Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafi gida, ni na
zo miki da maganin da za ki
warke daga wannan cizo da
gaggawa. Bayan jimawa muka
tashi ina cikin gayar tunani da
tsannin tsoro har muka iso zuwa
gida. Ban dade da dawowa ba, sai ga
mijina ya shigo, ya na duban
fuskata sai ya ce da ni, me ya ji
miki ciwo a kundukukinki,
wuri mani’imci? Na ce da shi,
ya yin da muka fita zuwa kasuwa,
mun hadu da rakuma
akan hanya, an yiwo mata laftu
na itace, garin in kauce in bata
hanya, itacen ya karce ni a
kundukuki har ya ji mini ciwo. Mijina
ya ce, babu shakka gobe
in yi karar mai rakumar nan ga
alkali, a daure shi kuma a
rataye wanda ya dauko wa
itacen ko wane ne a cikin
birnin nan. Na ce da shi, na roke ka
don Allah kada ka ga
laifin kowa. Ni jaka na hau sai
ta yi tutsu da ni, na fadi kasa,
dutse ya ji mini ciwo. Ya ce,
gobe kuwa na tafi gun Sarkin
Musulmi, in hakaita masa da wannan
hikaya, a kashe duk
mai jakin da ke cikin birnin
nan. Na ce, yanzu kai ka sa a
kashe mutane duka saboda ni?
Wannan al’amari ne da Allah
ya gudanar bisa ga ikonsa da
hukuncinsa, me za ka yi? Ya ce, babu
makawa ga haka.
Ya zabura ya mike tsaye cikin
fushi, ya yi kururuwa, kururuwa
mai tsanani. Kofa ta bude,
babbakun bayi guda uku suka
fito ta kofan nan, suka jawo ni daga
shimfidata, suka yashe ni
tsakar gida. Ya umurci bawa daya
daga
cikinsu da ya rike kafadata ya
zauna bisa ga kaina. Ya umurci
na biyu da ya zauna bisa
gwiwowina, shi danne
kafafuna. Na uku ya zo da takobi ga
hannunsa, ya ce, ya
shugabana in sare kanta da
takobin nan, ko in raba ta gida
biyu kowa ya dauki daya? Mijina ya
ce, sare ta gida biyu,
kowa ya dauki daya ku jefa ta
cikin kogin Dujillati, kifi ya
cinye ta, wannan shi ne
sakamakon wanda ya yi ha’inci
ga rantsuwar masoyi.
AA Misau Ke magana
Zan dakata anan Sai Allah yakaimu gobe
Suleiman Zidane Kd
015. HIKAYAR DAN
DAKO DA YAN MATA .
.
Copied
AA Misau
Ke magana
.
Labarin Yarinya
Mai Jiran Kofa
.
(2) Yarinya ta ci gaba da labarinta
da cewa: Lokacin da mijina ya
ji jawabina, ya zabura ya mike
tsaye cikin fushi, ya yi
kururuwa, kururuwa mai
tsanani. Sai na ga kofa ta bude, bayi
guda uku, bakake suka
fito daga cikinta, suka jawo ni
daga kan shimfidata, suka
yasar da ni tsakar gida. Ya umurci
bawa daya da ya
danne kaina, ya umurci na biyu
ya danne kafafuna. Bawa na
uku ya zo da takobi a
hannunsa ya ce, ya shugabana
in sare kanta ko in raba ta biyu kowa
ya dauki rabonsa. Mijina
ya ce, raba ta gida biyu da
takobinka, kowa ya dauki
daya, ku tafi ku jefa ta a cikin
kogin Dujillati kifi ya cinye ta,
wannan shi ne sakamakon mai yin
ha’inci ga rantsuwar
masoyi. Sannan sai ya waka
wadan nan baitoci: “Idan abokin
tarayya ya
kasance ga masoyiyata, na
haramtawa kaina son ta. Ya
raina mutuwata ita ta fi alheri,
ga son da ya kasance akwai
kishiya a cikinsa” Bayan ya gama
wannan waka,
ya dubi bawan nan ya ce, raba
ta biyu ya Sa’adu! Bawa ya
tsiraita takobi, ya daga ta
sama, sannan ya dube ni ya ce,
ki na da sauran bukata? Ki na da
wata wasiyya da za ki yi?
Wannan shi ne lokacin
rayuwarki na karshe a duniya. Yayin
nan na daga kaina, na
dubi halin da na ke ciki. Na
tuna da da daukakar da na ke
da ita, yau ga shi na zamanto
makaskanciya, na tuna irin
dukiyar da na ke da ita, da
matsayina, sai hawaye ya
zubo daga idona, shar shar
shar. Na waka wadan nan
baitoci: “Na zaunad da zuciyata cikin
so, ta zauna. Na hana idona
barci, suka hanu. Na saukad da
ku cikin zuciyata, ta karbe ku.
Kun yi mini alkawarin zama
cikin so, amma da kuka mallaki
zuciyata sai kuka
warware. Ba kwa jin tausayin
bakin cikina a gare ku? Shin
kun amince da juyawar
zamani ne? Shin ba ku yarda
da kaddara ba ne? To ina rokon ku,
domin Allah da Manzonsa,
idan na mutu ku rubuta a kan
allon kabarina, wannan mai
bege ce, ta sadaukar da ranta
ga abin da ta ke so, kuma ta
mutu a kan soyayya.” Yayin da
mijina ya ji wannan
waka, sai fushinsa ya karu a
kan fushi, sai ya yi wannan
waka ya na cewa: “Kin bar abin son
zuciyarki,
kika so abin zargi, kika nado
zunubi wanda ya halasta
kisanki. Kika nufi abokin
tarayya cikin tsarkakakken
son da ke tsakanimmu. Gaskiya ni
zuciyata ba ta yarda
da abokin tarayya a cikin
soyayya.” Yayin da ya gama waka
tasa,
na yi kuka, na rarrashe shi, na
ce shi yafe mini daga kisa, ya
dauki dukkan dukiyata ta
zama fansar laifin da na yi
masa. Na kuma ce da shi, da
girmanka idan ka bar ni, ba ka
kashe ni ba, Allah zai hukunta
tsakaninmu, hukunci
tsarkakakke. Ka daukaka mini
nauyin bege, ni na gajiya daga
daukar riga biyu in ribanya. Ba na
al’ajabin tallafar raina,
amma ina al’ajabin ina za ka
da alhakina? Da ya ji wannan
magana
tawa, sai ya shure ni, ya zage
ni, sannan ya yi wannan waka
ya na cewa: “Kun shagala da mu,
kuka so
wanimmu. Kun bayyana
kaurace mana, ba tare da mun
yi muku laifi ba. Tilas mu bar
ku, tun da kuka bar nufinmu.
Mu hakura da barinku, tamkar da
kuka bar mu.” Yayin da ya gama
wannan
waka, ya daka wa bawan nan
tsawa ya ce, raba ta gida biyu,
ba ta da wani amfani a gare
mu. Lokacin da bawa ya gabata, ya
daga takobinsa sama zai sare
ni, na sakankance da mutuwa,
na debe kauna daga rayuwa,
na bar al’amarina ga Allah,
Madaukakin Sarki. Na yi kalmar
shahada, na rufe idona
ina jiran na ji saukar takobi a
jikina. Daga nan sai ga
tsohuwa ta shigo. Ko da ta gan
ni cikin wannan yanayi, sai ta
fahimci abin da ya faru. Nan take ta
fadi gaban mijina,
karkashin kafafunsa, ta na
sumbatarsu. Ta ce, ya saurayi, don
martabar
goyon da na yi ma ka, ka yafi
wannan yarinya, ita ba ta
aikata wani zunubi da wannan
hukunci ya wajabta gare ta ba.
Kai yaro ne karami, ina ji maka tsoro
daga addu’a tata,
domin addu’ar wanda aka
zalunta abar karba ce ga
Ubangijin talikkai. Yayin nan
tsohuwa ta fashe da kuka. Tsohuwa
ba ta gushe ba tana
rarrashin mijina, tana kuka
tana buga kanta ga kafafunsa,
har ya ce da ita, tashi na yafe
mata, amma babu makawa in
aikata mata tabo mabayyani a jikinta
tsawon rayuwarta. Ya umurci bayi
suka tube ni
daga tufafina, aka hallaro
masa da tsumagiyar giginya,
ya saukar mini da duka a
jikina, duka mai tsanani. Bai
gushe ba yana duka na, bisa ga
bayana da hakarkarina, har na
suma na faku ga barin duniya
domin tsananin bugu. Ya
umurci bawa daya da ya
dauke ni, idan dare yayi, ya
jefar da ni a cikin gidana. Lokacin da
na farka, na gan ni
a yashe cikin gidana, na yi
godiya ga Allah da ya kubutar
da raina. Na yi ta jiyyar
wannan duka da mijina ya yi
mini, har na warke sarai. Amma
wannan tabo na bugu
yana nan tamkar da gan shi a
jikina, ya Sarkin musulmi. Bayan na
warke, na dawo
gidan mijina, sai na tarar da
gidan nan a rushe daga
farkonsa har karshe, na yi
mamaki a kan faruwar
wannan abu. Daga nan sai na ziyarci
wannan ‘yar uwa tawa
a gidanta. Na same ta tare da
wadan nan karnuka, ta labarta
mini abin da ya faru duka, gare
ta da kuma yan uwanta. Na
debo dukiyata na dawo gidanta muka
ci gaba da zama
tare. Muna zaune a cikin gidan nan,
sai ga wannan yar uwa tamu,
wacce ta kasance ita ce
karamarmu, muka dauke ta a
matsayin Jekadiyarmu, wadda
ke zuwa kasuwa tana sawo mana
kayan abinci da na
marmari. Muka zauna a
wannan gida babu ruwanmu
da maza, saboda abin da ya
faru da mu a baya, na daga
maza. Na kasance duk lokacin da na
ji wakar soyayya, tsikar
jikina ta kan tashi, hankalina
ya kan gushe har na suma,
saboda wannan abu da ya faru
da ni. Wannan shi ne labarina
da kuma dalilin tabon bugu da ke
jikina, ya Sarkin Musulmi. Halifa ya
yi matukar mamaki
da al’ajabin labarun wadan
nan yan mata. Ya yi umurni da
a rubuta wadan nan hikayoyi
na yan mata da kuma na
samari masu ido daya-daya a littafi,
a ajiye su a dakin adana
littattafai, domin na baya su
karanta su amfana da darussan
da ke cikin wadan nan
hikayoyi. Sannan ya juya ga yarinya
shugabar yan mata, ya ce,
yalla ko kin san inda aljanar da
ta sihirce yan uwanki ta ke?
Yarinya ta ce, a’a, amma ta ba
ni wani yanki na gashin kanta, ta ce
duk lokacin da na ke son
ganinta, na kona sili daya za ta
bayyana da gaggawa, ko da
kuwa tana bayan dutsen kaf. Halifa
ya sa yarinya ta kawo
gashi daya na aljana, ya sa aka
hada garwashin wuta, ya jefa
gashin a ciki. Lokacin da
hayaki ya tashi, iska ta kada
shi ko’ina, sai suka ji kasa na
girgiza, kamar za ta tsage.
Wata irin tsawa da hargowa
ta cika fadar. Jim kadan sai ga
aljana ta bayyana, cikin
kyakkyawar shiga ta
musulunci, da ma Allah ya yi ta
musulma ce. Tana bayyana, sai ta
gabatar
da sallam ga Halifa da cewa,
amincin Allah ya tabbata a
gare ka, ya Sarkin Muminai.
Halifa ya amsa mata da cewa,
amincin Allah ya tabbata a gare ki.
Sannan ta ce, ka sani ya Halifa,
wannan yarinya ta yi mini
taimakon da ba zan manta da
shi ba har duniya ta nade,
domin ita ce ta kashe mini
babban makiyina a duniya. Domin in
saka mata da
wannan alheri da ta yi mini, na
sihirce wadan nan miyagun
yan uwa nata, wadan da suka
yi niyyar halaka ta, zuwa
karnuka. Da na yi niyyar in kashe su
ne, sai na lura da
cewa za ta damu da hakan, shi
ya sa ban kashe su ba. Amma
bisa ga girmamawarka da
yardar yarinya, ya Sarkin
Musulmi, idan kuna so in mayar da
su ga siffarsu ta asali, to
zan mayar da su, na kasance
musulma mai biyayya ga
shugabanni. Halifa ya ce, na roke ki
tare da
yardar yarinya da ki mayar da
su ga siffarsu ta asali. Bayan
wannan sai mu binciki
al’amarin wannan yarinya da
aka yi wa duka, mu nemo wanda ya
zalunce ta, mu fitar
mata da hakkinta. Aljana ta ce, na ji
na karba.
Yanzun nan zan mayar da su
ga siffarsu ta asali. Amma
wanda ya doki yarinyar nan,
mutum ne makusanci da kai,
karewa ma, a cikin iyalinka ya ke. Ta
ce a kawo mata tasa da
ruwa. Da aka kawo mata, ta yi
wani zance ta tofa a cikin
ruwan. Sannan ta yayyafa wa
karnukan nan ruwan, ta ce, ku
fita daga cikin wannan siffar, ku
komo ga siffarku ta
mutane. Nan take karnukan
nan suka juye zuwa
kyawawan yan mata, son
kowa kin wanda ya rasa,
tamkar yadda suke a da. Tsarki ya
tabbata ga mahaliccin
wadan nan yan mata. Bayan aljana
ta mayar da yan
matan nan ga siffarsu ta asali
sai ta ce da Halifa, ya Sarkin
Musulmi, ka sani cewa ba
kowa ne yayi wa yarinyar nan
duka ba face danka Aminu. Shi ne ya
ji labarinta, da
kyawonta. Ya nemi yardarta
suka yi aure. Aljana ta kwashe
labari duka ta fada wa Halifa,
tamkar dai yadda yarinya ta
fada masa. Da Halifa ya ji haka, ya
ce,
tsarki ya tabbata ga Allah,
wanda ta sanadiyyata ne
wadan nan yan mata, da suka
shafe lokaci mai tsawo suna
cikin siffar karnuka da azabtarwa,
suka sami
yancinsu. Sannan ya sa aka
nemo masa dansa Aminu. Ya sa shi
ya biya yarinya
diyyar tabon da yayi mata a
jiki. Da yake kuma suna son
juna, ya sa aka mayar da
aurensu. Ya sa aka gina musu
wani gida mai kyau, fiye da wancan
da ya ruguje. Ya aurad da yarinya
shugabar
yan mata, da yan uwanta biyu
da aka kubutar daga siffar
karnuka, ga samarin nan uku
masu ido daya-daya, da ma
‘ya’yan sarakuna ne. Ya nada
samarin nan hakimai, ya sa su
a cikin mulkinsa. Ita kuma
yarinya jekadiya, Halifa ya
aure ta, ta zama matarsa, ya
kebe mata shiyarta dabam, ya
ba ta kuyangi masu yawa, wadan da
za su rika yi mata
hidima. Suka zauna cikin jin
dadi da more rayuwa, har mai
rabawa ta zo ta raba. TAMMAT.
Anan hikayar tazo karshe
AA Misau Ke magana
Suleiman Zidane kd
Domin samun wasun sabbin Littafi 08161272634
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment