Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin rumfar, na
zauna ina saye ina sayarwa.Amma
'yan uwana sai suka sayi haja mai
yawa, suka dauki ijarar jirgin ruwa
suka nufi wurin fatauci cikin duniya
nesa da garinmu. Na yi musu addu'a,
'Allah ka yi musu budi, ni kam na fi
so in zauna gida lafiya. Tsiya da
kwanciyar hankali ya fi arziki da
tashin hankali.' Na zauna tsawon
shekara guda cikin rumfata, tsawon
wannan lokaci kuwa Allah ya bude
mini kofofin arziki, na sami riba
ninkin-ba-ninkin, na tara dukiya
kamar yadda mahaifinmu ya bar
mana.Wata rana da hunturu, ana
zazzaga sanyi, ina zaune cikin
rumfata, na sanya riguna biyu, na
gashi mai taushi, masu tamanin
gaske, sai ga 'yan uwana sun zo gare
ni. Kowane daga cikinsu na sanye da
tsummar riga, duk ta kekkece har ana
ganin fatar jikinsu. Ga lebbansu sun
yi fari fat sun bushe, jikinsu sai
makyarkyata yakeyi saboda sanyin
da ke bugun su....
Admin
AA Misau Ke Magana
Suleiman Zidane Kd
HIKAYAR DAKO DA YAN MATA..
004. HIKAYAR DAN DAKO DA
YAN MATA
.
Copied
AA Misau Ke Magana
.
Labarin Saurayi Na Farko Mai Ido
Daya (2)
.
Saurayi na farko, mai ido daya, ya ci
gaba da ba da labarinsa da cewa:
“Lokacin da na gaya wa bappana
abin da ya faru da dansa, sai ya ce in
kai shi gidan da na bisne dan nasa
tare da matar nan, ko Allah ya datar
da mu da gane bigiren da na rufe su.
Muka tashi muka je gidan. Muna
zuwa, da dubawa haka, sai na shaida
wurin da kabarin nan yake, muka yi
farin ciki mai yawa.
Muka samu magirbi, muka tone
kasar, sai ga rufi ya bayyana, muka
cire shi sai ga tsani ya sauka kasan
ramin. Na tattaka tsani na sauka
kasa, gwargwadon tsawon ramin nan
zira’i hamsin, bappana ya biyo ni
daga baya. Yayin da muka riski
karshen tsani, muka sauka kasa, sai
ga wani hayaki ya bayyana bisa
garemu, sai na ji bappana ya fadi
kalmar nan da mafadinta ba shi
tsorata, ita ce, Innalillahi Wa’inna
Ilaihiraji’un!
Muka ci gaba da tafiya, sai ga mu a
cikin daki cikakke da abinci da kayan
marmari, da ruwan sha. Mun gani a
cikin dakin babban gado mai labule,
muka samu dan bappana kwance a
kan gado tare da matar nan da suka
shiga da ita cikin wannan rami, sun
zama bakin gawayi , suna rungume
da juna, ka ce su an jefa su cikin
rijiyar wuta.
Yayin da mahaifinsa ya ga haka,
fuska tasa ta sake, ya ce, “Haka ya
kamata da kai, ya kai daddauda,
wannan azabar duniya ce, saura
azabar lahira, ita ce mafi tsanani,
mafi wanzuwa.”
Yayin nan saurayi mai ido daya, ya
ce wa yarinya da sauran jama’ar da
ke sauraren labarinsa, “Kuna jin
zancena! Yayin nan bappana ya shuri
dansa da takalmi. Na ce da shi, abin
da suke ciki bai ishe ka ba har sai ka
shure shi da takalmi?”
Ya ce, “Ya dan dan uwana, wannan
da nawa, ya kasance a lokacin
kurciyarsa mai tsananin son yar
uwarsa, wannan da suke uwarsa, wannan da suke kwance
tare, na hane shi gare ta, ina cewa a
cikin raina don su yara ne, yayin da
suka girma barna za ta auku a
tsakaninsu. Na tsaya bisa ga haka.
Na tsawace su, tsawa mai tsanani, a
kan su rabu da son juna don babu
aure a tsakaninsu. Na tsare shi daga
gare ta, na tsare ta daga gare shi. Ita
kuma ta kasance ta na sonsa, so mai
tsanani. Shaidan ya tabbata
tsakaninsu. Shi ya yi wannan gidan
karkashin kasa a boye, ya tara abinci
a ciki, tamkar da ka gani, duk lokacin
da ya ga na shagala da wani abu, ko
na fita zuwa ga farauta, sai ya zo shi
da wannan yar uwa tasa, su boye
suna aikata abin da ransu ya kawata
musu.
Yayin nan ya yi kuka, muka yi kuka
tare da shi. Ya ce da ni, “Kai ne da na
maimakonsa!” Yayin nan na yi tunani
kadan na duniya da zantuttukanta da
al’amurranta, masu faruwa, na tuna
Waziri da yadda ya kashe ubana, ya
riki matsayinsa, ya cire mini idaniya
da gangan, da wannan dan bappah
nawa, da abin da ya same shi na
konewa shi da yar uwarsa.
Sannan muka hawo tsani, muka mai
da rufi, muka mayar da kasa, muka
aikata kabari tamkar yadda shi ke,
muka komo zuwa ga gidanmu.
Tun ba mu gama zaunawa ba, sai
muka ji bugun tambari, da ganguna
da algaitu, muka hangi masu da
takubban mayaka su na walkiya a
cikin rana. Duniya ta cika da kura,
karar kofatan dawaki da kukansu ya
gauraye ko’ina, hankulanmu su ka
kada, ba mu da labari.
Sarki ya tambayi labari, su waye
haka? Aka ce da shi, Wazirin dan
uwanka ne, ya tara askar da runduna
don shi abka maka da yaki, ya ci
birninka ba tare da kun shirya ba.
Domin shi yana jin tsoron ka sami
labarin ya kashe dan uwanka, ka
abka masa da yaki.
Koda na ji haka, sai na ji tsoro, na ce
a cikin raina, idan na sake na sake
fadawa hannun Waziri ba shakka zai
halaka ni. Bakin ciki ya rufe ni, na
tuna abubuwan da suka faru, na daga
musibu da suka abka wa mahaifina,
da dan bappana, na rasa yadda zan
yi.
Na tabbata idan mutanen Waziri suka
gan ni, za su shaida ni, su kama ni su
kai ni gabansa, ba ni samun daya da
zan tsira daga hannunsa. Sai na aske
gemuna, na sake tufafina, na fice
daga birnin na nufo wannan birni.
Wassalam, wannan shi ne labarina.
Yalla ko wani ya kai ni ga Sarkin
Musulmi Halifa, in labarta masa da
wannan hikaya tawa, da abin da ya
gudana gare ni. Na shigo wannan
birni a cikin wannan dare, na tsaya,
ina madimauci, ban san inda zan
nufa ba, sai ga wannan mai ido daya
yana tsaye. Na yi masa sallama, na
ce da shi ni bako ne! Ya ce da ni, ni
ma bako ne! Mu na cikin haka sai ga
wannan abokin namu, na uku ya zo
mana, ya yi sallama a garemu, ya ce
ni bako ne! Mu ka ce da shi mu ma
baki ne.
Muna tafiya duhu ya yi mana,
kaddara ta koro mu zuwa nan
gidanku, muka nemi masauki, kuka
saukar da mu, har abin da ya faru
yanzu ya faru. Wannan shi ne dalilin
rasa idaniyata ta hagu, da aske
gemuna da na yi.”
Suka yi mamakin zancensa, Halifa ya
kaikaici yan mata ya ce da Ja’afaru,
“Da dai ban taba jin tamkar abin da
ya gudana ga wannan saurayi ba.”
Yarinya Shugabar yam mata ta ce,
“Tube kanka daga igiya, ka kubutad
da ranka. Maza ka kama tafarkinka.”
Ya ce da ita “Ba ni tafiya, sai na ji
labarin wadan nan sauran mutane.”
Yayin nan saurayi na biyu, mai ido
daya, ya gabata gaban yam mata, ya
yi gaisuwa ga shugabarsu, ya ce “Ni
ba a haife ni da ido daya ba, akwai
abin mamaki mai yawa ga hikayata
wanda ya fi na wannan aboki nawa
da ya gama bayar da labarinsa.” Ya
fara bayar da labarinsa kamar
haka:
Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba
Admin AA Misau Ke Magana
WHATSAPP 08161272634
005. HIKAYAR DAN
DAKO DA YAN MATA
.
Copied
AA Misau Ke Magana
.
