Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta farka jikinta sai rawa yakeyi zatai ihu kenan yayi sauri ya toshe mata baki. "ANISAH it's me your Dad, "Daddy meyafaru meye kakeyimin haka. A rude ANISAH take magana , "Shhhh kiyi shuru if not daddynki zaiyi fushi dake ANISAH. "Daddy please kabarni, abunda kake shirin aikatawa bamai kyau bane kuma Allah.... Ko kafin ta karasa ya fara kissing din lips dinta, dak'er ANISAH ta samu ta kwaci kanta suka fara zagaye a dakin. "Daddy please kada shetan ya zugaka kazo kana dana sani, " babu dana sani a ciki ANISAH idan baki rufamin asiriba to wa kikeso ya rufamin. Kuka kawai takeyi tana rokonshi, "Daddy don Allah kaji tsoron Allah. Matsowa ya keyi tanaja da baya , " ANISAH banaso in tursasa maki kawai kiyi abunda nikeso. Takalmi ta dauko mai tsini ta buga mashi a goshi, nan take ya dafe goshinshi da wannan damar tasamu ta bar dakin a guje ta fice direct wajen motoci ta nufa saida tayi kokarin budewa sai ta tuna bata fito da key ba. Haka tayi saurin ta karasa wajen gate dak'er ta samu mai gadi ya fito, "Hajia lafiya kuwa, " don Allah kayi sauri ka budemun gate. Tambayoyi ya tsaya ya nayi mata ita kuwa jikinta sai rawa ya keyi, hannu ANISAH tadaga ta sharara ma mai gadi mari, aibabu gardama ya bude mata kofa ta fice a guje. Tana fitane sai ga Daddynta ya biyota da gudu gashi goshin shi sai zubda jini yakeyi, cikin tashin hankali yake tambayar mai gadi, "Kai ina ANISAH take. Ganin Yanayin da Alhaji ya fitone ya sake bawa mai gadi tsoro, " Alhaji tazo tacemun inyi maza in bude mata kofa harda marina tayi. Alhaji bakin cikine ya isheshi yasa ke fallawa mai gadi mari, "Yi maza kaje ka kunna jiniya gaba daya yan gidan su tashi, shegu sai kace baccin mutuwa sukeyi. Da gudu mai gadi ya kunna jiniya alamun babu lafiya kenan, gaba daya yan aikin tashi sukayi cikin fargaba da tsoro suka fito waje inda Alhaji yake, ita kuwa Nanny Marwa tunda ta farka kai tsaye ta wuce dakin ANISAH amma da mamakinta sai taga bata ganta ba, itama fitowa waje tayi inda sauran mutane suke. Alhaji saida ya tara yan aikin kaf sannan ya fara magana cikin fada, " kunje kunata baccin banza duk abinda ya faru cikin Daren nan babu wanda zai iya bani labarinsa. Dukkansu dukar da kai sukayi, tsawa ya daka musu dahar saida Nanny Marwa ta razana, "Har ANISAH ta gudu a cikin Daren nan duk kuna bacci saboda kun sami gidan ubanku ko,. Ita kuwa Nanny duk ta kagara ya gama hargowan shi tai mishi tambayoyi, cigaba yayi da masifar shi, " idan akwai mai abun cewa to tun wuri ya fada don gobe da sassafe zaku koma inda kuka fito, Nanny da mai gadi ne kawai bazan koraba. TO_BE_CONTINUE!!! Dedicated_to_readers Written_by_seemaluvHAWAYEN_ANISAH Written by seemaluv Page(60_65) "Alhaji amma garin yaya kaji wannan ciwon a goshinka. Nanny ce tayi tambayar cikeda neman amsa. Daddyn ANISAH tunanin amsar dazai bata ya farayi, "Hmm na fito zanje kitchen domin insha ruwa sai ganin ANISAH nayi tana lambo zata fita, lokacinda nike kokarin hanata shine ta buga mun takalminta a goshi. Abunda Daddyn ANISAH ya fadane ya daurema Nanny kai," taya za'ace ANISAH tayi haka sai dai idan akwai wani abu ' Allah kadai yasan daidai. Haka Nanny ta fada a zuciyarta "To shikenan Alhaji insha Allah ANISAH zata bayyana zata dawo da kanta, Umarni yabasu da su wuce su koma ciki, bayan tafiyar sune ya daga waya ya kira commissioner of police ya sanar dashi cewa 'yarsa ANISAH ta gudu daga gida saboda haka ya tabbatar ya baza jami'an tsaro a nemota. Sannan commissioner ya tabbatar mishi da cewa nemo ANISAH kamar anyi angama ne, Bayan sun gama wayarne ya kira family doctor dinsu dayazo ya duba shi. Bangaren ANISAH kuwa tunda ta fito gida gudu kawai takeyi ba tareda tanada wajen zuwa ba, gashi ta bar wayanta a gida balle ta kira KAUSAR to kodama ta kira KAUSAR din mene zata ce mata. Tana cikin wannan tunanin ne sai jikake kararaf mota ta bige ANISAH, haka ta fadi a sume. Wani mutum ne a cikin Moran kyakkyawa mai kamala, cikin tashin hankali ya fito daga motarsa yayo kan ANISAH, " Subhanallah. Ganin bata numfashi ne yasa yayi gaggawan daukanta hannu bibbiyu ya ajeta a cikin mota shima ya shiga, asibiti ya tafi direct ba tareda yawani bata lokaci ba aka fara duba ANISAH. Bayan angama duba tane sai doctor yazo ya sameshi, "Alhamdulillah Barrister ASAD babu abunda ya sameta saidai dan buguwa ne datayi a kai, kuma shima wannan ba matsala bace zaka iya tafiya da ita idan ta farfado. Agogon hannun shi ya kalla yaga karfe 11:42pm sannan ya maida kallonshi ga doctor, " doctor gaskiya bana tunanin zan iya jira har sai ta farfado, idan babu matsala zan iya daukanta in tafi da ita ahaka. "Eh barrister wannan ba matsala ba ce gobe da safe zata farka insha Allah, idan anga akasin haka to kanemeni a waya. Barrister ASAD godiya yayiwa doctor, sannan doctor yasa two nurses su dauki ANISAH sukai mota. Bayan an shigar da ANISAH motane barrister ASAD yaja motarshi ya tafi. Barrister ASAD mai taimakon al'umma ne wajen bada gudun mawa ta hanyoyi daban daban, bashida mata haka zalika ya rasa iyayensa sakamakon wani hadarin jirgin sama da akayi, su uku kawai aka bari daga shi sai kannenshi, Hydar da humaira. Kasan cewar humaira sunan mahaifiyansu ne yasa ake kiranta da zoya. Kasan cewar barrister ASAD shine babba yasa shiyake daukan nauyin yan uwansa. Gudu barrister ASAD yakeyi don yau yayi lattin dawowa gida, yana isa bakin gate yayi Horn mai gadi yazo ya bude ' ita kuwa zoya data hana idonta bacci ta tsaya saitaga dawowan yayanta, da sauri ta fito jin horn din motarsa tun kafin ya karasa yin packing ta rigashi bude motar a shagwabe, "Yaya yau baka dawo da wuri ba inata jiranka. Da murmushi a fuskarsa ya fito daga Motan, "Uhm zoya ai nima ba laifina bane wani dan aiki na tsaya yi, Hannun shi ta kama tana kokarin janshi zuwa cikin gida, " wait ina hydar yake tukunna, "Yana dakinshi ya na danna laptop. "To yanzu kinsan wani abu, ki rikemun key din motan nan inciro wata bakuwa tukunna. "Okey, Key din ta karba tana jiran taga wace bakuwa ce dahar Sai an cirota. Barrister ASAD rungumo ANISAH yayi ya fito da ita, baki zoya ta saki sannan ta kulle motar tabi bayanshi ' yana shiga guestroom yaje ya kwantar da ANISAH sannan ya dawo parlor ya zauna, itadai zoya ido kawai ta zura mashi. Hydar ne ya shigo parlon yayi wa yayanshi sannu da dawowa, sai da suka zauna sannan ya fada masu duk abunda ya faru. Hydar ne yace, " to yanzu yaya ina yarinyar take, "Na kaita guestroom bacci takeyi sai gobe da safe zata farka. Zoya kuwa abunne ya dameta ganin beyi mata tsaraban komai ba, "Yaya ASAD yauma nasan cewa zakayi ka manta bakaimin tsaraba ba kuma. Barrister ASAD dafe kansa yayi, "ohh am very sorry zoya bansami lokaci bane. Haushine ya cika hydar jin abunda zoya tace, "Mtsww wai ke bakida hankaline ba kiga abunda ya faru dashi ba amma har kina wani tambayar sa tsaraba. Zunburo baki tayi ta tashi ta wuce daki tana gunguni. Hydar da barrister ASAD suma tashi sukayi kowa ya tafi daki don dare yayi sosai. TO_BE_CONTINUE!!! Dedicated_to_readers Written_by_seemaluv
Like � 2 � Reply � Edit � Nov 10HAWAYEN_ANISAH Written by seemaluv Page(70_75) Washe gari da sassafe zoya ta tashi ta shirya tasaka uniform taje parlor ' ta zauna ita tana jiran breakfast, ganin babu wanda ya tashine yasa ta wuce dakin hydar ta tasheshi don kada ta makara , "Yaya hydar katashi ka hadamun tea insha. Banza yayi ya kyaleta ya cigaba da baccin shi, "Yaya hydar na kusa makara fah. Farkawa yayi ranshi a bace, "Ke waike zoya common tea bazaki iya hadawa ba mtsww, muje dalla sauna kawai. Zoya zata kai shekara 12, hydar kuwa 20, barrister ASAD kuma 32. Tashi yayi rai abace sannan ya wuce kitchen ya hada mata tea ya bata, ko kafin ta gama har yashiga bathroom yayi wanka ya shirya. Fitowa parlor yayi kai tsaye ya dauki key din mota zoya ta bishi ya kaita school. Bayan tafiyansu hydar ne ANISAH ta farka daga bacci, a hankali take bude ido saida ta lura da inda take sannan ta tashi a firgice, tuna abinda ya faru da ita a daren jiya takeyi ' tashi tayi ta fara neman hanyan fita. Fitowa daga dakin tayi tayo parlor, tsayawa ANISAH tayi tana karewa parlon kallo. Wajen kalle kallenta ne ta hango kitchen da sauri ta karasa wajen don kishin ruwane ya isheta, haka ANISAH ta dunga buruntu a kitchen ita kadai. Barrister ASAD buruntun ne ya tadashi daga bacci, saukowa gado yayi dagashi sai three quarter ya shiga bathroom yayi brush sannan ya fito, Harda zai koma sai kuma yaji karar fashewan abu daga kitchen da hanzari ya fito don ya duba. Ya na shiga sai ganin ANISAH yayi a duke tanason ta kwashe barnan da tayi, tsayawa yayi yana karewa halittarta kallo yadda gashin kanta ya kwanta a gadon bayanta. "Wow beautiful lady, ANISAH jin maganar tayi kamar daga sama, a tsorace ta dago kai ta kalleshi. Mikewa tayi tsaye nan da nan jikinta ya fara rawa, "Don Allah kada ka cutar dani na rokeka. Murmushi kawai Barrister ASAD yayi cike da jin tausayinta,. "Uhm karki damu ni ba mai cuta bane, so kidaina kuka zo muje parlor. Ganin yanayinshi yasa ANISAH ta yarda dashi domin daga ganin shi tasan ba macuci ba ne. Suna isa yasami waje ya zauna itama zama tayi a gefenshi ta dukar da kanta kasa, shi kuwa Barrister ASAD kura mata ido yayi, ya yaba da kyawunta matuka, "Menene sunanki, Dago kai tayi ta kalleshi suka hada ido, tayi saurin mayar da kanta kasa, Motsi kawai takeyi da baki Kamar bazata iya magana ba, "Sunana ANISAH. "Ehem ANISAH wane, Kuka ta saka mashi nan take jikinta ya fara rawa don tasan indai tayi kuskuren fadan sunan mahaifinta, to tabbas zai maida ta gidane. Barrister lura yayi da hakan yasa ya tsaida tambayar tasa, "Calm down, stop crying bari in hada mana tea musha ko. Kai ta daga sannan ya yatashi ya tafi kitchen. SOME MINUTES LATER Ya dawo da cups biyu a hannunshi ya a jiye a dinning table, sannan ya kira ta don suyi breakfast. Zuwa tayi ta zauna duk jikinta bai gama yarda da gidan ba, haka suka rika kallon juna ita da Barrister ASAD. Rigar jikinta ne ta isheta da tsami kasancewar batayi wanka ba, kallonshi kawai ta rikayi bakinta Yana motsi alamun akwai magana. Barrister ASAD ne ya fahimci a kwai abunda takeson fadi, "ANISAH menene kikeson Fada. Maida kallonta tayi ga cup dinshi, "Dama so nakeyi in tambayeka sunan ka. Murmushi yayi mata, "sunana Barrister ASAD BALARABE and am proud of my name, Abunne ya bawa ANISAH dariya amma saidai ta danyi murmushi, "Nice name, am also proud of my name too. "Wow really to amma ai baki fadi haka ba dazu, Sunkuyar da kai kawai tayi tana murmushi, "Dama so nakeyi inyi wanka. "To shikenan tashi muje in nuna maki bathroom. Tashi tayi ta bishi, dakin zoya ya kaita sannan ya bata towel ya fita. Bayan fitanshi ANISAH ta daura towel din sannan ta shiga bathroom. Parlor Barrister ASAD ya koma ya kunna TV yasaka News, ji yayi ana cigiyar wata Yarinya yar shekara 17 ' Hakanne yayi daidai da shigowar Hydar. TO_BE_CONTINUE!!!! FOLLOW BACK AT.. Twitter @Real Safiyya Idris Instagram @safiyya_Idris Facebook @Real Safiyya Idris Love you more and more and more!!! Dedicated_to_readers Written_by_seemaluv
Like � 1 � Reply � Edit � NovHAWAYEN_ANISAH Written by seemaluv Page (80_85) Dama Barrister ASAD shi kawai yake jira don zai aikeshi hakan yasa Hankalin ASAD ya dawo kan Hydar, "Yawwa Hydar hope kayi breakfast. Hydar karasowa yayi cikin parlon ya zauna sannan ya amsa mashi, "Eh yaya nayi shiyasa kaga na dade a restaurant na tsaya. "Good, wait for me here ina zuwa. Kudi ya dauko 25,000 ya bawa Hydar, "Gashi ka shiga kasuwa ka zabo dogayen riguna daidai tsawonka na mata. Karba Hydar yayi, "yaya meza ayi dashi zoya fa bata rasa kaya ba . "No ba zoya zanbawa ba ANISAH ce zata sa, bakuwanda mukayi, "Ok. Fita Hydar yayi ya shiga mota ya wuce, Juyowanda Barrister ASAD yayi ne yaga ansaka hoton ANISAH amatsayin itace yarinyar da ta bace, nan take ya mike tsaye cikin mamaki , "Dama wannan itace ANISAH yarinyar Alh MURTALA BATURE, to me zaisa ta gudu daga gida. Haka ya rika yima kansa Tambayoyin da bashida amsarsu, ANISAH kuwa tana daki don ta dade da fitowa harta bushe babu kayan sawa. Hydar bashi ya dawo gida ba Sai wajen 2:00pm kasancewar ya biya school dinsu zoya ya daukota, saida suka biya restaurant ya saya masu abinci sannan ya koma gida. Sallama Hydar yayi sannan suka shigo, da gudu ZOYA taje wajen yayanta. HYDAR waje yasamu ya zauna da kaya a hannunshi, "Yaya kaga na dade ko, abinci na tsaya nasiya. "Ok ba damuwa ai, kabawa ZOYA kayan ANISAH takai mata don tundazu take jira. "To. Mikawa ZOYA yayi sannan ya umarceta da ta cire uniform dinta tazo suyi Lunch. ZOYA tana shiga dakin taga ANISAH a zaune sai kuka takeyi ganin Hakanne jikinta yayi sanyi, mika mata kayan tayi sannan ta fita. Haka ANISAH ta dauki doguwan riga guda daya ta saka, Rigar taimata kyau sosai . Fitowa parlor tayi ta gansu gaba dayansu a parlor, gabantane ya fadi dak'er ta karasa wajen ta zauna. Barrister ita kawai yake kallo don kayan jikinta sun amsheta sosai, "Naga kaya nagode sosai don naji dadinsu. Murmushi yayi sannan ya lura kamar tayi kuka, "My pleasure, amma ANISAH kukan mene kikeyi dahar idonki suka kumbura haka. Ajiyan zuciya tayi a gajiye, "babu komai nadanyi bacci ne shiyasa kaga haka, "Ok good, ANISAH inason magana dake but banason kuka aciki. Kai ta daga mashi kawai, sannan ya cewa ZOYA data koma daki ta huta, Hydar ne kawai yabari. "ANISAH dama ke yar Alhj MURTALA BATURE ne, Gabanta yayi mugun faduwa da sauri ta dago kai ta kalleshi idanunta gaf suke da suzubo da hawaye. Bakinta rawa kawai yakeyi kwata kwata ANISAH kasa magana tayi, shi kuwa Barrister ASAD bai fasa tambayanta ba. "To idan kuwa haka ne faduwa tazo daidai da zama, dole in maidaki wajen mahaifinki. Nan take ta sauka daga kan kujerar da take zaune kuka kawai takeyi mai sauti, sai wannan lokacin ne tasami damar yin magana. "Please Barrister kada ka maidani wajen shi zai cigaba da cutar dani, don Allah ka barni a wajenka. Cikin kuka ta karasa maganar. Barrister ASAD kukan da ANISAH takeyi har cikin zuciyanshi yake jinshi, amma babu yadda zaiyi he just want to help her. "ANISAH kukan da kikeyi bazai taimakeki ba saboda akanki har aka kama wani yaro mai suna SAMEER wai ana tunanin shine yasa kika gudu. Nan fa hankalinta ya sake tashi, " Ohno SAMEER is innocent, SAMEER bai cencenci haka ba wajen daddyna . "To kinga kuwa dole zaki natsu ki fadamun duk abunda yake faruwa. Ajiyar zuciya tayi ta share hawayen fuskarta sannan ta koma kan kujera ta zauna, Nan ANISAH ta bayyanar da duk wani alakarta tsakaninta da mahaifinta da duk wani abunda yake faruwa, da yadda akayi ta gudo daga gida. Abunne ya daurema Barrister kai, HYDAR kuwa mamakine ya isheshi yasa yabar parlon ya koma daki, "ANISAH ki daina kuka insha Allah matsalarki tazo karshe. "No bazan taba komawa wajen Daddyna bafa , idan kuma aka tursasamin to kashe kaina zanyi, "Subhanallah ANISAH baxaki kashe kanki ba, abinda nikeso dake shine, ranar Monday ne Alhj MURTALA Bature zai shigar da kara Court ' saboda haka dole zakije kiyi shaidarsa akan bashine ya sace kiba. "No i can't Daddyna zai halarci wajen idan ya ganni dole zai tafi dani, "Hmm ANISAH bashida wannan damar because Bayan kinyi shaidar SAMEER kema zaki iya shigar da kararki. ANISAH taji dadin shawarar da Barrister ASAD ya bata but still jikinta yayi sanyi, saboda har yanzu tanason Daddynta she still love him. TO_BE_CONTINUE!! Love you more and more and more!!! Dedicated_to_readers Written_by_seemaluvHAWAYEN_ANISAH Written by seemaluv Page(90_95) Barrister ASAD ya lura kamar ANISAH bataso ba, "ANISAH idan wannan shawarar batayi ba to I don't think akwai wata shawarar bayan wannan, "Aa naji dadin shawarar amma saidai ina ganin kamar bai dace inkai Daddyna karaba, Har yanzu inasonshi a matsayinshi na mahaifina. "Yes akwai wannan soyayyar amma don dole yasa zakiyi hakan. Hakadai Barrister ASAD ya cigaba da tattausawa ANISAH zuciyarta , Har yasamu ta yarda. A kwana a tashi har ANISAH tayi sabo da su Barrister ASAD don kuwa ta dauki ZOYA tamkar kanwarta jini daya. A haka Har Monday ta zagayo, ANISAH Sai zulumi takeyi saboda tunda Asuba ta tashi ' Bayan tayi sallah, ta kasa komawa bacci kallon bangaren ta tayi taga ZOYA sai baccinta takeyi hankalinta kwance. Tashinta tayi don tayi sallah sannan tayi wanka don yau take monday, saida ANISAH ta tabbatar ta shirya ZOYA sannan suka koma bacci Sai wajen 6:59am ANISAH ta farka. Sauka tayi daga kan gado ta nufi kitchen don shirya masu breakfast, sai da ta kammala komai sannan taje ta tashi HYDAR da ZOYA don suyi breakfast dawuri ya kaita school. ANISAH daki ta koma tashiga bathroom tayi wanka sannan ta shirya itama, koda tafito parlor ta iske har ZOYA ta tafi school. Kitchen ta shiga donta soya masu kwai ita da Barrister ASAD, Harta fara farfasa kwan taji kamar da mutum a bayanta, a tsorace ta juyo don jikinta bai bata ba ' juyowanda zatayi sai ganin Barrister ASAD tayi atsaye, Gaba daya tsorone ya kamata dasauri ta maida kallonta ga bowl din kwai, "Ina kwana yaya ASAD. Shi kuwa dadi taji don ta kirashi da yaya, "Lafiya kalau kanwata ANISAH. Ita jikinta sai rawa yakeyi don batason taga ta kebe da wani na miji, karfin hali tayi ta dauko onion (albasa) ta fara yayyankawa, "Yawwa kanwata ANISAH yau saidai kinyi sauri saboda zuwanmu court 9:00am ne. Kai kawai ta daga mashi don ta kosa ya Wuce ya bata waje, tana cikin hakanne bata ankara ba sai ganin jini tayi a hannunta, wani mugun zafine yake shiga cikin jikinta ' Nan take ANISAH ta saki wani kara, cikin tashin hankali Barrister ASAD ya karaso kusa da ita, rukota yayi hannu bibbiyu. "ANISAH lafiya, Yatsanda ta yankene ta nuna mashi cikin kuka. "Oh no kanwata garin yaya kika yanke haka, Ganin jinin yaki tsayawa ne yasa yakaita parlor da hanzari ya dauko first aid box yayi treating dinta, sannan jinin YA tsaya. Daura kanta yayi saman kirjinshi yana rike da hannun nata. Tsoron kada wani abu ya farune yasa ANISAH tayi saurin mikewa tsaye, "Ammm Yaya ASAD bari inje in karasa aikin da nikeyi tunda yanzu na warke. Girgiza mata kai yayi, . "No ANISAH BanyarDa ba ai da ciwo a hannunki, saboda haka dawo ki zauna. "But.... Saurin katseta yayi, " No but.. please kidawo ki zauna nizan shiga kitchen din O.K. Dawowa tayi ta zauna tana kallonshi yashiga kitchen koh 30minutes ba'ayi ba, YA fito da kayan breakfast. Ajiyewa yayi gaban ANISAH, "Oya lets eat lokaci YA kusa. Shima a tsaitsaye yaci sannan yaje yayi wanka YA shirya. Key din mota yadauko sannan suka fita, har suka wuce HYDAR bai dawo ba . Sai bayan shigarsu mota ne Barrister ASAD yaima HYDAR text da cewar sun fita, Ita kiwa ANISAH tunda suka kama hanyar duk jikinta yayi sanyi, tana cikin tunane tunane ne taji yayi packing dago kai tayi ta kalleshi, "Har mun iso wajen ne. "Eh Mun iso, Hadiye miyau tayi dak'er don ita kokadan batason haduwansu da Daddynta. Umarni Barrister yabata da tafito su shiga ciki don kamar Alkalin Bai iso ba. Haka ta fito suna taku dai dai, wani abokin shine ya taresu suka gaisa, "Kaima kazo wajen shari'an ne. "Eh mana nazo tareda my wife to be ne, Da sauri ANISAH ta kalleshi kallo na rashin fahimta, hada ido sukayi da Barrister ASAD yayi winking dinta Tai maza ta maida kanta kasa. Cikin Hole din suka shiga a front seat suka zauna. TO_BE_CONTINUE!!! Dedicated_to_readers Written_by_seemaluv
Like � 4 � Reply � Edit � NHAWAYEN_ANISAH Written by seemaluv Page(100_150) Basu dade da shiga wajen ba, waje ya cika da mutane. Police ne tafe da wanda ake kara, wato SAMEER, daure yake da ankwa a hannunsa jikinshi duk ciwo. ANISAH cike take da tausayin shi ' tashi tayi zataje wajenshi Barrister ASAD ya hana, hakan yasa ta koma ta zauna. Barrister ASAD tashi yayi don yaje yasaka kayansu na lawyers, domin kuwa shine mai kare wanda ake tuhuma wato SAMEER. "Ki zauna anan zandawo yanzu karki kula kowa, "Toh. SOME MINUTES LATER Dawowar shine tayi daidai da shigowar mahaifin ANISAH tareda ALKALI, da kuma shi lawyer mai tuhumar wanda ake kara. Mikewa kowa yayi Sai awannan lokacinne ANISAH tasan cewa lallai ALKALI ya karaso, Amma ga mamakinta sai ganin Barrister ASAD tayi yaje cen gaban seat dinta ya zauna, da alaman shine mai yake kare wanda ake tuhuma. Zama kowa yayi sannan itama ta zauna but still idonta yana kan Barrister ASAD, Ji kake cikin hole tsit. ALKALI takarda ya dauko, ya karanto duk laifin da ake zargin SAMEER ya aikata, "A yau Asabar 29/10/2016 karfe 10:30am, Ana zargin SAMEER cewar shine yasace tar Alhj MURTALA BATURE, ko lawyer mai tuhuma akwai abinda zai iya cewa, Lawyer mai tuhuma, "Malam SAMEER ko zaka iya fadawa kotu yaushene ganinka na karshe da ANISAH. Nan take bakin SAMEER yahau rawa ummanshi kawai yake kallo da take zaune, "Lokacinda naje gidansu shine ganina na karshe da ANISAH. "Very good, aranar da kaje gidan meyafaru? "Aranar mundan sami rashin fahimta tsakanina da mahaifinta. "Kozaka iya fadawa kotu wace irin rashin fahimta ka samu tsakaninka da mahaifinta, "Eh cewa yayi inrabu da yarsa Sannan kada insake shigo mashi gida. "Ok, a wannan lokacin saikaga bari kayi amfani da wannan damar kasace ita yarinyar domin kaci galaba akanta koh . Nan take Barrister ASAD ya mike tsaye, "Objection my lord bai kamata a tursasa shiba ya fadi abinda bai san yayi ba. ALKALI: "Korafi ya ansu, lawyer mai tuhuma a kiyaye, Lawyer cigaba yayi da tambayoyin shi, "Kana nufin kace ANISAH guduwa tayi da kanta? "Wallahi bani nasace ANISAH ba, wallahi bansan inda take ba. Lawyer mai tuhuma godiya yayiwa ALKALI sannan ya koma ya zauna, ALKALI:"Kunji abinda SAMEER ya ce saboda haka ko lawyer mai kare wanda ake tuhuma yanada abin cewa? Barrister ASAD tasowa yayi yaje gaban ALKALI ya tsaya, "Ya mai girma mai shariya ina rokon kotu data bani dama in fitar da kwakkwaran shaidana wacce zatayi nuni da SAMEER Bashine ya sace ANISAH Ba. ALKALI:"Kotu ta baka dama, Juyawa yayi kalli ANISAH sannan ya umarceta tazo, ANISAH tana mikewa sukayi ido hudu da mahaifinta, nan tsoro ya kamata. Haka take takowa ahankali har tazo wajen, shima Barrister ASAD komawa yayi ya zauna. Sannan ALKALI yafara yin mata tambayoyi, saida ANISAH ta gabatar da kanta tukunna, ta fara bayyanar da gaskiya cikin rawar murya. "Ba SAMEER yasaceni ba nine na gudu da kaina saboda wasu dalilai. Mahaifin ANISAH jin takamo hanyar tona mashi asiri ne yasa yayi saurin mikewa tsaye, "Ya mai girma mai sharia karya takeyi hada baki sukayi donta kubutar dashi. Warning ALKALI yayi mashi akan laifine kayi magana batareda izni ba, cikin rashin kwari ya koma ya zauna. Sannan ANISAH ta kara da cewa cikin kuka, "Inarokon kotu datayi mana hannun riga tsakanina da mahaifina. Nan take wajen yagame da hayaniya kowa mamakin ANISAH yakeyi, Shima ALKALI karan kanshi abun yabashi mamaki. "Yarinya ko zaki iya fadawa kotu dalili? Nan fa ANISAH ido ya raina fata juyawa tayi ta kalli Barrister Sannan ta kalli mahaifinta, "Bazan iya fadawa kotu dalilina ba nayin hakan. Nan hankalin mahaifinta ya kwanta, Barrister ASAD mikewa yayi yace, "Ina rokon kotu

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment