Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dan Haka qarfe tara da rabi yafito a shirye cikin _Roberto cavalli_ straight trouser and shirt brown fuskarsa sanye da _Prada_ sunglasses black hannunsa sanye cikin aljihun wandonsa Hanifa dake tsaye tareda Isma'eel sai Hannah dake zuba qamshi Dan tuni tayi wanka suna jiran fitowarsa ta kallesa cikin kulawa da kewarsa da zatayi tace"

Marshal kamun alqawarin zuwa kodan baby right?

Kallonta yayi ya sakar Mata murmushinsa dakewa Hannah wuyar gani Yana gyada Mata Kai ahankali kafin ya Dan waiwayo ya kalli Hannah datake Masa kallon tsananin so da burgewa harma da sha'awa ya kalli kofar dakinta ahankali yace"

Tana ciki?

Bata gama fahimtar me yafadaba ya nufi dakin yayi knocking Kai tsaye duk suna tsaye suna kallonsa.

Ahankali ta tashi daga zaunen datake kan kujera idanuwanta da fuskarta gabaki daya a kumbure ta nufi kofar ta bude sbd tunanin ko hannace tadawo Dan Bata fita da card din dakinba.

Cikin idanuwansa nata idanuwan suka sauka ta dauke Kai take fuskarta na sauya zuwa wani mummunan yanayi ta juya zatabar gurin ya riqo hannunta Kai tsaye tareda Ciro abindake aljihunsa ya saka Mata a tafin hannu ta kalla da sauri ganin bra Dinta ta dago a fusace wata fitinanniyar kunyar Hanifa dake kallonsu tana dabaibayeta ta qwace hannunta tareda juyawa ciki a fusace.

Juyawa yayi baice komaiba shima yabar gurin ya nufi gurin Isma'eel dake jiransa a mota Hanifa da mamaki da wani boyayyan murmushi yagama kamata tabi bayansa tana waiwayan dakin
Hannah kuwa kusan mutuwar tsaye tayi ganin fitowar bra din mace daga aljihun Marshal dinta daqyar ta iya daga qafa tabi bayansu suka nufi airport kaisa.

Bayan dawowarsu Babu Wanda yaga wani sakin fuska daga Naj din sbd sosai ta fuske Dan Bata buqatar wani magana dazai danganci JALAL din Dan Haka Bata Bari Koda Wasa Hanifa Tai Mata wata maganar ba ahaka suka lallaba suka qarasa kwanakinsu bayan anyi gwaji an tabbatarda cikin ya tabbata.

Da farin cikin nasarar da aka samu suka dawo gida inda aketa murnar cikin Hanifan musamman umma da duk maraice da abinda zata aikowa Hanifa hakama Dadah,
Ta bangaren Dad Alfa ma Yana tsananin farin ciki da cikin uwa uba hajjo data qwallafawa 'yayan da Marsha Rai shida yake namiji sai gashi na Hanifan zasu fara samuwa ta dauki buri da qauna tasakawa cikin itama duk da hannuwansu a gabansu suke da cikin sbd yanayin lafiyar Hanifan suna fatar dai Allah yasa adace wannan karon.
##MAMUH#_*DM 22*_

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK๐Ÿ‘‡๐Ÿพ_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK๐Ÿ‘‡๐Ÿพ_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK๐Ÿ‘‡๐Ÿพ_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK๐Ÿ‘‡๐Ÿพ_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

*****************
Ba sosai take jimawaba yanzu a office sbd yanayin Hanifa da hankalinta yafi kwanciya idan taga batayin nesa sosai da ita Dan kwanakin tana Dan samun laulayi masu wahala dan yanzu cikin Yana wata na hudu harya fara Dan tasawa Ana hangensa.

Yau Bata samu damar zuwa office ba sbd yanayi na ciwon Mara data tashi dashi na period dayazo Mata dama Kuma tana ciwon Mara sosai idan zatayi period duk wata saidai wannan karon ciwon yafi tsananta Mata Wanda takejin Kamar ba yanda tasaba bane Dan Haka da yamma hajjo da kanta takira Dr sa'id yazo ya dubata sbd ganin duk Naj din tayi wani iri Babu qarfi sosai ajikinta.

Herbal tea hajjo tasa ruqayyat ta dafo Mata da Zuma kadan aka kawo Mata ta gyara zamanta daga takuren datake dunqule Kan kujerar kusada hajjon ta karba tana kallon cup din ahankali kafin takai bakinta tafara kurba tana Dan rufe ido sbd 'dandanon da baya Mata ko kadan a Baki ta kalla Hanifa dake Mata sannu tace"

Bani tissue akusa dake.

Hannu Hanifa takai ta zaro Mata tissues din dake gefenta na 'dan Taraย  yawu datakeyi sbd cikinta ta miqawa Naj din cikin kulawa tana cewa"

Sorry sweetie.

Gyada Mata Kai Naj din tayi tana dan lumshe idanu sbd saukar herbal tea din da zafinsa cikin cikinta yasa taji tana Dan Jin Kamar ciwon na Dan fadawa ta goge bakinta da tissue tana cigaba da kurban tea din harta shanye ta ajiye cup din hajjo na Mata sannu cikin kulawa.

Ahankali ahankali ta danji ciwon Yana fadawa Yana ragewa hartaji taji Dan saukinsa ba laifi sai alokacin ta miqe ahankali ta nufi dakinta Wanda take ita kadai yanzu aciki bayan an sauya Mata komai na dakin zuwa sabin furnitures dasukafi wainda aka sauya komai na dakin fari kamar yanda Hanifa ta bada zabin kalar sbd jalal ma yawanci komai na part dinsa farine,
Raba daki sukai da Hanifa sbd yanayin laulayin cikin hahifan dayakeda tsanani da zabe zabe Dan kuwa gabaki daya batason qamshin turare Wanda Naj Kuma ko zama tayi kusa dakai saita bar maka qamshinta me sanyi da dadi Wanda kamarma yariga yakama jikinta,
Hakama hahifa yawu takeyi wnda itakuma Naj takurane gareta,
Sai qamshin toilet din dakin nasu shower gels dasu feminine wash da bataso Wanda Suma Naj ke amfani dasu shiyasa Hanifan ta tarkata takoma dayan dakin dake palon aka sauya Mata wasu abubuwan dakin wainda bataso da sabbi.

Wanka tasamu tayi da ruwa masu zafi sosai tasake Jin Dan Jin qarfin jikin ta shirya cikin riga da wando masu Fadi sosai marasa nauyi ta saka hula ta Dan kwanta Dan samun bacci Bata Farkaba Saida Dr sa'id yazo aka tadota tafito sanyeda mayafi me Dan kauri rufe da jikinta ta qaraso palon tana tafiya cikin nutsuwa ahankali ta nufi kujera tana kokarin zama anty Amina na shigowa Nan suka zauna tare itama tana gaisawa da Dr sa'id din cikin sanayya da mutuntawa kafin ta miqe ta nufi dakin hajjo dake mutuniyar hirarta Dan suna qasan Kaka sosai da hajjon.

Kallonta Dr sa'id yayi kadan tareda Dan taqaitawa daga kallon Kai tsaye yace"

Menene matsalar?
Yaya kike jin ciwon Marar?

Numfashi ta Dan sauke tana dubansa a natse tace"

Wannan ne Karo na farko danake Jin wannan kalar ciwon duk da dai Ina ciwon Mara dama Amma wannan inajinsa dabam.

Kallonta yasakeyi Yana jeho Mata tambayoyi dabam dabam tana basa amsa tsawon lokaci Yana saurarenta ya hada amsoshinta Yana nazarinsu kafin ya dago Yana kallonta dason fada Mata abinda yake tunanin yasaka ciwon fin koyaushe wannan karon yace"

Ciwon mararki ya sauya yanayin tsarin ciwonsane ta hanyar tsananta da wani launin ciwom kamakon sha'awarki ta mace da aka motsa Wanda ke nuni da Baki taba ji ko aikata wani Abu daya taba motsa sha'awarki Wanda dakin Jima ahakan batareda an motsa Miki itaba kokuma yanayi yasa ta motsa da kanta Kika dauki shekaru ahaka kofofin sha'awan naki zasu rage qarfi matuqa kokuma suyi rauni sosai ta yanda zuwan sha'awan zaiyi Miki wuya.

Wani irin nauyi kanta ya dauka akaro na farko a rayuwarta da wata irin mummunan kunyar da Bata tabajiba ta Gama rufeta tako Ina har bazata iya kallonsaba saidai ta dago ahankali ta waiwayo duba Babu Wanda yafito bare yaji wannan mugun al'amarin daya sameta sukai ido biyu da Anty Amina data fito daga dakin hajjo takumaji abinda Dr sa'id din yafada Amma sbd ragewa Naj din nauyi da kunyar data hango tareda ita saita dauke Kai tana fuskewa tace"

Zan wuce nabarowa umma aikin hada sakon turarukan daza'a Kai mota gobe zuwa wani gari,Dr sa'id sai anjima.

Wucewa tayi batareda ta jira amsar Naj din ba sbd tasan bazata samu amsawar daga garetaba sbd halin datake ciki na tsananin Jin nauyi.

Babu wata kunya ko nauyin maganar dayaji sbd shi likita ne Babu kunya a tsakaninsa da patient dinsa Dan Haka Kai tsaye yabata shawaran ringa Shan ruwan dumi akai akai tareda bada shawaran zama guri daya da mijinta.

Tagane ma'anarsa ta cewa ta zauna guri daya da mijinta Dan Haka ko kallonsa bataiba tace"

Ngd Dr sa'id" tana miqewa daga zaunen shima ya miqe sukai sai anjima ya fice ita Kuma ta nufi daki tana dafa mararta datai nauyi.

Kwana biyu tagama period dinta ciwon Mara ya wuce Dan Haka ko maganar Dr sa'id Bata sake tunawaba bare sakawa arai taci gaba da sha'anoninta hankalinta kwance Babu tunani ko damuwar komai.

Yau da yamma sosai tadawo aiki sbd wani meeting da sukai me mahimmanci Wanda yasa take cikin farin ciki sosai sbd project ne dasuka Jima Suna buqatansa sai yanzu Allah yasa suka karbe.
Tana sanyo kan motarta cikin layin ta hangi qarin sojoji a kofar gidan Wanda yasa gabanta mummunan faduwa akaro na farko data tuna zai iya yiyuwa shine yadawo.
Sake faduwa gabanta yayi taji kaman tana neman shiga damuwa Amma dai ta danne ta qaraso suka bude Mata gate tashige da motarta tana amsa gaisuwar dasuke Mata daga ciki ta hanyar jinjina musu Kai da daga hannu.

Parking tayi tareda kashewa ta fito riqe da handbag dinta tasamu kanta da qin ko kallon daya daga cikin motocinsa dakeda alamar da ita akaje daukarsa airport ta dauke Kai ta nufi cikin gidan Kai tsaye tana nufar sashensu ma'ana na hajjo.

Da siririyar sallama ta shiga palon Kai tsaye tana kallon Hanifa dake zaune palon da tissue dinta ta yawu,
Gurinta ta qaraso tana sauke qaramin numfashi tace"

Maman baby Yaya??

Murmushin farin ciki Hanifa ta saki tana cewa"

Sannu da dawowa sirikar maman baby.

Naj din Bata tankata ba sbd yanzu tasaba da wannan neman fitinar da Hanifa keyi yanzu Dan Haka Kai tsaye daki ta nufa tana cewa"

Bari na tube nayi sallah yau na gaji sosai jikina na ciwo sosai.

Shigewa tayi daki tareda rufo kofar ta tana aje handbag dinta tareda Dan mayafin dake kanta ta tube tareda Kai kayan cikin laundry ta janyo towel ta daura tashige toilet.
Jin Ana Kiran sallar magriba yasa tafasa wankan tayo alwala tafito ta Sanya doguwar riga ta tafara yin sallolin Dake kanta saidata gamasu kafin ta miqe tana tubewa wayarta tahau ringing batabi ta kanta ba ta nufi toilet tashige.

Wanka tayo tafito ta shafa Mai kadan sai body mist da khumrah ta Sanya doguwar riga me qaramin hannu ta Sanya hular da Bata Gama rufe kanta gashin kanta dukaba tana kokarin fitowa taga lokacin sallar Isha yayi ta tsaya tayi abarta kafin ta dauko wayarta ta fito tana duba Kiran da aketa Mata tun dazu ga zallar mamakinta sai taga no din kamar ta santa ta sake dubawa taga 9misscalls Dan Haka sai mamakin Kiran ya Dan kamata ta nufi palon da hajjo da Hanifa ke zaune a dining ta nufa gurinsu Kai tsaye tana cewa"

Me maman baby keyi a dining hajjo itada baby bayason cin abinci a dining San......kasa qarasa maganarta tayi sakamakon Wanda idanuwanta suka Shiga cikin nasa Yana zaune kan kujerar da Bata hangosaba saidata iso gurin gabaki daya fararen idanuwansa masu rikitarwa a zubasu akanta jikinsa sanyeda jallabiya fara qal tana qyallin daya tabbatarda tsadarta,
Samun kanta tayi da kallon hajjo ahankali kafin ta maida kallonta kan Hanifa dake kallonta da murmushi a fuskarta sai kawai ta juya zatabar gurin Kai tsaye taji muryarsa a kame yace"

Dawo ki zauna.

Wani mamakin gaskene ya kamata dan ganin isar dayakeson nuna Wanda ita Bata basa wannan damar ba Dan Haka Bata dakataba ta wucewarta saidai ko taku uku bataiba taji an dauketa sama an qarasa cikin dakinta da ita tareda rufo kofar ya direta tareda manneta jikin bango Yana kallon fuskarta Yana Kuma controlling zuciyarsa dama kansa ya lumshe idanuwa ahankali yasake budesu akanta ya bude Baki cikin nutsuwa da kamewarsa yace"

Next time Kika Kuma Haka Zakiyi mamakin abinda Zan Miki agaban hajjo dama qawar Taki da kike Jin girma agabanta.

Qin kallonsa tayi tasa hakai hannu zata turesa daga jikinta dayake manne taji bazata iya Kai hannunta ajikinsa Dan kada wani tunanin ya shigesa ta dago ahankali ta kallesa da fararen idanuwanta shima idon nasa na kanta ya daga gira daya Yana jiran abin dazata fada ta Dan hade fuska tana dauke idonta daga cikin nasa murya a kame tace"

Bana buqatan sharadi ko doka akan waye Zan kula waye Zan gaida so can you just excuse me please.

Wani kallon daya tayar da tsikar jikinta batareda tasaniba yayi Mata kafin ya juya ya fice yabarta da qamshin turarensa daya maqale a kayanta takasa bin bayansa da kallo zuciyarta a Dan bace.

Kasa fitowa tayi lokacin saidata tabbatarda yabar sashen ta fito fuskarta a kame Dan kada Hanifa tasamu damar yimata wata magana
Tana fitowa cikinsu Babu Wanda yabi takanta taje dining din taciyo abinci kadan tagama ta taso tadawo gefen hajjo ta zauna tana Dan fuskewa dayin kallon wata Mexican drama the forbidden love A tashar telemundo suna fira.
Dai qarfe goma da arbain ta shige lokacin tuni hajjo ta shige daga ita sai Hanifa kusan tare suka shige dakunansu.
##MAMUH#

*DAN ALLAH ZAKU RINGAMUN UZURI KWANA BIYUN NAN ZUWA RANAR SATURDAY HIDAMAR BIKIN QANWATA MUKEYI ZANYI KOKARI NA RINGA BAKU INSHALLAH IDAN KUMA HIDIMA TA RIQENI ZAN RINGA SKIPPING HAR MUGAMA BIKIN RANAR SATURDAY INSHALLAH*
_NAGODE๐Ÿ™_




*_ZAFAFA BIYAR 2022๐Ÿ”ฅ_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_1aHALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
Dโ€™aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

09134848107*_DM 23_*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK๐Ÿ‘‡๐Ÿพ_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK๐Ÿ‘‡๐Ÿพ_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK๐Ÿ‘‡๐Ÿพ_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK๐Ÿ‘‡๐Ÿพ_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw


**************
Kwanciya tayi bayan tagama duk abubuwan dazatayi ta rufe idanuwanta Nayan ta rufe Rabin jikinta da bargo me taushi takai hannu ta rage hasken wutar dakin sosai.
Tsowon mintuna hudu ta juya kwanciyarta tana sake rintse ido saidai har lokacin qamshinsa dake maqale a kayan jikinta Bai daina Shiga hancintaba Yana damunta gabaki daya ta rasa sukuninta ta tashi zaune tana sake Dan qaramin tsaki tareda dan yamutsa fuska tana sauka daga kan gadon ta nufi closet tana zame rigar jikinta ta jefa cikin wardrobe ta Ciro wasu riga da wando na bacci guntaye masu santsi ta saka tareda komawa ta kwanta tana lumshe ido bayan tayi adduar bacci.


Karar vibrating wayane ya tada ita da safen bayan tayi sallar asuba Takoma bacci,
Hannu takai ahankali tafara lalubo wayar tana bude idonuwanta dake tareda sauran bacci ta dago wayar ta duba taga no din jiyane da akaita kiranta da ita ta tashi zaune tana Dan sake sakewa daga baccin ta dauka Kiran cikin muryarta me taushi tace"

Hello,aslm alkm!

Shiru taji ba'ai magana ba cikin nutsuwa tasake cewa"

Hello.
Jin shiru ba magana yasata kashe wayar tareda ajiyewa tana kallon agogo taga qarfe Tara da minti uku.

Saukowa tayi Kan gadon tareda zura bedroom slippers dinta na dolce and Gabbana ta nufi toilet da sauri tafada wanka sbd tayi kafin ta Isa office tasan zatai latti.

Tana fitowa wanka tafara shiri cikin nutsuwa tashafa Mai da body mist kawai sai khumrah ta shirya cikin Givenchy floral chiffon skirt navy blue da milk blouse dinsa sai veil datai rolling ta fito daukeda wayarta da _D&G_ handbag dinta tafito Palo cikin sa'a duk suna dining suna breakfast daga hajjo sai Hanifa bandashi Dan Haka ta jiye handbag din a kujera tana qarasawa dining din cikin nutsuwa da sakewa tace"

Barka da safiya hajjo,
Ina kwana?

Taja kujera ta zauna tana kallon Hanifa dake kallonta cikin yabawa da samunta da 'dan uwanta yayi amatsayin Mata tace"

Good morning maman baby, how's our baby?

Murmushi Hanifa tasaki tana cewa"

Morning Auntie din baby.

Sama sama taci slice biyu na toasted bread da tea Mara shugar ta miqe tana cewa"

Hajjo zantafi saina dawo.

Adawo lafiya Amma yau ki dawo da wuri sbd kece Zaki ringa Mana dinner daga yau.

Murmushi tasake tana wucewa tace daga yau kuwa Zaki ringa cin dinner me Dadi hajjo,
Maman baby saina dawo,take care.

Fitowa tayi Kai tsaye ta nufi hanyar sashen Dad Alfa tana duba wayarta ta qarasa shiga da Hannah tafaracin Karo ta fito daga kicin fuskarta shafe koina da face scrub data shafa tana jiran yayi mintunan dazaiyi kafin tashiga wanka ta wanke Dan Marshal na gari Bata Sanya da qarin gyare gyare.

Kallon juna sukayi Naj tana ganinta ta Dan basarda fuska tana wucewa palon Dad Alfa din bayan ta amsa "morning" dinda Hannan Tai Mata cikin qure ido akanta sbd har yau tana shinshinowa kanta barazana daga Naj shiyasa take buqatan ayi gaggawan aurenta da Marshal Dan kuwa kyawu da kyan jiki tareda daukan idon Naj na daban ne duk da Bata wani qyale qyalen kwalliya Dan zata iya cewa Naj Bata taba shafa su jambakiba musamman masu shwty kala shiyasa komai nata yake unique and natural.

Tsoki hannan taja tana dauke Kai daga bin inda Naj ta shige da kallo ta nufa dakinta tana Jin tsanar Naj har Dan kuwa tashiga gabanta Kuma ta hanyar wainda Babu abinda zata iyayi bayan ta danne duk abin datakeji tabisu da yaqen dole tunda sune dolen Marshal dinta Dan tasan suna tsanarta to har abada bazai auretaba sbd yanda yakejinsu a ransa.

Fitowa Naj tayi bayan sungama magana da Dad din Dan ba gaisuwa kawai ta kawotaba harda magana akan ALFA'S company Wanda suke buqatan meeting dasu na saka hannunsa Dana Marshal akan wasu takardu na wani babban project da zasu fitar.

Fitowa tayi bayan sunyi magana Akan zasuzo ALFA'S din gobe gurin meeting din.

Tana fitowa daga sashen wayarta tasake daukan vibrating ta bude handbag dinta tareda Ciro wayar tana nufar motarta ta dauka tareda cewa"

Hello Aslm alkm!

Shiru takuma ji ta daga wayar daga kunnenta ta duba taga tana aiki ta Mayar kunnenta tana sake cewa"

Hello.

Mrs DEEN MARSHAL zankiraki dashi kokuwa Antyn JALALUDDEEN MARSHAL?
To koma dai wanne duk dayane basuda wani amfani tunda bashine dalilin dayasa nakiraba,
Akwai meeting qarfe goma da rabi gashi Banga alamar kintuna da hakan ba Dan bama iya jira idan lokaci yayi sbd munada iyalan da mukai auren soyayya bana cushe ko sadakaba dasuke jiran dawowarmu gidan Kan lokaci.

Cire wayar tayi daga kunnenta tareda kashewa Kai tsaye batareda tasamu damar cewa maganarsa ko kalma dayaba ta maida wayar jaka tana Shirin Shiga mota ta hangosa tsaye a balcony dinsa da mug a hannunsa Yana kurba ruwa masu dumi kadan da Zuma kadan aciki Wanda yake dabiarsa kullum Shan ruwan zafi masu Zuma kadan aciki.
Sanye yake da three quarter black da armless shirt sai slippers brown a qafarsa yafitone sbd fresh air ya shigesa Dan exercise din dayayi gabaki dayansa yasashi zufa shiyasa ya fito Yana Shan fresh air din jikinsa sai daukan ido yakeyi acikin baqaqen kayan dake jikinsa.

Dauke Kai tayi tana ciro keys na motarta ta bude ta shige tareda tada motar tana Danna horn aka bude Mata gate ta figeta ta fice daga gidan
Cigaba da abinda yakeyi yayi batareda yabi inda motar tata taficeba da ido sbd tun fitowarta daga sashen Dad Alfa idonsa ya sauka akanta ya qarewa kayan jikinta idon Yana tsayar da idonsa Kan Dan qaramin qugunta da skirt din jikinta ya zauna akai daga sama ya Dan rintse idonsa Yana daukesu daga kanta.
Ciki yakoma kawai sbd Jin iskar ta sauya zuwa wani yanayi mara Dadi.

Tana Isa office tayi parking ta fito ta nufi ciki Sarah na qasa tana jiran isowarta Dan Haka kai tsaye tan isowa gurin meeting din suka wuce San sama hanyar office din chairman wato Abbas.
Ko data Shiga shareholders din companyn duk sun iso ita zatai representing Alfas,Marshal da Dad Alfa.

Sai qarfe biyu da arbain suka fito meeting din Dan Haka Kai tsaye ta wuce office dinta Dan duba wasu takardu tanayi tana duba agogo sbd komawa gida da wuri tunda tasan aikin dake jiranta a gidan.

Sai qarfe uku da hamsin da uku tasamu kanta ta fito tana sanarda Sarah Dake biye da ita takardun dazata kaiwa Abbas ya duba kafin goben a zauna next meeting.

Wayartace tahau vibrating ta Ciro tana dubawa cikin Dan yamutsa fuska ta kashe wayar tareda maidawa cikin jaka tana kallon Sarah tace"

Ki tabbatarda kin kaiwa chairman duka takardun da ake buqatan ya duba kafin goben sbd bana buqatan wani aiki dazaisa yaringa kirana.

Ok Inshallah.

Fitowa tayi tafada motarta tabar companyn gabaki daya tana sake duba agogon hannunta.

Tana Isa bataga motorsaba a harabar gidan hakama sojojinsa Dan Haka tasawa ranta sun koma kenan ta fito ta Kai tsaye ta nufi sashensu.

Bakowa a Palo hajjo na sallar la'asar a dakinta, Hanifa Kuma na daki tana baccin yamma.

Dakinta ta nufa Kai tsaye saidata Dan zauna ta huta kafin ta tashi tasauya cikin doguwar rigar roba Mara nauyi tayo alwala tayi sallah kafin ta fito ta nufi dakin hajjo.

Sai yamma sosai ta fito ta Isa dakin Hanifa har lokacin bacci takeyi ta Dan tayarda ita cikin kulawa sbd maraice yayi ta kamata ta tashi ta nufi toilet kafin it's ta nufi kicin Dan aikin abincin dare da itace yau zatayi.

Aiki suka hau yi itadasu ruqayyat masu kama Mata wasu ayyukan
Suka Dora tuwon semo da miyar waterleaf da nama kadan aciki sbd Jin daga bakinsu ruqayyat cewan idan Marshal na gari ba'a saka nama de yawa a abinci bayason nama sosai duk da dai bawai dansun fada tayiba itama Naman Bai wani dameta bane sosai hakama Hajjo itakuma sbd tsufa da manyanci.

Fruit salad tayi sbd Hanifa me juna biyu sai normal peach drink da black lemon tea me zuma data dafa Dan gidan gabaki daya kusan kowa mayen tea da zumane duk hajjo ce ta koyar dasu hakan tun suna qananu.

Basu Gama aikinba ta fito kicin sai bayan sallar magriba Dan Haka tana fitowa Kai tsaye ta nufi dakinta tafara tubewa gabaki daya ta nufi toilet yin wanka.
Ta Jima ciki kafin tafito daureda towel me girma blue tazo tafara saka doguwar riga tayi sallar magriba Da Isha kafin ta zare rigar ta zauna gaban madubi tashafa Mai kadan da spray din _Chanel_ ta sako doguwar riga Mara hannu ta fito daukeda wayarta lokacin hajjo da Hanifa tuni suka Isa dining Dan Haka Kai tsaye itama can ta nufa tana ajiye wayarta Kan kujerar palon.

Bata ganshiba Amma hancinta ya shaqo Mata qamshi _Tom Ford_ turarensa Dan Haka ta rage takun tahowar tata tana Dan Kai idanuwanta kujerar dayake zama a dining din wadda ba'a hangota sai ankawo cikin dining area din tana Kai idonta gurin tagansa zaune da tea gabansa Yana tiriri cikin Dan qaramin cup,Bai dagoba bare ya nuna yasan da zuwanta saidai ta tabbatarda yaji zuwan mutum agurin ta 'dan dakata kadan zata koma saikuma ta fasa ta qaraso ahankali tana Dan fuskewa batareda itama ta kalla inda yakenba tace"

Sorry nabarku jirana.

Bata zaunaba ta zubawa hajjo abincin kafin tazubawa Hanifa fruit salad da tuwon Dan kadan sai ta zuba itama Dan kadan Takoma ta zauna sai alokacin ya kalleta baice komaiba ya qarasa Shan tea dinsa ya miqe ahankali hajjo ta kallesa tace"

Abincin fa?
Najma kiyi serving mijinki abinci yagama Shan tea din.

Wani irin kallo yayi Mata dayasata kusan sarqewa duk da Bata dagoba Amma tanajin kallon ajikinta ga rigar jikinta duk tasata Jin haushi da takaicin fitowa ahaka.

Da muryarsa me kamewa yace"

Takaimun abincin acan ba anan zanciba.

Yana Gama fadar Haka ya wuce yabar gurin batareda yasake kallon inda takeba yabarta da wani irin takaici,baqin ciki da takaicin rashin gane meyake nufi da "Takaimun"
Wa yake nufi da kalmar Dan Bata tunanin da ita yake Dan kuwa bataga ranarda hakan zata faruba takai kanta sashensa to tace tazo ubanme.

Ganin idon hajjo akanta dake nuni da zallar rashin Wasa na tayi abinda yace din yasata sarqewa tana sakin tari ahankali
Hanifa ta dauki ruwa ta miqa Mata ta a cewa"

Sorry sweetie,sannu bi ahankali kije kidawo tukuna saiki qarasa.

Da manyan idanuwanta ta dago ta kalli Hanifa wannan karon Kamar sun sauya da yin Dan ja da Kamar hawayen takaici dasuka Dan ciko aciki sbd halinda take Jin zuciyarta aciki na takaici saidai Kuma Bata hango ranarda zata iyayiwa hajjo gardamaba.

Hanifa dakanta ta miqe taje ta dauko Kaya ta hada Masa abincin da komai aciki tasaka a basket ta miqawa Naj din tana cewa"

Bari na dauko Miki wayarki da hijab.
##MAMUH#



*_ZAFAFA BIYAR 2022๐Ÿ”ฅ_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
Dโ€™aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

09134848107

*_DM 25_*
Miqewa take kokarin Yi ya ajiye cup din dake hannunsa ya kalleta da mamaki akan fuskarsa datake sata dauke idonta daga kallonsa ya mayarda ita zaune kan qafafun NASA tareda zura hannayensa ya rungumota ta baya Ya zuro kansa ta wuyanta daidai kunnenta ya bude Baki ahankali ya furta"

Me kike yiwa gaggawa na guduwa bayan kin shanyemun yoghurtยฟ
Kinsan me hakan ke nufi kuwa?""" Ya qarasa maganar Yana shafa fuskarta da tasa.

Yi tayi kamar bataji abin daya fadan ba taci gaba da kokarin kwacewa daga jikin nasa yasake shigewa da ita jikinsa Yana kallon wuyanta dayake shaqo qamshi daga gurin ya lumshe fararen idanuwansa ahankali kafin ya saketa ahankali Yana Dan dauke kallonsa daga kanta ta miqe tsaye fuskarta a daure sosai duk da tanajin takaici da kunyar kanta data Sha yoghurt din gashi Yana

1 Comments On DEEN MARSHAL
avatar
hindatu-5

3 months ago

Reply

The novel is nice

Please Login or Register in order to submit comment