Labarin Saurayi
Na Biyu Mai
Ido Daya (1)
.
Saurayi na biyu mai ido
daya
ya gabata, ya yi gaisuwa ga
yarinya shugabar yam mata
sannan ya ce, “Ya shugabata,
ni ba a haifeni da ido daya ba,
akwai abin mamaki mai yawa ga
labarina. Da za a rubuta shi
da tsinin allura, a duba da
kaifin ido, da ya zama abin
lura ga masu hankali. Da farko dai ni
Dan Sarki ne
jikan Sarki. Na karanta
Alkur’ani bisa ga ruwaya
bakwai, na karanta littattafai
ga masu su, sannan wakoki, na
yi kokari a cikin dukkan saninsu, har
na tserewa
mutanen zamanina, na wuce
su. Sunana ya watsu, labarina ya
isa ga dukkan Sarakuna na
yankinmu. Sarkin Hindu ya ji
labarina, ya aika wa ubana
cewa yana son in tafi kasarsa
in kai masa ziyara, yalla ko sa karu
da wani yanki na daga
tarin ilimina. Ubana ya amince da
wannan
bukata ta Sarkin Hindu, ya
shirya mana jirage shida cike
da guzuri. Muka kama hanya
cikin bahar har tsawon wata
shida cikakku sannan muka isa bisa
tudu. Muka sauke kayanmu daga
cikin jirgi, muka labtawa
rakuma, muka tafi kadan-
kadan. Daga nan, sai muka
hangi kura ta daukaka, ta
tokare sararin samaniya. Da aka
jima, sa’a guda, sai ga
mahaya sittin sun bayyana a
gabanmu, duka zakokin fada
ne. Muka lura muka ishe su
duka Larabawa ne, mafasa
tafarki. Yayin da suka iso wurinmu,
ga
mu, mu jama’a kadan, muna
dauke da kaya niki-niki, sai
suka abka mana. Muka yi musu
ishara da cewa, mu manzanni
ne zuwa ga Sarkin Hindu, kada ku
cuce mu. Suka ce, mu ba mu
kasance karkashin hukuncinsa
ba, ballantana mu ji tsoronsa.
Suka kashe wasu daga
cikinmu, mu kuma saura muka
yi ta kammu, kowa ya kama
gabansa, muka bar wa ‘yan
fashi kayan. Na kasance ban san
inda zan
nufa ba, da ina Dan sarki
madaukaki amma yanzu cikin
sa’a guda na komo
wulakantacce. Na tafi har na
iso kan wani dutse, na shiga cikin
wani kogo na kwanta na
huta. Da rana ta fito, na ci gaba
da tafiya har na iso wani Birni
rayayye, cikakke da alheri,
lokacin tsananin dari ne, sai ka
ce damina domin ni’ima tasa da
kamshinsa, na yi farin ciki
da isowata wannan Birni. Saboda
tsananin gajiya da
tafiya da bakin cikin abin da
ya same ni da kurar hanya,
duka suka hadu suka canja
mini kama, idan an gan ni sai a
dauka wani miskini ne. Bayan na iso
Birnin, ban san inda zan
nufa ba, sai na karkata zuwa
ga gefensa, na ga madinki
cikin rumfa, na yi sallama gare
shi, ya mayad da sallama gare
ni. Ya yi mini shimfida. Ya tambaye ni
labarina. Na
labarta masa duka abin da ya
faru gare mu na daga mafasa. Bayan
ya ji labarina, ya
tausaya mini a kan abin da ya
faru, sannan ya ce da ni,
samari kada ka bayyana wa
kowa wannan labari naka,
domin ina ji maka tsoro ya kai ga
kunnen Sarkin wannan
Birni, domin kuwa shi ne
babban abokin gabar
mahaifinka, akwai wata fansa
da ya ke so ya dauka ga
mahaifinka, da kasarku da wannan
kasa ba a ga-maciji da
juna. Madinki ya halarta mini abinci
da abin sha, muka ci tare da
shi, muka zauna muna zance
har dare ya yi. Ya gyara mini
wani wuri kusa da turakarsa,
ya kawo mini abin da nake bukata
duka na daga shimfida
da abin rufa. Na zauna tare da
shi kwana uku, yayin nan ya
ce da ni, ba ka san wani aiki
da za ka fara yi ba a matsayin
sana’a domin samun abinci? Na ce
masa, ni almajiri ne, bayan
karatu ban san wata sana’a ba. Ya
ce, aikinka a cikin Birninmu
baya da martaba, babu wanda
ya san rubutu haka nan karatu,
kowa dukiya kawai ya sani.
Amma zan gaya maka wata
sana’a idan za ka iya yi. Na ce, wace
sana’a ce? Ya ce, ka
tashi, ka riki gatari da igiya, ka
tafi itace cikin daji, kaga da
wannan sana’a, mutane da
yawa sun yi arziki a cikin
wannan Birni. Na amince da wannan
zabi na
madinki. Ya hada ni da wasu
masu yin wannan sana’a,
sannan ya yi mini wasicci da
kada in gaya wa kowa
labarina ko asalina. Na fita tare da
su, na yiwo itace, na
komo da kaya bisa ga kaina,
na sayar da su rabin dinari, na
ci rabi na ajiye rabi. Na
dauwama bisa ga wannan hali
har tsawon shekara guda. Wata rana
na fita zuwa yin
itace, na zurfafa cikin daji ban
sani ba, sai na samu wata
matacciyar itaciya da itace da
yawa a kanta. Na shiga
karkashinta, na ga tamkar shuri mai
zuma, na tona
gefensa na gusad da kasar
kewayensa, na gan shi tamkar
katanga, na sara gatari bisa ga
kansa. Na ga rufi na farin
karfe, na share kasar daga nan sai ga
rufi na itace, na yaye
shi, tsani ya bayyana a
karkashinsa, na sauka zuwa ga
kasan tsanin sai ga kofa, na
shiga cikinta. Na ga soro mai
kyakkyawan gini da zane da lailaya.
Na ishe yarinya cikinsa, kai ka
ce an gina ta da lu’ulu’u, tana
sanyaya zuciyar mai bakin
ciki, tana tsarkaka tunanin mai
bacin zuciya. Yayin da na
dubeta, na yi sujuda ga mahaliccinta
domin abin da ya
bayar gare ta na daga kyawo
da cikar halitta. Ta yi duba zuwa gare
ni ta ce,
yalla kai mutum ne ko aljani?
Na ce da ita, ni mutum ne! Ta
ce da ni, wa ya sadar da kai ga
wannan bigiren da ni ke
cikinsa shekara goma sha daya ban
ga kowa na daga bil Adam
ba? Yayin da na ji zancenta, na ji
dadi a cikin raina na ce, ya
shugabata Allah ne ya kawo ni
zuwa ga wannan wuri, mai
yiwuwa ya yi nufin gusad da
abin da ke tare da ni na daga bakin
cikin rayuwa. Na labarta
ma ta hikayata tun daga farko
har karshe. Kafin na gama ba
ta labarina, tuni idanunta sun
cika da hawaye, saboda
tausayi. Ta ce da ni, lalle ka gamu da
jarabawar rayuwa
kwatankwacin irin tawa. Yarinya ta ci
gaba da cewa, ni
kuwa labarina shi ne, ni yar
Sarkin Hindu ce, mahaifina ya
aurar da ni ga dan bappah na,
ina ‘yar shekara goma sha
biyu. Daren amarcina, Ifiritu ya sace
ni, sunansa Jarjarisu dan
Rajimusu dan Ibilisa, ya kawo
ni cikin wannan wuri. Ya tara
mini dukkan abin da nake
bukata na daga tufafi da
kayan ado da na shimfida, da na
kayan abinci da abin sha. A
cikin kowane kwana goma, ya
kan zo ya kwana gare ni,
kwana daya. Amma idan ina
son ganinsa kafin lokacin, ya
ce in taba wadan nan sharuddan
rubutu na bisa
kubba da hannuna, yayin da na
shafa rubutun kafin in dauke
hannuna, ya bayyana. Yau kwanansa
hudu da tafiya,
sai ga ka na gani. Ko za ka
amince ka kwana biyar gare ni
kafin ya sake dawowa, ka
debe mini kewar rashin ganin
dan Adam na tsawon shekara goma
sha daya da ban yi ba?
Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba
Admin AA Misau Ke Magana
Suleiman Zidane Kd
006. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN
MATA
.
Copied
AA Misau Ke Magana
.
Labarin Saurayi Na Biyu Mai Ido
Daya (2)
.
Saurayi na biyu, mai ido daya, ya ci
gaba da
labarinsa da cewa:
“Sai na amince da bukatar yarinya,
‘yar Sarkin
Hindu wadda Ifiritu ya sace ta ya
boye a wannan
wuri da na same ta. Zan kwana biyar
a gare ta,
sannan in kama gabana kafin zuwan
Ifiritu.
Ta gabatar mini da abinci da
abinsha, muka ci,
muka sha tare da ita. Muka dade
muna zance,
tana mai matukar farin ciki da
kasancewata a
gare ta. Bayan mun gama zance, ta
ce da ni ka
kwanta ka huta ya shugabana, ka
kasance mai
aikin wahala ne. Ta kai ni wani daki,
ta nuna mini
gado, na hau na kwanta. Ban san
lokacin da barci
ya dauke ni ba saboda tsananin
gajiya.
Can da na farka daga barci, sai na
ishe yarinya
tana yi mini tausa ga kafafu, na
kiraye ta da
kyakkyawan suna, na gode mata, na
yi mata
addu’a a kan wannan karimci da take
nuna mini.
Ta ce, Wallahi ni na kasance mai
kunkuntar kirji
da zama wannan wuri ni kadai, cikin
karkashin
kasa, ba ni da abokin zance tsawon
shekaru. Na
gode Allahn da ya kawo ka gare ni.
Na kara yi mata godiya, sai kuma na
ji sonta ya
tabbata cikin zuciyata, fushina da
bacin raina, na
daga abin da ya same ni, ya yaye.
Muka zauna
muna zance, tsawon dare, daren da
babu
tamkarsa cikin raina.
Muka wayi gari muna masu farin
ciki. Na ce da
ita lalle ne sai na fitar da ita cikin
wannan wuri,
in hutar da ita da wannan aljani. Ta
yi dariya, ta
ce, “Ya shugabana, ka rufa wa kanka
asiri, mu yi
zamam mu a haka, cikin kwana
goma kana da
tara Ifiritu yana da daya, wannan ma
ai ya ishe
mu. Amma ina ji maka tsoron ka ce
za ka fitar da
ni daga wannan wuri.”
Da yake sonta ya riga ya mamaye
zuciyata, sai
na ce da ita, “Ki shafa rubutun kubbar
nan, ki
kirayi Ifiritu ya zo, ni kuwa na sare
kansa da
takobin nan in kubutar da ke daga
gareshi, ni na
saba da kisan Ifiritai.”
Koda yarinya ta ji zance na, sai ta yi
waka ta na
cewa, “Ya mai neman rabuwa, ka
jinkirta da
hilarka, ganinka ya ishe ni bege, hilarka, ganinka ya ishe ni bege, ka
hakura,
karshen haduwa rabuwakarshen haduwa rabuwa.”
Koda na ji wannan waka tata, ban
waiwaya zuwa
ga zancenta ba. Ban san lokacin da
na shuri
kubbar nan ba, shuri mai karfi. Da
yarinya ta ga
haka, sai ta rikice, ta fashe da kuka ta
ce,
“Wallahi ka cuce ni, amma ka yi
gaggawa ka
tserad da ranka, ka fita ta wurin da
ka shigo,
babu makawa tunda aka bugi kubbar
nan, yanzu
Ifiritu zai bayyana, ya ko halaka ka,
ya halaka ni.”
Don tsananin tsoro, ya shugabata, na
manta
takalmi na da gatari na a cikin ramin
nan. Yayin
da na hau mataka ta biyu, na
waiwaya don in
duba, na ga kasa ta kece, Ifiritu ya
fito mai
mummunar magana.
Na ji ya ce, me ya same ki, ki ka yi
kira na a
wannan lokaci? Ta ce, wani abu bai
same ni ba
face zuciyata ta kuntata, ina so in sha
abin shan
da zai sanyaya zuciyata. Na tashi
domin dauko
abinsha, sai na fadi bisa ga kubbar.
Ifiritu ya ce da ita, karya ki ke, fajira!
Ya duba
cikin soron sai ya ga gatarina da
takalmi, ya ce
da ita, wannan ba kayan mutum ba,
bil Adama.
Wa ya zo miki da su?
Yarinya ta ce, ni ban gan su ba face
yanzu da ka
shigo nan, wata kila kai ne ka shigo
da su, suna
a jikinka ba tare da ka sani ba.
Ya ce, karya ki ke, wannan zancen
banza ne, ba
shi yiwuwa gareni in shigo da wadan
nan kaya ba
tare da na sani ba. Amma da sannu
zan kamo
wanda ya shigo da su nan in zo miki
da shi.
Sannan ya tsiraita ta, ya daure ta
bisa ga
shisshinai hudu. Ya zama yana
azabtar da ita
domin ta fada masa gaskiya, amma
bai ji kukanta
ba. Ta yi kurum.
Na fito ta bisa ga tsanin ina
firgitacce, jikina na
rawa. Yayin da na taka doron kasa,
na mayar da
rufin ramin kamar yadda yake. Na yi
nadama bisa
ga abin da na aikata, gayar nadama.
Na tuna
yarinya da kyawunta, da yadda
wannan
la’anannen ke azabtar da ita bayan ta
kasance
tare da shi tsawon shekaru masu
yawa bai
azabta ta ba, sai ta sanadiyyar
zuwana gare ta.
Na tuna ubana da mulkinsa, da
yadda na zama
mai sai da itace, sai na waka
wannan baiti na ce:
“Idan zamani ya zo ma ka da musiba
wata rana,
wata rana ka ga sauki, wata rana ka
ga tsanani.”
Na tafi har na zo ga abokina madinki,
na same
shi yana hura wuta a gaban
rumfarsa, ya fito
waje yana duban hanyata. Da ya gan
ni, ya yi
murna ya ce, “Ni na kwana jiya ina
tunaninka ina
jin tsoron ko ka hadu da miyagun
namun daji ko
wani hatsari. Na gode Allah da ya
maido ka
lafiya.”
Na gode masa bisa ga tausayinsa da
kulawarsa a
gare ni. Na shiga cikin rumfata, na
zauna ina
tunanin abin da ya gudana gare ni,
ina zargin
kaina bisa ga shurin kubbar nan da
na yi.
Daga nan sai ga abokina madinki ya
shigo gare ni
ya ce, “Wani mutum, Ajami, ya zo
yana neman
ka, da gatarinka a gare shi da
takalminka. Ya ce
abokanka ne, masu saran icce suka
yiwo masa
kwatance da kai, bayan ya tsinci
gatarinka da
takalmi a daji, shi ne yanzu ya kawo
maka. Yana
nan zaune cikin rumfata yana
jiranka.”
Yayin da na ji wannan zance, nan
take kamata ta
sake, hankalina ya tashi, domin na
gane ko wane
ne Ajamin nan, ba kowa ba ne face
Ifiritu, ya
rikida mutum domin ya zo ya tafi da
ni ya hallaka
ni.
Ko kafin na bayyana wa madinki
halin da na ke
ciki, sai kasa ta tsage a gabanmu,
Ifiritu ya fito
ya sure ni, ya yi sama da ni, bayan
wani dan
lokaci kankane, ya komo kasa da ni,
sai ga mu a
cikin ramin nan, inda na tarar da
yarinya. Koda na
duba haka, sai na ga yarinya a daure,
tsirara, jini
na gudana daga gefenta. Idanuna
suka kada,
hawaye ya zubo mini.
Ifiritu ya rike ta, ya ce da ita, “Ya
munafuka, ba
wannan ne abin begenki ba?” Ta
dubo zuwa gare
ni ta ce da shi, “Ban san shi ba, ban
taba ganin
sa ba cikin raina, bai halatta ba gare
ni in yi
masa karya.”
Ifiritu ya ce, “Idan gaskiya ne
maganar da kike
fada, dauki takobi ki sare kansa.”
Ta dauki takobi, ta tsaya bisa ga
kaina, na yi
mata ishara da kundukuki na,
hawaye na gudu.
Ta yi mini ishara da cewa kai ne ka
aikata
wannan duka gare mu, da ba ka shuri
kubbar ba,
da yanzu muna nan hankalinmu
kwance. Ta daga
takobi sama za ta sare mini kai. Ta
jefar da ita
gefe, ta fadi kasa ta na kuka.
Yayin nan Ifiritu ya dauko takobi ya
mika mini, ya
ce da ni ka sare wuyanta ka kubutar
da kanka, in
sake ka, in dauke ka im mayar da kai
ga ubanka,
domin ni, na san labarinka duka. Na
riki takobi,
na gabata ga yarinya. Na daga takobi
sama zan
sare kanta, sai na ga hawaye na
gudana a
idanunta, sai takobi ya subuce daga
hannuna, ya
fadi kasa.
Na dubi Ifiritu na ce, “Ya kai Ifiritu,
mai girma,
sadaukin shugaba, idan har wannan
yarinya, mai
karamin hankali da tunani, ta kasa
sare mini kai,
ta yaya ni da hankalina zan sare
wuyanta ba tare
da laifin kome ba? Yadda bai halatta
gareta ta
sare wuyana ba, haka ba ya halatta
gare ni in
sare nata. Ba ni aikata haka har
abada.”
Ifiritu ya yi fushi, fushi mai tsanani,
kamarsa ta
juya, ya yi mana tsawa har sai da
kasa ta
girgiza, ya ce, “Kaiconku ya fajirai! Ya
tabbata ke
nan da so a tsakaninku, hakika sai na
yi muku
azaba, azaba mai tsanani wadda za
ku
gwammace da daya ya kashe daya
daga cikinku.
Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba
Admin AA Misau Ke Magana
08161272634
007. HIKAYAR DAN DAKO DA
YAN MATA
.
Copied
AA Misau Ke Magana
.
Labarin Saurayi Na Biyu Mai Ido
Daya (3)
.
Saurayi na biyu, mai ido daya, ya ci
gaba da labarta wa yarinya,
shugabar yam mata, da sauran
jama’a hikayarsa, da dalilin da ya sa
ya rasa idaniyarsa daya. Ya ce, “Kuna
jin zance na? Ya yin da Ifiritu ya ga
babu wanda zai iya kashe wani,
tsakanin ni da yarinya, sai ya ce,
kaiconku! Cewa tsakaninku da so! Ya
dauki takobi ya sare hannun yarinya
na dama, ya kuma sare na hagu,
sannan ya sare kafarta ta dama, ya
kuma sare ta hagu. Ni ko ina gani da
idona.
Na sakankance da mutuwata, na dubi
yarinya, ta yi ishara gare ni da idonta,
Ifiritu ya gan ta. Ya ce da ita, kin yi
zina da idonki! Ya sa takobi ya fille
kanta. Ya waiwayo zuwa gare ni, ya
ce, ya kai mutum, mu, ga shari’armu,
idan mace ta yi zina, kisanta ya
halatta gare mu. Wannan yarinya na
zaro ta cikin daren amarcinta, ta na
‘yar shekara goma sha biyu ba ta san
kowa ba, face ni.
Na kasance ina zuwa gareta sau
daya cikin kwanaki goma, na kan zo
mata ne a siffar mutum, Ba’ajamata ne a siffar mutum, Ba’ajami.
Yanzu na sakankance ta ha’ince ni,
shi ya sa na kasheta, amma kai bai
kamata ka ha’ince ni game da ita ba.
Amma babu makawa in wofinta ka, in
rabu da kai lafiya, amma ba ni kashe
ka.
Ifiritu ya tambaye ni, wace irin cuta
na ke so ya cuce ni? Na yi farin ciki
da murna mai yawa, na yi tsammani
ko zai yafe mini. Na ce da shi me zan
roke ka, ka yi mini? Ya ce, ka
tambaye ni, wace sura, cikin halittu,
ka ke so im mayar da kai? Ko kare, ko
jaki, ko biri, ko kuma wata sura
dabam?
Na ce da shi, ina tsammani za ka
yafe ni, ya kai shugaban aljannu, sai
Allah shi jikan ka. Na marairaita gare
shi gayar marairaita, ina rokonsa
yafuwa.
Ya ce da ni, kada ka tsawaita mini
magana, amma kada ka ji tsoron
kisa, don ba zan kashe ka ba, amma
ba ni yafe maka har abada. Babu
makawa in sihirce ka. Ya dauke ni, ya
kada da ni zuwa ga bisa, har na ga
duniya daga karkashina, ka ce ita
kwaryar ruwa ce. Yayin nan ya sauko
kasa da ni, ya ajiye ni bisa ga dutse,
ya debo ruwa kadan, ya gama da
kasar bisa dutsen, ya karanta wani
zance, wanda ban fahimta ba, cikin
ruwan, ya watsa mini shi, ya ce, fita
daga wannan sura zuwa ga surar biri
a cikin wannan lokaci! Nan take na
rikide, na zama biri, mai shekara
dari.
Lokacin da na ga kaina cikin wannan
mummunar sura, na yi kuka bisa ga
raina, na hakura bisa ga karkatar
zamani, na sani zamani bai bar kowa
ba. Na gangaro daga saman dutsen
zuwa ga karkashinsa, na yi tafiya
wata guda cur, sannan na iso bakin
gabar Baharal Maliha, na tsaya sa’a
guda, sai na hango jirgi a tsakiyar
Bahar, iska ta yi masa kyawo, ya nufo
tudu.
Bayan jirgin ya dangana jikinsa da
kasa, sai na lababo na shige ciki. Da
mutanen ciki suka gan ni, sai daya
daga cikinsu ya ce, mu fitad da
wannan shu’umi daga jirgimmu.
Wani ya ce, mu kashe shi! Wani kuma
ya ce, tsaya in kashe shi da wannan
takobi! Ya zaro takobi. Na yi kuka har
hawayena ya gudana. Babbansu ya ji
tausayina, ya ce, ya fatake, ku sani,
wannan biri ya nemi ceto gare ni, don
haka na cece shi, ku bar shi cikin
kuyangi na, kada kowa ya cuce shi.
Yayin nan uban tafiya ya kasance
yana kyautata mini, komai na fada
masa yakan fahimta, ina biya masa
bukatarsa zuwa ko ina. Ina bauta
masa cikin jirgi.
Jirgi ya dace da yanayin Bahar mai
dadi, bayan kwana hamsin, muka isa
wani Birni mai girma da yawan
jama’a, babu mai sanin adadinsu
face Allah, Madaukakin Sarki. Da
muka iso, muka tsayar da jirgimmu,
sai ga masinjojin Sarkin garin. Suka
shiga cikin jirgi suna yi wa mutane
maraba da zuwa, sannan kuma suka
ce, Sarki ya aiko mu zuwa gare ku da
wadan nan takardu, ko wanne
dayanku shi rubuta shadara na
jawabin kayansa.
Na tashi, ina cikin surar biri, na karbi
takardu a hannunsu, suka ji tsoron
kada in yayyaga su, in zuba cikin
ruwa, suka hanani, suka nemi su
kashe ni. Na yi musu ishara da cewa,
ni ma zan rubuta. Uban tafiyar mu ya
ce, ku barshi, shi rubuta! In ya
yayyaga takardun, ko ya bata
rubutun, mu kore shi daga gare mu,
in ya kyauta mu rike shi. Yalla ni, ban
taba ganin biri mai fahimta irin tasa
ba.
Aka ba ni takarda, na riki alkalami na
sa a cikin taddawa, na rubuta
shadara, na tsara wannan waka ina
cewa, “Hakika Allah ya rabanta ni,
zamani ya hukunta alherinsa gare ni
bayan mugunta tasa. Ya uban tafiya,
alherinka gareni ba ya kidayuwa,
Allah ba ya maraita talikkai idan
kana nan, cewa kai, alherinka ya
mayi mamayin uba.”
Sannan kuma na rubuta, “Idan an
bude taddawar daukaka da ni’ima, ka
tsoma alkalaminka na daga baiwa da
karimci, ka rubuta alheri, in ka
kasance mai iko, da haka nan ake
daukaka madaukakiyar daraja.”
Bayan na gama rubutu, na mika
musu takarda. Masinjoji suka tattara
takardu, suka tafi da su zuwa ga
Sarki. Lokacin da Sarki ya karanta
abinda ke cikin dukkan takardun nan,
rubutun kowa bai kayatar da shi ba
face rubutuna.
Sarki ya ce da masinjojinsa, ku tafi
ga wanda ya yi wannan rubutu, ku
tufasassheshi wannan riga, ku hawar
da shi bisa ga alfadara, ku zo da shi
da kida, ku hallaro shi gabana.
Ko da masinjoji suka ji zancen Sarki,
sai suka yi murmushi. Da Sarki ya ga
haka, sai yayi fushi, ya ce, yaya zan
umurce ku da umurni na daga bakina,
ku yi mini dariya?
Suka ce, ya Sarki, ba mu yi dariya ga
zancenka ba, face da cewa, wanda ya
rubuta wannan takarda ba mutum ba
ne, biri ne, yana tare da shugaban
masu jirgin.
Sarki yayi al’ajabin zancensu, ya yi
nishadi da farin ciki, ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment