Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

girgiza kai ahankali tace “yaran yanzu, Allah dai ya gyara mana jibi yanda ya maida gemunshi jama’a, wai Wanan ne gayu awajen su” secretary nata ta kwalama kira tana shigowa note and textbooks na Farrah da Zayn yabiya tanuna mata tace “kaima Farrah GSS1 Science” kwasa tayi tafice.



💫 FARRAH 💫


✍🏻M SHAKUR


EPISODE 2️⃣6️⃣
Sosai take concentrating a karatun da ake koyamusu her only problem shine rashin iya turenci, ranan gabaki daya maths da further math kadai tasan tagane shima sabida lissafi ne amman sauran abubuwan dasukayi bata ganeba sabida rashin iya turenci.

Break aka kada, kowa na ajin tashi yayi yafice banda ita dake zaune kaman an dasata awajen bude jakanta tayi sanan tadauko water bottle da Mami tasaka mata aciki dawani kula tabude, fries ne aciki da pepper chicken da sausage, sai fork murmushi tayi ahankali tasa fork tafaraci shigowa ajin akayi wata yarinya data dan dare Farrah tsayi da kadan tashigo ciki tana rike da cups biyu na parfait ta taho inda Farrah take kujeran dake facing Farrah ta zauna akai tana kallon Farrah da itama ke kallonta, dan murmushi tayi tamikama Farrah parfait daya tace “my name is Maryam, kowa call me Miemie agidan mu, I am a baker, na iya bakin cakes and so many many other thing kefa” abinda take bata Farrah takalla sanan ahankali tasa hannu ta karba dan kartaga kaman tamata wulakanci but bamata iyacin abinba, ahankali Farrah tace “sunana Farrah, ni ban iya yin cake ba but Mami tace zata koyamin” murmushi yarinyar tayi tace “ohh that’s nice, tun ina yarinya Mom tafara koyamin baking, yanzu is officially my business you can search me on Instagram @alfasimcakes, I really like you Farrah tunda kika shigo nake kallonki, you are so pretty” murmushi Farrah tayi batace komiba, ganin kaman batagane abinda take fadi yasa Maryam tamika mata hannu tace “friends? Muzama kawaye?” Shiru Farrah tayi tana kallonta batare daya mikamata hannunta ba, murmushi Maryam tayi tace “don’t be scared nima just last week aka sani a school dinan, a Saudi muke zama, sabida Yayan mu Ya Habeeb anturoshi yayi wani project anan Nigeria more like a course for 3yrs shine fa dukanmu muka dawo nan, Mom da Dad wai bazasu iya barin yaronsu yazo Nigeria yana wahala shi kadaiba babu mai girka mishi abinci ba, Dad dina is a Doctor, shima anan Nigeria aka haifeshi but he works at Saudi, the whole thing is so annoying nafison Saudi kan nan garin, tunda nazo banda any friends tundazu da aka shigo dake nake kallonki, kinga tsayinmu daya, though nafiki kadan, kuma kaman we are age mate, sanan bakida hayaniya, and you are very very very pretty, ni banma taba ganin someone as pretty as you are a school dinan ba sai yau kaman ke, so will you be my best friend, Babban kawata my Besty eh Farrah, I want us to be best friends forever BFF, ko baki sona” tunda take surutun Farrah ke kallonta saita tuna mata da Shafa, haka Shafa ke zuba gatada hayaniya, hannu Farrah tabata hakan yasa Maryam tai ihu. “Yeeeeee we are BFF” ahankali Farrah tace “Beef” dasauri Maryam tace “BFF” ahankali Farrah tace “BFF” “yauwa haka, menene baki gane ba” English Farrah tanuna mata da sauri tace “wanan” Gyadamata kai Maryam tayi tace “gamacin abinci zamuje library anjima muyi karatun tare we will be doing everything together tare daga yanzu” Gyadamata kai Farrah tayi tanadan murmushi dan Maryam is free spirited person hakama Shafa take.


3 aka tashi daga school parking books nata Farrah tayi tasa ajakanta, Maryam data gama hada komi nata takaraso wajen kujeran Farrah tana goya jakanta tace “muje headmistress office ki amshi uniform naki datace ki amsa idan an tashi” goya jakanta Farrah tayi tace “ok” murmushi Maryam tamata yakama hannunta tarike tace “let’s go Besty” fita sukayi daga ajin yan ajin na kallonsu yanda suka zama kawaye Maryam last week tazo bata taba kula kowa ba sai yau dataga Farrah toko tasan Farrah ne daga wani waje, office din headmistress suka shiga, tana ganin Farrah tace “good Farrah kin tuna kinzo, I was about nada secretary na ma takiramin ke kafin kitafi baki dauki uniform naki ba, here we go” headmistress tabata wani katon jaka na uniform nata kala kala da sport wears karba tayi ahankali tace “thank you” murmushi headmistress tamata tace “har kinye making friend Good job Maryam” washe baki Maryam tayi sanan suka wuce suka fita, lift suka shiga suka sauka kasa sanan sukai gate, tun kafin sukai gate Maryam tamata pointing wani mahaukacin jeep tace “ga motan gidan mu chan, me Ya Habeeb yazo wani daukana yau ni bazanje ba munyi fada” ta tsaya daga cikin school din, dan zaro idanu Farrah tayi tana kallonta tace “da yayanki kike fada Maryam”? Dan lumshe idanu Tayi tabude su sanan tace “Muryanki dadi Farrah gashi dan karami baya fita da kyau, by the way kinga ko tunda muka dawo Naija nake fushi da Ya Habeeb, driver ke zuwa daukana ni mezanyi da motanshi, da namazo da wayana dana kira Mom nace mata bazan shiga motan shi ba” dariya Farrah tayi dan Maryam is so funny, tana tunamata da Shafa sosai, kama hannunta tayi tace “kinga ko babu kyau ana fushi da dan uwa, kije hala ma yazo yace miki kiyakuri ne wuce kitafi” Farrah tai maganan tanajan hannunta suka fito gate, ganin motan Ya Zayn a pake ga bodyguard gaban motan yasa Farrah tasaki hannun Maryam dasauri tace “nima anzo dauka na bye Miemie” tadagama Maryam hannu, hannu itama Maryam tadaga mata tanadan dariya jin tacemata Miemie tace “bye Fairy🧚‍♂️ ” budemata bayan motan bodyguard yayi ahankali tashige cikin motan tana leken Maryam da itama tabude gaban motansu tashiga tana leken Farrah tana murmushi tamaida kofan tarufe.


Wani farin guy ne sol kaman balarabe zaune a driver seat yana sanye da suit brown hannunshi rikeda wani file hankalinshi gabaki daya na wajen yana karanta abin ciki, batare daya dagokai ba balle ya kalleta ba yace “who is she”? Kaman daga sama Miemie taji tambayan da Ya Habeeb yamata kuma tasan yamata tambayan ne sabida today is the first day tun last week data fara zuwa school dinan tajero tafito waje tareda wata tana murmushi, washe baki tayi jin tambayan da Ya Habeeb yamata tace “Ya Habeeb she’s my new friend her name is Farrah Muhammad Ganuwa, I call her Fairy, cus she’s as beautiful as all this fairies danike gani a cartoons” dan tabe baki Ya Habeeb yayi ya maida file din dayake karantawa ya rufe sanan ya ijiye yadago kanshi yazuba mata manya manyan idanunshi. Wow! Yanada wani kalan kyau kaman shi yayi kanshi, gashin kanshi baki sidik sun kwanta, yanada gashin gira dakeda cikan gaske baki kirin dashi yana wani kyalli, ga dogon hancinshi kaman shiya makala ma kanshi, wani dan karamin baki yakedashi dakenan ja, yanada saje mai kyau dakenan a kwance yazo yahade da dan gajeren black gemunshi, kamanninshi daya sak da Miemie saima haske dayaso yafita sosai, dan karamin bakinshi yabude yana kallon fuskanta yace “be careful with the kind of friends you make Miemie, you know I don’t like it” yay maganan yana maida hankalinshi kan motan dayake kokarin kunnawa, dan daure fuska tayi ashagwabe tace “I like Farrah Ya Habeeb a lot, she’s just definition of the kind of friend danake so, she’s cool, calm, batada surutu and tanada kirki sosai” dan juyowa yayi yakalleta ganin yanda take yaban wacce yau tafara ganinta sai kawai ya girgizakai batare dayace mata komi ba ganin ta gama zarewa, wani babban estate sukaje agaban wani babban gida yau horn aka budemusu gate suka shiga, parking yayi dasauri tafito tai gaba batare data jirashi ba.



Wani Babban falo tashiga, wata Babban mata ce dabazata wuce sa’an Mami ba zaune tareda wata mata suna magana, tana shiga da gudu tai wajen matan tace “oyoyo Mom” murmushi matan tayi tace “oyoyooo Miemie ya school” tashi tayi zaune tace “Mom I’ve finally made a friend today for the first time tunda muka dawo Nigeria” dan ware idanu Mom tayi tana kama baki tace “that girl must be special yanda kike da selecting abu dinan” Gyadamata kai tayi dasauri tace “sunanta Farrah Mom, tanada kirki, Mom she’s so beautiful Fulani ne su, Mom kinga gashinta kuwa gata da hank……” hadiye maganan tayi sabida Ya Habeeb daya bude kofan dakin yashigo wani mugun kallo yamata ahankali ta dudda kanta kasa sanan tadan kalli Matan dake zaune kusada Mom Yar Aiken Mom ne tasan kan Abuja Mom na ai kanta kasuwa da sauransu haka ahankali tace “ina yini Anty Lami” hararanta Anty Lami tayi tace “yanzu kika ganni” zatai magana Ya Habeeb yace “go upstairs and change kidawo kasa kici abinci” gyadamai kai tayi ahankali sanan ta tashi tana turo baki tai sama hararanshi Mom tayi tace “ka kiyayan mini yarinya fa Habeeb, yanda kake miskili haka kakeso ka maidamin da yarinya miskila, ga abincin ka a dinning” tashi yayi yace “I am not hungry Mom later” Anty Lami tace “matan Habeeb zatai fama baya iyacin abinci ko kadan” girgiza kai Mom tayi tace “ni harna gaji wlh Lami, dagashi har Miemie basa iyacin abinci wani zubin sainayi dagaske natasasu agaba nakasa na tsare sanan zan samu suci abinci, ita Miemie nata baya damuna sosai Dan ta iya kwadayi shiko kwata kwata Habeeb bayama son zaki bansan waya biyo ba dani da Baban shi munacin abinci” dariya Anty Lami tayi tace “Allah sarki Dakta, Allah dai yabiyashi ya rayamai yaranshi Habeeb da Miemie, ni babu abinda zan iya saka miki dashi Hajiya sai addu’a kawai nagode bari naje na karbo miki sakon” Gyadamata kai Mom tayi tace “kije da direba, bari nadubo Miemie najita shiru” dariya Anty Lami tayi tana bude kofa tace “yawuce tai bacci” sama Mom tayi zuwa dakin Miemie, bude kofan dakin tayi ahankali, Miemie na kwance kan gado daga ita sai white singlet da skirt din uniform dinta tana bacci hannunta rikeda pen ta rubuta sunan Farrah yakusan cika page din book dake kan gadon, hannu Mom tasaka ahankali ta dauki book din tareda karbe pen din, sunan Farrah ta kalla kafin ahankali tace “who are you Farrah? Diyata na sonki sosai” dan murmushi tayi ta maida book din tarufe sanan ta ijiye mata kan side drawer kafin taja bargo tarufa mata sanan tawuce tafita daGGga dakin.


💫 FARRAH💫



✍🏻M SHAKUR


EPISODE 2️⃣7️⃣

Saida tashiga cikin motan sanan tadan saci kallon Zayn, yana sanye da T-shirt fari kal, da 3quater maroon dasuka haska jikinshi, wani kalan hadadden kamshi natashi daga jikinshi kunnenshi daya yamakala wani diamond earring akai, waya yake danna waya kaman baisan mutum yashigo cikin motan ba, dauke kanta tayi tashiga wasa da yatsunta kaman bazata ce komiba saikuma ahankali tace “ina yini Ya Zayn!” Faduwa gabanshi yayi dum! Kiranshi da Ya Zayn data karayi janye idanunshi yayi daga wayanshi yadan kalleta gyalen kanta yadan zame baya hakan yasa yana iya ganin kitson da aka mata dayama kanta kyau sosai, dauke kanshi yayi dasauri kaman bazaice komiba murya chan kasa makoshi yace “wacece wannan yarinyar”? Wacece wannan yarinyar itama bama tagane hausan nashi ba wlh, gane kaman Maryam yake nufi yasa tadan saki cute smile tace “sunanta Maryam, Miemie, uhmmm uhmmm” tai maganan tana kokarin kiran sunan da Maryam tagaya mata saikuma da sauri tadagakai ta kalli Zayn din dake taba waya tace “B….F….F Uhmmmmmm…” tai shiru tana kokarin tunawa sanan dasauri tace “Bes…….” Dan dago kanshi Zayn yayi ya zubamata mayun idanunshi yana kallon effort din dayake putting on just to get the word, ayangance yace “Besty”? Gyadamai kai tayi ahankali tana hadiye murmushin datakeyi ganin idanunshi dataga sun wani kalan cikamata idanu, dauke kai yasakeyi ganin yanda tayi sanan ahankali yace “BFF means Best Friends Forever” sake gyadamai kai tayi sanan ahankali tace “ina sonta sosai” dan dago kanshi yayi yakalleta hada idanu sukayi atare dukansu kowa ya dauke kai tamaida kanta kan titi tana kallon hanya tana murmushi shikuma yana dan daddanna wayanshi, kaiwa gida sukayi ga aka bude musu gates din one bye one suna shiga harsuka karaso wanda zai sadasu to compound dinsu suka shige, Matayen Dad dukansu na zaune a garden sun kira wani spa home service ana musu gyaran farce, Mami ce tabude kofa tafito daga flat dinsu ganin motan Zayn yashigo, kafin ma abude mata kofan Farrah tabude kofan tafito rikeda jakan makarantan ta batare data dauki ledan uniform ba wani kalan murmushi tayi ganin Mami tafito dawani kalan sauri hade da gudu tai wajen Mami rungumeta tayi da karfi Mami ta kwashe da dariya tace “oyoyo oyoyo yarinta na tadawo daga school antafi da kuka andawo da dariya ko” boye fuskanta tayi acikin Mami tanadan dariya sanan tadago kanta tace “Mami nayi BFF sunanta Maryam, Besty na” ware idanu Mami tayi tace “Iyye jeki gaida su Hajiya saikizo muje daki kibani labarin” Mami tai magana tana nuna mata su Hajiya dake garden ana musu gyaran farce, karban jakan bayanta Mami tayi hakan yasa tawuce tana tafiya ahankali kanta akasa sabida yanda kowannen su kemata mugun kallo harda Hajiya Maryam Amaryan Alhaji dantunda taji labarin Alhaji yay adopting yarinya sanan Mami yakara bamawa taji ranta yabaci, tsugunnawa tayi agabansu ahankali sanan tace “ina yinin ku” gabaki dayansu babu wanda ya kalleta ma, Hajiya Maryam tace “Anty Mariya yaushe zamuje Dubai trip dinan” baki Farrah takara budewa ahankali zata kara gaidasu taji ance. “Farrah!” Faduwa gabanta yayi dasauri tajuyo da kanta, Zayn ne yana tsaye nisada su fuskanshi babu alamun murmushi yace “come here” tashi tayi ahankali tazo inda yake tsaye, wucewa hanyar dakin Mami yayi hakan yasa itama tabishi Hajiya Mariya tadaga murya tace “gantalalle wanda aka sameshi ta hanyar iskanci saisa yake dan iska, ubangiji Allah yasa ka kare ahaka” chak Farrah ta tsaya jin zagin da akamai juyowa tayi tabude baki zatai magana taji anfizgota afirgice tajuyo Zayn ne yajata yamata wani kalan mugun kallo binshi tayi suka shiga cikin dakin, Mami dake dinning murmushi tamusu dasauri Farrah tai wajenta tace “Mami wanchan matan nama Ya Zayn mugun addu’a” dan murmushin yake Mami tayi tace “Allah bazai amsa ba, zauna kici abinci saiki je kiyi wanka, Zayn” takira Zayn dake kokarin zama afalon tace “come and eat” tahowa yayi ahankali zuwa dinning din zubamai fried rice tayi da chicken ta tura gabanshi tace “please Zayn na sanka I don’t want more trouble kada kafadama Baban ka any of this kaji” dan kallonshi Farrah itama tayi, gGyadama Mami kai yayi sanan yasa spoon yafaracin abinci itama Mami ta zauna kusada Farrah tace “yi sauri ki cinye kibani labarin Maryam”


💫 FARRAH 💫


✍🏻M SHAKUR

THIS BOOK IS NOT FREE❌
Wanan littafin FARRAH 500 ne kacal.
Don magana dani M SHAKUR chat me up directly by clicking on this link;
wa.me/+2347012181461
DUK WANDA/WACCE TAKARANTA MIN LITTAFI BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA.


EPISODE 2️⃣8️⃣
Bayan 3 months
Farrah ta kile kaman ba itaba, tayi dan kiba taciko, Mami na kulada ita naban Mamaki, inba wayanda sukasan Mami ba ba’a banbance cewa Farrah ba yarta bace dan tamafi kama da ita kan Zayn dan Zayn bakin Baban shi yabiyo itakuma mani fara ce kaman Farrah.
Mami har tsoron brain din Farrah take yanda take gane karatu both Islamiya da boko, Mami na kulada ita na musamman har yanzu bata bari an bata waya ba cus tanaso ta natsu tai karatu kozata bari abata waya saitajai SS2, ta wayanta take waya da Miemie da yanzu suka bala’in shaku dudda haryau bata taba zuwa gidan su Miemie ba itama Miemie bata taba zuwa gidansu ba but babu wanda baisan kawancen su agidansu ba.
Farrah rabonta data saka Zayn a idanu harta manta tun ranan daya daukota daga school ita batasan inda yake ba kuma bata tambaya ba.


Yauma kaman kullum da sassafe tafito gidan ta gyara tass as usual ta kunna turare, saukowa tayi kasa tashiga kitchen taya Mami aiki dan yau Dady na wajenta Mami na ganinta tace “kinyi wanka” girgiza matakai tace “anjima zanyi zan tayaki girki ne Mami” dan hararanta Mami tayi tace “wuce kije kiyi wanka and get ready for school, keda zaku fara exam next week bacemin daga kitchen” wucewa tayi tafito daga kitchen din tana turo baki tai sama, wanka tashiga tafito ta shirya cikin uniform nata, jakanta tadauka tarike da beret da white sock nata da takalmin makaranta ta sauko kasa kalaban dake kanta ma lilo kaganta zaka dauka wata princess ne, ijiye komi tayi agefe sanan tazauna kan kujera tabude jakanta taciro wani book da pen tana karasa yin homework din da aka bata, fitowa Mami daga kitchen harta bude baki zata kwalamata kira tai shiru ganinta zaune afalo sanye da uniform dinta Riga da skirt tana rubutu looking serious, dan murmushi Mami tayi tabi jikinta da kallo, dayake saurin datake yasa bata gama rufe boturan riganta da kyau ba daganan inda Mami take she could see boobs dinta dan Farrah nada nono sosai, hakan yasa ta ijiye abinda ke hannunta tashigo falon tana kallonta tace “maisa baki saka white singlet naki ba” dago kanta tayi dasauri ta kalli Mami, dan ware idanu tayi tace “Mami na manta ne, Mami rikemin book dina bari naje nasa” karban book din Mami tayi itakuma tawuce dasauri tai sama bin book din tayi da kallo dan murmushi tayi she’s improving sosai a karatu da komi, handwriting dinta ne dai har yanzu sai ahankali rubutun ta baida kyau, murmushi Mami tayi jin sahun tafiyan Alhaji yasa tadago kanta takalli stairs wani cool smile yasakin mata yace “kinsan mesa nake sonki”? Girgizamai kai tayi daidai yakaraso gabanta yace “sabida akwai wani special care dakike bani, abincin dazanci dakanki kike shiga kitchen ki dafamin, koyaya kikaji motsi kinsan nawa kinsan wanda banawa ba sanan kina sona” murmushi tayi ta ijiye book din Farrah tace “zokaci abinci ba kanada meeting ba” Gyadamata kai yayi yace “eh inada shi daganan zanje na dauko Zayn a airport, an kwance daurin, sanan an kara running proper investigation he’s completely fine Alhamdulillah” ahankali Mami tace “Alhamdulillah” Shayin datake bashi yadauka ya kurba yace “kinsan menene yake cemin” dasauri Mami tace “a’a meyace” dan dariya Dad yayi sanan ya ijiye cup din yace “wai idan yadawo no more bodyguards tunda dai aka kama one of those kidnappers sauran sun gudu that he is safe yanzu nabarshi yayi yanda yaga dama” Mami dake sauraronshi tace “kabarshi to” dan hararan Mami yayi yace “me haka kike cewa” anatse Mami tace “Alhaji please start making Zayn looks responsible yadawo kace kayarda but yafara zuwa aiki, he should start managing company din, rashin barinshi yay komi yakesa yake rashin ji, get him engage in something zakaga ya natsu please Alhaji, I know yanda kakeson Zayn but kafara sashi yanayin da right thing” jin tafiya yasa duk suka juyo ganin Farrah ne yasa yace “come and sit and have breakfast yarinya na” Dad yay maganan cikeda wasa, zuwa tayi tana murmushi tazauna kusada kujeran Dad tace “good morning Abba” kanta yashafa yace “morning yarinyan Abba ya shirye shiryen exam, hope dake da Miemie ki kunadai karatu ba kawancen shashanci ba, dan inaso Dr dakikace min kinaso kizama kaman Mami ki inaso kizama” washe hakora Mami tayi tana kallonsu Farrah tace “ina karatu sosai Abba” shayinshi yabata yana murmushi yace “masha Allah ga shayi kisha, zuba mana pepper soup musha tare Mami” murmushi Mami tayi ta tashi tana zuba musu naturally Allah kawai yayi Alhaji mutum ne shi mai bala’in son yara, sai yanzu da Farrah tashigo gidan tagane bawai dan Zayn kadaine danshi yakemai Wanan kalan son ba shi kawai haka yakeson yara dan yanason Farrah itama sosai Farrah ma dazata barshi da itama yanda yabata Zayn haka zai bata ta sabida kawai yawanci Farrah bata saba gayamai tanason kaza kaza bane Ita Mami ita take gayama tanason this or that da tuni itama ya bata ta, saida suka gamaci sanan yace “jeki saka takalmin ki da safa yau dakaina zan saukeki a a school kafin nawuce meeting” sauka tayi daga kan kujeran tai tsalle tace “yessss! Yau Abba zaisan makarantan mu” tawuce dasauri duk suna mata dariya tashiga saka safan ta da takalmi, tashi Dad yayi yama Mami peck yace “muntafi” “adawo lpy Allah yabada sa’a, bye Farrah” bye Mami Farrah tai maganan tana gaba Alhaji biyeda ita abaya suka fito waje, Dad yace “muje kiraka ni dakin Hajiya Mariya na karbi wani file” gyadamai kai Farrah tayi suka wuce wajen tanamai hiran Maryam, kagansu saisun bala’in baka sha’awa, bude kofan dakin Hajiya Mariya yayi yashiga Farrah na biyedashi abaya suna zaune itada Layla suna breakfast tashi Layla tayi da sauri tace “ina kwana Dady” murmushi yamata yace “lafiya lau Layla manyan mata” Kallon Hajiya Farrah tayi data daure fuska ganinta tace “ina kwana Hajiya” wucewa sama tayi kaman batajita ba saigashi tadawo rikeda wani file din Alhaji yace “bakiji Farrah na gaidake bane kika mata shiru kin sanni fa banso ana wulakanta mini yara” hadiye wani abu daya tsayamata awuya Hajiya tayi ta kakalo murmushi tace “dayaushe ta gaidani sam banjiba kasan muryan Farrah tamu kaman na jarirai” tai maganan cikeda iya kissa tanakai hannunta kan fuskan Farrah tace “how are you beauty mu, za’a tafi school” wani kalan washe baki Alhaji yayi yakalli Farrah shima, dan murmushi Farrah tayi tana komawa baya tace ta gyadamata kai, Alhaji dake murmushi yace “mun tafi zan dropping nata off saina wuce,” adawo lpy, ficewa sukayi bodyguard yabude musu mota shiga sukayi sai school nasu Farrah sauketa Alhaji yayi daidai motan su Miemie nazuwa, dasauri ta kalli Alhaji tace “laaa ABBA gasu Miemie nan bari tazo ta gaidaka” dariya Alhaji yayi yace “to” dasauri Farrah tai wajen su motan Miemie daidai sunyi parking dawani kalan sauri tasa hannu tabude motan taduko tareda jan hannun Miemie tace “Miemie zoki gaida Abba” ware idanu Miemie tayi tace “Abba yana ina muje” tajuya dasauri takalli Ya Habeeb dake kallonta magana zatayi maganan ta makale batare data cire idanunta daga kanshi ba tace “Fairy greet Ya Habeeb” Farrah dake tsaye bama ta lurada Ya Habeeb ba jin maganan Miemie yasa ta duko ahankali tana murmushi takalli Ya Habeeb wanda yaune first time datake ganinshi hada idanu sukayi wani kalan faduwa gabanta yayi ganin kwayan idanunshi, ahankali lips dinta har rawa suke tace “go…….goood morning!” Bama tajira amsanshi ba tajuya dasauri sauka Miemie itama tayi tace “bye Ya Habeeb” tareda rufe kofan motan dasauri tabi bayan Farrah zuwa wajen motan Alhaji.

Yana ganin Miemie kafinma tagaidashi Alhaji yace “is this the famous Miemie da yarinyana keso” wani kalan kyalkyalewa da dariya Miemie tayi tace “Abba nima ina sonta sosai, good morning Abba” “morning Miemie haka nakeso kawancen arziki, you guys should study well exam starts next week and take care okay banda wasa” gyadama Alhaji kai sukayi sanan sukamai bye suka juya suka shiga cikin school hakanan Farrah samin kanta tayi da juyowa tana kallon inda su Miemie sukai parking motansu har lokacin motan na wurin.


The Wellness by Oriflame routine is designed to support your intake of protein, dietary fibre and micronutrients, in the right proportions, every day.


A = ACTIVATE
Set the foundation of your routine with vitamins, minerals and omega-3 fatty acids. These are needed every day to fill the nutritional gaps in your daily diet. You find them in our Wellness Multivitamin and mineral.

B = BUILD
Boost your defence system, and even build it over time, with the amazing Astaxanthin, together with bilberry extract and protein. Antioxidants are your active defense against environmental pollutants and help your body cope with a hectic lifestyle. Proteins help your body build new cells. You can find these in our Wellness Shakes.

C = CUSTOMISE
We all have individual needs depending on our age, lifestyle and general wellbeing. That’s why you should top up your routine with additional nutrition to feel and look your best. This includes using products like our Wellness soups and bars.



Meanwhile lemme all introduce you to supplement da I think we be solution to all problems na jikinmu.

Dukanmu nan munsan ORIFLAME is a reputable brand da aka sansu wajen wallafa abu mai kyau yanzu sunyi Supplement mai suna WELLNESS by

1 Comments On FARRAH
avatar
bertoul

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment