Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

data daga sharian nan saboda ANISAH yarinya ce karama tana bukatan tayi shawara da kanta. Nan take ALKALI ya buga tambari, "An daga wannan sharia zuwa wani sati. COURTTTTTTT!!!!"!!!!!!. Kowa tashi yayi saida ALKALI ya fara wucewa Sannan sauran Odiance suka fita. Barrister ASAD tasa ANISAH yayi a gaba gudun wata matsalar, har sunkai gaban motor zasu shiga ' sai Ji tayi ankira sunanta, "Little ANISAH , Da sauri ta juyo ta kalleshi, sunanshi ta kira a zuciyarta, "Daddy. Tabbas tayi kewarsa, sai kuma ta tuna cewa yanzu ba daddynta bane domin guje mashi shine mafita. "ANISAH kizo mutafi gida su Nanny MARWA duk sunyi kewar ki, "Don Allah kayi hakuri amma ni bazan bikaba , kuma ka gayawa Nanny nima nayi kewarta sosai to amma wannan. Barrister ASADA ta nuna da hannunta, "To shine uwata shine uban. Nan wajen ANISAH ta shige motor suka tafi ,suka bar Alhj MURTALA BATURE ana wajen ' shidai kawai fatanshi kada ANISAH ta tona mashi asiri!. TO_BE_CONTINUE!!! DEDICATED_TO_READERS WRITTEN_BY_SEEMALUV HAWAYEN_ANISAH Written by seemaluv Page(160_170) Juyawa yayi ya shige motarsa, ya tafi. Bangaren ANISAH kuwa cike take da damuwa, tabbas tayi kewar mahaifinta amma don dole zaisa ta nisanta dashi. Barrister ASAD ne ya lura da sauyawar fuskarta da alaman tana cikin damuwa, "Kanwata nasan irin yanayinda kike ciki, I can feel it but daurewa ya kamata kiyi domin kiyi abunda ya dace. Hawaye ne suka cika idonta basu kaiga zubowa ba, "Barrister hakuri yazama dole kabani and shawara ta rage gareni, but you can't feel the pain I'm feeling right now. Hawayenda ke cikin idonta suka zubo, duk da driving yakeyi saida ya ciro tissue paper ya bata ta goge hawayen. A haka suka isa gida, suna shigane Barrister ASAD ya tarad har HYDAR ya dauko ZOYA daga school, Oyoyo ZOYA tayi musu bayan tayi tsalle ta rungume ASAD, sannan ta koma kan ANISAH, but ANISAH batabi ta kantaba saboda halinda take ciki. Daki ta wuce fuuuuu, ZOYA ganin haka ta kalli Barrister ASAD, "Yaya me akaiwa Auntynah. Waje yasamu ya zauna, ya cire hulla ya ajiye agefe sannan yayiwa ZOYA smiling, "Jeki Wajen Auntynki ki taya ta fira, kila ki gano abinda akaimata. "Ok. Dakin ta bita don ko kadan ZOYA batason taga ran ANISAH ya baci. Shidai HYDAR ido kawai ya saka masu, kasancewar shi magana bata dame shiba , bayan tafiyan zoyane tasamu damar dago kai ya kalli yayanshi ASAD, "Yaya what wrong with her, ya sharian taku?. "Shariah ta tafi kamar yadda akeso Alhamdulillah, "Toh yaya yanaga ta dawo cikin fushi. "Mahaifinta ta gani shiyasa duk Hankalin ta yatashi, "Ayya. HYDAR maida hankalin shi yayi akan laptop dinshi, shikuwa Barrister ASAD tv ya kunna ya fara kallon news ' abundai babu hutu. Bangaren Mahaifin ANISAH kuwa tunda ya koma gida tunani kawai yakeyi, yaza ayi yadawo da ANISAH gida, "ANISAH dole ne zaki dawo gareni, ni Mahaifinki ne koma menene nakeyi miki dole hakan zaki jure. Haka ya rika zagaye cikin daki shikadai duk abin duniya ya dameshi, Nanny ce tayi knocking kofarsa sannan yabata izni data jirashi a parlor yana nan fitowa. Komawa parlon tayi ta zauna , bayan 5minutes ya fito parlon ya zauna suka fara magana, "Alhj ya aka kare a kotu? Ajiyar zuciya yayi kamar bazai bata amsa ba, saida ta kuma maimaita maganar sannan yadago kai ya kalleta, "Nanny MARWA andaga sharian ne, don kuwa ANISAH tazo wajen tayi shaidar SAMEER, kuma tazo da sabon al'amari. Mamakine ya cika Nanny MARWA ta dade tana maimaita maganar aranta, "Sabon al'amari kuma? To wane irin sabon al'amarine haka. Haka Alhj MURTALA BATURE ya fadawa MARWA komai. Haushine ya isheta ta mike tsaye, "Haba Alhj yanzu duk karfin ikonka ace, ka kasa dawo da ANISAH gida. Ganin yadda ta mike ta zakalkale tana yimashi magana ne abun ya bata mashi rai, "MARWA kisan a gaban wa kike, kuma kisan irin maganarda zaki yimun, ni mahaifin ANISAH ne nayi duk abunda zanyi don ganin na dawo da ita amma ANISAH ta gujemun. "To indai hakane kuwa, to lallai akwai alamar tambaya a cikin wannan al'amari, taya za ayi ace ta guje ma ubanta, Nan take ya mike tsaye yana huci, "Ke!!! MARWA wace alamar tambaya kikeso ki gano, idonfa kika faye zakewa toh sallamarki zanyi. Nanny MARWA murmushin takaici tayi, "Hmm Alhj kenan kaidai bakada girma saina jikinka to ka sallameni mana, daman na kosa domin duk abinda yake tsakaninka da yarka duk nasani ' kallonka kawai nakeyi, yanzu zan bar maka gidanka domin bazan iya zama dakai ba. TO_BE_CONTINUE!!! DEDICATEHAWAYEN_ANISAH Written by seemaluv Page(180_190) Tashi tayi ta wuce dakinta ta fara hada kayanta, bin bayanta yayi ya tarad tana hada kayanta, bata ankara ba taji anshake mata wuya. Nan take idanuwanta suka firfito, "Bazan kashe kiba amma inason ki bude kunnenki kiji abunda zan fada maki. Kai kawai Nanny MARWA take dagawa don kuwa ta kasa magana. Saida ya gama bata wuya sannan ya saketa, ta koma gefe tana maida numfashi, "MARWA kada kisake maganar nan tafita daga gidan nan, idan kuma ba haka ba to ki tabbatar saina kasheki. Kasa magana tayi saidai kai kawai daketa faman kadawa, "Saboda haka ki tattara kayanki ki barmin gidana. Hannu yasaka cikin aljihunsa ya ciro kudi bandir daya yabata sannan ya fice. Ai Nanny MARWA ko 5minutes bata bari tayi wasting ba agidan tabar mashi gidan shi. Bangaren ANISAH kuwa kwance take a daki, baccin karya tayiwa ZOYA don kuwa yau she is totally not in the mood, ZOYA kuwa ganin kamar ANISAH tayi bacci ne yasa ta koma wajen yayanta ASAD, tana zuwa parlon ta fada jikin shi, "Yaya, Aunt ANISAH tayi bacci, na bata hakuri kuma ta hakura. "Dagaske, "Eh. "Ok zauna anan wajen HYDAR bari inje insameta don nasan kunajin yunwa ko, . Da sauri ZOYA ta tsaidashi, "No yaya ni da yaya HYADAR bamujin yunwa, mun tsaya restaurant munci abinci dazu. Barrister ASAD kallon HYADAR yayi amma shi ko kadan baimasan sunayiba, "HYADAR i need your attention here, HYADAR juyowa yayi ya kalleshi, "Yaya menene. "Where is our food me&ANISAH, karkuma kafadamun cewa baka siyoba, "Am sorry yaya, gani nayi kamar tafison tayi dakanta thats the reason why ban tsaya na siya maku ba. Ranshi abace ya juya ya wuce, direct dakin ANISAH ya shiga. Kwance ya isketa tayi ruf da ciki tana wasa da y'an yatsunta, sunanta ya kira da sauri ta zabura ta zauna don ya bata tsoro sosai. Murmushi yayi don ganin irin zaburanda tayi, hakika idan tana cikin tsoro tafi kyau, "Sorry nasan kin tsorata sosai but i dont mean to. Dukar da kai tayi tana sauraron shi, . "Uhm nasandai yanzu kin gama fushin naki, so kizo mushiga kitchen munema abunda zamusa acikinmu , because ni bana wasa da yunwa. Dariyace ta kutto mata, da sauri ta riketa takuma bata rai. Shima barrister ASAD abun dariya yabashi yadda yaga tayi abu, takoma ta bata rai kamar ba ita tayi ba. "Idan kin gama dariyan kizo kitchen kusameni, nizanje infara blending kayan miyan. Bayan fitanshine ANISAH ta dago kanta sannan tarika godema Allah acikin zuciyarta, "Allah nagode maka dakasa na fado cikin gidan nan, a kullun idan ina tareda Barrister ASAD Sai inji all my worries melt out. Ajiyan zuciya tayi sannan ta tashi tabar dakin, kitchen ta wuce direct ta tadda shi haryayi blending kayan miya dube dube taga yanayi, "Yaya ASAD me kake nema. Tsayawa yayi ya rike kugu yadda kasan wani kuku, "Kanwa ANISAH groundnut oil din nan ne kuma banganshi ba. Murmushi tayi sannan ta dauko kujera ta ajiye tana shirin hawa sama, "Ai mangyadan yana saman cabinet ne. Ido kawai yabita dashi, ashe kujerar kafarta daya ya karye babu wanda ya lura cikinsu, hawanta keda wuya harta dauko garlon din tajuyo zata sauko ' nan take kujarar ta zame. ANISAH fadowa tayi jikin Barrister ASAD dukansu a kasa suka tsinci kansu, ANISAH kunya taji yadda taga tayi lame lame a jikinshi kasa tashi tayi. Shikuwa Barrister ASAD lura yayi da hakan yasa yakara gyara kwanciyar shi, jin hakan ne ANISAH tadago kai ta kalleshi suka hada ido, da hanzari tabar jikinshi. Shima tashi tsaye yayi, "Am sorry yaya ASAD bansan haka zai faruba daban hau ba. "Karki damu allah yasama bakiji ciwo ba ai. Kai tadaga mashi sannan tace, "please kabarmin komai inyi dakaina zanfi sauri. "Ok. Harya tafi sai yadawo, "ANISAH akwai maganarda zamuyi amma sai gobe kinji. Kai kawai tadaga mashi sannan ya tafi, harya fita bata daina kallonshi ba tana murmushi. TO BE CONTINUE!!! DEDICATED TO READERS WRITTEN BY SEEMALUV
Like � 4 � Reply � Edit � Nov 14D _TO_READERS WRITTEN _BY_SEEMALUVHAWAYEN_ANISAH Written by seemaluv . Page(200_210) Sai da ANISAH ta tabbatar ta kammala komai sannan ta kaiwa Barrister ASAD nashi, dayake indomie ce batada wahalan dafuwa. Harta juya zata tafi sai ya tsaida ita, "ANISAH na manta ban fada maki ba. Da sauri ta juyo ta kalleshi, "menene yaya ASAD, "Kinyi kyau ne yau. Rufe fuska tayi tana murmushi ta bar dakin, shima murmushi yayi sannan ya fara cin abinci. ANISAH parlor ta koma ta zauna bayan tagama cin abincinta, wasanni sukai tayi ita da zoya saida suka gaji sannan ANISAH ta tambayi ZOYA, "Baby ZOYA yanzu kina aji nawane a islamiya. "Laaaa aunty ANISAH ainayi sauka, ban dade dayin sauka ba ma ai. "Wow baby ZOYA at this age of yours? Gaskiya kinyi kokari. Murmushi ZOYA tayi, "Yes Aunt nayi kokari, kema at what age kikayi sauka? "Hmmm ZOYA ina ajin karshe a islamiyya Daddyna yahanani zuwa lokacin inada shekara 13, "Ouch!! Sorry aunt. Murmushi kawai ANISAH tayi Don batason ta tuna baya. Suna cikin hakane aka kira sallan magrib, da hanzari suka tashi don yin sallah. Bayan sun sallamene ANISAH ta tashi ta tafi wajen Barrister ASAD don tambayarsa abunda zata girka masu. Sallama tayi Sannan tashiga, zaune ta iskeshi yana danna laptop, yana ganinta ya kashe laptop din. "Lafiya dai kanwata, Dukar da kai tayi sannan ta ce, "yaya ASAD dama nazo tambayarka ne mene ne zan girka maku, don naga dare yayi. Mikewa yayi,"come on ANISAH, nibanason kina maida kanki tamkar wata yar aiki acikin gidan nan please, although kinada gata kuma bakiyi kalar wacce tasaba da wahala ba. Nan take hawaye suka cika idonta, "yaya ASAD kada ka famamin ciwon dake raina don Allah, banida kowa kuma banida komai inbanda ku... Jin yaddda muryanta ke rawa ne yasa yayi saurin karasowa wajenta, fuskarta yA dago da hannunsa. "Are you crying ANISAH?, am sorry I don't mean to make you cry. Share mata hawayen fuskarta yayi da hannunshi, "banason inganki kina kuka ANISAH , kije keda ZOYA ku shirya after isha'i saimu tafi restaurant kinji ko. "Ok. Kawai tace mashi sannan ta juya ta tafi. AFTER isha'i , ANISAH taci kwalliya ta sanya english wears riga da wando, sun lameta sosai ganin hakane yasa ta dauko jacket ta saka don yadan rufe mata jikinta kadan. Sannan ta ciro purple gele tayi rolling, irin shigarda ANISAH tayi shi ZOYA ma tayi amma duk da ZOYA yarinyace sunyi kyau sosai. Haka suka fito parlor suka iske HYDAR zaune yana kallon MBC MAX, mama kine ya cika ANISAH ganin HYDAR ko shiryawa beyiba, "HYDAR ba tare da kai zamuje restaurant bane? Da sauri HYDAR ya mike tsaye, "what? Restaurant shine yaya bai fadamun ba, wato har wata bare ta fini kenan koh, nibankai matsayinda za'ace in shiryaba kenan. ANISAH dukar da kanta tayi ganin batada abun cewa, ZOYA ranta kuwa inyayi dubu yabaci, "Haba yaya HYDAR meyasa zaka rika yiwa aunty ANISAH fada. Kafin ZOYA tagama rufe baki HYDAR ya dauketa da mari, a gigice ZOYA ta fasa uban ihu. Da sauri ANISAH ta rungumota, "haba HYDAR ZOYA yarinyace be kamata ka mareta ba. Hayaniyan ne tayi yawa yasa barrister ya fito cikin hanzari baima gama shiryawa ba. Yana zuwa yaga ANISAH rungume da ZOYA tana kuka , da sauri ASAD ya karbeta, "ANISAH meyasa ZOYA take kuka? Kasa bashi ansa tayi, da sauri ZOYA ta fada mashi duk abinda ya faru. Tsaki HYDAR yayi sannan yabar parlon ,dakinshi ya tafi direct ya kulle kanshi. Barrister ASAD binshi yayi ya dunga knocking kofar amma HYDAR yayi banza , "Yaya ni kakyaleni , tunda banida wani amfani a gidan nan, wai za'a fita amma akasa fadamun saidai inji abakin bare. Barrister ASAD mamaki ya cika shi, "HYDAR ka bude kofar please so that i can explain everything to you, "No ku tafi kawai yaya ASAD , you gave nothing to explain. Haka barrister ASAD ya koma parlor , ANISAH ya iske harta cenja kayan jikinta don kuwa tasan fitan bazai yuwuba. Waje yasamu ya zauna sannan yajawo ZOYA ajiki, "ZOYA yau bazamu fitaba sai gobe . "Yaya why? Barrister ASAD hada ido yayi da ANISAH don itama so takeyi taji dalili. "Because dare yayi sosai kuma inason inyi bacci . ZOYA zatayi magana kenan ANISAH ta katseta, "ZOYA muje ki cire kayan jikinki ki sanya na bacci. ANISAH tasata gaba tayi har zata wuce , ASAD yayi saurin rike mata hannu, "ZOYA tafi bari inyi magana da auntyn ki ko. Cewar ASAD, kai tadaga mashi sannan tayi tafiyar ta daki.. ANISAH kokari take taga ta kwace hannunta amma takasa,, haka ta hakura ta fuskan ceshi, "ANISAH kiyi hakuri da abunda ya faru a daren yau, kinsan halin HYDAR sabida bansanar dashi zamu fitaba shiyasa yake wannan fushin. "Uhm babu komai na fahimta , and please kadaina fadamun abu inhar baka sanar dashi ba, saboda ni barece acikin gidan nan . Murmushi yayi sosai sannan ya ce ," Ai kin kusa zama yar gida. Kallonshi tayi ido cikin ido amma sam takasa gane abunda yake nufi. Sake mata hannu yayi sannan ya umarceta data je ta kwanta. ANISAH tafiyarta tayi zuwa daki don itadai bawai ta fahimci abunda yake nufi bane, daki barrister ya tafi shima yana dariya. TO BE CONTINUE!!! DEDICATED TO READERS WRITTEN BY SEEMALUV.
Like � 3 � Reply � Edit � Nov 16HAWAYEN_ANISAH Written by seemaluv Page (211_212) Washe gari da sassafe Barrister ASAD yayi shirin tafiya Office, Bayan ya fito daga dakinshi ya tafi dakinsu ANISAH knocking kofar yafarayi sannan ya sanar mata da cewa shi ya wuce Office amma baxai dade ba. Cikin magagin bacci ANISAH ta tada ZOYA domin tayi wanka kuma tayi shirin tafiya school, ANISAH saida ta tabbatar ZOYA ta shirya sannan ta tashi ta nufi kitchen don hada mata breakfast. Saida ANISAH ta kammala komai sannan ZOYA tayi breakfast HYDAR yazo ya kaita School, Har HYDAR yakai bakin kofar fita ANISAH ta tsaidashi , "HYDAR inhada maka breakfast dinka yanzune kokuwa ba yanzu ba? Juyowa yayi yagama kare mata kallo ranshi abace,"ke angaya maki ni irin yaya ASAD ne, to kirike breakfast dinki. Tsaki yayi sannan ya juya ya wuce ' ANISAH yatsine tayi mashi don ita ko a jikinta , "cikin kane ba nawa ba. Itama zuwa tayi ta karya sannan ta kunna TV , tafara kallon horror film dukda ANISAH tanajin tsoro amma hakanan take daurewa kamar dole, tana cikin kallon ne taji anyi knocking kofa, duk tsoro yakamata tsayawa tayi tana nazari,"to waye zaizo a wannan lokacin, yaya ASAD da HYDAR dukansu da motor suka fita to waye. Jitayi ankuma yin knocking aibabu shiri ta nemi takalmi mai tsini ta ruke a hannunta, a hankali take takawa zuwa wajen kofar, tana bude kofar sai ganin Barrister ASAD tayi atsaye da sauri ta boye takalmin a bayanta, "Yaya ASAD sannu da dawowa, "yawwa. Ansa mata yayi cike da gajiya, karasowa yayi cikin parlon ya zauna sannan itama ta sami waje ta zauna. "Kanwata tun dazu nake tsaye abakin kofa ina kika je ne. ,"kallo nikeyi shiyasa banjiba, yaya ASAD ka karya kuwa. Wani shu'umin murmushi yayi mata sannan yace, "kanwata inajin yunwa amma bana abinci ba. Cike da mamaki tajuyo ta kalleshi fuskarta dauke da alaman tambaya, "yaya ASAD yunwar me kakeji komecece ka fadamun i am willing to cook anything you want. Kura mata ido yayi sannan ya sakar mata wani kalan kallo, kallonda ta kasa fassara abunda yake nufi. Dukar da kanta tayi kasa don tsigar jikinta taji yana tashi, "ANISAH yunwarki nakeji, ke nake so, ki taimakamin ki kashemin kishina. Nanfa gaban ANISAH ya fadi tsoronshi kawai taji tanaji, Barrister ASAD lura yayi da hakan yasa yatashi yaje ya zauna kusa da ita. Jin yadda gabanta ke faduwa ne abun yabashi mamaki, "kanwata relax please calm down, babu abinda zanmiki. "Yaya ASAD pls kada ka batamun rayuwa ni yarinyace don allah kaji tsoron Allah. Kallonta kawai yakeyi yadda yaga gaba daya a tsorace take,"ANISAH is not wat you think, ni bawai lalata nakeso inyi dake ba a'a , inason kine sona hakika so na aure, ANISAH don Allah ki amince dani. Tashi tayi da saurinta zata bar wajen yayi saurin fisgota da karfin tsiya, har saida ta fado jikinshi. Kara kankameta yayi nan take tafara kuka, "yaya ASAD don allah ka kyaleni, abunda kakeyi babu kyau. "Nasani ANISAH bazan daina ba harsai kince kina sona,kuma zaki aureni...Barrister ASAD bai gama rufe bakiba yaji anyi knocking kofa, da sauri ya saki ANISAH ta wuce daki da gudu tana shiga ta rufe dakin key, abakin gado ta zahna tana maida numfashi. TO BE CONTINUE!!! DEDICATED TO READERS WRITTEN BY SEEMALUV
Like � 2 � Reply � Edit � Nov 19HAWAYEN_ANISAH Written by seemaluv Page(213_214) Barrister ASAD tashi yayi cikin hanzari yaje ya bude kofar, ZOYA ya gani a tsaye ranta a bace,"ZOYA ina kuka tsaya yau baki dawo da wuri ba. Wuce warta tayi , bata ko amsa shiba saida ta tabbatar ta ganta a zaune tukunna tabi ta kanshi. "Yaya Gaskiya nagaji da abunda yaya HYDAR yakemin kawai ka samomin driver. Tsayawa yayi yana kallon yarinta irinta ZOYA, ganin bai amsata bane yasa ta dago kai ta kalleshi alamun shi take saurare,"ZOYA meyafaru da kikeson asami driver. Cire school bag dinta tayi daga bayanta ta ajiye agefe sannan tayi ajiyar zuciya, "yaya, Yaya HYDAR yau yawo yayitayi dani a motor dakuma wasu yan mata aciki, duk suka matseni. Tagumi yayi ya tsaya yana kallon ikon allah, "kada kidamu ni zanyi mashi magana, but maganan driver Gaskiya ZOYA kibarta ba yanzu ba. Tanajin ya fadi haka, ta tashi ta dauki schoolbag dinta ta wuce daki ba tare da ta ce mashi komai ba. Barrister ASAD tashi yayi yawuce dakinshi domin yawatsa ruwa a jikinshi, ZOYA murda hannun kofa tayi taji akulle ,"wai yau meke damun mutanen gidan nan ne, duk inda najd sai an batamun lokaci. Hannu tasa tafara buga kofar, da sauri ANISAH ta taso ta bude kofar domin tasan cewa ZOYA CE, murmushi ANISAH tayi mata sannan ta kama hannunta suka karasa cikin dakin, riga da skirt ta ciro mata domin ta cenja kayan jikinta. Har ANISAH ta juya zata bar dakin saikuma ta tuna cewa barrister ASAD ya na parlon, "ZOYA yayanki yana parlon ne haryanzu. Kai zoya ta girgiza mata alamun baya nan, hakan yabawa ANISAH kwarin gwiwan zuwa parlor domin tayi kallo. Bangaren ASAD kuwa haryayi wanka ya shirya shima parlon yakeso yaje. Yana fitowa suka hade da ANISAH a hanyar shiga parlor, ganin shine yasa tayi saurin juyawa zata koma daki Barrister ASAD ya tsaida ita. "ANISAH on monday zamu koma kotu, gobe kenan saboda haka ki zauna cikin shiri. Juyowa tayi ta kalleshi da manyan udanunta, "yaya ASAD gobe kenan fah, gashi ni bansan mezanje ince ba. Harya sa kafa zai wuce sai kuma ya tsaya jin abinda ANISAH tace, "ANISAH the decision now is yours, idan kinga dama zaki iya komawa wajen mahaifinki. Bai tsaya yaji abinda zata ceba yayi tafiyarsa, Nan fa ANISAH ta tsaya idanu cike da hawaye, kwatakwata bataji dadin abinda Barrister ASAD yace ba. "Meyasa bazai lallasheni ba, meyasa bazai bani shawara ba, amma kuma inda bai damu da halinda nake cikiba da bai bani masauki agidansa ba, hakan yanamin nuni da lallai yaya ASAD yana fushi dani. a sanyaye ta bishi parlon, zama tayi a kujerar dake facing dinshi suna kallon juna. TO BE CONTINUE!!! DEDICATED TO READERS WRITTEN BY SEEMALUV.
Like � 2 � Reply � Edit � Nov 20HAWAYEN_ANISAH Written by seemaluv Page(215_216) Ganin baya kallon tane yasa tadanyi gyaran murya,"yaya ASAD please can we talk? Banza yayi da ita ya ciro wayarshi yafara dubawa, kamar baiji abunda ta ce ba. Tashi tayi taje gaban TV ta dauki remote, ta kashe tv gaba daya domin ya fahimceta, but still kanshi yana kan wayarshi. Komawa tayi ta zauna ta cigaba da kallonsa, ganin ya tashi zai fita ne yasa itama tayi saurin mikewa tsaye,"yaya ASAD are you still mad at me? Harya juyo ya kalleta kamar zai tsaya sai kuma ya fice, har ya fita bata daina kallon kofarba. Jitayi ya tada mota yawuce, "ya ilahi, ni so nakeyi nayi magana dashi kafin goben, amma gashi yanata fushi dani. Haka ta hakura ta wuce daki cike da damuwa, tana shiga ta tadda ZOYA ta dauko book dinta zatayi assignment."yawwa aunty ANISAH dama ke nake jira, please can you assist me. Mika mata littafin tayi ANISAH ta karba ta duba, taji dadi sosai ganin subject dinda take so ne english. "Very good ZOYA tashi mutafi parlor muyi acen. Dukansu parlor suka tafi Sannan suka zauna ANISAH ta cigaba da nunawa ZOYA yadda zatayi, basuyi nisa ba ZOYA tayi insisting akan ta barmata haka nan, zata iya karasawa. Suna cikin hakan ne sukaji tsayawar motor, da hanzari ANISAH ta tashi ta leka ta window. Barrister ASAD ta gani yana kokarin fitowa daga motar. Dawowa tayi ta zauna kusa da ZOYA. Barrister ASAD ne ya budo kofa ya shigo, ganin yadda ANISAH ta zauna tana koyawa ZOYA assignment ne abun ya burgeshi, sallama yayi sannan ANISAH ta amsa cike da jin dadin ganinsa. Amma ko kadan baibi ta kanta ba, wajen ZOYA ya wuce direct domin ya tambaye ta ,"ZOYA, HYDAR har yanzu bai dawo ba koh? Kai ta daga mashi alamun eh, sannan tamaida kallonta ga littafin dake agabanta. Har zai wuce ANISA ta tsaidashi da cewa, "Yaya ASAD baka fadamun abinda zan girka ba saboda inaso inyi komai dawuri. Juyowa yayi ya fuskan ceta, "ANISAH me kikeso ince, ki girka koma mene ne indai anaci to kiyi since you insist to do so. Harya juya zai wuce tayi saurin tareshi, "yaya ASAD why are you avoiding me, menayi maka haka, just because na kasa baka amsar tambayarka shine zaka rika fushi dani haka, to yau zan fada maka abunda ke cikin zuciya ta. Jin hakan ne yasa barrister ASAD ya waiga ya kalli ZOYA yaga shi take kallo, "ANISAH dont say anything here, saboda ZOYA tana wajen. "And so? Ni bazanyi shuru ba yaya ASAD nagaji da kyaliyan da kakemin, YAYA ASAD inasonka wallahy inason ka with all my heart, tun ranarda ka kawoni cikin gidan kafara burgeni ' kuma a shirye nake da in aureka... hakan yayi daidai da shigowar HYDAr, jin ta fadi kalmar aure ne abun yayima HYDAR dadi sosai, "yawwa ANISAH dazaki taimaka ki aureshi da nima karan kaina naji dadi wallahy, domin tabbas kun dace da juna ' koya kika ce ZOYA, "yes yaya gaskiya ka auri aunty ANISAH tana debemin kewan mummy. Jin hakan ne yasa ANISAh tayi saurin rugawa zuwa daki tana shiga ta fada saman gado tunanin maganar HYDAR kawai takeyi, don kuwa abun ya daure mata kai sosai, yadda HYDAR ya yarda da maganar cikin dan kankanin lokaci. TO BE CONTINUE!!! DEDICATED TO READERS Written by seemaluv
Like � 3 � ReplyHAWAYEN_ANISAH Written by seemaluv Page(217_218) Around 4:30 ANISAH ta fito Daga daki, kitchen ta wuce direct domin ta san abunyi tun kafin lokaci ya kure. A gurguje ta daura sauwa sannan ta fito daga kitchen din, parlor ta nufa domin ta duba ZOYA don bataji motsinta ba, hango barrister ASAD tayi a zaune ita kuma ZOYA tana kwance ta dora kanta, a sama cinyanshi bacci kawai takeyi abunda. Kara sawa wajen tayi tasami waje ta zauna itama ta zurawa TV ido tana kallo, ko kallon Barrister ASAD batayi ba jin yayi gyaran murya ne yasa ta kara gyara zama, "ANISAH!. Juyowa tayi ta kalleshi batareda ta ce masa komai ba, "ANISAH

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment