai kawai bai ce komai ba, tace "Wllh na sake ganinta tare da shi Allah sai na ji mata ciwo kowa ma ya huta, ita kuma Ummi da taya bera 6ari sai wani nan nan take da shi, tarba dai yanda kasan mutumin arxiki haka tayi ma yaron, ni ko kunya kamar in nutse wllh, Salem kuma inda ya burgeni ko kallonsa bai yi ba da ya shigo parlon kawai yyi wucewarsa daki..." Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya kyauta...." Tace "Ameen sai ka kirata and talk sense into her head... Ba ni xata kwaso ma abun kunya ba" Mikewa yayi, tayi saurin cewa "Captain ban kai ka kaje kaga filin da na siya ba ae" Yace "Xuwa gobe in sha Allah" tace "Lahadin xaka koma aikin?" Yace "Idan Allah ya yarda" Tace "Wancan satin kasa nayi maka tamarind drink baka dawo ba..." Ya shafa kansa yace "Wlh daya daga pilot din da xai yi piloting jirgi daga lagos xuwa port Harcourt bai ji dadi ba shine ni nayi, wnn satin ma ban yi niyyar dawowa ba coz i was so stressed out during the week" Tace "Gashi ko ka xo kadunan ba wani hutawa kake ba tunda ba xama kake gida ba" yyi murmushi kawai, tace "Sai kaji an sa ranan Ahmad da Ramlatu" Yace "So Abba told me" Tace "Atoh bai fi mata ba, yar uwarta ta tsaya kula ya ku bayin garin nan, Ahmad ai d'an gayu ne d'an boko ga hankali da nutsuwa duk da dai ni ba wani shiri muke da shi ba, though auren xumunci ne ma ai amma gwara hakan, Nafisa ma tace min ai tasan tsohuwar Budurwarsa Maryam islamiyyar su daya kafin ta canxa islamiyyan" Abuturrab ya nufi kofa yace "To Allah ya kyauta" Tace "Bayan an gama da na Ramlah sae a dawo naka da Aneesah ko?" Murmushi yyi yace "Allah ya kai mu lokaci" Daga haka yyi mata sallama ya fita yana duba agogon wrist dinsa, kira ne ya shigo wayarsa, ya duba ganin Aneesah ya daga ya kai kunne yace "Don't tell me har kin sauka?" Tace "God!!! Nima Don't tell me baka fito ba Captain" Ya wara manyan idanuwansa yace "Ban dade da shigowa gida ba... But in few mins time xan karaso I'm sorry" Bai jira me xata ce ba ya katse wayar ya fita ya hau motarsa.... Tafiyar minti ashirin ya kai sa train station, murmushi yyi ganin yanda ta hade rai tana tsaye daga nisa, abaya ne baki jikinta da yyi matukar amsan farin fatarta, ja da bakin lallen dake hannunta ya kara contributing wajen haduwarta a lkcn, she looks so sweet, mutane dai daya ne ke wucewa wajen basu kalleta sun sake kallonta ba, ya karasa inda take smiling, cikin soft voice dinsa yace "Sorry Baby, kinsan dole in je in gaida su Ummi da Aunty beside dole ma sai na koma gidan na dauko mota tunda ban dade da sauka ba nima...." Cike da shagwaba tace "Kasan mutane nawa suka tambayeni numbata tsayuwar da nayi nan yanxu" Yace "Sai kika basu kenan" Ta juya masa fararen idonta ta ki cewa komai, murmushi yyi ya amshi trolley din hannunta ya fara tafiya xuwa gun motarsa tana biye da shi tana kallonsa don komai yyi burgeta yake. A hankali yake driving din Aneesah dake gefensa tace "I learnt about Ahmad's engagement with Ramlah" idonsa na kan titi yace "So i heard also" Tayi kasa da murya tace "To mu kuma namu fa?" Still bai kalleta ba yace "Xa ayi" Tace "Yaushe??" yace "Am trying to put things in order first, i don't get why u are in a rush Aneesah, ba dai ni nace xan aure ki ba, meye kike damun kanki haka? Do i look like a liar or do my words sounds deceptive?" Ta kai hannunta kan nasa cikin sanyin murya tace "I just can't imagine loosing u My Captain, i just can't...." Yace "Keep ur mind at rest Neesah, i am all urs and urs alone" Yana fadin haka ya sakar mata murmushinsa dake kara narkar da xuciyarta, dai dai nan kuma ya kai layinsu Jiddah, yau bata awara a bakin titin don babu alamar ma ta fito, sai dai mutane ne cike fal a d'an layin nasu, a hankali yake driving din yana kallon cikin layin, Aneesah dake kallon direction din ita ma tace "What's happening there, ko anyi rasuwa ne?" kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Ko in sauke journalist taje ta gano mana???" Dariya tayi tace "Oops a wnn local area din xanyi journalism dina Captain? Haba this is so disgusting..." Tana magana tana yamutse fuska, shi dai bai ce komai ba yana ci gaba da driving dinsa, can gidan Kanwar babanta ya ajiyeta a unguwar sarki, bayan ya yi mata few shopping na kayan ciye ciye, ta sauka motar bayan yyi parking tana kallonsa, shi ma ya sauko ya fiddo mata da trolley dinta ya kai bakin gate din ya ajiye, ta dau ledan shopping din da yyi mata tana kallonsa bayan ya dawo cikin sanyin muryarta tace "Thank you My Captain, plss ka daure ka xo anjima da daddare mu yi hira..." Ya kashe mata ido yace "Ohk babe...." Daga haka ya shiga motarsa yyi reverse ta bi sa da kallo har ya fita layin tana sake jin wutan sonsa na ruruwa a xuciyarta. Abuturrab na komawa gida yyi parking nan kofar gidansu ya shiga ciki yyi alwala snn ya fito ya shiga masallaci don ana ta kiran magrib, bayan an idar ya fito masallacin ya shiga motarsa ya xauna yana danna wayarsa, ajiye wayan yyi yana kallon flowers dake xagaye kofar gidan nasu trying to imagine the meaning of the crowd they saw earlier a layin yarinyar nan me awara, did someone die again, tunanin hakan ya sa ya tada motarsa ya bar layin, yana isa yyi parking bakin titi ya dau nose mask dinsa a motar ya saka snn ya bude motar ya sauka, ashe da daddare sana'a ake yi sosai bakin titin layin, just like sauran layukan anguwan gaba daya, daga me soya wancan sai me soya wannan, masu siyar da gyada, rake, abubuwan ci na gargajiya dai yawa... A hankali yake tafiya cikin layin yana yatsine fuska, he is even afraid kada allergy ya je ya kamasa cos he is so sensitive to anything Filth,... har dai ya kai dai dai kofar gidan da yaron nan ya ta6a kai sa a matsayin gidansu yarinyar, tsaye yyi yana bin duk wajen da kallo, ginin block ne sai dai ko plaster babu, sannan gidan karami ne sosai, duk gidajen layin haka suke, banda gida daya da ya d'an darasu girma shi ma da kadan wato gidan Iyah, wata yarinya ce ke tafe ko takalmi bbu a kafarta, ya bi ta da kallo yace "Baby...." Juyowa tayi tana kallonsa yace "Xo in aike ki cikin gidan nan" Yarinyar da baxata wuce

2 Comments On JIDDATUL KHAIR
avatar
khadija-7-7

1 year ago

Reply

Chapter 10

avatar
surayya-2

9 months ago

Reply

Cool

Please Login or Register in order to submit comment