Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rumfata. Bayan shekara hudu,
mazajen
yan uwannan nawa suka
banzatar da dukiyar yan
uwana suka wulakanta su
sannan suka kore su. Yan
uwana suka zo wurina, da farko ban
gane su ba domin
duka wahala ta tsufar da su.
Yayin da na shaida su na ce, ya
yan uwana me ya faru da ku
bayan aurenku? Suka ce, ya
yar uwar mu, zance ba shi da amfani
a halin yanzu, bakin
alkalami ya riga ya bushe, abin
da Allah ya hukunta ba shi
canjawa, cewa mu kaddara ta
fada mana na daga asarar
dukiyarmu, yanzu ba mu mallaki ko
dirhami ba. Koda na ji haka sai na
kwantar
musu da hankali, na ce haka
Allah ya kaddara, babu mai
ikon juyad da ita. Na aika da
su gidana, na tufatar da su
tufafi masu tamani. Sannan na ce da
su, ya yan uwana kune
manya ni kuma ni ce karama
daga cikin ku, don haka yanzu
ku ne a matsayin iyayena.
Rabon da na samu na gadon
kudin mahaifinmu, Allah ya sa
albarka a cikinsa, na juya shi
ta hanyar kasuwanci, na kuma
sami riba mai yawa don haka
ya ishe mu, ni da ku, mu raba
shi daidai. Ya Halifa, na kyautatawa
yan
uwan nan nawa, gayar
kyautatawa, mu ka zauna tare
muna kasuwanci tsawon
shekara guda, suka zama masu
arziki da dukiyata. Wata rana sai
suka ce da ni, suna son su
koma ga mazajensu. Na ce da
su, ya yan uwana ku sani cewa
kyawawan maza masu amana
kadan ne a wannan zamani, za
su karbe dukiyarku ne su wulakanta
ku, su kore ku daga
wurinsu, shin kun manta
abinda ya faru da ku a baya?
Suka ce, su dai za su koma. Na
yi na yi da su, suka ki. Na barsu
suka koma gun mazajensu. A cikin
sa’a kadan da
komawarsu, mazajen suka
rude su, suka karbe dukiyarsu
suka tafi suka bar su. Suka
komo zuwa gareni suna
matsiraita, suna mai kawo mini
hanzari cewa, ya yar
uwarmu, kada ki rike mu da
laifimmu, ke ce karama daga
gare mu amma kin fi mu
hankali, cewa mu ba za mu
sake yarda da maza ba har abada.
Na ce, maraba da ku ya
yan uwana, ba ni da tamkar ku
a duniya, ta yaya zan juya
muku baya. Na sumbace su, na
dada musu karimci. Muka zauna tare
da su tsawon
shekara cikakkiya, na yi nufin
zuwa fatuci birnin Bisira. Na
shirya babban jirgi, na cika shi
da kayan fatauci da guzurim
ma su jirgi. Na ce da yan uwana, ko
za ku zauna a gida
har in tafi Bisira in komo, ko
kuna da sha’awar mu tafi tare?
Suka ce, za mu tafi tare, mu ba
mu iya rabuwa da ke. Na raba
dukiyata, ta kudi,
kashi biyu, na boye daya a
gida na riki daya domin ban
sani ba kila wata kaddara ta
asara ta fada mana a can. Idan
mun koma ma samu abinda zai
amfane mu. Bayan mun gama shiri,
muka
shiga jirgi muka tsunduma
cikin bahar. Muka yi ta tafiya,
dare da rana babu tsayawa.
Muka yi kwanaki muna tafiya,
ashe ba mu sani ba mai jirgi ya bata
hanya, muka shiga wani
bahar wanda ba mu sani ba.
Bayan tsawon wani zamani,
sai muka hangi wani birni
daga nesa. Muka nufe shi har
muka isa kan tudu. Muka tambayi
mai jirgi sunan
wannan birni. Ya ce, Wallahi
ban sani ba, ni ban taba ganin
wannan birni ba, ban taba
zuwa gareshi ba. Ku sani cewa
mun bace hanya, amma al’amari
yayi mana kyau tunda
mun samai wannan birni. Ku
fitar da kayan ku, ku shiga
cikinsa ku yi ciniki. Amma ku
bari na shiga cikin garin na
duba yanayinsa da yanayin
mutanensa. Mai jirgi ya shiga cikin
birni ya
jima, bayan wani lokaci ya
dawo garemu. Ya ce, ku tashi
mu shiga cikin wannan birni
ku yi al’ajabin ikon Allah don
ku nemi tsari daga fushinsa. Ku bar
kayan ku a cikin jirgi. Muka shiga
cikin birni. Muka
iske dukan halitta mai rai da
ke cikinsa an shafeta ta koma
siffar bakin dutse. Muka yi
mamakin ganin wannan abu.
Muka shiga cikin kasuwa muka ga
kayayyaki, zinariya da
azurfa, zube ga rumfunan
sayar da su. Ga mutane, wasu
a tsaye, wasu a zaune, wasu
suna ciniki, wasu suna
gaisawa, wasu na cin abinci, amma
duk an shafe su zuwa
siffar dutse. Sai kayayyakin
siyarwa ke kyalkyali a cikin
rumfuna. Muka yi mamakin
wannan abu, muka ce
watakila wani babban al’amari ya
gudana ga jama’ar
wannan birni. Muka fita daga cikin
kasuwa
muka rarrabu cikin kwararo
kwararo na wannan birni, ko
wanne dayanmu ya manta da
abokinsa domin dimbin
dukiyar da ke cikin wannan birni.
Kowane kwararo akwai
mutane da dabbobi, amma dun
sun zama bakaken duwatsu. Amma
ni na hangi wani
babban gida, na shiga cikinsa.
Na same shi abin gajiyarwa ga
ido gun kallo, ashe nan ne
fada. Na shiga cikin soro, na
sami dukan koran da ke ciki an yi su
ne da zinariya da azurfa.
Yayin nan na ga Sarki zaune
akan karagar mulki, hakimai
da fadawa sun zagaye shi,
suna sanye da tufafi wadanda
ke dimauta wanda ya gansu. Yayin
da na kusata da Sarki, na
gan shi akan karaga abar
aikatawa da lu’ulu’u da
jauhari, ko wace fuska ta na
haske tamkar taurari. Da tufafi
a jikin Sarki zanannu da zinariya, da
wasu dakaru
mutum uku, daya a kowane
gefe da kuma daya a bayansa,
kowanensu na rike da zararren
takobi, duka suna cikin siffar
duwatsu. Yayin da na ga haka
hankali na ya tashi da ikon
Allah. Na shiga cikin gida, na iske
sarauniya da adon lu’ulu’u mai
yawa a jikinta, ta saka hula a
kanta wacce aka yi wa ado da
zinariya da jauhari, da wata
babbar sarka ta zinariya a wuyanta.
Ga kuyangi, kowace
da dangin kayan ado dabam a
jikinta, suna masu yin hidima
ga sarauniya, duka an shafesu
bakaken duwatsu. Na shiga wata
budaddiyar
kofa na ga matakai masu
hawa zuwa sama, na tattaka
su na hau sama. Na samu wuri
shimfidadde da shimfidun
darduma mai tasuhi, da gado na
marmar an yi masa ado da
zinariya da azurfa, da katifa
akan gadon. Na ga wani haske
yana tashi daga wani bangare
na wannan daki, na iske
jauhara tamkar kwan jimina, ita ce
mai hasken. Na yi
al’ajabi, matukar al’ajabi, na
dukiyar da ke cikin wannan
gida. Na ga fitilu a kunne cikin wani
daki, na shiga ban ga kowa a
ciki ba, na ce a raina, babu
makawa wani mai rai ne ya
kunna wadan nan fitilu. Na
zama ina bincike cikin wannan gida,
na dulmiya cikin tunani
har dare yayi. Na yi nufin fita
in koma inda jirgimmu, na
kasa gane kofar fita. Na juya
ga dakin da na ga gado a ciki,
na haye kan gado na rufa da mayafi
domin inyi barci, na
kasa. Can zuwa tsakiyar dare, ina
kwance na kasa barci, sai na ji
am fara karatun Alkur’ani da
wata murya mai dadi. Na
sauko daga kan gado, na fito,
sai na ji karatun na fitowa ne daga
dakin da na samu fitilu a
kunne. Na zo a hankali na leka
cikin dakin, sai na ga saurayi a
zaune kan shimfida, mai
kyakkyawar magana, da
Alkur’ani a gabansa yana karantawa.
Na yi mamaki da
ya kubuta daga sauran jama’ar
wannan birni da aka mayar da
su duwatsu.
Hm Zan Dakata An an Saikuma Allah Ya kaimu Gobe Zamu Cigaba
Admin
AA Misau
Ke Magana
Guyson Kenan
Suleiman Zidane Kd
012. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN
MATA
.
Copied
AA Misau Ke Magana
Guyson Kenan
.
Labarin Yarinya Shugabar Yan Mata
(2)
.
Yarinya shugabar yan mata, ta ci
gaba da
labarinta da cewa: Bayan na gama
kallon abin
mamaki, da ikon Allah, a cikin gidan
nan, sai na
yi nufin fita domin in koma inda yan
uwana. Na
nemi hanya na rasa, sai na koma
dakin da na ga
gado da shimfida. Na haye gado na
yi kwance, da
nufin in yi barci, amma ya gagara.
Can zuwa tsakar dare, sai na ji
karatun Alkur’ani
na fitowa, daga cikin dakin da na ga
fitilu a
kunne, da wata irin murya mai dadi.
Na tashi na
nufi wannan daki, sai na ga wani
saurayi ne yake
wannan karatu. Na yi mamakin ganin
cewa shi
kadai ne ya tsira a cikin wannan
birni, ba a mayar
da shi dutse ba.
Na shiga na yi masa sallama. Ya
dakatar da
karatunsa, ya juyo ya dube ni, sannan
ya mayar
mini da sallama. Na ce da shi, na
roke ka, don
girman wannan littafi da kake
karantawa, ka yi
mini bayani a kan tambayar da zan yi
maka.
Ya yi murmushi ya ce: Ki labarta mini
dalilin
zuwan ki wannan gari namu, har kika
shigo
wannan gida, sannan in labarta miki
duk wani
jawabi da za ki tambaya gare ni.
Na ba shi labarina, da na yan’uwana,
da kuma
niyyarmu ta zuwa birnin Bisira wurin
fatauci, da
yadda muka bace hanya har muka
iso wannan
birni. Ya yi al’ajabi, gayar al’ajabi.
Yayin nan ni
kuma na tambaye shi bayanin
wannan birni, da
abin da ya sa aka shafe su zuwa
duwatsu, da
kuma dalilin da ya sa shi ba a shafe
shi dutse ba.
Ya ce: Ki jinkirta mini. Ya nade
takardu, ya saka
su a cikin jikka ta hadalashi, ya
zaunar da ni a
gefensa. Na yi duba izuwa fuskarsa,
na gan shi
tamkar farin wata, mai kyawawan
siffofi, da
tattausan lafazi, mai kwarjini ga
magana,
madaidaicin tsayuwa, matsakaicin
kundukuki. Na
yi duba zuwa gare shi, dubar da ta
azabtar da
zuciyata, son shi ya huru, tamkar
wuta, a cikin
zuciyata. Na yi burin ina ma ya
zamanto mijina.
Na ce da shi, ya shugabana, ka yi
mini bayani a
kan abin da na tambaye ka. Ya ce: Na
ji, na
dauka. Sannan ya fara ba ni labari
kamar haka:
Ki sani, wannan alkarya birnin ubana
ce, shi ne
wanda ki ka gani a cikin wannan
fada, da dukkan
jama’ar da ke cikinta, da dimbin
dukiyar da Allah
ya ba su. Kuma Sarauniyar nan da ki
ka gani, ita
ce uwata. Jama’ar wannan gari, da
Sarkinsu
duka, sun kasance majusawa ne.
Suna bauta wa
wuta, suna barin bauta wa Allah Mai
iko. Sun
kasance suna rantsuwa da wuta, da
haskenta, da
inuwarta mai kuna.
Ubana ya kasance ba shi da da
tsawon lokaci, sai
Allah ya arzuta shi da ni. Bayan na
fara girma, ya
bayar da ni ga wata tsohuwa mai
reno, ya ce: Ki
rike shi, ki rene shi, ki koyar da shi
dabarun
addinimmu.
Tsohuwar nan ta kasance mai yawan
shekaru ce,
ta san ilimi na taurari, da na zaman
duniya, da
dukkan ilimomi. Ta kasance
musulma ce, ta
bayar da gaskiya ga Allah da
Manzonsa a boye.
Tana shiryar da mutane addinin
musulunci ba
tare da sanin Sarki ba. Ta rike ni,
tana koyar da ni
addinin Islama, maimakon addinin
bautar wuta. A
wurin ta na koyi tsarki, da farillar
alwala, da
salla. Ta koyar da ni karatun
Alkur’ani.
Yayin da ajalinta ya yi, ta ce da ni: Ya
dana, ka
boye wannan al’amari ga ubanka,
kada ka sanar
da shi, ya kashe ka. Bayan tsohuwa
ta mutu, na
ci gaba da bauta wa Allah a boye.
Mutanen gari
kuwa suka kara kafircinsu, da
butulcinsu, suka
kara zurfafa a cikin sabon Ubangiji.
Suna nan cikin wanan hali, sai wata
rana, daga
cikin ranaku, suka ji mai kira yana
kira da
madaukakin sauti, tamkar tsawar
aradu. Na nesa
da na kusa duka sun ji wannan
murya tana cewa:
Ya mazauna wannan birni! Ku juya
zuwa ga barin
bautar wuta! Ku bauta wa Sarki Mai
iko, wanda
yake saukar muku da ruwa daga
sama, ya ba ku
dukiya da abinci!
Mutane duka suka tsorata da jin
wannan murya,
da gargadin da ta yi musu. Suka tafi
wurin
ubana, Sarki, suka ce da shi: Ya
Sarki, mene ne
wannan sauti, mai tsanani, da muka
ji ya tsoratar
da mu? Ya ce: Kada jin wannan sauti
ya tsorata
ku, kada ku juya ga barin addininku
na bautar
wuta. Mutane suka dauki maganar
ubana, suka ci
gaba da bautar wuta.
Basu gushe ba suna ci gaba da bauta
wa wuta,
da yin butulci ga Allah Madaukakin
Sarki, tsawon
shekara guda da jin sautin nan na
gargadi. Aka
kara gargadin su da barin bautar
wuta, ba su bari
ba. An yi musu wannan gargadi sau
uku, kowace
shekara sukan ji wannan murya mai
gargadi, har
shekara uku, amma ba su bar bautar
wuta ba.
Ba su gushe ba suna madurkusa,
wurin bautar
wutarsu har masifa ta saukar musu.
Abin ya faru
ne wata rana bayan hudowar alfijir,
aka shafe su
zuwa babbakun duwatsu, haka nan
dabbobinsu,
wani bai kubuta daga mazauna
wannan birni ba,
face ni. Daga ranar da wannan abu ya
faru, ina
bisa ga wannan hali, na karatun
Alkur’ani. Na
tabbata a kan haka, har zuwa
wannan lokaci da
kika same ni.
Yarinya ta ci gaba da ba Halifa da
sauran jama’a
labarinta, ta ce: Ya Sarkin musulmi,
lokacin da na
ji labarin saurayi, da dalilin da ya sa
aka mayar
da mazauna wannan birni duwatsu,
na yi
mamaki, matukar mamaki. Sannan
na tambayi
saurayi, na ce da shi: Ya shugabana,
yalla ko za
ka bi ni zuwa garimmu, ka hadu da
masana, ka
karu da iliminsu, ni kuma in zama
kuyangarka?
Ina da jirage madaukaka da ake
zuwa mini
fatauci, da dukiya mai tarin yawa.
Watakila Allah
ya turo mu wannan birni ne naku
domin mu tafi
da kai zuwa garimmu. Na yi ta
lallashin sa dai,
har ya yarda zai tafi tare da mu.
Bayan gari ya waye, muka tashi, ni
da saurayi,
muka shiga cikin taskoki, muka debo
daga dukiya,
abubuwa masu saukin dauka amma
masu tsada.
Muka fito daga gidan, muka kama
hanyar zuwa
inda jirgimmu ya ke, a bakin bahar na
garin.
Muka hadu da bayina, da mai jirgi
suna nema na.
Yayin da suka gane ni, suka yi farin
ciki. Suka
tambaye ni inda na shiga, tun jiya
suna nema na.
Na labarta musu da abin da na gani,
da kuma
kissar mutanen wannan birni, da
kuma dalilin da
yasa aka shafe su. Suka yi mamaki.
Yayin da yan’uwana suka ga wannan
saurayi, da
irin kyawon da Allah ya yi masa, sai
suka yi kishi
na, suka hassade ni, suka kulla
makirci a cikin
zuciyarsu, amma ni ban san nufinsu
ba.
Muka shiga cikin jirgi. Muka zauna
muna jiran
iska, har ta yi mana dadi. Muka saki
jirgi, muka
nausa cikin bahar, muka tasamma
jahar da birnin
Bisira ya ke.
Yan’uwana suka tambaye ni, muna
cikin zance,
suka ce da ni: Ya yar’uwarmu, me
kike nufi da
wannan kyakkyawan saurayi? Na ce
da su, Ina so
in aure shi, ya zamanto mijina, kuma
in damka
masa amanar dukiyata, amma sai
idan ya yarda.
Bamu gushe ba muna tafiya, iska ta
yi mana
kyau, har muka fita daga bahar abar
tsoro, muka
shiga bahar mai aminci. Muka tafi
kwanaki kadan,
har muka kusato Bisira, gine-ginenta
suka
bayyana a gare mu.
Lokacin da dare yayi, muka shiga
barci,
yan’uwana suka tashi, suka dauke
mu, ni da
saurayin nan da shimfidummu, suka
kunduma mu
cikin bahar.
.
Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba
Admin
AA Misau Ke Magana
Guyson Kenan
Suleiman Zidane Kd
013. HIKAYAR DAN
DAKO DA YAN MATA
.
Copied
AA Misau ke magana
Guyson kenan
.
Labarin Yarinya
Shugabar Yan
Mata (3)
.
Yarinya shugabar yan mata
ta
ci gaba da labarinta da cewa:
Muka ci gaba da tafiya a cikin
bahar, kwana da kwanaki, har
muka fara hango gine-ginen
birnin Bisira. Wata rana da dare,
jirgimmu na tafiya a cikin
bahar, barci ya dauke mu duka,
sai matukin jirgin ne kawai ke
ta faman tuki. Sai yan uwana
suka lallabo, suka dauke mu, ni
da saurayi da shimfidummu, suka
kunduma a cikin ruwa,
jirgi yayi gaba. Allah ya nufa da
saurayin nan
bai iya ninkaya ba, nan take ya
dulmuye a cikin ruwa yayi
shahada. Ni kuwa, sai Allah ya
koro mini da wani itace, na
kama shi na hau, iska ta yi ta tura ni
har na zo bakin gabar
wani tsibiri, na taka na shiga
cikin tsibirin. Ban gushe ba ina tafiya
cikin
wannan tsibiri har gari ya
waye, da na dubi kasa sai na
ga sawun kafar dan Adam,
amma akwai alamun sawun ya
dade. Yayin da rana ta fito, na cire
tufafina na shanya su a
rana. Ina zaune gindin wata
itaciya ina jiran tufafina su
bushe, sai na hangi wasu
macizai guda biyu, sun nufo
inda na ke a guje, daya na biye da
daya. Da suka iso wurina, sai na lura
da cewa daya macijin ya biyo
dayan ne yana neman ya
hallaka shi. Wanda aka biyon
sai ya nufo inda na ke, ga
alama kamar yana neman taimako
daga gare ni. Sai na
dauki wani babban dutse nan
kusa da ni, na dubi macijin da
yake neman hallaka dan
uwanshi, na kwantsama masa
shi a kai. Nan take ya mutu. Macijin
da aka biyo kuwa da ya
ga na kashe abokin fadansa,
sai na ga ya fito da fuka-fukai,
ya tashi sama, ya kada cikin
sararin Subuhana, har ya bace
wa ganin idona. Na cika da al’ajabin
wannan abu. Na sa
tufafina, na ci gaba da tafiya
har rana ta yi zafi. Na kwanta a
karkashin wata itaciya domin
in dan sarara, sai barci ya
dauke ni. Yayin da na farka daga
barci,
sai na ga wata kyakkyawar
yarinya tana yi mini tausa ga
kafafuna. Na yi zumbur na
tashi zaune, na ce wace ce ke?
Yarinya ta ce, haba ya shugabata,
amma kin cika
mantuwa, yanzu har kin manta
ni? Ke ce wadda kika aikata
mini alheri, wanda ba zan taba
mantawa da shi ba har tsawon
rayuwata. Ke ce kika kashe makiyina
wanda yayi niyyar ya
halaka ni, ba domin kin cece ni
daga gare shi ba, da tuni ya
kashe ni. Ni ce macijin nan da
kika taimaka dazu. Ni aljana ce,
macijin nan ma
aljani ne, shi makiyina ne,
babu wanda ya kubutar da ni
daga gare shi, face ke, hatta
aljanu yan uwanmu tsoronsa
suke ji. Yayin da kika kubutar da ni
daga gare shi, na kada
cikin iska, na tafi zuwa ga
jirgin nan da yan uwanki suka
jefar da ke daga cikinsa. Na
kwashe dukan abin da ke ciki
na dukiya, na kai miki shi gidanki, na
dulmiyar da jirgin.
Yan uwanki kuwa, na sihirce su
karnuka, babbakun karnuka. Ni, na
san dukan abinda ya
gudana tsakaninki da su,
amma saurayinki ya halaka
cikin ruwa, na yi nema ko
gawarsa ban gani ba, ban san
abinda Allah ya nufa da shi ba.
