Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Inshallah.

Dafa hannunsa tayi tace"

Allah yacigaba da yiwa rayuwarka albarka,
ALLAH ya tsare yakai lfy.

Kofar dakinta ya kalla kafin ya nufa kofar dakin ya tura yashiga yaganta kwance baccin wuya yayi gaba da ita ya qarasa ahankali ya sunkuya ya shafa fuskarta tareda Bata light kiss ya Ciro katinsa na banki daya tareda paper me daya rubuta password ya ajiye Mata gefen pillow ya fice.

Yana fitowa shida Hanifa suka fito zata rakosa mota a bakin motar suka tararda Hannah shirye cikin kayan sanyi itama sbd safiyace Sosai akwai sanyi zata rakasa airport Kamar yanda tasaba duk zuwansa
Suka Shige motar driver yaja suka fito motar mutanensa na waje suka Mara musu baya suka harba titi.

Bayan dawowar Hanifa ciki Kai tsaye dakin Naj ta nufa Dan ita Kam Hannah ke wasu abubuwan itakeji wa Naj din ba Dadi tunda Naj din Bata yiwa kanta fada da karatun ta nutsu ta amsa aurenta tun kafin ayi Mata sagegeduwa tun Bata ganewa komai a aurenba.

Bacci ta taddata tanayi ta qarasa bakin gadon tana tunanin kilama ko sallar asuba Bata tashi tayiba
Tana Kai hannu jikin Naj din taji yadauka wani irin zafi sosai.

Da sauri ta kalleta tana sake taba jikin nata da har wani Dan guntun Nishi takeyi cikin sauri da damuwa tace"

Naj,Naj kina fama da zazzabi me zafine Haka?

Bude idanuwanta tayi ahankali cikin siriryar murya tace"

Nasha magani idan nayi bacci Koda Zan tashi Inshallah ya sauka.

Da kulawa Hanifa tace"

Wane magani Kika Sha?
Bari naje na sanarwa Dr sa'id a waya.

Girgiza Kai tayi ahankali tana cewa"

No please karki fada Masa ki Bari nayi bacci Dana tashi Inshallah shikenan.

Badan tasoba tace"

Shikenan Bari na kwanta anan din mugani zuwa anjima idan kin tashi daga baccin.

Duk da tana cikin zafin zazzabi saidata yunqura ta tashi zaune tana cewa"

Aa kije karki damu Inshallah nafada Miki ba wani ciwo bane.

Kallonta Hanifan take da mamakin ganin tashinta zaune Kai tsaye tace"

Naji Amma dai Zan kwanta anan ko natafi dakina bazan iya bacci ba idan nabarki ahaka.

Riqo hannunta Naj tayi da sauri tana Dan rufe ido ta bude sbd zafin zazzabin ta qaqalo murmushin daya sake sawa Hanifa zargin boyon wani abun Naj keyi tace"

Hanifa dan Allah kije dakinki
Na Miki alqawarin Ina lafiya Inshallah.

Naj is there anything you're not telling me??

Like what Hanifa?" Naj din tafada cikin Dan mamaki.

Hanifa tace"

Like abin dayasa bakyason na kwanta anan din sbd na tabbatarda ba sbd karna damu bane wannan din.

Ajiyar zuciya Naj ta sauke tana rintse ido sbd rashin sanin yanda zata Hana Hanifan kwanciya a gadon Dan duk Wanda yasan Jalal farin sani to Yana hawa gadon saiyasan jalal din ya kwana a gadon Dan kuwa daga bargon har zanin gadon da pillows din qamshin turarensa sukeyi.
Tasan Hanifa na hawa saitace qamshin JALAL takeji,
Me zatace idan ta tambayeta hakan?
Wannan wace irin masifa ce ta sameta ta kame kame,
Wlh dai angama da rayuwarta.
##MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡

09134848107

*_DM 31_*
Ahankali ta sake hannun Hanifar tana komawa ahankali ta kwanta sbd Jin hanifar tafara tunanin akwai dalilin dayasata batason ta zauna din tareda ita,
Har cikin zuciyarta tana Jin zafi da takaici tareda tsananin kunyar Hanifa ta Dan samu alama ta fahimta koma hasahsen wani Abu yafaru a dakin,bama dakin ba kawai a tsakaninta jalal din gabaki daya
Abune mafi kunya da tozarci gareta idan Hanifa tasan wani Abu gameda hakan,bazata taba Bari wani yasan wannan tsausayi da qaddarar data hau kantaba.

Ajiyar zuciya Hanifa ta sake cikin kulawa ta tako ta matso gaban gadon ahankali ta gyara Mata rufarta tana cewa"

Shikenan kiyi baccin zanje Nima na kwanta Dana tashi zandawo na dubaki.

Gyada Kai tayi ahankali tana rufe idanuwanta tareda gyara kwanciyar kanta a pillow.
Sai dataga fitar Hanifan ta saki Dan qaramin numfashi tana sake komawa baccinta dayake idanuwanta har lokacin.


Bacci tayi Sosai Bata fitoba Wanda yasa hajjo nacewa zancen tabbas Naj ba lafiya take ba Dan Haka Babu sanin Naj din tasa Hanifa takira Dr sa'id Wanda baizo gidan ba sai yamma bayan yataso daga asibiti.

Dagashi sai ita ya Mata Yan tambayoyi tabasa amsa a Dan gaggajarce sbd son qin bada hanyar dazata saka koshi ya Dan gane wani abun
Shima Bai wani zurfafaba sbd gane zazzabin tun ranarda Marshal yakirasa acan gidansane Bai Gama sakinta musamman idan sake kusantarta akai Wanda hakan ke nuni da Bata taba saduwa da kowane namijiba hakama Bata budeba ta hanyar tsallake tsallake da yawace yawace Wanda yake ragewa budurcin mace qarfi shiyasa take wannan wahalar Dan Haka Bai zurfafa tambayaba ya Bata maganin dazasu taimaka Mata nasu zazzabi da pain relief ya miqe Yana Dan kallonta yace"

Inshallah zaki warware zuwa gobe ko jibi idanma dai kinji bakyajin daidai har lokacin Zaki iya kirana kokuma ki sameni asibiti saimuyi waeu dube duben mugani Amma dai Inshallah ma Zaki warware din zuwa gobe.

Hajjo takira Masa ta fito tana kallonsa tana qarasowa tana cewa"

Dr sa'id zaka tafi?
Kagama dubatan?
Bansan menene wannan zazzabin sanyin dayaqi sakinta ba tun dawowarta na fahimci batada lafiya Amma tace sanyi ne,
Kuma anyi maganin sanyin kwana biyu yau Kuma abin yadawo.

Dan murmushi yayi Yana cewa"

Nabata magana Inshallah zata warware zuwa gobe
Ba wani ciwon daga hankali bane zazzabine kawai sai gabobi da zasuyi ciwo dama, ALLAH ya Bata lafiya Zan tafi hajjo idan kwana biyu zazzabin Bai tafiba nace ta sameni asibiti.

Ok Inshallah Dr sa'id,
Agaida gidan dasu hajiya.

Zasu shi Inshallah.

Ficewa yayi daidai fitowar Hanifa data fito daga kicin tagama ciyo wainar fulawar dataji kwai wadda umma ta Aiko Mata,ta qaraso palon ta zauna gefen Hanifa tana kwadawa ruqayyat Kiran takawowa Naj Naman Hantar datasa ta dafa Mata dazu tareda ruwa Tash magani.

A gabanta ta ajiye Mata Kan table Takoma takawo Mata ruwa marasa sanyi sosai Dan kaidar Naj dinne Bata Shan ruwan sanyi sosai.

Ahankali takeci sbd ya 'dan yimata Dadi dan yajin da ya 'danyi sbd bakinta da baida apatite na zazzabin,
Taci sosai Saida cikinta yacika Tasha maganin da Dr sa'id yabata tasake dorawa da Ginger tea me zafi
Ahankali taji jikinta ya Dan Yi Mata Dadi tasamu kuzari dakuma zazzabin daya sauka.

Ahankali ta kalli ruqayyat dake dauke kayan data Gama cin abincin tace"

Ruqayyat idan kinkai kije dakina ki dauke zanin gadon Dana cire Yana Nan Kan kujera kikai laundry.

Yes Ma." Ruqayyat din ta furta tana Kai kayan kicin tadawo ta nufa dakin Naj din ta kwaso zanin gadon ta fito.

Miqewa hajjo tayi ta nufa hanyar dakinta sbd kiran sallar magriba da aka fara daidai ruqayyat na kawowa da kayan zata wuce Hanifa tadawo daga dakinta dataje dauko Abu ruqayyat na giftawa gabanta ta kalleta cikin mamaki tace"

Ruqayyat wannan beddings din Marshal ne?me sukeyi a hannunki?
Ta Yaya sukazo hannunki?" Taqarasa fada tana sake shaqar qamshin Dake tashi ajikinsu kamar yanzu ya kwanta akai.

Hajjo ma dakatawa tayi tana kallon ruqayyat Jin abinda Hanifa ta fada Dan dai tasan Babu me shiga sashen nasa a taqaicema namijine me aikinsa dayake Masa gyaran sashensa da wankin kayan zanin gadonsa da komaiba.

Da sauri cikin tsananin tsoro da girmamawa ruqayyat ta kalli Hanifa tace"

Anty wannan da dakin Ma'am ne tace akai laundry ba na Sir Marshal bane.

Rintse ido Naj tayi zuciyarta na Shiga takaici wannan al'amari gashi ba damar tasa Baki tabada kanta dan Haka Tai shiru tana fatan ruqayyat din ta wuce ga hajjo ma datake saurarensu sbd Jin sunan Marshal Dan gskia ba'a Wasa da harkan Marshal ko bayanan ba'a yin abinda akasan bayaso.

Qamshin turensa ne yake tashi a kayan Nan sosai kin tabbata Wanda Naj tace ki dauko ne a dakinta,
Bafa sashensa tace kijeba a dakinta take nufi........

Da sauri ruqayyat tana sauke Kai tace"

A dakinta na dauko wlh
Acan ya kwana shine zanin yake qamshin,
Wlh banje sashensaba a dakin Ma'am na dauko.

Wata irin wuta Naj ta dauke zaune agurin wani zafi na huro Mata tako Ina ta dago ahankali zuciyarta na gaurayuwa da daci ta kalli inda hajjo take taga Bata gurin Dan tunda taji Ana neman tada sallah ta shigewarta Bata tsaya Jin zancenba tunda ga Hanifa.

Rufe ido tayi wani Dan sauki saukinda baida wani amfani na shigarta ganin hajjo bataji me ruqayyat din tafadaba
Taqi waiwayowa ta kalli Hanifa datai Kamar bataji me ruqayyat din taceba duk da ta girgiza matuqa dajin zancen ruqayyat din ta fuske tana cewa"

Wuce kije aikin gabanki kardai ki kuskura Koda aike kije sashensaba batareda iziniba.

Ruqayyat na barin garin hanifar Bata waiwayoba tayi dakinta tana cewa"

Naj Bari nayi sallah kafin na zauna.

Rufe ido Naj tayi tana dafe Kai cikin tsananin hali,gabaki daya zuciyarta ta cike da damuwa da bacin Rai tana zamanta cikin kwanciyar hankali da rufin asiri kame kame da boye boyen bacin Rai yaganta,wane tashin hankali da damuwa ne wannanΒΏBazata iya cigaba a hakaba kunya da baqin ciki zasu iya illatata kawai zata daukarwa abin mataki wlh kanta bazai iya daukan wannan ba.

Miqewa tayi ta nufa daki a sanyaye itama tayi alwala tayi sallah tana idarwa ta miqe ta nufi gaban madubi sbd abinda ta hango.
Sai alokacin idanuwanta suka gane Mata katin bankin Dake daukeda sunansa JALALUDDEEN ALFA da wayarta a gefe aje.
Wani sabon mamakinsane ya kamata ta kalli takardar dake daukeda pin na katin ta yamutsa fuska tana rintse ido tareda dafe goshinta sbd kanta dake sake daukan ciwon haukatata da komai nasa ke Naman yi,
Me hakan ke nufi daya bar Mata katinsa?
Ya dauki nauyintane da dawainiyarta sbd ya karbi auren kokuma zai karba kuwa matsayinsa Miji yake son nunawa?to ita Bata karba ba Kuma batajin zata iya Dan Haka ta hada katin da paper din ta nufi wardrobe ta bude safebox dinta ta bude ta jefa ciki ta rufe tareda rufe wardrobe din gaba daya tadawo ta zauna da wayarta a hannu tana kunnawa saiga massages suna shigowa kusan duk na Sarah ne saina Abbas Wanda ko budesu bataiba ta gogesu tana Danna Kiran Sarah.
##MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡

09134848107

*_DM 32_*
Da daddaren ta daurewa tayi ta fito sbd nuna taji sauki Dan kada hajjon tacigaba da matsa cewan Bata warkeba Azo Ana tsananta bincikawa.

Suna cin abinci Hannah ta shigo ko dining room din Bata qaraso ba hangosu sunacin abinci tayi zamanta Palo tana jiran su qarasa wasu kayan zaqine takawowa Hanifa tsaraban shopping dataje.

Koda suka Gama a palon suka zauna fira sama sama Banda hajjo data shige qaramin palonta dake hanyar gefen dining room suna magana da Dad Alfa dayazo gaisheta kamar yanda yasaba matuqar Yana gari kullum saiyazo gaisheta.

Ganin wani irin dogon surutu da Hannah ke janyowa Wanda duk rabi na firar Marshal ce Dan nuna irin kusanci da soyayyar datake tsakaninta dashi,
Hanifa sai basar da zancen take sbd Hannah ta barshi Dan Naj dake zaune Amma sai sake jansa takeyi cikin salo da nuna isar matsayinta agurinsa.

Miqewa Naj tayi tabar gurin sbd surutun ya isheta musamman indai akansa ne Bata buqatan ji ta nufi hanyar dakinta tana musu Saida safe tashige.

Tana shigewa Hannah ta saki murmushi tana sauya zancen da cewa"

My in-law kinyi waya da Marshal ya Isa lafiya ko?sbd nakasa samunsa tun dazu,bazan iya kwanciyar hankali ba sainajisa,
Please idan kunyi waya ki sanar dashi inata neman wayarsa, please.

Ya Isa lafiya inshallah saidai Bai Isa qarasawa gidaba bare ya huta harya kunna wayar sai zuwa gobe Inshallah,idan ya Kira Zan sanar Masa Inshallah..Zanje na kwanta ko,Saida safe.
Miqewa tayi ta bar Hannah din a zaune ta nufi dakinta sbd tasan idan ba tashi tayiba Hannah Bata gajiya da magana.
Bin bayanta Hannah tayi da kallo tana Dan yamutsa fuska itama sbd tamafita Jin gundura dasu dukan dannewa kawai takeyi.
Miqewa tayi itama ta fice daga sashen.


Washe gari ba laifi ta tashi lafiya kalau sai Dan qananun abinda baza'a tasaba Dan hakama tana tashi wanka tayi ta shirya cikin riga da skirt na lace me tsada Mara nauyi ta fito sukai breakfast daga Nan sukai Shirin zuwa asibiti scanning din Hanifa da akeyi akai akai.
Koda suka Isa asibiti Dr sa'id na jiransu Dan Haka Basu wani Bata lokaci ba suka baro.
Driver ne yakaisu sbd Hanifa Isma'eel da Marshal sun hanata tuqi itama Naj din sbd Bata Gama warwarewaba hajjo tace itama Kar tayi tuqin.
Driver daga waje yayi parking daidai kofar shiga gidansu Naj din suka fito Kai tsaye suka shige gidansu Naj din kafin driver ya shige da motar can gida.

Tun a hanyar qarasawa cikin gidan suka hadu da Asmau zata fita ta qaraso tana cewa"

Anty Naj Ina wuni?gurinki fa zani yanzu,
Ta kalli Hanifa tana cewa"
Anty Hanifa Ina wuni?
Ya hajjo?

Lafiya kalau Asmau,ya karatu?Ina Umma habiba tana ciki?

Eh.

Wucewa Hanifa tayi Gama ta nufi sashen umma habiban suka gaisa kafin ta wuce sashen ummansu acan ta tadda Dadah zaune tsakar gida tana Shan radio da qatuwar sabuwar butarta a gefe sauraron Shirin hantsi.

Qarasowa tayi tana cewa"

Dadah hantsi akesha Bari nazo na tayaki Sha idan Zaki sanmun goronki.

Kallon Hanifan Dadah tayi tana washe Baki cikin farin cikin ganin cikinta daya fito tace"

Goro Kam Zan sanmiki kici Amma karki zauna Nan iska yayi yawa Zaki kwasa sanyi tafi gurin ummanku nasan dama can kikai gulmar na sanmiki goron ne yasa za'ai zaman Shan hantsi Dani.

Miqa Mata qaramin farin goro tayi tana cewa"

Allah ya nunamun NAJMA tazo tambayar goron Nan ranar nayi kwanan niyar azumin godiya ga Allah.

Najma dake qarasowa taji abinda Dadahn tace ta kame fuska matuqa rashin Jin dadin zancen da qyamarsa na bayyana fili a fuskarta tafasa zama gefen Dadahn ta gaidata kawai ta wuce dakin ummanta
Dadah tabita da fadin"

Duk mugun halinki sai Naga 'yayanki da yardar Allah,
Mara godiyar Allah.

Daka tawa tayi ahankali ta waiwayo zatai magana gabaki daya ranta ba Dadi Anty Amina data fito daga dakinta ta riqo hannunta tana girgiza Mata alamar kada tafada koma menene tayi niyar fada.

Juyawa sukai suka nufa dakin ummansu dake zaune dakinta tana hada khumras masu shegen qamshi da kame jiki Kamar na _*YERWA INCENSE*_ tana jinsu takuma San da Amina Bata Hana Naj din mgn ba zata iya fadar abinda Dadah yau zata Hana uban kowa bacci a gidan sbd zaunarda Dattijo zatayi ta hada masu gurminda zai fatattaki kowa da bacin Rai.
Naj tareda Aminar ne suka shigo kafin Hanifa dake bayansu suka zauna Naj na cewa"

Umma barka da aiki,
Ina wuni?ya gidan?


Amsawa umman tayi batareda ta kalletaba sbd A qule take da ita akan wannan taurin Kan da muguwar zuciyar sbd Hanifa kawai ta kyaleta Dan batason tayi Mata fadan rashin son datake nunawa auren jalal a gaban Hanifa Dan kuwa tasan ko Dadah sbd Hanifan na gidan ta taqaita tata masifar.

Kusada umman Hanifa ta zauna tana daukar kwalban khumrah daya tana shinshinawa tace"

Umma wannan khumrahn wankane ko?
Eh Hanifa,Yaya jiki jikin?
Ankai Miki wainarki Kan lokaci kuwa?

Eh umma naci kafin mufita anjima alalan manja nakeso umma ko gobe da safe ruqayyat Basu iyaba idan sunyi qarfi yake.

Anjima Inshallah Zainab zata kawo Miki yanda kikesonta.

Yawwa Ngd ummana.

Ganin yanda umman fuskarta ba asakeba da alama ranta bace yake akan Naj hakama anty Amina ma Babu wani dogon magana ita kanta Naj din duk tayi wani iri ranta ba Dadi itama kowa sai kame kamen yaqen Dole yake Kuma duk tasan sbd itane ba'ason tada maganar Dan kada asa taji ba Dadi saidai ita Bata damu sosai da duk qin auren da Naj keyina sbd tasan Dole bazata iya karban aure irin wannan lokaci daya ba tunda har bata fitina ko fada akan auren ko ahakan ai ba laifi tasan wata Rana zata Aminta da auren.
Kallon umma da anty Amina tayi cikin nutsuwa da sanyin murya tace"

Umma kuyi hakuri ku sake bawa Naj lokaci Inshallah komai zai daidaita tunda na tabbatarda itama kasa amsar abin ne Kai tsaye yasa takejin bazata iyaba Amma ai komai lokaci yakeso.

Da kallon takaici umma tabi Naj din hakurinta na qarewa tace"

Kinji abin datake fada ko?
Fahimtarki takeso ayi abaki lokaci akan abinda kece aka rufawa asiri da kuwa da Bai aurekinba da yanzu kinanan kina zaman wulaqanci da matsuwa agidan wani,
Shine namiji shine yakeda damar cewa bayaso sbd shine me riqe auren Amma kece kike rainin wayon da kikaga dama sbd sun nuna suna sonki.

Dagowa Naj tayi da idanuwanta dasukai jajir suna neman cikowa da hawaye tace"

Umma.....

Katseta anty Amina tayi da cewa"

Naj bakida gskia ko kadan
Kuma wallahi kunya kike bani da wannan dabi'ar Taki sbd banyi tunanin ko Dan su hajjo ba ki nunawa wannan auren tsana haka,
Menene matsalarki?

Kukan baqin cikin datake dannewane tsawon lokaci ya kufce Mata tana cewa"

Wallahi bazan iyaba,
Nakasa,
Shin meyasa da aka tashi taimakon nawaba Amin taimakon da akasan Zan iya dauka,
Zuciyata zafi take,
Ciwo take,radadin hakan nakeji Dan Allah Araba wannan auren koba komai Ni bazan iya da Wanda yakeda wadda yakeso ba.....

Au bayan girman da kike ganin kinmasa yanzu Kuma hadda wadda yakeso tazama dalili kenan?

Sake fashewa tayi da wani kukan tana cewa"

Ni koma menene Dan Allah Araba auren Nan.....

Wani irin salatin Dadah sukaji data shigo tana kallon Najman bakinta na rawa gurin magana saikuma kawai ta fashe da kuka tana cewa"

Innalillahi-wainna ilaihirrajiun
Wace masifar ce zata kunno Kai rayuwarki Najma,
Wace tsanace kikewa wannan auren dako shekara daya baiyiba za'a kidawo zawarci,
Najma Dan Allah ki duba tsufana da mutuncin Dattijo ki hakura ki cirewa ranki masifa ki runguma aurenki....

Irin kukan da Najma da Dadah keyi yasa umman sake Shiga wata mummunar damuwa da baqin ciki ta tashi cikin tsananin fushi tayi Kan Naj din Hanifa da duk hankalinta itama ya tashi ta tashi da sauri ta janye Naj din tana kasa mgna sbd ganin cikin qanqanin lokaci Abu yazama tashin hankali.

Ba shiri Dadah tasa aka Kira Mata Dattijo tun kafin ya qaraso sashen yake jiyo fadan umma da ranta yayi mummunan baci qololuwa dakuma kukan dadah daya Gama daga hankalin kowa.

Anty Amina ce tayi Masa bayanin abin Dake faruwa tana dasa Aya ya kalli Naj cikin tsananin bacin Rai da baqin cikin daya rasa abin dazai Mata
Tana durqushe gefe har lokacin kuka takeyi me qarfi na rashin sanin mafitar abindayake cin ranta.

Kallon umma yayi cikin fushi da bacin Rai me tsanani yace"

Najma dai takai matakinda tafi qarfin umarnina Dan Haka ke dakika haifeta bakifi qarfin umarnin nawaba saiki shirya kayanki dan wallahi tallahi tana dawowa gidan Nan da sunan aurenta ya mutu bazata zaunaba tare zaku bar gidan nan.

Kallonsa umman tayi cikin baqin cikin koyaushe yayanta sukai laifi aurentane yake barazanar rawa,
Ta maida kallonta kan Najma tace"

Kinji ai saikije ki hado kayan naki mubi duniya tunda shine sakamakon dazaki bani.

Dadah cikin kula tace"

Najma Dan Allah ki dubi girman Allah kiyi hkr ki dangana wlh na zubarda makaman yaqina na yarda anmiki ba daidaiba ki dangana ki runguma aurenki wlh gaba Zakiyi farin ciki da yardar Allah.

Cikin fushi Dattijo yace"
Ki daina rarrashinta Dadah wlh ko ta tashi ta fice Kona nema mugun ice nai Mata dukan da bazata iya komawa da qafafuwantaba.
##MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡

09134848107

*_DM 33_*
Janyeta anty Amina da Hanifa sukayi ta suna sake bawa su dattijon da Umma hakuri Dadah kuwa kamata tayi tayi dakinta da ita ta zaunar tana kallonta tace"

Ki dauka dangana 'yar Nan kibi umarnin mahaifinki da mahaifiyarki tunda dai kinsan bazamu zabar Miki mugun abu ba,
Banda abinki Najma kinyi aurenki kina cikin kwanciyar hankali da nutsuwa meyafi hakan,
Dan shekarun da Kika basa waye yasani tunda idan aka kalleku ma sai adauka sa'an babban yayanki ne,
Shin menene illar auren qaninka tunda?
Shin kin manta Nana Khadija ko data aura Manzon Allah ya girmesa da shekarun dasukafi Wanda kikaiwa naki mijin ita datafi daraja ma ko farin ciki da wannan koyin bazakiyiba ki faranta Mana?
Mu idan bakya Yi danmu munada fada da takura to kiyi Dan hajjo da Alfa Mana,ga Hanifa Nan haryanxu Bata ganin laifinki tana bayanki sbd irin qaunar datake miki
Dan Allah kiyi hkr kiyi zamanki gidan aurenki tunda har daga mijin harsu hajjon sun amincew zamanki ba takura sai kinji kin samu nutsuwa da auren.

Haka Dadah ta ringa Bata rarrashi da maganganu sbd ganin fadan ba inda zai kaisu saiga tone tone har Azo abata goma biyar Bata gyaru Dan ita da wannan aure ya mutu gwara aje ahakan tana zaune gurin hajjo indai da auren yafi musu zasui jira har Allah yasa auren yazama Kamar kowanne auren.

A dakin Dadah tayi zamanta saidata nutsu kafin Dadahn da kanta ta rakasu har palon hajjo suka Kuma taruwa suka rarrasheta kafin Dadah ta tafi
Har dare hajjo da hanifa na tarairayarta Dan tasake Haka suka Kwana
Ko Dad Alfa da kansa Saida yakirata suka sake zama da hajjo suka ringa rarrashinta cikin kulawa hartazo tanajin kunyar abin qarshe Dole ta sake Dan ganin yanda duk suketa sake lallabata shiyasa ta sake sosai ta koma bakin aikinta,

Hannah da mum Malika Koda sukaji abindaya faru Dadi Kamar me musamman suka sake maida himma gurin ganin auren Hannah da MARSHAL din ya tabbata,
Duk yanda Hannah taso fadawa marshal din rigimar Bata samu damaba sbd baida lokacinta busy yake sosai gashi yanata tafiye tafiye acan din Dole ta hakura harta samu lokacinda zata fada Masa.

Umma da Dattijo Basu duk da zancen yayi kwanaki sosai Basu daina fushi da itaba sama sama suke amsa gaisuwarta idan tashigo gidan Dadah ce dai take lallabata dataga fushin ba yayi sai anty Amina daketa aikin dawainiya da duk abinda Hanifa keso sbd cikinta daya fito sosai yanzu.

Takoma aikinta gadan gadan sai yamma take dawowa musamman da ayyuka sukai Mata yawa na 'yar rigimar da ake wadda ta tarar Marshal ya fige Abbas daga ALFAs Amma sauran shareholders din Basu yardaba shikuma sbd yafi kowa hannun jari aciki yace hukuncinsa kenan.
Rigimar tasa ayyuka sun Mata yawa sbd dukkanin ayyukan office din president na companyn yadawo office dinta tunda Abbas an dakatar dashi say angama rikicin gashi Marshal din yatafiyarsa saiya dawo Kuma.

Da mamakin wannan qarfin halin nasa take aikin office din kullum sbd ayyukan sun Mata yawa ko yawon meetings yasa har wata Yar rama ta taso mata.
Saidatai wata daya da sati biyu tana fama da ayyuka kafin ayyukan suka Dan daidaita tafara samun kanta har tana dawowa gida da wuri.

Yau tunda tazo office din batai komaiba sbd jiri datake gani tun jiyan tafara jinsa yanayi Yana tafiya.

Dafe kanta tayi tana Dan rufe ido ta bude ahankali ta dago tana kallon Sarah data shigo office din ta bude Baki ahankali tace"

Sarah please bani ruwa me sanyi nasha.

Kallonta Sarah tayi da mamaki tace"

Me sanyi ko me Dan sanyi kadan?

Batareda ta dagoba tace"

Me sanyi sosai.

Da mamakin Sarah takuma kallonta sanin Bata Shan ruwan sanyi zatai mgn saikuma ta fasa ta nufa fridge ta bude ta dauko Mata ruwan roba masu sanyi sosai ta kawo Mata ta miqa Mata.

Karba tayi ta bude Kai tsaye takai bakinta tana Sha Sarah na kallonta da mamaki.

Ajiyar zuciya kadan ta sauke bayan tagama sha ta ajiye sauran ruwan tana cewa"

Sarah zanje gida yanzu kaina na ciwo Ina buqatan hutawa ko zai sake.

Tare suka fito da Sarah din itace take tuqin takaita gida suka nufa cikin gidan tare.

A Palo suka tararda Hanifa zaune tareda anty Amina data kawo Mata sabuwar Awarar da Umma ta Aiko Mata wadda akaiwa sauce din kayan miya dasu carrots da kwai.

Kallo daya Naj tayiwa Awarar taji tana son ci abinda Bata taba yiba shine ko dakinta Bata shigaba ta qaraso gefen Hanifan ta zauna ahankali tana cewa"

Yunwa nakeji sosai har kaina Yana ciwo.
Ta dauka plate tana miqawa Hanifan tana cewa"

Samun zanci.

Zuba Mata Hanifa tayi tana cewa"

Lallai yau 'yar gaban goshin hajjo yunwa takeji tunda ko daki bazaki iya qarasawaba.

Batace kalaba saidataci Awarar a bakinta taji kanta dake sarawa ya daina ta dago ta kalli Hanifan ahankali tace"

Thanks.

Sai alokacin ta kalla anty Amina tana cigaba daci suna gaisawa anty Amina na kallonta dakyau cikin nazari tace"

Naj bakida lafiyane Naga kamar kin fada.

Kallonta Hanifa tayi tana cewa"

Ramar aikice Amma duk da hakan Ni Banga ramarba haske dai Naga tayi sosai kodai bakida jini ne Naj?" Taqarasa fada tana Dan zare ido.

Batareda ta dagoba tace"

Lafiyata kalau stress ne kawai amma zanshiga hutu sbd komai yakoma yanda yake a office din Inshallah.

Saidata qoshi kafin ta qarasa

1 Comments On DEEN MARSHAL
avatar
hindatu-5

3 months ago

Reply

The novel is nice

Please Login or Register in order to submit comment