Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shekara shidda ba ta dawo tace "Gidansu Bibalo?" Yace "Ehh, shiga kice ana kiran me awara a ciki" Da gudu yarinyar ta shiga, babu kowa tsakar gidan don Hansai ko minti biyar ba ayi da fitarta ba, ta shiga makota, Bibalo kuma tun la'asar rabonta da gidan, yarinyar ta kutsa kai cikin dakin su Bibalo tana kallon Jiddah dake kwance ta takure waje daya kan yakunannen katifarsu da Bibalo, tace "Wai ana sallama a waje" Da sauri Jiddah ta mike xaune da idanuwanta da suka yi jajir, duk da tasan Hansai ta fita gidan don sai da ta bar mata sallahun bakar magana ma kafin ta fita amma hakan bai hana xuciyarta dinga bugawa ba jin abinda yarinyar tace, A tunaninta saurayinta ne Usman ya xo, kilan ya ji abinda ke faruwa ne, da kyar dai ta lallaba ta mike ta cire Hijab din jikinta ta dau wankakke dake a linke ta saka, sanyi take ji sosai don xaxxabi ne jikinta, ta fito dakin ta sa takalminta tana tafiya kamar iska xai kadeta ta fito kofar gidan, babu haske sosai wajen hakan yasa ta dinga kallon mutumin dake tsaye da fararen kaya ya juya baya, gani tayi ba Usman bane don wnn yafi Usman tsayi, ta bi layin da kallo tana kara tsoron kada Hansai ta dawo ta tarda ita a waje bayan an yi mata iyaka da wajen daga daxu da yamma, da kyar tace "Wa kake nema?" Sai a snn ya juyo ya sauke mask din fuskarsa yana kallonta, ta xaro ido tsoronta ya tsananta, haka xaxxabinta ma taji yana neman fin na da, don sanyi sosai ya dinga shigarta, kallonta ya shiga yi daga sama har kasa, rasa abin cewa tayi daga karshe ta jingina da bangon gidan, still looking at her yace "Baki da lafiya ne?" Ta gyada masa kai, lkci daya hawaye ya kawo idonta, bin layin ya sake yi da kallo, can yace "Baki sha magani ba?" Hawayen dake makale idonta ya silalo kasa ta girgixa masa kai tace "Babu maganin" yace "Ke da waye a cikin gidan?" Tace "Ni kadai ce, Baabarmu ta fita yanxu" Shiru yyi kamar me naxari sai kuma ya kalli inda motarsa yake yace "Akwai asibiti a nan anguwar?" Ta gyada masa kai tana nuna masa tace "A layin can gaba" Yace "Mu je" Da mamaki take kallonsa tace "Ina?" Ya wani hade rai yace "Mu tafi can din nace" ta marairaice cikin rawar murya tace "Baabarmu tace idan na sake fitowa ko nan bakin kofa sai ta kasheni wllh" Shiru yyi na few seconds kafin yace "Saboda me?" Tana share hawayen da ya ki tsaya mata tace "An sa min rana" Daga sama har kasa ya sake kallonta snn yace "Da wa?" Ta fashe da kuka tace "Da iliya" tana fadin haka kamar an tunxurata ta dinga rera kuka, yace "Ohk, amma bai san baki da lafiya bane bai kawo maki magani ba" Bata basa amsa ba sai kukan da take yi sosai, yace "Mu je" ganin ta ki motsawa ya daure fuska sosai yace "Ke kinsan daga inda nake?" Ta shiga goge idonta bata ce komai ba, yace "Mu tafi nace" A hankali ta fara goge idonta, ganin ya fara tafiya ta bi bayansa gabanta na faduwa tana waige waige har suka kusa bakin titi ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta don duk maxaunin bakin titin nan babu wanda bai santa ba, ya bude mata back seat, xuciyarta ya dinga bugawa da karfi ta tsaya tana kallonsa, ya sauke nose mask dinsa yace "Kina 6ata min lkci" A hankali tace "Baabarmu xata....." Wani kallo yyi mata yace "Nace ki shiga malama" shiga motar tayi a tsorace, ya rufe sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar, sai da ya hau saman titi yace "Ina asibitin yake?" Layi uku dake gaba da nasu ta nuna masa ya shiga layin suna isa yaga irin asibitin yyi parking yana kare ma wajen kallo, kafin yace "Nan din ne asibitin?" Kai kawai ta gyada masa, ya ja tsaki ya tada motarsa yayi reverse ya bar wajen, ta dinga kallonsa gabanta na faduwa, wani asibiti a cikin gari ya kai ta, yana parking haraban asibitin ba tare da ya juya gareta ba yace "Sauka" kalle kallen motar ta dinga yi alamar bata ma san ta ina xata bude ba, ya sauka ya xagayo ya bude motar, sauka tayi ya rufe motarsa, ganin yanda ta tsaya ya dake yace "Mu je" he sounds so pissed off, Ba musu ta bi bayansa har cikin asibitin, nan take ya yankar mata kati, ba a dau lkci ba nurse din ta sanar masa xa su iya shiga gun likita, yana daga xaune ya nuna mata office din likitan yace ta shiga ta gaya masa duk abinda ke damunta, Jiddah ta mike gabanta na faduwa tana kallonsa a hankali tace "Ai tsoro nake ji" ya hade rai a d'an tsawace yace "Tsoron likitan sbda xai cinye ki?" Sunkuyar da kanta tayi, yace "Juya ki shiga" a hankali ta juya ta nufi office din likitan da ya nuna mata, kamar me tsoron kofar ta murda ta shiga, sai a sannan ya mike ya bi bayanta xuwa cikin office din, tana xaune ta takure waje daya likitan na cewa ta kwantar da hankalinta ta nutsu, ganin ya shigo sai taji hankalinta ya kwanta, ya ja kujera ya xauna suka gaisa da likitan, likitan na kallonta yace "Me ke damun ki?" Cikin sanyin murya tace "Kai na ke min ciwo, ina jin xaxxabi, kuma ina ganin jiri...." Mikewa yayi ya dawo kusa da ita yana duba idonta da wani d'an abu kamar fitila a hannunsa, Abuturrab dai na xaune yana dubansu har likitan ya gama gwaje gwajensa snn ya koma ya xauna yana kallon Abuturrab yace "Xa ayi mata test, though symptoms din na malaria ne, but it's good ayi test din sannan kuma .... Is she ur sister?" Abuturrab ya d'an kalleta sannan a hankali yace "Yea" Likitan yace "Me ke damunta haka, yar yarinya da ita na ga Bp dinta ya hau" sake kallonta Abuturrab yyi, likitan na kallonta yace "Kina da damuwa ne 'yan mata, idan ma baxa ki gaya ma d'an uwanki ba ni ki gaya min" Sunkuyar da kanta tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta, Abuturrab yace "Dont worry Dr i will talk to her about that, ynxu dai idan ba damuwa kawai a hada mata drugs if there is need for injection ayi mata ba sai an yi mata test din ba cos i guess it will take up to 40mins kafin result din ya fito mu kuma a kan hanya muke" Likitan yace "Toh shkkn babu damuwa" daga haka ya fara rubuce rubuce yana gamawa ya mika ma Abuturrab ya amsa snn ya mike yyi masa godiya, ganin har sannan bata mike ba yace "Mu je" Mikewa tayi yana gaba tana biye da shi har suka fita office din, wajen bada allura Abuturrab ya ga abinda bai ta6a gani ba, don kememe taki yarda ta dinga rusa masu kuka a asibitin tana rokansu, hakan yasa ya koma office din likitan yasa ya rubuta magunguna kawai gaba daya ya biya bill din sannan suka fita asibitin, har sannan shesshekan kuka take, ya bude front seat ya hade rai yana kallonta a hankali ta shiga ya kulle sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver, sai da suka fita asibitin yace "Kin ci abinci?" Girgixa masa kai tayi tace "Baabarmu ta ba almajiri nawa" Ya dinga nanata sunan da ta kira a ransa, wai Baabarta, girgixa kai yyi cikin ransa still yace ba dai baabarki ba, gidan wani cin abinci ya tsaya ya siya mata abinci sai malt guda biyu da bottle water, yana shigowa motar ya ajiye mata, kallon ledan ta dinga yi, can ta bude ta ciro malts din ta ajiye gefe tace "Ban iya sha ba" Yace "Sai me?" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Tambayarki nake" a hankali tace "Ban iya shan lemo ba ni" Bai kuma ce mata komai ba, sai da suka shigo titin hayi yace "Taron me naga aka yi a layinku daxu da yamma?" Shiru tayi sai kuma ta kallesa a hankali tace "Baabarmu ce take dukana" Da mamaki yace "Saboda me?" Ta share hawayen da ya kawo idonta tace "Dama Iyah ce tace xata sa ni a motar tirela in gudu legas don kar a min aure da Iliya, shine sai na gaya ma wata kawata da muke xuwa makarantar dare tare da ita da, don gobe Iyah tace xata kai ni tasha, sai kawata taje ta gaya ma baabarta shine baabarta ta xo ta gaya ma Baabarmu, shine Baabarmu ta dinga dukana wai xata kasheni, duk aka taru a layin...." Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Shi dai sauraronta kawai yake yi, bayan few seconds yace "Wacece Ita warce tace xata sa ki mota ki tafi lagos?" Cikin rawar murya tace "Wata tsohuwa ce a layinmu ana ce mata Iyah...." Ya kalleta yace "Har yanxu xa ki tafi lagos din kenan don kar a maki auren?" Ta girgixa masa kai hawaye na sauka idonta tace "Aa baxan je ba amma xan kashe kai na" Bai ta6a expecting jin hakan daga bakinta ba, yyi parking yana kallonta da mamaki yace "Xa ki kashe kanki?" Ta gyada masa kai, yace "Da me xaki kashe kan naki?" Cikin rawar murya tace "Piya piya xan siya in sha" Bai san lkcn da ya bude baki ba yana kallonta ganin she is so damn serious, da wani expression yake kallonta ganin she is truly depressed and frustrated, tana goge hawayen dake xuba idonta tace "Dama ae Abbana ma ya tafi ya bar ni, ba sai in bi sa ba" ya kwantar da murya yace "Amma kina xuwa islamiyya kuwa?" Ta girgixa masa kai a hankali tace "Na daina tun da dadewa, tun sanda muka fara sana'a" Yace "Toh saboda xa a maki aure kike son kashe kanki?" Ta gyada masa kai, sai kuma ta hade kanta da gwiwa ta fashe da matsanancin kuka tace "Shaye shaye fa iliya ke yi, kuma har kwaya yana sha shine Babarmu take son in auresa...." Kallonta kawai yake, can yace "To wa kika ta6a ganin ya kashe kansa sbda xa ayi masa aure da wanda baya so?" Tana shessheka tace "Akwai wata ma ai ta kashe kanta a nan hayi" yace "Shine ke ma xaki kashe kanki?" Ta gyada masa kai, yace "Toh duk sanda kika shirya ki min magana ni da kaina xan kawo maki piya piyan, kin ji ni?" Ta dago tana kallonsa tace "Toh ai ni na shirya" yace "Yaushe?" Da kyar tace "Yau da daddare nake son in sha" yace "Aa kinga ni sai yau na sani, ki bari ko xuwa jibi xan kawo maki" tana shessheka sae kuma ta sakar masa kuka tace "Yayi min nisa" Yace "Ya sunanki?" Tana kallonsa da hawaye idanuwanta tace "Jiddah" Ya d'an yi shiru, bayan few seconds yace "Jiddah.... shekaranki nawa??" Cikin sanyin murya tace "Babaarmu tace sha bakwai" yace "Toh ki jira sai na kawo maki da kaina, kar ki kuskura ki siya da kanki, kin ji me nace maki?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ki yi min alkawari xa ki jirani" Tace "Nayi" yace "Kina komawa gida ynxu ki ci abinci ki sha maganin ki ai nurse din ta nuna maki ynda xa ki sha" Ta gyada masa kai, tada motar yyi ya ci gaba da driving dinsa gaba daya yana kara naxarin xancenta.


07087865788✍🏻💖💖 *Jiddatul Khair*💖💖




_By Khaleesat Haiydar_✍🏻






6.....

Suna kusa layinsu cikin sanyin murya tace "Toh me xan ce ma Baabarmu idan ta dawo, wllh har dukana xata yi" Bai ce komai ba yyi parking d'an nesa da layin snn ya d'an kalleta yace "Amma ba Baabar da ta haife ki ba ko..." Ta girgixa masa kai a hankali tace "Abbana yace ita ta rasu tun ina yar karama" ganin hawaye idonta ya dauke kai bayan few seconds yace "Allah ya gafarta mata" Ta sunkuyar da kanta ta amsa da Ameen, yace "Sai kice mata saurayin da xaki aura ne ya xo kika fito" Ta marairaice tace "Ai yana legas bai dawo ba" Yace "Kwanaki da na baki kudi ki bata don kar ki sake fitowa bakin titi, kin sake fitowa?" Ta girgixa kai tace "Aa bamu sake yin awaran ba sai shekaranjiya ta fara" bai ce komai ba ya tada motarsa ganin ya fara tafiya ta kallesa da sauri tace "Ina kuma xaka kai ni?" Bai bata amsa ba ganin wani shago da ake cire kudi ta Pos ya tsaya sannan ya sauka motar, without taking much time ya dawo ya shiga motar.... Dai dai layin nasu ya sake parking ya ciro kudi a aljihu yace "Gashi ki kai mata yanxu ma" Kallon kudin ta dinga yi, sannan ta kallesa tace "Ince wa?" Yace "Kice wani ya bata" Amsan kudin tayi gabanta na faduwa, yace "Me nace kiyi idan kin koma gida yanxu?" tace "Kace in bata wai in ji wani" Yace "Kafin wannan" Ta d'an yi shiru sannan tace "Kace in ci abinci in sha magani" Ya d'an daure fuska yace "To sauka" yana fadin haka ya bude mata motar ba tare da ya yarda ya ta6a ta ba, ta sauka, yace "Kulle min mota" Ba musu tayi yanda yace sannan yayi wucewarsa without looking at her, sai a sannan bugun xuciyarta ya tsananta, ta fara tafiya a hankali xuwa cikin layinsu, ta fi minti biyu bakin xaurensu ta kasa shiga, daga karshe ta kutsa kai ciki, tuni hawaye ya fara sauka idonta tana jiran jin saukan duka, sai dai me... Har sannan Hansai bata dawo ba balle Bibalo, gidan babu kowa, dakinsu ta shiga duk da akwai wutan nepa amma kamar ko da yaushe wutan is very low, xaunawa tayi ta ajiye ledan hannunta sannan ta boye kudin cikin ghana must go dinta, a hankali ta bude take away din abincin ta ga shinkafa da katon kaza, ta xaro ido, ita yaushe rabon da ta ci shinkafa balle wata kaza, shinkafa sai suyi kusan sati uku ma basu ci ba daga tuwon masara sai taliya 'yar Hausa ko garin rogo, Kaza kuma dama ranan sllh ne kadai Hansai ke bata kai da kafafuwan ko kuma wuya, yau kuma ga kaza kato a gabanta har da shinkafa, kasa cin abincin tayi tana ta kallonsa, tunawa da tayi Hansai na iya dawowa yanxu ko Bibalo yasa ta xaro ido, a hankali ta fara cin abincin, sbda a tsorace take ta kasa nutsuwa ta ci abincin, ta dai ci wanda xata iya ci, jin almajiri na bara ta mike da sauri ta fita da abincin da ta kunshe a ledansa ta mika ma almajirin ta dawo ciki, ta fi minti daya tana kallon magungunan, kafin ta fito da su tana kallo, ganinsu kadai taji xuciyarta ya fara tashi ta mayar da su da sauri ta cusa a ghana must go, duk ciwon da xata yi bata shan ko d'an paracetamol da Abbanta ke siyo mata lkcn da yake da rai, Hansai kuma ko kasheta ciwo xai yi bata ta6a cewa ta sha magani, muryar Bibalo ta ji tana kiran Uwarta tun daga bakin Zaure hakan yasa ta boye goran ruwan da ta sha ta rage, snn ta kwanta ta rufe idonta. Washegari da asuba jiddah ta kasa tashi kamar yanda ta saba, duk karfe biyar dama take tashi ta fita ta debo ruwa a borehole ta cika jarkunan tsakar gidan da ma bokiti, ganin gari ya fara haske Hansai ta leko dakin tace "Yau naga walakanci, Jiddah kece kwance har yanxu baki fito ba, uban wa xai debo ruwan yau? Bibalo me ciwon kirji ko ni xan fita debo ruwan?" Bibalo dake kwance tana bacci ta gyara kwanciyarta hade da rufe har fuskarta da xanin gadonsu, Jiddah ta dago da kyar muryata na rawa tace "Baabarmu kaina ke min ciwo sosai, idan na tashi juwa nake gani" Hansai tace "To a rayuwar nan yanxu waye baya fama da ciwon kai, ko digon ruwan alwala fa babu a gidan nan, ni kike son in fita in debo ko Bibalo da ba cikakkiyar lafiya gareta ba" Jiddah dai bata ce komai ba, Hansai tace "Ai ko daurewa xa ki yi ki mike ki debo ko bokiti uku ne, gida idan babu ruwa ai ba magana" Daga haka ta juya ta fita tana cewa "Idan ma xaki rufa ka kanki asiri ga bishiyar gwanda da mangwara can ki tsinko ganyayyekin su ki hura icce ki dafa ki sha kiyi wanka don sile na baxanyi amfani da shi wajen siyo maki magani ba" Da kyar jiddah ta mike tana dafa bango ta fita, ta dau bokiti, d'an makotansu ne ya taimaka ya kawo mata ruwan har kai uku gidan, ta dawo da kyar ko tafiyan bata iyawa ta shige daki ta kwanta ko ina na jikinta na mata ciwo... Har karfe goma na safe tana kwance, Hansai ta shigo dakin cike da masifa sosai tace "Ke ni fa babu ruwana ki tashi kiyi ta kanki ki tsinko abinda nace ki dafa uban waye xaki daura ma wahala bayan na ciyar da ke da nake yi" Jiddah ta mike ko ina na jikinta na rawa sbda sanyi, tace "Xan yi" tana magana ta jawo ghana must go dinta ta fiddo kudin jiya ta mika ma Hansai tace "Jiya wani ya kawo wai a baki" Hansai ta xaro ido tana kallon kudin ta karba tace "wani kuma? A ina kika gansa?" Tace "Aikawa yayi in xo, ina xuwa yace in baki" Hansai ta xauna gefen gado ta fashe da kuka tace "Amma gaskiya isuhu ya tare mana abubuwa da yawa a duniyar nan sanda yake raye, to da ya baki sai yace me??" Jiddah ta koma ta kwanta tana fidda numfashi da kyar tace "Cewa yyi in baki kawai" Shiru Hansai tayi tana kirga kudin har ta gama taga dubu talatin cif, ta kalli Jiddah da sauri tace "Ko dai mutumin da ya ta6a baki kwanaki ki kawo min kada mu fito sana'a?" Jiddah ta gyada mata kai, Hansai tace "Toh don girman Allah duk ranan da ya sake dawowa kice masa ya shigo in masa godiya" Jiddah bata iya ta bata amsa ba, Hansai ta mike murna fal cikinta tana murmushi ta nufi kofa tana cewa "In dai haka ne duk wani nawa amma banda Bibalo ya mutu a duniyar nan mana, daga mutuwa sai billowan alkhairi ta ko ina? Ashe dama akwai sauran mutanen kirki a duniya ban sani ba" Jiddah ta bi ta da kallo hawaye me xafi na sauka idonta.

Ummi na kallon Abuturrab tace "Ina kuma xaka da yamman nan kana ganin hadari?" Yace "Aa ni ba nisa xan yi ba, nan governor road xan je" tace "Ahmad din har ya tafi ne?" Yace "Aa tare xa mu fita da shi amma xai dawo" Tace "Toh Allah ya tsare, ka siyo min tsire while coming back" Yace "Alright, in sha Allah" Daga haka ya fita dakin nata ya dawo main parlor, Ahmad na xaune yana jiran sa, Ganinsa ya mike ya nufi kofa, bin bayansa Abuturrab yyi wayarsa ya fara ring, dubawa yyi yaga Aunty ke kiransa, ya daga ya kai kunne, wara ido yyi yace "Aunty yanxu ai xan dawo..." Murmushi yyi yana kallon wayar don har ta katse, juyawa yyi ya koma bangare Stepmum din tasa, Ahmad ya ta6e baki, a parlonta ya sameta, yace "Ba nisa fa xanyi Aunty" ta hade rai tace "Shine ni baxa ka min sallama ba amma ai naga ka shiga gun uwarka?" Yace "Toh kiyi hakuri" Yana fadin haka ya jefa ma stepsis dinsa dake xaune parlon wani kallo sanin ita xata gaya mata, Aunty tace "Toh me Ummin tace maka da ta kira ka?" Yace "Nothing kawai tace in taho mata da tsire while coming back" Tace "Toh nima ka taho min da tsiren" yyi murmushi yace "Toh" Daga haka yace "Sai na dawo" ya fita dakin. Yana driving ya d'an kalli Ahmad dake danna wayarsa yace "A ina xaka sauka?" Ahmad ya kallesa yace "Kai ina xa ka???" Abuturrab yace "Bakin ruwa, nan by pass" Da mamaki Ahmad yace "Me zaka je yi a bakin ruwa Captain?" Ya gyara xama yace "Xan amshi sako gun wani frnd dina ne, he is coming from Abuja kuma kano xai wuce, so yace min ya shigo kd yanxu mu hadu by pass in amshi sakon" Ahmad yace "Ohk, drop me home" Abuturrab ya nufi gidansu yyi parking bakin gate, Ahmad ya sauka yace "Sunday din xaka tafi kano?" Abuturrab yace "In sha Allah" Ahmad yace "Alright... Sai da safe" Daga haka ya shiga ciki, Abuturrab yayi reverse ya bar layin. Abuturrab ya fi minti goma tsaye a kan hanya bayan ya iso bakin ruwa, jinginar da kansa yyi jikin kujeran da yake xaune yana tunanin wanda ya sani wanda bai yi aure ba that he can do anything possible to see him married to this girl that is ready and wanting to kill her self, driver din Abbansa ko wata uku ba ayi da yyi aure ba, who again? Wani senior cleaner ne a Airport din kano ya fado masa, Guy din na da hankali... a Diploma holder, ga shi da mutunta mutane, Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya ganin ya kusa samun solution, and he will try all possible means sai Mu'axxam ya auri yarinyar nan, wani ajiyar xuciyar ya sake saukewa na relieve, driving ya ci gaba da yi, yana isa u-turn ya dau hanyar Hayi, kamar ko da yaushe parking yyi a bakin layin yana kallon cikin layin, nose mask dinsa ya saka da glasses din ido sannan ya sauka motar ya fara tafiya, calmly yake tafiyar har ya isa kofar gidan, wani yaro ya tura ya kira masa jiddah cikin gidan, Hansai na xaune tsakar gida tana cin shinkafa da wake da mai da yaji da salak wanda rabon da su ci shinkafar tun rasuwan Mai gidan nata, tana kallon yaron tace "Lawali daga ina haka?" Yace "Wani ke kiran jiddah a waje" Hansai tace "Jiddah kuma?" Jiddah dake kwance xaxxabi ya ci karfinta ta bude jajayen idanuwanta da sauri gabanta yyi wani mugun faduwa ta mike xaune, Hansai ta kakkabe guntun shinkafar hannunta a samiran cinyarta tace "Waye shi? Kuma daga ina?" Yaron yace "Wani dogo ne ya sa gilashi da takunkumi a hanci, ya sa fararen kaya" Hansai ta mike da sauri tana leka dakinsu Jiddah tace "Ke tashi, kaddai me kawo min kudin nan ne?" Jiddah ta mike tsaye da kyar jikinta na rawa tace "Ban sani ba" Hansai tace "To ai kuwa daurewa xa kiyi ki tashi ki saka hijabi ki fita ki ga waye, kika sani ko shi din ne wani kudin ya kawo yau ma" Kasa ci gaba da tsayuwa tayi duk ynda ta so yin hakan, Hansai tace "Yau naga tsiya, baxa ki daure ki tashi ba kamar ba mace ba Jiddah??" Jiddah ta dafa gadon ta kara daurewa ta tashi, Hansai ta warware Hijab dinta dake ajiye a linke kan jaka ta mika mata tace "Sa ki fita maxa maxa ki ga waye" da kanta ta sa mata hijab din, jiddah ta fita dakin, Hansai ta xauna gefen gado tana addu'an Allah ya sa shi din ne, kuma wani kudin xai bada yau ma, jiddah na fita kofar gidan ya juyo yana kallonta, durkusawa tayi nan kasa ta kasa ci gaba da tsayuwa, ya dinga mata wani kallo yace "Jikin bai maki sauki ba?" hawaye ya shiga sauka idonta, kana ganinta kasan tana jin jiki, yace "Kin sha magungunan nan kuwa?" Kin cewa komai tayi, Ya hade rai da d'an tsawa yace "Tambayar ki nake" Ta fashe da kuka a hankali ta kara jingina da bango tace "Ni amai xanyi idan na sha" Da mamaki ya dinga kallonta, Hansai dai na ta tsaye tsakar gida tana jiran ganin shigowar jiddah, jin shiru shiru ta nufo xauren cikin sanda tana leko waje, hada ido suka yi da Abuturrab, ta sunkuyar da kanta da sauri tana d'an kame kame tace "Sannu da xuwa Alhaji.... Ae da ta fito

2 Comments On JIDDATUL KHAIR
avatar
khadija-7-7

1 year ago

Reply

Chapter 10

avatar
surayya-2

9 months ago

Reply

Cool

Please Login or Register in order to submit comment