Bayan aljana ta gama ba ni
labari na abinda ya faru da yan
uwana, ta dauke ni tamkar
kibtawar ido, ta ajiye ni a cikin
gidana. Na samu dukagidana. Na samu dukan
dukiyata, ko allaura ba ta bata ba a
ciki. Sannan kuma na ga
karnuka biyu a daure. Yayin nan
aljana, macijiya, ta
ce da ni cikin kakkausar muryce da ni cikin kakkausar murya:
Da girman rubutun nan da ke
jikin zoben Annabi Sulaimanu,
idan ba ki bugi kowace daya
daga cikinsu, a cikin kowane dare,
bulala dari uku ba, babu
rangwame, zan zo in yi miki
azaba mafi tsanani daga tasu,
in maishe ki tamkar su. Na ce, na ji,
na dauka! Ban
gushe ba, ya Sarkin Musulmi,
ina dukan su wannan duka, ina
kuma jin tausayinsu bayakuma jin tausayinsu bayan na
gama dukan nasu. Wannan gama dukan nasu. Wannan shi
ne labarina da wadan nan karnuka,
ya Sarkin Musulmi. Halifa da sauran
jama’a suka yi
mamakin wannan labari na
yarinya, mamaki mai yawa.
Yayin nan Halifa ya yi umurni
da a rubuta wannan labari a
ajiye shi domin ya zama abin misali
ga al’umma mai zuwa.
Sannan ya dubi yarinya mai
jiran kofa ya ce, ki labarta
mana da abinda
Zan dakata anan saikuma Allan ya kaimu gobe zamucigaba
Admin AA Misau ke magana
Guyson kenan
08161272634
014. HIKAYAR DAN
DAKO DA YAN MATA
.
Copied
AA Misau Ke magana
.

Labarin Yarinya
Mai Jiran Kofa
.
(1) Bayan yarinya shugabar yan
mata ta kare bayar da
labarinta, sai Halifa ya dubi
yarinya ta biyu, mai jiran kofa,
ya ce, ki labarta mana da
abinda ya same ki na daga tabon
bulala da muka gani a
jikinki. Yarinya ta fara bayar
da labarinta, da kuma dalilin
tabon bulala da ke jikinta, ta
ce: Ya Sarkin Musulmi, ubana ya
kasance attajiri ne, ya mallaki
dukiya mai tarin yawa wadda
Allah kadai ya san yawan
adadinta. Kuma na kasance ni
kadai ce ‘ya tasa. Bayan ya mutu, na
gadi dukkan dukiya
tasa. Bayan yan shekaru kadan
na yi aure. Na auri wani saurayi
wanda shi ma ubansa ya mutu
ya bar masa gadon dukan
dukiyarsa. Bayan aurenmu da
shekara
guda, sai Allah ya yi masa
rasuwa. Na gada daga gare shi
dinari dubu tamanin da gidan
da mu ke ciki, shari’a ta bar
mini. Bayan na gama takabarsa, na
sa aka dinka
mini riguna guda goma, aka
kawata kowace riga da kayan
ado kala-kala, a takaice dai
kowace riga sai da aka kashe
dinari dubu wurin dinka ta. Ina zaune
a gidana, wata rana
sai ga wata tsohuwa ta shigo,
mai daurarriyar fuska, mai
nadadden goshi da nitattsun
idanu, da wawilon baki,
harshenta na rawa, wuyanta
karkatacce tamkar da wakar
wani mawaki da yake cewa:
“Muguwar tsohuwa mai sanar
da Ibilis da abin da bai sani ba,
a cikin aikinta mafi sauki ta
kan dabaibaye alfadara dubu
da abawar tautau da aka
wadarta. Muguwar tsohuwa mai
halasta haram da kaifin
zamba da kissarta, da za a
auna makircinta da nauyin
dutsen Uhudu da ya rinjaye
shi.” Yayin da tsohuwa ta shigo
wurina, ta yi mini sallama, na
amsa mata. Sannan ta durkusa
ta gaisheni da girmamawa, ta
ce da ni, ‘yata, na zo ne in nemi
wata alfarma a gare ki. Yarinya ta
kasance a gare ni,
yau ne kuma daren amarcinta,
ina so ki sami ladarta da tawa,
ki hallarci zaman amarcinta, ki
zamanto bakuwarta ta
musamman, ita mai yawan tunani ce
domin rashin gata,
ba mu da kowa sai Allah
madaukakin Sarki. Yayin nan
tsohuwa ta yi kuka,
ta sumbaci kafafuna.
Tausayinta ya kama ni, na
yanke shawara zan karbi goron
gayyatarta. Na ce da ita, na ji
na dauka. Ta ce da ni, ki shirya da
isha’i zan zo mu tafi tare da
ke. Yayin nan ta sumbaci
hannuna ta fita. Na tashi na yi
wanka, na yi
kwalliya sosai na shirya jikina
tsaf, na debi kudi masu yawa
wanda zan ba amarya, na
zauna ina jiran isowar
tsohuwa. Jim kadan sai ga ta, ta
gabato ta ce da ni, ya
shugabata tashi mu tafi,
jama’a na can duk sun hallara,
na shaida musu da zuwanki,
sun yi farin ciki da
kasancewarki babbar bakuwa ta
musamman, suna can suna
jiran zuwanki. Na tashi na bi
tsohuwa a baya,
muna ta tafiya tinkis-tinkis har
muka shiga cikin wani
kwararo, da shigarmu
kwararon na ji wani irin
kamshin turare na tashi a cikinsa.
Muka nufi kofar wani
katafaren gida, muna dada
dosar gidan kamshin nan na
karuwa, har muka iso kofar
gidan. Na gan shi gida ne
ginanne na kasa, an adanta bayansa
da zane. Muka ishe
masu gadin kofa a tsaye. Da
suka gan mu sai suka bude
mana kofa muka shiga. Muka ishe
zaure, an rataye
fitulu a kowace kusurwa ta
zauren suna ci, suna haske
tamkar rana. Muka wuce cikin
gidan muka shiga cikin wani
soro, muka ishe shi da shimfida ta
kilisai masu taushi,
ga fitulu ko’ina suna haske
tamkar rana. Ga kuma gado na
mirmir an yi masa ado da
lu’ulu’u da jauhari, an lullube
shi da shifida Siniya da hadalashi
namusiya. A zaune akan gadon, na
ga
yarinya cikin sitira, ka ce ita
farin wata ce a cikin taurari.
Tana gani na, ta sauko daga
kan gado ta tare ni da murna
da farin ciki tana cewa, maraba,
marhabin da ‘yar
uwata da ta zo ta debe mini
kewa, ta faranta zuciyata. Ta
kama hannuna ta zaunar da ni
akan gadon nan, sannan ita ma
ta zauna kusa da ni, tsohuwa kuwa
ta fita ta bar mu. Bayan mun zauna,
yarinya ta
dube ni ta ce, ya ‘yar uwata,
aminiyata, ina da dan uwa
wanda ya gan ki wata rana,
ban san lokacin ba, ya ji yana
son ki da aure. Shi saurayi ne mafi
kyawo daga gare ni,
zuciyarsa ta so ki, so mai
tsanani, ya rasa yadda zai yi ya
bayyana miki. Ya ba wannan
tsohuwa kudi ta shirya wannan
hila a gare ki domin ki yarda ki zo
nan gidan dan uwana, shi
kuma ya sami damar da zai
bayyana miki abun da yake
cikin ransa. Dan uwana yana
son ya aure ki bisa ga sunnar
Ma’aiki, babu aibi ga halal. Ko kin
yarda na kira shi domin ku
daidaita da juna? Yayin da na ji
zancen wannan
yarinya, na dubi kaina, na ga
na abku a cikin gida, ga masu
gadi tsare da kofa, babu
hanyar guduwa. Na ce da ita na
yarda. Ta yi farin ciki, ta tashi ta bude
wata kofa da take
boye a cikin soron. Na ga
saurayi ya fito daga cikin wani
daki. Wannan saurayi da kyau
ya ke tamkar wakar wani
mawaki da ya ke cewa: “Alheri ya
yawaita ga Allah da
ya yi baiwa a gare shi, ya
halicce shi, ya daidaita shi, ya
tara masa dukkan kyawo, ya sa
dukkan talikkai su dimauta da
ganin kyawonsa. An rubuta kyawo
karkashin
kundukukinsa, mun shaida
babu birbishinsa da kyawo a
cikin talikai” Yayin da na dube shi,
nan take
kibiyar sonsa ta daki zuciyata,
na ji babu wanda na ke so
kamar shi. Lokacin da ya shigo
sai ya sami kujera ya zauna. Ya
gabatar mini da bukatarsa ta son
aurena, na amince da ita. Bayan an
daura mana aure da
wannan saurayi, a daren
amarcina muna zaune tare da
shi, sai ya dube ni ya ce,
amaryata ina so ki yi mini wani
alkawari, alkawarin kuwa shine,
zuciyarki ba za ta taba
karkata ga wani na ba, muddin
ina raye kuma a matsayin
mijinki, domin ni na kasance
mai tsananin kishi ne. Na ce da
shi na yarda da wannan alkawari ya
shugabana. Ya
dauko Alkur’ani mai tsarki ya
ce in rantse akan wannan
alkawari. Na rantse masa da
ba zan kula ko wane da namiji
ba. Na zauna tare da mijina, cikin
jin dadi da annashuwa har
tsawon wata guda. Wata rana
na nemi izini ga mijina, ina so
in tafi kasuwa in siyo wadansu
zannuwa, ya yi mini izini da in tafi.
Bayan na rufe jikina kaf
da tufafi, na riki tsohuwa
domin ta raka ni zuwa kasuwa.
Muka tafi har muka iso cikin
kasuwa. Tsohuwa ta ja ni zuwa
rumfar
wani yaro tajiri mai sayar da
zannuwa na ado. Da muka isa
muka yi masa sallama, bayan
ya karba muka sheda masa
cewa mun zo ne domin sayen
zannuwa, na ce ya kawo mana
zannuwan da babu irin su
wajen kyau a cikin shagonsa,
komai tsadarsu. Ya ce, to. Ya
kawo mana kujeri muka
zauna, shi kuma ya shiga cikin shago
domin zabo mana kalar
zannuwan da muke so. Bayan
saurayin nan ya shiga
cikin shago, sai tsohuwar nan
ta dinga yabonsa da koda shi a
wuri na. Tana cewa ai wannan
yaro mutumin kirki ne, yana da
ladabi, ubansa ya mutu ya bar masa
dukiya mai yawa. Na
dube ta na ce, ba na bukatar ki
yabe shi a wurina, muradina
mu sayi abin da ya kawo mu
mu juya zuwa gida. Bayan yaro ya
dawo da
zannuwa, na zabi wadan da na
ke so, na ce su yi ciniki da
tsohuwa, suka yi ciniki, na ba
tsohuwa kudi na ce ta ba shi.
Da ta ba shi kudin sai ya ki karba, ya
ce, haba wannan shi
ne zuwanku na farko shagona,
bai kamata na karbi kudinku
ba. Tsohuwa ta ce idan bai
karba ba me ya kamata mu yi?
Na ce mu mayar masa da
zannuwansa, mu tafi wani
shago mu siya. Yaro ya dube ni ya ce,
wallahi
ba na karbar ko daya, dukkan
abin da ke cikin shagon nan,
sumba daya da zan yi miki ta fi
shi. Da za ki amince na
sumbace ki, sumba daya, da na ba ki
dukkan kayan da ke cikin
wannan shago nawa. Na ce, tir
da kai! Allah ya kare ni da in
ha’inci mijina, shin ko ba ka
san cewa ni matar aure ce ba?
Tsohuwa ta dube ni ta ce, haba
‘yata! Don dai sumba guda me
zai same ki, ki yarda da
wannan yaro, hakika ya jarrabu
da son ki, ki ji tausayinsa ki
biya masa da bukatarsa. Na ce da
ita, hala kin manta da cewa
ni rantsattsiya ce daga kula
wani namiji ba mijina ba? Ta ce da
ni, bar shi ya sumbace
ki sumba daya, babu abin da
zai same ki, ya ‘yata da me
sumbatar ki za ta amfane shi?
Abin da zai yi cikin yan dakiku
ya gama, mu kuwa mu yi tafiyarmu.
Tsohuwa ba ta
gushe ba tana kyautata mini
wannan abu tana gusar da
laifin aikata haka har na
amince da bukatar yaro. Na rufe
fuskata da mayafi, yaro
ya zo kusa da ni, ya sumbaci
kundukukina ta cikin mayafi.
Yayin da ya sumbace ni, sai ya
gatsa mini cizo da hakoransa,
cizo mai zafi har sai da ya cire fata
daga kundukukina. Na
fadi kasa somammiya saboda
zafin wannan cizo. Yayin da na farka,
sai na ga
tsohuwa rungume da ni, shago
a rufe, babu yaro babu
dalilinsa. Tsohuwa ta ce, abin
da Allah ya so shi ne mai
yiwuwa, wannan yaro ya cuce mu. Ki
tashi mu

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment