Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce, ina so in
sayi wannan biri, mai hikima da
ilimi. Ya aika manzanni zuwa ga
shugaban jirgi da alfadara, da tufafi,
ya ce, babu makawa a tufatar da birin
nan a aza shi bisa alfadara, a zo mini
da shi, da kade-kade da bushe-
bushe.
Da manzanni suka ji haka, suka
fuskanta zuwa ga mai jirgi, suka riko
ni daga gareshi, suka sa mini tufafi
na alfarma, aka aza ni bisa alfadara,
ana yi mini kida da busa. Mutanen
cikin jirgi suka dimauta da ganin
haka, suka zama suna kallona cikin
mamaki.
Yayin da na tsinkayo fada, na yi farin
ciki, aka kawo ni gaban Sarki. Yayin
da na gan shi, sai na durkusa na
gayar da shi sannan na zauna bisa
ga gwiwowina. Fadawa suka yi
al’ajibin ladabina. Sarki ya zura min
ido cikin mamaki da wannan abu da
na yi.
Sarki ya umurci mutane da su watse
daga fada, duka suka watse, wani bai
yi saura ba a cikin fadar face ni da
Sarki, da kuyangi, da kananan bayi.
Sarki ya yi umurni da a kawo abinci
da abinsha. Aka hallaro da su da
gaggawa. Aka gabatar da kabaki da
dukkan abin da rai ke sha’awa ke jin
dadi a cikinsa, abin kallo ga ido.
Sarki yayi ishara gareni da cewa in ci.
Na tashi na durkusa, na yi godiya,
yayin nan na zauna ina cin abinci
tare da shi. Na ci ya isheni, na wanke
hannuwana, na dauki takarda da
alkalami da taddawa na rubuta
wannan waka, na ce: ” Yau na ci
tsokar rago, maganin dukan
ciwarwata, na ga kabakin da abin
marmari ke cikinsa, matukar buri. Ya
bakin cikin zuciyata bisa ga wannan
kabaki, yayin da na ishe shi da abin
da ban sani ba, an darwaye shi da
mai gami da zuma.”
Sarki ya duba abin da na rubuta, ya
karanta shi, ya yi al’ajibi da shi, ya
ce, lalle akwai ga biri wannan fasaha
da wannan rubutu, hakika ban taba
ganin dabba mai hankali da kuma
hikama tamkar wannan biri ba. Yayin
nan ya gabatad da dara, ya ce da ni,
ka iya wannan wasa? Na yi ishara da
kai na, na ce, na’am!
Na gabata na jeranta dara dai dai
sahunta, muka yi wasa da shi sau
biyu, na rinjaye shi. Hankalin Sarki
ya tashi, ya ce, hakika wannan da bil
Adam ne, da ya fi dukan mutanen
zamaninsa ilimi da fasaha. Yayin
nan ya ce da wata kuyangarsa, ki tafi
zuwa ga shugabarki, ki ce da ita,
Sarki ya ce, ta zo ta yi wasa da
wannan biri ta yi kallon abin al’ajibi!
Kuyanga ta tafi, ta dawo tare da
shugabarta, ‘yar Sarki. Koda ta shigo
ta gan ni sai ta rufe jikinta ta ce, ya
mahaifina, ta yaya za ka aika mini in
zo in ga maza, ajanabai? Ya ce, ya
‘yata, babu wani namiji a nan sai ni,
sai ko wannan biri, wadan nan saura
kuma duka kuyangin ki ne. Wa kike
rufewa jikin ki a nan?
Ta ce, wannan biri dan Sarki ne,
sunan ubansa, Imar, ma’abucin
jazirorin Labunus, an sihirce shi ne
biri. Ba kowa ne ya sihirce shi ba face
Ifiritu wanda ake kira Jarjarisu na
daga zuri’ar Ibilisa. Amma wannan
ba biri ne ba, cewa shi namiji ne,
masani, mai hankali.
Sarki ya yi al’ajibin wannan zance na
‘ya tasa, ya dubo zuwa gare ni, ya ce,
yalla abin nan da ta fada mini
gaskiya ne? Na ce da kaina, na’am!
Sarki ya ce ma ‘ya tasa, A ina kika
san shi? Da kaka kika sani shi
sihirtachche ne? Ta ce, Ya ubana,
tsohuwa ta kasance a gare ni tun ina
yarinya, makira, sahira, ta sanashshe
ni sana’ar sihiri, na boye shi, na
tsoraci Allah, Ubangijina, amma na
kiyaye shi. Na san kofa dari da
saba’in daga kofofin sihiri, mafi
karanta daga kofofin nan in cire
duwatsun Birninka, in jefa su bayan
Dutsin Kaf, im maishe shi kogi, im
mai da mazaunansa kifi a cikin
kogin.
Ubanta ya ce da ita, Don girman
sunan Allah, mai-girma, ki kubutad
da wannan yaro, in sa shi Wazirina.
Yalla kina da wan nan alheri, wata
kila shi amfane ki? Idan kin kubutad
da shi, in sa shi Waziri, domin shi
saurayi ne, mai mukami, da hankali.
Ta ce da shi, So da girmamawa!
Yayin nan ta rike wuka rubutacciya
da sunannakin Ibraniya, ta zana da
ita hatimi a cikin tsakar soron, ta
rubuta sunannaki a cikinsa da
dalamusai, ta yi anniya da wani
zance, tana karatu da halshen da ba
shi fahimtuwa. Bayan jimawa jihohin
soro suka duhunta gare mu, har
muka zaci duniya ta nade bisa ga
kammu. Daga nan sai ga Ifiritu ya
bayyano bisa gare mu cikin
mugunyar sura da hannuwa kamar
reshe, da Kafafu tamkar soraye, da
idanduna tamkar murhun da aka hura
wuta a cikinsa.
Muka firgita da shi. ‘Yar Sarki ta ce,
Babu maraba gare ka, babu farin ciki!
Ifiritu ya ce, Ya ha’ina, yaya kika
ha’inci rantsuwa? Ba mun rantse
bisa ga babu mai-bijiram ma wani,
ni da ke ba? Tace, Ya la’ananne, ina
kai, balle rantsuwarka? Ifiritu ya yi
kururuwa har sai da kasa ta girgiza
kamar za ta tsage, ya juye siffar zaki
ya tasam ma yarinya ‘yar sarki zai
halaka ta.
Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba
Admin AA Misau Ke Magana
Suleiman Zidane Kd
008. HIKAYAR DAN
DAKO DA YAN MATA
.
Labarin Saurayi
Na Biyu Mai
Ido Daya (4)
.

Admin
AA Misau Ke Magana
.
Saurayi na biyu, mai ido
daya,
ya ci gaba da ba da labarinsa,
ya ce: Yayin da Ifiritu ya rikida
zuwa siffar zaki ya tasar wa
yarinya, ‘yar Sarki, bakinsa a
bude zai halaka ta. Yarinya ta yi
gaggawa ta ciri gashi daya
daga gashin kanta, ta shafe shi
da yawun bakinta, nan take ya
zama takobi, mai zarcewa, ta
sare wannan zaki, ya rabu
biyu. Nan take ya koma Ifiritu, ya
hade wuri daya. Yarinya kuma ta juye
macijiya,
mai girma, ta zabura bisa ga
wannan la’ananne. Suka yi
fada, fada mai tsanani. Da
Ifiritu ya ga yarinya ta kusa ta
rinjaye shi, sai ya rikida ya zama
tsibiri a tsakiyar tabki,
da kuraye a kan tsibirin.
Yarinya kuma ta zama iska,
mai karfi, ta kafe wannan
tabki, sannan kuma ta zama
mazaje tamkar mutum dari, kowanne
rike da makami,
suka taru suka karkashe
wadannan kuraye. Da Ifiritu ya ga ba
dama, sai ya
zama kwayoyin hatsi, a
barbaje, ko ina. Yarinya kuma
ta rikida zakara, ta bi duk ta
tsince kwayoyin hatsin nan,
sai kwaya daya ce ta boye daga
ganin zakaran, bai tsince
ta ba. Daga nan sai muka ji an yi
wata kururuwa, kururuwar da
ta dimauta mu, cewa soron da
muke ciki ya rushe bisa
kammu. Daga nan sai ga wani
babban tabki na ruwa ya bayyana a
gabammu. Kwayar
nan daya ta hatsi da zakara
bai cinye ba, ta gangara ta
fada cikin ruwa, nan take ta
rikede zuwa kifi, ya nitse cikin
ruwan. Daga nan sai zakaran ya daga
kansa sama, ya yi cara, ya
kada fukafukansa sannan ya
juye babbar kifanya a cikin
ruwan, ta yi nitso ta faku daga
ganimmu zuwa sa’a guda. Can, sai
muka ji wata irin kururuwa
madaukakiya, muka tsorata.
Bayan haka Ifiritu ya fito,
wuta na fita daga bakinsa da
kofofin hancinsa. Muka yi kusa
mu nitsa cikin kasa don tsoro bisa ga
rayukammu na daga
konewa da hallaka. Daga nan sai ga
yarinya ta fito
daga ruwan nan, cikin siffarta
ta mutum, babu wani abu da
ya sameta na daga rauni.
Ifiritu ya juyo wajen da muke
ya buso mana wutar nan da ke fita
daga bakinsa zuwa ga
fuskokimmu. Yarinya ta yi
sauri ta shiga tsaknimmu da
wutar da Ifiritu ya buso mana
domin ta karemu daga hallaka. Duk
da yarinya ta kare wutar
da jikinta, sai da tartsatsinta
ya riskemu, tartsatsin
garwashi ya sameni ga
idaniyata, ta hagu, nan take ta
tsiyaye, na zama mai ido daya a
cikin wannan lokaci, duk dai
ina cikin siffar biri da Ifiritu ya
mayar da ni. Tartsatsi ya sami
Sarki ga fuskarsa, rabinta ya
kone da gemunsa da habarsa,
hakoransa suka zube. Tartsatsin ya
kuma sami wasu
daga cikin kuyangin da muke
tare da su a wannnan wuri,
wasu suka mutu nan take,
wasu suka sami raunuka. Muka
sakankance da halaka, muka debe
kauna daga rayuwa. Muna cikin
haka, sai mu ka ji
mai fada ya na fada, “Allah
mai girma! Allah mai girma!
Ubangiji ya yi budi da nasara
tasa, wanda ya kafirta ya
tabe, yayin da ya yi butulci da addinin
shugabam mu,
Muhammadu, shugaban
talikkai.” Daga nan sai muka
ga yar Sarki ta yi fushi, fushi
mai tsanani akan raunin da
Ifiritu ya yi ma ta, lokacin da ta ke
kokarin kare mu da
jikinta daga wutar da ya feso
mana, da kuma raunukan da
muka samu daga tartsatsin
wutar, yayin nan ta yi wani
kalar sihiri ta jefi Ifiritu da shi, nan
take ya kone, ya zama
toka da gawayi. Yarinya ta zo gare
mu, cikin
matsanancin ciwo, ta ce, ku zo
mini da tasa da ruwa in
kubutar da wannan bawan
Allah kafin ta Allah ta kasance
a gare ni. Aka zo da shi zuwa gare ta,
ta yi wani zance
wanda ba a fahimta a cikin
ruwan. Yayin nan ta yayyafa
mini, ta ce, ka kubuta da
girman gaskiya da girman
sunan Allah, mai girma, ya zuwa ga
siffarka ta farko! Nan take na koma
mutum,
kamar yadda ni ke da farko,
sai dai babu idaniya daya.
Yarinya ta ce da ni, wuta wuta
ce, ni ba ni da ikon mai da
wani abu na daga idaniyarka da ka
rasa, wannan kaddara ce
daga Allah, ka gode ma sa da
ba ka rasa ranka ba. Ka sani
cewa, Ifiritu ya sami damar
raunata ku, gami da ni, saboda
rashin ganin kwayar hatsin nan daya
da ban yi ba lokacin
da na ke tsince hatsin, wannan
kwaya ta kasance ita ce ta ke
dauke da ran shi, da na tsince
ta, da ya mutu a cikin wannan
sa’a. Ya kasance ya na bude mini
kofa ta sihiri ina bude ma sa
ma fi girma daga ta sa, har ya
bude mini kofar wuta. Wa ake
bude wa kofar wuta ya tsira
daga gareta? Cewa kaddara ta
taimakeni bisa gare shi har na
kone shi. Wannan taimako ne
daga Allah madaukakin Sarki.
Daga nan sai ta ce, na shaida
babu Sarki sai Allah,
Muhammadu manzon Allah ne, sai ta
fadi, ranta ya fita. Mu ka yi bakin
cikin
mutuwarta, na yi burin da ma
ba ta kara jikinta ga wutar nan
da Ifiritu ya feso ba, domin ta
karemu daga halaka, ga shi ita
ta halaka kanta wajen ceton rammu,
sai dai cewa, ba a
juyad da hukuncin Allah. Yayin da
Sarki ya ga ‘yar sa ta
fadi ta mutu, ya fige sauran
gemunsa ya na marin fuskar
sa, ya yayyaga tufafinsa. Na
aikata tamkar yadda ya
aikata, muka zauna muna kuka.
Lokacin da Hakimai da
fadawa suka shigo, suka ishe
mu cikin wannan hali, suka yi
mamakin abin da ya faru, suka
kewaye gefen Sarki sa’a guda.
