Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din datagama sallah tasaka ta fito tana Shirin nufar kofa ya rungumota ta baya Yana sauke ajiyar zuciya a hankali yakai fuskarsa Kan wuyanta Yana cewa"

Karkiyi wahalan tafiya Zaki qarawa kanki ciwone basai kintafiba nasan irin fushi da masifan dake cinki zo ki zauna ki huta idan kin warke Zaki iya sauke duka fushinki ba damuwa bane.

Daukanta yayi yadawo da ita palon ya zauna Yana kwantar da ita a jikinsa yace"

Ki daina Bata ranki Babu Wanda zaisan me qanin qawarki yamiki bare a rainaki Kiji kunya nasan duk wannan ne damuwar ko???" Yafada Yana shinshina wuyanta da sauke Mata numshinsa me dumi da qamshi tanajin hannunsa na yawo Kan shafaffen cikinta Yana shafawa tafara kokarin miqewa ya riqeda Yana kwantar da kansa a bayanta.

Yamma nasake dosowa zazzabinta ya dawo me qarfi ya sake Bata magani tareda kwantar da ita cikin jikinsa ya rufe zafin jikinta na shiga jikinsa nasa Dan daga ita sai qaramar shimin daya Sanya Mata kuka yadawo sabo dama Kuma tunda garin ya waye take tsiyayar hawaye Bata dainaba baqin cikin duniya ganin takeyi yau yaqare acikin zuciyarta da rayuwarta datake ganin ta rushe saidai har cikin ranta bazata iya wannan rayuwarba dashi sbd Babu Randa matsayinsa na qanin qawarta zai goge a ranta yanzu Kuma yakai kololuwar wuce hurumin haquri da juriyarta Dan Haka yakai maqura bazata Bari wannan abin daya faruba yabasa damar ji da daukan kansa cikakken miji me iko agareta,
Bazata Bari yasake samun wannan damarba dan Haka ya dauka hakan amatsayin kuskure zata sanarda iyayensu araba auren kawai Koda hakan zai kawo bacin Rai tasan zai wuce.

Koda gari ya waye ta bude idanuwanta akan fuskarsa suka sauka ta juyar da Kai tana cire jikinta daga nasa ta sauka Kan gadon tareda ficewa dakin ta koma dayan dakin tayi sallah tahirya cikin hijab ta fito palon da niyar ficewa saigashi tagansa a tsaye cikin jallabiya da waya da laptop dinsa a hannu sai key din mota ya kalleta da fararen idanuwansa kafin ya tako ahankali ya qaraso gabanta Yana kallon fuskarta ya ranqwafa ahankali yakai bakinsa saitin kunnenta ya furta"

Yanzune kike Kama da matan sure cikkaki Dan Haka be very careful idan bana nan,
Maganar aikinki Kuma Zaki iya komawa kafin wani dalilin na hanaki zuwa ya bayyana.

Kallo ma Bata samu damar binsa dashiba ta nufi kofar ta fice Allah yasa driver zai jasu Dan Haka tana fitowa motar ta nufa ta shige Koda yafito fuskarsa a matuqar kame sai zuba qamshi da kwarjini yake kamar bashine yagama maganaba aciki yanzu ta hade fuska sosai tana kallon gefe harya shigo aka tada motar suka bar gidan Babu Wanda yasake magana acikinsu suna barin anguwar suka hau titi ta bude Baki tareda Dan kallon drivern ta dauke Kai tana cewa"

Kayi parking Zan sauka anan.

Ta madubi ya kalla uban gidansa yaga ko kallonsa baiyiba yasan ba wannan maganar Dan hakan Bai tsayaba yaci gaba da tafiya har Saida suka Kai gida ta kallesa cikin bacin Rai zatai magana Deen din ya waiwayo ya kalleta Kai tsaye yace"

Bakya gane shiru ne idan anmiki?
Koba yau ba duk ranarda na samu labarin anganki a hanya bazaki Kuma marmarin ko fita ba.

Anayin parking ta fito ta daidai fitowar Hannah zata fita a mota ta gansu zuciyarta na wata irin bugawa da ganinsu tare suda akace musu Naj tayi tafiyar aiki tareda Sarah ko hajjo ma Haka Hanifa ta fada Mata to daga Ina suka hadu suke tahowa gida tare da sassafen Nan bayan shi Daren yau jirginsa zai tashi na komawa.

Dannewa tayi tana qarasowa gurinsa cikin wani irin yanayi na Jan hankali tana cewa"

Good morning my Zawj.

Kota kansu batabiba tayi hanyar sashen hajjo tana tafiya ahankali Dan har lokacin Bata Gama warkewaba.
##MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡

09134848107

*_DM 28_*
Da wani irin kallo yabi bayanta da fitinannin idanunsa Yana karewa tafiyar datakeyi ahankali kallo wadda ke sake tabbatar Masa da ita din tasace tako ina,wannan hurumin nasane iya shi daya.
Saidata shige ya dan sake kamewa Yana kallon Hannah kadan wadda tagama shagwabe Masa tana cewa"

A hanya ka hadu da Naj ne ka rage Mata Hanya?
Sbd nasan dai cewan tayi tafiyane tareda secretary dinta yakamata ace tare suka dawo.

Wucewa yayi hanyar sashensa batareda ya Bata amsar tambayar dataiba cikin muryarsa datake bayyanarda kamewarsa Yana tafiya tana biye dashi yace"

Tambayan nada mahimmanci ne?

Zatai mgna ya bude kofar palonsa tareda waiwayowa kadan sai alokacin ya kalleta dakyau tana sanyeda Gucci pencil jeans da farar long sleeves me yankakken hannu sai scarf qarami dake kanta daure ya dauke Kai Yana nuna Mata kofar da ido da alamar kosawa da ita yace"

Kinada abin yi ne idan kinbini ciki?

Dakatawa tayi tana kallonsa cikin tsananin sonsa dayasa Sam batajin haushi ko zafin duk abinda zai Mata ta saki wani yalwataccen murmushi tana kashe Masa ido daya tace"

A yanzu dai banidashi Amma zuwa gaba nice nakeda abinyi aciki
Zan fita,bye,take care I love you.

Juyawa tayi ta bar gurin tana murmushin farin cikin ganinsa Dan kwananta biyu rabonta da ganinsa saidai waya shima idan ta nace da kirane yake dagawa.

Rufe kofarsa yayi bayan ya shige ya aje wayarsa da key din mota ya nufa hanyar bedroom dinsa Yana zare jallabiyar jikinsa.

Maimakon ta nufi motarta datai niyar fita saita juya ta nufa hanyar sashen hajjo tana ayyanawa ranta son sanin meyake faruwa.

Naj ko data shiga palon Babu kowa saisu ruqayyat dake aikin gyara koina hajjo na daki,hanifa ma tana dakinta tana bacci Dan Haka Kai tsaye dakinta ta wuce tana amsa gaisuwar dasu ruqayyat ke Mata da Kai Dan bazata iya bude bakin ba Yar tafiyar datai tasa tanajin Kamar ciwon datakeji ya dawo sabo ta lallaba ta shige dakinta tareda rufowa.

Hijab dinta tafara cirewa kafin ta zare kayansa dake jikinta takai cikin water ta jefa ta shige toilet tareda hada ruwa masu shegen zafi ta shige tana sauke ajiyar zuciya tareda rufe ido ahankali sbd Dan sauki da rahamar dataji sai hawayen dasuka balle suna tsiyayo mata ta rasa Ina zata saka ranta taji saukin abinda takeji a zuciyarta Dan bazata iya wannan aurenba,suqeta al'amarin keyi gabaki daya.

Ta Jima sosai acikin toilet din kafin tafito bayan tayi hadda wanka Wanda yasa jikinta sakewa sosai saidai fuskarta da zuciyarta cike suke da zallar damuwa da baqin ciki
Ta shafa Mai kadan ta shirya cikin riga da skirt na atampa dark purple dataiwa farar fatarta kyau sosai musamman yau din da fuskarta tayi fresh duk da kumburin idanuwanta datasha kuka Yana nunawa ta fesa turare ta fito kanta ba dankwali sai qaramar hular da Bata rufe gashinta duka ba hakan Kuma ya qara Mata kyau ta nufa dakin hajjo tana kokarin nutsar da kanta Dan kada agano halinda take ciki.

Saida takai tsakiyar dakin ta tsaya cak ganinsa zaune gefen hajjo gabaki daya dakin yadauki qamshinsa yayi wanka yana sanyeda riga da wando na farin yadin filtex me laushi da tsada
Yaji shigowarta da dakatawarta Bai juyoba hankalinsa na Kan hajjo dasuke mgn Amma ganin Naj din itama saita tsaya kallonta cikin mamaki tace"

Najma kindawo ne?
Yanzu kuka dawo kokuwa cikin dare?
Qaraso mana,
Sai tafiya Kuma takamaki daga office Baki dawoba,
Anya wannan aikin yakamaceki kuwa yanzu Najma?
Shi wannan na tambayesa tun ranar da kukai tafiyar yace da saninsa Kika tafi,ga wayarki akashe haniface kawai tace tana samunki Kuna mgn.

Daqyar ta iya qaqalo wani munafukin murmushi tana kallon hajjon a natse tace"

Da safen nan nadawo duk Kuna bacci Bari naje gurin Hanifa kafin ki Gama.

Juyawa tayi ta fice batareda tajira wani zancenba Dan
Batareda ya waiwayoba yasaki wani irin murmushin dayasa hajjo kallonsa da dukkanin nutsuwarta cikin mamaki dan ba abune daya fiya yiba ta maido hankalinta kansa yace"

Yaushe ka shirya tafiya da matarka?

Bai kalletaba hankalinsa nakan waya yace"

Saita shirya Bina da kanta.

Bana tunanin zatai hakan sbd haryanxu Bata amintaba da auren
Kuma Sam banason a takurata Akan komai.

Wani shegen guntun murmushin yakuma saki Yana cewa"

Kar a takurata abarta harta Aminta dan kanta.

Tsoki hajjo tasaki cikin quluwa dashi tace"

Tashi ka ficemun sbd kedai haryau zance dakai bayada Dadi
Mutum saiya zage yamaka mgn me tsayi ko mahimmanci ka jeho Masa kalma daya amsa,banason kayan takaici tashi kaje kafin na qarasa quluwa da wannan muguwar dabi'ar taka mara Dadi.

Bai tashiba saima kallonta da yayi yanaci gaba da duba wayarsa Yana cewa"

Ahaka fa kike damuna yaushe Zan dawo idan bana nan.

Murmushi tasaki tana cewa"

Ta Nan ka bullo Kuma.


Naj Kuma tana fitowa dakin ta nufa dakin Hanifa ta tura kofar Kai tsaye ta Shiga saiga Hannah zaune a kejarar dakin tana Taya Hanifa yanka qatuwar guava data tashi tunda safen da marmarin ci
Da mamaki Hanifan ke kallon Naj fuskarta na yalwatuwa da farin cikin ganinta ta ware Hannu tana cewa"

Hey sweetheart sannu da dawowa nayi kewarki sosai sirikata.

Tsuke fuska Naj din tayi tana Mata kallon daya sanyata rufe Baki tana cewa"

Sorry sorry.

Qarasowa tayi tana zama bakin gadon kusada Hanifan ta bude Baki cikin kulawa tace"

Ya ya?ya babyn?

Lafiya kalau muke,ya Hanya? Da gajiyan tafiya?

Alhmdlh" kawai ta furta tana basar da zancen ta hanyar Dan kallon Hannah datace"

Naj sannu da Hanya?
Inane kukaje aikin ne hala?

Yi tayi kamar bataji Hannan ba ta miqe tana nufar kofa tace"

Zanci abinci a dining.

Miqewa Hanifa tayi tana cewa"

Nima yunwar nakeji,
Hannah ko Zakiyi breakfast damu?muke ko.

No nariga naci abinci bana buqatansa qarawa Zan fitanema nace Bari nashigo na dubaki tun shekaran jiya banshigoba.

Dining suka nufa ita Kuma ta fice daga sashen batareda tasan Marshal na sashenba Dan da Babu inda zata.

Tea kawai ta iya Sha sai doya kadan da aka soya da egg sauce ta miqe tana kallon Hanifa dakecin doyar sosai tace"

Inajin Dan ciwon Kai da gajiya zanje na kwanta ko zansamu bacci kafin lokacin sallah.

Ok ki kula, Allah ya hutarda gajiya.

Daki Takoma ta Isa gadon ta kwanta tareda qarawa AC qarfi sbd zufi takeji na zazzabi dake hawa Yana sauka ajikinta ta rufe cikin bargo tareda rufe idanu ahankali bacci me qarfi ya dauketa.

Bacci Sosai tayi Bata Farkaba sai guraren la'asar ta tashi zaune ahankali tanajin tasamu sauki Sosai ko Ina nata ya sake ba laifi ta sauko gadon tareda cire kayan jikinta ta nufi toilet tadake wankan ruwan zafi sosai ta fito da walwalarta tafarayin sallar azahar da la'asar kafin ta Dan shafa Mai ta Sanya doguwar rigar atampa ta fito.

Daga hajjo har Hanifa na zaune palon Hanifa na kallo hajjo na karantunta data Saba da medical glass dinta a fuskarta,
Naj din na fitowa duk suka bita da ido hajjo Kai tsaye tana cewa"

Najma lafiyarki kalau kuwa?Naga duk kinyi wani iri kamar bakyajin Dadi?
Anya Baki debo sanyi a tafiyar Nan ba fuskarki duk ta kumbura,kodai bakyajin Dadi ne?

Hanifan ma zuba Mata idanuwa tayi tana jiran amsar da Naj din zata Bata Dan itama dai taga alamar Kamar batada lafiyar duk fuskarta a kumbure Dan ko yanzu data shiga wanka saidatasha kukan qaqa nikayi kafin tafito.

Dan murmushin Dole tasaki tana qarasawa dining tace"

Lafiyata kalau hajjo kawai dai garin akwai sanyi ne sosai shine yake damuna matuqa Amma zankira Dr sa'id saiya kawomin maganin sanyin Inshallah Kuma ma zuwa gobe Inshallah Zan warware tunda nadawo gida.

Zama tayi ta diba abinci tafara ci bayan Tasha ruwan zafi Dan tafijin dadinsu fiyeda abincin,
Saidata koshi ta taso tadawo gurinsu palon ta zauna Hanifa na janta da Hira sosai tana Dan qoqarin sakewa da amsawa
Hajjo kuwa saiyi takeyi tana kallonta sbd hankalinta kamar Bai kwanta da lafiyar ba ganin take Najma din batada lafiya boyewa takeyi sbd kada ta daga musu hankali idan taga ankwana biyu Bata warware ba zata Kira Dr sa'id da kanta yazo ya duba musu ita.

Ba laifi ta Dan sake sunata hirarsu akan babyn Hanifa da duk suka qwallafa Masa Rai har akai magriba suka shige sallah
A dakin Hanifa sukai sallar acan tayi zamanta har ishai Hanifa nata Koro Mata bayanin scanning dasukai shekaran jiya da Kuma dawowar da Isma'eel zaiyi qarshen wata.
Saida sukai sallar ishai suka Gama zantukansu da Naj daurewa kawai takeyi tana danne damuwar halinda take ciki kafin suka fito cin abincin dare.

Dukkaninsu suna zama Kan dining din ko fara cin abincin basuiba saiga qamshinsa ya fara tunkaro dining din tanajin hakan tasan waye ke zuwa Dan Haka ta Dan hade fuska tana daurewa Dan Hana kanta miqewa tabar gurin sbd hajjo dake gurin gashi tariga tana zaune ne da a tsaye take saitabar gurin..

Muryar Hannah taji cikin wani irin salon nemawa Kai gurbi tana cewa"

Hajjo anan zanci abinci Nima yau can masu aikin mum Malika abincin dasukai yayi Mai sosai zaisani zafin Zuciya.

Da Yar kulawa hajjo tace"

Eh gskia karki ci idan zai saki damuwa zoki zauna kici anan din.

Da sauri ta qaraso taja kujerar dake kusa data Marshal din ta zauna tana jifansa da wani irin kallo
Shikuma hankalinsa gabaki daya baya kanta Yana Kan abincin da Naj ta zubawa kanta taqi ko dagowa ta kalla inda suke Dan Jin take cikinta yagama cika da wani irin takaici.
##MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡

09134848107

*_DM 29_*
Hannah da kanta ta miqe tariga kowa zuba Masa abincin duk da tana iya kokarinta na riqewa da kiyaye duk wani abin dayake so dakuma ya shafesa Dan Haka abincin iya daidai Wanda tasan yanaci ta zuba masa tareda lemon juice me zuma datasan bayan _RED BULL Blue edition Energy drink_ shikadai yakesha.

Zama tayi tana zuba nata abincin kadan sbd Babu wata yunwar datakeji taci abincinta tun dazu sbd Marshal din yasa tace zataci anan din duk da zuwa yanzu da Naj ke sake zamar Mata abin takaici da baqin ciki Sam said Dole take iya zama guri daya da Naj din Dan dai kawai tana mum Malika nasata dannewane tana boyewa.

Naj cin abincin takeyi a hankali duk da yariga ya gundureta cin kawai takeyi a natse batareda ta kalla kowaba sai hajjo data kalleta cikin kulawa ganin yanda takecin abincin cikin nutsuwa ahankali duk da tasan sanyi da komai a natse hali da dabi'ar Najman ne Amma ita dai tafiyar Nan duk tasake sakurkuce Najman,
Cikin kulawa tana kallonta tace"

Najma jikin ne haryanxu?
Nace ruqayyat ta dafa Miki Ginger tea da Zuma sbd da alamar wannan sanyi ya kamaki sosai a wannan tafiyar,
Gobe Dr sa'id zaizo ya dubaki.

Dagowa tayi ta kalla hajjon tana aje spoon din hannunta cikin nutsuwa tace"

Naji sauki fa Kuma bawani ciwo bane sanyi ne kawai basai Dr sa'id din yazo ba zansha Ginger tea din zuwa gobe Zan qarasa warwarewa.

Zanfi samun nutsuwa idan Dr sa'id yazo yadubaki" hajjo tafada Kai tsaye tana kallon Najman kafin taci gaba da cin abincinta.

Shiru Naj din tayi tana daukan spoon taci gaba da cin abincin tana ganin irin kallon da Hanifa ke binta dashi tayi Mata banza Bata bi ta kantaba.
Hannah ta karba zancen da cewa"

Naj inane kukaje da Sanya zai kamaki Haka?

Sai alokacin ya dago ya 'dan zubawa Naj din ido wadda tun dazu dasuke zancen Bai dagoba Yana jinsu tambayar hannah tasa ya dago yana kallon Naj din.

Ahankali taji idanuwansa akanta Dan Haka ta sake kame fuska tanacin abinci tana share tambayar hannah da shirun yasake habbaqa tsanar Naj din aranta ta dauke Kai daga kanta ta juyo gurin Marshal din zatai mgn ya aje tissue dinda ya goge Baki Yana miqewa tsaye ahankali alamar yagama ya zuba hannayensa ahankali ya tako zuwa inda take zaune ya sunkuya ya saukar Mata da wani irin lafiyayyan kiss a kumatunta na hannun dama ya Kai Bakinsa kan kunnenta ahankali qasan maqoshi da wata irin murya me tsananin taushi ya furta"

Ki tabbata kinsha ginger tea dinnan sbd wani sanyin dazai iya kamaki.

Dagowa yayi ya kalli su hajjo Kai tsaye cikin attitude yace"

Goodnight,Mu kwana lafiya." Ya juya ya wuce yabar gurin.

Mutuwar zaune tayi abincin dake cikin bakinta na neman dawo Mata da qarfi sbd mummunan yanayin mutuwar zaunen datai,wani irin tari ya taso Mata Hanifa tayi saurin daukan ruwa tana Bata daqyar ruwan suka wuce Mata ta dauki tissue tana goge bakin idanuwanta na yin ja sbd wahalar sarqewar datai dakuma ta halin data shiga na tsananin kunya da takaicinsa,
Ta dago ahankali ta saci kallon inda hajjo ke zaune taga abincinta take ci kawai tayi kamar batamasan menene ya faruba agurin sbd JALAL tasan zaiyi fin hakan agaban ko uban waye tunda rayuwar daya tashi acikine yake Kuma rayuwa aciki gabaki daya rayuwarsa irin ta 'yan can yake ta Dade da sanin kaai tsaye yake.

Ruwan juice Hannah ta zubarwa Naj ajiki ta hanyar ture cup din cikin tsananin bacin Rai da baqin ciki dukkaninsu suka kalleta Naj na miqewa sbd sanyin juice din na shigarta ta dago ya kalli Hannah data miqe itama tace"

Sorry ba da ganganbane hannuna ne yayi santsi cup din ya subuce, sorry.

Hanifa dake goge jikin Naj din tace"

Hannah tana fama da sanyi Zaki qara Mata wani juice din nada sanyi sosai fa ki ringa kulawa ko gaba please,
Naj kije ki cire kayan Kar sanyin ya shigeki.

Hajjo ma kallon Hannah tayi barin barin Naj gurin cikin yanayi na manyanci tace"

Hannatu wannan baida kyau kwata kwata kiyi gaggawan aje shashanci ki saka kula.

Barin gurin hajjo tayi Hannah tabi bayanta da wani irin mugun kallon tsana zuciyarta Kamar zata cinnu da wuta sbd baqin ciki da takaicinsu duk su dukan, Ahankali ta furta"

Munafukan Allah ta'ala.
Juyawa tayi ta bar sashen gabaki daya idanuwanta ko gani basayi Sosai sbd baqin ciki.

Naj na shiga dakinta Kai tsaye tube kayan jikinta tayi duka ta jefasu cikin kwandon kayan wanki ta daura towel ta nufa toilet ta bude Kai tsaye ta wanke jikinta tasake Dan watsa ruwan zafi tafito ta saka kayan bacci masu kauri riga da wando ta fito ta nufi kicin Dan Shan Ginger tea dinta da aka dafa Mata.

Tana fitowa palon taji qamshin Tom Ford turarensa taso dakatawa Amma sbd Bataga alamar kowaba a palon saita wucewarta kicin ta zubo tea din a cup me Dan girmata fito ta nufa dakin hajjo Dan batai Mata Saida safe a Kai tsaye tashiga dakin da cup dinta a hannu saidata rufe dakin ta juyo tagansu zaune a kujera daya shida hajjo Yana riqeda hannunta sai Hanifa dake Kan gadon hajjon kwance tana facing dinsu da alama duk su dukan magana suke.

Juyarda fuskarta tayi daga kallon dayake Mata zuwa gefen Hanifa a tausashe tace"

Zanje na kwanta saida safenku.
Juyawa tayi ta fice batama tsaya sauraron abinda hajjo ke fadaba na tambayarta jikin nata.

Dakinta ta koma ta zauna ahankali tafara shan ginger tea din Yana tiririn zafi harta shanye duka
Take zafi yataso Mata tako Ina taji Kamar tana cikin Rana ta miqe tsaye tana cire kayan baccinta masu shegen kauri ta sanya rigar bacci me Dan tsayi Mara nauyi ta qara qarfin AC sai alokacin taji tanajin daidai Kuma taji jikinta yasake sakewa sosai ta nufi gadonta ta Haye ta shige bargo tana kashe wuta Dan yau Kam baccin wuri zatai Dole tunda abokanan firarta nada abokin fira.
Bata Jima da kwanciya ba bacci ya dauketa.

Qarfe goma Sha daya saura yashigo dakin ya qaraso bakin gadonta ya tsaya kanta Yana qare Mata kallo cikin wani yanayi dashi kadai yasan sirrin abinsa.
Fuskarta zuwa bakinta dayake yanka wuyanta ya tsayar da idanuwansa kafin ya cire hannuwansa daga aljihun wandonsa ya zauna bakin gadon Yana gyara Mata rufarta data Dan bude rigar baccin red color na Dan daukan hankalinsa sbd kalar hot red ce ba transparent bace Amma ta lafe ajikinta ta kwanta,ya 'dan rufe ido ahankali Yana budewa ya shafa fuskarta da har lokacin Bata koma daidaiba da kuka da zazzabin datai.
Qarfe bakwai jirginsa zai tashi gobe shiyasa kawai yashigo gurinta saidai samunta da yayi tayi bacci yasa yafasa tafiya ya Haye gadon ya kwanta gefenta tareda shigar da ita jikinsa Yana sake gyara musu rufa.

Asubar fari alarm din gefen gadonta ya tada ita ta bude idanuwanta ahankali tana kokarin Kai hannu ta kashe taji mutum tareda ita
Gabanta ya buga da qarfi cikin sauri takai hannu gefen gadon ta kunna wutar dakin Mara haske daidai Yana bude idanuwansa ahankali ya kalleta da yanayin daya sake kayar Mata gaba da ganinsa ta yunqura da qarfi zata tashi ya girgiza Mata Kai ahankali Yana maidata jikinsa cikin kasala yace"

Banason farkawa da hayaniya Yana sani ciwon kai,ki riqe hakan.

A hasalce da bacin Rai da mamaki tana qin daga murya danma Kar tsautsayi yasa aji tace"

Meya kawoka Nan?
Menene hakan?
Banason wuce wuri fa,Abinka yayi yawa....

Bude idanuwansa yayi da kyau akanta har lokacin tana cikin jikinsa ya shafo bayanta da hannunsa dake cikin rigarta yace"

Ke bakinki baya mutuwa ne?
Just shut up okΒΏNafada Miki banason farkawa da hayaniya.

Turesa tahau Yi tako Ina sai hannuwanta daketa turesan suna Masa wani irin waiwayi dayasashi dagowa ya kalleta da mayun idanuwansa cikin kunnenta ya furta"

Kinsan me kikeyi kuwa?

Da sauri tasake turasa batareda ta kalli fuskarsa ba sbd Jin muryarsa data sauya.
##MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡

09134848107

*_DM 30_*
Riqe hannunta yayi ahankali yana sake kallonta da yanayinda yasake fadar Mata da gaba yace"

Ya Isa haka,kece Kika jawo wannan yanzu..

Shinshinan wuyanta yashiga Yi Yana sake shafa bayanta zuwa wuyanta da hannunsa dake cikin rigarta har lokacin,tsikar jikinta dasuka tashi gabaki daya sbd wani irin fitannan kiss daya sauke Mata a wuyanta da Babu komai,
Tasake daga hannuwan zata turasa can qasan maqoshinsa ya furta"
Kinayi Zaki Zaki ja na rasa jirgina Kuma wlh na rasa jirgina saimun bar gidan Nan ayau.

Bata tsaya sauraronsaba sbd idonta dasuka Gama rufewa taringa turasa Wanda hakan yake qarasa sauya yanayinsa ya juyar da ita gabaki daya Yana Mata rumfa tareda dago fuskarta yana hade bakinsa da nata hannuwansa Kuma na zare rigar baccinta ya jefar da ita Yana hada jikinsa da nata da Babu riga shima dama Bai Kwana da riga jikinsa dagashi sai dogon wandon baccinsa rigar sanyice yazo da ita Kuma yacire.
Saida kukanta ya daina fita gabaki daya kafin ya taqaita aikinsa daya mugun shagala ayi musammam yau daya samu hanyar da kyau
ya dauketa da kansa ya nufi toilet da ita,
Yana sauketa ahankali duk da batada qarfi da kuzari Haka tabi bango ta fito ko gani batayi sosai duk wani rauninta ya fama matashi zallar azaba takeji tana fitowa toilet din ta zube qasa da Jan jiki ta qarasa gadon ta kwanta bakin gadon hawaye na tsiyayo idanuwanta dasuke a matuqar kumbure.

Kamar zai biyota yasan Rigima kawai zatai Kuma batada qarfin yin rigimar Dan Haka ya barta kawai yayo wankansa duk biyu da yafito daureda qaramin towel dinta dayayi Masa kadan yahau goge jikinsa Yana duba agogon sallar asuba da aka tada tuni ya kalleta Yana qarasawa inda take bai tsaya komaiba yakuma daukanta duka ya nufi toilet da ita ya aje ahankali,
Zata qwace jikinta ya saketa a hankali Yana cewa"

Relax fita zanyi.

Juyawa yayi ya fice ya saka kayansa ya fice da sauri zuwa masallaci.

A palon kuwa Yana fitowa daga dakin ruqayyat na fitowa daga kicin data shigo ta kofar baya ta kicin din Dan fara aikace aikacensu dasuke farawa tun qarfe shida da rabi Amma yanayin ciki da Hanifa take dashi yanzu tun asuba take shigowa Dan hanifar tun asuba tana tashi saitaci abinci tayi sallah Takoma bacci kafin Kuma ayi breakfast da ita.

Tana ganinsa tayi saurin sauke Kai cikin tsananin girmamawa tana dakatawa daga inda take harsaida ya fice tukuna.

Ahankali ta gyara kanta tayi wanka da ruwan zafi sosai tasake shiga cikinsu sosai kafin tayi wankan Dole jikinta yayi Mata daidai tsamin jikin ya Dan tafi ta fito ahankali ta saka kayan data fara sawa jiyan ta cire riga da wando masu kauri tayi sallah ta koma gado ta kwanta sbd zazzafan zazzabin datake Jin Yana saukar Mata.

Qarfe shida da rabi ya fito shirye tsaf cikin Roberto cavalli jeans da white Armani rugbay shirt sai qatuwar tsaddadiyar rigar sanyi jacket daya Dora me tsayi sai qamshinsa ke tashi tuni aka fitarda motarda zata kaisa airport ya kalli hajjo cikin kulawa yayi Kama hannunta Kamar yanda yasaba cikin kulawa yace"

Allah ya sadamu da alkhairi,saina dawo

1 Comments On DEEN MARSHAL
avatar
hindatu-5

3 months ago

Reply

The novel is nice

Please Login or Register in order to submit comment