Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikin ki" Ya mike ya yace "Mu je in raka ki" Tashi yyi ya dagota xai cire Hijab din jikinta ta rike da sauri cikin rawar murya tace "Aa wllh sanyi nake ji" Bai saurareta ba ya cire Hijab din ya jefar kan gado ya nufi kofa ya bude yace "Mu je kiyi fitsarin" Ta bi sa da sauri jikinta na rawa, wani lungu ya nuna mata a jikin gidan, tun bata kai nan ba take jin zarni na tashi a wajen, yace "Kije kiyi ki dawo ki sha lemo kinji amarya" Ta gyada masa kai ta nufi wajen, komawa ciki yyi da sauri ya dau wandonsa ya laluba ciki ya fiddo wani karamin kwalba, sannan ya dau lemon coke dake ajiye a dakin ya bude, ya bude kwalban ya tsiyaya abinda ke ciki cikin lemon sannan ya rufe ya d'an jijjiga lemon ya sha kadan ya ajiye sauran, ya mayar da kwalban aljihunsa yana murmushi yace "Tass xa ki shanye lemon nan" xaunawa yyi gefen katifa yana jiranta, da sauri ya mike kamar wanda ya tuna abu ya nufi waje ya leka yace "Ke Jiddah, har yanxu baki yi fitsarin bane" A wangale ya ga d'an zinc din da aka yi kofa da shi na gidan, ya xaro ido ya fita da gudu yana kwala mata kira, gudu kawai Jiddah take wajajen da bbu kowa babu wasu gidaje sai ciyayi, sai da tayi gudu sosai taga wani me adaidaita ta tsayar da shi jikinta na rawa tace "Don girman Allah ka taimakeni wllh sato ni yayi, don Allah ka rufa min asiri ka taimakeni" Bata jira cewarsa ba ta shige adaidaitan don ya tsaya, shi ma mai adaidaitan duk a tsorace yake ya dinga gudu har suka shigo cikin mutane, har sannan Jiddah waige waige take gabanta na faduwa, sai da suka shigo hayi sosai sannan yace "Daga ina suka dauke ki?" Tace "Can cikin gari" Ya girgixa kai yace "Yanxu ina xa ki?" Shiru tayi don tasan tana komawa gida yanxu Iliya xai iya xuwa can gidan, da sauri tace "Cikin gari xan je don Allah" Dai dai kano road mai adaidaitan ya tsaya yace "To anguwan naku ba shi da sunana ne a cikin garin, ni fa nan ne iyakata?" Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta bude tafin hannunta tana kallon takardan da Abuturrab ya bata daxu, har lkcn takardan na hannunta gam, ta kalli mai adaidaitan cikin sanyin murya tace "Don Allah kana da waya?" Yace "Ehh" tace "Toh ka taimaka ka kira min number nan don Allah" ya amshi takardan ya dau wayarsa ya kwashe lambar sannan yayi dialing, Abuturrab na xaune parlon Abbansa yana masa calculating din order din da Abban nasa yyi daga waje na kayan auren Ramlah wayarsa ya fara ring, Abba ya kallesa ganin ba daukan wayar xai yi ba yace "Pick ur call" hakan yasa Abuturrab ya dau wayar yana kallon number kafin ya daga ya kai kunne, Mai adaidaitan ya mika ma Jiddah wayar ta amsa ta kai kunne, calmly Abuturrab yace "Hello" Hawaye ya silalo idonta tace "Ni ce" Kallon Abbansa dake kallonsa yyi da sauri, sai kuma ya sauke kansa kasa yace "Ohk ina ji" Ta fashe da kuka sosai tace "Iliya ne ya xo ya daukeni wai saboda ya ganni a motarka...." Abuturrab ya dago da sauri yace "Xuwa ina?" Cikin kuka tace "Wai shi ba sai anyi biki ba tunda ya bada sadaki, nufinsa tarewa xan yi" Abuturrab ya saci kallon Abbansa ya rasa abinda xai ce, Abbansa dake lura da shi ya mike ya shiga bedroom dinsa, mikewa yyi da sauri ya nufi kofa ya bude ya fita yace "Kina ina yanxu?" Ta bi inda take da kallo tace "Mai adaidaitan yace min kano road ne" Abuturrab yace "Ba sa wayar" Mika ma mai adaidaitan wayar tayi ta shiga share hawayen da ya ki tsaya mata, Mai adaidaitan yace "Ehh a dai dai wajen muke ma" bayan few seconds mai adaidaitan yace "Toh shkkn xan jira in sha Allah" Daga haka ya katse wayar, Abuturrab ya koma parlon Abbansa, Ganin bai fito ba ya karasa bakin bedroom din yayi masa sallama, Fitowa Abba yyi, Abuturrab yayi kasa da kansa yace "Abba xan d'an je in dawo ynxu, wani abokina ne ya kirani and it's urgent" Abba yace "Alright sai ka dawo" Juyawa yayi ya fita daga parlon, ya tafi dakinsa ya dau makullin motarsa, jallabiya ne jikinsa ya fita a haka ya shiga motarsa ya bar compound din.....


07087865788✍🏻💖💖 *Jiddatul Khair* 💖💖





_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻





9.....

Abuturrab yayi parking yana bin wajen da kallo ya dau wayarsa yayi dialing number da suka kirasa da shi, yana fara ring mai adaidaitan dake hira da wani me d'an kiosk a wajen ya daga, Abuturrab yace "Ka duba wani bakar mota a wajen da kace" Mai adaidaitan ya mike yana dube duben wajen, can ya hango motar Abuturrab ya kalli Jiddah dake xaune cikin adaidaitan har sannan ta takure waje daya yace "Ga sa can ya iso" Dago kai tayi da sauri sannan ta sauka daga cikin adaidaitan, tare suka tsallaka titi da shi xuwa daya side din ya nufi motar Abuturrab tana biye da shi a baya, Abuturrab ya bude motar ya sauko yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi sbda hawayen da ya kawo idonta, ya kalli mai adaidaitan ya ciro dubu biyu aljihunsa ya mika masa yace "Nagode" Mai adaidaitan ya amsa shi ma yyi masa godiya sannan ya tsallaka ya koma gun Napep dinsa, Ba tare da Abuturrab ya kalleta ba yace "Shiga" Ba musu ta shiga gaban motar, ya shiga maxaunin driver ya tada motar suka bar wajen, a hankali yake driving din yace "Bayan na tafi sai me ya faru?" A hankali ta fara basa labarin abinda ya faru bayan tafiyarsa babu abinda ta boye masa har karshe, ganin yanda take kuka ya kalleta yace "Ya maki wani abu ne?" Ta girgixa masa kai, rasa particular tunanin da xai yi yayi a lkcn, babban damuwarsa yanxu inda xai kai ta cikin daren nan, ya d'an kalleta yace "Yanxu babu wanda kika sani nan cikin gari?" Ta girgixa masa kai tace "Ba kowa" ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yana ci gaba da driving dinsa almost absentminded, parking yayi bakin gate din gidan, har Mai gadin ya mike xai bude gate ganin yayi parking a nan waje sai ya koma ya xauna, Abuturrab ya sauke glass ganin haka mai gadin ya sake tasowa da sauri ya nufosa yana murmushi cike da girmamawa yace "Barka dai ranka shi dade..." Abuturrab yace "Ya aikin?" Mai gadi yace "Alhmdlh, Baxa ka shiga ciki ba?" Abuturrab ya d'an shafa kai yace "A'a, wani d'an alfarma nake nema gun ka" Cike da natsuwa yace "Toh ina saurarenka yallabai" Abuturrab yace "Erm... Mai dakinka na nan ai?" Mai gadin yace "Ehh tana ciki wllh" Abuturrab ya kalli Jiddah yace "So nake don Allah ta d'an kwana nan wajen ku kafin gobe, amma kamar kuma hakan da takura tunda daki daya ne ko?" Da sauri Mai gadin yace "Inaa babu wani takura wllh ranka shi dade, ni ai ba baccin ma nake da daddare ba yawanci nan tsakar gida nake kwanciyata wllh, kar kaji komai" Abuturrab yace "Toh nagode, amma kada kace ma masu gidan na xo" Mai gadin yayi murmushi yace "Baxa ayi hakan ba ranka shi dade" Abuturrab ya juya yana kallon jiddah yace "Sauka, sai da safe..." Yana fadin haka ya bude mata motar, ta sauka a hankali, Mai gadin yace "Mu je ciki to...." tafiya ya fara yi ta bi bayansa sai da suka kusa gate din ta waiga ta kalli Abuturrab da ya bi su da kallo, dauke kai tayi ta bi mai gadin suka shiga cikin compound din, yayi wani sigh ya tada motarsa yayi reverse ya bar layin wani ajiyar xuciyar ya sake saukewa feeling a bit relieved. Har aka idar da sallan asuba Jiddah bacci take, matar mai gadin na idar da sallah ta d'an ta6ata tace "Ki tashi kiyi sallah lokaci yayi" a hankali Jiddah ta bude idonta ta mike xaune da sauri, daki ne babba gun katifar kadai ne suka yi demarcating da labule, yaronsu daya wanda ko yayesa ma ba ayi ba, jiddah ta mike matar ta nuna mata bandakinsu dake cikin dakin, tana fitowa matar ta bata hijab, bayan ta idar abun ka da bata saba komawa bacci ba ta kalli matar ta gaisheta sannan tace "Babu wani aikin da xa ayi?" Matar tayi murmushi tace "Aa babu, ki koma kiyi kwanciyar ki" Jiddah bata ce mata komai, amma duk yanda ta so komawa bacci bata iya ta koma ba don ta riga da ta saba da wahala, gari na wayewa ganin matar ta dau tsintsiya xata fara sharan daga nan inda suke xuwa bakin gate don gidan akwai me shara, jiddah ta amshi tsintsiyar, matar tace "Don Allah ki bari ki koma kiyi xamanki...." Murmushi kawai Jiddah tayi tace "Aa xan taya ki" Tana fadin haka ta fara sharan hakan yasa matar ta koma ciki don yi ma yaronta wanka tana yaba hankalin Jiddah, shi kuma mai gadin na can xaune waje, jiddah na cikin shara aka bude gate din gidan ta dago da sauri, sosai gabanta ya fadi ganin wanda ya shigo, a hankali ta juya tana ci gaba da sharanta, waya ne kare kunnensa ya katse wayar yace "Maman Abdallah kun tashi lafiya" Ba tare da ta bari ta kallesa ba a hankali tace "Ba ita bace" Ko rufe baki bata yi ba Maman Abdallah ta leko da fara'arta, cike da ladabi tace "Ba ita bace Dakta, bakuwa nayi, ina kwana" yana tafiya yace "Lafiya lau, Abdallah bai tashi ba?" Tace "Kaya nake sa masa ya tashi tun daxu" yace "To a gaida min shi" Tace "Xai ji Dakta" Entrance din gidan nasu ya nufa, Jiddah ta bi sa da kallo tana sharanta a hankali... Karfe takwas Maman Abdallah ta kalli Jidda bayan ta gama shiryawa cikin kayan da ta bata tace "Tunda kinyi wanka mu shiga daga ciki mu gaisa da 'yan gidan in amso mana kumallon mu, ko" Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, Maman Abdallah ta goya d'anta tace "Tashi mu je, Hajiyar gidan ta tashi yanxu" A hankali Jiddah ta mike ta dau Hijabin matar ta sa sannan suka fita, Maman Abdallah ta bude kofar hade da sallama ta shiga ciki Jiddah na biye da ita, Xaunawa tayi kasa jiddah ma ta xauna kasa, Hajiya Ramlah dake parlon da murmushi fuskarta tace "Bakuwa kika yi Shafa" Maman Abdallah ta washe baki tace "Ehh wllh Hajiya, bakuwa nayi da yammacin jiya" Cike da ladabi ta risina tace "Ina kwana Hajiya" Umma tace "Lafiya lau kun tashi lafiya?" Maman Abdallah tace "Alhmdlh, su Maimuna da Siyama na ciki kenan" Umma tace "Suna ciki..." Jiddah na kallonta a hankali tace "Ina kwana?" Umma tace "Lafiya lau yan mata, sannu da xuwa.... ya sunanki?" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Jiddah" jin footstep ta dago tana kallon direction din, Ahmad ne ke sakkowa daga sama yana kallonta babu ko kiftawa, Umma tace "Ahh me babban suna ce ashe" Jiddah tayi murmushin karfin hali ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Maa sha Allah, sunan yayata gare ki, sannu da xuwa" Maman Abdallah dai sai washe baki take, Umma tace "Yar uwarki ce amma" Maman Abdallah ta sosa kai tace "Ehh kauyenmu daya" Ahmad dai sai kallon Jiddah yake, ita kuma taki yarda ta sake kallonsa, Maman Abdallah ta mike ta wuce kitchen don daukan kumallonsu, tana shiga ta dauka a inda mai aiki ta ajiye masu ta fito, Umma ta kira mai aikin tace "Tunda suna da bakuwa ki kara masu" Mai aikin ta amsa ta koma kitchen din, ba a dau lkci ba ta dawo ta mika ma maman Abdallah coolern, Cike da ladabi Maman Abdallah tace "Mun gode hajiya Allah ya kara girma" Umma tace "Ameen" Mikewa Jiddah tayi ta amshi warmer din a hannunta sbda Abdallah dake bayanta ita ma ta yi ma Umma godiya sannan suka fita, Ahmad dai ya bi ta da kallo.... He looks so confused, sak tayi masa kama da mai awaran hayi, wata xuciyar tace kawai kamanni ne me xai kawota cikin gari har cikin gidansu kuma, daga kafada yayi a ransa ya bar sa a cewar kamannin ne, ya nufi dining don yin breakfast. Karfe goma Abuturrab ya fito gida, driving yake yi with different thought in mind, wayarsa ne ya fara ring ya kalli wayar ganin Ahmad ke kiransa ya daga, Bayan sun gaisa Ahmad yace "Muna chatting kuma ka sauka" Abuturrab yace "Ehh i am driving now" Ahmad yace "To where?" Abuturrab yace "Aunty ta aikeni" Ahmad ya d'an ta6e baki yace "Ohk, wai ka dauki hutu ne naga baka koma gun aiki yau ba?" Abuturrab yace "Kai me ya dawo da kai during week day?" Ahmad yace "Wani taro xa mu yi nan kaduna, amma gobe xan koma ai, in sha Allah" Abuturrab yace "Ohk anjima xan shigo idan na dawo" Ahmad yace "Alright" daga haka ya katse wayar ya ajiye, parking yyi inda ya saba parking din, ya sauka motar yana kallon layin dake cike da mutane, wani d'an saurayi dake fitowa daga layin ya kalla yace "Abokina me ke faruwa a nan?" Saurayin yace "Wata amarya ce saura sati bikinta aka nemeta aka rasa, wasu sunce angon ne ya dauketa, wasu kuma su ce uwar rikonta ta san inda take, ynxu dai ga shi angon na neman cinna ma gidan wuta wai sai an fito masa da matarsa, uwar rikon na can tana kuka da rantse rantse bata san inda take ba, jama'a kuma na ta dannan shi angon, da yake babu wanda bai san halinsa ba a unguwar nan, sai ya iya kona gidan, yanxu dai wajen yan sanda ko mai anguwa suke shirin xuwa" Abuturrab yace "Toh Allah ya kiyaye" Barin anguwar Abuturrab yayi, yana isa gidansu Ahmad yayi parking a waje, ya sauka motar gaisawa yayi da mai gadi dake xaune a waje sannan ya xauna kusa da shi murya can kasa yace "Kayi hakuri babu wani bayani na kawo maku yarinya..." Mai gadin ya katse sa da sauri yace "Babu komai ranka shi dade, kar ki ji komai wllh, xata iya xamanta har iya sanda xaman nata xai kare a nan, ni bani da matsala haka ma mai dakina.." Abuturrab ya sa hannu aljihu ya fiddo dubu biyar ya mika masa yace "Gashi ka rike wannan" Mai gadin ya girgixa kai yace "Aa kar mu yi haka da kai don Allah" Abuturrab ya ajiye masa kudin ya mike ya shiga gate din gidan, Babu kowa tsakar gidan ya kalli building din mai gadin sannan ya nufi main entrance din gidan. Kiran azahar ne ya sa shi fitowa tare da Ahmad xa su tafi masallaci, Jiddah na xaune compound din kan karamin kujera kusa da dakin mai gadin da ruwa cikin buta a gabanta tayi nisa tunanin da take, Har suka kusa isowa wajen Abuturrab kallonta yake haka ma Ahmad, kamar ance ta daga kai tayi ido hudu da su, sosai gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta da sauri ta fara alwala da ruwan butan gabanta har suka fita compound din, sai a sannan Ahmad ya kalli Abuturrab yace "Don Allah wa yarinyar nan tayi maka kama da???" Abuturrab yace "Wacce yarinya?" Ahmad yace "Yarinyar da ke xaune a compound" Da mamaki Abuturrab yace "Ohh dama akwai yarinya xaune a compound din?" Wani kallo Ahmad ya jefa masa, Abuturrab ya daga shoulders dinsa yace "Banyi noticing ba" Ahmad yace Karya kake "Wllh" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba, Ahmad yace "Joke apart captain, bata yi maka kama da wannan yarinyar da muke siyan awara a wajenta a hayi ba" Abuturrab ya ta6e baki yace "Kai da kake kallonta kenan idan kaje siyan awaran, ni kam banda murhu babu abinda nake gani a wajen" yana fadin haka ya shige Masallaci kafin Ahmad ya sake ce masa komai, Ahmad ya bi bayansa kawai. Ko da suka fito masallacin Ahmad ya tsaya gaisawa da abokansa na layin, Abuturrab ya shiga compound din kawai, Jiddah na ta sauri tana kwashe kayan shanyan da Maman Abdallah ta shanya don garin akwai hadari, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai sai da ya iso dai dai inda take tace "Ina yini?" Bai amsa ba yace "Kina da wani matsala?" Ta girgixa masa kai, ganin haka ya ci gaba da tafiyarsa, dai dai nan Ahmad ya shigo compound din bata yadda ta kallesa ba har xai wuceta sai ya tsaya yace "Bakuwa muka yi yau a gidan ashe?" Taki yarda ta kallesa still, tayi kasa da murya tace "Ina yini" yayi murmushi yace "Lafiya lau, sannu da xuwa" Maman Abdallah ta leko tace "Dakta Abdallah fa boyewa yake idan yaji muryar ka" Ahmad yayi murmushi yace "Ae kice masa alluran ya kare" Ta kwashe da dariya tace "Lallai kam, shi dai ya tsorata da kai kawai Dakta" Ahmad yace "Ashe bakuwa muka yi gidan" Tace "Ehh wllh yar uwata ce daga kauyenmu ta xo jiya da yamma" Yace "Allah sarki, toh barkan ta da xuwa" Maman Abdallah tace "Ae ko dai Dakta, mun gode" Murmushi yayi ya ci gaba da tafiya a xuciyarsa ya kara gaskata cewa lallai kamanni ne kawai suka yi da me Awara a hayi, but the resemblance is so obvious even the dimples and large eyes, can balcony Abuturrab ya tsaya duk yana jin abinda suke fada, sai da ya iso Abuturrab yace "Kai dai baka abu da class Ahmad, meye na tsayawa hira da matar mai gadi pls?" Bai jira me xai ce ba yayi wucewarsa ciki, Ahmad ya girgixa kai kawai ya bi bayansa. Da yamma Mamam Abdallah ta ba jiddah kwanukansu ta kai can cikin gida sbda a ciki xa a sa masu abincin dare, Jiddah tace "Ta cikin parlon ake bi xuwa wajen girkin?" Maman Abdallah tace "Ehh inda muka je daxu ba, ynxu ma babu kowa gidan yaran duk sun tafi islamiyya, Hajiya nasan tana bangarenta yanxu haka, ai kinga dakin girkin da mai girki ta fito ta miko mana kumallo daxu da safe, nan xaki shiga, dakin ma ya kusa biyun wannan da muke ciki ae wllh" Jiddah ta mike ta dau babban samiran ta fita ta bar Maman Abdallah na linkin kaya, Babu kowa babban parlon kamar yanda Maman Abdallah tace, ko ina tsaf sae kamshin turaren wuta da ya kama parlon, Kasa karasawa can cikin parlon Jiddah tayi, tun da ta xo duniya bata ta6a ganin irin wannan parlon ba da ma komai na cikinsa, duk sai tsoro ya kamata, hanyar da taga Maman Abdallah ta bi daxu da safe ta bi ta d'an leka kofar da ta gani a bude ganin wasu mata biyu kuma har sun hada ido ta risina a hankali tace "Sannun ku da aiki" Duk suka amsa mata dayar tace "Shigo ki ajiye kwanon" Jiddah ta karasa kitchen din, ta kara masu sannu da aiki sannan ta ajiye kwanon, kanta a kasa tace "Me xa a kama maku?" Dayar matar tace "Aa babu komai 'yan mata, mun gode" Doguwar tace "Sae dai kawai wanke wanken dake cikin bahon wanke wanke, ba shi da yawa" Jiddah ta juya tana kallon sink da matar ke nuna mata, karasawa tayi wajen ta tsaya tana tunanin ta ya xata yi wanke wanke a takurarren waje haka sannan ta ina xa ta dinga xubar da ruwan wanke wanken, a hankali ta juya tana kallonsu tace "Ruwa da omo fa" Matar tace "Ga pampo a gabanki ki kunna, wannan roban kuma sabulun wanke wanke ne a ciki xaki matso ya fito"

Bayan magrib Abuturrab yyi parking inda ya sa6a parking ya sauka motarsa ya kulle da kafa ya karasa kofar gidansu Jiddah. Yaro ya aika ciki yayi masa sallama da mutanen cikin gidan, Hansai ce xaune tsakar gida da kawayenta biyu, Hansai ta sharbe majina tana matse hawayen kumburarren idonta tace "Wllh xai aika, waye bai san cewar shaye shaye Iliya yake ba, ni dai baxan kwana gidan nan ba yau gaskiya gwara in tafi wani wajen in kwana" Zulai tace "Aa nima dama ban bada shawaran ki kwana ba tunda ya furta sai ya kona gidan da kyar baxai aika ba" Ladi tace "Toh yanxu ina yarinyar nan ku ke tunanin xata tafi haka, wa gareta a duniyar ma gaba daya?" Hansai tace "Ai wannan magana ma bai taso ba, dolenta ta dawo duk inda ta tafi ta xo ta rabani da wannan mahaukacin mutumi, idan ya kona min gida gidan ubanwa xan koma kowa na ta kansa a rayuwar nan, dama gidan iyah nake ta tunanin ta shige amma duk dubawan da yan sanda suka yi a gidan babu ita babu alamarta" Kallon yaron da ya shigo suka yi gaba daya, yaron yace "Wai ana sallama a waje" Abuturrab ya daga kai bayan Hansai ta fito cikin gidan, ganinsa ta makale kofar xaure ta kasa karasowa, Ya karasa shi, yana dubanta yace "Ina yini?" Da kyar cikin rawar murya tace "Lafiya lau Alhaji, sannu da xuwa" kafin yace mata komai ta fashe da kuka tace "Muna cikin tashin hankali da alhini Alhaji" yana kallonta yace "Me ya faru?" Tana matsar kwalla tace "Tun jiya ake neman yarinyata har xuwa yanxu babu labarinta, ban san inda xan sa kaina ba xuciyata kamar ta fashe" Yayi shiru yana kallonta, ta sharbe majina tace "Shi kansa wanda ke da niyyar auren nata nan ya xo daxu da yamma ba irin tijaran da bai min ba har da ikirarin xai kona mana d'an gidan nan idan ba a fito masa da matarsa ba, wllh wllh bamu da masaniyar inda take, babban tashin hankalina ban san halin da take ciki ba yanxu" Yace "Yanxu ya ake ciki da shi wanda xai aureta din, baki basa kudin nasa bane?" Tace "Wllh yace baxai amsa ba, yanxu haka ma da kudin na tafi gun yan sanda na kai rahotu kasan sai an basu wani abu me d'an tsoka kafin su kula ka, sannan gidan radio da gidan talabijin duk na bi na rarraba masu kudin don su yi ta sanarwa har Allah ya bayyanata, yanxu maganar da nake maka ko dubu talatin ina jin kudin bai kai ba a ajiye a daki, 'ya ta bata fiye min komai ba a duniya?" Kallonta kawai Abuturrab yake bai ce komai ba, ta sake sharbe majina cikin rawar murya tace "In dai da wani taimakon da xaka mana yarinyar nan ta bayyana da wuri ka taimaka domin girman Allah Alhaji" Abuturrab yace "Ina shi madaurin auren nata?" Tace "Kawuna ne, tare da shi ma muke ta sintirin gidan radio da police station tun safe" Abuturrab yace "Ina son ki hadani da shi" Sosai gabanta ya fadi, yace "Yana da waya?" Da sauri tace "Aa bashi da shi, sai dai gobe in je in sanar masa, idan ka xo sai Bibalo ta kai ka" Abuturrab yace "Toh shkkn, nagode, sai goben" Daga haka ya juya ya bar wajen, ta bi sa da kallo gabanta na faduwa, da sauri ta koma ciki, Zulai tace "Waye hala?" Hansai ta share wani xufa da ya keto mata tace "Aa yan xuwa jaje ne, yanxu dai gidan Kawu Jibril xan tafi tare da Bibalo idan ya so sai mu kwana can kawai kada Iliya ya far mana cikin dare mu mutu" Ladi tace "Gaskiya kam, ku tafi can din kawai ku kwana, don kwana gidan nan ba karamin hatsari bane" Sai kusan karfe tara Hansai ta isa gidan kawun nata da Bibalo, Suna shiga d'an tsakar gidan yace "Me kuma kika xo yi nan kina neman ki ja min fitina Hansatu, ni nasan Iliya d'an daba ne amma bansan dabancin nasa ya kai haka ba, babu irin tijaran da iliya bai xo nan da tawagarsa sun min ba, in don dai shegiyar dubu ukun da kika bani ne cikin kudin sadakin yarinyar Allah ya kai mu gobe da safe in tafi in siyar da kaji na in baki kudinki, wannan tashin hankali har ina a kan dubu uku, wllh ban san tantirancin iliya

2 Comments On JIDDATUL KHAIR
avatar
khadija-7-7

1 year ago

Reply

Chapter 10

avatar
surayya-2

9 months ago

Reply

Cool

Please Login or Register in order to submit comment