Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maka da tabarma ko" kallonta kawai Abuturrab ke yi daga sama har kasa, can yace "ina wuni" Hansai ta rutsuna tace "Lafiya lau Alhaji, sannu da xuwa, ko xaka shigo daga ciki...." Yana kallon jiddah yace "Ya mai jikin?" Hansai ta marairaice tace "Wllh da sauki kenan xa a ce, kuma fa ta sha magunguna amma shiru har yanxu" yace "Toh bari mu je asibiti" Hansai tace "Kai Alhaji da dai a je chemist kar hidiman yyi yawa, ga chemist can bayan mu" yace "Aa xa a je asibitin kawai" Hansai tace "Toh shkkn Alhaji, daure ki tashi Jiddan Mama, sannu... Ga dai ana shan maganin kamar ba a sha" tana fadin haka ta dagota, Abuturrab na kallon Hansai yace "Motata na bakin titi" Hansai ta kwance dankwalin kanta ta rufe jikinta da shi tace "Toh bari mu je can din" tana rike da jiddah suka isa bakin titin ya bude back seat ta saka jiddah ciki, mutanen layin sae kallonsu suke, Abuturrab na kallonta yace "Ina 'yar uwarta mu tafi tare" Hansai tace "Au wai Bibalo, ai kuwa bata anguwar nan yanxu haka, ko in shiga mu je ni?" Ya kalleta daga sama har kasa sannan yace "Yanxu xa mu dawo in sha Allah, ba sai kin je ba" tace "Atoh dama ae bai ma kamata in bi ku ba, toh Allah ya kiyaye Alhaji, a dawo lafiya" xagawa yyi ya shiga driver seat ya tada motar ya bar wajen Hansai sai washe baki take tana daga masa hannu, sai kuma ta hade rai tana kallon 'yan layin da suka xuba mata ido da kallo tace "To wai lafiya wannan shegen kallo haka??" Tsaki ta ja ta juya ta fara wucewa tana cewa "Jama'ah baxa su ji da talaucin da yyi masu katutu ba sai shegen sa ido da neman abun fade, to d'an uwanmu ne daga Habuja sai kowa yyi ta kansa haka kuma" Abuturrab na hawan saman titi ya kalli Jiddah ta madubi yace "Wato baki sha maganin jiya ba??" Shiru tayi bata ce komai ba, ya hade rai yace "Ki bude baki kiyi min magana ina tambayarki" kai kawai ta gyada masa, yace "Me yasa baki sha ba?" Kamar xata yi kuka tace "Nace maka amai xan yi idan na sha" Yace "To xa mu je su maki alluran yanxu ai" Ta mike xaune da kyar tace "Aa ni bana son allura" Wani kallo ya wurga mata, tayi shiru bata sake cewa komai ba.... Sai kusan karfe taran dare Abuturrab ya dawo da ita bakin layin nasu, yau ma da ledan take away din abincin da ya siya mata, ya sauko motar ya xaga ya bude mata side din da take xaune, da kyar ta sauko motar da wasu ledan magungunan daban da aka kara bata a asibitin da ledan abinci, ya rufe motarsa, har ya xaga xai shiga maxaunin driver ya sa hannu aljihu ya ciro dubu goma ya dawo ya bata yace "Sai ki ba Baabar taku" daga haka ya shiga motar yayi wucewarsa, da kyar ta dinga jan kafa har ta isa gida, Hansai na xaune da Bibalo dake cin abinci, ganin ta shigo Hansai ta mike a xabure tace "Me ya baki?" Jiddah ta mika mata duk ledojin hannunta da kudin sannan ta xauna nan bakin kofa ta jingina da bango kanta na juya mata, Hansai ta kirga kudin ganin dubu goma ne tace "Toh ya baxai bani dubu goma ba bayan kudi ya kare a shegun magungunanki, munafuka kawai, ciwo kalilan duk ta bi ta langwabe ma mutane kamar kyanwa, kuma da ganin asibitin me tsada xai kai ki, to Allah ya isa wllh...." Kallonta kawai Jiddah ke yi, Hansai ta ja tsaki ta shiga fiddo magungunan a fusace tana kyabe baki, can ta watsa mata su tace "Abun takaicin ma asaran kudinsa kawai yyi, ke din ce xaki sha ma mutane magani" watsa mata ledan magungunan tayi gaba daya sannan ta bude dayan ledan ganin shinkafa da dunkulelen kaza ta murmusa tace "Allah sarki bawan Allah" Tuni Bibalo ta tura kwanon gabanta ta dawo kusa da uwarta, Hansai tace "Toh bai saka da lemo ba sai ruwan gora?" Jiddah dai bata ce komai ba, Hansai da Bibalo suka shiga cin abincin kamar mayunwata, sai da suka kusa cinyewa ta kallo jiddah tace "Au, to ai ba mu sam mata ba" kwanon abincin da Bibalo ke ci ta jawo, tana kallon guntun shinkafar da Bibala ta rage ta debi na take away din loma biyu ta yarfa a kai, sannan ta dau tsoka me K'ashi, sai da ta ta66atar ta kwaye tsokan sannan ta saka k'ashin a kwanon ta tura ma Jiddah tace "Gashi kema" Jiddah dai bata ce komai ba, suka cinye nama da abincin tass sannan Hansai ta maka uban gyatsa ta mike ta shige daki tana cewa "Bibalo ke da yar yabi sai ku bibbi gobe ku kai cingam da sweet din sa ranan da aka yi, har yau ba a ba jama'a ba" Bibalo ta mike ta bi bayan uwarta tana cewa "Yo ai cingam din kwali daya ya rage..." Jiddah ta jingina da bango hawaye ya kawo idonta a hankali tace "Kuma bai kawo min piya piyan ba" Washegari lahadi Abuturrab ya fito gida misalin karfe sha daya na safe, Waya ne kare kunnensa yana driving a hankali don bai fita layinsu ba, girgixa kai yyi yace "No kai dai ka samu adaidaita ni na riga da na fito da mota, sai ka fadi inda xan sameka" Murmushi yayi bayan few seconds yace "Okay then, tunda kasan hospital din ba sai ka tafi ba" Yana fadin haka ya katse wayar hannunsa. Dai dai inda suka yi xai dau Ahmad yyi parking yana jiransa, bayan kusan minti goma Ahmad ya iso wajen da adaidaita ya shiga motar yana kallon Abuturrab yace "Amma ba yau xaka bar kaduna ba Captain" Abuturrab yace "probably.... Akwai abinda xan yi yau din" Ahmad yace "Ni train xan bi in sha Allah yau xan koma Abuja..." Abuturrab bai ce komai ba har suka isa wani hospital domin duba wani frnd dinsu da aka yi admitting, fruits iri iri suka siya masa a hanyarsu ta xuwa wajen, suna shiga ward din da yake suka tarar da abokansu hudu su ma sun xo dubiya, bayan an gaisa, wani frnd dinsu Umar na kallon Abuturrab cike da tsokana yace "Captain ko dai a hayin rigasa kake gini ne? Or probably neman aure...." Da mamaki Abuturrab ke kallonsa har ma da sauran abokansu, Ahmad yayi dariya yace "Haka yace maka Umar?" Umar ya gyara xamansa yace "To for the past 4 days kullum sai na ga motarsa a hayi" Abuturrab ya xaro ido yace "Ni kuwa?" Umar yace "Kai mana, yawanci kana ta daya side din nake ganinka, kai akwai ranan da ma na kiraka ina jin ka bar wayar a mota and u didn't even follow my miss call" Abuturrab yace "Subhanallah on a serious note ban lura ba...." Umar yace "To airport xa a bude mana a hayi ne kullum muke ganin Captain a can" Murmushin yake kawai Abuturrab yyi yana kallon Nasir dake kwance da drip a hannunsa yace "Barrister guda a gadon hospital, so how are u feeling now?" Nasir ya jefa masa wani kallo yace "Kai ma baka wuce a kwantar da kai gadon asibitin ba ai" Dariya kawai Abuturrab yyi, sun fi minti ashirin a dakin suna labarin duniya, daga karshe Ahmad ya sanar masu xa su koma bayan sun ma Nasir addu'an samun lfya, a tare suka fito da Umar daga ward din don shi ma wucewa xai yi, Abuturrab ya d'an kalli Ahmad dake bayansa suna magana da wani abokinsu da ya fito rakasu, ya kalli Umar da har ya kusa fita reception din hospital, ya kara pace dinsa har ya isa gunsa yace "Kai me kake xuwa yi hayi har kake ganina?" Umar yyi murmushi yace "A can fa Mahaifiyata take, so kusan kullum nakan je can din" Abuturrab yace "Ohhh Allah sarki..." Umar yace "To kai wajen wa kake xuwa?" Abuturrab ya d'an shafa kansa ya saci kallon Ahmad dake tahowa yace "Aboki nayi nima a can din" daga haka ya fiddo wayarsa ya d'an yi gaba kamar xai yi answering call don bai son Umar ya ci gaba da maganan gaban Ahmad. Abuturrab yana kallon Ahmad bayan sun hau saman titi yace "Gida xan sauke ka?" Ahmad yace "Yeah..." Driving kawai Abuturrab ke yi, Ahmad dake kallonsa yace "Wajen wa kake xuwa a hayi Captain?" Abuturrab ya kallesa da sauri cos the question came unexpected, ya dake yace "Ka yarda da Umar kenan, he was just pulling my leg idan ba dai a train station ba ya gan ni wa gareni a hayi da xanje? Wa na sani a hayi? Kawai dai idan mun hadu dole sai ya tsokane ni ne..." Ahmad na gyara xama yace "To na sani ko budurwa kayi a can baka sanar min ba kake boye min, ai idan tayi tsami ma ji" Wani kallo Abuturrab ya jefa masa yace "In rasa inda xanyi budurwa sai anguwar nan???" Ahmad na kallonsa da mamaki yace "Meye da su 'yan anguwan, ba mutane bane su din? Or sai da aka halicceka specially sannan aka halicce su aka ce maka? What's wrong with u Abuturrab? Why do u sometimes behave like...." Abuturrab yace "Illiterate right?" Ahmad yace "Of course" Abuturrab yace "Fine, but do not forget everyone is entitled to his or her opinion, ra'ayinka daban ra'ayina daban, kai xaka iya budurwa a can infact har ma ka aureta ku xauna a can din, it's ur opinion, ni kuma last thing da baxanyi ba kenan a rayuwata, and this is my opinion, so stay entitled to urs, and i stay entitle to mine also" Ahmad yace "Baxa ka iya aure a can ba sbda kafi su a wajen Allah ko??" Abuturrab yyi masa wani shegen kallo yace "Wai Ahmad ance maka ni kai ne?? Ni fa ina da class ina da taste, as in i am far beyond that ka daina yi min irin wannan maganan bana so wllh" Ahmad yyi d'an murmushi bai kuma ce masa komai ba, Abuturrab yyi tsaki yace "Haka kawai sai kace kowa sai ya bi ra'ayinka, kai mace ko min kazantarta da locality dinta xaka iya aurenta ku xauna lafiya, ni kuwa it's a big No for me, bana walakanta 'yan adam kai shaida ne, sannan kasan ko kai baka kaini tausayin d'an Adam ba, idan naga mutum na cikin damuwa ko wani yanayi more especially mace ina bakin kokarin ganin nayi duk abinda xan iya yi ko a ina ne kuwa, even with my last card i can help, amma sai ka dinga hadani da su kana wasu maganganu marasu ma'ana" Ahmad bai kuma ce masa komai ba har suka iso gidansu, Abuturrab yyi parking, Ahmad ya juya yana kallonsa still bai ce komai ba ya bude motar ya sauka ya rufe masa motarsa, tsaki Abuturrab yyi, yyi reverse ya bar layin kallon agogonsa dake nuna masa sha biyu da rabi yyi ya nufi gida kawai....


07087865788....✍🏻 Almost done with free pagesπŸ’–πŸ’– *Jiddatul Khair*πŸ’–πŸ’–




_By khaleesat Haiydar_πŸ“šβœπŸ»





7.....

Fitowa Hansai tayi tsakar gida jin ana sallama, ganin aminyarta Zulai ta ce "Aa ashe Zulai ce, shigo daga ciki mana" Zulai tace "Ina ta addu'ar Allah ya sa in sameki wllh" Hansai tayi dariya tace "Ai ko kin ci sa'a, don yanxu haka shiri nake xan fita kasuwar tasha in saro kayan sana'ata" Zulai ta rike ha6a tace "Kin fara wani sana'ar ne banda awara?" Hansai tayi shewa tace "Ai ni na kwan biyu ma banyi awarar ba, amma kilan idan na fita yau dai in siyo har da waken suyan, yanxu su maggi, kubewa, kuka, daddawa... Kai duk dai mahadin miya da kika sani nake siyarwa, ko kwana hudu ban yi da farawa ba, sannan ina sa ran fara dillalanci kwanan nan" Zulai dake ta kallonta tace "Ikon Allahhh..." Hansai ta shiga d'an dakinta tana murmushi, Zulai na biye da ita a baya, bayan sun xauna Zulai tace "To ina yaran?" Hansai tace "Bibalo yanxun nan ta shiga makota, Ita kuma warcan gantalalliyar na can kwance wai ba lafiya" Zulai tace "To Hansai wani labari dai nake ji a gari, shine nace bari dai in sa6o gyale in taho..." Hansai ta gyara xama tana kallonta tace "Me ke faruwa? Wani labarin kika ji?" Zulai tayi kasa da murya tace "Yawo ake da ke wai bayan an kawo gaisuwan wannan yarinya jiddah har an saka rana kina turata gun wani me katuwar mota kullum sai ya xo kofar gidan nan, meye gaskiyan lamarin nan?" Hansai ta saki salati tana tafe hannu tayi mici mici da ido tace "Amma dai Allah ya tsine ma duk wani me sa ido a duniya, da yaushe da yaushe na turata gun me mota? Yau naga lalacewa, Jiya ne fa bata da lafiya shine ya siyo mata magunguna, kai ni Hansatu jama'a basu da gadonka amma suna da gadon maganarka..." Zulai tace "To waye shi me motar ma dai tukun" Hansai na huci ta lafto wani uban ashar tace "Duk wanda ya fasa sa min ido bai haifu cikin uwarsa ba a garin nan, tunda isuhu ya rasuwa wani shege ne ya ta6a kawo min kwayar masara balle shinkafa ko man kulli yace gashi ki ci kanki Hansai?? kawai sai don bawan Allah ya ga muna cikin matsatsi da yanayin rayuwa yana xuwa yana taimaka mana domin Allah sai a sa mana ido a hau mana bakin ciki da hassada a anguwa? Ni wllh ji nake kamar in siyar da gidan nan in bar gantalallen anguwar nan ko xan samu ci gaba" Zulai tace "Ke ni duk ba wannan ba tsoho ne mutumin nan ko yaro?" Hansai ta ja tsaki tana gyara xama tana huci tace "D'an yaro ne fa Zulai, ina jin ma saurayi ne bai ta6a aure ba, baki gansa ba bawan Allah wllh...." Zulai tace "Gun jiddar yake xuwa?" Hansai ta kalleta da sauri tace "Waye kuma jiddah? ita a wa xai xo wajenta? kema dai da wani xance wllh, xuwa fa yake idan yaga tana tuyar awara bakin titi ya mika mata kudade masu yawa ta kawo mana, ai ya san halin da muke ciki, d'an gayu ne fa sai kin gansa me kuma xai yi da wata jiddah kamar warce uwarsa tace masa je ka ka gani?? Haba Zulai, wllh da kyar ma idan ba daga Habuja yake xuwa ba don d'an gaye ne" Zulai ta d'an leka waje a hankali tace "Bacci jiddar take?" Hansai tace "Oho...." Daga haka ta mike ta fita, bude labulen dakinsu jiddah tayi ganinta a kwance tace "Wannan shegen kwanciyar baxai fissheki ba idan xa ki tashi ki kwashi bokitai ki fita gashi can an kawo famfo bakin titi ki jido mana ruwa ko na alwala ina jin babu a gidan nan, tun safe kin wani makale daki a kwance kamar ruwa" daga haka ta fice daga dakin ta koma nata, jiddah ta mike xaune daga kan darduman da take a kwance bayan tayi sllhn azahar, duk da jikin nata ya mata sauki, amma idan ta tashi jiri take gani ga yunwa dake dawainiya da ita, tun safe kunu kadai ta sha kosan da aka siyo ma bata ga idonsa ba balle a bata ta ci, sai da Jiddah ta bar gidan da bokitai sannan Zulai ta rike kunnenta daya tace "Anya ba son jiddah mutumin nan yake ba kuwa Hansai, banda haka hidimar uban me xai maku, ku da ku ke gida, ga almajirai can a titi, ga gidajen marayu a gari" Hansai tayi kasake, sae kuma tace "Sonta kuma? Ta ina xai so ta Zulai, babban mutum ne fa, kudi yake bata ta kawo min mu kula da kanmu tun bayan mutuwar Isuhu fa...." Zulai tayi wani murmushi irin na boss tace "Lallai Hansai, ashe har ynxu da sauran ki, to wllh da kyar idan ba sonta yake ba me yasa bai mika ma Bibalo ta kawo kudin ba sai Jiddar" Hansai tayi tsaki tace "To Bibalo sana'a take min a bakin titi da xai ganta ya bata? Ai sai dai Jiddar dake bakin titi kullum" Zulai tace "To wllh ki farka daga wnn baccin da kike, kada ki kuskura ki bada kofar da xai shigo da wani batu bayan ihsanin da yake maku, idan kuwa kika yrda to kina ruwa, ga dai Bibalo ai ita ya kamata a so tunda da gatan ta, amma har kika yarda ya shigo maki da wani batu kan Jiddah to kashin ki ya bushe kina ji kina gani Jiddah xata xama matar babban mutum...." Shiru Hansai tayi tana kallonta ko kiftawa babu da alamar xancen Zulai ya gigitata, Zulai tace "Atoh, kada ki kuskura wllh, ihsanin ma idan son samu ne kada ki sake amsa don a bisa dukkan alamu ya ga Jiddah ne ya kyasa, to jiddah kuma a wa Allah na tuba, yarinyar da ko dangin kirki bata da, kai ina ma ta gansu, ke fa kadai ce gatan ta a duniya, ba dangin uwa balle na uba, yau da xaki koreta sai dai ta bi duniya bata da wajen xuwa...." Hansai tace "Toh wai hauka nake yi ne Zulai, bayan an amshi gaisuwa gun Iliya so kike d'an iskan ya 6a66aka ma gidan nan wuta mu shiga uku? ai jiddah yanxu bata da maraba da matar aure, Iliya ya kawo komai sadaki kawai ya rage da daurin aure, shi ma ni ce na ja lkcn ai an sa ranan kusa kusa na daga" Zulai tace "Atoh, tun wuri sanar masa ya dawo ayi ayi auren kawai, kinga wannan mutumi kam dole ya komo ma Bibalo...." Hansai ta sharce wani xufa tace "Ni dadina da ke akwai hangen nesa wllh Zulai, kinga bbu wanda ya xo ya wayar min da kai banda ke ina nan ina ta haukana, bari in sa a kira min Iliyan dama sbda kudin katifar da xan siya mata ya sa nake ta jan auren naki yrda a sa sati biyu kamar yanda ya bukata, amma tunda haka ne kuma ga wnn bawan Allah ya bamu kudade masu tsoka kema har na cire maki dubu biyu a ciki, sai ki rakani kawai gobe ko tsohuwar katifa ce in siya mata da 'yar robobin aikin gida" Zulai tace "Shkkn kuwa" kasa karasawa cikin compound din Jiddah tayi da bokitin ruwa a kanta jin abinda su Hansai ke cewa, ta fi minti uku tsaye duk tana sauraronsu Zulai tace "Idan kin kirasa kice yace a sa bikin sati biyu kawai kin shirya a wuce wajen" Hansai tace "In sha Allahu haka xan yi" A hankali Jiddah ta karaso ciki ta juye ruwan kanta duk suka yi tsit, ta juya ta fita tsakar gidan lkci daya hawaye ya kawo idonta, ita dai bata ji xancensu na farko ba amma daga inda suke cewa xa su ce Iliya ya dawo ayi auren ta tsinci maganar su. Bayan ta fito ta so shiga gidan Iyah amma sbda irin warning din da Hansai tayi mata yasa bata shiga ba, inda xata shiga tayi kukanta me isarta take nema, a haka ta dinga jan kafa har ta isa inda pampon yake ta jingina da bangon wani gida tana share hawayen dake makale idonta, ko yaushe xai kawo mata piya piyan da yace xai kawo mata, ji tayi baxata iya jiransa ba kuma, gwara kawai ta siya da kanta duk da kudin da ya rage mata yanxu bai wuce dari biyu ba tunda Hansai ta rabata da Usman dinta ta karfi da yaji, don kuwa wanke kafa tayi ta tafi har gidansu can cikin gari ta sanar ma iyayensa su ja ma d'an su kunne ya fita harkar 'yar ta jiddah don an sa mata rana, tun daga sannan kuma rabonta da Usman. Washegari da sassafe Hansai ta fita xuwa gidan Zulai don daga can xasu wuce kasuwan dillalai yi ma Jiddah siyayyar aure, wata tsohuwar katifa ce da ko riga babu suka siya a farashi me sauki da pillow kwaya daya, sai robobin kitchen su ma duk tsofaffi, hatta wuka basu siya sabo ba sai tsoho, suka dai kwaso tarkacen da xa a iya kai ta gidan miji da shi, suna shirin barin kasuwan Zulai tace "To baki siya xanin gado ba" Hansai tace "Ina da wani a karkashin akwati xai yi shekara goma da ajiyesa sai in bata kawai, buta kuma ta tafi da na ubanta yana can ba amfani muke da shi ba" A barrow suka kima kayan suka dau hanyar gida. Tunda Jiddah taga siyayyar da suka yi wanda ke nuna cewar an kusa aurenta da Iliya hankalinta yyi mugun tashi, Hansai kuwa tuni tayi kiran Iliya da ya sanar mata sun ma kusa shigowa kaduna, bayan ta katse kiran tana kallon Zulai da wata kawarsu Dije da ta rakasu siyayya tace "Atoh ai shkkn, yace sun wuce Abuja, kun ga wannan karan kenan da matarsa xai koma legas din" Zulai tace "Ahh shkkn, Allah dai yasa ayi bikin da mu" Dije tace "Ameen, ai Hansai 'yar halaq ce, babu wanda yayi tunanin xata yi ma jiddah wannan abun arxikin, kowa gani yake tunda Malam Isuhu ya kwanta dama shkkn watsi xata yi da jiddah, sai gashi ta ba mara da kunya, kuma in sha Allahu baxa ki ta6e ba, kin cika yar halaq wllh" Hansai tayi murmushi tace "Toh Allah na tuba ko uban na da rai wllh ba samun hakan xata yi daga garesa ba, sai in idanuwansa xai kwakule ya siyar yyi mata kayan daki, uban me garesa banda wannan rubabben gidan, bashi da komai sai wahala wllh" Zulai ta kwashe da dariya tace "Allah dai ya ji kansa, gashi nan kin rufa masa asiri kin rufa ma 'yar sa asiri, kin mata abun arxiki" Washegari Hansai ta azalzali Iliya da kira nan ya sanar mata nan da kwana biyu xa su je can gidan kawun nata da ake xancen auren a wajensa tare da magabatansa sai a saka sati biyun da tace, amma fa ba shi da kudin sadaki a yanxu sai dai a biyosa bashi, Hansai tayi shiru tana sauraronsa, can tayi kasa da murya tace "Iliya da kudin sadakin fa nake son yi mata dinki tunda ba lefe xaka yi mata ba kace baka da halin yi...." Ya katse ta cikin fada yace "Gashi nan da duk kudin hannuna na siyo maki masara kwano 8 da gawayi, ko in siyar in kai kudin sadakin?" Da sauri tace "Aa to ai tunda kace idan ka samu xaka bada babu wani damuwa xan ma kawun nawa bayani, Allah yayi maka albarka, ai kowa yasan kai me xuciyar yi ne Iliya, to a ina xaka ajiye Jiddar?" Yace "Ehh akwai shago daya gaban gidan kakana sai ta xauna nan kafin in sama mata haya" Tace "Atoh shkkn, ni na xata legas din xaku wuce tare ince shkkn xaka rabani da Jiddah gaba daya" Yace "Aa nan xan bar ta, mu ma gareji muke kwana a legas din" Hansai ta xaro ido tace "Atoh Allah ya rufa asiri, tunda ga gida ka samar mata a nan din shkkn, Allah ya kai mu wannan rana dai" Yace "Ameen" daga haka ta katse wayar tace "Toh ba shkkn ba"

Abuturrab na kwance cikin resting cabin din jirgin da yayi piloting tare da Co-pilots dinsa daga lagos xuwa kano, ko minti talatin basu yi da alighting ba, idonsa a lumshe suke duk da ya rufe fuskarsa da hulan uniform dinsu na pilot dake jikinsa, tapping dinsa aka yi a kafa, ya xame hulan a hankali, Co-pilot dinsa ne tsaye kansa, pilot din yyi wani sigh yace "Done with the Secure Cockpit checklist.... Can we??" Abuturrab ya mike xaune yace "Alright..." Pilot din yace "Ain't you changing??" Abuturrab ya kalli uniform din jikinsa yace "Not at all" Jakunkunansu suka dauka suka sauka jirgin, sai da suka gaisa da incoming crew da suka hadu da sannan suka shiga cikin airport din. Driving Abuturrab ke yi cikin motarsa da yake bari a airport, hotel din da yake sauka yawanci idan yana kano ya nufa, duk da

2 Comments On JIDDATUL KHAIR
avatar
khadija-7-7

1 year ago

Reply

Chapter 10

avatar
surayya-2

9 months ago

Reply

Cool

Please Login or Register in order to submit comment