Lokacin da hankalin Sarki ya
dawo, ya labartawa fadawa
abin da ya faru tsakanin ‘yarsa
da Ifiritu. Aka yi masa
gaisuwa kwana bakwai, yayin
nan ya yi umurni da gina kubba a
wurin da aka yi wa
‘yarsa kabari. Aka kunna fitilu
da shama’u a ciki. Tokar Ifiritu
kuwa, aka hau dogon tsauni
aka sheka ta, iska ta tafi da
ita, Allah ya la’ance shi. Wata rana
Sarki ya kira ni, ya
ce da ni, ya saurayi, mun zauna
zamanim mu a cikin dadin rai
da aminci, muna tsararru daga
musibun zamani, sai da ka zo,
musibu suka sabkam mana. Kaito ni!
Da ban gane ka ba, da
lokacin da na gane ka, in kore
ka ga mugunyar zuwan ka,
wadda sababin ta na rasa
‘yata da na ke matukar so, na
rasa hakorana, rabin fuskata ya kone,
amma ba laifinka ba
ne, wannan hukunci ne na
Allah da ya kasance a garemu,
da kai duka. Yabo ya tabbata
ga Allah da ‘yata ta kubutad da
kai, ta halakad da Ifiritu tare da
kanta. Ka fita, ya da na, daga gari na,
abin da ya gudana sababiabin da ya gudana sababinka
ya ishemu, ka fita da lafiya,
domin ganin ka kusa dani zai
ci gaba da tuna mini da
mutuwar ‘yata. Saurayi na biyu, mai
ido daya,
ya ci gaba da ba wa yarinya,
shugabar yam mata, da sauran
yam mata biyu, Jekadiya da
Mai jiran kofa, da samari biyu,
masu ido dai daya, da Dan Dako, da
su Halifa da
Wazirinsa Ja’afaru, da Sarkin
Fadansa Masururu, suna cikin
siffar fatake, da bakaken
bayin yarinya su bakwai rike
da takubba a hannuwansu, cewa: Na
fita, ya shugabata, daga
wannan birni, ban gasgata da
kubuta ta ba, ban san inda na
fuskanta ba, na damu da
zuciyata da abin da ya faru
gareni. Na yi tafiya tsawon wata
guda ina tunanin yadda
na fito gida, da yadda yan
fashi suka tarwatsa
tawagarmu, da shigata Birni
ina bako, da gamuwata da
madinki, da yadda na zama mai
sayar da ice, da
gamuwata da yarinya ‘yar
Sarkin Hindu a karkashin kasa,
da kubuta ta daga Ifiritu bayan
ya kashe yarinya ya mayar da
ni biri. Na tuna abin da ya faru gare
ni, tun daga farko har
karshe, na gode wa Allah na
ce, ga idaniyata ya kare ba ga
raina ba. Na ci gaba da tafiya, har
Allah
ya kawo ni wannan gari na
Bagadada ko na sadu da Sarkin
Musulmi, Halifa, in labarta
masa da abin da ya gudana a
gareni. Kafin na shigo, na tsaya bakin
gari na aske
gemuna, na shigo wannan gari
cikin dare, ina madimauci, ban
san inda zan nufa ba. Sai na ga
wannan saurayi na fari, mai
ido daya, yana tsaye, na yi masa
sallama, ya amsa mini.
Na ce, ni bako ne. Ya ce mini,
shima bako ne, yanzu ya shigo,
bai san inda zai nufa ba. Muna nan
tsaye, sai ga wannan
saurayi na uku, yayi mana
sallama, muka mayar ma sa.
Ya ce shi bako ne. Muka ce, mu
ma baki ne. Muka shigo cikin
gari, har Allah ya sa muka iso
wannan gida na ku, muka
nemi ku saukar da mu zuwa
wayewar gari. Ku ka amince
da bukatar mu, har abun da ya
faru, ya faru a wannan gida,
mu ka sami kammu daurarri cikin
igiya. Wannan shine
labarina, ya shugabata. Yarinya,
shugabar ‘yam mata,
ta ce, wannan labari na ka
abin marmari ne da
wa’azantarwa ga masu
hankali, tube kan ka daga
igiya, ka kubuta da ranka. Maza ka
kama tafarkinka.
Saurayi ya ce ba zai tafi ba har
sai ya ji labarin saurayi na uku,
mai ido daya, da kuma labarin
wadannan fatake, watau
Halifa da Wazirinsa da Sarkin
Fadansa. Yarinya ta dubi saurayi na
uku,
mai ido daya, ta ce, fada mini
labarinka, da yadda ka zama
mai ido daya sannan ka tube
kan ka daga daurin igiya
.
Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba
Admin AA Misau Ke Magana
08161272634
009. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN
MATA
.
Copied
AA Misau Ke Magana
.
Labarin Saurayi Na Uku Mai Ido Daya
(1)

Saurayi na uku, mai ido daya, ya
gabata a gaban
yarinya, ya ce, ya ke, shugaba
mabayyaniya,
kissata ba ta kasance tamkar
kissarsu ba, a’a,
kissata ita ce mafi al’ajabi daga
wadannan,
domin su kaddara ta zo musu game
da hukumci,
amma ni, sababin aske gemuna da
tallafar
idaniyata, ni, na jawo hukumci ga
kaina da bakin
chiki ga zuciyata.
Ni, na kasance Sarki, dan Sarki,
ubana ya mutu,
na yi sarauta bayansa, ina hukuncina yi sarauta bayansa, ina hukunci da
adalci, ina
kyautata ma talikkai. Na kasance
mai sha’awar
tafiya cikin bahar, Birane da Jazirori
ma su ban
sha’awa sun kasance a gefen bahar.
Na yi nufin
in yi yawo bisa ga jazirun. Na sauka
da jirage
goma, na riki guzurin wata, na tafi
kwana ashirin.
A chikin wani dare na darakku iska ta
tashi gare
mu da iskoki mabambamta, har
asbahin ya
bayyana, iska ta lafa, bahar ya nitsu,
har rana ta
yi fari, yayin nan muka daukaka bisa
ga jazira.
Muka tsinkayi tudu, muka dakata mu
ka sami
abin da za mu ci, daga cikin guzurim
mu, muka
ci, muka zauna kwana biyu ga
wannan tudu.
Bayan mun gama hutawa, muka tafi
kwana
ashirin, ruwaye suka canja mana,
tafarki ya sa6a.
Mai-jirigi ya iso ga wani wuri, ya che
wa masu-
tsinkaya, Ku duba chikin bahar, mun
isa jazira,
mai-wuyar hawa.
Yayin nan masu-duba suka duba,
suka che, mun
gani daga dama kifi bisa ga ruwa,
amma mun ga
baki daga nesa ga tsakar bahar, wata
sa’a baki,
wata sa’a fari, wata sa’a shina
haske.
Yayin da mai-jirigin ya ji zanchen
masu-dubawar,
ya buga rawaninsa ga kasa, ya fige
gemanya
tasa, ya che wa mutane, Ku ji labarin
hallakarmu,
dukan mu, daya ba shi kubuta a
chikinmu. Ya
zama shina kuka, mu duka hankalin
mu ya tashi
bisa ga rayuwammu.
Muka che, Ya mai-jirigi, ka labarta
mana da abin
da ka gani.
Ya che, Ya shugabana, ka sani, mu,
mun 6ata
ranad da iskan nan mabambamchiya
ta zo mana,
ba ta nitsa ba, fache da hantsi, muka
zauna
kwana biyu, ran nan muka 6ata ga
bahar. Ba mu
gushe ba madimauta kwana goma
sha daya daga
wannan dare, har yau ba mu da iska,
mai maishe
mu ya zuwa ga tafarkimmu;
Idan ranar yau ta kare, a chikin gobe
za mu sadu
da dutsi na daga bakin dutsin da a ke
che ma sa,
Dutsin Maganadishu, ruwa ya ja mu
tilas zuwa
gare shi. Idan mun isa, jirigi zai
farfashe,
kowanne allo shi tafi chikin ruwa.
Idan mun gamu
da wannan dutsi, za mu damfara da
shi, ba mu
sani ba domin Allah ya kaddara
wannan dutsi
sirri ne ga dukan karfe;
Chewa dukan bakin karife shina
tafiya gare shi,
karfuna da yawa na tare ga wannan
dutsi, babu
wan da ya san adadinsu, fache Allah,
madaukakin, Sarki; daga dadadden
zamani jirage
da yawa sun karairaye, jama’a da
yawa sun
hallaka sababi da wannan dutsi da
ke cikin
wannan bahar;
A saman dutsen akwai kubba ta farin
karfe da
tagulla, zamnanniya bisa ga
shikashikai goma, da
gatari bisa ga kubbar, ba mu san
aikinsa ba, da
mahayi bisa gare ta, da doki na farin
karfe, da
mashi na farin karfe a hannun
wannan mahayi,
rataye ga kirjin mahayin allo na
darma, da rubutu
a jikinsa sunannaki da dalamusai;
Ya Sarki, iyakar dauwamar wannan
mahayi bisa
ga wannan doki, jirgagen da suka
biya ta
karkashinsa, mahayansu duka sun
hallaka. Dukan
Karfen da ke jikn jirigin shina damfara
ga dutsin,
babu kubuta, fache wannan mahayi
ya fadi daga
kan wan nan doki.
Yayin nan mai-jirigin, ya shugabata,
ya yi kuka,
kuka, maitsanani, muka sakankance
mu
hallakakku ne babu shakka,
kowammu ya yi ban
kwana da abokinsa.
Yayin da asbahin ya yi, muka kusato
wannan
dutsi, ruwa ya jawo mu gare shi dole.
Yayin da
jiragem mu suka zama daga
karkashin Dutsin
Maganadishu, suka bugu da shi,
suka kyarkeche,
suka tarwatse. Akwai daga gare mu
wanda ya
dulmuya, akwai daga gare mu wanda
ya kubuta,
amma yawa yawammu sun dulmuya.
Wadannan
da suka kubuta ba su san junansu
ba, domin
wannan iska ta sa6a, ta dimauta su.
Ni kuwa, ya shugabata, Allah
madaukakin Sarki,
ya kubutad da ni, yayin da ya yi nufin
shi
kuftutad da ni daga azaba da wahala,
na hau bisa
ga allo na daga allunan jirgin, iska ta
jefa shi
game da rakumman ruwa zuwa ga
dutsi, na samu
tafarki, mai-hawa birbishin dutsin
tamkar
kwaranga, jingine ga dutsin, amma
dutsin ne. Na
ambachi Allah, madaukakin Sarki.
Chewa saurayi na ukku ya che ma
yarinya, da
jama’a daurarru, da bayi na tsaye da
takubba ga
hannuwansu bisa ga kawunan
daurarrun, Yayin
nan na ambachi Allah, na kiraye shi,
na koma
zuwa gare shi, na yi dabarar hawa
bisa ga
dutsen, na zama ina kama hakorin
nan majeranta
na jikinsa tamkar tsani, har Allah ya
lafad da iska
ga wannan sa’a, ya taimake ni ga
fita, na hau
bisa ga dutsi lafiya, na yi murna da
kubutata,
gayar murna.
Na nufi kubbar nan, wadda mahayi
ya ke kanta,
na shige ta, na yi salla chikinta
raka’o’i biyu, na
gode ma Allah bisa ga kubutata.
Yayin nan na yi
barchi karkashin kubbar, na ji mai
fada shina fada
a cikin mafarkina, shina chewa, Ya
dan Hasibu,
idan ka farka daga barchinka, ka tona
karkashin
kafafunka, za ka ga baka na farin
karfe da
kibiyoyi ukku na darma, rubutachche
da
dalamusai;
Ka riki bakan da kibaun, ka harbi
mahayin nan da
ke bisa kubba, ka futad da mutane da
wannan
bala’i, mai-girma. Idan ka harbi
mahayin, ya
abku chikin bahar, bakan zai fadi
daga hannunka,
ka dauki bakan, ka bisne shi a
gurbinsa;
Idan ka aikata haka, bahar ya biche,
shi komo,
shi daukaka, har shi daidaita da
dutsin, ka ga jirgi
a chikinsa da mutum a chikin jirigin,
wanin wanda
ka harbe shi, zai zo gare ka da
abinchi tare da
shi;
Ka hau tare da shi, kada ka ambaci
sunan Allah,
zai tafi da kai kwana goma zuwa
wani
amintaccen bahar. Idan ka isa can ka
samu mai
kai ka zuwa ga garinku, chewa idan
ba ka
ambachi Allah ba.
Yayin nan na farka daga barchina, na
tashi da
nishadi, na tone karkashin kafafuna
na dauko
bakan nan. Na harbi mahayin, na
harbe shi, ya
fadi chikin ruwa, baka ya fadi daga
hannuna. Na
dauki bakan, na bisne shi. Bahar ya
tashi, ya
daukaka har ya daidaita da dutsin
nan da ni ke
bisa kansa.
Yayin nan ban zauna ba, fache sa’a,
na ga
karamin jirgi daga bahar, ya gabato
ni. Na gode
ma Allah, madaukakin Sarki. Yayin
da karamin
jirigi ya sadu da ni, na ishe mutum-
mutumi a
chikinsa na farin karfe da allo ga
kirjinsa na
darma, rubutachche da sunannaki da
dalamusai.
Na shiga chikin jirigin, ina kawai, ba
ni magana.
Mutum-mutumin nan ya dauke ni
ranar fari, da ta
biyu, da ta ukku ya zuwa ga chikon
kwana goma.
Ran nan na ga jazirar aminchi, na yi
farin chiki da
murna, mai yawa. Don tsananin
murnata ban san
lokacin da na ambachi sunan Allah
ba, ina mai
godiya gareshi da ya kubutar da ni.
Ban gama rufe bakina ba sai na ji an
yi jifa da ni
chikin bahar daga jirgin. Na kasance
na iya
ninkaya, na yi ta iyo a cikin wannan
rana ya
zuwa ga dare, damutstsana suka
gaji, kafaduna
suka kasa, na zama cikin halaka,
yayin nan na yi
kalamash
.
Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba
Admin AA Misau Ke Magana
Suleiman Zidane Kd
010. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN
MATA
.
Copied
AA Misau
ke Magana
.
Labarin Saurayi Na Uku Mai Ido Daya
(2)
.
Bahar ya tashi da yawan iska, kumfa
ta zama
tamkar duwatsu, ta dauke ni, ta jefar
da ni, na
zama bisa tudu. Yayin da Allah ya yi
nufin im fita
tudu, na taka, na matse tufafina, na
baza su bisa
ga kasa, na yi kwanche.
Yayin da gari ya waye, na saka
tufafina, ina
tunanin inda zan nufa sai na tsinkayi
jigawa da
itatuwa, na nufi zuwa gare ta, ina
gewaya ta, na
ishe wurin nan da ni ke jazira che
karama, bahar
ya kewaye ta. Na che a chikin raina
ko yaushe na
kubuta daga masiba sai kuma im
fada wata.
Ina chikin tunanin al’amarina, ina
burin mutuwa
domin na huta da wannan wahala,
sai na hangi
jirgi daga nesa ya nufo wannan
tsibiri.
Na tashi, na hau bisa itachiya. Bayan
wani lokaci
jirgin ya iso bakin tudu, bayi goma
suka fito daga
gare shi da magirbai ga
hannuwansu. Suka zo
har suka iso tsakar jazirar, suka tona
kasa suka
daukake rufi, suka share, sai ga kofa
ta bayyana,
suka bude kofar. Yayin nan suka
koma zuwa ga
jirigin, suka zama suna debowa daga
gare shi
waina, da gari da mai, da zuma, da
ganimomi, da
dukkan abin da mai-zama ke bukata.
Bayi suka zama suna kokkomawa
tsakanin jirgi
da rufi, suna tarawa a chikin rufin, har
suka debe
dukkan abin da ke chikin jirigin.
Yayin nan bayi
suka komo tare da tufafi kyawawa da
wani tsoho,
duddugagge, dogo, ya kasance
zamani ya dade
tare da shi, ya zama kararre, daga
kashi sai fata.
Na ga kuma wani yaro, saurayi
tsohon na rike da
hannunsa. Wannan yaro ya cika duk
wata siffa ta
kyawo, har ana buga misali da
kyawonsa, cewa
shi tamkar danyar sanda ne a cikin
rairayin
hamada, shina kore kowache zuchiya
da
kyawonsa, shina tu6e wayon mai
wayo da chikar
halittar sa.
Wannan saurayi na sanye da
kyawawan tufafi.
Ba su gushe ba suna tafiya, ya
shugabata, har
suka iso zuwa ga rufi suka sauka
chikinsa, suka
faku ga ganina. Yayin da suka shige
karkashin
kasa, na tashi, na sauko daga bisan
itachiya, na
tafi zuwa ga wurin na share kasar na
chire rufin,
na saurara kadan ko na ji motsinsu,
ban ji motsin
kome ba.
Na duba rufin, na ishe itache ne
tamkar duwatsun
dahunu, na daukake su, tsani ya
bayyana daga
Karkashinsa, na tattaka tsanin na
sauka kasa, na
iske wuri tsatstsarka, na ga gona, da
ta biyu, da
ta ukku, har ya zuwa ga chikar talatin
da tara.
Kowache gona na ga abin da ya
gajiyad da
kwatanchi a chikinta na daga
itatuwa, da
Korammu, da ‘ya’yan itatuwa, da
kayan taska
daga jauhari zuwa ga waninsa.
Na ga wata kofa, na che a chikin
raina, yalla
menene a chikin wannan bigire?
Babu makawa im
bude ta, in ga abin da ke chiki. Yayin
nan na bude
kofar, na ishe a chikinta wani doki
fari fat, da
sirdi, da linzami, a daure, na kwanche
shi na hau.
Ya kada da ni zuwa ga kuryar gidan,
ya ajiye ni
bisa ga tsakar gida bakin kofar wani
soro. Ya
saukad da ni, ya buge ni da
wutsiyarsa ga
idaniyata ta hagu, nan take ta
tsiyaye, ta tallafa,
ya juya ya koma ta inda muka fito.
Na shiga cikin soron na samu samari
goma,
masu-ido daya daya. Yayin da suka
gane ni, suka
che, Babu maraba a gare ka! Na che
da su, kwa
tarye ni da haka, ni mai niyyar zama
a gare ku?
Suka che, Wallahi, ba ka zama a gare
mu, suka
kore ni daga wurinsu. Na fita daga
gare su, ina
mai bacin zuchiya, mai-kuka ga ido.
Bayan na fito daga cikin rufin nan na
karkashin
kasa, na shiga cikin jirgin da tsohon
nan da
saurayi suka zo da shi, na fada cikin
bahar, Allah
ya kaddara iska ta yi mini kyawo, ya
kubutad da
ni, na sadu zuwa ga Bagadada, na
aske gemuna.
Na shigo cikin wannan gari da dare
na sami
wadannan biyu, masu ido dai daya,
na yi sallama
a gare su. Na che da su, Ni bako ne!
Suka che,
Mu, ma, baki ne. Wannan shi ne
dalilin tallafar
idaniyata da aske gemanyata, ya
shugabata.
Yarinya shugabar yam mata ta che
da shi, ka
samu kanka! Kwance kan ka daga
dauri ka tafi!
Ya che, Wallahi, ba ni tafiya, sai na ji
kissar
wadan nan fataken.
Yayin nan yarinya ta waiwaya zuwa
ga Halifa, da
Ja’afaru, da Masruru. Ta che da su,
Ku labarta
ma ni da labarinku. Ja’afaru ya
gabata, ya
hakaita ma ta hikayan nan da ya
gaya wa
yarinya mai jiran kofa yayin
shigowarsu wannan
gida.
Yayin da ta ji zanchensa, ta che, Na
ba da
sashenku ga sashe, ku tashi ku fita
ku barmu.
Suka fito, Dan Dako ya nufi gida yana
mai
matukar mamaki, gayan mamaki,
akan yam mata
da samari uku masu ido daya da
hikayoyinsu.
Bayan sun fito har sun iso chikin
kwararo. Halifa
ya che ma samarin nan, Ya ku,
jama’a ina za ku?
Suka che, Ba mu san inda za mu ba.
Halifa ya
che da su, ku tafi, ku kwana a gare
mu. Ya che
ma Ja’afaru, rike su, ka zo ma ni da
su da safe,
har in ga abin da zai kasance.
Ja’afaru ya bi abin
da Halifa ya umurche shi da shi.
Yayin nan Halifa
ya shiga zuwa ga gidansa, barchi bai
zo ma sa
ba chikin wannan dare.
Yayin da gari ya waye, ya zauna bisa
ga gadon
sarauta, Sarakuna suka shiga,
fadanchi ya
kankama. Ya waiwaya zuwa ga
Ja’afaru, bayan
ma’abutan daula sun taru, ya che, ka
zo mini da
samarina ukku, da yam mata ukku,
da karnuka
biyu. Ja’afaru ya zabura, ya
hallarasu gaba gare
shi. Mata suka shiga bayan sitira.
Ja’afaru ya waiwaya zuwa ga yam
mata, ya che
da su, Mun yafe muku daurin da kuka
yi mana
jiya domin abin da kuka gabatar na
daga
kyautatawa gare mu, ba tare da kun
san mu ba.
Yanzu kuna gaba ga Halifa na biyar
daga Banu
Abbas, shi ne Harunar Rashid. Kada
ku labarta
ma sa, fache gaskiya.
Yayin da yam mata suka ji zanchen
Ja’afaru bisa
ga harshen Sarkin Musulmi, suka fadi
suka yi
gaisuwa. Babbarsu ta gabata ta che,
Ya Sarkin
Musulmi, ina da zanche na daga
wadan nan
karnuka, wanda da za a rubuta shi da
tsinin
allura bisa ga gefen idanu, da ya
zama abin lura
ga mai hankali. Ta fara bayar da
labarinta kamar
haka:
.
Zan dakata an an saikuma Allah yakaimu Gobe zamu cigaba
Admin
AA Misau
ke Magana
Suleiman Zidane Kd
011. HIKAYAR DAN
DAKO DA YAN MATA.
.
Copied
AA Misau Ke Magana
Guyson Kenan
.
Labarin Yarinya
Shugabar Yam
Mata (1)
.
Yarinya shugabar yam mata
ta
ce da Halifa da sauran jama’a,
wadan nan karnuka biyu yan
uwana ne, ubanmu daya
amma su biyu mahaifiyarsu
dabam, na kasance ni ce karamarsu.
Mahaifinmu ya
mutu ya bar mana gadon kudi,
dinare dubu biyar, bayan an
raba kudin nan sai su biyu suka
yi aure, suka damka amanar
dukiyarsu ga mazajensu suna yi
musu fatauci tsawon
zamani. Ni kuwa ina cininiki a
cikin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment