Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

state mg's na godiya may your pocket never lck azo asiya Kaya hilis karnakoma kauyenmu๐ŸฅบYar shawarmannan karta gagareni๐Ÿคง๐Ÿ˜‚
Henajiku lvs๐Ÿคญ
Meso should chat
08062991549
07046881166
Call 08064532391
Soap:3k, beauty kit:11k,bridal kit 18k
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

Team glowโœ…




***************
Washe gari ki data farka da jiri ta tashi sai Bata damu sosaiba tasan warwarewar da Bata Gama Yi bane Dan Haka breakfast kawai tayi taredasu hajjo Takoma daki tayi kwanciyarta Hanifa kuma tayi gurin umma.

Sai Rana ta farko shima ko yau din hanifa ce ta tadata sbd lokacin sallah daya wuce sosai bayan ta idar Koda Hanifa ke sake tambayarta lafiyarta kalau itama zuwa yanzu tafara jin kamar ba lafiyaba Dan Kamar tanajin komai nata batajinsa daidai ta dago ta kalli Hanifan dake jiran amsarta tasaki wani qaramin numfashi tareda murmushi sbd kada tasa sufara Kiran sunan Dr sa'id hajjo tabi ta damu tace"

Lafiyata kalau dama bana fada Muku zanyi hutuneba kwana biyu shine naketa kokarin ganin nasamu hutun yanda ya kamata,Yaya harkin dawo daga gidan.ยฟ

Ajiyar zuciya Hanifa ta sauke tana cewa"

Nadawo Amma please Naj idan dai kinji akwai abinda yake damunki ki fadamun sbd Kar abin yayi qarfi ok??

Gyada Mata Kai tayi tana kallonta cikin kulawa tace"
Yes madam.

Daughnuts din da anty Amina tabata tazo Mata dashi ta miqa Mata tana cewa"

Ganshinan Bari naje nayi sallar nima.

Karba tayi tana budewa qamshinsa na shigar Mata hanci ta lumshe fararen idanuwanta ahankali tana daukan daya tareda kaiwa bakinta tana fara Ci.

Sai dataci sosai kafin ta fito da sauran ta miqawa ruqayyat a kicin ta aje Kai tsaye ta nufa dakin Hanifa acan suka zauna Yar fira datakeson ta wartsake sbd Dan zazzabin yamma datake ji.

Da daddare suna zaune suna fira a dakin Naj din Dake kwance Kan gado daga ita sai riga da wandon bacci gajeru hankalinta na Kan wayar datakeyi da Sarah data Kira tana sake jin Yaya jikin nata wayar Hanifa tayi ringing tana dubawa taga sunan Marshal akan wayar Kamar yawanci yanda yasaba dai video call ne Dan Haka earphn dake kusa ta dauka tayi connecting sbd kada Naj taji muryarsa ta dauka kirana tana kallonsa Yana gidansa yau ba gurin aikiba cikin kulawa da farin cikin ganinsa tace"

Hi.

Wani irin qayataccen murmushi ya saki Yana kallonta shima sbd yanda ta maidasa baturen gaske ganin rayuwar dayafi sabawa kenan.

Cikin nutsuwa da sauti me dadi yace"

Assalm alaikm.

Qaramar dariya Mara sauti tayi tana kallonsa tace"

W slm,how are...kasa qarawa tayi ganin Naj Dan kallonta da fararen idanuwanta Jin tana wayar da turanci Wanda tasan shi kadaine baturen gidan Wanda kowa ke waya dashi da turancin fiyeda hausarsa.

Basarwa Hanifa tayi tana maida zancen cikin hausa tace"

Yaya aiki?

Ahankali ya bude Baki yace"

Alhmdlh,hw are you and The Baby?
And the other baby next to you?

Satar kallon Naj dake waya har lokacin tayi tana murmushi tace"

Duk lafiyanmu kalau kawai dai the other babyn is not that ok,I mean she's not..kasa qarasawa tayi sbd Naj dake kokarin Gama wayar karta gane maganarta takeyi Dan Haka ta basar da zancen da kallonsa tace"

Duk lafiyanmu kalau sai Dan zazzabin da ba'a rasabane kawai.

Sakamun ita Zan ganta" yafada Kai tsaye Yana aje cup din lemon tea me zafi dayake Sha.

Cire cameran daga front tayi tana maida Masa cameran wayar ta baya
Naj dake kwance akan gado ta bayyana kan screen din iPad dinsa dayake vidcall da ita,kwance take tana waya fuskarta fresh da alama Bata Dade da yin wankan bacciba ya tsayar da idanuwansa Kan fararen cinyoyinta dogaye dake bayyane suna sheqin haske da lafiyan fata da Allah yabata.

Lumshe fararen idanuwansa yayi ahankali Yana jinginarda bayansa jikin kujera ahankali Hanifa tayi Masa sauti da wayar akan Naj ya aje wayar ta miqe ta fice tana cewa Naj din tana zuwa zata dawo.

Bayan fitarta gyara kwanciyar Naj tayi bayan tagama wayar da Sarah ta juyo da idanuwanta kan sauran boiled plantains da Hanifa tabari acikin plate take taji zuciyarta ta motsa ta dauke ido daga kan plate din sbd zuciyarta data fara tashi akan Amai datakeji
Yana kallonta yakumaga abinda ta daukewa kan,
Duk da ta juyarda Kai zuciyarta takasa daina tashin ta sake juyowa tareda tashi zaune ta zuro qafafunta qasa ta miqe ta tako da niyar dauke plate din ta fita dashi saidai tana qarasowa kafin ta dauka wani irin amai me qarfi yataso Mata da gudu ta nufa toilet tana rufe Baki tashige tafara zuba Amai me qarfi.

Rintse idanuwansa dasukai wani iri yayi tareda dauke Kai daga wayar bayan ya kashe ya Nemo no din Hanifan yasake Danna Mata wani Kiran wanda ba video ba Amma ba'a daukabaya saki wani guntun numfashi me Dan zafi tana jefar da wayar gefensa Kan kejera ya lumshe idanuwansa ahankali.

Amai tayi Sosai Wanda ya mugun galabaitar da ita ta sake watso ruwan zafi sosai ta fito ta saka Kaya masu kauri sbd zazzabin daya taso Mata ga mutuwar jiki ta Haye gado tareda shigewa bargo tana rufe idanuwanta.

Baccin rashin lafiya ne ya dauketa Koda Hanifa tashigo daukan wayarta Bata tashetaba ta dauka wayar ta fice sai alokacin taga misscall dinsa ta saka kiransa saidai Bai dagaba Dan Haka itama ta wuce daki Kai tsaye tafara Shirin kwanciya tana gamawa ta kwanta.

Washe gari sosai Naj din ta tashi da zazzabi, hankalin hajjo ya 'dan tashi sbd dama tasan Najma batada lafiya boyewa kawai takeyi sbd duka alamun Bata daidai ya bayyana.

Dr sa'id aka Kira yazo dubata Dan ko abinci daqyar aka samu ta iya ci sai Amai takeyi Wanda duk ya qarar Mata da qarfin jiki.

Koda Dr sa'id ya iso Anty Amina na gidan itama harta shigo duba Naj din Dan Haka itace ta kamota suka fito Palo bayan ta sanyo doguwar hijab akan kayan baccinta.
Zama sukai Dr sa'id ya Dan zubawa Naj din ido Yana yimata kallon tsaf.
Dauke idonsa yayi tareda Ciro paracetamol ya miqawa Hanifa yace"

Inaga Tasha paracetamol sbd wannan Dan zafin zazzabin ya sauka tukuna Dan gskia inaga saitaje asibiti saina dubata acan Dan inason Zan Mata wasu test musan asalin menene yake damunta.

Cikin kulawa hajjo dake kallonta tace"

Babu wani maganin wannan Aman datajeyine?duk qarfinta ya qare,kodai food poison ne yake wahalar da ita?

Eh zai iya yiyuwa hakan ne Amma dai saimun gwadata zamu sani.

Bayan tafiyar Dr sa'id aka kawo Mata abinci taci ko kadan Amma takasa cin komai,
Kallonta Anty Amina tayi tace"

To akwai abinda kikaji Zaki iyacin sai akawo kici ko kadan ne Kisha maganin.

Ahankali tace"

Aban orange drink ma kawai is ok.

Kawo Mata akai Tasha sosai Tasha maganin sai alokacin tasamu damar watsa ruwan zafi tayi salloli kafin ta iyacin white rice da miyar busasshen kifi.

Tana gamawa anty Amina dasu biyun ne kawai suka rage a dakin ta kalleta dakyau hat zuwa yatsin hannayenta dasukai wani irin fresh ta maida kallonta zuwa Kan fuskarta data Dan ciko kadan Kai tsaye cikin mamaki da shakku idanuwanta cikeda kasa boye mamakin tambayar tace"

Naj ciki ne dake?????

Dukan zuciyarta da qarfi maganar tayi harsaida kanta ya Sara ta dago ahankali ta kalli anty Aminan data tsareta da ido a waje tana jiran amsarta ta dauke Kai Yana sauke wani irin numfashi me wahala na gabanta daya dauki faduwa da tambayar sbd Karo na biyu kenan Ana Mata wannan tambayar,Sarah tayi yanzu Kuma Anty Amina.

Girgiza Kai tayi Kai tsaye tace"

Tayaya zakice ciki ajikina Anty Amina.
Cikin fa haihuwa kike mgn,Ina Zan samesa.

Da wani sabon mamakin anty Amina tace"

Kinada Miji kike tambayar Ina Zaki samu Miji duk da dai ansan auren baigama daidaitaba Amma yanayin naki ne da sauye sauyen danaga duk kin samu a Yan kwanakin Nan yasa nayi tunanin hakan sorry.
Duk da hakan kije asibitin gobe Dr yadubaki ciwo Haka batareda kasan menene yake damunka ba Dadi wuya zakiyita Sha.

Gyada Kai tayi ahankali zuciyarta na wani irin daukan nauyi da maganar Anty Aminan ta farko,
Ta Yaya za'a ringa tunanin ciki ajikinta?
Shin ciki zai iya shigartane a mu'amala biyu da akai bama da so ko yardartaba?
Rufe idonta dasuka sauya tayi tana girgiza Kai da cewan bazai yiyuba wannan masiface me girma,
Aa aa Bata fata, Allah ya tsareta daga wannan abun kunyar me girmanda bazata taba iya kallon ko kanta a madubi ba bare wani.

Bayan tafiyar Anty Amina daurewa tayi ta cije tafara nuna tasamu sauki Sosai sbd abar wani maganar zuwa asibitin Dan kuwa da kanta zata samu zuwa asibitin ita kadai saita fara Jin abinda yake damunta.

Haka ta tilastawa kanta dauriyar ciwon Wanda take matuqar jinsa Amma ta daure tana kannewa ta nuna taji sauki Sosai da wannan tasa aka bar zancen zuwanta asibiti har aka kwana biyu anty Amina ma data saka Mata ido Dan ta basar da ita akan zancen kullum tare suke zuwa gidan da Hanifa gurin gyara da ake Mata na zuwan Isma'eel itama wani lokacin takanyi wani lokacin Kuma batayi sbd qamshin su kurkum da bataso.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022๐Ÿ”ฅ_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
Dโ€™aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

09134848107

*_DM 37_*
A gidansu duk wani Abu dazai sake bawa Anty Amina damar sake saka ido akanta tana kokarin kauce Masa
Sbd gabaki dayama ta rasa tunanin Yi abinda dai tasani shine cikin Marshal ajikinta bazai zama gskia ba.

Washe garin ranarda taji abun yafara Mata yawa ta yanke shawaran komawa aiki ranar Isma'eel ya dawo suna zaune Palo tareda hajjo Hanifa na daki tana sake shiryawa ya iso da sallama ya shigo palon bayan ruqayyat taje ta bude Masa kofa ya qaraso fuskarsa daukeda murmushi ya nema gurin ya zauna Yana gaida hajjo cikin tsananin girmamawa
Naj kuwa kallonsa tayi murmushi akan fuskarta tace"

Sannu da dawowa dadyn baby da maman babyn.

Dariya yayi Yana kallonta yace"

Sannu da zaman hutawa Amarya Kuma uwar gidan Marshal,
Hajjo ta daure Miki kina zuba ikonki akan Marshal.

Basarwa tayi tareda sauya zancen da cewa"

Yanzu dauke matarka zakayi ko kunyar hajjo bakwaji.

Satar kallon hajjo dake duba sako a waya yayi Yana maida da kallonsa kanta Yana hadiye dariyarsa Dan kuwa ta shammacesa agaban hajjon yace"

Zan Rama ne kinci bashi Naj.

Murmushi tayi tana maida kallonta kan Hanifa data fito cikin Ado sai daukan ido takeyi sbd fatarta datai kyau Tasha gyaran umma dakuma cikin daya qara Mata kyau sbd ya fito sosai.

Zaunawa tayi tana Masa sannu da isowa daganan suka koma dayar palon hajjo kafin aka gama jere abinci Sukaci abincin dare kafin suka wuce Naj din ta rakasu har mota bayan Isma'eel yaje gurin Dad Alfa ya dade Kuma acan din suna mgna.

Bayan tafiyarsu a hanyarta takomawa sashensu ta hadu da mum Malika da Hannah zasu nufa part din zuwa gurin hajjo
Mum Malika na ganin Naj din ta zuba Mata ido tana Dan bude idanuwanta akanta sosai tana qare Mata kallo a sirrance,
Dan shiga tunani tayi tana sake kallon Naj har Naj din ta iso gabansu cikin nutsuwa tace"

Barka da maraice mum Malika.

Washe Baki mum din tayi tana Dan dawowa daga tunanin data shiga ta kalli Naj din suna qarasawa tace"

Naj Yaya kike?yaya jikin naki kinji sauki kuwa?
Ki daure kije asibiti,idanma bakyason zuwa akwai wani babban likita Dan uwan baban Hannah dake Nan ko Zan kirasa yazo ya dubaki harma da kayan dibar samples na awon idan ya Kama kokuma Hannah ma zata iya kaiki ki gansa.

Da Dan wani yanayi na kame fuska Naj din ta kalli mum din kadan kafin ta dauke Kai batareda ko inda Hannah take ta kallaba tace"

No thank you mum Malika ba buqatan hakan,Dr sa'id ma ya Isa.

Wucewa take kokarin Yi Hannah da tuni Naj din tagama isarta data bar gurin ta daga wayarta tana dorawa a kunne tace"

Hey sweetheart harka qara missing Dina yanzu fa muka Gama waya.

Ko dakatawa Naj bataiba ta wuce sbd Kota kanta zancen baibi ba Dan Haka ko data Isa palon Bata tsayaba ta wuce dakinta Kai tsaye Dan tasan fira suka kawowa hajjo Kamar yanda sukeyi akai akai.

Washe gari Haka ta shirya Takoma aikinta sbd rashin Hanifa ma agidan duk kadaici takeji sbd hajjo ko yaushe karatun littafantane a gabanta.

A office ko dataje kasa samun sukuni da nutsuwa tayi ta ringa zuba Amai Wanda yasa hankalin Sarah tashi Haka dai suka lallaba harta tashi Takoma gida,
Tana Isa gida abinci taci sosai tayi wanka tayi kokari ta zauna Palo sbd Kar hajjo tasan batajin Dadi.

Hakama washe gari a office Bata ganewa komaiba Haka ta jera kwanaki tana zuwa office Amma Babu wani sauki qarshe dai haka taji kamar qamshin office din ne yake sata wannan yanayin Haka tasa Sarah aka kusan sauya Mata komai na office din tasamu Dan saukin abinda take ji Amma duk da hakan gabaki daya tana cikin wani irin yanayi me wahala sbd yawan cin abinci akai akai ga yawan zazzabi da jiri dasuka sakota gaba uwa uba Amai dayafi komai wahalar da ita,
Takasa Kai kanta asibiti sbd tsoro da shakkar Jin wani ciwone ke damunta zuciyarta na cika da wani irin mummunan yanayi idanma tunanin hakan ya shigeta wato na zuwa asibitin.

Sarah duk tabi ta damu akan rashin lafiyan Naj din gashi tana boyewa hajjo sbd Karta damu Dan Haka ta takurata akan Dole suje asibiti kokuma ta sanarda hajjo rashin lafiyan.

Itama al'amarin ya isheta tana buqatan ganin Dr Dan Haka ta yanke shawaran zuwa asibitin,
Daga office batareda sanin kowaba suka nufa asibitin itada Sarah wadda itama tata zuciyar ke harbawa da abinda zasu jiyo sbd zuwa yanzun tagama tabbatarwa kanta cikine da Naj din Wanda tasan akwai tashin hankali idan har hakan ta tabbata agurin Naj,qarin mamakinta Kuma yaushe har hakan yafaru duk da dai ba abin mamaki bane tunda tanada aure Amma auren da mijin Kuma.....

Isowarsu asibitin yasa ta dakatarda tunaninta suka fito Kai tsaye office din Dr sa'id Wanda takira a waya suka nufa.

Tana buga kofar yasan itace Dan Haka ya taso ya bude Yana kallonta yace"

Kafin mu zauna muje a dauka sample dinki ko?

Gyada Masa Kai kawai tayi ahankali suna juyawa zuwa Lab yana sake Mata tambayoyi akan yanayin datakeji tana basa amsa ahankali sbd jikinta dake amace.

Bayan an dibi jininta a lab din suna fitowa daqyar suka Isa office dinsa ta ringa Amai a toilet dinsa daqyar ya tsaya Mata ta dawo ta zauna Sarah na shafa bayanta tana Mata sannu cikin kulawa da tausayawa.

Ruwan roba Dr Sa'id ya dauko daga fridge ya kawo ya miqa Mata Yana Mata sannu cikin kulawa saiga result din ankawo.

Karba yayi Yana budewa ya nufi kujerarsa ya zauna Yana fara karantawa.

Ajiyar zuciya ya sauke ahankali bayan yagama dubawa ya dauki biro yayi signing ahankali ya miqa Mata Yana cewa"

Well kamar dai yanda nayi tunanin ciwon shine kina daukeda juna, You're pregnant Naj.
Yanxu zanmiki scanning sai muga ko wata nawa ne.

Daukewa numfashinta yayi cak sbd wutar jikinta tako Ina data dauke ta zubawa bakinsa dake bayanin ido tana daina fahimtar abinda yake fada.

Da sauri Sarah ta dafata tana shafa bayanta tareda bude Mata ruwan tana kaiwa bakinta cikin kulawa da tsoron yanayinda Naj din tashiga tafara Kiran sunanta tana cewa"

Naj, Naj, Naj are you okay?
Please ki saki numfashinki Mana,
Say something Naj.

Buga bayanta tayi da Dan qarfi sai alokacin numfashinta yadawo da qarfi ta dago ta kalli fuskar Dr sa'id din da idanuwanta dasukai jajir Nan take sbd firgici da tashin hankali Babu tunanin komai sbd kanta da tunaninta dasuka cushe Kai tsaye tace"

Banason sanin ko wata nawa ne ka ciremun cikin.

Wani kallon tsananin mamaki da Dan qaramin firgici Dr sa'id dama Sarah sukai Mata atare yasake kallonta Yana cewa"

Ciki fa nace Miki kinadashi Naj.

Rintse ido tayi wasu irin hawaye na balle Mata tace"

Ka ciremun kawai Dan Allah bana buqatan kowama yasan da cikin Nan.

Ajiyar zuciya ya sauke sbd abinda yakeson fada Mata ba lallai ta fahimtaba ya kalli Sarah da itama shi take kallo tana fatar karya amince din ya maida kallonsa kan Naj din cikin nutsuwa yace"

Kije gida yanzu kina buqatan hutawa tukuna zuwa gobe ko jibi zamu sake mgna sbd Dole saina Miki scanning dinnan kafin wani maganar Amma dai cire cikin shine abinda bazai faruba.

Miqewa tayi Sarah na riqeta ta zame ta fice ahankali result din awon na hannunta ta share hawayenta ta Isa mota ta bude ta shige sai alokacin tasaki wani irin kukan daya daga hankalin Sarah takasa tada motar Kuma batace kalaba sbd karata damu Naj din Dan kuwa ko ita Jin wannan Batu yasa taji hankalinta ya tashi da yanda cikin zai bayyana ga maganar cirewa da Naj din keyi Wanda bazata bartaba gskia saidai suyi fada kowama yaji abinda yake faruwa.

Tada motar tayi suka nufi hanyar gida Naj din ta dauka tissue ta goge fuskarta datai ja sbd kukan datai din
Saikuma zuciyarta dake doka wani irin tsalle.
Suna shigowa layin gida Sarah ta hango sojojin dasuka saka gabanta faduwa itama Dan kuwa da yiyuwar Marshal ne yadawo.

Naj Bata lura dasuba Saida suka Shiga harabar gidan taga motarsa dake quryar rumfar motoci a fili sai sheqi takeyi ta dauke ido sbd gabaki halinda take ciki baya barinta bi takan tunanin komai ta fito ta nufi ciki bayan Sarah ta wuce batareda ta Shiga cikiba itama.

Kai tsaye ta shigo palon ahankali cikin yanayi na son boye halinda take ciki ta qaraso cikin palon ba kowa sai hajjo dake waya hankalinta Kuma duka Yana Kan wayat ta nufi hanyar dakinta takai hannu zata bude taji an rungumota ta bayanta ahankali hannuwansa na sauka Kan takardar dake hannunta har lokacin
Ya sako fuskarsa wuyanta ahankali tareda sakar Mata wani irin numfashin daya sakata juyowa da sauri bugun zuciyarta na tsananta
Idanuwanta suka sauka cikin nasa Ya qaro wani irin haske da fresh na hutun gske da rayuwarsa take ciki ahankali yakai bakinsa kunnenta ganin irin kallon datake Masa zaiyi mgn hawayen idonta suka balle tana sake damqe result din a hannunta.
##MAMUH#



*_ZAFAFA BIYAR 2022๐Ÿ”ฅ_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
Dโ€™aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

09134848107



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On DEEN MARSHAL
avatar
hindatu-5

3 months ago

Reply

The novel is nice

Please Login or Register in order to submit comment